Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abaya.
Ganin Abba yasa ya nufesa Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da kallon sa kana yace.
“Babana daga ina haka kake?”.
Langwaɓar da kai M Jameel yayi tare da sanyaya muryarsa kana yace.
“Abbah daga gidan Ummina nake”.
Numfashi Abbah ya fesar kana ya kalli agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa tare da cewa.
“Babana kalli fa yanzu ƙarfe sha ɗaya da rabi Meyesa baka tsoro ne”.
Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da kallon Abba kana yace.
“To Abba tsoron me Mutum zaiji, duk guduna fa bazan guji ƙaddarata ba haka zalika duk saurina ƙaddarata ta fini sauri, kana duk hamzarina da kuma ɓuyana ƙaddarata tafini sanin inda nake”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Duk da haka bana so Babana, duk inda kake indai ƙarfe sha ɗaya yayi ka kwana awajen, ba wani abin ni na amince ma nasan ba baza kwana alalaceccen waje ba ko kuma inda zai jaza min magana”.
Cike da ladabi ya jinjina kai kana yace.
“Toh Abbana”.
Kansa Abba ya shafa yace.
“Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ka Allah yatsareka da duk kan abinƙi”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Ameen Abbana”.
Kana ya juya ya nufi ɗakinsa.


Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Aysha ce zaune da ƴaƴanta acikin falon su.
Ramadan dake zaune gefen Khausar ya ɗago kai tare da kallon ta kana yace.
“Addah Khausi ke kam kin huta da zuwa makaranta”.
Murmushi Khausar tayi tare da kallon Ramadan kana tace.
“Yanzu zan fara wani ai Ramadan”.
Ya mutse fuska yayi kana ya kalli Mommy dake zaune kan 2sitter yace.
“Mommy na”.
Ahankali Mommy ta ɗago kanta tare da cewa.
“Na'am Ramadan ɗina”.
Langwaɓar da kai yayi tare da marairaice murya kana yace.
“Ayyah Mommy am gobe abarni kar Inje makaranta mana”.
Kallonsa Mommy tayi tare da cewa.
“Toh Meyesa Ramadan?”.
Kai ya Girgiza kana ya marairaice murya tare da cewa.
“Mommy nidai kawai bana son zuwa Makarantar nan”.
Hankalinta ta mayar kansa kana tace.
“A'a Babana ba yadda za'a yi haka ace baka son zuwa makaranta. Ai yanzu ka fara zuwa ma”.
Araunace ya kalli Mommy tare da cewa.
“Dan Allah Mommy Gobe kawai.
Na goben nan dan Allah Mommy na kada Inje Mommy na goben nan kawai kada abarni Inje makaranta kada inje”.
Girgiza Kai Mommy tayi cike da kulawa tace.
“A'a Ramadan ya za'a yi inbarka ba kaje makaranta ba ai bazai yuwu ba dole ne kaje makaranta kam”.
Jan zuciya yayi tare da dafe kuncinsa kana yace.
“Mommy shikenan kin yarda in tafi?”.
Jinjina masa kai tayi tare da cewa.
“Na yarda mana kaje”.
Miƙewa yayi daga wajenta ya koma kusa da Khausar tare da riƙe Hannunta cikin yanayin roƙo ya langwaɓar da kai tare da marairaice murya yace.
“Addah Khausy ki tayani bawa Mommy haƙuri gobe kada Inje makaranta kice tabarni gobe kar Inje makaranta mu zauna da ita bana son zuwa makarantar nan Addah Khausi bana so ki faɗawa Mommy”.
Khausar kuwa Kallonsa ta riƙa yi har ya kai ƙarshe, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da riƙe tafin hannunsa acikin nata kana tace.
“Toh Ramadan tun daga yanzun ka kana primary 3 sannan kace bakason zuwa makaranta Primary mafa yanzu kayi rabin gamawa ai Ramadan ka fara da wuri”.
Araunace Ramadan ya kalleta tare da cewa.
“Yanzu Addah Khausi zaki bari inje”.
Cikin rashin ɗaukar maganarsa da muhimmanci Khausar tace.
“Eh Sosai ma”.


Haiydar dake kwance kan 3sitter ya ɗago kansa tare da kallon Ramadan kana yace.
“Eh dolenka. Dolenka ma kaje”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Mommy dake kallon Ramadan kana yace.
“Allah Mommy Idan aka sakewa Ramadan ma bazai yi karatu ba”.
Tura baki Ramadan yayi tare da sake hannun Khausar ya koma jikin Mommy kana yace.
“Mommy ki faɗa masa ƙoƙarin da nake a hadda ai yasani ko.
Gasa akaje ni nake zuwa mana na ɗaya a sate ɗin mu”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.
“Na sani Ramadan kana ma da kokari kawai dai da kake cewa kar abari kaje gobe abarka ka hutane bai yi ba. Idan ka tuna ma gobe Laraba ne idan kaje gobe jibi Alhamis zaka huta gata Friday shima zaka huta kaji ko Ramadan”.
Girgiza kai yayi still Idanunsa akan Mommy yace.
“Ayyah Mommy ni Banason zuwa ki barni mana”.
Khausar ne ta kallesa cike da mamaki tace.
“Ohh Ni Khausar yau kam naga ikon Allah da nacin yaro”.
Taɓe baki Haiydar yayi tare da cewa.
“Rabu dashi duk zai gama kuma dole gobe sai yaje makaranta”.


Acan Bedroom ɗin Hajiya Bunayya kuwa kwance take akan makeken gadonta daya ji shimfiɗa na alfarma kana kunnenta maƙale da babbar waya ta gyara kwanciyarta tare da cewa.
“Nama gama ɗaukar wannan matakin in Allah ya yarda in dai wannan anyi angama ya wuce Babban shima Insha Allah za asan abinda za'a yi akai”.
Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Lami dariya tayi kana tace.
“Da dai yafimiki in ba Haka ba kina gani ƴaƴan ki zasu zama bayi, dan da zaran sarautar nan ta fita ahannun ku kinyi bankwana da ita ƴaƴan ki kuwa sun zama tamkar ba ƴaƴan Sarauta ba, duk da cewa Masarautar ba wata babba bace ai baka so ya wuce kaba ya fita ahannunka!”.
Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauƙe kana tace.
“Hakane”.
Murmushi Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“Kinga ai Gimbiya Fadeela ta cikin Taraba Aminiya tace duk iya ƙoƙari tanayi dan ganin sarauta ya zauna ahanununta ke kanki kinsani ai ina faɗa miki saboda iya na cinka iya samun abin ka”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Hakane ai ma duk na gama shi in faɗa miki”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe kana tace.
“Ai haka yafi kam kada ki tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa”.
Dariya Hajiya Bunayya ta sheƙe dashi kana tace.
“Kede ki bari zaki sha kallo”.
Hira suka sake taɓawa daga haka Hajiya Bunayya ta katse kiran.




Washe gari.
Da safe baki ɗaya yaran aka shirya su cikin Uniform Bayan Khausar ta gama shirya Ramadan cikin Uniform ɗin sa tamiƙe ta shiga kichen dan ɗauko masa Lunch box ɗin sa.
Ramadan kuwa yana ganin fitan cikin sanɗa ya fice daga sashen nasu zuwa sashen Hajiya Bunayya ya ɓoye.


Khausar kuwa kai tsaye Bedroom ɗin su ta nufa bakinta ɗauke da Sallama Cak ta tsaya ganin Ramadan bai ciki ƙara sawa ciki tayi tare da kiran sunan sa amma shiru toilet da Wadrope ta buɗe still baya ciki.
Cikin sauri ta fito tare da nufar Bedroom ɗin Mommy kana ta kalli Mommy dake zaune gefen gado tace.
“Mommy na gama shirya Ramadan da Raudat kuma ga Raudat amma banga Ramadan ba har munje wajen mota bamu gansa ba”.
Miƙewa Mommy tayi tare da cewa.
“Ikon Allah to ina kuma yashiga?”.
Buɗa hannu Khausar tayi da faɗin.
“Allahu A'alam”.
Falon suka fito tare da duba ko ina amma baya nan.


Kallon Khausar dake leƙa bayan Kushin Mommy tayi kana tace.
“Khausar jeki duba ɗakin Haiydar ko yaje ya ɓuya acan yau, Bansan meke damun Yaron nan ba tun jiya baya so ayi masa batun zuwa makaranta abinda bai taɓa yi ba”.
Taɓe baki Khausar tayi kana tace.
“Iyayi mana Mommy daga anyi masa wasa shikenan ya ɗauka”.
Ta ida maganar tare da fita zuwa ɗakin Haiydar.
Abakin ƙofan ta tsaya tare da ɗan ɗaga sautin Muryanta kana tace.
“Ramadan kafito fa?”.
Shiru ba amsa jin haka yasa ta buɗe ƙofar ɗakin tashiga shiru ba kowa da mamaki take kallon ko ina dake kimtse tsaf har toilet ta ɓude still baya ciki siririn tsaki taja tare da ficewa ta koma sashen Mommy.


Ƙugunta ta riƙe da hannu ɗaya kana ta kalli Mommy dake tsaye tace.
“Mommy ban gansa ba fa”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da faɗin.
“Toh kije ki duba sashen Ummanku ko yaje ya ɓuya acan kinsan itama zata iya ɓoyesa”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana ta juya ta fice.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon zune ta samu Hajiya Bunayya akan 1sittee.
Kallon ta Khausar tayi tare da cewa.
“Ummah Ramadan yazo nan?”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da gyaɗa kai kana tace.
“Eh gashi nan yazo ya ɓuya wai yau baya son zuwa makaranta”.


Ƙwaffa Khausar tayi kana tace.
“Aikuwa dole sai yaje”. ta faɗa tare da wuce Bedroom Kana tace.
“Wallahi Ramadan kafita idona”.
Jin muryan Khausar yasa Ramadan miƙewa tare da hawa can karshen gadon Hajiya Bunayya kana ya ɗaga sautin muryansa tare da cewa.
“Dan Allah Ummah ki hanasu kice yau dai kawai subarni kada Inje makaranta”.


Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da haɗa hannunta biyu waje ɗaya kana tace.
“Dole sai kaje maza ka fito ka tafi nikam kasan bazan hanaka zuwa makaranta ba, Ramadan dole zaka je”.
Dai-dai lokacin Sulaiman ya fito tare da faɗin..
“Ikon Allah yau Ramadan da kanka kake cewa baka son zuwa makaranta duk ƙoƙarin kan nan?”.
Shi dai bai ce komai ba Khausar na ƙoƙarin za gayawa gefen gadon ta riƙo sa yayi saurin ɗirƙa ta ɗaya side ɗin gadon ya fice waje da gudu.


Dafe kai Khausar tayi tare da bin bayansa yana cewa.
Ramadan kazo mu tafi Sulaiman duk sun shiga mota saura kai ka ɗai ake jira”.
Shi kuwa Ramadan sashen Mommy ya nufa da gudu yana shiga ya ɓuya abayan Mommy.
Muryarsa na rawa tamkar wanda ke shirin fashewa da kuka yace.
“Mommy dan Allah kar inje”.
Hararansa Mommy tayi kana tace.
“Sai kaje Meyesa ba kason zuwa Ramadan ka faɗa min dalili”.
Rau-rau da idanunsa yayi kana yace.
“Ni dai bana so bazan jeba Mommy”.
Dai dai nan Khausar ta shigo kansa ta nufa tare da miƙa hannunta da niyyar kamasa tayi saurin damƙe maranta tare da rintse Idanunta kana tace.
“Wayyo Allah na!”.
Cike da kulawa Mommy ta kalleta tare da cewa.
“Yau kuma ciwon cikin ki ko?”.
Kai ta gyaɗa mata cikin sanyi murya ta kalli Ramadan kana tace.
“Ramadan kazo mana kai kaɗai fa ake jira”.
Maƙale kafaɗa yayi dai-dai nan suka jiyo hong ɗin mota cikin sanyin murya Khausar tace.
“Mommy kin jifa shi kaɗai ake jira zasuyi letti fa Allah zaija idan sunje azanesu kinsan, Moddibo ba ruwansa ko yara sawa yake aci ƙaniyarsu!”.
Ta ida magansr tare da miƙa hannu da niyar janyo sa.
Cikin sauri Ramadan ya sake Matsawa baya tare da riƙe ƙafafun Mommy tare da fashewa da kuka kana cikin raunin murya yace.
“Mommy dan Allah kice abarni ni dai yau bana son zuwa makaranta bana so Mommy dan Allah ki barni”.
Mommy kuwa Kallonsa tayi lokaci ɗaya taji jikinta yayi masifar sanyi janye ƙafafunta tayi tare da Kallonsa kana tace.
“Kai Ramadan wai meyesa bakason zuwa makarantar?”.
Cikin kuka sosai yace.
“Ayyah Mommy dan Allah yau ɗin nan kaɗai ki barni kada Inje makaranta nafi so yau In wuni ina kallonki kina kallona”.


Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ramadan kaje yau kaga gobe idan Allah yakai mu Alhamis ne baza kaje makaranta ba zamu wuni agida juma'a ma zamu wuni tare kaga har Asabar ma baza ka jeba”.
Girgiza kai yayi still hawaye na bin Fuskarsa yace.
“Mommy ni dai bana so”.
Miƙewa Khausar tayi tare da kama hannunsa tana jansa shima hannun Mommy ya riƙe yana kuka Khausar na jansa yana jan Mommy da ƙar ta fincike sa suka fita kana ta sanya shi amota tana kallon Haiydar dake hararan Ramadan tace.
“Gashi ku tafi”.
Kana ta juya ta koma ci.
Da yake shi Haiydar haddan safe suke zuwa na maza.


Kusa da Mommy ta zauna tare da riƙe mararta tana yarfe hannunta kana ta runtse Idanunta tare da faɗin.
“Wayyo Cikina ciwo Mommy!”.
Mommy kuwa jikinta ne yayi sanyi kallon Khausar dake riƙe da marar ta tayi tare da cewa.
“Ke tashi kijeki ɗauko min Yarona, bana so yau abar minshi kada yaje makarantar nan, tunda tun jiya da daddare yake Matsawa kada abarshi yaje nima raina baya so kawai abarshi ya dawo yafi min tashi ki ɗauko min ɗana”.
Ahankali Khausar ta ɗago tare da kallon Mommy kana cikin sanyin murya tace.
“Ayyah Mommy cikina ya kama bazan iya ba kuma Mommy meyesa zaki biye mishi?”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da cewa.
“Khausar naji kawai bana so ya tafi ɗauko min shi”.
Dai-dai lokacin kuma suka ji Girinirin alamun an rufe gate Kallon Mommy Khausar tayi kana tace.
“Toh Mommy kin jin anrufe gate sun tafi”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da lumshe Idanunta kana tace.
“Toh shikenan Allah ya tsare Allah ya dawo dashi lafiya”.
Khausar kuwa Ameen tace tare da kwanciya akan 3sitter still Hannunta na dafe saman maranta.


Kallonta Mommy tayi cike da kulawa tace.
“Yau kuma cikin ki yau nawa ga wata ne?”.
Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta tare da cewa.
“Yau Sha biyar Mommy”.
Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“To aima kusan saura kwana huɗuma Period ɗinki yazo date ɗin da saura?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da matsa saman maranta kana tace.
“Eh Mommy haka dama yake min kafin kwanakin su cika yana min yawan ciwon ciki”.
Numfashi Mommy ta fesar kana tace.
“Allah dai ya sawwaƙa kije ki haɗa ruwan zafi da zuma kisha”.
Ahankali Khausar ta motsa laɓɓanta tare da faɗin.
“Toh”.
Kana ta yunƙura zata tashi tayi saurin komawa saboda yanda cikin ya murɗa.


Ganin haka yasa Mommy ta miƙe tare da zuba mata Zuma da ruwan zafi akofi ta kawo mata amsa tayi tasha tare da gyara kwanciyar ta akan kujeran tana jin ciwon na sauƙa ahankali Mommy kuwa zaman ta ta gyara akan kujeran tare da lumshe Idanunta...


Acan mota kuwa bayan sun isa bakin makarantar Amina dake baya ta kalli Driver tare da cewa.
“Malam Habu ka sauƙe su ba sai mun shiga cikin gate ba sai ka wuce ka kaini unguwar Waziri gidansu Samira Sani”.
Anutse Malam Habu ya juya ya kalleta kana yace.
“In dai shigar dasu kinga Yara ne ba zasu iya tsallaka wa daga kan titin nan ba bare yanda motoci suke wucewa”.
Wani kallon ta watsa masa tare da cewa.
“Yau suka fara zuwa makarantar kuma ga Haiydar ai zai riƙe su”.
Kai Malam Habu ya gyaɗa tare da sauƙe su kana yaja motar ya tafi.
Haiydar kuwa juyawa yayi tare da ɗaukar Raudat kana ya juya da nufin zai riƙe hannun Ramadan kawai ya hangosa Atsakiyar titin Aminu kuwa tuni ya tsallaka.
Kamar daga sama wata baƙar mota jeep ta taho aguje.
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu Haiydar yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Ramadannnn”.
Motar kuwa da mugun gudu tazo tare da nufar kan Ramadan...!




*Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k ne 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*


*
Isrnett. Gaban motar ne ya bugi Ramadan, kamar gilmawar walƙiya ya faɗi agefen kwaltan.
Akuma dai-dai lokacin motar Moddibo da M Jameel ya tsaya awajen cikin sauri M Jameel ya buɗe motar tare da fita yana cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”. kana ya nufi inda Ramadan ke kwance.
Moddibo kuwa kansa ya dafe tare da rintse idanunsa.
Akuma dai-dai lokacin Malam Isa,Malam Ahmad da malam Sa'id suka ƙara so Kasancewar lokacin ne Malamai suka fara zuwa wasu ma ko Parking basuyi ba.
Motar daya bige Ramadan kuwa ko tsayawa bai yiba ya ɗiba aguje.
Aminu kuwa cikin tsoro da tashin hankali ya juya tare da kallon Ramadan dake kwance yayin da M Jameel ke tsugunne kansa zuwa lokacin tuni Ramadan ya suma ɗagosa M Jameel yayi tare da ɗan buga kuncinsa yana cewa.
“Ramadan! Ramadan!!”.
Amma ko motsa wa baiyi ba alamar babu nunfashi atare dashi.
Cikin sauri Malam Arɗo ya fito daga cikin makaranta kasancewar ɗaya daga cikin Malaman yashiga ya sanar masa an samu hatsari awaje.
Moddibo kuwa cikin sauri yayi wa motar key tare da ƙoƙarin bin bayansu ganin basu da niyyar tsayawa yana ƙoƙarin gilmawa M Jameel ya ɗaga masa hannu tare da faɗin.
“A.J ka tsaya mu ɗauke sa mu kaisa asibiti”.
Jin haka yasa Moddibo fasa bin bayan motar kana ya tsirawa bayan motar Ido ya tsaida ganinsa kan number burki ya taka.
M Jameel kuwa cikin sauri ya ɗauko Ramadan ya sanya shi cikin motar ya tada suka nufi asibiti, Malam Arɗo kuma motar Malam Isa suka shiga tare da kallon sauran Malaman dake tsaye kana yace.
“Malam Isma'il ku shiga ciki”.
Kana Malam Isa yaja motar suka tafi.


Haiydar kuwa har zuwa yanzu ya kasa buɗe Idanunsa saboda tsananin tsoro da tashin hankali ji yake yana buɗe idanunsa zai ga ƙwaƙwalwar Ramadan abaje akan kwalta hakan yasa ya runtse Idanunsa kana ya sanya hannunsa duka biyu ya dafe kansa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Raudat kuwa kuka take tamkar ranta zai fita yayin da take yarfe hannunta tare da bubbuga ƙafarta tana cewa.
“Wayyo Ramadan ina za ku kaisa Meyesa mesa Wayyo Ramadan ɗina!”.
Malam Isma'il ne ya ƙara so kusa da Haiydar tare da riƙe hannunsa ganin yanda jikinsa ke rawa kana yace.
“Haiydar buɗe idon ka”.
Girgiza kai Haiydar yayi still cikin Muryan kuka yace.
“A'a tsoro nakeji in buɗe ido na inga ƙwaƙwalwan Ramadan akan kwalta”.
Girgiza kai Malam Isma'il yayi tare da cewa.
“Babu komai babu abinda ya sameshi beji ciwo ba motar ce ta bigesa ya koma gefe amma bata bi ta kansa ba!”.


A hankali ya buɗe Idanunsa da sauri kuma ya sake ware su ganin babu kowa sannan Ramadan ma baya nan cikin rawan murya ya kalli malam Isma'il tare da cewa.
“Ina Ramadan ɗin?”.
Kallon titin Malam Isma'il yayi tare da faɗin.
“Malam Jameel da Moddibo sun tafi kaishi asibiti sannan Malam Arɗo yabi bayansu yanzu kutafi cikin makaranta ka kwantar da hankalinka kaji?”.


Girgiza kai Haiydar yayi yace.
“Ya za'ayi kace in kwantar da hankalina kansa yafashe ko?
ya karye ko? Ko dai ya mutu ne?.
Cikin sa ya fashe ko? Kan kare sa akayi akwalta ko!?”.
Duk alokaci ɗaya ya jero masa tambayar.


Girgiza kai Malam Isma'il yayi kana yace.
“Wallahi babu abinda ya sameshi kawai dai tsoro ne idan mutum bai taɓa accident ba dole tsoro zai sa ya suma kaje kashiga cikin makarantar maza kushiga ciki”.
Dai-dai lokacin kuma ɗalibai suka fara zuwa cikin rarrashi Malam Isma'il yace.
“Ku shiga ciki”.
Raudat kuwa kuka ta riƙa yi tana yarfe hannu tsugunna wa Malam Isma'il yayi ya ɗauketa suka shiga cikin makarantar kana ya shiga bawa Haiydar ƙarfin guiwa.


Acan ɓangaren su M Jameel kuwa suna isa Hospital ɗin aka karɓi Ramadan tare da kaisa Emergency Room.
Atake aka fara bashi temakon Gaggawa kasancewar akwai ƙwararrun Likitoci cikin ikon Allah beji wani rauni ba sai karaya daya samu aƙafarsa na hagu.
Cikin mintunan da baza su gaza talatin ba ya farfaɗo tare da fashewa da kuka kana ya buɗe Idanunsa tare da cewa.
“Wayyo ƙafata Addah Khausi Ƙafata, Wayyo Addah Khausi Ƙafata”.
Ahankali Moddibo dake gefensa ya matsa tare da riƙe hannunsa kana yace.
“Sorry Ramadan kayi haƙuri kayi shiru kaji”.
Cikin kuka sosai Ramadan ya kallesa tare da cewa.
“Mommy na Malam akaini wajen Addah Khausi.
Ina Addah Khausi na Ƙafata ciwo yake min zafi?”.
Ya ida maganar yana jujjuya kai yayin da gaba ɗaya zufa ya wanke masa ilahirin jikinsa Musamman saman goshin sa amma babu hawaye a Idanunsa yayinda ƙafansa ya sake kamar roba ya langwaɓe.
Cike da rarrashi da kuma tausayawa Moddibo yace.
“Kayi haƙuri zai daina insha Allah”.
M Jameel kuwa magunguna da abubuwan da za'ayi ɗauri Dr ya rubuta masa kana ya ya fice tsaye ya samu malam Arɗo maƙale da waya akunnen da alama da Lamiɗo yake magana.


Cikin yanayin jimami ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.
“Wallahi kuwa akwai yaron wajenka da mota ta ɗan kuskuresa yanzu haka ma muna asibiti”.
M Jameel ne ya gyara tsayuwar sa tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya lumshe idanunsa.
Cikin sauri Malam Arɗo yace.
“A'a ka kwantar da hankalin ka Mai Martaba baiji wani ciwo ba.
Dan Allah dan Annabi ka kwantar da hankalin ka”.
Ganin Malam Arɗo ya katse kiran yasa M Jameel cewa.
“Malam wai batun ɗauri ne ƙafarsa ta karye to yanzu ance za'a yi masa ɗauri”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi kana suka fita da M Jameel.


A can Gidan Lamiɗo kuwa tun bayan tafiyarsu Ramadan Makaranta Mommy ta kasa miƙewa taje ta gyara ɗakin mijin nata.
Duk da kuwa cewa itace da girki baki ɗaya jikinta Asanyaye yake bata da wani kuzarin kirki yayin da Khausar ke kwance gefenta har zuwa lokacin hannunta na dafe da maranta.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta yunƙura da niyyar miƙewa dai-dai lokacin Lamiɗo ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.


Yana shiga idanunsa akan Mommy tare da cewa.
“Aysha!, Aysha”.
Cikin sanyin murya da mutuwar jiki Mommy tace.
“Na'am”.
Sai da yayi ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa tare da cewa.
“Zo muje ki rakani?”.
Kallon Mamaki Mommy tayi masa tare da faɗin.
“Ina zamu je?”.
ƙasa yayi da kansa kana yace.
“Ke kam zoki rakani wani waje mana”.


Atake zuciyarta ya tsinke ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi kana tace.
“Rakiya kuma ina kuma zamuje. Mai Martaba ka faɗa min?”.
Ta ƙara sa maganar tare da kallon ƙwayar idanunsa da take iya hango tsantsar tashin hankali da damuwa.
Cikin rawan murya tace.
“Meyesa mu Ramadan”.
Jin abinda tace yasa Khausar dake kwance tayi saurin miƙewa Atake Idanunta suka cika da ruwan hawaye lokaci ɗaya tsoro ya rufeta!.


Cikin dakiya Lamiɗo yace.
“Babu Abinda Ya samu Ramadan ke kam zoki rakani”.
Cikin yanayin sadaukar wa Mommy ta kallesa kana tace.
“Dan Allah ka faɗa min Meya samu Ramadan ɗina!”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Kizo mu tafi mana”.
Miƙewa Khausar tayi cikin rawan murya dan tuni hawaye suka wanke mata fuska kana tace.
“Dan Allah Abba inzo mu tafi”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh”.
Cikin sauri ta sanya dogon hijabinta dake fitar da sanyayyan ƙamshin ta fita, shima Lamiɗo fita yayi sashen Hajiya Bunayya ya nufa yana kirata kasancewar shi kansa be san waya samu hatsari acikin ƴaƴan nasa ba Haiydar, Aminu, ko Ramadan.


Mota suka shiga Khausar na gaba Lamiɗo Gimbiya Bunayya da Mommy suna baya.
Lokaci ɗaya hankalin Mommy ya sake tashi ganin sun nufi hanyar asibiti cikin tsanananin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n dan Allah Mai Martaba ka faɗa min me yasamu Ramadan ɗina?”.
Girgiza kai yayi tare da kallonta kana yace.
“Nima kaina ban sani ba Aysha babu yanda muka iya da hukuncin Ubangiji”.
Hajiya Bunayya kuwa ƙasa tayi da kanta cikin tsananin farin ciki da jin daɗi ta saki murmushi aranta tace Alhamdulillah burina ya cika in. Allah ya yarda yau ankawar min da Haiydar da Ramadan na huta dole inƙara musu kuɗi me tsoka yanda zasuji farin ciki na kawar min da ƴaƴa biyu maza ɗin nan shikenan Mai martaba bashida wani ɗa Namiji sai Aminu dole Aminuna shi zai gaji sarauta.


Ahankali ta ɗago kanta Idanunta cike taf da ruwan hawaye ta kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n. Mai martaba mai yafaru?”.
Cikin yanayin damuwa yace.
“Ni kaina ban sani ba ance min dai ɗana Namiji ne amma ban sani ba Aminu ne...”.
Aruɗe Hajiya Bunayya tasa hannu ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ɗaya-ɗayan nawa”.
A hankali ya fesar da iska daga bakinsa kana yace.
“Kuma ban sani ba ko Haiydar, ko Ramadan ne ban sani ba sai mun shiga”.
Mommy kuwa lumshe Idanunta tayi tare da faɗin.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan min ha”_.
Suna isa suka fito bayan Driver Yayi parking Malam Arɗo na ganin Lamiɗo yayi saurin miƙewa tare da isa inda suke kana yace.
“Sannunku da zuwa Mai Martaba”.
Khausar kuwa tun da suka fito take kuka baki ɗaya jikinta ya gama bata Ramadan ne kuma ya rasune.


Batare da Lamiɗo ya amsa Barka da zuwan da yake masa ba yace.
“Acikin ƴaƴana waye ne yasamu hatsarin?”.
Malam Arɗo ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Ƙaramin ne”.
Ƙasa daure wa Khausar tayi kuka ta fashe dashi tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Mommy Ramadan ne,
sai da yace kada yaje makaranta yau kawai abarshi kada yaje kamar yasan me zai faru dashi na nace dole na muka turashi”.
Mommy kuwa kasa daure wa tayi hawaye masu zafi suka shiga zubo mata.


Dai dai lokacin M Jameel ya dawo daga sayo magungunan a Pharmacy dake cikin Hospital ɗin.
Kallon Malam Arɗo Lamiɗo yayi kana yace.
“Ku kaimu ciki”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare dayi musu Jagora kasancewar Mai matarba ne da iyalansa yasa aka barsu suka shiga.


Suna Shiga idanun Khausar ya sauƙa akan Moddibo dake Rungumeta da Ramadan yana lallashinsa.
Ramadan na kallonta ya fashe da sabon kuka tare da cewa.
“Adda Khausi ƙafata Addah Khausi zoki riƙe min ƙafata”.
Kallonsa ya mayar kan Mommy tare da cewa.
“Mommy ancire min ƙafata ko? Bana jinta a jikina”.
Sai kuma ya kalli Lamiɗo daya zuba masa Idanu cikin matsanancin kuka yace.
“Abbah Ƙafata, Ƙafata”.
Kallonsa ya mayar kan Hajiya Bunayya ya langwaɓar da kai amma baice komai ba.


Hajiya Bunayya kuwa kallon Moddibo tayi jikinta na tsuma tace.
“Ina Haiydar kadde shi yana mutuware?, Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ido Moddibo ya zuba mata tare da tsaida idanunsa acikin nata abinda ba ɗabi'arsa bace ba kuma al'adarsa bace haɗa ido da mutum amma haka nan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akan matar yana kuma nazartan ta.
Cikin yanayin ɓacin rai M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.
“Haba Hajiya wannan wani irin kalma ne ya za ayi kice yana mutuware?”.
Hannu tasa tare da share hawayen fuskarta kana tace.
“To ina yake? Ina Haiydar Allah sarki babban ɗan mu wanda zai gaji Mahaifinsa a sarauta Wayyo Haiydar”.


Malam Arɗo da shigowarsa kenan ya kalleta tare da cewa.
“Haiydar na nan lafiya yana makaranta yana karatu kana suna cikin kulawa!”.
Da sauri Ta haɗiye wani abu mai masifar

Please Login or Register in order to submit comment