Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin shi zaki na rinƙa aiki ba???. Kallon ta Ummu tayi ,duk da ranta da yake a dagule ,amma ganin yanda jikin mama Asabe ke rawa na tsoron Omar Farouk ya sa Abun ka ga mai fara'a bata san lokacin da ta ƙwashe mawa Asabe da Dariya ba...! La'ilah ha'ilallahu Ummu Ni zaki jefa a matsala ,ki taimake Ni ki koma ,kar Amin korar kare ace na fara ja da maganan Yallaɓao Farouk . Ganin yanda Asabe ta gama ruɗewa yasa Ummu saurin cewa " Mama Asabe ki kwantar da hankali n ki kibar Tsoro . Ta yaya Ummu? Na bar tsoro fa kika ce.?.


Eh mana .! Shi yasan na dawo nan shi ya barni . Hummmm Har naji iskar rahma ,shine kike cinye mun abincin .? Haba mama Mama ai wannan ma yayi mana yawa jubi yawan sa fa??. Ummu tayi maganan tana ɗaga Ƙwanon Jaloap rice ɗin . Amma sanin kan ki ne ina da ci sosai . Sa Dariya Ummu tayi tana cewa "Ƙwarai kuwa Mama Asabe na sani ,kefa har cikin Dare tashi kike yi kina cin Abinci ... Dariya Asabe tayi tana cewa ":Shakiyiya maza ki ci , sai ki ƙwanta kiyi barci , Don har yanzu ana can ana kai ruwa Rana da Wancen fitinanniyar Beenerfa ɗin ....Tana ta rigima su Hjy Salma na aikin rarrashi ,don haka ki ƙwanta yau kar ki fito sam ,sai zuwa gobe ,nasan komai ya mutasa . Gyaɗa kai Ummu tayi tana yin shiru kaman ba itace mai wannan barkwancin ba?.

***

A washe gari , wuraren ƙarfe biyu na rana , gidan sai kaye² ake yi ,kowa ka ganshi yana a bakin aikin sa , Ko ba'a faɗa maka ba ,kai kasan an yi babban baƙuwa . Ɓangaren Ummu dake can Part ɗin su tana zaune a dakin su , Asabe ta shigo ranta a dagule , kallon tausayi tabi Ummu dashi kamin tace " Ummu taho muje ki tayani Aiki a part din Hajiya Salma ,munyi Baki yau ... Murmusawa Ummu tayi a sanyaye ta bi bayan Asabe zuwa Falon . Wani irin babban Dirning room suka shiga tare da Asabe ,inda ta hango Hajiya Salma , Mom Zeena gyefen ta Beenerfa , sai Farouk da idanun sa ke akan Wayar hannun sa , Gyefen Mom Salma kuma Nurein ne da gaba ɗaya hankalin sa ke akan hanyar da Su Ummu ke shigo ita da Asabe....!

Alamun miƙewa Zaiyi Mom Salma tayi saurin cewa " Ina kuma zaka je , Zauna mana.! Murmushi yayi idanun sa na akan Ummu dake ƙariko cikin sanyin Murya tace " Barka da Rana ." Brk Ummu yau baki taho da Safe ba , barci ne kika yi??. Mom Salma tayi maganan cike da sokana...bayan ita babu wanda ya tanka , sai Nurein dake murmushi yana kallon Ummu ... Sunkuyar da kan ta tayi ƙasa don bata Son haɗa ido da su duka , Asabe ne tace " Umma fara srving ɗin kowa .... A hankali Ummu ta matsa tana kai hannun ta tare da Fara Buɗe plstic Bowl ɗin tana fara aje Plate a gaban Binafa don tafi jin tsoron fitinan ta .... Fatan Irish ne da kifi ta fara zuba mata , tana aje mata ruwa da lemu a gyefen ta....Haushi ne ya kama Beenerfa ,wanda kamin Ummu tayi Aune gani tayi Beenerfa ta ɗauki Plate ɗin faten Irish din tana yaɓo mata a jikin ta duka har Plate din ....Cikin Sauri Ummu tayi baya tare da yin narai narai da ido ƙwallah na ciko idanun ta ,cike da sanyin Muryar ta tace " Beenerfa What's This? Me nayi miki???. Uban ki kikayi mata.! Cewan Mom Zeena tana yarfe hannu na bala'i .
Miƙewa Nurein yayi yana nufo inda Ummu ke tsaye....!M²T
MAMAN TEDDY COLLECTION
Dealers in All kind of Supplements natural herbal with Zero chemical Reactions such As: Breast Elargement ,Hips elargement , slimming capsules ,body Whitening capsule and more...;
Contact us via this number 08081202932 M²T come 1 come All🕊️
*Littafin nan na kudi ne , Regular group ₦300... VIP group₦500... Special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932 ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biya Ni ba Don ALLAH*

M
Hannu Nurein yasa yana riƙo Hannun Ummu tare da dafa ta yana shirin yin magana ne Mom Zeena ta daka masa tsawa cikin Muryar tijara ta ke faɗin " Nurein Meye kake yi haka? Okay dama maganan da maganan da yazo mun a kan ka gaskiya ce kenan?. Mom... Don Allah ki fahimce Ni , Niiii...Ya isa babu abun da zaka faɗa mun ,sai dai umarni ɗaya da zan baka shine kayi gaggawar cire yarinyar nan a zuciyar ka , Don ba zan lamunta wannan shashancin ba...
Idanun Ummu ne suka karkaɗa , cikin sauri ta janye hannun ta daga na Nurein da ya riƙe mata , cikin Sanyin Muryar ta ta kalle su duka kamin a sanyaye tace " Kuyi haƙuri ... Eyyeee..! Lallai wannan yarinya ta samu wuri ,ji idon ta ƙyar³ a cikin idanun mu ,babu alaman shakka ko tsoron mu ,wai muyi haƙuri ....Waye Uban ki meye sana'ar shi ? Kuma sannan Ke a wani matakin ilimi kike da har kike ƙoƙarin haɗa kafaɗa da Ɗana wanda yake da Masters degree ....Nawa Uban ki ya tara??. Pls Mom Stop.!!! Nurein Yayi maganan cike da jin Zafin Maganganun Mom Zeenatu akan Ummun , Wanda Beenerfa da daɗi ya gama cikata , tsayawa tayi tana bin Ummu da wani irin kallo na sama da ƙasa zuciyar ta fari ƙal". Cike da rashin Karsashi Mom Salma ta kalli Hajiya Zeena tana cewa " Abi a hankali Hajiya Zeena komai zai....A'a Hajiya Salma magana ce ta gaskiya , Sam ba zan amince yaro na ya Auri Yar matsiyatan talaka ba...Ai Auren ƙwarya tabi ƙwarya muke yi ...ina mu ina talaka...!

Kamin wani ya kuma magana ne Omar Farouk ya miƙe tare da aje spoon din yana cewa " Mom Da misalin 11am zamu wuce jaji daga can zamu tafi inda za'a muje domin binciken .... Hummmm sauke numfashi Mom Salma tayi kamin tace " Okay Allah ya kuma tsarewa Son A dawo lafiya ..."

Cike da takon sa na ingarman Soja Ya fara takawa tare da barin dirning room din .....!



Manage🙏N




*Littafin nan na kudi ne Regular group ₦300...VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*


Jikin Ummu ta ko ina Rawa yake yi , Maganan sa taji kaman na mai raɗa ,wanda duk girman wurin babu wanda zai iya jiyo Abun da Taji kunnuwan ta Farouk na faɗa mata sai ita kaɗai , Ina Son Ɗayan Amma ba Wannan ba.! Wuce ta yayi yana barin dirning Room ɗin ,babu wani Damuwa a tare dashi ... Mom Salma ne ta kalli Ummu tana kawar da kan ta ,babu alamun nuni ga tausayawa ko kan cin mutuncin da sukayi mata tace " Asabe tasa ta ku tafi ,idan ina bukatar wani Abu zan saka a kirawo ki ... Cikin Sauri Asabe ta kama hannun Ummu suna barin falon . Kamin Shima Nurein A fusace ya mike yana barin falon ,ransa a matuƙar dagule akan Abun da Mom Zeena tayi mawa Ummun ita da Beener .

***


Wani irin kuka Ummu keyi mai ban tausayi da taɓa zuciya , gaba ɗaya a ƙwana ɗaya zuwa biyu ta gana ficewa daga natsuwar ta ,komai a daburce take yin sa ....cikin dasasheshiyar Murya na wanda yayi kuka kuka kaman ran sa zai fita take cewa " Me nayi masu suke Son Kullum sugan Ni cikin rashin walwala? A wata ɗaya baya izaya ɗaya na sani tun farkon Rayuwa ta ,amma kuma a yanzu ya linku zuwa linkin linki izaya na mutane da ban daban , ba zan iya Ba ya Allah....Zubewa take shirin yi ,don duhuwa ta fara gani kan ta na mata wani irin bugu ,yayin da idanun ta ke rufewa..... Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun Ummu..! Ummu...Shine kalmar Da Mama Asabe tayi tana riƙota jikin ta ba tare da ta bari tayi ƙasan ba... Ɗaukar ta tayi cakkk don Mama Asabe irin matan nan ne gija-gija Wanda Sam duk girman jikin su basa jin nauyin shi, Aƙwai Zafin nama Kaman ba mata ba ,basu da Salɓi ko kaɗan .

A saman Katifan Ɗakin ta ƙwantar da Ummu tare da Saurin ɗaukar Mafici tana mata firfita ,tare da shafa fuskar ta tana kirar sunan Ummu ...kusan mintuna biyar ta ɗauka bata san Inda kan ta yake ba ,sai dai tana iya juyo Muryar Mama Asabe .... Ummul khairy buɗe idanun ki kinji." Ta ƙare maganan tare da ɗan shafa mata ruwa a fuskar ta ,cikin sauri Ummu tajah wani irin ajiyar zuciya ,tare da yin zumbur tana miƙewa daga Zaune ... Pls Beenerfa live me alone pls ,me nayi maki??. Ƙwallah ne ya zubo mawa Mama Asabe cike da jin Bala'in tausayin Ummu ta yi saurin dafa kafaɗan ta tare da cewa " Ummu babu ita anan ,nice Maman ki ,mama Asabe juyo ki kalle Ni ..." A hankali Ummu ta juyo tana ƙara Ware idanun ta akan Fuskar Mama Asabe ,kamin ta saki Kuka a maraice tace " Mama Pls What did I do for them? Me nayi masu ? Me nayi masu Ni Ummu??. Hannu Mama Asabe tasa tana shafa kan Ummu tare da cewa " Kiyi haƙuri Ummu Kinji , Duk ɗan aiki yana fuskantar dama Wannan matsalolin , Walau ya samu soyayya ko kuma ƙiyayyar Yaran gida...Yanzu faɗa mun mene kike ji a tare da ke? Ina yake maki ciwo.?


Hannu Ummu tasa tana ɗago na Mama Asabe tare da ɗaura shi saman ƙirjin ta , Mama nan yake mun zafi , ina tunanin yunwa nake ji ,zanci Abinci ... cike da jin tsoron Saitin bugun zuciyar ta da Ummu ta nuna mata Mama Asabe tace " sha ruwa sai kici abinci , ki goge lissafin kowa a zuciyar ki ,koda kuwa ɓata miki rai akayi Kinji Ummu na?. Gyaɗa kai Ummu tayi tana jan jikin ta daga na Mama Asabe tare da komawa tana ƙwantawa a saman Katifan har kuma Wannan lokacin Zuciyar ta bai daina mata zafin da take ji kaman ana watsa mata ruwan zafi ba...

***


A wannan Rana ne Farouk ya koma barack ɗin su...Abun da yaba Mom Salma Mamaki shine ,kamin ya tafi da yake sanar mata cewa " A dawo da Ummu cikin Part ɗin ta ...empty Room ɗin nan dake passing din na Beenerfa a gyara mata ta koma nan da zama ,kamin ya dawo . Wannan sosai ya jefa Mom Salma cikin tunanin furucin nasa . Wanda wuraren yammaci tasa Mama Asabe ta dawo da Ummu nan Part din nasu , Sam Mom Bata bari Beenerfa ta sani ba , har sai da tazo ƙwanciya , Anan ne tana Rarrashin ta ta faɗa mata . Duk da shakkar Farouk da take yi ,amma sai da tayi masifan ta iya Son ranta da koke koken ta , a cewan ta ita kawai ta tsani Ummu ne . Haka mom tayi ta rarrashin ta har ta samu tayi barci kana ta mike tana kashe mata hasken Bedroom tare da fitowa . Wuce Bedroom Din Ummu da aka bata tayi , tare da shirin nufar Down Stairs na falon ,don Ɗakunan nasu yana Upstairs ne su . Har ta fara Sauka Stairs ɗin sai kuma ta juyo tare da nufar Dakin da Ummu ke ciki .... Tsayawa tayi a jikin ƙofan tana kai hannun ta tare da murɗa Handle door ɗin sai kuma ta saki a hankali tana juyawa tare da nufar Window inda zata iya hango Ummu daga ciki .... A zaune ta hango ta a tsakiyar Gadon tasa Hannun ta biyu ta rafka uban tagumi ,da ganin ta ko ba'a faɗa maka ba , kasan tana kyewar abubuwa da dama ...ciki kuwa har da rashin kulawar Uwa ... Tsayawa Mom Salma tayi kusan Na mintuna Biyar tana a tsaye , ji take kaman taje itama ta rarrashe ta ,ta sata tayi barci sannan ta fito , amma kuma sam zuciyar ta ta kasa yin hakan... Ɗiyata nake ji...Saboda nafi Son Beener ,nafi Son Farin cikin ƴata gaskiya ...' juyawa Tayi tana sakin cotton din Window Glass din tare da barin wurin ....


Itako Ummu a haka ta zauna har kusan 11 na dare , tana tunanin Abubuwa da yawa ,ciki har da Umman ta , Nayi kyewar ki Umma na , Yaushe xan gan ki ? Yaushe zan dawo gida ,mu cigaba da rayuwar mu...Kuka ta fara yi har da jan Su Ajiyar zuciya ita dai kawai burin ta Taga Umma . A haka tana a zaunen ba tare da ta ƙwanta ba ,barci ya fara fizgar ta ....Wanda a hankali taja jikin ta ,tana ƙwantawa .

Ɓangaren Umma itama haka yake ,tun da Ummu ta bar gidan barci yayi mata ƙaura a idanun ta ,kullum bata iya barci sai dai nafila da salloli tana kai kukan ta zuwa ga mahalicci , don ita har a yau bata san meye gaskiyar al'amarin ba .!


***

Da safe ne bayan Mama Asabe sun kammala aikin hada karin kumallo , Beener Mom da Daddy duka suna zaune a dirning Area , mama Asabe cike da Girmamawa kan ta a ƙasa take cewa " Hajiya Bara na taso Ummu , Don yarinya ce bata tashi da wuri ,kullum sai na tashe ta , Don ALLAH Kuyi haƙuri da baku gan ta a bakin aikin ta ba." Shiru Duka suka yi mata ,har beener dake jifan ta da wani irin mugun kallo , don a yanxu har da ita Asaben take jin haushi .
Jin shirun nasu yasa Mama Asabe saurin raɓawa tana wucewa tare da nufar Bedroom din Ummu ta take acan tun da ta farka motsi ta kasa yi....Sai tunani barkatai take yi a kan zaman nata da kuma rayuwar ta na cikin wannan gida .


Murɗo Handle door din da akayi yasata saurin ɗago kan ta tana kallon mai shigowa . Mama Asabe kin tashi?. Allah ya tashe mu Ummu.' me yasa baki watsa ruwa ba ,gaki kuma ga Toilet . Kallon Mama Asabe Ummu tayi idanun ta duk sun kumbura saboda tsaban kuka , a hankali ta furta " Na shiga ciki ,ban san ya ake amfani da koman privacyn bane . Ayya muje na koya miki.


A tare suka shiga Toilet din ,yayin da Mama Asabe ta koya mata abubuwa da dama na amfanin wurin , wanka tayi tana dauro Alwala ,duk da Mama Asabe sai faɗa take yi mata akan Ta makara bata yi sallah ba har rana ya fito . Shiru Ummu tayi bata tankata ba har sai da ta gama sallahn ta kimtsa sannan ta kalli Mama Asabe da suke shirin fitowa zuwa falo tana cewa " To laifin waye Mama Asabe da Banyi sallah ba , kene Mana Tun da ke kika kawoni nan Ɓangaren .
Yanxu dai kina so Kice laifina ne ? Shrkaranki nawa ne?? Kin isa hukunci a shari'ar Musulunci ... A haka suka isa Dirning table ɗin inda Su Daddy Ke zaune a yau su uku ne ,babu Farouk babu Nurein . Momy ina ƙwana .! Daddy Ina ƙwana". Cike da Harka wanda Mama Asabe sakin baki tayi don bata taɓa ganin Daddy cikin wannan yanayin ba ya amsa Ummu da cewa " Morning dear daughter ,Kin tashi lafiya?. Barcin yau yayi yawa, Jiya bakiyi barcin da wuri bane ba?. Gyaɗa kai Ummu tayi tana murmushin nan nata , don ita kun san ta ma'abociya fara'a ce , nan da nan ta watsake tana fara cewa " Eh Daddy , Gashi yanzu na tashi ,dana shiga Privacy na kasa amfani da komai ban iya ba , Sai da Yanzu Mama Asabe ta koya mun , ban yi Sallah da wuri ba , ai Daddy laifin Mama Asabe ne ba laifi na ba , Allah ba zai rubuta mun zunubi ba , tun da itane bata zo da wuri ba .... Dariya Daddy da Mom Salma suka saka , mama Asabe dai shiru tayi itama tana murmushin jin wannan wauta irin na Ummu .... Kamin suyi magana ne Ummu ta juya tana kallon Beenerfa dake ta tuƙuƙi tana cewa ' Beenerfa kin.... Keeee! Shut up.! Kar ki kuskura kimun magana ,im I your Mate?.


Shuru Ummu tayi tare da Girgiza kan ta tana cewa " Sorry . Hannun ta takai tana shirin fara gyara zaman abucucuwan Wurin , Sai taji Muryar Daddy na cewa " Ummu zauna kema a yanxu Farouk ya yan taki yace ba yar aiki bace ba , baki ga Har daki ya baki ba...zauna muyi break tare ....Shiru Momy Salma tayi sam maganan tasa bai mata daɗi ba , kallon Beenerfa tayi wanda itama Daddy take kallo . Ban fahimta ba Daddy wacece ba ƴar Aikin ba? Wannan dai yarinyar?? To ta koma gidan uban ta mana...!


No Beenerfa Ba ƙawar ki bace ,kinga idan kun koma school sai kuna zuwa tare da ita...! Wace wai? Ni zan je da wannan yar talakar School Dad? Allah ya mun tsari , ta tashi ta bar wurin nan ,ko kuma Ni na tashi ....Tsayawa Daddy Yayi yana mamakin ƙiyayyar dake tsakanin Beener da kuma Ummu . Kamin yayi magana ne tuni ta mike tare da barin wurin ...ganin haka yasa Mom Salma Itama miƙewa tana bin Daddy da Ummu da wani iri kallo , Wanda yasa Ummu saurin sada kan ta ƙasa , jikin ta duk yayi sanyi . Barin wurin Momy Salma tayi tana bin bayan Beenerfa ....!



*AISHA MMN TEDDY*O




*Littafin nan na kudi ne Regular group ₦300...VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*


Bin bayan Mom Salma Ummu tayi da kallo ,kamin ta ɗaga ƙafarta tana shirin barin wuri ne taji Muryar Daddy Yana cewa " Ummul khair dawo ki zauna , Ni ai nace muyi break tare ...kuma daga Yau Can Bedroom ɗin da kika ƙwana nan ne ɗakin ki , lokacin da kowa ke a dirning Area kema ki tabbatar kin taho ayi dake kina jina ? . Yayi maganan yana ware idanun shi a kan Ummu wanda ta tsaya tsumi ,wannan fara'ar nata Duk ya ɓace daga fuskar ta a lokaci guda . Gyaɗa masa kai tayi a hankali ,kamin Daddy yace " Good zauna anan ki saki jikin ki kinji , Ai Daddyn Beenerfa shima Daddyn ki ne... Kallon Mama Asabe Ummu tayi kamin ta yi mata ido da ta ci mana zaman me take yi... A hankali Ummu ta ɗauki Fork tana fara cin Talia ,Kun san Abun ka ga Rainon Boko , babu abu mai daɗi da ya wuce indomie sai Spaghetti , wannan yasa a cikin schedule na time table din Kitchen Talia a ko wacce safe ana yin shi da yawa best food din Beenerfa kenan . Daɗi Talian tayi mata ,wannan yasa ta sam mantawa da Daddy dake Wurin , Sambaɗan Abincin ta take ya ,tare da kallon Mama Asabe tana fadin " Mama kin iya girki yayi dadi sosai na Yau .


Ai kullum ma indai abinci na ne yana daɗi , Kedai kawai Kice a yunwa ce kike ...! Murmushi Daddy Yayi yana jinjina kai ,a Zuciyar shi cewa yake " tana da Saurin Sakewa da mutane . Ummu wani Position Kika Zo a school din ku...Cak ta ja ta tsaya ,sai ji kake ƙufulll...ƙuful ƙuful ta ƙware . Don hankalin ta tashi yayi tuno da wannan shine silsilar komai har ƙiyayyar su da Beenerfa . Shiru ta masa ta kasa magana sai kallon sa da take yi ...Ehemm ina jinki kodai na baya ne kika zo?. Yayi maganan cike da sokana . Tuntsirewa da Dariya Ummu tayi har tana kyakyatawa rabon da tayi irin wannan dariyar har ta manta . A'a Daddyn Beenerfa ,Ni nazo 1 position a class din mu Baki daya . Wow' mashaallh yayi kyau , yau idan na fita zan sayo maki kyautar ta ɗaya da kika yi ....Buɗe Baki Ummu tayi cike da yarinta tace " Serious Daddy? Eh mana ai kin yi kokari sosai . Murmushi Ummu tayi tana cewa " Thank you Dad ngd . Murmushi Daddy Yayi yana miƙewa tare da kallon Mama Asabe yana ce mata" Don ALLAH ki tabbatar da Ummu tana cin abinci sosai . Cikin sauri Mama Asabe tace " Inshaallhu .


Daddy sai ka dawo , Allah ya tsare ya kiyaye hanya ,ya dawo kai lafiya yanda ka barmu lafiya. Amin ya Rabb ya furta cike da jin dadin Addu'oi n Ummu a gare shi ....

***


Sojoji ne birjik a ƙame duka suna sauraron Maganan Babban naso wato kanar ne ake fadi da Hausa ko😂 yayin da Captain Omar Farouk ke tsaye a daga gaban su yana fuskantar Kanar Jabir Baban gida ....Sauran kuma yaran sojojin Omar Farouk na daga bayan sa . Bayani ya gama yi mawa Omar kamin ,Farouk ya juya yana kallon Sauran taron sojojin ...Cike da Muryar sa ta matashin Soja mai ji da ƙarfin ƙuruciya ya fara da cewa ". Dajin nan da zamu shiga domin binciken Abun dake kashe da yawa mutanen dake gyegar Wurin ,ciki kuwa har da Sojojin mu da dama sun mutu a sanadiyar wannan bincike akan Dajin . Mu sani a yanzu mun amsa Wannan aiki , tawagata mu zamu shiga Wannan daji ,don musan meye a ciki ,waye abokin hamayyar Al'umma....numfawa yayi kamin yace " The only thing I remembered you is that , gamu a Zamu tafi , amma kuma ba lallai mu dawo duka ba ,ina so kowa yasa hakan a ran sa , Sannan abun da nake tuna maku na biyu shine " Mutuwa a wurin yaƙi wannan wajibi ne ga ko wani Soja ,sunnar yaki kenan . Fatan kowa na tare dani.! Hannun su suka saka suna ƙame masa tare da sara masa tare da cewa" yesss Captain.!

Juyawa yayi yana kallon Fahad tare da cewa " Kowa yaje yayi shiri gobe zamu dauki hanya in Sha Allah . Yana gama faɗin haka ya juya tare da Fahad Suna barin wurin . Can rumfar su ta manyan Sojoji ya nufa yayin da Fahad ke cewa " Omar kai a tunanin ka me yasa Sojojin mu da yawa ke mutuwa a wannan dajin? Shin....Hummmm ban sani ba Fahad ,Amma daga gobe zamu sani , zan kokarin ganin na Ga karshen wannan Makiyin , mai kashe mutane basu ji basu gani ba . Fito dasu Zamuyi a masu hukunci yanda kowa zai shiga taitayin su ,idan ma ɗan ta'adda ne ... Cewan Fahad Yana Kallon Farouk dake bude taswirar Nijeriya yana ci gaba da bincike akan wannan baƙin daji . Wanda yake shirin tunkarar sa babu tsoro .


Kai waye Zai ba Gomnati Wannan mugun ,ai bazasu amshe sa a raye ba ,sai dai a mace ,kai kasan ƙa'idar farauta na indai a jeji ne , ban taɓa ganin mugu na barshi da gomnati ba ...! Shiru Fahad Yayi Yana jinjina kai tare da cewa " Ko mun basu ,shekaru ƙalilan zasu sake su ..yanzu bari naje mu fara shirin mu .


***

Wuraren Karfe Biyu na rana , Mom Salma ne ta fito tare da Beener cikin shigar Alfarma Atampha ce jikin ta mai ratsin Brown da milk , gyefen ta guda Beenerfa ce da shigar ta irin na comrade marasa kirki ,dama ita haka take shigar ta irin na turawan England . Shiga ce tayi shi na kanunun kaya , riga da Wando , tayi rolling da yar karamar mayafi , sai ɗauki tabarau bangajeje Ja tana saka ma fuskar ta ...Tare da dauko irin wannan manyan rigunan masu kama dana sanyi tana daurawa a sama Turkish switter , ƙafarta kuma cikin Takalmi ne mai rufi , sai tashin wani irin ƙamshi take yi ....bakin ta ne ke rawa cike da mmkin ganin wannan sauyi take kallon masu decoration din dirning Area tana cewa " You people what are you doing there?? .

Please Login or Register in order to submit comment