Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

adadi ,ka sakani dariya a lokacin dane cikin kunci ...I really Love you ya Farouk ... Kissing Ɗin Hoton shi tayi tare da ajewa kana ta dauki Hoton ta tana kallo , a hankali ta furta " Beenerfa taho ki koma wurin naki iyayen na asali. Juyawa Tayi tana saka hoton ta a cikin trolly bag din tare da ɗaukar mayafin ta tana saka kafa tare da kallon dakin nata . Daga hannun ta tayi cikin kuka tana cewa " Mom ,dad Farouk byeeeeeeeeeeee.!

Juyawa tayi tana share Hawayen ta tare da barin Falon kasa tana ficewa daga farfajiyar gidan . Kai tsaye moto park ta nufa inda ta shiga buss da zai kaita garin Gombe , don tun a ranan da taji maganan Daddy na ita ba yar su bace ta yi bincike akan nata iyayen ta kuma san inda suke Rayuwa . A moton haya duk ta jigata ƙwarai don bata saba wannan wahalar ba ,ammma kuma babu yanda zata yi kamin su sauka ta gama ficewa hayyacin ta . A haka har Allah ya sauke su a garin Gombe .
**

Shigowa gidan sukayi Familyn duka har da Nurein mom Zeena , ko wannan su fuskar sa ɗauke da fara'a don jikin Ummu Alhmdllh. Farouk ne ya kalli Momy tare da cewa " bari na kirawo Beenerfa yanzu . Okay idan tana barci ne kar ka taso ta . Okay momy Yayi maganan tare da hayewa saman Stairs ɗin falon . Kama hannun Ummu Mom Zeena tayi tana zaunar da ita tare da taba saman goshin ta tana cewa " Babu abun dake Mali ciwo ko??. Gyaɗa mata kai Ummu tayi don ita dai duk bata da walwala a tare da ita . Kin tabbata? Cewan Mom Salma tana kallon Fuskar Ummu wacce tayi kasa da idanun ta . Muryar Omar suka ji yana cewa " Momy na duba ban ga Beenerfa ba . Saurin ɗagowa sukayi mom na dafe kirji kamin tace " Ka duba ko ina mana.! Momy na duba babu Beener a cikin gidan nan ." Wani iri Dauke wuta Duka suka yi kamin Momy ta kalli Daddy tana faɗin sunan sa kai tsaye ,wanda tun da Su Omar suke basu taɓa ji ba , Abdullah Kaine ka gani ko?. Tayi maganan hawaye na fara sauka mata . Dafe kai Farouk yayi yayin da Nurein yace " Mom yanzu ina zata je kenan .? Tsayawa sukayi cirko cirko yayin da Ummu gaban ta ke matsanancin faduwa .

**
A gaban gidan mai adaidaita ya dauke Beenerfa yayin da ta fara sauko da trolly bag din ta , sallamar Mai adaidaita Tayi tana tsayawa ƙurrr tana kallon gidan , wanda ƙofan arziƙi babu , this is my own destination . Kalmar da tayi kenan tare da furta" Alhmdllh . Jan trolly din take Yi ,Kamin Ta fara nufo kofar gidan ne taga Auwalu ya fito yana buƙar Sigari ...Tsayawa yara da manyan layin sukayi suna kallon Beenerfa tare da tambayar wacece ita?. Auwalu ne yasha gaban ta yana cewa " Ke Nan ba inda kika zo bane ba , ko baki ga gidan ba irin naku bane ba ?.

A'a Yallaɓai nan nazo , Umma na ciki?. Wata Umman kuma wurin wa zaki zo a gidan nan ,kalle ki da kalli fatar ki , Banbancin ki da yan Nigeria.... Umma ne ta fito daga gidan nata da mayafi da'alama wani wurin zata tafi ...Kallon Auwalu tayi tana cewa " Yanzu Naira Talatin din magin miyar shine ka ɗauka ka siye Sigari ? To Umma a haƙura da girkin yau ,Ni idan ban sha sigari ba ban jin dadin Rayuwa . Ummmaaa.!

Beener ta kira sunan Umma tana tsayawa tare da bin ta da kallo . Cakk Umma ta tsaya tana yin mawa Beener ƙurrr da ido . Girgiza kai Umma tayi tana saka gyefen mayafin ta tana sharce hawayen daya zubo mata . Nasan dama wannan ranan dole wata rana zai zo . Domun duk abun dake faruwa zuwan Alh Abdullahi Shuwa naji duk abun da ya wakana da Malam Kadarko . Shigo daga ciki . Bin bayan umma Beenerfa tayi jikin ta a sanyaye babu wannan kuzarin nata . Wacece Wannan kuma Umma? A ina kuka samo mana jinin turawa?. Auwalu yayi maganan yana cigaba da buƙar sigarin sa .

Sam umma bata basa Amsa ba , Trolly din Beenerfa ta Amsa suna shigewa daga ciki , a cikin zauren ne Beenerfa ta riƙe Umma gammm don gani take tamkar Soron zauren zai faɗo mata aka . A haka suka shiga tsakar gidan dai dai Malam Kadarko na fitowa daga dakin sa da buta a hannun sa . Wacece Wannan ?. Kallon sa Umma tayi tana kauda kai cike da jin Zafin abubuwan da ya aikata shekaru sha bakwai baya . Abun da ka shuka ne yau ka girbo , baka gane ba ? Ai yar kace Beenerfa da ka musanya a asibiti ,yau Ummu ta koma gidan su itama kuma da kafarta ta dawo nasu gidan. Tari ne ya kwace mawa malam Kadarko kuful³ . Haushi ne ya kama Umma wannan yasa ta kama hannun Beenerfa tana cewa " Shigo daga ciki . A bakin gadon Umma Beenerfa ta zauna tana yin shiru ,kamin ta ji Muryar Umma cikin kuka tana cewa " Ina Son Umma na ,ina Son Shalele na a yau ta bar Ni...! Malam ka cuceni kuma ka cuci kan ka. Saurin miƙewa Beenerfa tayi tana tsugunawa gaban Umma tare da rungume ta tana cewa " Umma kiyi Haƙuri komai bai Baba yayi maki ki yafe masa . Ke Kadarko baya da hali ,kalli Abun da yayi maki Wanda nasan har Abada ba kowani yaro zai yafe mawa iyayen sa da sukayi masa wannan yankar ƙaunar ba . Girgiza kai Beenerfa tayi sai hawaye sharrrrrr³ , Umma Ni na yafe mawa Baba kema ki yafe masa , koba komai shine wanda ya haife Ni ....! Shiru Umma tayi tana nazarin kalaman Beenerfa kamin ta miƙe tana ficewa daga Ɗakin tare da nufar Ɗakin Malam Kadarko wanda ya shige tun ganin Beenerfa da yayi .

***
Ɓangaren Momy da Daddy sun ɗauka Beenerfa tana gidan kaka ne ,wannan yasa Su nufar gidan ,da duk inda suke tunanin zata je amma babu ita , a ƙwana na ɗaya ne Ummu itama ta gudu ,wanda anan ne suka mai da hankalin su wurin nufo Gombe .
Da misalin hantsi wuraren ƙarfe Biyu na yammaci ne Auwalu na Zaune a a dakalin Mudi mai rake yaga fitowar Ummu daga napep . Cikin Sauri ya ƙarisa inda take ,tana kallon sa ta fashe da kuka Ya Auwalu ina Umma na?. Sakin Baki Auwalu yayi kamin yace "Ashe ke shashasha ce Allah yakaiki gaba kin huta da kangin Talauci shine kika sake dawowa cikin fitinan wannan talaucin gidan ?. To an gane ke ba yar su bace ba ,dama Baba ne yayi komai don haka yanzu shawara Ummu ki koma wurin iyayen ki masu kuɗi ,idan kin samu nasan ki da zuciyar rahama don ALLAH kar ki manta dani... Juyawa Ummu tayi tana yin gaba tare da nufar cikin gidan , kan ta tsaye ta kutsa tana kirar Sunan " Umma na.! Umma na .!!

A farfajiyar gidan ta hango su , Umma na tankaɗar Gari , Beenerfa na Wanke wanke...Miƙewa Umma tayi da Sauri , Yayin da Ummu ta nufe ta tana rungume ta jikin ta . Aje Soson Beenerfa tayi tare da nufowa inda Ummu take , A hankali tasa hannun ta tana ɓanɓare Ummu daga jikin Umma kamin tace " Nan ba gidan ku bane ,Gidan mu ne ,ki fita bana Son ƙara ganin ki a cikin gidan nan . Beener Pls Beenerfa ki Yi haƙuri , ni Umma na nake so.! Nima ita nake so. Just Outttt...! Tayi maganan tana fizgar Ummu tare da hankaɗata nan take tayi ƙasa tana faɗi.

Can yafi dacewa dake Ummu ki tafi . Umma tayi maganan tana xubda hawaye , Saurin miƙewa Ummu tayi tana cewa "a'a Umma na ke nake So. Sallamar Momy Salma ne yasa su duka juyawa suna kallon ta . Tsayawa tayi tana bin Beenerfa da kallo wanda itama tana ganin Momyn naya zuciyar ta ya karaya . Bin gidan da Take ciki Beenerfa a yau tayi ,kawai sai Momy ta fashe da kuka , Ware mata hannu tayi wanda da sauri Beenerfa ta faɗa jikin ta tana rungume ta....!


*Littafin THE VIRGIN MAID na kudi ne ... Regular group ₦300... VIP group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932....Ina Kira ga masu ba wasu kudin littafaina suna faɗin wai Ni maman teddy na wakiltasu ,su ɗin Wai wakilai na ne , To Wallahi Ni Maman teddy ban san su ba , Kawai Scammers ne yan damfara su amsan miki kuɗin ki ,daga bisani suyi blocking naki , da yawa a rana fiye da mutane 4 biyar suna zuwa mun akan wannan matsalar sun tura mawa wasu kudaden su since masu wakilai na ne To ƘARYA ne , bana Wakilta kowa a harkar Sayar da littafaina ,Ni nake rubutawa don haka nice mai sayarwa , ga number na da kullum zaku same Ni 08081202932 ko kuma wannan numbern 09061466409 bayan Wannan nombobin ban san kowa ba , Scammers ne . Ga kuma gerangiyar littafan nawa nan a ƙasa , saboda na ƙara Wayar mawa mutane kai akan wa'annan masu damfarar yasani na saki wannan PAGE din Bonus.* *WALIJAAM, YAR WAYE , SIYASATA ,DIJAMA YAR FULANI, GIDAN ƘWARATA , KWARTON MANYA , THE SEXXYY BOSS ,MY LADY BOSS ,ZUMA DA MAƊACI , KAWALIYA ,HABIBI DA'IMAN, BINTOTO, BAFULLATANAN RUGA , SIYASATA , GIDAN KWARATA , ƘWARTAR SAMA , SADAKA YALLA , TAƁARAH , ƳAR AIKI NA GASUNAN LITTAFAINA DA YAWA A SOCIAL MEDIA ,DUKA NIKE SAYAR DA KAYA NA , BA WANDA NA TAƁA WAKILTAWA GA KUMA NUMBER NA 08081202932 BAYAN HAKA KO WAYA AMSA KUDIN KU TO DAMFARA NE ,NI BAN SAN SHI BA BAN KUMA SAN TABA, DON ALLAH ZAKU NA IYA SHARING WANNAN SAƘON DOMUN WANDA AKE DAMFARA SU FARGA SU GANI SU KUMA SANI...MUN GODE...!*https://www.youtube.com/@mamanteddy4123 Subscribe our new YouTube channel pls @ MAMAN TEDDY HAUSA NOVELS AUDIO

DOMUN SAMUN LITTAFAN MMN TEDDY NA SAURARE DA ZARAR MUN ƊAURA MAZA KU YI MANA SUBSCRIBE KAR KU MANTA DA DANNA MANA LIKE MUN GODE....
https://www.youtube.com/@mamanteddy4123

T
Rungume Juna suka yi Beenerfa da Momy ko wannen su na ƙwallah na ƙwaranya daga idanun sa, cikin Sauri Ummu ta nufi Umma tana faɗawa jikin ta ,tare da Fashewa da Kuka , dai dai su Yah Farouk Daddy ya Nurein na shigowa gidan . Ko wannan su ja yayi tsaya zuciyar su a karaye kuma cike da Tausayin junan su . Malam Kadarko ne ya tsaya jiki a sanyaye domin shima fitowar sa kenan daga Ɗakin sa . Kallon sa Hajiya Zeenatu tayi kamin cike da ɓacin Rai ta hau cewa " Yanzu me kayi kenan? Abun da ka shuka yau gashi ka girbe kayan ka , Anya Wa'annan Yaran da kayi masu yankar ƙauna zasu yafe maka kuwa?. Wallahi ka nemi gafarar su ,sannan kuma ka nemi tuba zuwa ga nahalicci ... Kallon Mom Zeena Ummu tayi idanun ta na tsaka da zubo da hawaye ta motsa bakin ta daƙyar wurin cewa " A'a Momy duk Abun da Baba na yayi ,ba kansa bane , Allah ya hukunta dama hakan zata faru , Kuma da sharrin shaiɗan kuyi haƙuri Ku yafe mawa Baba ". Kallon ta Umma tayi tana girgiza kai Ƙurum ,zuciyar ta tafi mata zafi fiye da raɗaɗin hawayen dake sauka mata . Tabbas zan yi rashi kuma zan yi kyewar Ummu , Yarinya mai Hankali tawakalli haƙuri juriya , Amma yana iya hakanan zan baku ɗiyar ku , Daga Kuma ƙarshe Don ALLAH Hajiya Salma , Alh Abdullah Ina Mai Baku haƙuri bisa ga Abun da Malam ya aikata maku akan jinin ku . Umma ta ƙare maganan wasu irin Zafafan Ƙwallah na zubo mata . Malam Kadarko ne ya amshe maganan nata cike da matsanancin nadama da dana sani ,ga kuma kunyar Abun da ya aikata .


Kuyi haƙuri bani da baki ko wata kalmar da ta wuce mun wannan ,duk da na san da wuya ku iya yafe mun . Baba Nice Ƴar ka kayi mawa Hakan , kuma tsakanin Uba da Ɗa babu kalmar yafiya ,Ni yar kace kome kayi mun dai dai ne Baba . Ummu tayi maganan tana Matsawa Kusa da Malam Kadarko da idanun sa suka kaɗa sukayi jajir , Ƙwallah ne ya ciko idanun sa jin furucin Ummu akan sa . Tabbas sai a sannan ya fara jin Abun da Umma take ji na Rabuwa da Ummun ,tabbas zasu yi kyewa ƙwarai kuma sun yi rashi . Gaban sa ta tsaya tana sa hannun ta tare da goge masa ƙwallahn idanun sa kana cikin maida komai ba komai tace " Baba Meye na kuka ,ka bari don ALLAH , Idan Beenerfa kake tunani Daddy Umma na ko Momy duka Ni nasan sun yafe maka .


Gyarar Muryar Da Daddy Yayi ne yasa su ,su duka mai da hankulan su akan sa . Kamin ya ce " Ƙwarai Kuwa Ummu ,an zama Ɗaya komai ya faru na rashin jin daɗi mun yafe , Allah ya yafe mana baki Ɗaya . Amin Ya rabil Alamin , cewan Su duka kamin Momy da Umma su shige Ɗakin Umma , duka har da Hajiya Zeenatu , Farouk Nurein ,Auwalu daddyn Nurein ,Daddy Baba Kadarko a tsakar gidan suka zauna ana shimfida masu tabarma , anan suka zauna kowa nan su na ba ɗan uwan sa haƙurin Abubuwan da ya faru . Kusan ƙarfe Biyar na yammaci Daddy ƴace su fito domin su ɗauki Hanyar komawa Abuja . Gaba Ɗaya Ummu babu walwala duka a tare da ita ,duk da tana san ran dawowar Beenerfa cikin gidan , don sosai taga ta saki jikin ta tun da Momy Tazo tana jikin ta har izuwa yanzu da suka fito domin tafiya . Hannun Beenerfa Momy ta kama dana Ummu ,wanda cikin Sauri Beenerfa ta kalli Momy tana girgiza mata kai No Mom ba Zan bi KU ba , Ina so na zauna da Umma anan nima . Wani irin bugawa Ƙirjin Momy yayi wanda ya sata saurin kallon Beenerfa kamin tace mata Wani Abu ne Farouk yace " Ke Beener taho mu wuce , me zakiyi anan Ɗin ?. Taho .! Ɗago da rinannun idanun ta tayi tana kallon sa ,kamin da sauri ta nufe sa tana faɗa wa jikin sa rungume ta yayi tsam jikin sa , wannan wacce irin musiba ce? Tambayar da yake mawa kan sa kenan ? Kamin yaji Muryar ta tana cewa " Yah Farouk bye. Tana Juyawa da sauri tana shirin wuce Momy , cike da zafin nama Momy Tasa hannu tana riƙo ta . Pls Beener Kar ki son zama damu ,don a yanzu Kinji mu ba iyayen ki bane , Beener Ni Momyn Kice ba zan taɓa sauyawa daga hakan ba har abada . Wani irin huci Beenerfa ta sauke Na Wanda yayi kuka yayi har ya gode Ma Allah ,kana ta kalli Mom Salma tana cewa " I love You Momy , And I love my family , Ina Son zama da Umma na ,ba don komai ba sai don itama na saba da ita kaman yanda na saba daku , Kuma zan ji Dadi nima naga nasan Wasu dangi na ko ba duka ba , Mom Ku tafi ,ina fa anan , a duk lokacin da nake son Ganin ku zan zo.! Kar kisa Wannan a Ranki har abada bazan taɓa iya sauya ki a uwa ba , Saboda ba zan iya ba ....ta ƙare maganan tare da Fashewa da wani irin kuka mai gunji , Cike da tashin hankali Mom Salma ta sa hannun tana hugging ɗin Beener zuwa jikin ta ,kuka suke sosai , yayin da kowa na wurin sai da ya xubda ƙwallah na tausayawa . Kusan mintuna biyu suna ƙanƙame da juna kamin Beenerfa ta ɓanɓare kan ta ,da sauri tana faɗin " Momy Bye bye , ta ƙare maganan tana barin wurin da gudu . Ummu dake tsaye ne idanun ta har basa gani saboda kuka da kumburar da suka yi , Ba tare da ta ankare da zuwan sa ba , Sai hannun ta da taji ya riƙe yana furta " Mu tafi .!


Saurin ware idanun ta tayi a saman fuskar Nurein ,kamin ta juya tana kallon Farouk wanda suna haɗa ido yayi mata wani irin kallo ko na meye bata fahimta ba . A hankali ta fara bin bayan Nurein yayin da Momy Salma cikin matsanancin damuwa ta fito gidan , Hajiya Zeenatu ita ta tsaya sallama da Umma ,itama duk taurin zuciya irin nata ta gagara ɓoye Hawayen ta . A wannan yammaci suka ɗauki Hanyar dawowa Abuja ,ko wannan su Ka kalli Fuskar sa babu walwala sam."

"Bayan Wasu watanni".

Parking moton sa yayi a Inda aka tanada na aje motocin gidan , Kana ya fito cikin zatin sa ,idanun sa na a cikin ɓakar tabarau . Ga wani Saje da ya kuma ajewa fiye dana da baya . Wani ƙyau ya ƙara na musamman . Cike da earphone ɗin Kunnen sa yaji Muryar Momy tana cewa " Welcome back my Son , Ina Under ground . Murmushi Farouk yayi kamin yace " Okay mam . Cike da takonsa na matashin Soja yake takawa cikin sassarfa yana nufar Part din Momy Salma .
Cike da matsanancin Farin ciki ya fara wuce falon gidan yayin da ma'aikatan ke gaishe sa amma da yake baya ta kansu ,mutum biyu ya kosa ya gani Ummu da Momy , don sun fi watanni Hudu basu haɗu ba , Ta dawo gidan da kwana biyu yayi tafiyar su ta sojoji sai a yau ya dawo . Yana shirin bin lifta zuwa under ground na ga mom har ta fito da Sauri tana hugging din Farouk cike da matsanancin Farin cikin ganin sa . I'm happy to see you Son . Ya hanya ? Tayi maganan tana ɗagowa daga jikin sa cike da matsanancin Farin ciki . Murmushi yayi yana faɗin " All is Well Mam , Ina Ummu take?.


Fuskar Momy ne ya sauya a lokaci guda ,idanun ta na ciko da ƙwallah , a sanyaye tace " Tana Bedroom ɗin ta . Okay Yayi maganan yana raba jikin sa dana Momy tare da Son nufar Bedroom din Ummun . Hannun sa Momy ta riƙe a hankali ta fara faɗa masa halin da suke ciki da Ummu a gidan , Sam kullum ka ganta cikin damuwa take ,taƙi sakewa dasu , Idan kaga Walwalar ta to da Nurein ne idan ya zo , ko break fast Bata Sanyi dasu , idan ko ta zauna a ɗaki ita kadai bata da aikin da ya wuce na kuka . Idan na tambayeta meke damun ta sai tace babu komai . Momy Kiyi haƙuri Kinji ? Zata dawo yanda kike so Inshaallh . Farouk don Allah kayi mun kokarin hakan , ina damuwa sosai idan na ganta a hakan . Gyaɗa kan sa yayi alamun to ,kamin ya juya yana saurin hayewa Stairs ɗin da zai kasa Bedroom din Ummu .

**

Zaune ya hangota kafafun ta na naɗe saman kujerar da take kai , hannun ta rungume da teddyn ta , Idanun ta a lumshe suke amma hawaye ke zuba mata , Sosai ta sauya tayi kyau ta ƙara murjewa fatan ta har sheƙi yake , tsayawa yayi yana kallon ta don bata san da shigowan sa ba ,alamu tayi nisa a tunanin da ta saba . Ummu.! Taji Muryar wanda bata yi expecting ba ya Kira sunan ta , cikin Sauri ta ware idanun ta tana kallon inda yake a tsaye . Murmushi ya sakin mata ,wanda tun da suke bai taɓa mata irin shi ba . Yah Farouk ka dawo?. Hummmm bai bata amsa ba sai zama da yayi kusa da ita ,yana sa hannun sa tare da zagayowa ta gyefen kafaɗan ta . Meke damunki?. Yayi mata maganan yana mata ƙurrr da ido . Saurin Girgiza masa kai tayi alamun a'a babu komai . Amma sai ya kauda kan sa kaman bai ga me tayi ba ,cewa nayi meke damunki ,buɗe baki kimun magana . Cikin Ɗan rawar murya ta ce " Babu komai . Kin tabbata?. Yayi mata maganan yana kallon ta ido cikin ido . Shiru tayi masa kamin ta kuma cewa " Eh . Murmushi yayi yana ɗan yin shiru tare da nazarin ta , hannun sa taji yasa yana ɗago Fuskar ta ,kamin tayi Aune ita dai taji ya haɗa bakin shi da nata ne yana tsotsan laɓɓan ta , wani irin abu taji yana mata yawo a ƙwanya wanda bata taɓa ji ba ...Ƙoƙarin janye kan ta take amma ina riƙon tamau yayi mata motsi ƙwaƙƙwara ta kasa . Ji tayi yana lalubar Harshen ta tare da cafkar sa yana cigaba da sha mata yana tsotsa mata tare da mannata jikin shi , nan take ta koma wata ƴar Babe da ita , gaba ɗaya ya rufe ta . Numfashin ta ne ya fara ɗaukewa na tsoro ,wanda sai a sannan ya zare harshen sa yana sauke numfashi tare da kauda kan sa tamkar bai mata komai ba . Gyefen sa ma yake kallo inda kayan tarkacen make up din ta Suke . Tsayawa tayi jikin ta ko ina rawa yake yi wanda kamin ta gama dawowa hayyacin ta ne taji ya kuma cewa" Meke Damun ki kike kuka kaɗai anan ?. Yah Farouk babu komai . Okay Yayi maganan tare da juyowa yana passing din Fuskar ta ,hannun sa taga yasa yana ɗago fuskar ta tare da shirin haɗa bakin shi da nata ,wato yayi mata irin yanda yayi mata yanzu . Ya...yah Farouk Please ,ka bari don ALLAH ...shii meke damun ki to?. Yayi maganan yana ɗaura yatsar sa a labɓan ta alamun tayi masa shiru sai kuma ya kuma maimaita mata tambayar? . Cikin Muryar shagwaɓa kuka na shirin ƙwace mata tace " Gida nake So naje. Ina kyewar Umma na , Beenerfa duka .

Jikin sa ne yayi sanyi ,a hankali ya sa hannun sa yana tallabo fuskar ta kamin yace " Okay zan kai ki gida ,amma sai da sharaɗi guda ,kome ne nasaki yanzu babu musu kin amince? Idan kin amince next week Zan Kai ki Gombe ,kuma ki daina noƙe mawa Momy tamkar ba Mahaifiyar ki ba ,ina so ki sake da ita tamkar yanda kika saba da Umma Kinji . Gyaɗa masa kai Ummu tayi cikin sauri ,kamin taga Ya miƙe yana cewa " Yau goyaki zanyi ,sau nawa kike Son mu zagaya Bedroom din Nan naki ?. Ware idanun ta tayi cike da mmki kamin tace " A'a . Kallon ta yayi yana jin babu daɗi ,don so yake yaga yasata nishaɗi da walwala kaman yanda Mom ke So. Wayar ta ne ya fara ringing ,Wanda cikin sauri idanun ta suka fito ganin sunan Nurein , hankalin ta ne ya fara tashi , kasan daga Wayar tayi sai kallon Farouk da take yi ,wanda shima ita yake kallo . Saurin aje Wayar tayi tana kashe ta baki daya . Har a lokacin Farouk bai ce mata komai ba yana kuma anan tsayen da yake , wannan yasa ta miƙewa a hankali idanun ta na cikowa da ƙwallah , takawa tayi tana zagayawa ta bayan sa kaman yanda yace mata , hannun ta tasa tana rungume sa tare da ƙwantar da kan ta a gadon bayan sa . Wani irin zuuu zamm zamm yaji ,wanda yasa shi Saurin lumshe idon sa yan jan ajiyar zuciya . Ƙwantawa tayi a bayan basa yayin da a hankali ya ɗan rage tsawon sa tana hayewa ya goya ta cak... Shashsheƙar kukan ta yaji amma bai dakata ba , nufar ƙofar fita yayi yana ficewa da ita zuwa love garden nasu na gidan ,inda suka saba hutawa . Tsayawa tayi tana kallon wurin don bata taɓa sanin dashi a gidan ba".




*Littafin

Please Login or Register in order to submit comment