Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tayi maganan Mom Salma na amshewa da cewa " Waye ya saka ku sauya Dirning Area daga kujeru Huɗu yanzu ya koma biyar?....
GN🥱
MMN TEDDYP




*Littafin nan na kudi ne Regular group ₦300...VIP group ₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*


Mom Salma ne ta amshi Beenerfa da cewa " Waya saka ku wannan Aikin ne? Babban sune ya fara mawa Mom Salma bayani akan Daddy ne yasaka ayi wannan Aikin .... Shiru Mom Salma tayi kamin ta juya tana faɗin " Okay Beener mu tafi ...Zuciyar Beenerfa a dagule cike da rashin fahimtar inda Wannan gyara na Daddy ya nufa ta bi bayan Mom Salma , a tare suka fice daga Falon Suna nufar Harabar farfajiyar Gidan , Driver ne ya ƙari ko don ya tafi dasu inda zasu je ,amma nan take Beenerfa ta dakatar dashi tare da cewa " A'a Adamu ka bar shi ,Ni zan yi driving da kai na ,bana buƙatar kowa . An gama Ranki yadade a dawo lafiya ...ba tare da Beener ta tanka shi ba ,tayi shigewar ta moton , wanda dama Tuni mom Salma ta dade da shiga ita Beenerfa take jira . A haka ta yi ma moton key tana yin horn masu gadin suka wangale tamfatsestsen Gate Ɗin tana ficewa daga Gidan .

Ƙarfe Uku na Yammaci Daddy ya dawo gidan , yayin da Tun da ya shigo Ummu dake Falo take jin Ƙara kaman na jiniya , Gyaran Pillows din kujerun Falon take Yi , tare da shirya su inda ya dace , a takaice tana taya sauran yan Aikin gyaran Falon . Ƙamshin Turaren Daddy yasata Saurin juyowa ,yayin da Masu aikin suka zube suna kwasar gaisuwan su ...itama Ummu yanda suka yi tayi ,tana faɗin Sannu da Dawowa . Murmushi Alh Abdullahi Ɗan Shuwa yayi yana Mawa Ummu alamun ta taho inda yake ...Miƙewa tayi daga Tsugunun da take tana takawa a hankali tare da nufar inda Yake . Hannun ta ya kama yana jan ta da hira yanda zata saki jikin ta sosai ,kana ya nufi Under ground room din shi da ita .

Bin falon Daddy take da kallo ,cike da mamakin tsaruwan shi , Wow shine Kalmar da ta furta a zuciyar ta , Dama falon Daddy yafi na Waje kyau ?. Muryar Daddy taji Wanda shi ya katse mata tunanin ta ,da kuma zancen zucin da take yi . Ummu zauna anan , Bari na shiga na fito . Murmushi ta sakin masa tare da gyaɗa masa kai ,tana ja baya tare da bin dakin duka da kallo . Wuce ta yayi yana nufar Inner room din shi .... Yayin da Ummu ta ja baya tana bin babban Hoton Su duka Familyn da kallo , Beenerfa a jikin Daddy ,sai Farouk dake gyefen Momy tana riƙe da hannun sa...dukan su fuskar su ɗauke yake da matsanancin Fara'a ,ko ba'a faɗa ba kai da gani kasan Suna a cikin farin ciki a wannan lokacin .

Me yasa yanzu Momy Salma Bata dariya ne kaman yanda na ganta a hoton nan??. Abun da Ummu tace kenan kamin ta ɗan taɓe baki na ban sani ba dai . Sai kuma ta juya tana nufar Wani teddy da ta gani ƙaton gaske irin wanda ake ajewa just for decoration na falo . Hannu ta tasa tana Murmushi tare da shafa Yar tsanan tana dariya .... Tana a wannan wurin sam bata ji fitowar Daddy ba, Sai dai jin Muryar sa da tayi yana cewa" Kina Son Teddy bear ne sosai Ummu?. Saurin ɗago da kan ta tayi tana kallon sa ,tare da wangale masa baki tana dariya tare da cewa " Ehh Daddy. Okay Taho muje ki rakani Wani wuri . Hummmm... Bin bayan sa tayi tana ƙwance Mayafin Doguwar rigar ta da ta ɗaura a kanta , tare da yafa shi yana sauka mata sosai . A tare suka fito zuwa babban Falon gidan , wanda yan Aikin kowa baki bude yake kallon Ummu da Kuma Daddyn, kowa da tambayar da yake a cikin zuciyar sa . Meye alaƙar Ummu da Daddy? Shine tambayar ta kowa . Nufar farfajiyar Gidan Suka yi yayin da cikin Sauri Excourt din Daddy suka rufa masa baya wasu na yin gaba tare da buɗe masa moton Ummu yasa ta fara shiga mazaunin baya ,kamin shima ya shige suna rufo ƙofar Securities na biyo bayan su , Driver ne ya shigo kamin yace " Alhaji ina muka nufa yanzu ?. Joy Mall ". Kallon Sa Ummu tayi kamin tace " Daddy me zamu yi acan ?. Zaki ɗauki duk abun da kike so ne ,sai na siya miki . Shiru Ummu tayi kamin tace " Daddy me yasa to? Beenerfa zata yi faɗa fa.! Ko itama zaka siya mata ne?.


Murmushi Daddy Yayi cike da jin tausayin Yar nashi kana yace " Eh itama sai ki zaɓa mata nata . Kallon sa tayi tana dariya cike da jin dadi kamin ta juya tana kallon gyefen hanyar da suke wucewa ...!


***

Mom Abun da kika yi baiyi ba , Ummu itama ƴace fa , Aihuwar ta akayi ..bai dace kina rinƙa....Ya isa.! Nace ya isaaa...!! Na zageta ka rama mata ,idan ka isa, ƙarikon So da ƙauna tun da na ɓata mawa Habibty n ka Rai ,nima ka ɓata mun sai zuciyoyin ku yayi sanyi kaji Ko Nurein ? Me kuma ka tsaya yi eyye ...? Mom I'm sorry ,ba Haka nake nufi ba...Ya kake nufi eyyeee ,dama nasan yace , Amma ba kaman namu ya'yan ba , ita baka ga tsitson da ta fito ba , Tsitson talauci , ba kaman kai ba , Wanda Idan ka so Rana ba zai taɓa jikin ka ba , hakan kuma zai yiwu ,amma su kuwa fa ,talakawa dole Rana ta zama masu tamkar AC ɗin da kai a yanzu a cikin ta kake ... Dole suyi mana ƙwadigo mu kuma mu biya su ,haka Allah ya tsara masu nasu rayuwar a duniya suci wahala , a kuma lahira idan basu yi aiki na mai kyau ba ,Suma suci ƙaniyar su....Mu kuma life Destiny namu shine muji daɗi anan muji acan shima.... Kaga muna ba talaka kudi a matsayin Zakka ,muje hajji muje umra mai yayi saura mu kuma yi ibadan nan da aka turo mu duniya domin ta ... Don haka ka fahimta aƙwai babbancin ƙwarao tsakanin ka da Wancen yar matsiyatan....ko hannun talaka ka taɓa zakaji kaushi ne tamkar Bayan Bushiya .... Kallon Mom Zeena Nurein ya tsaya yana yi cike da rashin jin dadin furucin nata ...Muryar ta ya kuma tsinkaya tana cewa " Har yaushe ka daina kyamatar talaka ,kaida Abincin yar aiki baka ci sai dai Ni na dafa maka , baka so inda kake talaka yazo ,amma a yanzu kace kana Son ƴar matsiyata ƴar Mai gadi a rana?. Yaushe ka sauya haka Nurein?.


Mom daga Lokacin da nayi ido Biyu da Ummu ,ki sani gaba ɗaya life style ɗina ya sauya , Ki sa a Ranki ba Wancen Nurein ɗin ne a gaban ki ba ,mai kyamatar talakawa a yanzu yar talakan nake So.! Ina Son Ummu ,ita kuma zan Aura Inshaallh . Kiyi haƙuri Mom Zan sanar da Dad yanzu.! Ba tare da ya jira jin na bakin Mom Zeena ba ya juya cikin sassarfa yana hayewa up stairs Inda Falon Daddyn Sa yake ....

***

Zaune ya hango Alh Ahmad Ɗan Shuwa ,wanda ya kasance Mahaifin su duka , Wato Omar Farouk da kuma shi Nurein Ɗin , Sai kuma ƙaramar su Wato Saratu ,wanda ta ci sunan kakan su ,suna kirar ta da Saraaa. A yanzu haka tana Ƙasar Spain a can take Digiri ɗin ta na farko kuma itace Autan su....Mom Zeena tana kirar Nurein da ɗa ɗaya tilo ne ba don komai ba ,don ta cire Omar a cikin ya'yan ta , tuni ta bada shi Ga Mom Salma , halak har Abada . Sosai suka shaku ita da Nurein , shine abokin hirar ta , abokin koman ta ,Son ɗan nata take tamkar rayuwar ta . In ba Ka sani ba ,ka ɗauka shine kadai dan ta a duniya , in ba an faɗa maka akwai mace ba ,wato Saraah.

Nufar inda Alh Ahmad Shuwa yake yayi yana zaune idanun sa cikin farin tabarau medical eye glss , Yana duba magazine ɗin dake a gaban sa ..ko ba'a faɗa maka ba kai dagani kasan sune yan sahun farko a boko , sosai girma ya fara kama shi ,don ya kai shekaru kusan 68 a duniya . A kasan carpet din Nurein ya zauna yayin da Dad ɗin ya ɗago Kan sa yana cewa " Aa Babban mutumin ya dai me ya faru kuma na ganka haka babu walwala?. Hummmm.... Nisawa Nurein yayi kamin ya ɗago idanun sa da suka kada kaman zaiyi kuka yace " Daddy Ummu nake So.! A'aahhh Dad yayi maganan cike da mamaki kamin ya aje magazine ɗin yana sa masa Dariya , Haba Nurein To wacece Ummun ita? Ko an kasa ka ne , Ummun tace bata yi kazo nan zakayi kuka???. Yayi maganan cikin nuna Caring ɗin sa ga ɗan nasa ,cike kuma da Zolaya wato shi mutum ne mai barƙwanci . Murmushi Nurein yayi yana ɗan jin sanyi a zuciyar sa , kamin yace " A'a Daddy ita Bata ce bata So na ba , mom CE tace Bata Son ta ,Wai ba zan Aure ta ba .


Shiru Daddy Yayi kamin yace " Wacece Ummun waye iyayen ta ? A kuma ina suke ?. Ɗan cizan laɓɓan sa Nurein yayi kamin yace " A'a Daddy ita ba yar kowa bane ba , Basu da kudi ,yar talakawa ce ,shi yasa mom tace Bata son ta ...Kuma Dad Ni Ina Son Ummu , wallahi idan ban Aure ta ba mutuwa zanyi .....Ai ko sai dai ka mutun ,don baza ka Auro mun gayyar tsiya ba , Talaka ai gayyar tsiya ne....Su kaji Muryar Mom Zeena dake shigowa ...kayya ..! Zeena meke faruwa dake ne? Haba wannan maganan bai dace ta fito daga Bakin ki ba ...

Daddyn Nurein dole na fadi haka , da fari yarinyar bata da wani abu da zanji eh zan iya suruta da ita...Matsayin karatu secondary . Iyayen ta Talakawa both side Uwa da uba . Haba Daddy ba zan bari wannan Abu ya faru ba...Ya alkawarin auren ku da Beenerfa?? Eyyeee?? Kuma baka ga Yarinyar ba ,da gani a ƙwai yunwar talauci Babu abinci, Sannan ba auki shi fa kalle shi ƙaton mutumi dakai kaga Yarinya Teenage girl kana wani maganan Aure ,kashe ta zaka yi ne idan ka Aure ta ko mene??.

Huuuuu haba Hajiya Zeena wannan ba magana bace ba , Yana Son Yarinya dai ko , to ba zai taba bari ya cutar da ita ba , Don haka yaje idan ya shirya Auren su da kuma zama dasu duka ,ita Ummun da kuma Beenerfa yayi mana magana a kowani lokaci , a shirye nake nayi masa Aure dasu duka ,sai a hada dana Farouk da Mufeedarh . Allah ya kyauta ya kuma kiyaye mu , ya tsare Ni Ni Zeena .! Nurein..!! TA kira sunan Nurein babu alamun wasa a tare da ita . Ka je kayi shawara ,indai kana Son Kan ka da arziki . Tana faɗin haka ta juya fuuuuu tare da barin Falon . Kallon Daddy Nurein Yayi idanun sa sun yi jahhh ,hakan yasa Daddy ƙwantar Masa da hankali tare da masa Alƙawari n Aura masa Ummu , a nan kuma take ya daga Wayar sa yana kirar Alh Abdullahi Shuwa ,don suyi maganan Auren nasu duka . Cike da jin Dadi Nurein ya tashi yana godiya tare da nufar bangaren sa don ya watsa ruwa yaji sanyi ,kana ya nufo gidan Mom Salma don Yaga nur ƙalbi ɗin tasa .
Kaiwa da komowa Mom Salma keyi yayin da Beenerfa ke tsaye tana bin Asabe da wani irin kallo , kamin Momy tace " Shi Daddy ɗin ne suka fita da Ummu??. Eh Hajiya sun ɗan jima da fita . Hummmm numfasawa Mom Salma tayi , tana a tsaye a falon ne taji Shigowan Nurein yana isowa tare da faɗin Momy Barka da gida . Danne damuwar ta tayi kamin tace " Nurein Ya hanya , maza zauna Asabe kawo masa ....No no Momy Ina Ummu Wurin ta nazo.! Saurin juyawa Mom Tayi tana kallon Beenerfa itama wacce Momy take kallo , tana jin wani irin tsananin tsanar Ummu a zuciyar ta...! Sun fita da Daddy tun... Kamin mom tayi maganan ne suka jiyo dararrakun Ummu tana magana da Daddy tare da cewa "Gobe Daddy Zamu ƙara zuwa ko?. Ehh mana gobe ki shirya....Cakkk Duka suka tsaya su duka shidan Mama Asabe ,mom Salma Beener , Daddy Nurein Ummu duka suna kallon kallo . Hannun Ummu riƙe da wani teddy Mai ƙyaun gaske So romantic , Nurein ne cike da rawar jiki irin na wanda yaga abun da yake So ya nufo inda Ummu take , Hannun sa yasa yana amsan Teddyn tare da faɗin " Wow so Romantic Yayi kyau . Murmushi Ummu tayi a hankali ,kamin tace Wani Abu ne taga ya kama hannun ta yana cewa " Come lemme show you something.......https://www.youtube.com/@mamanteddy4123 Subscribe our new YouTube channel pls @ MAMAN TEDDY HAUSA NOVELS AUDIO

DOMUN SAMUN LITTAFAN MMN TEDDY NA SAURARE DA ZARAR MUN ƊAURA MAZA KU YI MANA SUBSCRIBE KAR KU MANTA DA DANNA MANA LIKE MUN GODE....
https://www.youtube.com/@mamanteddy4123

Q


"Bayan Fitar Nurein ne Ummu ta kalli Daddy ,Kamin tayi magana ne Beenerfa cike da complain ta fara cewa " Daddy meyasa Ka ɗauki Wannan yarinyar ku ka fita tare? Me yasa kake Son ta eyee Dad?. Tayi maganan cike da Son jin Amsa daga Bakin Alh Ɗan Shuwa ....ammm Beenerfa ai itama kinga Yarinya ce kamar ki teddy na sayo mata....Kamin ya ƙare maganan ne ta juya fuuuu tana barin Wurin cike da jin haushin Abun da Daddy Yayi mawa Ummu . Wannan Abun sam baiyi ba , Bai kuma dace ba . Haba Daddy Banbanci kake kokarin nunawa akan Beenerfa? Wannan ba dai dai bane ba sam..."

"Mom Salma tayi maganan tana takowa zuwa inda Daddy yake tsaye".

Banbanci Salma kike cewa ? Ai kece wacce kike nuna banbanci da halin ko in kula akan ƴar ki ta cikin ki...Kar ki manta Ummu Ƴar ki ce ,kuma jinin ki , Wallahi ko na faɗa maki ko ban faɗa ba ke kin san bakya nuna Soyayya dai dai da ƙalilan Akan Ummu , kin mance da Uƙubar da ta fito ? Kin manta Wahalar da ƴar mu tasha a hannun mahaifin Beenerfa ? Waye ya jawo duka wannan ? Shine shidai Malam Kadarko ,munyi masa Rana yayi mana Dare , Dare baƙinƙirin. Hummm Nisawa yayi yana juya baya kaman zai bar wurin sai kuma ya ja ya tsaya yana cewa " Ni ba zan ƙyamata jini na ba , don kawai na faranta mawa Ƴar Wanda ya raba ya ta ,gudan jinin mu daga jikin mu , Zan nuna mawa Ummu Soyayyar Ɗa da Uba ,ke kuma kije ki nuna mata ƙiyayya ba zan hanaki ba ,amma Hjy Salma ki sani ba a taɓa sauya mawa Tuwo suna ,yana nan a inda yake ... Yana gama faɗa mata haka ya juya tare da saka ƙafarsa yana nufar hanyar da zai sada shi da Apartment din shi...Daddy."


"Mom Salma ta Kira sunan Daddy Wanda Jin hakan yasa shi dakatawa ba tare da ya juyo ba ya tsaya yana sauraren ta ..." Ba'a taɓa Sauya mawa Tuwo suna kace? , Humm to Ni zan sauya , Ba zan riƙe Ummu ba , idan mukayi haka bamu cika iyaye ba , Beenerfa wani irin tashin hankali zata shiga ? Kar ka manta bata saba da Wannan Rayuwar talauci ba sam , Amma ita Ummu ta saba mu barta don ALLAH acan , mu bar ta a hannun iyayen Beenerfa kaman yanda ta taso a hannun su ...mu kuma mu cigaba da riƙon namu Ƴar . Ka duba mun na saba da Beenerfa ,kuma sannan itama Ummu zata fi jin dadin zama da Iyayen ta su Malam Kadarko .


"A matukar fusace Daddy ya juyo Kamin ya fara cewa" Ina Son Ƴata ,kuma tun da ta shigo gidan Uban ta ,ba zata fita ba , Saboda ina Son itama tayi rayuwar jin dadi kaman na saura . Ke ki riƙe Beenerfa Ni kuma zana kula dasu na riƙe su duka . Daddy hakan ba zai yiwu ba. Momy tayi maganan idanun ta na fara tsiyayar da Hawaye . Zai yiwu ,daga lokacin da kika cigaba da yi mawa Ummu riƙon sakaina daga lokacin Ni kuma zan sanar mata da komai ,domun yana ba zata kamu da wani ciwo na daban ba . Juyawa Yayi yana ba Momy wuri , yayin da ta ja baya tana zubewa a 3ster ɗin falon , Idanun ta Duk sun duddulo waje sunyi ja waye na cigaba da zuba mata....ta rasa samun mawa kan ta mafita sam . Mama Asabe dake Bayan su duk abun da ya faru a gaban idanun ta ,itama saurin jan jiki tayi ba tare da ta bari Momy Salma ta ganta ba ta fice daga Ɓangaren ,hankalin ta kaf a matuƙar dagule...Waye yayi wannan Aiki ? Tambayar da take mawa kan ta kenan kamin a zuciyar ta tayi ta hailala tana kirar sunayen Allah tsarkaka .

Tun daga Wannan Rana , Momy Salma ta daina Walwala , Haka Ta rarrashi Beenerfa har ta sakko a yanzu suna yin break fast tare da Ummu ,sai dai Abu kaɗan Beenerfa zata fara zagin Ummu tana cin mata mutunci . A haka Ummu take rayuwa a cikin gidan , babu wurin wanda take samun sassauci sai mutane biyu , Nurein da Daddy . Don ɓangaren Daddyn Nurein tuni ya sami Daddy sunyi maganan Auren Ummu da Nurein ,amma anan Daddyn ya dakatar da maganan akan cewa " A bari su kammala Secondary . A haka rayuwa ke tafiya yake gungurawa . Yau hutun su Ummu ya ƙare , wanda Daddy sam yace ba zasu koma yin kwanan makaranta ba , Kullum Driver zai rinka kai su ,idan an tashi ya dauko su ..Sam hakan baiyi mawa Beenerfa daɗi ba , Don sosai tayi kywar abokanan Iskancin nata . Amma ya ta iya ,dole ta amince da maganan Daddy . Safiyar Litinin . Sanye suke cikin uniform iri guda ,school shoe , school bag komai nasu iri daya har lunching basket . Hugging Din Beener Momy Salma tayi tare da mata sai ta dawo . Wuce su Ummu tayi cike da jin dadin yau zata koma makaranta wani masifar na Beenerfa yayi mata Sauki . Sam bata damuwa da Yanda Momy ke nuna Soyayyar ta ga Beenerfa a cewan Ummu ai dama Ɗiyar tace .

Gidan baya ta shiga yayin da Beenerfa ta zauna a gidan gaba gyefen Driver a cewan ta ba zata zauna gata ga Ummu ba." A hankali Ummu ta lumshe idanun ta tana rufe su tare da buɗewa , Fuskar Omar Farouk ta tuno , yayin da mafarkin nan nata da kullum take yi akan sa ya dawo mata ƙwaƙwalwa. Ummu kiyi ma Farouk Addu'a Kinji?. Jikin ta ne yayi wani irin sanyi , hankalin ta yana neman ya tashi , me yasa Yace mun haka ?. Yana ko a cikin koshin lafiya??. Ummu sauko an iso." Muryar Drivern taji wannan yasa Ummu saurin sakkowa tana cewa " To mun gode . Ba tare da ta tsaya jirar Beenerfa ba ta nufi cikin makarantar nasu kan ta tsaye....Oyoyo kissss me , kissss meeeee uhmmm💋 . Anam ce ta nufo Ummu tana Kissing din kumatun ta tana faɗin Wannan maganan . Murmushi Ummu tayi suna Rungume juna tare da nufar class ɗin su fuskokin su duka cike da matsanancin Farin cikin haɗuwar su .

***

"Zaune Suke a falon Momy Salma , Beenerfa na a can tana playing game Yayin da Nurein yake gyefe kunnen sa cikin head phone , Alamu magana yake yi .... Okay ya Farouk . Cewan Nurein yana miƙa mawa Beenerfa Wayar sa tare da cewa " Yah Farouk ne . Cike da shagwaɓa har da hawayen ta ,take fadin " Yah Farouk i miss You , When are you back?. Ba tare da naji mai yake cewa ba ,naga ta saki ranta tana murmushi tare da miƙa mawa Nurein Wayar , A kuma dai dai Nan Ummu na saukowa cikin shirin zuwa islamiyan da Dad ya saka su. Ohhh Yah Farouk ga Ummu itama ku gaisa . Wani irin bugawa ƙirjin ta yayi dammm...wanda jiki a sanyaye tasa hannu tana amsan Wayan Tare da ƙara shi a kunnen ta . Shiru babu wanda yace masa komai daga ita har shi Farouk ɗin , kusan mintuna uku , shidai Nurein bai san me suke yi ba ,don da ya bata juyawa yayi yana cigaba da aikin gaban sa... Beenerfa ce ke kallon komai dake faruwa , Wannan yasa Farouk cike da jin haushin wato shine zai mata magana cewa " Ke dallah bashi wayar sa , yar ƙauye kawai mtswww". Yayi maganan yana jan dogon tsaki tare da kashe wayar nasa . Tsayawa Ummu tayi tana yin shiru kusan mintuna biyar . Kamin Beenerfa ta wani sheƙe da dariya tana cigaba da danna Laptop din ta . Baki masa magana ba ne ?. Taji Muryar Nurein wanda yasa Ummu saurin cewa " A'a Yah Nurein . Okay kin shirin Islamiyan ne?. Eh . To muje na kai ki .


"Nima yah Nurein ka jira Ni ,ka kaini . Ni Driver n ki ne?. Yayi maganan yana haɗe girar sama da ƙasa . To ai itama din kai ba drivern ta bane ba". Cewan Beenerfa tana turo bakin ta gaba . Okay naji wuce kiyi sauri ki shirya ,idan kuma baki fito da wuri ba ,Zamuyi tafiyar mu . Ya ƙare maganan yana kallon Fuskar Beenerfa . Juyawa tayi cikin Sauri tana nufar Bedroom ɗin ta don ta shirya .

Mai do da hankalin sa yayi akan Ummu kamin cikin tausasiyar Murya yace " Babe me , ina iPhone din Dana siya mikii? Me yasa Bakya using dashi ,ban taɓa kirar ki na same ki ba ,Kullum switch off . Kin taɓa kunna ta ma kuwa?. Shiru Ummu tayi kaman ba zata masa magana ba ,sai kuma ta kalle sa tana cewa " A'a Ban amfani da ita ne. Amshe ta yayi da cewa " Bakya So ne ? , Sai a sauya wani . At list Ina so na rinƙa jin Muryar ki kamin nayi barci a kullum . Idan kuma so kike duk dare na rinƙa zuwa na ganki sannan na koma nayi bacci to". Saurin kallon sa tayi tana girgiza kan ta alamun a'a don sarai tasan zai aikata hakan fiye ma . To zaki kunna wayan taki?. Murmushi tayi tana cewa " Eh , Amma kar ka fito da da da saboda Ni . Ba gani nan ka ganni ba.


Ina miss ɗin ki ko wani dakika ,kin sani babe me ". I miss you always . Ina Son ki Bana gajiya da kallon ki , Burina kawai muyi Aure na cigaba da Son ki , Mu ƙwana mu tashi duka tare ... Saurin saka hannun ta tayi tana rufe fuskar ta cike da jin kunya , wanda yasa shi dariya yana sa hannun sa tare da buɗe mata fuskar ta , Seriously Ummu ina Son ki.! Na san kuma kema zaki Soni. Kamin tayi masa magana ne taji yasa bakin sa saman goshin ta yana ɗan sunkuyowa kasa tare da rage tsawon sa yana Kissing din ta . kallon sa tayi tare da narke masa fuska cike da shagwaɓa . Yah Nurein babu kyau haka . Sorry I'm eager Naga na Aure ki Ummu , Na kosa na ganki tare dani a gida na . Ware idanun ta tayi da Sauri kamin cike da kunya tayi waje da sauri tana dariya . Beener ce ta fito tana kallon Nurein itama cikin hijabi wanda yau

Please Login or Register in order to submit comment