Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mun na roƙeku ...ga masu buƙatar labarin Womanizing Boss and the Virgin maid regular group ₦300... VIP group₦500... Special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*

***

"Tsayawa yayi yana parking moton sa cikin Harabar asibitin Faith Special Hospital inda Beener a ƙwantar da ita ... shigowan sa yasa Wasu nurses Saurin ƙarakowa zuwa inda yake ,ya ɗauko Ummu cakk a hannun sa . yallaɓai Kawo ta mu shiga da ita ɗakin gaggawa (Emergency room) . Bai tsaya tanka masu ba tafiyar sa yake har sai da ya iso Emergency kana ya miƙa Ummu yana ja da baya tare da zama a kujerar jira . Ba tare da yaji takon ta ba ,Muryar ta kawai yaji tana dafa shi tare da cewa " Ya Farouk ka dawo ?. Jin Muryar Beenerfa yasa shi ɗago da fuskar shi yana kai hannun sa tare da shafa gyefen fuskar sa yana sakin murmushi tare da cewa ' Beenee How is Your body? . Pretty good ,Tayi maganan tana zama a gyefen sa tare da ƙwantar da kan ta saman kafaɗan sa . Hannun sa ya sauke a saman kanta , wanda tasa Hular maginyata haka riga ce mai kamar yar shimi a jikin ta , dagani kasan na asibitin ne da suka saba saka masa duk wani maginyaci wanda suka bashi gado . Beener tashi muje ki koma , ai basu sallame mu ba ,ya akayi kika fito ?. Kallon sa tayi kaman zata masa magana sai kuma ta kauda kan ta gyefe tana kallon cleaner ɗin asibitin da suke kaiwa da komowa .


Abun ka ga saurin ƙufuluwa irin nasa , hakan da tayi masa yasa shi dakamata tsawa yana cewa " Ki tashi muje nace .! Kalli yanda kika fito ko hijabi babu bare mayafi ,nan asibiti muke ba Gidan Daddy ba tashi maza. Ƙwallah ne ya taru mata duk da tasan halin sa , a hankali ta miƙe tana yin gaba ba tare da tace dashi komai ba . Ɗakin da take ƙwance ta shiga tana Ƙwantawa a gadon majinyatan . Tsayawa Omar yayi ba tare da ya zauna ba . Gani yayi ta rufe ido tana ware su akan sa , tare da cuno baki alamun tayi fushi . Ka tafi to tun da na shigo ,bana buƙatar ka a nan .


Jin wannan maganan da tayi masa yasa shi fahimtar tayi fushi ne akan abun da yayi mata ,wannan yasa shi sakin murmushi yana cizan laɓɓan sa ,kamin yayi magana ne yaji Muryar ta tana cigaba da cewa " ya Farouk a haka ne kake Cewa kana So na? Bayan kwana nayi ban ganka ba , Idan ka samu wata ƙanwar bani ba daina So na zaka yi Ni nasani ,ta ƙare maganan ƙwallah na gangaro ma fuskar ta , domin a rayuwar ta babu wanda take jin Son shi sama da yayan nata . A hankali ya lumshe ido yana tuno da Fara Tafiyar sojan sa na Farko ,yanda daƙyar aka iya raba Beenerfa da jikin sa ,har Ƙwanciya a asibiti sai da tayi na rabuwar su . Kullum a cikin Damuwa da kyewarsa take .... Tsugunawa yayi gaban gadon nata yana rage tsawon sa ,hannun sa yasa a saman goshin ta yana shafa zagayen girar ta . I'm so sorry My princess , Ba zan sauya ki ba , Kinji ƙanwata . Kawai naje wani Ɗan aiki ne da ya shafe Ni . Aiki Kuma Yah Farouk? . Tayi maganan tana kallon sa da yake goge mata hawayen fuskar ta. Na meye aikin? Da yafini ƙanwar ka muhimmanci daka barni a halin rayuwa ko mutuwa .
Shiru yayi yana kallon ta,sam baya Son faɗa mata wacece wannan yarinya. Ina Son ki My Beener kin San meye yanzu ?. Kiyi barci mai kike A taho maki dashi yanzu na koma gida nasa a miki .


Murmushi tayi kana tace " Rice and vegetable soup , Kar asa nama ko Kifi ban san komai . Sai a hado mun Da chocolate . Okay yayi maganan yana sakin mata murmushi . Komawa tayi tana lumshe ido tare da cewa " Yaya kar ka dade fa . Shiru taji bai tanka ta ba ,wannan yasa ta buɗe idanun ta dai dai yana rufo ƙofar .

***


A kan hanyar sa ce ta barin asibitin ya haɗu da Dr Rakiya ,wanda anan take shaida masa ciwon Mom Ɗin sa ya tashi yanZu haka itama sun bata gado ....sosai Hankalin sa ya tashi ,nan kuma take yake tambayar Ta meyake faruwa? Amma sam bata faɗa masa gaskiyar al'amarin ba . Har sai da ta kawo sa Room din da Mom Salma take sannan ta juya , dai dai yana saka hannu zai burɗa ƙofan yaji Muryar Momy tana shashsheƙa tare da cewa " Tayaya hakan ya faru? Me yasa aka yi mana wannan yankar ƙaunar? Abun da muke jin sa a labarai da fina finai na sauran ƙasashe yau ace yazo kaina? Wai ni ba Mahaifiyar Beener bace, An sauya mun yata ta asali ,waye yayi wannan aikin ? Wani azzalumin ne?. Daddy ne ya fara bata haƙuri da rarrashin ta ,tare da bata gamsashun hujjoji na cewar yasa ayi masa bin cike a wannan asibitin na A.B.U , abun da ya faru ashekarar 2007 ,tabbas yasan a wannan lokacin bazaa rasa aiki da CCTV camera ba .


Dammmm Ƙirjin Farouk ya buga , idanun sa ne suka kada suna yo Waje na tashin hankali kan abun da yaji Mom Salma na faɗi yanzu . Muryar ta yaji tana cigaba da cewa " No Daddy Kar kayi haka ,bana So a rabani da Beener , ko an gano gaskiyar inda yata take ,Ni na bar masu yata ,mu rufa mu cigaba da rainon Yar mu Beener har Auren ta har mutuwa. Cike da Mamaki Daddy yake kallon Mom Salma Kamin yace " Salma kina cikin hayyacin ki kuwa ? Bafa kisan halin da tamu yar take ciki a yanzu ba.


Cikin fusata da Zafin zuciyar da Bata taɓa ɗaga masa murya ba tace " Tun yanzu ka fara jin yar ka ta asali kake So ba Beener ba? To bazan amshe ta ba ,Ni nace na bar musu ,ko wani hali take ciki ba sai muna rinƙa taimakon su ba ,idan kuma ma suna cikin wadata ne duka sai mu bar ma Allah mu manta da ita a zuciyar mu.... Ammma Idan ka raba Beenerfa da jiki na Wallahi mutuwa zata fin alheri... Cike da Sanyin murya da rarrashi Daddy ya fara cewa " Ya isa haka , duka shikenan . Allah yasa tana hannu mafi Alheri . Amin ya rabby . Ta furta tare da kai hannun ta tana ɗaukar Cup din coffee tana kurɓa tare da ajewa a gyefe .

Jiki a sanyaye Omar Farouk ya juya yana takawa ji yake kaman ransa baya tare dashi , juyawa yayi yana barin asibitin baki ɗaya. Sam ya rasa tunanin sa , kirar Wayar sa Fahad yake amma sam bai iya ɗagawa ba ,wannan yasa shi direct Nufo gidan Daddy don Yaga Halin Da Aminin nasa yake ciki.

***

Bayan kwana biyu Aka sallami Momy da Beenerfa , yayin da Ita kuma Ummu jiki Alhmdllh ,kwana biyu Bata ganin wulƙiyar mugun da ya kawota sai dai Fahad da shi yake kawo mata abinci da komai nata har kayan da ta sauya shiya kawo mata akwati guda . Ita dai ba uhm bare uhm'uhm bata kulasa ...a haka jikin ta ya warware . Ƙwanan ta uku aka sallame ta , anan ne Fahad ya ɗauki Aƙwatin ta yana nufa da ita farfajiyar Asibitin ,can inda Moton Farouk yake suka nufa . Sai a sannan ne ta kalli Fahad tana cewa " Yaya na Ina zaka kaini? Don ALLAH kar ka maida Ni Wurin wancen mugun Sojan kashe Ni zaiyi , bindiga ya nuna mun , wallahi Ni na ɗauka bazan farfaɗo a gidan duniya ba sai a ƙiyama 😥 ta ƙare maganan tana sakin kuka da hawaye sharrrrrr³ .

Wani irin yaji a zuciyar shi tausayin Ummu yaji ya kama shi ,wanda bai taɓa jin irin sa a zuciyar sa akan ko wacce ɗiya mace ba . Kallon ta yayi yana shirin magana ne yaji ta kuma cewa " Na tsani Sojoji mugaye ne ,bana Son su ,tsoron su nake ji basa da imani ,musamman wancen yanda ya ɗaga bindiga kaɗai zai nunar maka da yasa ba da kashe mutane . Murmushi Fahad Yayi yana kallon Ummu tare da cewa " Meye Sunan ki beuty? . Jiki a saluɓe Ummu tace " Ummul khairy. A'aa ashe Khairat ne , Maman Alhairai . Sunana Fahad , Me yasa Bakya son Sojoji , nima Soja ne .


Ƙuuuuuuurrrrrr Hantar cikin Ummu ya kada , cike da tsoro take kallon Fahad Kamin tayi magana ne taji yana cewa " Sojoji ba mugaye bane ba , babu abun da zai miki Kinji , aiki kawai zai baki a gidan su , Yana da Mahaifiya mai kirki kuma Sannan yana Ƙanwa wanda nasan zata ɗauke ki tamkar yar uwa . Share hawayen ki ki bar kuka . Hannu ta sa tana goge Hawayen fuskar ta . A haka suka ƙarisa Inda moton Omar ke tsaye . Bari nazo .!


Fahad Yayi maganan yana shiga moton da Omar ke ciki .


Ita ba zata shigo bane ba?. Omar yayi masa maganan cikin dakiyar murya . Ni nace ta tsaya . Farouk kasan menene? Pls duk wani Plan da muka shirya na mugun ta akan wannan Jaririyar yarinyar mu aje a gyefe , don Allah kayi haƙuri kayafe mata yarinta ne . Taban tausayi . Wani kallo Omar ya watsa masa ,bai basa amsa ba sai dai gani yayi ya fice daga moton yana daka mawa Ummu tsawa tare da cewa " Malama Zaki shigo ne ko sai na zo na karairaya ki ,na karya banza .!


Jin Muryar sa kaman saukar Aradu yasa Ummu saurin yi kaman zata kifa ,jikin ta ne ya ɗau rawa kar³ , kamin tayi wani motsi Fahad ya fito ,Inda take ya zo yana amsan Aƙwatin hannun ta tare da buɗe mata mazaunin baya yana cewa " Sorry kar ki tsorata shiga mu tafi . Ba tare da tace komai ta shiga moton yana rufowa , tare da nufar bayan Boot yana saka aƙwatin nata . Muryar Omar yaji yana cewa " Ɗan Wahala , Ko son ta kake ne ,sai na baka kuyi kwana biyu .


Kallon sa Fahad yayi tare da cewa " Ƙagan ka da wani magana ,me zan cinta a jikin ta yar yarinyar nan , ai sai ta kara girma . To na sani Da Allah shiga mu tafi . Allah ya sanyaya zafin zuciyar nan taka Omar , Abun da Fahad yace kenan yana nufar moton tare da shigewa ,nan take Omar ya fara driving tare da ficewa daga Asibitin yana nufar Gidan Madam Dr Salma......

****
Tsayawa Daddy Yayi cakkk Yana bin gidan Malam Kadarko da kallo . Wani irin tafasa zuciyar sa keyi zufa na sakko masa har ƙirji ....nan take ya fito daga moton yana dakatar da Sauran makararraban sa masu take masa baya . Nufar inda mudi yake mai saida Rake yayi yana sallama tare da zama babu nuna girman kai ko banbancin girman mai kuɗi da talaka . Sannu da Zuwa Alhaji wani Abu kake bukata ?. Sauke ajiyar zuciya Daddy Yayi kana a siyasance ya fara Tambayar Mudi yaran malam Kadarko ,wanda nan take ya fara Rattabo masa . Yana cikin maganan ne Mom ta fara kirar Wayar sa , wanda nan ya dakatar Da Mudi yana ɗaukar Wayar Mom tare da sanar mata inda yake . Jin haka yasa Mom cewa kar ya kashe wayar tana Son jin abun da Mudi zai faɗi . Haka Dad ya Sauke wayar ba tare da ya datse kirar ba yace ina jinka malam. akwai Auwalu , Akwai Nasiru , Da Ishaq sai kuma autan su mace Wato Ummu . Yarinyar kirki ,amma izayar da yake mawa yarinyar nan Alhaji wallahi bani kaɗai ba ,har mutanen layin nan tunani ake akan cewa ,sai kace ba yar cikin sa ba. Akwai ranan da Da Wutan itace yayi mata lalas yana dukan ta dashi haka abun ka ga farar mace jikin ta duk ya salɓe ko ina ta wuce sai an ga dukan nan. Yanzu haka Umman yarinyar matan shi kadarkon tayi yaji sakamakon ɗaukar ƴar Ummu da yayi yabada ita wai acewan shi aikatau ..... Innalilahi wa'inna ilaihir rajiun shine kalmar da Daddy Ke furtawa kamin yace taimake Ni kayi mun sallama da shi malam Kadarkon....!




*VIP da mutanen SPC don Allah haƙuri zuwa ranan sati zamu fara maku update Sau biyu a rana ..na gode.**🕊️THE VIRGIN MAID🕊️*


....Mmn teddy


*C*

*Kiyi haƙuri don Allah Kar ki karanta mun wannan labarin indai baki biyani haƙƙi na ba , Haka don Allah kar wanda suka biyani su fitar mun na roƙeku ...ga masu buƙatar labarin Womanizing Boss and the Virgin maid regular group ₦300... VIP group₦500... Special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta wannan number 08081202932*

***


Cikin Sauri Mudi yake faɗin An gama Alhaji , yayi maganan tare da nufar Soron gidan yayin da shi kuma Daddy Ke bin sa a baya. A bakin kofar gidan suka tsaya Malam Mudi na shirin ƙwaɗa Sallama ne suka ji motsin tafiyar daga Bayan su . Umma ne da Wasu Tsofaffi mata biyu ,da Alama sun dawo da ita ne ,sai kuma bayan su Malam Kadarko . Cikin Girmamawa Daddy ya matsa yana basu hanya ,don shi sam bai gane ko ɗayan su ba . Sannu Alhaji yau kaine a gidan namu da ƙafarka? Umma tayi maganan tana gyara zaman mayafin kan ta tare da jah tana tsayawa a gaban Daddy Jikin ta na Rawa na girmamawa . Allahu Akbar ashe kece matar Malam Kadarko yi mun sallama dashi . Saurin juyawa Umma tayi inda Malam Kadarko yake gaba ɗaya ya gama jiƙewa da zufa na zullumi da tsoro . A'a Malam Ga Alhaji ...ehh.ahhh sannu Alhaji mu shiga daga ciki ....cewan Malam Kadarko yana maganan tare da in Ina . A'a nan ma ya isa Malam Kadarko bana shigo gidan mata ba da wannan yammacin . Kamin Malam Kadarko yace wani Abu ne Umma ta amshe Daddy da cewa " Alhaji ka manta kai ka saya mana wannan gidan da muke ciki? A lokacin da tsohon cikin ɗana na fari , masu haya suka kore mu akan bamu biya su kuɗin su na shekara ba ,kaine ka bada kudi aka saya mana wannan gidan ,wanda baka taɓa shigar ta ba . Alharan ka ba zamu taɓa mantawa dashi ba ,shigo Alhaji don Allah . Jin haka yasa Daddy sakin murmushin su ta manya , kamin yace Wani Abu ne malam Kadarko yayi gaba yana shiga gidan tare da cewa " Bismillah Alhaji .

Ganin haka yasa Su inna Atine tambayar Umma waye Wannan mutumin? Nan ta basu takaitaccen Labari Akan Alh Ɗan Shuwa . Kamin suyi sallama da ita a soro suna kuma bata haƙuri akan lamarin Baba Kadarko .


Tabarma Malam Kadarko ya zauna haka Daddy a tsakar gidan , Umma ne ta shigo cikin sauri ta nufi ɗakin ta tare da Fitowa da sabuwar Ƙwanan sha da ruwa me sanyi a ciki. A gaban Daddy ta aje tana kuma tsugunawa tare da gaishe sa har ƙasa.kana ta miƙe daga bisani tana nufar Ɗakin ta .

Ganin tafiyar Umma yasa Daddy Cigaba da cewa " Malam Kadarko abun da mukayi mun zalunci kan mu , Ƙasa duka yaran nan cikin rayuwar garari , Bazan mu taɓa tona wannan sirrin ba , saboda Bamu san halin da Beenerfa zata shiga ba , mun bar maka Ƴar tamu halak malak duniya da lahira , muma muna So kabar mana Beenerfa har Abada.! Wani irin sanyi zuciyar Malam Kadarko yayi akasin da baya da ya fara tunanin nufar gidan kurkuku . Wani irin matso hawaye ya fara yi na ƙarya wai ala dole yayi nadama ,kana ya fara magana da cewa" Ku yafe mun Alhaji nayi kuskure komai ya faru sharrin sheɗan ne , ban....Aaaa Haba Malam Kadarko ai wannan ya wuce har a cikin zuciyoyin mu . Sai dai ina Son Naga Ɗiyar tawa ta wurin ka , kamin na wuce ... Jin wannan furucin nasa yasa malam Kadarko saurin kallon Daddy kuma cike da kame² yake cewa " Ai Omar Farouk yaron ka ya zo yau ƙwana huɗu kenan ya ɗauke ta a matsayin ƴar Aikin gidan sa.


Kaman yaya ban gane ba.! Cewan Alhaji Ɗan Shuwa cike da Rashin fahimtar inda zancen Baba ya nufa . Nan take ya feɗe masa biri har wutsiya tun daga samun makarantar scholarship ɗin da Ummu tayi har marin Omar da tayi ,da kuma yanda yazo nan yace ya basa ita ,shi kuma ya miƙa masa . Jin wannan maganganun nasa yasa Daddy ɗauke Wuta . A hankali ya miƙe yana cewa " Tana babu damuwa nasan zai dawo maku da ita ,amma don ALLAH kar mu manta mu rufe wannan sirrin a iya nan . Ina sha Allah Alhaji . Bin bayan Daddy malam Kadarko yayi har moton sa ,kamin yayi masa Alherin da ya saba yana kirar Mudi shima yayi masa nasa , secutin da yake tare dasu ne sukayi saurin buɗe masa moton yana shiga . Nan take motocin nan kusan goma sha suka fara barin layin a tare , Yayin da Malam Kadarko ke a tsaye har sai da yaga wucewan su ,sannan ya sa hannu yana sauke ajiyar zuciya tare da furta " Ƙadsarar ki kenan Ummu zama a gidana , ita kuma ya ta nata ƙaddarar kenan ta rayu cikin jin daɗi ."


A farfajiyar gidan Alh Ɗan Shuwa Farouk ya aje moton sa kamin ya buɗe ne ya juya yana kallon Fahad tare da cewa " Fahad Ina da buƙatar Mace yau na ƙwana da ita a gidana ,sam bana tsammanin zan iya ƙwanan gidan nan yau . Murmushi Fahad Yayi yana sakin Dariya tare da cewa " Kace kana buƙatar cin durin Ƴammatan naka . To wanne ciki na sanar masu , Hajiyoyin ko Yara yammata. Tsitt Ummu tayi tana wurga ido ta ko ina jikin ta har a wannan lokacin ɓari yake yi. Don ALLAH Yaya na ku maidani gida .


Dafe kai Fahad Yayi don ya manta sam da Ummu a moton , Cike da jin kunya tamkar a gaban ƙanwar sa ya faɗi wannan magana yace " Ayya Sorry my Khairat , Fito mu shiga ciki . Saurin saka hannun ta tayi tana buɗe murfin moton yayin da suma suke fitowa a daga ɓangaren su . Tsayawa Ummu tayi tana bin wannan gida da kallo tare da faɗawa Duniyar tunanin wannan wani irin makeken gida ne , parking lot yafi Guda sha biyu ta ko ina motoci ne kake gani na zamani sai mala'ikatan gidan ,ciki har da sojoji .... Ɗaga kan ta tayi tana kallon benen gidan , kamin daga Sama taga Wani Rubutu tare da zanen love ❤️ an rubuta they're Forever lovers, Yah Farouk and Anty Rufaida . Sai kuma taga an kuma rubuta Beener & Nurein anyi alamun love . Tsayawa tayi tana tunanin inda tasan mai irin wannan rubutun wanda tana tsaka da wannan tunanin ne Taji Muryar Fahad Yana cewa " Ummu Khairat taho mu shiga daga ciki .


Wani irin kallo Farouk ya watsa masa yana masa kallon cewa "Wannan sanaben duk na meye ?. Ganin haka yasa Fahad sakin murmushin babu komai tare da kauda komai da cewa " Farouk Ashe Nurein Ya dawo daga Span ?. Gyaɗa Masa kai yayi alamun eh kamin ya wuce ciki...Yah Fahad waye shi Nurein Ɗin ?. Ummu tayi maganan a ɗaɗare dasu duka . Murmushi Fahad Yayi yana cewa " Ƙannin Farouk ne . Jin haka yasa ta kama bakin ta tana bin bayan su duka .
****
Ɓangaren Daddy Kuwa yana shiga moton sa ya kara wayar a kunnen sa , shashsheƙar kukan Madam Salma Ke tashi daga ciki , wanda dama yasan tabbas za'a yi hakan tun da duk taji komai . Kamin yayi mata magana ne yaji tana cewa " Yanzu Ita yarinyar tana hannun Farouk?. Ƙwarai kuwa yanda Malam Kadarko ya faɗi. Leƙawa tayi ta window tana sa hannun ta tare da hango farfajiyar parking lot din , okay Ina zuwa ina ganin kaman ga Omar ɗin nan ya shigo yanzu . Datse kirar tayi tana saurin miƙewa tare da nufar hanyar saukowa daga Up stairs ɗin da take .

Wal³ Ummu ta gani aljannar duniya irin arzikin da ko a mafarki bata taɓa ganin irin sa ba . Youuuu??? Taji Muryar Beenerfa tana ce mata tare da miƙewa daga kan Royal ɗin da take . Juyawa tayi tana kallon Farouk da yake shirin wuce su ya nufi stair Inda Yaga Mom na saukowa . A wani irin zafafe Beenerfa ta nufo Ummu ,wanda ganin haka yasa Ummu saurin yin bayan Fahad , Amma Ina fizgota Beener Tayi tana wanke fuskar ta da mari tassssss . Tare da fincike mayafin kan ta da tayi rolling .Nan take Abun ka ga gashi irin na Shuwa ya barbazo har fuskar ta ,kama gashin nata tayi tana dukan ta tare da jan gashin tana fizgar gashin kaman zata cire mata kan duka . Ihu Ummu keyi tana faɗin Don Allah Beenerfa ki ƙyale niiiii....Bazan rabu dake ba dan uban ki ,yar matsiyan talakawa , marar hankali muguwa.... kasa takawa Momy tayi haka shima Omar da bayajin zai iya ƙwatar Ummu a hannun Beenerfa saboda abun da tayi masa yake kullun ta . Fahad ne ke kokarin riƙe Beenerfa amma sai shirme take masa da hauka dukan Ummu kawai take ya tare da kwalleta da mari....Kee Wacce irin muguwar yarinya ce ? Taji wani irin Murya na in a Arrogannt voice ya daka mata tsawa tare da fincikar Beenerfa yana wurgi da ita ɓarayi guda , Dukan da Ummu tasha yasa ta fizagar Beenerfa da akayi tayi baya zata faɗi ,cike da zafi da kuma zafin Nama Nurein ya riƙo ta....!


Ware lulun idanun ta tayi tana zuba su akan Fuskar Nurein ,sai Hawaye sharrr³ . Hannun sa yasa yana gyara gashin kan ta da ya rufe mata fuska daƙyar take iya ganin su . Wani irin Ƙarar ihun Beenerfa yasa Nurein juyowa a fusace yana cewa" Ki mun shiru ko nazo na tattaki anan ." Gummm cike da tsoron sa Beenerfa tayi shiru kamin ta juya tana kallon Mom Salma tana ƙara rushewa da kuka .

Omar ne ya katse Nurein da faɗin " Tarkata ka bar gidan nan ,ka koma gidan ku , Ina yawan ja maka kunne akan Beenerfa , ina ruwan ka ,in ma kasheta tayi ai yar aikin gida ce ,ko tana da abun da zata iya yi ne ,ita ko iyayen ta ?.


Huuuuhhhh Sauke Numfashi Nurein yayi tare da furxar da iska , haushi ne ya Kamasa kurar da Farouk yayi masa daga gidan su . Cike da kunar rai yace " Ohk Yah Farouk zan tafi gidan mu ,dama nasan ai nan ba gidan mu bane na tafi . Yana faɗin haka ya juya a fusace yana barin falon . Mom Salma ne tayi saurin kirar sunan Nurein Amma ina bai ma san tana yi ba don yayi nisa da nufar parking lot .


What's This , All this for What?? Meye Haka Omar? Abun da Nurein ya fadi ai gaskiya ne....malam kaima jeka Abun ka . Omar ya katse Fahad da yake shirin shiga daga tsini. Beener kuwa nufar Mom Salma tayi , yayin da Mom ta rungume ta tana shafa bayan ta alamun rarrashi . Kama ta tayi tana hayewa da ita Up stairs tare da cigaba da rarrashin ta . A hankali Ummu ta tsuguna a nan wurin ƙwallah duk ya gama ɓata mata fuska . Malam jeka Abun ka .okay Sorry My boss . Fahad Yayi maganan cike da zolaya yana juyawa tare da barin falon.

Please Login or Register in order to submit comment