Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hafeeza Saudia ranar sauka?"

Inna ta gyada kanta da sauri sannan tace" naji de,Alhaji waye da sunan sa? Alhaji Ali ko?"

Kawu Hamza yasake yin murmushi sannan yace" Alhaji Isa Yunusa de, to yaturo min mutane jiya akan yana neman auren Hafeeza"

Gaban Hafeeza yayi wata irin faduwa,cikin sauri ta dago kanta ta Kalle shi.

Kawu Hamza yaci gaba da fadin" To Alhamdulillah gaskiya mutanan daya turomin mutane ne masu dattako,na tabbatar idan ta aure shi zasu riqeta da daraja,to amma banyi gaggawar amince waba, nace yarinyar nan Amana ce agareni, marainiya ce, zan tuntu6e ta inji ta bakinta, saboda haka Yaya kike gani keta Rasulu tunda yanzu kam kece mahaifiyar ta"

Inna tace"Ahhh Hamza ni kuwa me zance? ai data auri wannan tsohon saurayin nata baqin maqaryaci Gaddafi,gara taje gidan wannan din, ko banza zata sauya,zata samu Cima me kyau, kana gani daga zuwa Saudia yanda ta koma kamar balarabiya,ai bazan so Hafeeza tayi aure agidan wahala ba, ai tana ganin yanda muke fadi tashin rayuwa"

Kawu Hamza yace"to nima de abinda nagani kenan, kina ganin yanda yake rawar jiki akan ta,yace Idan har ta amince zai tafi da'ita Abuja,bazai hadata da Matan sa ba,Matan sa uku, itace zataje ata hudu,kuma kinga yace bazai hadasu ba, Abuja zasu wuce anayin auren"

Inna ta washe bakinta tare fadin" Abuja de danakeji? a a, a a, to ai shikkenan,Allah ya basu Zaman lafiya, Allah yasa ayi damu"

Hafeeza ta kalli Inna ganin ita harta amince da wannan maganar, yanzu Yaya zatayi da wannan tsohon, kenan tanaji tana gani haka zata aure shi? Tasan cewa tabbas Gaddafi yanzu baida halin yin aure, shima ta Kansa yake,kawai qarya ce tasa yake nuna cewa shi yanada kudi,yanzu Yaya zatayi?.

Kafin tagama tunanin da take taji Kawu Hamza ya juyo gareta yace"Hafeeza Yaya kika gani?, kina son sa?"

Hafeeza taji kamar andoka Mata Sanda akanta, batada wani za6i a yanzu, dade ace ta auri wannan Sanatan Gara ta auri Gaddafi sau dubu, cikin da kewa ta dago kanta ta kalli kawu Hamza sannan tace" Kawu ni GADDAFI nakeso"

Kafin Kawu Hamza yayi magana Ta Rasulu tace"Gaddafi dai Hafeeza? Nina rasa me kika gani ajikin wannan yaron"

Kawu Hamza yayi murmushi ya juya ya kalli Inna yace"Gaddafi de wannan dan gidan Malam Usman?"

Ta Rasulu tace" shifa, yana nan bashida aiki sai qarya"

Kawu Hamza yayi murmushi tareda kallon Hafeeza yace"tashi kije, zan nemi mahaifinsa muyi magana dashi"

batare da damuwa ba Hafeeza ta wuce daki.
Ta Rasulu tabita da kallo tana Girgiza kai.


*** *** ***

Cikin farinciki yashigo dakin Hajiya Kaka, ya zauna daga gefen qafafunta kasancewar tana kwance ne akan gadon.
Qafafun nata ya dauka yad'ora akan cinyoyinsa yafara matsawa,sannan yadago Kansa ya kalleta yace"Kaka na tambayi yaran nan sunce min kina kwance adaki, nace me kika tara har Zaki shige daki ki kwanta?"

Hajiya Kaka ta Kalleshi tace" Bar batun na ajiye ko ban ajiyeba,tunda na ajiye wadda ta haifeka ai kasan nayi ajiya"(=ØÞ=ØFÞ)

dan yamutsa fuskarsa yayi sannan yace"naji... naji,ni wasa nake miki Kaka"

Hajiya Kaka tace"inma da gaske kake kar nake kallonka Hafeezu,daidai nake daku agidan nan,fadamin meya kawoka? dan nasan wannan zuwan naka akwai dalili"

farincikin sane yasake qaruwa yace"yawwa Kaka dama... am dama zan fada miki ne nasamu wata yarinya"

Cikin sauri Hajiya Kaka ta Kalle shi, sannan ta saka tafukan hannunta ta murtsika idonta ta tabbatar ba bacci take ba, ahankali ta yunqura tatashi zaune, sannan ta Kalle shi tace"Hafeezu mafarki nake koda gaske ne?"

hannayenta yakamo ya mintsineta, cikin sauri takai masa duka abayansa yakauce yana sakin dariya.
Hajiya Kaka ta daga hannayenta sama tace"Ya ubangiji nagode ma, Allah Abun godia ashe zanga wannan ranar ni Rabi'atu, Allah na gode ma"
Ta shafa Addu'ah sannan ta fuskanceshi da kyau tace"ka tabbata da gaske kake Hafeezu?"

Kansa ya gyada Mata, sannan yace" da gaske nake Kaka, ina sonta sosai"

"gaskiya na yarda kana sonta tunda harka iya bude baki da kanka ka fadamin, yau wacce rana, Alhamdulillah, amma 'yar waye? inane gidansu?"
Cikin kunya yadan shafa sumar Kansa yace"Kaka aikin santa ma, qawar yarannan ce, yarinyar da tazo wajan su kwana ki, Hafeeza"

Cikin tsananin mamaki Hajiya Kaka ta rufe bakinta da hannayenta sannan ta bude tace"Almiri,ni nasan awajan saukar nan Kaine katura Mata wannan kudin ko?"
Cikin salon shagwa6a yace" Kakaaa"

Kaka tayi murmushi sannan tace" to shikkenan naji, aiba laifi bane hakan Hafeezu,ladanka yana wajan Allah"

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan yasake matsa hannayenta dasuke cikin nasa yace"tun ranar da nazo na ganta, ina yawan bibibyar ta,itace take saida qosan da'ake siyo miki, tana cikin halin rashi Kaka, sannan sana'ar datakeyi itace tasake jefa min tausayin ta araina, da wannan hannayen nawa nayi irin wannan sana'ar datakeyi, waje-waje nake yawo da qosai akaina... "

ya qarasa maganar yanayin sa yana sauyawa, yayinda ya zubawa tafukan hannunsa ido yana kallonsu.

jikin Hajiya Kaka yayi sanyi,tasaki Ajiyar zuciya sannan tace"kadena tuna baya, ka fuskanci gaba, nasan cewa idan mukaje nema maka auren ta akwai qalubalen da zamu fuskanta,nariga nasan rade-radin da'ake agari a kanmu"

maimakon yabata amsa saiya sauya akalar maganar tasa zuwa wani abun daban, ya kalleta yace"amma Kaka ai kin yaba da hankalinta ko?"

Cikin gamsuwa Hajiya Kaka tace"sosai, ai naga tanada nutsuwa babu laifi,amma de abunda yake damuna daya ne, naji yaran nan su Hassana suna cewa tanada kwankwaso yarinyar, inji de ba abinda yakaika kenan ba ko?" (>ØÝ)

Wani irin kallo yayi mata ya Girgiza kansa,sannan yace"saida safe"

Hajiya Kaka tasaki dariya ita kadai,tana sake daga hannu tana godewa Allah.

Kawu Hamza ya kalli Malam Usman bayan sun gama gaisawa dashi yace"Maganar yarinyar nan marainiya yar wajan Yayanah haladu marigayi ce ta kawo ni, to kasan yaron wajanka Gaddafi yana zuwa wajanta zance, to abinda yake faruwa shine, akwai manemi da yarinyar tasamu, na zauna da'ita nayi Mata maganar sa, amma ta nunamin batason shi wanda yafuto din, yaron wajanka Gaddafi takeso, to shine nazo dakaina, kasancewar yanzu ita amana ce awajena, koda mahaifinta yana raye, ni zai wakilta wajan wannan al'amarin, banaso manemin nata yazo ya da maganar turo wa gida kuma mu ce munyi Mata miji alhalin kuma babu wata tsaiyayar magana daga wajan ku, saboda haka idan da gaske yaron wajan naka yake nabashi dama yafuto"

Malam Usman yayi Ajiyar zuciya yace"wallahi Malam Hamza tunda naji labarin Gaddafi yana zuwa wajan Hafeeza awajan qannansa,nake cikin farinciki da wannan alaqa saboda nasan cewa Gaddafi yaza6i yarinya gidan tarbiya uwa uba kowa kwatance yake da Hafeeza musanman a makarantun Islamia,Hafeeza babu ruwan ta kowa yana yabon halayen ta, saide wani hanzari ba gudu ba, inda ace inada wani yaron Babba toda nida kaina zan bashi Umarni yaje ya auri Hafeeza amma ba Gaddafi ba, saboda yanzu haka maganar danake ma Gaddafi sonake yakama hanya yatafi kudu neman kudi,shi kuma bayaso yafi so ya zauna yana bibibyar wadannan Yan siyasa yau wannan yabasu dubu Ashirin wannan yabasu dubu biyar dubu goma, ina rayuwa zata iyu dahaka Malam Hamza?"

Kawu Hamza ya jinjina Kansa sannan ya dago ya kalli Mahaifin Gaddafi yace" to ita de Wannan yarinya Hafeeza ta nuna shi takeso, kuma kasan su Mata da kunya amma yarinyar nan haka ta ajiye kunya ta bude baki tacemin ita sai Gaddafi, yanzu babu wata sana'ah dayake yine ko min qanqantarta wadda zai iya riqe yarinyar?"

Malam Usman yace" Bashida sana'ah,kaga saboda shi bai kamata a dakatar da wanda yafuto yanzu ya shirya ba, tunda kun tabbatar wanda yafuto din da gaske yake to ita mace ce, wanda yafuto ai dashi za'a yi, ba za'a jira Wanda ko muhalli bashi dashi bare sana'ah ba"

Kawu Hamza yace"hakane, toba damuwa Malam Usman godia nake"

Malam Usman yabashi hannu suka sake gaisawa sannan ya juya yatafi.


*** *** ***


Hajiya Kaka ce ta shigo falon ta zauna tareda fadin "wash Allah, wannan qafafu nawa sun riqe kamar wanda nayi doguwar tafiya"

Husna datake cin abinci ahankali kamar bataso ta kalli Hajiya Kaka tace"harna gama girki kina maqota a kwance"

Hajiya Kaka ta kalleta a sheqe, cikin gatse itama tace" eh wallahi bacci nake sai yanzu nafarka"(=ØÞ)

Husna tata6e baki taci gaba da cin abincin ta.

Hassana datake danna waya tatashi ta zauna tace"Hajiya Kaka har kin dawo?"

"nadawo Hassana, ina can muna tattauna wa da Alhaji Ali, akan maganar neman auren yayanku"

Cikin sauri Husna ta ajiye spoon din hannunta, yayinda Hassana ta ajiye wayarta har hada baki suke suna tambayar "wanne yaya?"

Kaka tace"Hafeezu mana,yazo ya sameni yace yana son wannan qawar taku Hafeeza,shine naje gidan Alhaji Ali nafada masa, ko zai tambayo mana idan ba'a yi Mata miji ba"

ihu suka saki gaba dayan su,sannan suka hada hannu suka tafa, Hassana tace"Yaya zai huta wallahi"(=ØHÞ)

Hajiya Kaka tayi Mata daquwa tace"Hassana gidanku,Allah yasa yajiki keda shine"

Husna ta jinjina kanta tace" tabdi, lalle Yaya, kiga ranar da tazo gidannan yawani basar kamar baisan taba?"

Hassana tace" to Husna ai bakisan wani abuba, inaga fa sun dade da shirya wa, damukace tafada mana irin mijin datake so ai gaba daya suffar Yaya Hafeez ta zayyano mana"

Husna tace"wallahi hakane,ko tayaya suke zance?"

suka sake kwashewa da dariya.

Hajiya Kaka tace"Allah ya shirye ku"


*** *** ***


Kawu Hamza ya kalli Hafeeza, bayan yagama kwashe labarin abinda yafaru tsakaninsa da mahaifin Gaddafi ya fada Mata, sannan yaqara da fadin"saikiyi haquri ki kar6i shi Alhaji Isah da hannu bibbiyu, ke malama ce,kinsan ayar datake magana akan mafi yawan abinda mukeso yana iya zama sharri agaremu, wanda bama so kuma sai ya zama alkhairi agaremu, nayi magana dashi yace zaizo yaganki kuyi magana ku fahimci juna idan kunyi maganar saiya turo magabatan sa"

tunda kawu Hamza yafara wannan maganar Hafeeza kanta yake qasa,jikinta ne yayi sanyi bayan kawun yagama tunatar da'ita ayar da itace ya kamata ace tafada masa ita.

Cikin biyaiya tace"to kawu, Allah yasa hakane yafi Alkhairi"





Complete document 1k


8621296018
Amina Muhammad
fcmb.

kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034






Amnah El Yaqoub
'þ
[6/14, 2:26 PM] El Yaqoub:

Kawu Hamza yace"Amin ya Allah, Allah yayi miki albarka, idan yazo din duk yanda ku kayi dashi zanzo sai inji me kuka tattauna"

Hafeeza ta amsa Masa cikin ladabi, sannan ta shige daki.

Bayan kawu Hamza yatafi Ta Rasulu tabi bayan Hafeeza ta ganta a zaune agefen d'an qaramin gadon su tayi shiru, zama tayi Akusa da'ita sannan tace"yanzu Hafeeza 'yar Habujar damuke kwadayin zuwa Zaki mana manaqisa?,banda abun ki abinda Hamza yakeyi akanki aiko wadda ya Haifa acikinsa sai haka, Hamza ko wuta yace ki shiga Hafeeza banajin kinada za6i, bare ma shi wannan sanata kina gani de qoqarin da yayi miki, kika bibiya ma wannan miliyan biyar din da'aka rasa wanda yabaki nasan shine zai bayar saboda Kar talakawa Irina mu dinga tsine masa muna cewa kudin mu ne shiyasa ya6oye sunansa, kiyi haquri mana Hafeeza"

Hafeeza tace" to ni Inna menace? wallahi na amince dashi har raina"

Cikin farinciki Ta Rasulu tace"yauwa, Allah yayi miki albarka"

*** *** ***

washegari da yamma Ta Rasulu tana zaune daga falo tana ganin yanda Hafeeza take aiki kamar bataso, ta daga murya tace"Hafeeza kiyi da jikinki mana Kar yazo baki gama girkin ba, Babban Mutum irin wannan yaushe zaizo ki barshi yana jira, nida kinji tawa ma dafadukan taliya zakiyi masa kisa masa dan kifi aciki, amma kin tsiri dafa masa Shinkafa"

Hafeeza ta kalli Inna tace"to Inna yanzu ai Shinkafar tafi tsada, muma ita mukeci, shima idan yazo saiyaci"

Inna tace"ai shikkenan"

sosai Hafeeza ta nutsu tadafawa baqon nata Shinkafa da miyar qwai, sai lemuka data siyo masa dakuma ruwan gora.
saide baisamu damar zuwa ba sai bayan magrib, baqar Abaya ta saka me kyau irin wanda ta siyo a Saudia,sosai rigar tayi mata kyau, sai zuba qamshi take kamar amarya, ta juya zata tafi Ta Rasulu ta tsayar da'ita tasake fesheta da turaruka,sannan tatafi.
tana futowa qofar gida taga wata hamshaqiyar Mota aqofar gidan,daga jikin motar ta tsaya tareda qwanqwasawa, shima daga cikin yabude Mata tareda fadin"qaraso mana"

mamaki ya kama Hafeeza, tayi tunanin zai futo ne su qarasa cikin gidan, duk da haka batayi qasa a gwiwa ba, tashiga cikin motar, tana shiga ya rufe motar tareda kallon ta cikin murmushi yace"kinsan ba kowane yasan nazo garin ba, ina buqatar privacy"

Hafeeza ta Kalleshi, Babban Mutum ne sosai,shi kadai ma yacika kujerar dayake zaune,cikinsa kuwa qwarya guda kamar me shirin haihuwa, kanta aqasa batare data Kalle shi ba tace"ina wuni?"

Cikin wani irin Jin dadi sanata yagama qarewa jikinta kallo sannan yakai hannunsa ya ruqo ha6arta yace"dago ki Kalle ni mana Baby"

Wata irin faduwa gabanta yayi, ganin yanda ya Kamo ha6ar tata batare da wata damuwa ba, ahankali takawar da fuskar ta gefe, hakan yasa hannun nasa ya zame daga kan ha6ar tata, saide maimakon ya janye hannunsa saiya saukeshi kai tsaye akan nashanunta, cikin sauri ta Kalleshi, jikinta yafara rawa, shi kuwa hankalinsa kwance yake kallonta saima murmushi dayake zubawa yanajin dadin yanda yaga ta tsorata saboda yanda yad'ora hannun nasa akan nashanunta hakan ne yasake tabbatar masa da cewa shine zai koya Mata harkar,da alama bata ta6a aikata hakan da wani ba.
Cikin 6acin rai Hafeeza ta Dora hannunta akan nasa tafara qoqarin janye masa hannunsa akan nonuwanta, murmushi ya saki maimakon ya dauke hannun nasa saida ya matsa Mata da qarfi, sannan ya saki.

baqin ciki ne yasata fashewa da kuka.

Cikin tashin hankali ya gyara zamansa,sannan ya sassauta murya yace"Haba Baby, menene abun kuka kuma? to kiyi haquri kiyi shiru kinji Baby na, hakan bazata sake faruwa ba kinji?"

ahankali ta gyada kanta alamun amsawa, saide gaba daya jikinta rawa yake, ta sare da al'amarin sa.

ganin ta daina kukan hakan yasa yace"to goge hawayen ko?"

ahankali tasa gefen mayafin Abayar jikinta ta goge hawayen, sannan ta Kalleshi tace"nayi tunanin zaka shiga gida ne, meyasa kakeso ka koya min abinda kai kanka kasani Allah subhanahu...."

Cikin sauri ya dakatar da'ita yace"Dakata Hafeeza, ya kike wani abu kamar baki wayeba? duk Yara sa'anninki yanzu sun San haka rayuwar takoma, menene aciki? bafa komai bane dan romance ne kawai,ki kwantar da hankalin ki, Zaki samu kudi sosai, ki saki jiki musha soyaiya kafin a daura auren, ni mutum ne Maison soyaiya a aikace, banason nuqu-nuqu naku irinna malamai, saboda haka karki fara yimin wa'azi, yawwa ki saki jiki ki kwashi kudi iya rabonki, inaso ana daure aure mubar qasar muje qasar waje nasake bude miki ido akan harkar kingane?"

Hafeeza da jikinta yake rawa cikin sauri ta gyada kanta, jitake kamar ta zura da gudu zuwa gida, Babban Mutum da yayi jika da'ita shine yake fada Mata haka.

ganin ta amince da maganar tasa hakan yasa yace" yaushe zakuyi musabuqa ta jiha? ko bakyason musabuqa?"

muryar tace tafara rawa,ahankali tace"ba'a fara maganar musabuqa ba, idan anfara idan na cancanta makaranta zata dauka dani"

Cikin sauri yace"wanne irin cancanta kuma? tunda kina dani ai kin gama cancanta Baby, zakiyi musabuqa kuma zakici saboda zan tsaya miki,bayan ta jiha ma harta qasa saikin je, kinji?"

Cikin nutsuwarta ta gyada masa kai, sannan ta Kalleshi tace" nagode, ni zan shiga gida"

Hannunsa yasaka a aljihunsa ya dauko damin kudi Yan dubu daya, kimanin dubu dari, sannan ya miqa Mata yace"Gashi Kisha Chocolate ko?"

Cikin sauri Hafeeza tafara Girgiza kanta, gefe daya kuma tana qoqarin bude Motar.

Cikin sauri yace" ki kar6a mana, yanzun nan fa nagama cewa ki saki jikinki kisamu kudi,inaso na maidake babbar yarinya,very soon zan siya miki Mota, Zaki kai iyayen ki dukansu makkah keda kanki, sannan duk lokacin dakike buqatar kudi kawai kimin magana kinji?"

Hannu biyu tasa ta kar6i kudin sannan tace" nagode, Allah yaqara budi"

Cikin Jin dadi yace"Amin ya Allah Baby,dadi na da malamai akwai Addu'ah"

Dan murmushin yaqe tayi sannan ta bude motar, cikin Jin dadi ya kalleta yace"kinga"

ahankali ta juyo, aikuwa ya huro Mata kiss, sannan yace"idan kinje gida kidan turomin photon wannan abun dakikai min rowa kika hanani matsawa dakyau"

gabanta ne yasake faduwa,wanne irin mutum Allah ya hadata dashi? cikin sauri ta gyada masa kai, sannan tafi ce tareda rufo masa motar.

tana shiga gida Ta Rasulu data kafa ta tsare a tsakar gida ta kalleta tace"ke yana ganki kamar bakya cikin hayyaci? Ina baqon naki yake?"

Kudin hannunta ta bata sannan tace" yatafi Inna, kuma gaskiya ni bazan aureshi ba, bazan iyaba,wallahi dan'iska ne, kwarto ne"

Ta Rasulu ta kamota ganin kamar bata cikin hayyacinta,tace" Hafeeza Kalleni nan, meya miki? yayi miki wani abu ne?"

Hafeeza ta dafe kanta da hannunta ta rasa me zata fadawa Inna,to me zata ce? cemata zatai yata6a Mata nono ya huro Mata kiss sannan yace taturo masa photon nono?, cikin tashin hankali ta Girgiza kanta sannan tace"nide dabi'unsa basu min ba,bana son sa kawai"

tana fadar haka ta wuce daki, ta Rasulu ta kalli dubu Darin datake hannunta sannan ta daga murya tace"shashancin banza, to tunda ba jikinki ya ta6a ba, menene zaisa kiqi aurensa? aikuwa aure dole"

Hafeeza de tana jiyota daga daki,kanta har wani sarawa yake saboda damuwa, bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba, iskanci qiri-qiri azahiri?,da farko tayi tunanin zai dauki nasiha da wa'azi shiyasa tafara qoqarin tunatar dashi, ashe yariga yayi nisa, hannunta ta kai kan breast dinta taji yanayi Mata wani irin ciwo sakamakon matsawar da akamai yanzu bata hankali bace, tashi Tayi tagabatar da sallah ta kwanta sakamakon wani zazza6i daya rufeta.

washegari bayan tayi sallar asuba bacci takoma, sosai take bacci sama-sama taji Inna tana kiran ta, ahankali tatashi zaune, Ta Rasulu tace"kizo Hamza yana jiranki, kin kwanta kina faman bacci har qarfe Tara tayi"

ahankali Hafeeza tatashi,tana futowa tsakar gida ta tsugunna ta gaida shi ya amsa, sannan tatashi ta Debi ruwa tashiga bayan gida,tafuto daga ciki bayan ta wanke bakinta, ta zauna agabansa tace"gani kawu"

Kawu Hamza yace"Hafeeza, jiya Alhaji Isah yazo,munyi magana dashi yacemin kun gama daidaitawa,yanzu kuma na shigo sai Ta Rasulu take min wata magana cewa kince ke bakya sonsa, bayan kuma jiya ba haka mukai dake ba,menene yake faruwa?"

Hafeeza tayi shiru ta rasa abun cewa,tariga tasan cewa haqqin uba ne akan ya nemawa yayansa uwa ta gari, haka itama yanzu haqqin tane ta nemawa yaran ta uba nagari, kuma abinda yafaru tsakanin ta da wannan bawan Allah bai kamata ta sanar dasu ba, saboda duk wanda ka rufawa asiri kaima Allah zai rufama, wannan bawan Allah bai dace daya zama uban 'ya'yanta ba, domin kuwa duk abinda ya aikata da'ita dole sai anyiwa yayansa,ba wannan bama, kafin ita tasan adadin yaran mutane nawa yagama lalatawa? inda ace bashida wannan halin haqiqa zata yiwa kawu biyaiya ta aureshi, to amma wannan dabi'ar tasa bata sababa, bazata iyaba.

Kawu Hamza ya katse Mata tunani yace"kinyi shiru Hafeeza,meyake faruwa ne?"
Ta Rasulu tace" ta fadi dalili kam muji, nan ta shigo min gida kamar mahaukaciya tana cewa ita bata sonsa, to ai kinji yanda akai da iyayen Gaddafi, ba aure zaiyi yanzu ba saboda bashida ko sisi saide qarya kawai, Shikuma wannan ai ba zamu hanashi ba kuma musaki agaba mu dinga kallonki bayan ba wani ne dake ba, Habuja de kike mana manaqisa ko? to kije kin kyauta"

Kawu Hamza yace"Ta Rasulu ya'isa, kibarta tafadi dalilinta na cewa tafasa"

Hafeeza tasake sunkuyar da kanta qasa sannan cikin nutsuwa tace"kawu munyi magana dashi sosai, shide ya fahimce ni, amma maganar gaskiya kawu nide ban fahimce shi ba, dabi'unsa basuyi daidai da nawaba"

"nide gaskiya dabi'unsa basuyi daidai da nawaba, yen yen yen kaji ta sai kace yar gidan shugaban qasa, nan kuwa ubanki Haladu ko dangi bai hada da Kansila ba" (=ØÞ)
cewar Ta Rasulu.

Kawu Hamza yace"ya'isa mana Ta Rasulu"

Ta Rasulu tace"nayi shiru Hamza,Abun ne yake qonamin rai wallahi,ga arziqi yana kiran ta amma tana neman liqewa Gaddafi, kuma bazata watsa mana qasa a'idoba, dole ta aureshi"

Hafeeza tana Jin furucin Inna ta fashe da kuka tace"Allah kawu nide bana sonsa,kabani koma waye nayarda"

Ta Rasulu tafara tafa hannaye cikin mamaki.

Kawu Hamza yace"to naji, yanzu kinga shi wannan bawan Allah Babban Mutum ne, bazai iyu bakida wani tsayaiye, mukuma muce masa kinadashi ba, idan akwai wani daban bayan Gaddafi, saiki fada mana muji"

Hafeeza tayi shiru sanin da tayi batada kowa,dama Gaddafi ne, Shikuma ga abinda mahaifinsa yafada, sannan shi wannan dan majalissar da'ake maganar sa bazata iya aurensa ba, ina ta dosa yanzu? nan take wata zuciyar tace Mata ga Hafeez..., kanta ta Girgiza ahankali domin kuwa shima Hafeez din daga ganin sa turawa sun gama yimasa huduba duba da yanda yake yawo da dan kunne akunnansa, ga Zane dayake yi a jikinsa kamar ba musulmi ba, saide kuma akan de ta auri wannan d'an siyasar har Gara Hafeez din.

Ahankali ta dago kanta ta kalli kawu Hamza, kamar an qwato maganar daga bakinta tace"Kawu ni HAFEEZ nakeso"

Kawu Hamza kokadan bai kawo Hafeez aransa ba,saboda tun lokacin da sukai rabuwar rashin arziqi shida Hafeez ya tattara yaron ya ajiye agefe, lokaci daya shida Inna ta Rasulu suka kai dubansu gareta.

Cikin rashin sani Kawu Hamza yace"waye hakan kenan?"

Gaban Hafeeza yafara luguden fad'uwa ganin irin kato6arar da tayi saboda batada tabbacin cewa shi Hafeez din da gaske yake sonta, da aure yake son ta kamar yanda ya fada kokuma da soyaiya yake sonta.
Cikin in-ina tace" kawu shi din Yayan qawayena ne,acan layin yake,kusa da gidan Alhaji Tafida''

Tana qarasa fadar haka kawu Hamza ya zuba Mata ido yana kallon ta,tana cewa layin gidan Alhaji tafida yariga ya gane yaron da take nufi, saboda Akusa da gidan masallacin dayake zuwa sallah yake, kuma Akusa da masallacin yayiwa shi Hafeez tayin auren Hafeeza.

Ganin kawu Hamza ya zuba Mata ido yana kallon ta yasa Hafeeza tayi sauri ta sunkuyar da kanta qasa.
Inna ta Rasulu ta jinjina kanta sannan tace"waye kuma Hafeezu? yaushe kika hadu dashi bansani ba Hafeeza? Kuma Yaya akai har kikasan gidan su? kede nasan wannan layin ba wajan zuwan ki bane"

Hafeeza tayi shiru itade kanta yana qasa, shi kuwa Kawu Hamza har lokacin baice komai ba, Inna ta Kalle shi tace"kayi Shiru Hamza"

Ajiyar zuciya ya saki yace" Ta Rasulu bakisan gidan Hajiya Rabi'atu ba?"

Inna tayi shiruuu sai can tace" nagane ta, tabbas nagane ta,wadda take zaune tareda jikokin ta ko?"

Kawu Hamza yace"tabbas,ai abinda zanyi magana akai kenan,yaron nan da Hafeeza take maganar sa dan gidan ne, shima jikan Hajiya Rabin ne,kuma ni dashi mun zauna nayi masa tayin auren Hafeeza amma yaron nan firr yaqi,ya nuna min baya sonta, qarshe ma cemin yayi idan yarinyar tawa tanada ma nema to in batasu, shine yaron danake baki labarin sa kwanaki"

Cikin sauri Hafeeza ta dago kanta ta kalli kawun nata,kanta ya daure,yaushe akai haka? Kuma Hafeez din? To menene amfanin zuwansa wajan ta kenan? inde yariga ya fadawa kawun ta haka dama yaudara ce ta kawo shi wajanta kenan?

Kafin tagama tunanin da take Inna ta Rasulu tace"to kode bashi bane qaninsa ne?"(=ØÞ)

Cikin tabbatar wa kawu Hamza yace"Shine"

Inna ta gyara Zaman ta sannan ta kalli Hafeeza da kanta ke qasa har yanzu,ta dawo da kallon ta wajan Kawu Hamza sannan tace" tonikam Hamza tun farko ma dakace min kaje wajan sa da maganar Auren Hafeeza nake ta tunanin dalilin zuwanka wajansa? yaron da ake yawo dashi agari ana cewa baya mu'amular kirki shida iyayensa?"

Kan Hafeeza ya Sara,tafara tambayar kanta da gaske baya mu'amular kirki da iyayen nasa? tatuna lokacin da suka hadu a Saudia, agabanta mahaifiyar sa takirashi yakai sau uku,amma baya dauka, sannan lokaci daya taga yanayin fuskar sa ya sauya saboda ganin kiran, tayi tunanin ko me mutum yake muddin mahaifiyar sa takirashi to dole zaibar abinda yake ya saurari kiran mahaifiyar sa.

Inna ta kalli Hafeeza sannan tace"to kinji de anyi masa tayin aurenki yace bayaso,sannan Nima shaida ce kaf layin unguwar nan babu wanda baisan cewa yaron nan anyi masa shedar baya mutunta iyayensa ba,to wanda bai bawa iyayensa mutunci ba tayaya kike tunanin ke Zaki samu girmamawa daga wajan sa? me zaki dashi ?"

Kawu Hamza yace"to nima de abinda nagani kenan, ban duba wannan surutun ba nataka qafa ya qafa naje har inda yake nayi masa tayin auren ta, amma yaron nan yace bayaso"

Inna tayi ajiyar zuciya tace"to ai shikkenan,dama Bansan inda ta debo Shiba,kasan Allah Hamza, Allah daya ne bansan inda Hafeeza ta hadu dashi ba, saboda ita ba yawo take ba"

Tamaida kallon ta wajan Hafeeza tace"wanne irin aiki yake ne? ko shima a Habujan yake?"

Kan Hafeeza aqasa tace"a a Inna,awata qasa yake aiki"

Cikin sauri Inna ta dafe qirjnta sannan tace"wata

Please Login or Register in order to submit comment