Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai sakewa da mutane bane, musanman yanmata, amma gashi a zaune dab da yarinyar kuma ko a jikinsa.

Ta kalli Hafeeza taga kamar atakure take da Zaman, ta zauna tareda fadin" 'yar nan cire hijabin naki mana kisha is'ka"

Hafeeza tatuno maganar Maman Fadila da take cewa abinda yagani ne ya dawo yaqarasa gani, Wato ta cire hijabi yanzu ma yasake kallon qirjinta, ahankali ta danyi murmushi tace" a a babu damuwa Kaka"

Hajiya Kaka tace"tokici abinda qawayen naki suka kawo miki mana,ko adafa miki wani abincin?"

Cikin sauri Hafeeza ta Girgiza kanta, batare da tayi magana ba.

Hajiya Kaka tayi murmushi, gaba daya tagama karantar yarinyar a firgice take, ta kuma tabbatar saboda Zaman Hafeez Akusa da'ita ne, cikin son Jan magana tace" ni qosai Naso ci kuma sunje nemomin basu samu ba"

Hassana ta kawo wa Hafeez Coffee ta'ajiye agaban sa.

Ahankali yasaka hannu ya dauki coffee din sannan ya kalli Kaka cikin maganar sa me aji yace"Aina fada miki tadena,ba zatayi ba"

Gaban Hafeeza ya Yanke ya fadi ganin akanta ake maganar.

Hajiya Kaka tace" ko zatayi ma abaqin miskilancin ka ai zaka min baki taqiyi, kaide Matarka ta shiga ukunta da baqin miskilanci"

Hafeez yayi sipping Coffee din hannun sa sannan yajuyo yana satar kallon Hafeeza,duk da cewa ta kasance tana masa kwarjini yarinyar Gara yayi kokari ya kawar da hakan aransa kada yan maza suji kunya.


Wannan Karon ma sun sake hada ido shida ita,hakan yasa cikin ranta ta Yanke shawarar tafiya gida, kafin ta miqe Hassana tace" Hafeeza yaushe ne tafiyar ki Saudia?"

Cikin murmushi ta Kallesu tace"bazan wuce sati biyu ba"

Hafeez yajuyo Kansa tsaye ya kalleta, sannan ya ajiye Coffee din ya tashi yafice daga falon.

Yanajiyo Hajiya Kaka tana cewa "to nide Abayar da Zaki siya kiyiwa saurayin ki ado da'ita, Nima irin ta Zaki siyo min"

Hafeeza tayi murmushi ta miqe tsaye tace"Kaka duk abinda nasiyo kema naki daban zan siyo miki"

Hajiya Kaka tace" to Allah yayi muku albarka, Allah yabaku mazaje nagari"

Hafeeza tace"Amin Kaka,zan tafi gida kada anemeni"

Su Husna suka kwashe duk kayan snack din da suka kawo Mata da lemuka suka zuba Mata aleda, sannan suka rakota bakin get sunata tsokanar ta,daga bakin get din ta dakatar dasu saboda babu Nisa sosai tayi musu godia bayan sunsha Fama da'ita kafin ta karbi snack din da suka biyota dashi.

Zuciyarta daya ta futo daga gidan ta dauki hanyar gida tareda ajiyar zuciya tanajin wani irin dadi saboda cikin gidan atakure take kasancewar Hafeez yana wajan.

Ba tayi nisa sosai ba kawai taga mutum agaban ta,qiris ya rage su hadu da juna hakan yasa tayi saurin yin baya,hannunsa ya harde a faffadan qirjinsa ya zuba Mata narkakkun idanunsa, gabanta ne ya fadi ganin irin kallon dayake Mata,ahankali ta matsa zata wuce ta gefensa cikin sauri yasake shan gabanta, Hafeeza ta kalli ko'ina taga layi shiru babu mutane, gashi tana tsoro kada yayi mata wani abu,kuma dama Maman Fadila tafada mata cewa idan zatazo wajan sa kada tatafi ita kadai, to dawa zatazo bayan ita ba wasu qawaye ne da'ita ba?
Cikin dauriya ta dago kanta ta Kalle shi tace" kabani kudin Inna zan kai Mata"

Haka nan Hafeez ya tsinci Kansa dajin dadin yanda suke maganar su biyu,cikin wani irin nishadi yace"wanne kudi?"

Hafeeza ta lumshe idonta cike da damuwa sannan ta bude shi akansa,Hafeez yazubawa qwayar idonta kallo me kama data mage,cikin sauri dakuma qaguwa da tsaiwar ta awajan tace" Kabani"

Wani miskilin murmushi yasa ki,yanayin yanda tayi maganar cikin fishi sai hakan yasake birgeshi, duk da gabansa yana dan faduwa sakamakon rashin Sabo, hakan ya daure yajefo Mata tambaya, yace"Babyn wa kika kai asbiti rannan?"

Gabanta ya Yanke ya fadi,cikin taqaici ta runtse idonta sannan ta bude tace"Malam Kadena min wannan maganar,bana so!!"

Ta qarasa maganar cikin tsananin 6acin rai dakuma quluwa.

Hafeez yadan shafa sumar Kansa sannan ya kalli layin dasuke tsaye yace"gidannan akwai qaran Gen. , kina min bayanin Babyn dana ganku tare,sai naji kamar kince narabu dake"

Cikin 6acin rai Hafeeza tace"malam cewa nayi Kadena min wannan maganar, kabani kudina natafi "

Hafeez yace" waye zai baki kudi?"

Cikin sauri tace" waye zai bani idan bakai ba? "

"an rad'awa kudin cewa nine kawai mai ba dashi? nabaki kudin ki mana, kiduba nabaki"

"yaushe kabani?"
Cewar Hafeeza.

Hafeez yasaki ajiyar zuciya yace"kiduba rigar ki yana ciki,kokuma nina duba"

Ran Hafeeza yasake 6aci ganin irin rainin hankalin da Hafeez din yazo Mata dashi,yaushe yabata kudi? yaushe yasaka mata kudi arigar ta?

Cikin 6acin rai tace"Malam bazan duba ba kawai kabani natafi"

Cikin dakiya dakuma aji yasake matsowa dab da'ita, gabanta yasake tsananta faduwa har tana iya juyo numfashinsa akan fuskarta,cikin wata irin muryar rad'a yace"tsaya na dauko miki"

Bai saurari amsar ta ba yakai hannun sa cikin aljihun doguwar rigar da take jikinta,Hafeeza tanajin haka ta zaro idonta,cikin hanzari tafara kiciniyar qwacewa, nan da nan kokawa ta 6arke a tsakanin su, shi yana kokarin dauko Mata kudin daya Riga yasan cewa yasaka Mata kudin a jikinta, ita kuma tana kokarin qwace kanta tana so taraba kanta dashi,cikin azama tayi kokarin ruqo hannun sa mai cike da gashi,tayi Sama da hannun nasa zata bige hannun,Shikuma Hafeez a maimakon dawo da hannun sa cikin aljihun rigarta by mistek hannun sa yadan bige boob's dinta, laushin da yaji ne yasa yakai idonsa kan hannun sa,adede lokacin itama takai idonta kan abinda ko a mafarki bata ta6a tunanin kafin tayi aure wani namiji zai iya kai hannunsa wajan ba, atare suka zaro idonsu, cikin sauri Hafeez ya janye hannunsa, wata irin kunya ta kamashi,yakasa hada ido da'ita,hakan yasa Kansa aqasa yace mata" I'm sorry,pls I'm sorry"

Cikin sauri yabar wajan yajuya zuwa gida,ko takan motarsa da take ajiye agefe baibi ba.

Cikin tsananin baqin ciki Hafeeza ta tsugunna awajan ta fashe da wani irin kuka.

Lokaci daya,maganar Maman Fadila ta fad'o Mata, cewa idan zatazo wajan sa karta kuskura tazo ita kadai, sosai take kuka kamar anyi mata mutuwa, saida ta gama shan kukan ta kafin tamiqe cikin baqin ciki tanufi gida,kana ganin yanayin tafiyar ta dakuma fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a6ace yake.

Tana zuwa gida kai tsaye tanufi daki ko kallon Inna da take zaune cikin rumfa ba tayi ba.
Ta Rasulu ta kalleta tace"kin kar6o kudin ne?"

Ataqaice Hafeeza tace"A a"

Ajiyar zuciya Ta Rasulu tayi, sannan tace"dama bakida niyya"

Hafeeza tayi shiru batace uffan ba.
Ta Rasulu tasake kallon ta tace"kin zauna kinyi shiru sai zun6urawa mutane baki kike, kinyi waya da saurayin naki yau kuwa?"

Yanzunma a taqaice Hafeeza tace"A a"

Inna ta jinjina kanta tace"zan baki shawara Hafeeza,wannan saurayin naki dakika dora ranki akansa batake yakeba, duk lokacin da kikaje Saudia kawai kiyi Addu'ah Allah yabaki wani"(=)

Cikin sauri Hafeeza ta kalleta,ta rasa me Gaddafi yayi mata bata sonsa,bawani saurayi da zata roqa face tayi Addu'ah Allah ya tabbatar Mata da Alkhairi ita da Gaddafi.


Tana gama yanke wannan tunanin ta tashi tashige cikin daki tafara qoqarin cire kayanta domin shiga wanka, tana cire rigar jikinta taga wata takarda ta fad'o daga aljihun rigarta,cikin tsananin mamaki ta tsugunna ta dauka, tana budewa taga dala dari, gabanta yayi mugun faduwa, idan bata manta ba kwana ki anta6a fada musu cewa duk dala d'aya ta haura dubu da dari biyar, wannan mutumin Kansa daya kuwa? Meyake damunsa? mezatai da wannan kudin? Idan Inna tasani aita shiga ukunta, yaushe ma yasaka Mata kudin? tunani tatafi, ta tuna yanda yasake matsowa jikinta afalon gidan su, babu makawa a wannan Zaman yasaka Mata, shiyasa bayan tafuto yace yariga ya bata taduba jikinta, lokaci daya hannun ta ya dauki rawa, ta tashi ta saka dalar acikin kayanta, sannan tashige wanka.



*** *** ***


Acikin satin Hafeeza tatafi Saudia, gida ya rage daga Inna sai masu dan leqo mata suna dan tayata fira, sai kuma Maman Fadila tadake yawan shigowa tana kawo Mata Fadila duk da suna fafatawa kafin Inna ta kar6eta.

Duk wani motsin Hafeeza dayake Saudia Hafeez yana sani, satinta daya da tafiya da daddare yana kwance adakinsa bayan yagama shirin bacci yadokawa Ma'aruf waya.

Daga can 6angaren Ma'aruf ya kalli wayar sa cikin tsananin mamaki ganin shabiyu saura, cikin sauri ya dauki wayar, Yace"Hafeez lafiya kake kuwa?"

Murmushi Hafeez yayi yace" lafiya ta kalau Ma'aruf ,inaso muyi sallama ne gobe zan tafi Saudia"

"zakaje Umarah ne?"

Cikin aji yace"zanje Umarah da neman iri,akwai yarinyar da take hargitsa min lissafi Ma'aruf,inajin abubuwa dayawa akanta"

Ma'aruf dayake kwance agadonsa ya tashi zaune tareda dora fillo akan cinyarsa cikin tsananin murna yace"wow,wacce me sa'ar ce wannan?"

Hafeez yasake juyi akan gadonsa cikin jin dadi,wannan firar dasuke ta Hafeeza tafi masa komai dadi, cikin wani irin Nishadi yace" ina yawan Jin faduwar gaba duk lokacin dana tun kare ta, tanada kwarjini sosai,ina yawan Jin feeling akanta, Ma'aruf rana daidai ne banayin mafarki da'ita wallahi"(=H=J)

Ma'aruf ya kwashe da wata irin dariya yace"Abokina kakamu wallahi, please kayi Mata magana mana,meyasa zaka tafi Saudia? ka tsaya ku fuskanci juna tukunna,but Wai Kaka ma tasani kuwa?"

Hafeez yayi ajiyar zuciya yace" idan Kaka tasani ai tun kafin na fadawa yarinyar zataje ta nema min auren ta,gaskiya bata sani ba, inaso ne nafara tunkarar yarinyar dakaina, naga ita din ustaziya ce, kullum tana cikin hijabi, yanzu taje Saudia,inaso nasameta acan muyi magana,daga nan zanyi Addu'ah saina dawo."

Ma'aruf yasa ki ajiyar zuciya yace"harna matsu ayi abunnan wallahi Hafeez,kuma kayi sa'ah mutumina, kasan ustazan yaran nan komai kaine zaka koya musu,babu damuwa saika dawo,Allah yasa muji alkhairi,amma ka kawar da wannan kwarjinin dakace tana ma kuyi magana"

Hafeez yace"ok"

Daga nan sukai sallama fuskar Ma'aruf cike da farinciki.


Bayan kwana hudu acan Saudia Hafeeza tabar harami tana zaune awani wajan shan shayi tana jiran akawo mata,sanye take cikin baqar abaya me adon stone baqi da kuma fari,saide baqin stone din yafi farin yawa, tasake yin fari tayi Shar abun ta bazaka taba cewa bahaushiya ceba musanman yanda tayi rolling da mayafin abayar akanta, daga Saman goshinta kana iya hango yanda gashinta ya kwanta luf.

Waya ce a hannun ta babba tana dannawa hankalin ta kacokam yana kan wayar, tana so tasan abubuwan dayake kan wayar kasancewar ba iya wayar tayi ba, har yanzu tana so tasan waye yake aiko Mata abubuwa na more rayuwa tunda tazo qasar, hakan yasa tayi wa Kawunta Hamza magana ganin yanda data bar harami idan takoma masauqin ta zata ga an ajiye Mata abubuwa naci da Sha masu kyau, kuma kawun nata ya tabbatar Mata cewa dan majalissa ne, Wato wanda yabiyamata kujerar zuwa Saudia, bata kawo komai aranta ba, hankalin ta kwance take ibadarta, tana yiwa kanta Addu'ah da qasa da kuma Sauran musulmi, saide rabi Addu'ar tata tafi yawa ne ga iyayen ta dasukabar duniya.

Wannan hutu da sauyin Cima data samu shine yasa tasake yin wani fresh,tayi fari sosai hatta nashanunta sun sake cika sosai.

Wani irin daddan qamshin daya daki hancin ta, shine yasa ta dago kanta da sauri, dede lokacin shima ya zauna hakan yasa idonta ya fada cikin na Hafeez, yayi masifar kyau cikin qananun Kaya,farar rika sai kuma baqin wando, yasaka glass Jan duhu wanda yasake qawata fuskar sa.

Cikin sauri ta janye idonta daga Kansa,duk da gabanta yana faduwa haka ta maze taci gaba da danna wayarta.

Adede lokacin aka kawo Mata shayin, wanda yakawo Mata yayi magana da larabci taba shi amsa, sannan yajuya, hakan ba qaramin dadi yayiwa Hafeez ba, sosai ta birgeshi.

Cikin dakewa yadan motsa lips dinsa sannan yace Mata "Sunana HAFEEZ"

Ataqaice tace"HAFEEZA"

Murmushi yasa ki yace"nasani"

Kallonsa tayi ta dauke kanta, sannan ta dauki cup din shayin tafara Sha, Adede lokacin shima aka ajiye masa wani, ya dauka yafara Sha idonsa akanta, sosai yake kallon dan mitsitsin bakinta yanda take shan shayin kamar yakai bakinsa ya lashe lips din nata.

Hafeeza tafara tsarguwa da kallon dayake Mata, ahankali itama ta dago kanta ta Kalleshi ko zai janye idonsa daga kanta,tana kallon sa idonta ya sauka akan faffadan qirjinsa har tana hango gashi a kwance akan qirjin nasa kasancewar bai gama rufe botir din gaban rigar ba, saide kuma abun mamaki data kalleshin ma ko alamun janye idonsa baiyi ba, sai ma wani murmushi dayake binta dashi wanda yasake qawata kyakykywar fuskar sa.

Adede lokacin Kira yashigo wayar sa, kasancewar wayar tasa a ajiye take agaban su akan table din dake gabansu hakan yasa Hafeeza taga sunan MAMA 6aro-6aro akan fuskar wayar, wata irin ajiyar zuciya ta saki tana hamdala aranta, ko banza dole ya dauki wayar, hakan zaisa ya dauke idonsa daga kanta.

Amma abun mamaki saitaga kallo daya yayiwa wayar yanayin fuskar sa ya sauya, kuma be dauki wayar ba harta gama ringing,kiran yana yankewa wani yasake shigowa saide wannan Karon cikin sauri ya kashe wayar gaba daya.

Kan Hafeeza ya daure, Mama tagani a fuskar wayar, meyasa hakan? mahaifiyar sa na Kira meyasa bazai daukaba?

Maganar sa ce ta dawo da'ita daga tunanin data Lula,duk da shima daga nasa 6angaren gabansa faduwa yake haka ya daure ya dauki tissue ya goge kyakykywan sajen daya sake qawata fuskar sa, sannan ya fuskanceta cikin wata irin murya mai aji yace"nasha wahala awasu shekaru can baya arayuwata,hakan yanada nasaba da quncin danake ciki a koda yaushe har zuwa yanzu, tunda nahadu dake nakejin sauyi acikin zuciyata,inajin nishadi dakuma walwala aduk lokacin dana ke6e dake azahiri dakuma cikin mafarkina,inason inci gaba jin wannan farincikin,but nasan cewa hakan bazai samu ba dole saikin zama tawa,kafin nasamu hakan dole saikin fara bani dama nashiga cikin jerin manema auren ki..."

Hafeeza ta zuba masa ido tanajin yanda yake zuba Mata zance, bazaka taba tunanin shine yake zancen ba.
Hafeez yasaki ajiyar zuciya sannan yaci gaba da fadin"na fuskanci qalubalen rayuwa kafin na kawo matsayin da nake a yanzu,ki bani dama inaso na qarar da Rayuwata tare dake,zan baki lokaci kiyi shawara da mahaifiyar ki"

Kafin Hafeeza tayi magana ruwa yafara saukowa,kasancewar Abaya ce a jikinta shiyasa nan take ruwan yajiqata jalaf,shima anasa 6angaren rigar jikinsa tafara jiqewa,ya kalleta zaiyi magana idonsa ya sauka a qirjinta ga shatin bra duk ya futo, cikin sauri ya nuna Mata wani waje da hannun sa, cikin sauri suka qarasa wajan suka tsaya saide gaba daya ya daburce itama daga nata bangaren haka, duka su biyun kowa yakasa kallon kowa, hannun sa yazuba cikin aljihun wandonsa, ya dauko katinsa yabata yace"gashi"

Kanta aqasa batare data dago ba tasa hannu ta karbi katin, saide jikinta yayi sanyi sosai dajin kalaman sa,duk yanda akai ya fuskanci abubuwa dayawa acikin rayuwar sa, amma abunda yafi daure mata kai meyasa be dauki wayar Mamansa ba? meyasa dataje gidansu iya shida qannansa da Kakarsa ne kawai agidan? Ina mahaifiyar sa?, ina mahaifinsa? meyasa Basa tare gida daya?

Sun dade awajan har saida ruwa ya tsaya, babu mai magana acikin su face satar kallon juna dasuke.
Bayan ruwan ya tsaya ya nuna Mata hanya yace"muje ko?"

Kanta ta gyada masa,suka fara takawa ahankali, ita kanta ba tasan ina zasuje ba,babu wanda zai kallesu baiji sun birgeshi ba, sosai suka dace da juna.

Kai tsaye wani super market suka shiga,qa'idar super market din sai ma'aurata ne kawai suke shiga, amma ganinsu tare yasa babu wanda yamusu magana kai tsaye zakace su din ma'aurata ne, bayan sun shiga saida yayi mata siyaiyar Kaya kamar hauka, Hafeeza kawai Kallonsa take, saida yajido Mata Kaya masu shegen kyau da tsada sannan suka futo,bayan sun futo ma saida Yakoma wani shagon yasiyo Mata sabuwar waya dalleliya babbar ta hannun ta, sannan ya dauki kayan suka wuce masauqinta, har zuwa lokacin babu wanda ya cewa dan'uwansa uffan.

Saida ya ajiye mata kayan sannan yazuba hannun sa cikin aljihun wandonsa ya kalleta yace"zan tafi"

Ba tayi kuskuren Kallonsa ba tace"nagode"

"saina jiki"

Abinda yace kenan yajuya ya tafi, harya 6acewa ganinta batabar wajanba, ahankali ta sunkuya ta dauki kayan, taji nauyi sosai, hakan yasa takai wani, tasake dawowa ta dauki Sauran, bayan ta shiga dakin ta tabude kayan gaba dayan su, ta rafka uban tagumi tana tunanin yanda zatai da wannan bawan Allah, kokadan baza tace ga abinda takeji akansa ba.

Ga kuma Gaddafi agefe, ajiyar zuciya ta saki,ta dauki wayarta ta dokawa abokiyar shawarar ta kira, Wato Maman Fadila.

Ta dade tana kiran wayar amma kwata-kwata wayar taqi shiga.
Tagumi tayi tareda zubawa kayan ido,har yanzu ba zata ce ga abinda takeji akansa ba,abinda tasani kawai shine Gaddafi shine acikin zuciyar ta,harga Allah tana son mutum mahaddacin Alqur'ani,Shikuma wannan babu alamar ma yasan addinin bare ayi maganar karatun Alqur'ani.
Ajiyar zuciya ta saki tamiqe ta cire Abayar jikinta ta shiga toilet domin watsa ruwa.

Ko kwana uku Hafeeza bata qara a Saudia ba ta kammala duk wata ibadar ta,tayi shirin dawowa Nigeria, har zuwa wannan lokacin bata sake ganin Hafeez ba, haka katin daya bata me dauke da numbers dinsa ajiki shima ba tayi kuskuren saka number ta kirashi ba.

Suna sauka a Airport taga kawu Hamza da wasu daga cikin malaman makarantar su, acikin wata hadaddiyar Mota suka tafi gida, itade Hafeeza tunda suka fara tafiya zuciyarta cike da mamakin motar,tarin tambayoyi fal ranta saide babu me bata amsa,kawu Hamza kuwa sai janta yake da zance ahaka har suka qarasa gida.

Anan taci Karo da gyare-gyaren da'ake yi musu agidan, sosai gidan ya sauya yayi kyau sai son barka.
Tundaga qofar gida Inna da Maman Fadila da Sauran maqota suka tarota kowa yana murna har suna neman kada ta aqasa, daga nan suka dunguma zuwa gida aka baje kolin fira, gida yacika da Jama'ah kowa yana yi Mata sannu da zuwa.

Da daddare bayan ta nutsu suna zaune da Maman Fadila afalo, Inna kuma tana daga can gefe tana kakkarya bagaruwa wadda zata rabawa maqota, Hafeeza ta janyo 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ kayan da Hafeez ya siya Mata a Saudia taturashi gaban Maman Fadila, sannan ta kwashe labarin komai tafada mata.

Maman Fadila tayi shiru na tsawon mintuna kusan biyar, sannan tasaki ajiyar zuciya tace"to yanzu ke Hafeeza me kikeji game dashi? kinsan de kina tareda Gaddafi ko?"

Ajiyar zuciya Hafeeza tasaki tace"gaskiya ni bazan ce ga abinda nakeji araina game dashi ba,saboda dabi'una da nasa sunada banbanci, kinga shi niga ne, hatta kunnan sa harda dan kunne irin wanda Yan film suke sakawa, sannan lokacin da naje kar6ar kudi gidansu bakiga shigar datake jikinsa ba, gaba daya jikinsa anyi masa Zane irin na Yan dambe,kai nide gaba daya ma wannan dabi'un nasa basu min ba"

Maman Fadila takama hannayenta, sannan ta kalli gefen Inna taga Inna redio ma takeji qasa qasa a wayarta, hankalin ta baya kansu, sannan ta dawo da hankalin ta wajan Hafeeza tace"Hafeeza, ki nutsu,kiyi tunani, sannan kiyi istikhara,wani lokacin abinda muke so ba shine yake zama alkhairi agaremu ba, wanda bama so din shine yake zame mana alkhairi, duk acikin dabi'unsa banji inda kikace baya sallah ba, asali ma a Saudia kuka hadu harya fada miki abinda yake ransa, Hafeeza ba'a shedar littafi ta bangonsa, kamar yanda baki zauna dashi ba, ba kiyi bincike akansa ba, bazai iyu ki Yanke masa hukunci ba,atawa shawarar ki bashi dama kamar yanda ya nema, sannan kiyi Addu'ah akan Allah ya tabbatar muku da alkhairi, kuma ya miki za6in wanda yafi alkhairi tsakanin shi da Gaddafi"

Cikin rashin wayo Hafeeza tace"to yanzu me zan masa?"

Maman Fadila tace" ki kirashi awaya kice Hafeeza ce,dama Kira nayi mu gaisa,shikkenan daga haka karki sake kiransa awaya,kuma koya kiraki karki yi zuruf ki dauka,kidan ja aji, idan kinga kiransa karki daga,sannan karkibi kiran nasa saide ki tura masa saqo kice kina aiki ya kiraki,idan kin gama Zaki Kira,to karki kirashi koda an dan dauki wasu awanni,ki barshi shida Kansa ya kiraki, wannan hanyar kadai ma zata tabbatar mana da irin son dayake miki"

Hafeeza ta kalleta tace"to amma Maman Fadila menene hikimar hakan?"

Maman Fadila tace" haba Hafeeza,ya za'ai daga haduwar ku kawai babu dan Jan aji saiki bada kai dawuri? aiki nuna masa kinada masu sonki sosai,farinjini gareki, saboda kada yaga kamar bakida samari yayi tunanin shi kadai ne,idan harda gaske yana sonki to zai bada himma wajan ganin yasameki,daga nan mukuma saimu Yanke shawarar data dace akansa"

Hafeeza ta gyada kanta cikeda gamsuwa sannan tace"kuma dama ai kinga inada Gaddafi na ban rasa masoyi ba"

Maman Fadila tace"hakane kam tagidana, oh, ikon Allah kenan, abu kamar wasa shide wannan Hafeez yadage yana so yasake kallon abinda Fadila ta tsotsa"

Cikin tsananin kunya Hafeeza ta rufe idonta da tafin hannunta, cikin salon kawar da maganar tace"to yanzu ni Yaya zanyi da wannan kayan daya bani?"
Maman Fadila tace" waya de ki bawa Inna ta hannun ki sai Adinga turo Mata film tana gani,ke kuma saiki dauki wadda ya siya miki tunda tafi girma,kayan kuma kiyi amfani dashi,haba Hafeeza komai sai an koya miki?"

Hafeeza tayi dariya tace"to kema ki dauki abinda kikeso"

Maman Fadila tayi murmushi ta dauki turare,daga nan Hafeeza ta bude wayar tafara kokarin sakata a caji.

Maman Fadila ta kalleta bayan ta dawo ta zauna tace"nifa Hafeeza duk ba wannan abubuwan ne suke damuna ba, damuwa ta shine insan waye yabaki kyautar million biyar dinnan awajan saukar ku, na tabbatar bahaka kawai ya dauki wannan zunzurutun kudin yabaki ba, wallahi da wata aqasa"

Hafeeza tayi shiru tatafi tunani,sannan ta dago tace"to Maman Fadila kode wannan dan majalissar ne?"

Maman Fadila ta Girgiza kai tace" bana tunanin haka,shi kinga yace a6oye sunansa, sannan shi Alhaji Isa Yunusa ai a bayyane yake kowa yaji million biyu yabaki, su Yan siyasa anfada miki sunada sirri ne? komai nasu a bayyane yake kodan asan cewa sunyi"

Hafeeza ta daga kafadunta alamun rashin damuwa tace"shiya sani Maman Fadila"


*** *** ***


Zaune suke afalo gaba dayan su, Hajiya Kaka tana shan tea tana satar kallon Hafeez daya nutsu waje daya, tana lura dashi tunda ya dawo daga Saudia baya fita, kuma haka zai zauna ya ajiye wayar sa agefe ko nan da can baya tafiya yabar wayar sa.

Husna ce ta kawo masa bread slide hudu da wainar qwai agefe dakuma tea mai kauri,cikin nutsuwa tace"gashi yaya"

Kafin yayi magana wayar sa tayi qara, cikin sauri ya kaiwa wayar wata irin wawura har saida ya bige cup din tea dake gabansa.

Hajiya Kaka tace"subhanallah,Hafeezu lafiyarka kalau kuwa?"

Ko kallon Hajiya Kaka baiyi ba, ya dauki wayar cikin sauri yana Addu'ah Allah yasa Hafeeza ce saboda yaga new number,daga can 6angaren Hafeeza tayi shiru gabanta yana faduwa, har saida shi da Kansa yayi sallama cikakkiya, cikin ransa yana fatan ace itace, Jin yanda yayi sallamar cikakkiya hakan yasa Hafeeza ta bude baki cikin zazzaqar muryarta tace"ina kwana,Hafeeza ce"

Wani irin murmushi ya qwacewa Hafeez,cikin farinciki ya shafa sumar Kansa cikeda Jin dadi sannan yawuce cikin dakinsa.

Kaka da yan'biyu suka saki baki da hanci suna kallonsa har ya shige dakin tareda rufowa.

Kaka tayi sauri tafara ta6a jikin Hassana tana cewa"yi sauri,yi sauri kije kijiyo mana dawa yake waya"(=)

Hassana tace"wa? lalle Kaka, salon ya kamani ya karya ni a banza, lokacin da mutane zasu zomin jaje cewa zakiyi bakisan anyi ba''(=)

Hajiya kaka ta juya wajan Husna,tun kafin tayi magana Husna tace"karma ki fara, ba inda zanje"

"Kar Allah yasa kuje,Shikuma nasan yanda yake wannan rawar jikin yana mazari nasan mace ce ta kirashi, bari yafuto Kar wanda yasake zubo masa shayi, yanda ya Zubar da wannan din haka zai Sha Sauran"


Daga cikin dakin Hafeez kuwa zama yayi agefen gadonsa, fuskar sa fal murmushi yace"ina kwana?"

Mamaki ya kama Hafeeza,ina kwana kuma? ita akewa ina kwana?
Cikin mamaki tace"Alhamdulillah''

"inata tsammanin kiranki,maganar gaskiya kinada nutsuwa,kuma kinada hankali,yaushe Zaki bani dama nazo gidanku naganki?"

Mamaki yasake kama Hafeeza ganin yanda yake magana kamar arikice yake, daga cewa yana tsammanin Kira, kuma sai zancen hankali da nutsuwa,daga ji kawai shima yin zancen yake,bai sababa.

Hafeeza tace"idan ka shirya zuwa saika Kira wayata"

"nagode,saikin jini"

Yana fadar haka ya kashe wayar, yasaki wata irin nauyaiyar ajiyar zuciya sannan yafuto falon fuskar sa dauke da walwala.

Saida yaga Husna tana gyara wajan daya Zubar da tea sannan hankalin sa ya dawo jikinsa ya tuna abinda yayi.

Kallon Hassana yayi yace"ke zoki kawo min tea"

Hassana tace"wallahi Yaya har zamu kawo ma wani Kaka tace karmu kawo"

Kallon Kaka yayi, cikin sauri ta kawar da kanta sannan tace"to kai ka yarda nizan iya hanasu su kawo ma Shayi? ina nasan anyi hakanma,?oho bansani ba"

Hafeez ya Girgiza Kansa kawai yana sakin ajiyar zuciya,wannan wayar da yayi da Hafeeza jiyake kamar an sauke masa wani nauyi daga kan qirjinsa.


*** *** ***


Da yamma kawu Hamza yazo gidan,bayan sun gaisa ya kalli Inna yace" Ta Rasulu maganar Hafeeza ce ta kawo ni"

Inna ta karyi goro tace"to ya akayi? Inji dai lafiya?"

Kawu Hamza yayi murmushi yace"lafiya kalau saide alkhairi,ina Sanatan daya biyawa

Please Login or Register in order to submit comment