Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cireshi, ga wannan fenti daka fente jiki dashi Hafeezu kamar ba namu ba"(=>-)

Girarsa guda d'aya yadage yana kallonta da mamaki, sannan yasaka hannu yacire d'an kunnan yabata, batare dayace uffan ba yafice daga falon.

Kasancewar yashiga masallacin da wuri hakan yasa yasamu sahun farko, bayan an idar da sallah anyi Addu'ah yatashi ya qarasa wajan liman yabashi hannu suka gaisa, sannan yasaka hannu a aljihun rigar shaddar dake jikinsa yadauko Dala d'ari biyu canjajju 'yan dala goma-goma yabawa liman cikin ajin sa dakuma miskilanci yace"gashi ayi sadaka"


Liman yayi qasa da murya yayi godia, Hafeez baice komai ba yafuto daga cikin masallacin mutane kuwa sai kallonsa suke.

Liman yatashi tsaye ya nunawa jama'ah kudin, a kayiwa Hafeez Addu'ah sosai, sannan aka raba kudi wasu suka samu dala ashirin-ashirin wasu kuma suka samu dala goma-goma.

Acikin wanda suka samu dala ashirin harda Kawu Hamza,Qanin mahaifin Hafeeza.

Bayan jama'ah sun futo daga masallaci kawu Hamza ma yafuto shida abokinsa Malam Musa.

Suna cikin tafiya zuwa gida saboda akwai 'yar tafiya tsakanin su da masallacin, Kawu Hamza ya kalli abokinsa yace"Malam Musa, Wato wannan matashin yaron daya bada sadaka yanzu,na dade ina tunani akansa,yaron yana birgeni,sannan na yaba da hankalin sa,yanada nutsuwa sosai, ina yawan ganinsa duk lokacin daya shigo gari,naga kamar bashida hayaniya, shiyasa nake masa sha'awar yarinyar nan Hafeeza 'yar wajan Yayana Haladu wanda yarasu, inaso naje nasamu yaron inyi masa tayin aurenta tunda yin hakan ba laifi bane a addinance"

Malam Musa ya jinjina kansa sannan ya gyada kai yace" eh yin hakan ba laifi bane,inda ace iyayen Yara zasu Dinga irin wannan tunanin inde har sun yaba da hankalin matasan kuma sun San za'a riqe musu yaransu da amana to kaga aida ansamu sauqin rashin aure awajan matasa,amma maganar gaskiya Hamza, karka fara wannan hadin, saboda yarinyar nan Hafeeza marainiya ce,daga kai sai Ta Rasulu kawai kuka rage mata,karka dauketa kabawa wannan yaron saboda wannan yaron dakake gani iyayensa suna raye, yana rayuwane da yan'uwansa guda biyu dakuma Kakarsa anan, har yanzu ba'a san dalilin dayasa baya tare da iyayensa ba, kuma daga majiya me qarfi ance yaron baya shiri da iyayensa,yanada matsala dasu"





(malam Musa kallamu ka 6aro aiki=2=2=2)




Complete document 1k


8621296018
Amina Muhammad
fcmb


kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034






Amnah El Yaqoub
'<
[5/25, 10:51 AM] El Yaqoub: =ؘMATAR ABBANA=ؘ
(Luv Story)



Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update=G<
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45


6


Kawu Hamza yayi murmushi Sannan ya d'an bugi kafadar abokinsa yace"Haba Malam Musa, yaushe zakai duba da maganar mutane akan sha'anin aure? to inde zaka saurari jita-jitar mutane kwata-kwata bazakai auren 'yarka ba"

Malam Musa yace"Hamza,yarinyar nanfa Amanace a wajanku damu baki daya, tunda marainiya ce da munqi da munso muma ai iyayenta ne,bazai iyu mu zuba ido ka dauketa kakaita cikin matsala ba,nafadama gaskiya yaron nan yanada matsala da iyayensa kuma daga majiya me qarfi naji hakan, to saboda me munaji muna gani zamu bari kadauki marainiyar yarinya kakaita cikin matsala? kasake duba wannan maganar de"

Kawu Hamza yayi murmushi yace"karka samu damuwa abokina,Alkhairin da nakeson hadawa insha Allah saina baka mamaki,zakaga yanda Hafeeza zatai zamanta lafiya adakin mijinta,babu ruwana da maganar mutane tunda ba shi yaron ne da bakinsa yafada min haka ba,saboda haka kayi musu Addu'ah kawai"

Malam Musa yace"Hamza kenan, dama tayaya yaro zai fadama damuwar sa dakansa?, mude mun fadi gaskiya, yanzu kuma duk abinda zai biyo baya, idone namu"


*** *** ***


Da daddare suna zaune aqofar gida suna fira, cikin soyaiya ya kalleta yace"Malama sai murmushi kike kode murnar saukar goben ce?"

Hafeeza tasa hannu ta rufe fuskar ta cikin kunya tace"saboda Ganinka ne"

Wani irin dadi ya kama Gaddafi,cikin sauri yasake gyara zamansa yace"waida gaske kike Hafeeza tah?''

Dan kallon sa tayi kadan sannan tace"da gaske nake, gashi wannan nakane, dazu muka dafama, wannan kuma kayan rabon sauka ne na dibar ma naka"

ta qarasa maganar tana bashi dan qaramin kwanon silba me kyau da dahuwar nama aciki,sai kuma ledar thank you guda biyu ancikasu da snacks din da sukai saboda rabawa gobe.
Hannun Gaddafi har rawa yake wajan kar6ar kayan, ya dora kwanon silbar akan cinyarsa, sannan yabude ledojin suma yagani, ya washe baki yace"lala lala, wai duk wannan awajan saukar taku zaku raba?"
Kafin ta bashi amsa ya ajiye ledar yaci gaba da fadin"bari muga menene acikin kwanon"

yana budewa wani irin qamshi yadaki hancinsa, ya shaqa ya d'ago Kansa yana jinjina kai sannan yakai dubansa gareta yace" yau kinaji dani Malama, menene tukwicin wannan kyautar?"

Hafeeza ta Girgiza kanta tace"Babu komai"

Gaddafi yayi murmushi yace"a a wannan kayan ai dole abiya tukwicin su"
bai jira amsar taba yasaka cokalin da'aka hado masa dashi yafara cin naman, yacika baki da tsokar nama yace"Um um um um" sannan ya jinjina Kansa yanaji kamar kunnansa zai cire.
ya juyo ya kalleta yace"amma yayi dadi sosai,Kinaji dani Hafeeza tah"

Hafeeza tayi murmushi tana kallon sa, tanajin wata soyaiyar sa tana sake shiga ranta.
Shikuwaa sosai yakecin naman, saida ya cinye tas, yasha ruwan pure water data kawo masa guda daya, sannan ya kalleta yace"gaskiya yayi dadi sosai,yanzu wannan naman nawa Kika kashe?"

Hafeeza tace"meyafaru? amma de ba biyana zakayi ba ko?"

Cikin Jin dadi yace"a a, dama kawai tambaya nayi"

daga nan ya kalli agogon wayarsa ya miqe yace"to zan wuce Malama, dan Allah ki gaida Inna, kice Mata ina Mata Allah yasanya Alkhairin saukar gobe"

kokadan Hafeeza bataji komai aranta ba, asali ma bataji soyaiyar sa ta ragu aranta ba, abinda tasani shine tana sonsa dan Allah, tana sonsa saboda ya'iya rera karatun Alqur'ani.

sallama suka qarasa Gaddafi ya dauki ledojin data kawo masa yatafi dashi.

tana shiga gida Maman Fadila dake zaune suna fira da Ta Rasulu ta kalleta tace"A'a, masoya har kin dawo?"

Hafeeza ta cire Hijabin jikinta ta ajiye sannan ta zauna akan babbar tabarmar dasuke zaune tace"nadawo, yatafi gida shima"

Maman Fadila ta sake kallon ta tace"ya haka? Hafeeza yanaganki hannu Rabbana? babu abinda yabaki?"

tun kafin Hafeeza tace wani abu Inna Ta Rasulu ta kwashe da wata irin dariya harda tafa hannayenta biyu tafara rera waqa tace"munaji muna gani muna kuma saurare...."=


*** *** ***

Washegari sauka,tun qarfe hudu na dare Hafeeza tatashi tayi nafila bata koma bacci ba tana zaune tanata tulawar karatun Alqur'ani,har aka idar da sallar asuba sannan tafuto tafara gyara gidan nasu, bayan tagama gyaran gidan ta zauna a tsakar gida tayi tagumi hannu bibbiyu tana kallon malkaden waken dake gabanta, shawarar da Maman Fadila tabata akan rashin son yin suyar qosai shi take tuna wa, wannan qosan da batason zuwa ta siyar shine yarufa musu asiri itada Inna, dashi sukeci dashi suke sha, tun tasowar ta bata ta6a ganin wani daga unguwa yakawo musu tallafin ko fallen zani ba, haka tataso acikin gwagwarmayar rayuwa harta kawo yanzu.

Ahankali tasaki ajiyar zuciya tasake jin wani qwarin gwiwar yashige ta akan sana'ar tasu, cikin hanzari tatashi ta shirya tsaf, cikin dogon hijabin ta, tahada kayanta tafice wajan sana'ar su, abinda tasa aranta shine koda qosan be qare da wuri ba zatayi haquri harya qare sannan tazo ta shirya tatafi wajan saukar tasu, saboda inda ace ba suyi qosan ba kuma babu Kawu Hamza to babu yanda za'ai tasamu damar shiga cikin sauran dalibai da za'ayi saukar dasu


*** *** ***


Tunda sukai sallar asuba basu koma bacci ba, gaba d'ayansu su ukun suka shiga kitchen suna yin donut da cake dakuma sauran kayan rabo da zasu rabawa jama'arsu bayan angama sauka, hakan yasa suka zama busy kowa da aikin da yake a kitchen din, suna aikinsu cikin sauri saboda kada lokaci ya qure musu.

Cikin hanzari yafuto daga cikin dakinsa yana Sanye da baqaqen kaya riga da wando,kayan nasa sunada laushi sosai kuma roba ne, hakan yasa wandon ya d'an kamashi wanda tsawon sa bai sauko har can qasa ba, da kad'an ya wuce gwiwar sa,rigar kuma tana hade da hula daga Qasan hular akwai zare guda biyu wanda mutum zai iya daure hular a kansa da wannan zaren,kayan sunyi mutuqar yimasa kyau kamar ka saceshi,saurin dayake yasa yafuto yana qoqarin daura agogo a tsintsiyar hannunsa me cikeda gargasa.

Kallon gefen kitchen din nasu yayi, kafin yayi magana 'yanbiyu suka gaidashi, Kaka ta kalleshi taga kamar sauri yake, cikin hanzari tace"ina zakaje haka da sassafe Hafeezu?"

Saida ya runtse idonsa cikin taqaici saboda yanda ta furta sunan nasa,bayason wannan Hafeezun datake fada, idon nasa ya bude sannan ya amsa mata cikin daure fuska kamar kullum yace"yanzu zan dawo Kaka,akwai abinda zan gani ne me muhinmanci"

Kafin Kaka tabashi amsa yayi wuf yafice daga falon nasu cikin sauri, yana futowa compound bai saurari kowa ba yashiga motar da kansa sannan yafice cikin sauri, tuqi yake yana jin wani irin nishadi acikin zuciyarsa wanda yarasa meyasa yakejin hakan,agefe guda kuma ya kunna waqa acikin motar tasa sautin waqar yana tashi kad'an-kad'an.

Bai zame ko'inaba sai wajan da Hafeeza take suyar qosai, daga nesa da'ita yayi parking motarsa, sannan yakashe motar yana kallonta tacikin tinted glass din motar, wata irin wawiyar ajiyar zuciya ya sauke da idonsa ya sauka akan kyakykywar fuskarta, duk da fuskar tasa babu walwala akanta, ahankali can qasan maqoshin sa ya furta " had'addiya ce"

Yasake gyara zamansa acikin motar tareda harde hannunsa akan qirjinsa yana faman kallonta,ya dade yana nazari akanta, haka kuma baibar wajanba har saida yaga tagama saida qosan tas, sannan ahankali yaja motarsa yabar wajan batare dayaje inda take ba.


Inna tayi mamakin yanda Hafeeza tafita suya bayan tasan cewa yau ce ranar saukar su,abun yabata mamaki sosai kuma taji dadi aranta, tasan cewa haqiqa ita aka haifawa Hafeeza tunda gashi yarinyar kullum cikin fafutukar nema musu na abinci take, cikin sauri tatashi ta kar6i kayan hannunta tafara wanke wa ita kuma Hafeeza da gudu tashiga wanka saboda kada lokaci ya qure, garin gudu gefen zanin nata ya kunce kafin ta farga ta gyara har tsayaiyan nashanunta guda d'aya yafuto waje, cikin sauri ta zaro idonta waje tana kai dubanta wajan Inna, aikuwa komai daya faru akan idon Inna ne, cikin sauri Hafeeza ta runtse idonta, Inna ta dauraye babbar robar dasuke had'a wake aciki sannan ta girgiza kanta tace"ainace dama mijinki saura zaigani inde bazaki hankali ba Hafeeza,menene abun gudu a shiga wanka in banda sakarci? inda baqi mukai ma haka zaki kama gudu kwankwaso yana miki rawa kedama abu ba kad'an ba, kici gaba Allah yabaki sa'ah"

Hafeeza de tana jinta tayi shiru batace komai ba tashige cikin bandakin nasu, agurguje tayi wankan ta tafuto tashirya cikin material d'in da Maman Fadila ta dinka mata,duk da Rigar tanada fad'i ba qaramin kyau tayi mata ba,riga ce me fad'i doguwa dakuma zare agaban rigar wanda zata kama ta daure acikinta, kamar yanda taga zaren agefen rigar itama ta kama ta daure shafaffen cikinta dashi, yanda ta daure rigar hakan yasa Hips dinta yasake futowa duk da Rigar tanada fad'i, dogon gashinta dayake daure tayi sauri ta kunce tashafa masa Vaseline sannan tasa mataji ta tajeshi daqyar, lokaci daya ya dauki wani irin sheqi kasancewar a wanke yake fes.

Dogon hijabin saukar su gogegge ta dauka ta saka,lokaci daya zahirin kyawun ta yafuto acikin hijabin,tayi mutuqar kyau duk da ba kwalliya tayiba kawai gashin girarta ta taje saikuma dan lipstick data saka shima d'an kad'an.

Maman Fadila ce ta shigo gidan itama tana jiranta, daga nan suka dunguma suka tafi.
Duk yanda take komai cikin sauri saida ta makara,tana zuwa makarantar shugaban makaranta yafara yimata fada kasancewar ita kadai ce bata zo dawuri ba, bayan dogon bayani da yayi musu kai tsaye suka qarasa wajan da aka tanada domin yin taron,gaba dayan su daliban rumfa daya aka ware musu da kujerun da kowacce zata zauna, banda sauran mutane suma dasuke cikin tasu Rumfar, wajan yacika sosai kamar me, manya-manyan baqi sun samu halartar taron saukar kasancewar islamiyar tasu babbar makaranta ce.

Malaman makarantar aka bawa dama daya daga cikinsu yayi bayanin muhinmancin ilmi dakuma muhinmancin karatun Alqur'ani, yayi da larabci sannan ya fassara da hausa.

daga nan aka kira Sunanta amatsayin daliba ta farko dazata fara karatu.

Tunda suka zauna awajan kanta yake qasa tana karanta (Bismillahirrahmanir-Rahim) acikin zuciyar ta,saboda gabanta banda fad'uwa babu abinda yake,bata ta6a shiga cikin babban taro kamar wannan ba,taso ace had'a baki zasuyi gaba dayansu daliban malami guda daya ya karanta suma su karanta kamar yanda wasu makarantun sukeyi, to saide tasu makarantar tazo musu ta daban, hakan yasa take karanta Basmala kasancewar duk wanda yakejin fad'uwar gaba kokuma yakejin tsoron tunkarar wani abu kamar jarabawa ko wani abu daban, to muddin yakama Basmala yana maimaitawa acikin zuciyar sa insha Allahu zaiyi komai nasa cikin nutsuwa kuma zaiji fad'uwar gaban ta ragu.

kasancewar tariga tasan itace zata fara karatun hakan yasa gabanta yaketa faduwa, kokadan bata fahimtar jawabin da'ake awajan, saide ta tsinkayi me jawabi yana kiran HAFEEZA KHALID USMAN amatsayin dalibar farko dazata fara karatun Alqur'ani.

Wata daliba dake gefenta tace"Hafeeza kitashi"

Ahankali ta miqe da Bismillah abakinta, tafara tafiya cikin nutsuwa kanta aqasa harta qarasa inda aka tanada domin tsayawar dalibai masu sauka.

Tunda tataso idonsa yake kanta,yana zaune akan akujerun da'aka tanada domin baqi na musanman, gabansa ne yayi wata irin faduwa ganinta awajan,cikin tsananin mamaki yasake kallon ta yana gyara zamansa aransa yace dama itace?, ahankali ya maimaita sunan nata acan qasan maqoshin sa HAFEEZA....

Cikin nutsuwa tafara rera karatun Alqur'ani cikin zazzaqar muryar ta, lokaci daya wajan yayi tsit kowa yana sauraron karatun nata, Alhaji ISAH YUNUSA babban dan majalissar yankin daya halarci wajan saukar, tun taso war yarinyar yaji ta birgeshi, da alama tanada nutsuwa sosai, lokaci daya ransa ya kwadaitu da aurenta.

Hafeeza kuwa cikin fitar da makaarij take rera karatun ta kamar karta daina,zaqin muryar tata yasa Hafeez dake zaune agefen Kaka acikin Rumfar da aka sauki manyan baqi ya lumshe idonsa yana sauraron karatun nata, a tarihin rayuwar sa zai iya cewa bai ta6a jin karatun wata mace dayayi masa dadi kamar nata ba.

Hajiya Kaka dake zaune agefe tajuya ta kalli Hafeez taga idonsa a lumshe, ta dauke kanta tana girgiza kai, tayi tunanin yanda yarinyar take karatu hakan zai dauki hankalin sa ta yanda zai zuba mata ido yana kallonta ko Allah zaisa adace, saide abun mamakin saita ga kamar ma yarinyar bata birgeshi ba.

Har Hafeeza tagama karatu taje ta zauna mutane basu daina kallonta ba, Ta Rasulu da Kawu Hamza da matar kawu Hamza da yaransa da kuma maman Fadila duk suna waje daya basu samu wajan zama ba, daga tsaye suke hango komai (=)

Gaddafi kuwa sai washe baki yake yanajin wani irin dadi aransa yana Alfahri kasancewar sa saurayi awajan Hafeeza.

Kasancewar daliban basu da yawa mutum biyu ne sukai karatun, daga Hafeeza sai wani namiji guda daya daga cikin dalibai maza guda biyar da'akai saukar dasu.

daga nan aka bawa shugaban makaranta dama yafuto yayi Nasa jawabin, yabada tarihin makarantar kanta.
Sannan aka bawa wani Babban malami shima yayi fadakarwa sosai akan amfanin ilmi, sannan matemakin shugaban makaranta yafara kiran dalibai daya bayan daya ko wacce ana bata allon sauka dakuma certificate.

Bayan angama basu ko wacce takoma ta zauna, Babban limamin unguwar yazo gabansu ya zauna yafara karantawa suma suna biyawa, masu camera kuwa sai zagayasu suke suna daukar su.
daga qarshe kuma baqin da aka gayyata suka fara bawa Dalibai gudunmawa ta kyauta,cikin daliban da suka samu babbar kyauta harda Hafeeza, wadda Alhaji Isah Yunusa dan majalissa yabata kyautar zunzurutun kudi har naira million biyu tareda kujerar Umarah.

Inna tanajin kud'in tayi Suman tsaye har saida Maman Fadila datake yiwa Hafeeza video ta taro ta saboda qiris yarage tafad'i qasa.(=)

daga nan manyan baqi suka fara sanarwa kowa da irin kyautar dayake yiwa makaranta, wannan yace yabada sadakar dubu Hamsin, wasu dubu goma, wasu dubu dari biyu, wasu dubu biyar, harda Mata masu bada dubu daya, wannan duka kyautar makaranta ce.
ma'ajin makaranta ne yatashi yafara rabawa manyan baki wasu fararen takardu masu dauke da number account din makaranta ajiki, idan da wanda zasuyi transfer saisu tura, cikin wanda aka bawa paper harda Hajiya Kaka data hakimce akujera.

Anbawa shugaban makaranta damar jawabi dakuma godia ga baqin dasuka samu zuwa, wani kudin yasake shigowa cikin asusun makarantar, ma'aji ya matso kusa da me gabatarwa yayi masa bayani, me gabatarwa yace"to Alhamdulillah masha Allah, muna kan rufe babin godia ga manyan mutanan dasuka yimana kyautar girmamawa dakuma kyautar kudi, sai kuma gashi wani bawan Allah wanda ya nemi a 6oye sunansa yaturo wa wannan makaranta tamu kudi har naira million goma Sha biyar, million goma na makaranta, sannan dalibar data fara karatun Alqur'ani wato Hafeeza Khalid yace abata million biyar sadaka fisabilillah"

Lokaci daya waje ya kaure da ihun murna kowa sai kabbara yakeyi.
Hafeez yayi sauri yamaida wayarsa cikin aljihun wandon sa ganin kaka ta zubawa wayar tasa ido tana kallo kamar tana so ta gano cewa shine yayi wannan kyautar, shikuma ba komai ne yasa yayiwa yarinyar kyautar ba saboda yaga kamar tanada karancin hijabai, kud'in zai Isa tasake dinka wasu hijaban.(>-=2>+)

Ta Rasulu tanajin wannan kyauta tafashe da kuka wiwi.(=-)

Yayinda Hafeeza ta sunkuyar da kanta qasa tana goge hawayen idonta.

Bayan angama karbar kyautar kudade daga nan aka fara saida calendar mai dauke da photon dalibai ajiki.

Hafeez ya kalli Hajiya Kaka yace"kin riqe takardar account, ki basu takardar su tunda bazaki iya tura musu ba"

Hajiya Kaka ta harareshi tace"saikace kai?"

daga nan ta daga murya ta Kira me gabatarwa, Yana zuwa wajanta tace"bawan Allah ka daga murya kafada a speaker cewa Hajiya Rabi'atu kakar Hassana da Hussaina wadda akafi sani da Hajiya Kaka, ta sai calendar naira dubu Dari"

Aikuwa ya karbi kudi Yakoma tsakiyar taro yafada kamar yanda Hajiya Kaka takeso, su Hassana suna zance qasa qasa saiji sukai sunansu yafado cikin kwatancen Kaka.

me gabatarwa yadawo yakawo wa Hajiya Kaka Calendar ta, Hajiya Kaka ta kar6a sannan tayi wa Hafeez wani kallo me alamun nafi qarfin raini ta kauda kai, shi kuwa dariya ma ta bashi, amma kasancewar miskilin mutum ne saiya yi dan murmushi kadan ya basar.

daga nan akayi Addu'ar tashi daga taro, aka sallami dalibai kowa ya nufi wajan 'yan'uwansa.

Hafeeza tafuto zata nemi su Inna, 'yanbiyu suka tareta Husna tace"Hafeeza tsaya ki mana photo"

Tafadi haka tana miqa mata wayar hannunta iPhone me camera uku, Hafeeza ta kar6i wayar tana murmushi har dimples dinta suna lotsawa.
Hassana ta rungume Husna sannan itama tace"kuma ki tabbatar munyi kyau sosai ehe, idan bamuyi kyau ba saikin sake mana sabo"

Hafeeza ta girgiza kanta tana murmushi sannan tafara qoqarin yimusu photon da qyar kasancewar bata ta6a riqe babbar waya irin wannan ba, tarasa yanda zatayi ta dauki photon, batasan yanda ake photon ba.

Su Husna suka sauya style, Hassana tace"kin dauka?"

Hafeeza tace"A a ban dauka ba"

Husna tace"har yanzu de baki dauka ba?"(>)

Lokaci d'aya Hafeeza duk ta rikice, tarasa yanda zatayi, yanda ta rikice din saita sake yiwa Hafeez kyau wanda yake tsaye ajikin motarsu yana kallonta,mayan kayan dake jikinsa sun sake qawata kyansa,sosai ya shagala wajan kallonta saide miskilancin sa ba zaisa ka gane cewa kallon arziqi yake mata ba.


Cikin zazzaqar muryar ta tace"narasa yanda zanyi ne, ku sake matsawa kusa"

Cikin sauri 'yanbiyu suka matsa suka sake rungume juna.

Hafeeza ta qoqarta ta dauke su, sannan cikin zazzaqar muryar ta, tasake cewa "kuyi murmushi to,kekuma Husna gyara tsayuwarki"
Duk abinda take fada musu haka sukayi, sannan ta dauka tabasu wayar domin su gani, kokadan bata lura da Hafeez dake tsaye agefe ba,shima Koda wasa baiyi gigin yimata magana ba,gaba daya ya shagala a kallonta, wani side na zuciyarsa yanajin tausayin yarinyar,dazu da safe yaganta tana suyar qosai, sannan yanzu gata awajan sauka, hakan yana nufin saida tagama yin sana'ar tasu sannan tataho wajan saukar.
Idonsa ya lumshe kad'an yana tuno shekarun baya yanda rayuwa ta kasance masa,yatuna yanda yake daukar qosai a kansa yana yawo dashi waje-waje.
Cikin sauri yadawo daga tunanin daya tafi kasancewar yaji zuciyar sa tafara tafarfasa akan rayuwar daya tuno, fuskarsa babu yabo babu fallasa yakai dubansa zuwa ga 'yanbiyu anan yaga suna yin selfie tareda Hafeeza, murmushin daya gani kwance akan fuskarta shine yasa haka nan ya tsinci kansa cikin farinciki.

Maman Fadila ce tazo ta janye ta suka nufi wajansu Inna, har zuwa wannan lokacin Ta Rasulu kuka take, kawu Hamza dake tsaye a gefenta shida matarsa Maryama sai baki suke bata akan tayi haquri tadena kuka, daqyar aka samu tayi shiru sannan suka had'u waje daya gaba dayansu, Hafeeza tashiga Tsakiyar su, Maman Fadila kuma tafara yimusu photuna.


*** *** ***


Da daddare suna zaune afalo gaba d'ayansu, kayan shan'iska ne ajikin 'yanbiyu, Kaka kuwa Hijabi ne ajikinta tana jan carbi.

'yanbiyu ne suke zancen taron saukar su ta dazu.

Hafeez yana zaune agefe wando ne ajikinsa three quarter da wata riga wadda batada maraba da singlet saboda yanda dantsan hannunsa yake abude, hatta nipples dinsa kana ganin tsininsu ta cikin rigar saboda yanda rigar take ba kauri.
Jarida ce a hannunsa yana dubawa amma gaba daya idonsa ne akan takardar, tunanin sa dakuma jinsa yana wajan 'yanbiyu saboda yanaso yasake jin sunyi zancen Hafeeza ko zaiji wani abu daga cikin halayen yarinyar.

Kaka ta ajiye carbin hannunta ta shafa Addu'ah sannan tacire Hijabin jikinta ta kalli 'yanbiyu tace"Allah de kuma yakawo muku mazaje nagari, wannan yarinya data fara karatu dazu da zafe awajan sauka, haqiqa wannan kyautar data samu nasan ba saboda karatun ne kadai ba, harda masu sonta"(=)

Hassana tace"ai Hafeeza tasamu kudi gaskiya,Kaka itace fa wannan wadda muke fada miki ta'iya karatun Alqur'ani, kuma suma malaman namu sai nan-nan suke da'ita daga gani sonta suke"

Gaban Hafeez yayi wata irin muguwar faduwa, yasaki dan qaramin tsaki sannan yasake bude wani shafin jaridar.

Kaka tace"Allah sarki ashe itace, amma daga gani tanada nutsuwa yarinyar,kuma kana kallonta zaka tabbatar ba asalin yar qasar nan bace gaskiya,kode ruwa biyu ce kokuma daga wata qasar sukazo, ni naso inji wanda yabata million biyar dinnan,ai kyautar farko ance d'an majalissa ne yabata"

Hafeez ya d'an kalli Kaka sannan ya dauke kansa.

Kafin 'yanbiyu su sake magana wayar Hafeez dake gefe tafara ringing, cikin nutsuwa da aji irin nasa yadauki wayar tareda fadin "I.B kaga saqon dana turo mane?"

Daga d'aya 6angaren I.B yace"nagani, naje nakai masa, na sameshi cikin aminci, yana lafiya babu wata matsala"

Ahankali ya lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya, batare dayace komai ba yakashe wayar.

Kafin wani daga cikinsu yayi magana wata Babbar mata tashigo falon, zata iya kaiwa kimanin shekara Arba'in dawani abu, Hafeez yanajin muryar ta yagane ta,ko a mafarki bazai ta6a mantawa da muryar taba, lokaci daya fuskarsa ta sauya ya runtse idonsa, kokadan bayason ganinta.
Matar taqaraso cikin falon, tana qoqarin zama akan kujera shikuma Hafeez yana qoqarin tashi,yanajin yanda 'yanbiyu suke qoqarin gaida matar, wadda ta kasance qanwar mahaifiyar su ce uwa d'aya uba d'aya,amma Hafeez ko kad'an baima nuna yasan taba, maganar fatar baki bata hadashi da itaba yabar jaridar dayake karantawa awajan yashige cikin dakinsa.

Kaka tabi bayan sa da kallo harya rufe qofar dakinsa.
Cikin sanyin jiki tadawo da dubanta zuwa wajan 'yartata cikin tsananin damuwa dakuma sanyin jiki take duban ta, ta rasa yanda zatai ta gyara baya, tarasa yanda zatai ta dedeta kan ahalinta yazama daya,kuskure an riga anyi, saide ayi haquri a fuskanci gaba,inda ace zata iya maida hannun Agogo baya, to haqiqa da zata dawo da nasu agogon qaddarar baya domin ta gyara matsalolin cikin ahalinta.




(meyake faruwa da ahalin Hafeezu ne? >)

(Jama'ah wa zai turamin 5 million Nima in sake hijabai=-=-)





Complete document 1k


8621296018
Amina Muhammad
fcmb

Kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034





Amnah El Yaqoub
'<
[5/26, 1:59 PM] El Yaqoub: =ؘMATAR ABBANA=ؘ
(Luv Story)



Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update=G<
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45



7



Matar data shigo falon tayi murmushin yaqe ta kalli Kaka tace"Ummah ashe Hafeez yazo qasar"

Kaka tace"Hafeezu yazo SADIYA, su Hassana ne sukai masa magana nayi tunanin ma bazai samu zuwa ba, kuma sai gashi yazo"

Cikin Sanyin jiki Wadda aka kira da Sadiya tace" Allah sarki, nima tun safen naso zuwa kuma saboda yanayin abun hawa yayi qaranci yanzu, ba'a samun fasinjoji masu yawa atasha, shiyasa na makara, Allah ya sanya Alkhairi"

Kaka tace"Amin Sadiya, amma ai zaki zauna damu muyi kwana biyu ko?"

Cikin sauri Sadiya tace"

Please Login or Register in order to submit comment