Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa dala dari de ba qaramin kudi bane, cikin sauri ta girgiza kanta tace"ni banda canji"

Hafeez ya kalli d'an qaramin bakinta sannan yace"kamarya? baga kud'i nan ina gani ba?"

Hafeeza ta daure fuska sannan ta kawar da kanta gefe tace" sababbin kudi ne,tarasu nake saboda bikin wani yayana"

Cikin dabara yace"inane gidanku sai inzo in kar6i canjina?"


Ahankali tajuya ta masa wani kallo sannan tace" kaga riqe kudin ka kawai,zanyi ma sadakar kyauta"

Cikin sauri shima yace"bangane ba? ni banason kyautar ki,kawai ki riqe kudin nan kiyi qosai kiyimin sadaka kuma ni inason canji na, canji na kawai zaki bani"

Hafeeza tasaki ajiyar zuciya sannan ta lumshe idonta tabude su tareda juya idanuwan nata cikin wani irin salo, hakan datayi ba qaramin tafiya da imanin Hafeez tayi ba, ta matsu yatafi, hakan yasa tace"ka riqe kudin ka,zanyi qosan da kudi na, nikuma zanzo na kar6a awajanka"

Cikin wani irin jin dadi yace"Really?"

Cikin zaquwa yatafi tagyada masa kanta,ahankali yajuya cikin motarsa yadauko mata wani Kati wanda address din gidan yake jiki ya ajiye mata agabanta, daga haka bai sake cemata komai ba yajuya yashiga motarsa yatafi, sai alokacin tasaki wata irin ajiyar zuciya, tadafe kanta daya fara yimata ciwo,sai yanzu tayi dana sanin abinda ta aikata a asbiti,gashi yanzu wannan bawan Allah yana bibiyarta,kuma duk yanda akai da alama yasanta, idan be santa ba tayaya zai zo har inda take sana'ah?

Cikin tashin hankali tatashi tabar wajan ko ta kan dutsin datakeson janye wa bata biba,kai tsaye ta nufi gidan Maman Fadila, adede lokacin Baban Fadila yafita kasuwa , ita kuma Maman Fadila tana zaune tana karyawa da taliya da Manja.

Hafeeza tana qarasowa ta zauna awajan tare fashewa da wani irin kuka,sosai take kuka harda shashsheka.

Maman Fadila tafara Salati sannan tatashi ta wanko hannunta ta zauna agefen Hafeeza tace"Hafeeza keda waye? menene ya hadaki da Inna yau kuma?"

Hafeeza tayi shiru taci gaba da kuka.

Maman Fadila tace"kode wani ne ya dakeki?"

Cikin sauri ta girgiza kanta, sannan ta dago idonta daya fara yin ja, ta kalli Maman Hafeeza tace"dan Allah kiyi haquri,rannan ne danakai Fadila asbiti, sai take ta kuka, shine....shine nabata ta tsotsa"

Mama Fadila tarasa gane kan maganar,me aka bawa Fadilan ta tsotsa?, cikin rashin sani tace"kika bata me?"

Cikin kuka Hafeeza tace"nabata Nono, shikuma yaganni, shine yau yabiyo ni,wai namasa qosai harda cewa nafada masa gidanmu zaizo ya kar6i canjin sa,kuma ya tsugunna agabana kusa dani kamar zai rungume ni,shikkenan yanzu kallon yar'iska zai dinga yimin"



(finally de Hafeez yayi magana da Hafeeza.=؃=؃=؃)

(Yaya batun soyaiyar Hafeeza da Gaddafi? kuna ganin Hafeez zaiyi nasarar sace zuciyar ta? >)

(Yaya batun maganar Hajiya Kaka da tace zata nema masa aure?)

karku manta Hafeez ya watsawa kawu Hamza qasa a'ido>#=

Wai ma menene yake faruwa ne tsakanin Hafeez da iyayensa?


(Alhamdulillah free page yaqare) =؃<=؃<=؃<


Complete document 1k

8621296018
Amina Muhammad
fcmb

kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034









Amnah El Yaqoub
'<
[6/14, 2:25 PM] El Yaqoub:
Cikin tsoratar wa Maman Fadila tafara tafa hannayenta tana salati,duk da dariya da take son qwace mata haka ta danne dariyarta tace"Hafeeza!!!?"

Hafeeza tana jin yanayin yanda Maman Fadila takira sunanta tasake fashewa da wani irin kuka.
Maman Fadila tace" yanzu de ita Fadila tariga tasha Fata,amma nangaba ko zatayi kukan me, karki sake bata nono tasha, Hafeeza wannan aina mijinki ne bana Fadila ba,shiyake da damar dazai sha amma ba Fadila ba"

Cikin taqaici Hafeeza ta dago ido ta kalleta idanunta duk hawaye tace"ni kidena cemin wani zaisha min abuna"

Maman Fadila tayi murmushi tace"nadena, amma inde ba so kike maganar Inna ta Rasulu datake cewa Saura zaki kai gidan mijinki ta tabbata ba,tokidena bawa Fadila nono,Shikuma abinda na lura dashi shine abinda yagani a asbiti ne yake so yasake gani shiyasa yabiyo ki,saboda haka kiyi hankali dashi ki kumayi taka tsantsan"

Hafeeza tashare hawayen idonta tareda ajiyar zuciya tace" ni dama ba ruwana dashi,qosan ma ba zanyi ba,yaje yanemi wata tayi masa"

Maman Fadila tace"waida gaske qosan yace kiyi?"

Hafeeza tafada mata yanda sukai itada Hafeez, dangane da batun sadakar qosai.
Maman Fadila tace" a a karkice haka Hafeeza,batun sadaka tunda kin riga kinyi masa alqawari to kiyi masa, baki san buqatar sa akan sadakar ba,kuma aiba had'uwa zakiyi dashi ba,kiyi qosan ki masa sadakar, kema Allah zai baki Lada, batun kudin dakika kashe kuma karki kuskura ki hadu dashi da daddare idan zaki kar6a,ki nemi wata tarakaki kije ki kar6i kudinki kokuma kije da rana atsaka, idon kowa akanku babu yanda za'ai inma da wata manufa yazo yayi miki wani abu"

Sai a wannan lokacin Hafeeza tasaki wata irin zuciya sannan ta gyad'a kanta alamun amsawa.


*** *** ***


Cikin wani irin farinciki da annashuwa yake driving dinsa har wani shafa lallausar sumar Kansa yake,ya dade rabon daya tsinci Kansa a'irin wannan farincikin,sai faman ajiyar zuciya yake kamar an sauke masa wani nannauyen dutse daga kan faffadan qirjinsa.

Yana shiga ya gansu afalo suna kallo, cikin nutsuwa ya zauna akan kujera tareda ajiye wa Kaka goro cikin gajerar maganar sa ta kullum kullum yace"gashi"
Kaka ta kar6a tareda washe baki tadauki guda daya ta saka abakinta tadan karya tareda kallon sa tace"kamar kasan nemanka nake, dama kwana biyu banci qosai ba,nace tunda Hafeezu ya warke harya fara fita bari yazo sai yaje ya siyomin''

Wani irin kallo Hafeez yayi mata sannan yace"saboda ita yarinyar batada aiki saide yin qosai kullum? tota daina,ba zata sake yiba"

Kaka ta ta6e bakinta sannan ta kalleshi tace"kada Allah yasa tayi, idan kayi aure matarka saita dinga yimin"

Cikin sauri yadago Kansa ya kalleta, saide kafin yayi magana wata Kyakykyawar budurwa tashigo falon, lokaci daya dan annurin fuskar tasa daya rage ya dauke gaba daya.
Kaka da Yanbiyu kuwa lokaci daya fuskar su ta wanzu da farinciki, hassana da Hussaina suka miqe sum sum sukai hanyar dakinsu, Hafeez yabisu da wani irin kallo tun daga nan ya gane manufar zuwan budurwar, cikin taqaici ya Lumshe idonsa tareda budewa,adede lokacin Kaka tace"sannu da zuwa Munawwara,zoki zauna, bari nabaku waje ku zanta kafin akawo muku dan abun ta6awa"

Hafeez yadago Kansa yayiwa Hajiya Kaka wani irin kallo,kallon dayake nuni da cewa zamu gauraya ni dake.

Itama Sarai tagane kallon dayake Mata, hakan yasa cikin dakewa ta watsa masa wani irin kallo sannan tabi bayan su hassana.

Falon ya rage daga shi sai madinatul Munauwara, ajiyar zuciya ya sauke sannan yajuyo ya kalleta, batada laifi kokadan, saide bata daga cikin irin tsarin Matan dayake so,ahankali yasake Lumshe idonsa, cikin ransa yana jinjinawa kwashe-kwashe irin na Hajiya Kaka, har zuwa lokacin kan Munauwara yana qasa tana wasa da gefen mayafin ta, ahankali ya motsa lips dinsa tareda dan gyaran murya kadan, hakan yasa ta dago kanta ta kalleshi cikin kunya tace"Yaya Hafeez ina kwana?"

Hajiya Kaka da Hassana da Hussaina dasuke la6e daga bakin qofar daki suna leqensu sai ture juna suke yi,Kaka tace" ku matsa mana sai tureni kukeyi bana hangosu fa"(>-)

Husna tace"toke Kaka ai munfi ki Jin magana yanzu,ki tsaya mujiyo saimu fada miki"

Hassana tace"a a Husna,kece Zaki tsugunna nikuma zan rissina ita kuma Kaka saita tsaya kinga kowa zai dinga hangosu"

Adede wannan lokacin Hafeez ya dan gyara Zaman sa, Hajiya Kaka dasuka la6e suna kallo cikin sigar rad'a tace musu "kuyi shiru,kuyi shiru zaiyi magana"

Hafeez yadan yi wani murmushi sannan ya shafa girarsa daya yace"ai bankai matsayin yayanki ba,nikam ai sa'anki ne,any way, niba yaro bane,kamar yanda kema ba yarinya bace, kina buqatar jin gaskiya kokuma yaudara kikeso irin ta qananun samari?"

Cikin nutsuwa munawwara tace"gaskiya"

Cikin dakewa yasake kallon ta sannan yace"to gaskiya baki min ba"

Cikin sauri ta dago kanta ta kalleshi,cikin tabbatar wa shima yagyada Mata Kansa alamun tabbatar wa,lokaci daya fuskarta ta sauya zuwa 6acin rai,hakan yana nufin kwallin da Babanta yabata tasaka kafin tazo beyi amfani ba kenan.

Hafeez ya miqe tareda kallon dakin su Husna,cikin sauri suka gudu daga bakin qofar,Hajiya Kaka da take shirin guduwa itama saide kafin takai ga barin wajan Hafeez yace" ji mana"

Hajiya Kaka ta juyo tana kallon sa,Hafeez yace"idan kun gama leqen kizo kibawa baquwar ki ruwa,basai kinyi min tambaya yanda muka qare ba, kin Riga kin la6e kinji komai"

Yana fadar haka yashige da kinsa yana Girgiza kai,zama yayi agefen gadonsa yana tunanin tayaya ma zai yarda bayan yayi aure yayi amarcinsa acikin gidannan bayan Yan la6e sunyi yawa?(>)



*** *** ***


"Hafeeza"

Cikin nutsuwarta tajuyo ta kalleta, "Na'am Inna''

" ni qosan da kikayi dazu da yamma naga kin fita waje kin rabar, qosan menene?"

"Inna sadaka nayi dashi"

Inna ta Rasulu ta jinjina kanta sannan tace"ba shakka,towa kika yiwa sadaka?,ko iyayen ki?"

Hafeeza ta Girgiza kanta batare da tayi magana ba.

Sadiyan Abdullahi da tazo yi musu Allah ya Sanya Alkhairi na saukar su Hafeeza ta karyi goron dake hannunta tace" yau naji ikon Allah, toke ta Rasulu ta Yaya Zaki dage sai kinji wa aka yiwa sadaka?"

Inna ta kalleta tace" Sadiyan Abdullahi dole inji mana,idan banji ba ta ina zan fara yiwa tufakar hanci?, yanzu fa kiwon mutum ake, tace nabata dubu goma sha biyar zatayi wa wani qosai, kinga ai dole inji waye"

Sadiya tayi murmushi tace" Ta Rasulu kuda ake cewa kun samu miliyoyin kudi kiyi Mata haquri mana"

Ta Rasulu tace"kudi fa basu shigo hannu ba Sadiya,ana turo wa kawun nata banki suka rufe masa komai, dole sai yaje anbude masa"

Sadiya ta juya ta kalli Hafeeza tace" to ke Hafeeza ina kudin yake? ko kyauta kikai sadakar?"

Hafeeza tayi shiru.

Sadiya tasake cewa"kinyi shiru"

Inna ta Rasulu tace"to ai wannan shine abinda yake cimin tuwo a qwarya tsakanina da'ita, shegen baqin miskilancin ta yayi mata yawa"

Sadiya tace"to ai sai kiyi haquri ki rabu da'ita"

Ta Rasulu ta kalli Hafeeza tace"waye yace kiyi sadakar qosai?"


Hafeeza tace"kash! Inna zan kar6o miki kudin ki"

Daga haka tamiqe tabar wajan.

Inna ta saki baki tabi bayan Hafeeza da kallo.
Sadiya tadawo da hankalin ta wajan ta Rasulu tace"aikuwa yauda asuba naji liman yana wa'azi akan sadaka, inaga shi tayi wa"

Inna ta Rasulu tace"ina ruwana inma Limamin Saudia ne,nikam ai kudina na sani,nan tazo wajena dazu ta tambayeni kudin,kamar ta rufemin baki na dauki kudin nabata naga tafara shirin yin qosai, ta zauna agida taja wani qosai me shegen dadi jinake nasiyarwa ne tayi, kawai sai ihun Yara naji awaje suna kar6ar sadaka"

Hafeeza da take zubawa na'a na'arta ruwa tana jin su ta dafe kanta cike da damuwa,ka kar6i kudin Inna ma koka kar6i kudin tonon asiri.(>&)


*** *** ***


Yau tunda safe har zuwa yanzu qarfe shida na yamma Hafeez yana gida baije ko'ina ba, Hajiya Kaka tana lura dashi banda zarya dayake daga compound zuwa cikin falo babu abinda yake.
Yanzun ma suna zaune suna kallo amma kwata-kwata hankalin sa baya kan abinda ake kallo, agogon dake daure a lallausar fatar hannun sa ya kalla sannan ya miqe yafuto zuwa Compound, kai tsaye wajan masu gadi yanufa yace"wata yarinya tazo dubani yanzu?"

Megadi da tsananin mamakin yalla6ai Hafeez din yagama kashe shi yace"wallahi babu wacce tazo, ai tun safe dakake zuwa Nima babu inda nake tashi ina zaune anan ina jira ko Allah zaisa inji sallama in shiga in sanar dakai"

Cikin damuwa Hafeez yajuya batare dayace komai ba,yana shiga falo kai tsaye dakinsa ya wuce Hajiya Kaka tabishi da kallo, har akan fuskar sa tana iya hango damuwar dayake ciki.


*** *** ***


Washe gari kawu Hamza yazo gidan, Ta Rasulu ta zuba masa abinci, yanaci suna dan zance kadan-kadan, Inna ta kalli Hafeeza, tace"Hafeeza wa kika yiwa sadaka da qosan ne jiya?"

Hafeeza ta zaro idonta waje, gabanta yafara faduwa ga kawu Hamza a zaune, cikin sauri ta tashi ta zari hijabinta tace" bari inje in kar6o miki kudin''

Sai bayan tafuto tarasa yanda zatayi, yanzu gidan zataje saboda kawai kar6ar kudi? kai tsaye ta nufi gidan Maman Fadila, saide tana zuwa taga gidan arufe da alamun ta fita.

Awajan ta tsugunna tana dana sani meyasa ma tace masa zatazo ta kar6i kudin awajansa? kawai sai taje wajansa tace kudin nazo kabani? to ai kuma dama ta fada masa cewa zatazo dinne kawai dan ya rabu da'ita.

Gabanta banda faduwa babu abinda yake, haka ta dauki hanya tafara tafiya tana tunanin haduwa dashi, saida tayi Nisa sosai sannan ta tuna takardar address din gidan daya bata tana gida, haka ta juya tasake komawa gida har lokacin kawu Hamza yana nan Suna tattauna yanda za'a fara yi musu gyaran gidan shida Inna, cikin kayanta ta duba ta dauko takardar sannan tasake ficewa,kai tsaye tanufi hanyar gidan tana Addu'ah cikin ranta, saide idan ta tuna shawarar Maman Fadila saita danji sauqi aranta.

Tunda ta shiga layin unguwar gabanta yasake tsananta faduwa ganin manya manyan gidajen dasuke layin,number gidan tasake dubawa a katin dake hannunta ahankali taci gaba da takawa har tazo gaban wani hadadden gida,gabanta yasake yankewa ya fadi cikin sauri taja da baya saboda gidan ya bata tsoro sosai, can gefe ta matsa jikin wani gida ta tsaya tana jira ko Allah zaisa yafuto su hadu, batare data shiga gidan ba.

Kusan minti ashirin tana tsaye,gashi unguwa shiru tsaf za'a sace mutum batare da an sani ba,hakan yasa takoma bakin get din gidan, hannunta yana rawa tafara nocking get din gidan.
Babu 6ata lokaci taga anbude qofa,danladi direba ya kalleta, saiya ga kamar ya santa, amma kuma ya manta inda yasanta, cikin rashin sani yace"daga ina?"

Cikin zazzaqar muryarta tace"wajan...wajan...."
Gaba daya saita rikice tarasa sunan wa zata kama,Shikuma danladi ganin tarasa abun fada yasa ya rufe qofar Yakoma ciki.

Cikin damuwa tadafe goshinta,tasake kallon get din gidan, har zata sake nocking saita dakata tafara tambayar kanta idan yasake budewa to wajan wa zatace tazo?
Hakan yasa ta Yanke shawarar juyawa takoma gidan Maman Fadila idan Allah yasa ta dawo saita ari kudi awajan ta tabawa Inna, Shikuma idan suka hadu saiya bawa Maman Fadilan.

Cikin kwanciyar hankali ta juya tatafi, bayan zuciyarta ta gama nutsuwa da shawarar data yanke.

Acikin gidan kuwa Hafeez yana zaune shida Hajiya Kaka afalo,sanye yake da wando three quarter iya gwiwar sa, sai Riga marar hannu hakan yasa murdaddan dantsan sa yasake bayyana, waya yake qasa qasa,yayinda Hajiya Kaka ta kasa kunne tana so taji dawa yake wannan wayar qasa qasa kamar yana magana da mace, juyowa yayi ya kalleta tareda kashe wayar yace"tona kashe,saiki dena meqomin kunne"

Hajiya Kaka ta harare shi,ko kunya kuma saita matsar da kunnen ta daga kusa dashi din.(>#)

Ajiyar zuciya ya sauke yace "ina yaran nan suke?"

Kai tsaye Hajiya Kaka tace"na aikesu suje su nemo min qosai,dan ladi Naso intura saboda dama shine yake siyo min, kuma baya nan"

Hafeez ko tanka mata baiyi ba ya tashi yafuto daga falon, kai tsaye wajan me gadi yanufa yace"Baba yauma wata yarinya 'yar buzuwa haka ba tazo nemana ba?"

Baba Megadi yace" ito,gaskiya yanzu de babu, amma danladi yafuta yanzun nan,kafin ya tafi yacemin in sake kula da qofa sosai saboda dazu wata yarinya tazo yana tunanin irin larabawan nan ne Yan gudun hijira suka shigo gari"

Tun kafin yagama magana Hafeez ya runtse idonsa, baqin ciki ya kamashi, cikin 6acin rai ya kalli Megadi yace"kace danladi driver ya koreta?"

Baba Megadi yace" tabbas haka akayi ranka ya dade,tuba nake yalla6ai wallahi na zaga toilet ne alokacin"

Cikin damuwa Hafeez yace"amma ba danladi ba ko dan litinin ne aibe kamata ku koreta ba ko?"

Baba Megadi yayi shiru,tabbas duk yanda akayi Hafeez din yana cikin damuwa akan rashin haduwar sa da yarinyar duba da yanda tun jiya yake faman tambaya ko tazo.

Cikin bacin rai Hafeez ya buga qafarsa aqasa tareda juyawa ciki kamar zai fashe da kuka.
Kai tsaye dakinsa yashiga zai dauko car key yafita ko Allah zaisa ya ganta.

Hafeeza kuwa tana cikin tafiya taji anja hijab dinta tabaya,tana juyawa taga hassana da Hussaina Yan ajinsu, lokaci daya ta saki murmushi har dimples dinta suna futowa, Husna tace"Hafeeza dama ana ganinki?"

Kafin tayi magana hassana tace"aikuwa tunda kikazo layin mu dole kizo muje gidanmu ku gaisa da Kaka"

Hafeeza tace"zan dawo daga baya yanzun ne...."

Tun kafin ta qarasa magana Husna tace"yanzun me? gaskiya ki juya muje inba haka ba da daddare zakiga kunama"

Hafeeza tayi murmushi tajuyo suka taho tare dasu hannun ta yana cikin na Husna.
Tunaninta begama tsinkewa ba saida taga gadan-gadan sun nufi gidan da wannan mutumin yabata address, lokaci daya kanta ya kulle,me hakan yake nufi? dama gidansu Husna ne nan? menene hadinsa dasu? tana cikin wannan tunani taga anbude musu gidan cikin girmamawa saide wani ne daban yabude musu yanzu, ba wanda yabude Mata bane dazu.

Gabanta ne yasake tsinkewa bayan sun shigo cikin harabar gidan, ba qaramin tsorata tayi da gidan ba, saboda a tarihin rayuwar ta bata ta6a shiga gida mai kyan wannan ba,su Husna sai tsokanar ta suke suna mata magana amma hankalin ta begama kwanciya da gidan ba, kokadan bazaka ce gidan hausa wa bane saide turawa.

Suna shiga falon wani irin qamshi me sanyi ya daki hancin Hafeeza,ga sanyin esi, ta nutsa qafarta cikin capet tana jinjina irin wannan daula dasu Hassana suke ciki amma koda wasa basuda girman kai da dagawa irinna wasu daga cikin Yayan masu kudi.

Hajiya Kaka tana ganinsu tace"yana ganku hannu wayam"

Hassana taja hannun Hafeeza suka qarasa wajan Kaka tareda fadin" Kaka ga qawarmu Hafeeza, wadda ta samu kyaututtuka ranar da mukai sauka? kin tuna?"

Hajiya Kaka tayi shiru tatafi tunani sai can tace" natuna mana,ba itace me zaqin muryar nanba? wacce kwana ki kuke cewa dinki ya muku yawa saide qugun Hafeeza?"(=2=F)

Cikin sauri dakuma son basarwa Husna tace"Haba Kaka, yaushe akai hakan?"

Cikin tantama Hajiya Kaka tace"au to kode ba'ita bace? tonima de bansan anyi hakan ba"(=)

Hafeeza tayi murmushi ta kalli Hajiya Kaka sannan tace"kuma kika fada?"

Hassana tayi dariya tace" bakisan Kaka ba kenan"

Tajuya ta maida kallon ta zuwa wajan Kaka sannan tace"Kaka bamu Samo miki qosan ba, ance wacce takeyi din waita daina"

Gaban Hafeeza daya Yanke ya fadi ba tasan lokacin data zura hannun ta cikin hijabi ta dafe qirjinta ba, wajan ta sukaje neman qosai kenan?
Bata gama tunanin da take ba taji Kaka tana cewa"ai tunda wancen baqin miskilin yace ta daina nasan za'a Rina, bari yafuto yau duk inda qosai yake saiya nemomin shi"

Hafeeza ta danyi murmushi sannan tace"ina kwana Kaka?"

Cikin Jin dadi dakuma yaba hankalin yarinyar Kaka tace" lafiya kalau Hafeeza,kinada hankali da nutsuwa Allah yasa kina jin magana ba kamar takwaranki ba"

Kan Hafeeza ya daure tarasa gane waye takwaranta, sai tayi murmushi kawai ba tace komai ba.

Husna ta kawo lemuka da ruwa da meat pie ta ajiye agaban Hafeeza sannan ta bawa Kaka wayarta tana cewa "Kaka kinga dinkin da telan mu yayi mana, ankon gidan Uncle Shu'aibu,ni kwata kwata dinkin bemin ba"

Hajiya Kaka tayi zooming photon dinkin tagani sannan tabata wayar tace"ai anko ne, koma Yaya ne kunde saka,kada yan'uba suce baku saba"

Tajuya ta kalli Hafeeza cikin salon jan magana tace"koba haka ba Hafeeza?"

Hafeeza tayi murmushi tace"hakane kam"

Hajiya Kaka tasake cewa"ko kin iya dinki su dinga kawowa kinayi musu?"

Hafeeza tayi murmushi tace"A a Kaka ban'iya ba"

Hajiya Kaka tace"Au to! jinake kin iya,Nima da sai in dinga bawa HAFEEZU nawa yana kawo miki, amma gaskiya ni in dinkin Zaki min ma saide kimin irin wanda kike sakawa,koba haka ba? saboda Idan zanzo gidanki inci kwalliya ta dashi inzo ko Allah zaisa mijin ki ya yaba"(=)

Hafeeza tayi murmushi,ta lura matar tanada barkwanci sosai dakuma iya zama da mutane,cikin murmushi tace"Kaka ai abunda zan d'inga mikin ma shine zai siyo miki da kudinsa"

Hassana ta bude lemon da Husna ta kawowa Hafeeza ta zuba Mata a cup sannan ta tura Mata gabanta tana cewa "inde Kaka ce to zata qwace miki miji kuwa"

Hajiya Kaka ta miqe zata shiga kitchen ta kalli Hafeeza tace"kici dan abun ta6awar 'yar nan,bari na baku waje ku danyi gulmar samarin ku"

Gaba dayan su dariya suka saki,Husna ta gyara zama tace"Hafeeza bakici komai ba"

Sai alokacin ta dauki meat pie din taci dan kadan, ta ajiye sauran.

Cikin nutsuwarta ta kallesu tace"bari in tafi gida,kada a nemeni"

Husna ta Harare ta tace"har wani? daga zuwan naki? gaskiya ki tsaya muyi fira tukunna"

Hassana tace"Hafeeza ya samari? nasan suna nan lodi-lodi yaushe zamusha biki?"

Hafeeza tayi murmushi tace"wa? a a wallahi nima bansani ba"

Hassana tace" mukam wallahi Gara ayi mana auren mu,mazaje suna futowa zamuyi wuf, mu shige"

Hafeeza tayi murmushi tadan saki jikinta ganin Kaka bata wajan, tace"to wanne irin mazaje kuke so? ance yawanci yanbiyu sunfi son su auri mazaje suma Yan biyu"

Husna tace"hakan ma yanada dadi,ko banza kasan cewa kana tareda yar'uwarka, amma kinga ai abun dace ne, nide gaskiya inason namiji mai irin halin Yaya HAFEEZ, bana son hayaniya"

Hafeeza tanajin sunan gabanta ya fadi, tun kafin tayi magana Hassana tace"maganar gaskiya nide duk wanda nasamu banda za6i, kefa Hafeeza?"

Tafadi maganar tana kallon Hafeeza.

Adede lokacin Hafeez yabude qofar d'akinsa zai futo fuskar nan tasa ahade kamar hadari,har yanzu taqaicin rashin haduwarsa da'ita yake, saide sako kan da zaiyi zuwa falon idonsa ya sauka a kanta, gabansa yayi wata irin faduwa, cikin sauri yajuya da baya, ganin babu wacce ta lura da budewar qofar dakin nasa acikin su,saide bai maida qofar ya rufeta duka ba, yana iya hangosu, sannan kuma yana iya jiyo abinda suke magana akai.

Hafeeza kuwa zuciyarta daya tadan juya fararen idonta sannan tatafi duniyar tunani tana hango siffar saurayin ta Gaddafi acikin idon zuciyar ta sannan tace" inason namiji hafizin Alqur'ani,ban damu da rashin kudinsa ba,saide inaso ya kasance me qirar jarumai,me murdadden dantsan hannu"

Cikin sauri Hafeez dayake Jin firar ya kalli dantsan hannun sa,mamaki yagama kashe shi dama tana magana haka? hakan yana nufin batada aure kenan.

Hafeeza taci gaba da fadin"miskili wanda baya son hayaniya,kuma kyakykywan gaske"

Wannan Karon ma cikin sauri ya kalli fuskar sa ta screen din wayar sa dake hannun sa,har wani gyara sumar Kansa yake,gaba daya hankalin sa ya tafi zuwa gareta,besan ma yana wannan dube duben ba.

Adede lokacin wayar sa ta dauki qara,cikin sauri su Hafeeza suka juya suna kallon wajan, saide dayake ala6e yake, basu ganshi ba saide qarar wayar kawai.
Cikin taqaicin shigowar kiran Hafeez ya runtse idonsa,ya daidaita Kansa fuskar nan tasa ya daure ta kamar bashi ba,kawai yayi shahada yafuto daga dakin yana d'an danna waya.

Yana dan dago Kansa daga danna wayar dayake,idonsa ya fada cikin na Hafeeza,gabanta yayi wata irin faduwa sakamakon kayan data ga yana sanye dashi,kwata kwata wandon iyakar sa gwiwa,ga wannan Riga gaba daya dantsan sa awaje suke anyi masa zanen tattoo ajikin hannayen nasa,ga dan kunne amaqale a kunnansa na hagu, bata ta6a ganin namiji haka azahiri ba, hakan yasa cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa,gabanta banda faduwa babu abinda yake tana Addu'ah cikin ranta Allah yasa baiji abinda ta gama fadaba.

Complete document 1k




Amnah El Yaqoub
'<

[6/14, 2:25 PM] El Yaqoub:


Koda wasa bai nuna wata magana tata6a had'ashi da'ita ba,d'auke Kansa yayi fuskar sa ahad'e kamar koda yaushe.
Hassana da Husna atare suka had'a baki wajan gaidashi tunma kafin ya zauna.

Furucin YAYA da Hafeeza taji 'yanbiyun sun fada hakan yasa tagane cewa kenan shid'in Yayan sune, tsananin mamaki yagama kamata,kuma har zuwa wannan lokacin gabanta banda faduwa babu abinda yake, kanta aqasa tana tuna abubuwan da suka faru tsakanin su ita dashi, yanzu fa kamar fanko yake ganinta tunda yariga yaga qirjinta,wani irin baqin cikin abinda ta aikata na bawa Fadila nono ya kamata,mema yakai ta ne? meyasa tayi hakan? Kowa yana ganinta da daraja, amma ban dashi, shi din kallon da zai dinga yimata daban.
Tunanin tane ya tsinke,taji kamar wani abu ya fada cikin qirjinta sakamakon Zaman da Hafeez yayi dab da'ita,saide akwai 'yar tazara atsakanin Zaman nasu, amma duk da hakan, awajan Hafeeza kusancin yayi kusanci sakamakon bata sababa.

Kanta aqasa yake har lokacin,gade esi iya esi afalon amma fuskarta harta fara hada gumi,cikin rawar murya tadan kalli gefensa kadan sannan tace"Ina kwana''

Agajarce ya amsa da "Lafiya"

Yadan kalli gefenta yaga abinda yake nema Wato remote,hakan yasa yakai hannun sa ya dauki remote din sannan yafaki idon qannan nasa, yayi sauri Yadan sake matsawa kusa da Hafeeza,itade Hafeeza kanta yana qasa,gabanta sai faman faduwa yake,Sarai taga lokacin daya sake matsowa kusa da'ita.

Hafeez ya kalli Hassana yace"Ke kawo min Coffee"

Cikin sauri Hassana ta miqe tashige kitchen.

Ahankali Hafeeza ta dan dago kanta, adede lokacin Hafeez ya kalleta afakaice,idonsu yana haduwa tayi sauri tasake yin qasa da kanta.

Hajiya Kaka tashigo falon taga yanayin Zaman Hafeez da Hafeeza yayi d'an kusanci,mamaki ya kamata ganin yanda Hafeez din ba

Please Login or Register in order to submit comment