Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

💙💙
RABON KWADO.. 💙💙




Tare da Khayratie Er Mutan Ungogo..💋




Ina roqon Allah S.W.A yadda ya bani ikon farawa ya bani ikon ganin na kammala wannan littafi.
Wannan littafi qirqirarren labari ne,wanda nake fata ya fadakar,wa'axantar,Ilimantar da kuma nishadantar da masu karatu. A matsayi na yar kowo wanda wannan shine littafi na na farko ina son idan anga kuskure ko gyara ayi gaggawar sanar dani.


Na sadaukar ga wannan littafi ga Qawata,Aminiyata kuma yaruwa mafi soyuwa agareni wato RUQAYYA RABI'U MUSA(RUKY NICE)Allah yabar qauna.


Bismillahirrahmanirrahim🙏


🅿1-🅿5




Kamar kullum yauma kwance nake akan makeken gadona ina sana'ar tawa wato kuka,wanda ya zamar min jiki duk daren duniya sai nayi shi tunda na tsinci kaena a sabuwar rayuwa.Jin Alamar bude qofa yasa na fara qiqarin hadiye kukana dan ko kadan banason yara na suxo su ganni a wannan hali.
Iman ce ta qaraso ta fara tashi na don a zatonta bacci nake.


"Aunty!Aunty!ki tashi daddy yace kiyi mana shirin bacci mu kwanta gobe akwai school"


Saida na qarasa goge hawayena da hijabin dake jikina kafin na fara sakkowa daka bed din.
Wanka nayi mata na shiryata cikin nighty dinta pink sannan na hade mata qashinta da band.


"Kije ki kira ya shahida itama tazo tayi bacci"nace ina mai nuna mata qofa dan surutunta ya fara haddasan ciwon kai ga kuma kukan da nasha.


A tare suka shigo da yoghurt dinsu a hannu.


"Aunty kinga daddy ya siyo mana kuma harda coculate ita mun shanyeta a falin daddy"shahida tace tana nuna min jarkar dake hannunta.


Murmushi nayi tare da cewa"gsky daddy ya kyauta,kunce masa kun gode koh?


"Mu mun fada amma ya shahid bai fada ba"shahida ta kuma fada.


"Wai da gaske babyna?"na tambayi iman ina shafa kanta ganin alamun bacci ta fara ji.


Cak na dauketa kasancewa suma basu da jiki kamar ni na dorata bisa gado,kafin na kama dayar akun tawa nayi mata wanka.
Saida nayi musu addu'a na tabbatar sunyi bacci kafin na fara shirin nawa wanka.
Shirina na gama cikin nawa kayan baccin milk calour kafin na feshe jikina da turare kasancewa ta ma'abociyar son qamshi.
Kaina na qurawa ido ta jikin mirrow,basai an fada min ba nasan ni kaena na rame,to ba dole na rame ba?kullum cikin aiki da walahar yara ga kuma kuka da yawan tunani.


Allah sarki Amminah gsky ina kewarta amma ita da abbi naga alamar sun manta dani tunda ko kiransu nayi a waya bata ma shiga bare nasa ran jin muryarsu.zaman kadaecin nan ya fara damuna tunda idan su iman suka tapi school tun safe sai yamma,shi kuwa mai gidan sai nayi kwana biyar,shida kai har sati daya ma ni banganshi ba.
Kana naka Allah na nasa,wai ni khadija Autar Amminta nice rayuwatah ta dawo haka?Ba haka na tsara rayuwar aure na ba amma ga a yanda taxo min.Amma a hakanma cikin godiyar Allah nake kuma na yarda da qaddara.


Nasan mai karatu yana cikin zaquwa da sonjin cikakken tarihi na,to ga asalin wacece ni👇




FLASHBACK.


Cikakken sunana shine khadija isah muhd,mu cikakkun hausawa ne maxauna garin kano unguwar karkasa.
Mahaifinmu ma'aikacin gwamnati ne ba wani mai kudi ba,muna rayuwa cikin rufin asiri da kuma qoqarin farantawa juna.


Amminmu mu biyar ta haifa duka mata,hakan yasa dangin mahaifinmu suka dora mata karan tsana acewarsu uwar mata ce taqi haifar da namiji,ko a xatansu mutun shike xabarwa kansa abinda zai haifa?oho.
Rashin jituwar dake xakanin Ammi da dangin abbi yasa ko kadan bamu qaunar zuwa wani abu daya dangancesu,tun abbi yana fada har ya gaji ya qyale mu,sbd ko munje ma ranmu a bace yake dawowa.


Yaya Aisha itace babba a gidanmu,sai Ya Ruqayya,ya Fatima,sai kuma yaya zainab wadda daga ita Ammita qara haifar wata amma babu rai,tun daga lokacin haihuwar ta tsaya sai bayan shekara 3 sannan ta samu cikina wanda kowa ya cire tsammani dashi,hakan yasa kowa ya dora soyayyarsa kan cikin tare da fatan sauka lafiya.




Bayan wata tare Ammi ta haifeni,wanda kowa yake cewa kyawun yan gidanmu aka tattaramin,a cewarsu nafi kowa kyau tun ina jaririya.


Haka na taso cikin gata da kulawar iyaye na da yayyena abin alfarina,dan kowacce ji take dani komai aka samo to na autar ammi ne,haka abbi duk fitar da zaiyi to sai da tsarabar auta zai dawo.


Ina primary 5 akayi bikin yaya Aisha inda aka kaita unguwar sharada.
Munyi kewarta sosae duk da a lokacin ba wani wayo ne dani ba amma nasan shaquwar dake tsakaninmu,dan so da dama muna sharing problems ayi a gama ammi batasan anyi ba,duk da lokacin ba wani fahimtar abinda suke mgn nake ba hakan bayasa su ware ni muna tare koda yaushe school ce kawai take raba mu,hakan yasa bani da wasu qawaye bayan yayyena sai Nusaiba da muke class daya kuma a farkon layinmu gidansu yake shiyasa muke tafiya tare mu dawo tare.


Tafiyar yaya aisha yasa gidan ya fara shiru dan ya ruqayya ba xama take ba tana schooling a CAS kano.
Ya fatima tayi candy tana waiting result yanxu koda yaushe tana gida,amma kasancewarta bamai yawan mgn ba yasa bama wani hira sosai,to ni dimma ba wata gwanar surutu bace,barni da da shagwaba da son jiki,koda yaushe ina jikin ammina ko su yaya fatima.
Ya zainab yanxu tana Ss1,mu kuma muna shirye shiryen common interest.


Cikin ikon allah mukai Exam,inda rana tsaka abbi yazo da mgnr data tayarwa da duk yan gidan hankali,wai xa'a kai autar ammi bording school.saida aka kai ruwa rana kafin aka shayo kan ammi ta yarda akaini ni kuwa banda kuka babu abinda nakeyi.
Ammi dasu yaya fatima kullum cikin rarrashi,nice a siyon wannan a siyon wancan har ranar tafiya mkrnt tazo aka kaini makarantar yan mata ta DALA.
Fadin irin kukan dasha bata lkc ne dan harta abbi nasan kawai dauriya yake amma su yaya zainab suma sunsha kuka.


Bansha wani wahala ba kasancewa ta kyakkyawa kuma mai tsafta yasa seniors suka ringa nan nan dani nidae a daddafe mukae first term,sbd ni irin mutanennance masu maqon uwa bare tawa uwar da muka shaqu sosai.


Ranar da muka samu hutu kuwa murna biki har baka😬.
Abbi ne yaxo ya daukeni a machine dinsa.muna xuwa gida kuwa duk yanuwana sun hallara,abinci kuwa kala kala kamar ana jiran dalibi daga malesia😜.
Ranar nayi yinin farin ciki,inda nake maqale da jaririyar yaya Aisha mai suna muhibba.Anan nakejin zancen sa ranar ya ruqayya amma abin takaicin ina school xa'ayi.
Tun daga lkcn na fara kukan shagwaba ina buga qafata a qasa ni a dole yar auta😄


"Kinga ni miqon 'yata karki fadarmin da ita"ya aisha ta fada tana karbar muhibba.
"Dan allah ya ruqayya kice a daga bikin sai na nawo"na fada ina zama akan cinyarta.


"To Ammi haka za'ayi"tace tana ture ni daga jikinta.
Dukansu dariya suka saka hakan ya bani haushi nayi dakunmu da gudu kamar xanyi kuka.
Ina jiyosu suna hira akan yawan shagwaba da son jikina Ammina tana shigarmin.
Sai dare mijin ya aisha yaxo ya dauketa,ba mgnr da bata min ba naqi kulata dan har lkcn fushi nake dasu hakan yasa ko dakin ban kwana ba na tafi gadon ammi na kwanta.


Washe gari gidansu Nusaiba na yini inata bata labarin bording ita kuma allah da yayita tana sha'awar bording school.Sai wajen magriba na dawo.


Haka har hutunmu ya qare babu yadda ya aisha batai ba naxo gidanta hutu naqi,nace ni ban gaji da gani abbi da ammi ba.haka dai na tattara na koma inata kumbure kumbure na.








🥰Khayratie Er mutan Ungogo😘


💙💙 RABON KWADO... 💙💙






💋 Er mutan Ungogo💋






🅿6-🅿10


Haka rayuwa ta cigaba da tapiya,inda akayi bikin ya ruqayya da mijinta abbas aka kaita gidanta dake tarauni.


Ya fatima ta samu gurbin karatu a polytechnich dake nan kano.


Yau satinmu daya da dawowa daga mkrnt,sosai nake jindadin holyday din dan nakaiwa yanuwa na xiyara nida ya zainab kasancewar ya fatima lectures sun mata zafi.
Yau Lahadi na tashi da shirin xuwa gidansu qawata Nusaiba dan ammi tace xuwanta biyu bama nan,kuma nayo mata guxurin labarurruka kala kala na mkrntrmu.


Ammi nayiwa sallama na dauki sabon hijab din data siyamin ina mkrnt na saka na fice abuna kicin nutsuwa.


Sallama naita kwadawa a qofar falon kafin daga bisani najiyo alamar tafiya.


Dogon saurayi ne mai cikar halitta sai saje da qasunba da sukayiwa dogon hancinsa qawanya,duk da a lokacin shekaruna 13 ba wani kyakkyawa na sani ba amma xan iya cewa wannan kyakkyawa ne.ko ba'a fadan ba nasan wannan yayan nusaiba ne duk da ban taba ganinsa ba amma kamanninsu ya nuna hakan.


Kamar yadda ya zuba masa ido haka shima ya zuba min nasa idanun.bazan iya tantance iya lokutan da muka dauka a haka ba kowa da abinda yake kissimawa a ransa.
Sallamar Nusaiba ce ta katse mana kallon da mukewa juna na qurrilla.Duk sai naji kunya ta kamani amma shi gogannaka falon ya koma ba tare da yace komai ba.


Da gudu nusaiba taxo ta rungume ni tana dariya.


"Ai naxata baxaki xo ba harki koma"


"haba dae xanxo mana,Ammi ma tace zuwanki biyu bama nan"


"Eh mn,ai na qagu nasha lbrn bording,daxu ma fa har umma na tmby da xata fita nace xanxo gidanku shine ya sadiq ya hanani"


"Au dama wannan shine ya sadiq din?"nace ina rage muryar kamar ina tsoron karya jini.


"Eh shine,shima shekaran jiya ya dawo,ni banso dawowarsa ba gashi sai aiki yake saka mutan....."bata qarasa ba mukajuyo muryarsa mai sanyi yana cewa"Nusaiba!!


A tare muka xaro ido dan a xatonmu yaji mgnr da mukeyi.
Da sauri ta shiga falon.
Bata dade ba ta fito tana tura baki gaba.


"kinga ni koh?wai chemist zanje na siyo masa mgnin mura,kuma fa idan umma nanan ba'a aikena titi"


"To muje na raka ki dan nima yau yawo nakeso"


Tafiya muke ina bata labarin bording,mun kusa tsallakawa titi kawai naji kamar an watsamin ruwa a jiki.Mexan gani?kwata a jikin hijabi na sabo??
Bin motar nayi da ido dataketa sharara gudu ba alamar zata tsaya ma.


Nusaiba na kalla dan tuni idanuna suka ciko da kwalla ganin yadda mutane suke kallo na wasu har dariya suke min.


"Kiyi hqr bari naje na siyo na dawo,shi kuma shida allah"nusaiba tace tana yin gaba da sauri.


Bazan iya tsayawa a gurin ba,ga zuciyata dake zafi hakan yasa nayi tafiyata.
Ina shigo layinmu na hango motar dazu a kusa da uncompleted building din dake layinmu,ban san lokacin da zuciya ta tiqoni ba na nufi motar dan ni kaina bansan idan naje mexanyi ba.
Ina xuwa nayi knocking glass din dan ba'a ganin na ciki.Nafi munti biyu a tsaye dan harna fara tunanin mai motar baya ciki kafin naga an fara sauke glass din qasa.


Saida na fara galla masa harara kafin na fara mgn da fada dan ya kaini bango.


Kai makaho ne da kana ganin ka fallatsawa mutum kwata bazaka iya tsayawa ka bashi hqr ba?ko an fada maka kudi haukane?aikin banxa kawai."nace tare da jan tsaki nayi hanyar gida.


Ina shiga soron gidanmu na fashe da kuka sannan na shiga.da ya fatima naci karo taci kwalliya xata fita ta riqeni.


"Me akai miki auta?fadawa kwata kikayi?"
Duk tmbyoyin da tamin ban amsa ba saima qara sautin kukan da nayi dan Ammina ta jiyo.
Ai kuwa saeda ta fito nayi mgn.


"Ba wani ne a mota ya fallatsamin kwata ba"


"Allah sarki yi hqr qila ma bai sani ba"ya fatima tace tana ciren hijabin.


Jin Ammi taqi mgn yasa na kuma fashewa da kuka😩.


Itadai ya fatima gaba tayi dan tasan halina sai Ammi ta rarrasheni xanyi shiru.
Dakinmu na shiga ya zainab sai bacci take,kanta na fada na cigaba da kukana har bacci ya dauke ni.


Sai magriba na tashi sannan Abbi ya dawo dan haka yana bani tsaraba na ware aka cigaba da hira dani.


Washegari nusaiba tazo itama daqar na kulata dan haka nace itace ta jamin aka zuban kwata.da yake tana da hqr har hqr ta vani sannan muka cigaba da hira.




Ana gobe xamu kama mkrnt na fito raka nusaiba naci karo da ya fatima da wannan mutumin da nayiwa rashin kunya ranar daya xuban kwata a hijabi.
Inaji nusaiba ta gaida shi ni kuwa na maka masa harara nayi gaba abina.


"Kai khadija meyasa baki gaida saurayin ya fatima ba?kinga baxata ji dadi ba"Nusaeba tace.


"Bazan gaida shi dinba,kuma insha allah bazata aureshi ba mugu kawai😏"


Kinsanshi ne?"


"Eh mn shine ya xuba min kwata ranar,bakiga na taho ba?zuwa nayi nayi masa rashin kunya"


Zaro ido nusaiba tayi"a ina kika ganshi?


A...mgnr ce ta maqale sakamakon hango yayan nusaiba da nayi yana nufo inda muke.


kallo na yake yana tahowa nima kuma na kasa dauke ido daga kansa ko meyasa?oho
Saida ya qaraso sannan na iya dauke idona daga kansa.Qasa nayi da idon ina wasa da azurfar dake hannuna.


"Yaya har kun dawo?"nusaiba tace da alama ba'asan ta fito ba.


"Kika qaramin mgn saina bigeki,wuce gida kafin ka Karya ki"
ya sadiq yace.


Sumsum nusaeba ta wuce ko sallamar da muka sabayi idan xan koma mkrnt yau ba muyi ba.


"Ke kuma baki iya gaisuwa ba koh?"najiyo muryarsa.
Har lkcn na kasa dago ido.


Ina yini?"na fada a hankali


"Bazan amsa tunda saida na roqa"


Murmushi kawai nayi dan wata kunyarsa nakeji ban san dalili ba.


Gobe sai scul ko?"naji yace


Daga masa kai kawai nayi alamar eh dan duk a takure nake kodan ban taba tsayuwa da wani haka ba,kuma ga kallona da yake yi duk da ina kallon qasa amma a jikina inajin kallona yake.


"To kimin alqawari xakiyi krt kuma kece Xakiyi first position wannan term din"


Bansan lkcn dana daga idona ba na kalleshi.gyada min kansa yayi alamar haka yake nufi.


"Nayi maka alqawari"nace


"Tom kije gida kinga anfara kiran magriba."


To nagode"nace tare da juyawa na nufi gida.


Ina idar da sallah ya fatima ta kama kunnena na dama.


"Dama jira nake ki idar yarinya,shine dazu kina ganin Abdul kikaqi gaidashi koh?har nusaiba ta gaidashi amma ke kikayi kaga koh?"


"To wai ba shine ya zubamin kwata ranar ba"na fada kamar xanyi kuka sbd har lkcn bata sakar min kunne ba.


"Sbd ya zuba miki kwata sai kiqi gaida shi koh?so kike yace yan gidannan bamu da tarbiyya?"


Aa kiyi hqr zan gaidashi gobe🙁"na fada danta sakarmin kunne na.


Daya fi miki yarinya"tace kafin ta sake ni.


Da dare kwatakwata bacci ya qaurace min,in banda tunanin yan maganganun da mukayi da ya sadiq ba abinda nake.To me hakan ke nufi?
Daqar bacci barawo ya dauke ni.
Washegari da safe Abbi ya lula dani mkrnt cike da kewar yan gida da kuma........
Guess who?


Duk wadda ta fada dai dai Mari uku


💙💙 RABON KWADO..💙💙




Na Er mutan ungogo💋💋




Luv u oll Readers❤❤❤






🅿11-🅿15




Haka na mayar da hankalina akan krt domin ina son na cika alqawarin dana daukarwa ya sadiq duk da damacan ina mai da hankali dan ana sakani sani farko farko a class dinmu,amma wannan term din saina qara jajircewa dan ganin na bawa kowa rata a class dinmu.


Da lokacin visiting tazo naji dadin ranar domin duka yanuwa sunxo wani abin dadinma harda nusaiba.
Haka mukaita zaga mkrnt ina nuna mata abubuwa da kuma mutanen da nake bata lbrnsu.
Da lokacin tapiyarsu yayi kuwa rasa inda xansa kaina nayi dan saida ya aisha taji haushina wai na fiya fitina indai ban nutsuba bazasu qara zuwa ba.
Dan dole na nutsu na goge hawayena amma xuciyata suya kawai takeyi.
Nusaiba ce ta kama hannu na mukai inda ba mutane sosai ta bani wata qaramar leda wai inji ya sadiq😀


Dama yananan?"nace da ita ina murmushi.


"Eh to da ina zaije?kullum ya dameni wai saina bashi lbrnki,yanxu bakiga shirin da mukeyi da shi ba"


"Allah sarki,kice ina gaidashi"


Hararar wasa tayi min"ni yar aikenki ce?"


To shikenan karki fada din"nace ina yin gaba.


Saida muka koma hostel na nutsu sannan na bude ledar.
Kayan zaqi ne akai wrapping a wata leda mai gyalli sai zobe mai kyau da qaramar takarda.
Takardar na bude ina murmushi.
Harna gama karantawa ban fahimci komai ba,kawai dai nasan akwai tunin alqawarin dana daukar masa.
To meyasa ya damu nayi krt?tmbyr danayi tayiwa kaina kenan amma ban samu amsa ba.
Kodai sona yake?Aa bazan yaudari kaina ba nasan ni ba mate dinsa bace,dan nasan bazai rasa budurwa ba.mutumin da ya gama service Yana neman aiki me xaiyi da Er Js 3.
Haka dai na gama tunani na na tattara kayan na ajiye.


Jiya muka dawo daga mkrnt amma allah allah nake naje gidansu nusaeba,abinda da sae ammi tayi ta mita banason fita kullum ni kenan a gida kamar daddawa amma yau nice washegarin da na dawo xan fita.
Dana tambayi ammi xanje gidansu nusaiba saida ta tmby me ake a gidan?nace kawai dai na gaji da zama ne xanje muyi hira.Dama su ya fatima tunda na dawo basa xama wai shirin bikinta ita da wannan mutumin.
A jiyanma dana dawo saida mukai da ita nace mata"wai ya fatima ki rasa wa xaki aura sai wannan mutumin?


Janyo ni tayi"wai dan allah me abdul yai miki kika tsaneshi haka?"


"Kawai mugu ne shiyasa,kuma dan yaga yana da kyau da mota shine yake wulaqanta mutane"


Bata cemin komai ba ta sake ni.


Dan haka ni ba wani shirin bikin da nakeyi dan a zuciyata haka nace dama muna mkrnt xa'ayi,dan yanxu har ya fatiman ma haushinta nakeji.


Na dade a bakin get din gidansu nusaeba na kasa shiga,ni kaina bansan dalili ba.
Ganin qaninta haidar yasa nace yaje yace mata taxo ina kiranta.
Bai dade ba ya dawo wai ya sadiq yace idan bazan shigo ba na koma.
Murmushi kawai nayi na samu wani dutse a qofar gidan na zauna dan na koma gida tmbyoyi xansha a wajen ammi.
Wasa nake da qasa ina rubutu ina gogewa naji tsayuwar mutum a kaina.
Ya sadiq ne tsaye ya xuban mayatattun idanunsa,ba shiri na maida kaina qasa dan gani nayi ya qara wani kyau.


"Gidan surukanki ne shiyasa kk kasa shiga koh?"
Ban dago ba saima qara boye fuskata da nayi cikin hijab.


"Ki tashi ki shiga ciki kinga kowa yazo wucewa saiya kallemin ke"


Maganganun nasa naita juyawa a kwakwalwata "a kalle masa ni?"
Maganarsa ce ta katsen tunani.


"Tunda bazaki shigo ba ki tafi gida"ya tada yana shigewa gida.
A hankali naja qafafuna nayi gida dan ji nake kamar ban kyauta masa ba.
Haka naje gida sukuku nacewa ammi nusaeban batanan.
Washegari inata zuba idon ganin nusaeba shiru har dare.
Tsahon kwana biyu ba nusaiba duk sai naji ba dadi dan nasan haka kawai bazata qi zuwa ba,dazu ammi har tmbyta tayi wai nusaeba nanan kuwa.


"Auta xo ga cingam din biki ki kae gidansu nusaiba"ammi tace tana lissafa cingam.


"Wlh dan gidansu nusaeba ne da bazan kai cingam din bikin mugu ba" na fada ina kallon qofar dakinmu dan nasan ya fatima ta jiyo ni.
Ai kuwa fitowa tayi nawo hanyar waje da gudu ina dariya.


"Ammi ki rabani da yarinyar nan wlh xan zane ta"ya fatima tace.


"Ke yanxu akan saurayin kike wannan abun?ke kuma bansan sakarci xo kije inda na aike ki"ammi tace.


"To Ammi kiyi mata mgn karta dake ni"
Jin anyi min shiru yasa na shigo ina rabe rabe.
Wullo min ledar cingam din tayi na dauka na fice,dama hanyar xuwa gidan nake nema,dan inaso naga nusaeba(nasan wata sai tace na fadi gsk🤣).
Ganin ya sadiq danayi da abokinsa yasa nayi sauri na shige gidan duk a zatona bai ganni ba.
Nusaeba na tarar dana wanke wanke ai kuwa tana ganina ta dafe ni.


"Ke kam nusaeba bakya girma,yanzu sae kin kayar da ita."najiyo muryar umma.
Har qasa na tsugunna na gaida ita na bata saqon kafin mu shige daki nida nusaeba.


"Wai ranar kikazo kikaqi shigowa"


"Ke sauri nake ammi tace karna dade"


"Ba wani nan,gashi kinja yaya yace ya qara ganin qafata a qofar gidanku saeya karya ni"


"Dan allah da gsk?"Nace jikina a sanyaye.


"to da baki ganni a gidan ba washe gari?kindai sanni da son labari"


"To meyasa ya hanaki zuwa?


"Oho masa,ni kinga na qagu ma ya fara aiki yayi aure yabar mana gidan"


Rass!!!naji gaba na ya fadi,amma na qaqalo wani murmushi kawai.


"Kinga tapiya zanyi kinga munata shirin biki"Nace ina miqewa.


"Kai dan allah yanxu baxaki bani lbrn ba"


"Zan baki idan kinxo gida"nace ina fita daga dakin.
Har bakin get ta rakoni,ai kuwa muka ci karo da ya sadiq dina🙊🙈.
Da gudu nusaeba ta koma ni kuwa nayi kasaqe.


Khadija!!"naji yace a hankali


Daqar na samu kalmar Na'am ta fito a bakina.




🥰Khayratie Er mutan Ungogo😘
💙💙 RABON KWADO...💙💙






NA ER MUTAN UNGOGO🥰






🅿16-🅿20


"Meyasa bakyajin mgn?
Dagowa nayi na kalleshi dan bansan rashin jin da nayi ba.


Banaso nasa mutum abu ya qiyi kinji?daga yau idan nace kiyi abu ki ringa yi,ko kinaso muyi fada?
Girgixa kai kawai nayi ina tuna me yasa ni banyi ba.


"Jiya banji dadin abinda kikai min ba,nace ki shigo kk qi"


"Kayi hqr"nace ina satar kallonsa.


"Ni dama banyi fishi ba,kinsan meyasa?"
Qara girgixa kai nayi.


"Sbd bazan iya fishi dake ba"
Shuru nayi dan gaba daya na kasa gano ma'anar mgnr.


"Idan kin gama school me kk son xama?"ua katsen tunani.


"Inason zama zama doctor"


"Aa khadija ba doctor xaki zama ba,kinsan me nakeson ki xama?"
Girgixa kai nayi.
"Inaso ki zama lawyer,nayi miki alqawarin baki gudummawa da goyon vaya da aljihuna da lokacina indai kikai min alqawari zaki maida hankali kiyi krt"
Juya maganganunsa kawai nake dan naji yana mgn kamar wani abbinah.


"Koda yake gana abbi aure yake muku koh"naji ya fada


"Indai nace inason krt zai barni"
"To ki maida hankali indai kinaso mu shiryaa"


"Tom"




"Kije gida kar ammi taga kin dade"
Mamaki nake yadda sunan ammi da abbi yake radau a bakinsa.


"Ko akwai wani abu"yace dan ganin na tsaya.


"Eh,dan allah kabar nusaeba ta runga zuwa gidanmu"


"Murmushi yayi"kema zaki ringa zuwa nan gidan?"


Eh"


To zan barta ta ringa zuwa"


"Ngd"nace ina wucewa.


Ranar asabar aka daura auren ya fatima da wannan mutumin,lahadi aka kaita gidanta dake rijiyar zaki.
Sosai gidan ya daina yimin dadi sbd daga ni sai ammi dan ya zee ma ta fara zuwa wata computer school.
Hakanne yasa kusan kullum muna tare da nusaeba,idan batazo ba ni zanje.A hankali muka fara shaquwa nida ya sadiq,har takai indai a rana banganshi ba sai inji duk na damu🙁.
Hakan yasa na bashi no.din ammi duk dare muna waya ba tare data sani ba.
Ana gobe xan koma school kuwa kuka ne kawai banyi masa ba amma shagwaba ba'a mgn.
Daqar ya lallasheni mukai sallama dan saida ya nunamin indai ban maida hankali nayi krt yadda anan gaba zaiyi alfahari dani ba zai daina kulani.
Haka washegaru na tashi sukuku har abbi saida ya tmby ni koh lpy?nace masa kaina yana min ciwo.




AFTER 3YEARS


Abubawa da yawa sun faru a cikin shekaru uku,ciki kuwa harda kammala krtna na secondry,inda na dawo gida cikin dokin ganin iyayena,yanuwa,aminiyata da kuma masoyana a haqiqa wato ya sadiq.
Zuwa wannan lkc soyayya mai qarfi ta qullu a tsakanina da ya sadiq amma a gidanmu ya zainab ce kawai tasan tsakaninmu.
Ya aisha yanxu yaranta 4 biyu maza biyu mata,ya ruqayya itama yaranta 4 duk maza,sai ya fatima da take da yara 3 namiji sai mata guda biyu,ya zainab yarta daya amma allah yayi mata rasuwa,sai yanxu da take dauke da wani cikin.
Sosai nakeson yaran yanuwana kamar yadda iyayensu suke sona,amma wani abinda zai bawa mai krt mamaki har yanxu bama ga maciji da mijin yaya fatima,shiyasa da wuya idan nazo hutu naje gidanta,tun tana fishi dani harta bari ganin abin nawa bana qarewa bane.Ammi har abbi ta fadawa shima yayi min nasiha akan riqo nidai na bishi da to amma banajin wata ma'amala xata shiga tsakaninmu dashi.
Gama mkrnt ta yasa ya aisha ta siyamin waya mai kyau da tsada,ya ruqayya ta bada kudi a saka ni a mkrntr koyan girki da kuma kwalliya,ya fatima baiwar allah dinkuna tayimin wajen kala bakwai,Inda ya zainab ta siyamin kayan kwalliya dana shafa.
Gsky ni yar gata ce shiyasa a kowani lkc nake alfahari da yanuwana duk da kasancewarsu mata amma suna qoqarin yimin abinda koda yanuwa maza gare ni ba lallai suyi min haka ba.


Zuwa yanxu tsantsar kyauna ya qara fitowa,duk da kasancewata baqa amma inada wani kyau na ban mamaki,inada gashina dai dai na zaman falo,sannan ni bamai qiba bace,doguwace ni mai dogon hanci sannan inada beauty point a kumatuna,kai na taqaice muku dai ni mai kyau ce kawai😉.
Wayar da nayi yasa muka bude sabon babin soyayya nida ya sadiq,abinda yake qara min qaunar ya sadiq shine yadda yake bani kwarin gwiwa akan karatu,ya damu da krt na sosai dan lkcn da zamu fara SSCE kamar shi zaiyi exam din duk ya damu,kullum cikin nasiha da qarfafa gwiwa,dan yace sai yaga na fara krt a university sannan zai kai mgnr mu gaban abbi.
Cikin ikon allah na mayar da hankali na akan koyan kwalliya da girki dan naga yanxu sune mace duk wadda bata iyasu ba ita ce baya.
Yauma kwance nake a kan katifar dakinmu ina waya da ya sadiq ammi ta dago labule.


"Sannu daddawar daka,ni bansan yaushe kk koyi zaman daki ba mutum ma ya rasa abinda kikeyi a daki"
Janye wayar nayi a kunne na kafin nace.


"kaii ammi ni maixan qulla baki sani va"


Kya dai ji dashi idan tayi wari

Please Login or Register in order to submit comment