Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakya so,kinsan dai banason ganin wannan yanayin a fuskarki"
Batai masa mgn ba don hk ya cigaba.


Ummi jiya kwata kwata kasa bacci nayi,rabona da abinci tun jiya da safe,plzz ki tausamin,kuma bazan qara mgnr ba tunda bakyaso"


Rashin bacci ko cin abinci duk kaine ka jawowa kanka,tunda kana zaman zamanka zaka jajibowa kanka wani aure,kuma inhar kanaso mu shirya dakai karna qarajin makamanciyar wannan maganar daga gareka"


Allah sarki ummi ashe duk akan mgnr aure take wannan fushin,data amince yayi aurensa kawai maybe yana buqatar hakanne.


Sama sama suke mgn akan abinda ya shafi company,kafin ya sanar mata cewa a satinnan yakeson zuwa dubai wajen wasu abokan kasuwancinsu daganan zaije US dan ganawa da uncle.


Tashi ummi tayi domin samo masa abinda zaici nidai har lkcn kaina a qasa don bazakayi zaton ina falon ba ma.


Jiya su Ammi na gaidake"najiyo shi.


Ina amsawa"na fada a qasan maqoshi ba tare dana dago ba.
Gashi ta bani saqo wai inji qawarki"


Da sauri na dago dan nasan bani da wata qawa sama da nusaiba,don sosai nake missing dinta kawai dai daurewa nake,bama ita ba duka family dina,musamman ma su muhibba,sauqinta ma ina ganinsu shahida inajin dadi.


Ina dagowa naganshi yana danna waya kamar bashine yayi mgnr ba.


Ganin ummi ta taho yasa banyi mgn ba.


Madaidaicin farantin hannunta ta ajiye.Ganin zata fara hada tea yasa nayi saurin tashi don karba domin bai kamata tana aiki ina zaune ba.


Batai musu ba ta bani na shiga hada tea din ita kuma ta zauna tana ganin kayan da yak nuna mata a waya ko za'a siyawa su mubina.


Ina gama hadawa naje ta gefensa na miqa masa,banyi aune ba naji ya kama harda hannu na kuma yaqi saki ya wani basar ya cigaba dayi mata bayani batare daya kalleni ba bare yasan yanayin danake ciki.


Duk a firgice nake dan banaso ummi ta dago taganmu a haka,amma shi bashida niyyar saki na.


Sunyi kyau sosai,bari na tasosu su gani,idan sunyi musu sai kowacce ta zabi colour"ummi tace tana miqewa,amma inada tabbacin zata ganmu shiyasa ma nayi qasa da idona.


Tana dan nisa kamar jira yake ya hanyoni har tea din na zuba akan hannu na.


Qara na qwalla kadan sbd zafin danaji,inda shi kuma ya rude ya ajiye tea din a centre table ya shiga fifitamin hannu da iskar bakinsa.


Ba qonewa nayi ba don kadan tea din ya zuba a hannun amma ganin ya rude yasa na qara langwabewa ni a dole zafi nakeji.


Fahimtar da yayi kukan na shaqiyanci ne yasa yayi smiling tare da janyoni jiknsa.


Nernah rigima"ya radamin a kunne da sexy voice dinsa hakan yasa naji yani yarrrrr.


Plzz ka sakeni kar ummi ta dawo"nace muryata na rawa jin numfashinsa akan wuyana.


Zan sakeki idan kin fadan dalilinku na gudowa kuda yara kuka barni ni kadai,nernah jiya kwata kwata kasa bacci nayi sbd ummi fushi take dani dan nace zanyi miki kishiya,ummi bata taba fushi dani irin haka ba"


Kishiya kuma?ai matarka zakace zaka yiwa kishiya kuma ta rasu,ni ai a matsayin qanwarka nake ko ka manta?"nace ina nuna halin ko in kula.


Nasan kallona yake don hk naqi dagowa na kalleshi.


Plss kar wani yazo ya ganmu a haka yayi tunanin wani abu"nace ina ture hannunshi dayayi min qawanya.
Da alama yana cikin shok dan bansha wahala wajen tureshi na tashi ba.


Ga abincin nan kaci karyayi sanyi"nace ina barin falon da dan gudu na.


Turus naja na tsaya don ganin aunty anisa tsaye akan stair ta rungume hannu a qirji tana murmushi,da alama ta dade a wajen,duk da nasan bazata jiyo abinda muke cewa ba amma da alama taji dadin ganinmu a haka.


A kunyace na tsaya inda ta qarasa saukowa.


Hk dama akace miki ana kula da miji?maza muje ki bashi abincin kinga fita zaiyi"tace tana riqo hannu na


Allah aunty zaici da kansa"nace ina turjewa.


Idan kinje saman mezakiyi?"tace tana qara jana.


A gefensa ta zaunar dani kafin itama ta zauna a daya gefen nasa.


Gud mrng broh"


Tace tana murmushi.
Mrng angel,how was ur nyt"yace cikin kumawa.


Its cool,but yaya yanayinka yana nuna kamar jiya baka samu bacci ba"tace tana binsa da kallo.


uhmm Kinsan na tafi ummi tana fushi"yace


Ai kasan kaima dole ummi tayi fushi yaya"
Koma dai me
nene yanxu na janye tunda kunfi qarfina baby"yace yana smiling.


Harka tunomin mum dakace baby"tace itama cikin nishidi,hakan ya qara tabbatarmin da shaquwar dake tsakaninsu ganin yadda ya ware yake zuba tare da bata dukkan hankalinsa.


ni kaina naYi missing nasu over,amma a satin nan nakeso naje don qarasa tattaunawa akan bikinsu twins.


Ni dauka zuwa yanzu mum tazo dan tace ita zata gyara amare "


Sai dai naje sai muje yaushe zasu taho din"


Wai ba kaine mai co
mplain kanajin yunwa ba,amma ka tasa abinci gaba kana surutu kamar ba office zakaje ba"ummi tace tana nufar qofar da take sadamutum da kitchen.


Ummi kefa nake jira kiyi feeding dina"yace a shagwabe.
Ka bari idan kaje wa
jen iyayenka da suka sangartaka sai suyi maka haka"tace tana shigewa.
Kallonsa ya
dawo dashi kan aunty anisa"Yanxu ummi ta daina ji dani"yace kamar wani dan 7years.


Yanxu tana aiki ne bari ni na baka"tace kamar tana lallaba yaro qarami.


Um um ni wannan nakeso ta bani"yace yana poiting dina.
Yarda yayi yasa na kasa
riqe dariyata na shiga yi,itama aunty anisa dariyar take.


Shi kuwa tsayawa yayi yana kallona da alama bai tava ganina ina dariya irin haka ba.








Khayratie ce!!πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹


[09-17, 9:28 PM] 😘rukiey😘: πŸ’™πŸ’™πŸ’™RABON KWADO......πŸ’™πŸ’™πŸ’™


17, 9:28 PM] 😘rukiey😘: πŸ’™πŸ’™πŸ’™RABON KWADO......πŸ’™πŸ’™πŸ’™










πŸ…Ώ206-πŸ…Ώ210






Sakkowar su mubina yasa na fara tsagaitawa da dariyar da nake.




Ita kuma wannan ita da wa?"mubina tace tana samun wajen zama.


Ita da mijinta?"Aunty anisa ta bata amsa.


Miji manya muma dai mun....."bata qarasa ba saboda mugun kallon daya watsa mata.


Ai kadan kaji indai mubina ce wlh"aunty anisa ta fada.


Uncle mrng"zarah tace masa.


Mrng queen"yace yana maida kallonsa gareni.
Sarai na fahimci mgn yakemin da ido,kawai na basar kamar ban gane me yake nufi ba.


Broh ummi tace zaka nuna mana furnitures mu zaba"mubina tace.


Bazan nuna ba"yace a hasale kamar anyi masa laifi.


Shiru falon yayi sai mubina dake kumbure kumbure.


Miqewa yayi ya dauki car keys dinsa dake center table.




Neesa bari na wuce nabar saddam da aiki,Gashi zuwa anjima muna da baqi"yace yana wani shan mur tare da fara tpy.


Ba yunwar dama kakeji ba,inbanda haka mai jin yunwa ne zai tsaya yace dole sai an bashi abinci a baki?nifa shirmen nan naka ya fara isata babanah"ummi data fito a kitchen take fada.


Ummi yace rabonsa da abinci tun jiya,bai kamata ya kuma fita baici komai ba,kuma kinsan yaya ba wani tsayawa yaci zaiyi ba idan ya fita"Aunty anisa tace cikin damuwa kamar cikinta zai kaiwa.
Kada allah yasa yaci ai jiki magayi na fada a raina.


To anisa shi qaramin yaro ne da sai an tasa shi gaba yaci abinci?kullum girma yake yana tara iyali amma bazai nutsu ya ringa cin abinci ba?Almost 35years ace sai an zauna ana feeding dinsa?"fada take sosai da alama ba rashin cin abincin bane kawai laifin da yayi,shidai tuni ya fice hakan yasa aunty anisa bin bayansa da sauri.


Ta dade bata dawo ba hakan yasa ummi tace muje dinning area mu fara cin abinci ita kuma ta zauna a falon tana nazarin wata newspaper.


Ummi kinga ya tafi bai nuna mana ba"mubina tace kamar zatai kuka.


Ummi dai batai mgn ba sai aunty anisa data bi da ido da take shigowa.


Kitchen ta shiga kafin ta fito da basket ta nufi waje da alama mutumin naku zata kaiwa.


Aunty anisa ta yaya"mufida tace tana dariya.


Saji dashi,suje can su qarata"ummi tace da alama ta jiyo abinda mufidan tace.


Aunty wai yaushe ne bikin naku?momma tace bikinku za'ayi pa"zarah tace.


Ki kwantar da hankalinki darling an kusa saura kadan"mubina tace tana fifita mata tea.


Dawowar aunty anisa yasa kowa yayi shiru,inda ta nufi wajen ummi ta zauna.






Ummi wai yaya ya kuma wani laifinne?plzz kiyi hqr tunda yace ya fasa zuwa yanxu saiki daina fushi dashi,wlh duk ya shiga damuwa"


Ki tashi ki bani guri kafin na dawo kanki,meyasashi baki tmbyshi abinda yayi min ba?harni zai fadawa ya fasa bacin sun gama mgn da uncle dinku cewa za'a hada bikin dana 'yan biyu,ni kenan ban isa na nuna banason abu a qiyi ba"


Kiyi hqr,Amma koni haka yace min ya fasa amma zamu kuma mgnr"


Ni ba aure ne banaso yayi ba anisa,amma fisabillahi wani kallo yakeso mutane suyi mana?kofa shekara ba'ayi ba da rasuwar matarsa,bayan haka duk irin halarcin da iyayenta sukai mana na bashi auren qanwara sai kuma yanxu suji zai qara aure?shima babban yayan ya gayo da bayansa sbd shi bayaso ace yayi laifi"


Dukansu kallon tausayi suke min,nima kawai dai ina daurewa ne,domin zuwa yanxu kowa ya fahimci ni din ce bayaso,kuma nima insha allah zan cireshi a raina.


Ganin mufida ta tashi yasa nima na tashi don banaso suyi zaton sbd mgnr ne zan tashi,kuma har lkcnsu ummi mgn suke sai dai yanxu bama iya juyo abinda suke cewa ba.


Da sauri na nufi sama domin kadan ya rage kuka ya kwace min.Dakin aunty anisa na shiga inda na fada gado tare da rushewa da kuka mai ban tausayi.


A saboda qaddararren aurensa na rasa kowa nawa da komai nawa,akan wannan auren nasa burina na zama lawyer ya tarwatse,saboda shi kowa ya gujeni amma wannan itace sakayyar da zaimin.
Ta wani bangaren bashi da laifi tunda ba sona yake ba aka qaqaba masa ni,kuma an gina auren akan cewa zan kula masa da yara ne bawai zaman aure ba.




Jin kamar za'a bude qofar yasa na fara share hawayen fuskata ba tare dana juy ba don na juyawa qofar baya.


Aunty khadija"tace tana dafa ni.


Ban amsa b sai yaqen da natimata duk a qoqari na na boye halin da nake ciki.


Kuka"?tace tana mini kallon tausayi.


Saurin girgiza mata kai nayi don ina mgn kuka ne zai taho.
Bata ce komai ba sai rungumoni da tayi,hakan ya bani damar sakin wani kukan don dama ina buqatar mai rarrashi.


Yaushe kika fara sonshi"




Rasss!gabana ya fadi,badai kowa ya gano inasonshi ba?


Khadija meyasa zaki fara sonshi tun yanxu?"tace tana dagoni.


Kiyi hqr nima bansan yaushe hakan ta faru ba,ki fadan yadda zan cireshi a raina don allah aunty"
Kuka na cigaba dayi sosai.


Ki daina wannan kukan plxx,zamuyi nasara insha allah"tace tana sharemin hawayen fuskata


Badan na aminta da maganarta na tsagaita da kukan,don nasan wannan mafarkin nata bazai tabbata ba,amma kasancewarta wadda ta damu da damuwata Da dukkan al'amura na dole nayi abinda takeso.


Labarai ta shiga bani na dramar zaid da zarah duka qoqarinta na ganun na saki raina na manta komai.


Har yamma muna tare da ita,duk abinda tasan zanji dadinsa shi takemin,Hakan yasa na saki jiki mukaita hira tana bani lbn zamansu a U.S.




Mubina ce tashigo ita da iman da alama basu dade da dawowa a scul ba don 5pm ta wuce.


Da gudu ta kwace hannunta tazo ta rungume ni,hakan yasa aunty anisa sakarmin gashin da take tajemin da hand dryer bayan ta wankemin da shampoo masu qamshi.


Gsky kin shagwaba yarinyar nan da yawa,bakiga yadda akaita rarrashinta ba ummihar goyata tayi amma kamar bata sammu ba ita dole wajen mommy zata"tace tana dungure mata kai.




Qara rungumeta nayi a jikina"Ai yanxu gashi tazo kuka ya qare"nace ina kallonta ta lumshe ido sai ajiyar zcy take da alama tasha kuka.




Shigowa mubina tayi"wai me ake qullawa ne tun safe aka qule a daki?"


Zoki zauna kiji me ake fada?"aunty neesa tace.


Aa fita zamuyi zanyiwa ummi rakiya karkasara,sis kinga motarki kuwa?gsky tayi kyau nima allah yasa a bani irinta"


Har ya kawo motar ne"aunty anisa tace.




Eh tana Can waje arsh color broh ya zabar mata,nidai ku fito ku gni tafiya zamuyi har su zarah duka"tace tana ficewa.


Mu gani ta window kawai don saukarma aiki ce"tace tana yaye curtain din window.


Arsh color ce sabuwa dal don banda qyallinta ba abinda kake hangowa.
Wai wannan motarce da sunan tawa?ni ko a mafarki bana kawo zanyi mota bare a irin wannan qananan shekarun nawa.Abbi kawai zance ya ringa hawa donni ba abinda zanyi da ita.


Tsaf tagyaramin kaina sai sheqi yake da qamshi,ni kaina nishadi nake dan sakayau nakeji na.


Tare muka Shiga kitchen inda muka gabatar da sakwara da miyar agushi.
Basu dawo da wuri ba sai wajen 9 inda muka baje ana hira tare da cin gyadar Da amminah ta basu.


Sailkcn na tuno da saqon da daddyn shahid yace ammi ta bashi,don haka na matsu ya shigo gidan don na karba,amma abin takaicin har muka koma upstair don kwanciiya bai dawo ba.Washe gari ma kwata kwata bai shigo gidan ba,naji dai aunty anisa tayi maganar rashin zuwanshi ummi taita fada tana cewa kada yazo din ai itama ba nemanshi take ba.
Allah sarki ita
dai ummi har lkcn fushi take da babannata.




Er mutan un
gogoπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
😘: πŸ’™πŸ’™πŸ’™RABON KWADO.....πŸ’™πŸ’™πŸ’™










Er mutan ungogoπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹






Ina neman afuwarku readers akan rashin jina tsahon kwanaki,hakan ya faru ne sakamakon rashin Nepa da aka fama dashi ina fata za'ayi min afuwa.
Sannan akwai mistake na page number da nayi,last page zai kama 201-205 yanxu zamu tashi 206-210.Ngd.






😍😍Wannan page sadaukarwa ne ga tsofaffin daliban G.G.S.S kwah 2015 musamman B Class.




Khadija isah muhd
Ruqayya musa
Ummahani adam
Hauwa musa bello
Rabi Aminu sulaiman dungurawa.
Bashariyya abdulhamid
Khadija Bala muhd
Jamila ibrahim(jam jam)
Aisha usaini yarkanya
Asma'u Aliyu ungogo.


Kuna raina bazan manta daku ba tsahon rayuwa😍😍








πŸ…Ώ206-πŸ…Ώ210




Tun daga ranar bai qara zuwa gidan ba,kuma in aka kira numbr dinsa batashiga kamar yadda naji aunty anisa ta fada.


Sosai suka shiga damuwa idan ka cire ummi da kullum cikin mita take,yaransa kansu sun faratmby ina daddy dinsu,nidai ko a jikina dan nasan ta hanyar daina ganinshi ne kawai zanyi nasarar cireshi a zcytah.


Jin dadin gidan nake sosai,dan kowa ji yakeyi dani ba kamar ummi da take min kamar ta goyani ko yaya taga nayi shiru xata shiga tmbytah ko ina buqatar wani abu.


Samunsu aunty anisa da mufida yasa na daina damuwa akan rashin yanuwana.
Shirye shiryen biki sukeyi sosai,ba kamar mubina da take ji kamar ta janyo ranar bikin.


Cikin ikon allah na fara nasarar cire daddyn shahid a zcytah domin shidin bai cancanci a so shi din ba.idan na tuno da matsayinshi na mijin ya fatima sai naga butulci ne ace na fada tarkon sonshi.




Ana saura 1month bikin mutanen U.S suka diro ciki kuwa harda mutumin naku.
Sosai matar da suke kira da mum take da fara'a da jan mutum a jiki,tun inajin nauyinta har nazo na sake da ita kamar yadda naga yan gidan sunayi.


Uncle din kuwa kallo daya zakayi ka gano tsantsar kamar da sukeyi da cwt daddyn shahid😜 da kuma ummi,shim na samu karbuwa a gurinsa.


Kwanarsu biyu da zuwa aka fara gyara amare ciki kuwa harda ni,ba yadda na iya dole nake tsayawa duk abinda akayi musu ayi min don mum da aunty anisa sun tsaya kai da fata ai nima amaryar ce.


Cikin kwanaki kadan muka fara canjawa asalin kyawunmu yana bayyana,don abune akeyinsa kamar cin kwan makauniya,safe rana da kuma dare duk da su mum din ba anan suke kwana ba kullum da safe suke xuwa ayi break fast dasu sai idan uncle sun dawo daga company da dare bayan dinner sai su wuce masauki.


Das qamshi ya zauna ajikinmu duk inda muka zauna muka tashi sai mun bar qamshi don hatta wanka da ruwan turare mukeyinsa.


Daddyn shahid kuwa bama haduwa dashi don downstair dinma bama Sauka komai biyomu akeyi dashi.


Duk yadda sukai kyau amma sai suyita zuzita kyauna,nidai kawai jinsu nake dan su da suke farare ai sune zasufi yin kyau.




Yau ta kama saura 3weeks biki,Kamar kullum yau ma abin da mum ta saba dama mana aka dama nidai kwata kwata bana jin dadinsa don haka kowa saiya shanye a barni a baya wataran mum har dura takemin.
Ganin mum ta fata yasa na ajiyeshi a bedside drawer nayi kwanciyata.


Ashe da rabon yau ma ayiwa wata dura"mufita tace.


Sis bazaki gane menake ji idan inashan abin nan ba,kwata kwata babu dadi ko pa suger babu"nace ina gyara kwanciya.


Kowa ma ai babu suger din yakesa,wlh ki tashi kisha dan mum tace yana da matuqar amfani"mubina amarya tace.


A wajenku amare ba"nace ina dariyar mugunta.


Eh koma dai mezaki ce ki tashi ki shanye ko naje na kira aunty anisa"tace tana harara ta.


Wlh har tausaya miki nakeyi mubina,wannan gigin da rawar kan da kikeyi duk a sati daya za'a sauke miki shi"mufida tace muna ci gaba da dariya.


Pillows ta dauka tana dukanmu dasu muna cigaba da dariya.


Zuwan zaid yasa muka dakata da dariyar sai mubina daketa harare harare.


Mommyn shahid wai gashi inji uncle saqonki ne sai yanxu ya tuno dashi"ya fada yana bani wata leda.


Bude ledar na shigayi batare dana tuno da ko wani saqo bane.


Inner wears ne masu kyau,sai pictures din nusaiba dakuma wanda mukayi tare a waya aka wanko,sai kwalin chewing gum da sweet sai kuma letter.


Letter din na hau karantawa don daga note din nagane daga nusaiba take.


Slm sistr


Ina fata kina lpy kamar yadda nake duk da kewa da rashinki a kusa har zuwa wannan lkcn ya kasa bari na nayi rayuwa kamar ko wani dan adam.


Baxan iya kwatanta yadda nakeji a kullum idan na tuno irin rabuwar da mukayi ba,amma hakan ba yana nufin canja miki matsayin a gurina ba.


Wani albishir kuma shine on 7 may bikin sistr dinki,rashin halartarki yana nufin rashin gudanar da biki cikin walwala.


Luv u so much sistr.




Yau nawa ga wata"na tmbyi su mubina ina share hawaye ba tare dana kula irin kallon da suke min ba.


Five"mufida tace.


Tsalle na daka sbd murnar lkc bai wuce ba zanje bikin nusaiba.


Lpy sis"suka fada a tare.


Bikin besty dina za'ayi jibi ai zaku je koh?"na fada ina murna.


Sosai m dama zaman gidan ya isheni,gashi an karbe mana phone kamar wasu prisoners"mubina tace


Amma ummi xata bari?"na tmby


Zata bari insha allah"mufida tace


Ai kuwa muna tmby ta bari harda bada wani purple din material mai kyau wai a dinka mana muje bikin dashi.
Ban gama m
amaki ba saida naga washe gari da yamma an kawo dinkin,dinkin doguwar riga ce qasanta ya bude sosai.Da yake su mubina sun dan fini qiba siririyar ciki na dauka ina gwadawa kuwa dai dai ni,sai lkcn mufida take fadamin aunty anisa ta dauki measurement dina don tuni an kai mana dinkunan biki.
Tun safe na fara shiri sbd zumudi,ga murnar ganin amminah da kuma nusaiba.


Daqar na bari mukai azahar kafin mu shirya mu tafi tare da driver,fadin irin kyau din da mukayi kuwa bata baki ne,kamar wasu triple haka muka fito.


Tun shigowarmu layi nake tuno abubuwa da dama da suka faru tun daga yarinta ta har zuwa lkcn da akai min auren rashin gataπŸ˜“


A qofar gidanmu m.sabo yayi,jikina a sanyaye na bude murfin na fito don lkc daya fargaba ta shigeni dana tuno yadda mukayi da Ammi a wannan can xuwan.


Tun daga soron gidan zakasan an samu cigaba,dan haka sallama dauke a bakunan mu muka shiga gidan inda nake bin gidan da kallo kamar wata baquwa.


Ammi ce ke qoqarin amsa sallamar tana fitowa daga kitchen.


Banyi sanya ba na tafi da gudu na riqeta tare da sakin marayan kuka.


Aa yau manyan baqi ne a gidannamu"tace tana fara'a.


Ke kuma daga zuwa sai kuka"ta kuma fada tana dago ni a jikinta.


Falo muka shiga har Lkcn inamatsar kwalla,su kuwa su mufida suna min dariya.


Shima falon kamar bashi ba dan komai bana dabane a ciki an gyarashi kamar na yan gayu.


Gaisuwa aka shigayi nidai ina maqale jikn Ammi kamar wani zai kwace min ita.
Ki tashi ki samo muku abinsha kafin abincin ya qarasa,suma su ruqayya sunce zasu xo,ita zainab ma dake kusa kuma ita ba yara ba amma har yanxu shiru"




Ammi suma zasu xo"nace ina mai jindadi.


Eh haka aisha ta fada min jiya da mukayi waya"




Fridge Dana gani a falon na nufa don samo abin sha.kunun aya ne da zobo juice dan haka na dauko mana kafin naje kitchen dauko cups.
Shi kanshi kitchen din kamar na wata amarya Ko yaushe aka samu wannan cigaban oho.


Ammi abbinah pa?Nasan dai yau ba aiki"nace ina tsiyayawa su mubina juice.
Tun daida
suka shigo bayan daurin aure suka fita amma duk inda yake yana kusa da gida don a qasa ya fita"tace tanashiga ciki.


Sallamar ya zee dana jiyo yasa na dire jug din na fita a million.Kamar wata baby haka na dafeta har muna qoqarin faduwa.


Oh my lil sis har yanxu kinanan a yadda kk,kwata kwata gudu da tsalle bayayi miki walaha"


nayi missing dinki ne pa"nace a shagwabe. jin kamar goyo a bayanta yasa nayi saurin sakinta.


Baby boy ne kwance a bayanta yanata sharar bacci.
Ya zee dama kin haihu shine ko a sanar dani"nace hawaye na taruwa a idona.


Kiyi hqr auta wlh munso sanar miki amma...."




Amma abbi ya hana koh?shikenan tunda an cireni cikin family dinnan"nace ina shigewa daki.


kuka na shigayi suka hadu suna lallashina,sai da ammi tasa baki kafin nayi shiru na dauki yaron mai suna muhammad Aameen.


muka shiga hira,suma su mubina warewa sukayi mukaita labaran duniya,harsu ya aisha sukaxo bamu sani ba sai dai kamai mukaga muhibba.rungume juna mukai muna murnar ganin juna falo muka fito Na rasa Gurin wanda zan nufa Kaawai na Fashe da kukan murna.Dama inada wannan bataliyar amma da nake rayuwar kadaici?


Haba auta keda zakiyi murnar ganinmu saiki buge da kuka?common share hawayenki"ya aisha tace tana ruqoni Tare da share min hawaye.


Duka yaran nawa sukayo kaina kowa yanaso Na daukeshi.haka naita dagasu sama muna nishadi abinmu.
Ranar jinta nake kamar sallah danagamun hadu dukanmu muna kwasar dambun ammi,sai naji haushi da bamu taho dasu iman ba da suma sunga yanuwansu ai. Kwata kwata na manta biki mukazo sai da aka fara kiran la'asar kafin ammi ta fara fadan mu tashi mu shiga gidan bikin.


wajen da muka ci abinci Na shiga gyarawa su kuma suna sallah da yake ni ina off.












πŸ’™πŸ’™πŸ’™RABON KWADOπŸ’™πŸ’™πŸ’™












Er mutan ungogoπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹






Rabon kwado fans ina yinku irin totally dinnan,fatana a koda yaushe mu kasance daku domin da yabo da kwarin gwiwarku komai ke gudana.


Ana mugun tare🀝








πŸ…Ώ211-πŸ…Ώ215






Bayan idar da sallar qarayin wata kwalliyar su mubina sukayi,nidai gyara fuska kawai nayi nayi yafen mayafina kamar yadda naga suma sunyi.


Har tym din ammi tana cikin dakinta hakan yasa naje domin sanar mata zamu wuce.




Oh wlh nayi missing gadon nan naki ammi,kai duka gidanma nayi missing,amma ku sam baku damu dani ba kamar an cire ni daga cikin yaran gidan nan"na fada muryata na rawa alamar kuka.


Waya ce miki mun manta dake auta?wlh kullum a gidan nan sai anyi mgnrki,bama ni ba ko abbinku koda yaushe maganarsa ke ce,tayaya za'ayi mu haifi 'ya mu manta da ita?"Ammi tace cikin rarrashi.


To amma Ammi meyasa kowa yayi avoiding dina kamar bani da dangi"




Ai yanxu komai ya wuce auta kuma sai yanxu na gamsu da hukuncin da abbinku ya dauka,gashi yanxu kin kwantar da hankalinki kina zaune da mijinki da yanuwansa lpy.Hajiya asiya ta fadan kwanaki bakiji dadi ba ranar da suka kawo mota,dama Abbinku yace zamuje mu duba jikinnaki hajiyar tace kin warware kunacan gidan nasu ba.kuma mgnr motar yace zai ajiye duk ranar da kikazo sai ayi mgnr yadda za'ayi da ita"


Ammi ni na barwa Abbi motar ya jiqa hawa"


Dama hakan shine ya dace,amma dama inake ina hawa wannan motar khadija?sai ki qara mana gdy wayan shi mai gidan naki don duk qarshen wata baya gajiya da hidima,tun abbinku baya karba har yazo yana karba,yaron dan mutunci ne ba ruwanshi"


Ammi naga an samu canja canja a gidannan ya koma kamar na wata sabuwar amarya"nace ina dariya don son kawar da waccan maganar.


Abbinku ne ya samu qarin matsayi a wurin aiki shine yaketa gyara"


Ai gwara ya gyara amarya tazo ta ganshi da kyanshi"na fada da zolaya.


Ke ni banson shaqiyanci kinxo kenan zakimayar dani kamar kakarki,ga wannan sai ki kaiwa nusaiban gudummawa"tace tana zaro qaton kwali daga qasan gado.


Kai ammi angoda"nace ina bude set din kulolin masu kyau.


Tashi nayi ina gyara zaman mayafina"Ammi bari muje suna jirana,zan turo su mufid su dauki gudunmawar"nace ina neman hanyar fita.


Zo nan auta,badai a haka zaki fita ba sbd sakarci,maza ki gyara lullubinki kafin na saba miki,ince dai har yanxu kina nan da shiriritarki,ace kina matar aure bazaki lullube jiki ba"


Ware mayafin nayi na dora a kai ina turo baki,domin ni kwata kwata mantawa nake ni matar aure ce😏




Gidan cike yake kamar ko wani gidan biki anata hidima da kai komo da dangin abinci kala kala,Umman tasu ma bamu samu ganinta ba muka shige dakinsu nusaiba kamar yadda aka sanar mana sunacan ita da tawagarta.


Ganinmu yasa ta saki ihun murna tare da tasowa muka rungume juna.A tare muka saki kuka domin a lokutan baya aka fada mana zamu kai wannan lkc bamuga juna ba tsaf zamu qaryata.


Sis dama zaki xa?wlh tun shekaran jiya da aka fara event nake saka ran zuwanki ganin har yau maki zo ba yasa na fitar da rai"Nusy tace bayan mun tsagaita da kukan.


Zanzo mana sis,idan banxo ba ai naci amanar aminta"


Qara rungume

Please Login or Register in order to submit comment