Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juna mukayi,inda ilahirin yan dakin suka mana kallon tausayi musamman wadanda sukasan yadda muke a lkcn baya.


Wato kinxo da muta ne kin manta dasu ko?To mu bari mu shiga muyiwa umma allah ya sanya alkhairi daganan zamu koma gida sai kun taho"ya ruqayya tace kafin suka fita.


Sorry sisters,yau ina farin cikin ganin besty ne shiyasa,amma karku damu ana tare"nace ina zaunar dasu a kan katafar dakin.


Qara jiqo nusaiba nayi,itama ta riqeni gam kamar za'a kwace mata ni.


Amma sis yau da za'a kaini shine ranar da zakixo?bafa kano zan zauna ba can kd ne"tace tana matsar kwalla.


Gsky baiwar allah ki saketa haka,lpy lou muke za'ayi mata kwalliya amma daga zuwanki kin sakata kuka"
Juyowa nayi don ganin meyin wannan furucin na fada mata mgn dai dai da wacca tayi min,amma me kallon mamaki muka bi juna dashi domin tabbas wannan classmate dina ce a G.G.C Dala.




Khadija isah!!..


Hauwa musa!!..


Muka fada a tare domin tabbatarwa.




Duk da cikin dake jikinta batai qasa a gwiwa ba tazo ta rungume ni.


Hirar yaushe gamo data school muka shigayi ba qaqqautawa hakan yasa kiwa a dakin yayi shiru yana saurarenmu kunsan dai yan bording suka hadu ba sauqi ni,bare mu da muke class daya tun j.s 1.




Hauwa musa bani numbrs din yan mate dinmu dama inata nema don nayi missing contact"Na fada ina zaro wayata daga hand bag.


ki kwantar da hankalinki har DOGAS zansa a sakaki,Dama yan grp dinku sai cigiyarki suke"


Allah sarki yan biyar nasan zasu neme ni sosai musamman ummulkhair A. ungogo,Ruqayya musa da kuma ummahany adam"


Ai kuwa muna waya da ruqayya musa bari na baki number dinta sauran kuwa ko a grp kwa hade"


Wai sis damakunsan juna ne"nusaiba da aka fara yiwa kwalliya ta tmby.


Eh tare mukayi Dala da ita"nace ina kwashe number din ruqayya musa a wayata.


Yawwa saiki saka min taki,zanyi miki mgn ta watsap sai kiyi adding din nawa"


tana saka mn number din wata yarinya ta shigo.


Aunty jidda wai kizo inji ya sadiq yana falon baqi"


Ambatar sunan ya sadiq yasa na zuba ido dan gani wadda zata tashi domun tabbas sunan matarsa jidda kamar yadda ya fada da muka hadu a Mall.


Ga mamakina naga hauwa musa ta miqe.


Khadija isah ina zuwa mijinah yana kira kinsan ba'a sanya da kiran mai house"


Harta fita ban samu zarafin amsa mata ba,kallo na mayar kan nusaiba domin samun amsa tmbyoyina.Akaci sa'a itama ni take kallo don hk ta daga min kai alamar eh"


Eh itace matar ya sadiq?Eh hauwa musa itace mace mai sa'ar data samu ya sadiq?Eh cikin jikinta na ya sadiq ne?


Ganin kamar mutane zasu fahimci wani abu yasa nayi qoqarin saita kaina inajansu mufida da hira.


Da aka kawo abinci ma mufida ce kawai taci alala din dukkanmu bama tare da yunwa.
A lkcn su mufid suka kawo kayan suka tafi.


Rade radin da aka fara anxo daukar amarya yasa nusaiba zuwa ta qanqameni.


Dan allah sis kice min dake za'aje kaini,wlh ke kadai zan gani na ringa jin sanyi a raina,kin sani munyi missing juna,And we have a lot of thing to talk,gashi kinxo a qurarren lkc"ta fada kwalla na zubowa.


Plzz sis karki bata kwalliyarki mana,banzo da shirin zuwa kd ba amma da babu abinda zai hanani kai cwthrt dina dakin mijinta,kuma kinga tare nake da baqi,qannen daddyn shahid ne kuma shima ban sanar dashi tpyr ba,Amma insha Allah ko banxo ba akwai waya kuma zamu ringa haduwa indai kinxo"nace cikin dauriya don qarfafa mata gwiwa.
Ga
wayar ki saka min number din,ga wannan kayan inji Ammi tace a baki,bari muje mu gaisa da umma sai mu wuce,sai munyi waya"


Har lkcn kuka take bata samu damar mgn ba.Zuwan wata mata kirantaza'ayi mata fada ya qara sakawa da riqeni,don haka kwallar da nake riqewa da zubo ba tare dana shirya ba,daqar ta sakeni suka fita da ita ni kuma ina cigaba da sharar kwalla.
A tsaitsaye m
uka gaisa da umma muka fito don tana busy sosai haka mukai mata allah ya sanya alkhairi muka fito.


Rassss!Gabana ya fadi don hangosu suna tahowa fuskokinsu dauke da farin ciki,Da inada halin canja hanya da nayi domin banso muka hadu dasu ba,ita kanta hauwa musan na bari kawai mu hadu a chat kawai mu ringa gaisawa.
Badai har kun fito ba"na tsinkayo muryarta.




Eh zamu wuce can gidane kinga yan daukar amarya sunxo"na fada da yaqe domin banason ta fahimci wani abu don ko inda mijinta yake ban kalla ba.


Amma duk yadda kuke da amaryar bazaki tsaya akai ta da ke ba?"ta kuma fada


Wlh naso hakan amma ina tare da baqi shiyasa"na fada cikin qosawa da tsayuwar wajen domin kamar akan wuta haka nakeji na.


Mijin jidda ga qawata khadija,Maybe kunsan juna don naga qawar Nusy ce"tace tana kallonshi.


Wai nernah?Ai keya kamata nayi introducing a wajenta"yace yana sakin killer smiling.
Kamar na rusa ihu haka naji.


Nernah?kana nufin wannan ce nernan da kullum kake damun mutane da zancenta"ta fada tana nuna ni da yatsa tare da qanqance ido kamar bata taba sani na ba.




Yp ko bata cancanta bane?"yace yana harde hannu a qirji.


Dogon tsaki taja kafin ta bangajeni ta wuce tanata huce kamar wata zakanya.


Da kallon mamaki muka bita dukanmu ba kamar su mubina da sukaga hirar da mukasha dazu dazun nan.
Yana
qoqarin yimin mgn nayi saurin jan hannun mufida muka bar gurin don hankulan mutane ya fara dawowa kammu.


Wlh Allah ya taimaketa ciki ne a jikinta amma da taga qarshen rashin m"mubina ta fada.
Barta zafin kishi ke dawainiya da ita,Amma a tunani na ko miji muka hada da hauwa bazatai min wannan wulaqancin ba bare yanxu data auri Ex dina"na fada ina share hawaye.


Dama wasu matan haka suke,ko yaya kuke dasu qaddara ta hadaku miji daya ko saurayi sai kasha mamaki"mufida tace.
Murmushin takaici kawai nayi don idan akace hauwa zata min abinda tamin yanzu tsaf zan qaryata.
Har muka qarasa gidan za
ncen sukeyi nidaiban kuma cewa komai ba.
Badai har kun
dawo Ba"Ammi dake kishingide ta fada
Eh yan daukar am
arya ne sukazo shiya muka taho"nace
Allah sarki Allah ya b
asu zaman lpy,ai nusai ba akwai hankali ko bayan da bakyanan bata bar zuwa muna gaisawa ba,duk da a lkcn mahaifiyarta fishi take dani gani take kamar da gayya aka hana danta aurenki,shine tayi masa auren huce haushi da yar aminiyarta"Ammi tace


Ashe dai da gaske ya sadiq yake daya ce ba aure yayi ba aure akai masa,Amma hakan bai hanashi yin biyayya ga iyayenshi ba ya zauna da matarsa lpy gashi cikin qanqanin lkc ya samu Riba ga matarsa dauke da juna biyu.
Su mubina suka
shiga bawa su ya aisha lbrn yadda mukayi da hauwa musa.Gajiya nayi da zancen na shige daki na kwanta kafin nayi dialing number din ruqayya musa,Allah ma yaso na karbi ta tan don nasan yanxu kam hauwa musa bazata saurareni ba bare ta sakani wani grp.Allah ya taimaka itama ruqayyan Admin ce tace zata sakani a grps din.
Daf da magriba mukaje raka ya zee don zataje tayi girki a gida,a dawowa muka hadu da Abbi,duk da layi ne banji kunya ba naje na daneshi.
Aa khadijatu karki


qarasa abbin naki mana"Yace yana dariya.


Abbi nayi kewarka ne pa"Na fada cikin shagwaba.
Daga shi harsu mufida dariya
sukemin har muka koma gida.
Dawowarmu
Abbi ya fatattaki su ya ruqayya akan su tafi gidajensu,sunaja kumburi wai don yau ya samu auta shiyasa yake korarsu.
Ana wannan dramar mijin
ya aisha yazo,don haka suka tattara duka bayan na karbi numbers dinsu inda zasu raqewa su ya ruqayya hanya.
Kamar yadda na saba lkcn ina
gida yauma haka ina kwance cinyar abbinah,su mufida na gefe munashan hira gaba daya.
Yan biyu ince dai kwana biy
u akazo yi mana,don naji abdurrahman yace kuma gaf ake dayin naku bikin"Abbi yace.


Aa abbi m.sabo muke jira idan yazo zamu wuce"mubina tace.
To allah ya tabbatar da alkhairi ya jiqan mahaifinku"
Saida mukaci tuwon dare kafin m.sabo yazo,zan fara kukan shagwaba Ammi tace zasuxo dukansu bikinsu mufida.ba shiri na fara goge hawayen.


Dakinmu na shiga na kwashi sauran tarkace na danake buqatamuka tattara muka wuce.






Khaeraty ce!! Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment