Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai xamuji,ki tashi ki damawa abbinku fura nasan yanxu yana hanya"
Da to na bita,saeda ta fita mukai sallama dashi na tafi yin aikin.


Kwana biyu abbi yayi tpy qauyensu ziyara,kadaici ya isheni na shirya na tafi gidan ya Aisha.
Sosai muke hira inda yaranta suka baibaye ni kamar su maidani ciki.
Babbar itace muhibba yanxu shekararsa 6,sai Ammar,hanif sai kuma Hudallahi.


"Wai bazaku qyaleta ta huta bane ba muhibba?kuyita damun mutane kamar xaku shige cikinsa"ya aisha tace ganin yadda suka tarusuna sukuwa a kaina.


"Qyalesu yaya ai nama fasa kwana tunda basa jin mgn"
Da sauri suka sauka kowa ya nutsu dan anaso na kwana.
Kwana biyu nayi niyyar yi amma washegari nace ni gida zan tafi na baro ammina ita kadai.


"Ai dayake wani abune xai cinyeta ko kuma ke inkinje wani abu xatayi miki"ya aisha tace


"Yaya baxaki gane ba,ita uwa dadine da ita,jina nake kamar na shekara bama tare duk da dazu munyi waya,kuma nusaiba tace tanason gani na da lbr"


"Oho kudai kuka sani,dan ba tun yau ba nasan akwai abinda kuke qullawa dake da nusaiban"


"Wlh ba abinda muke qullawa sai alkhairi"nace ina ninke kayan dana cire xan shiga wanka.


"Oho dae idan tayi wani maji"tace tana fita a dakin.
Sai yamma na baro unguwar,kamar kullum saida muka sha dabi da yaran sannan na taho,wai kowa sai ya bini,wayyo ni uwar yara๐Ÿ˜œ.
Tun dana sauka a titi wani yake bina a baya,ina sane dashi,qara sauri kawai nayi dan banaso ya biyoni cikin layinmu dan yau juma'a nasan yanxu ya sadiq yana gida kar ya jamin fishin sahibil qalb๐Ÿ˜.


Assalamu alaikum"najiyo sallamarsa a baya na.
Saida na runtse idona kafin na amsa sallamar,dan banso ya min mgn ba dan mun kusa da gidansu ya sadiq.


"Baiwar allah idan baxaki damuba ba ki bani mintina biyu muyi mgn"
Banyi mgn ba dan sallamarma nasan muhummancinta shiyasa ba amsa,gashi hankalina yana kan qofar gidansu ya sadiq dan ban manta marin da nasha shekaru biyu da suka wuce ba agunsa,akan wasusun biyomu nida nusaiba munje gidan wata qawarmu.
A lkcn harna koma mkrnt ban qara ganin dariyar ya sadiq ba,a lkcn muka fara ganowa sona yake dan alamu duk sun bayyana.
Ganin har lkcn mutumin nan bina yake yasa na tsaya dan neman maslaha.


"Dan allah bawan allah kayi hqr,wlh an kusa bikina kuma babanmu idan ya ganni dakai dukana zaiyi"


"To shikenan yanmata na gode,yaushe ne bikin sai nazo idan an gayyace ni"


Murmushi kawai nayi wanda yayi dai dai ta qarasowar ya sadiq inda muke tsaye,kallon da yayimin kawai yasa nasha jinin jikina.Wucewa yayi dama akan lifan dinsa yake da dukkan alamu daga wajen aiki yake dan a gidan radio yake aiki kasancewarshi dan jarida.
Ban kuma bita kan wannan mutumin ba nayi gaba dan duk shiya jamin nasan halin ya sadiq da kishi amma saiya wayence wai karatu karatu,wai na daena kula kowa inba haka ba zan samu rauni a krt na kuma daga baya yaxo ya kasheni da kalaman soyayya๐Ÿ˜„.


Daga lkcn xuwa dare nayi masa missed calls sunyi goma,hakan ya bani tabbacin na taro march.
Da wuri nayi bacci dan yau ba abokin hirar.nusaiba na kira itama swich off dan haka baccin takaici ne ya daukeni.
๐Ÿ’™๐Ÿ’™ RABON KWADO..๐Ÿ’™๐Ÿ’™




Na Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹




Luv u oll Readersโคโคโค




๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™






๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹






๐Ÿ…ฟ21-๐Ÿ…ฟ25


Washegari ma haka naita kiran ya sadiq wayar a kashe,duk sai naji ba dadi duk da allah ya sani ba laifina bane.
Wayar nusaiba na kira dan samun mafita kasancewarta abar shawaratah.


Hello sis"najiyo muryarta daga can bangaren.


Naam sis kin tashi lpy?"


Lpy lau,yadae najiki haka?"


Sis ya sadiq ne ke wahalar da zuciyata"


Hhhh,me kuma ya faru?"


Labarin abinda ya faru na shiga bata.


Tab!ashe kece kk jamin yau akaqi amsa gaisuwata"


Dan allah da gsk?wayyo ni ya zanyi?"


Kawai ki shareshi malama idan ya gama fishin nasa ya sauko,mutum yaita wani abu sai kace mijinki?"


Aa sis kar miyi haka dake,kishi pa halak ne,nasan nice mai laifi dan haka dole sai na bashi hqr"


Kedai kk sani"


Au haka ma xakice koh?"


Allah kuwa sis wani lokacin kamar a dakeki,ki qyaleshi dan allah kepa mace ce allurar cikin ruwa mai rabo ka dauka"


Kinga ni shawara na kiraki ki bani ba wani qarin bayani ba,in kuma baxan samu ba nayi gaba"


Maida wuqar to,yanxu ya kk so ayi"


Inaso ki tayani bawa ya sadiq hqr har mu shawo kansa"


Tom xan gwada na gani"


Haka mukai sallama na ajiye wayar na shiga aikin gida,amma xuciyata duk a jagule.


Har dare ba wani canji dan ya kunna wayar amma yaqi amsa kiran.
Dan dole na hqr,amma xuwa yanxu na fara fusata akan lamarin,Taya zanta kiransa yaqi dagawa,dole nabi shawarar nusaiba na qyaleshi har lkcn da xai sakko.
Haka na cigaba da harkokina dukda xuciyata ta kasa jure rashin ya sadiq amma haka naita dauriya,qarshe dai na yanke shawarar barin unguwar gaba daya.


Inason xuwa gidan ya fatima amma wannan mijinnata mai baqar zcy shine banson gani.dan hk gidan ya ruqayya nace zanje.


Da azahar na shirya na tafi tarauni dan nusaiba ma text nayi mata nace na tapi.


ya ruqayya taji dadin zuwana sosai haka itama muka sha hira,yan samarinta haka suka dameni kowa da irin tasa fitinar.
Munif ne babba,sai mufid shine mai sunan abbi,affan da kuma qaramin mubin.
Qaunarsu nakeji har cikin raina,amma abinda zai bawa kowa mamaki shine duk yaran yayyena nafi qaunar yaran ya fatima,duk da rashin jin shahid amma ina qaunarsa.yaron fitinanne ne yafi kowa rigima a cikinsu hakan yasa nake cewa halin babansa yayo,itadai ya fatima murmushi ne kawai nata.
Yaran ya fatima shahid ne babba,sai shahida sannan iman ita yanxu shekarta daya da rabi.
Da dare haka mukaita tatsuniya munashan dariya,itadai ya ruqayya gurin mijinta ta tafi ta barmu anan.
Bacci sukayi suka barni ina zuba,qarshe dai da dai daya na kaisu makwancinsu kafin nima na nemi nawa.
Tunda na taho na kashe wayata,sai yanxu da kadaici ya isheni na kunna,dan da a gidane yanxu ina kwance kan qafar abbi munashan hira.


Kamar jira ake kiran nusaiba ya shigo.


Haba sis tun dazu inata kiranki a kashe"


Wlh sis kashe wayar nayi"


To ai kin kyauta,naga text wai kin bar unguwar?"


Eh wlh unguwar ce ta daina min dadi"


Eh lallai,dama ya sadiq ne ya tmby ni wai mene ya samu wayarki ya kira a kashe"


Dan allah da gsk?


Eh mn,dama bana fada miki ba,shi kanshi bazai iya jurewa ba,amma duk kibi ki damu kanki"


Uhmm sis baxaki gane matsayin ya sadiq a zcytah bane,baki san zafin so ba da fushin masoyi shiyasa kk fadar haka"




Sannu wadanda suka yankewa soyayya cibiya,ni kinga yaushe zaki dawo?"


Ki tmby ya sadiq,dan sai ranar daya daina fishi dani xan dawo"


Dif!naji ta kashe wayar ko ba'a fadan ba nasa haushin mgn ta taji.oh nusaiba danger,ita gani take banida aikin yi idan ina irin wadannan maganganun batasa ita kadai nake iya fallasawa sirrin zuciyata ba,dan koshi ya sadiq din cikin qorafi yake wai banasonshi.
Jin danayi nusaiba tace ya sadiq ya tmbyta ni ya tabbatar min ya sauko daga fushin da yayi,kuma a kowani lkc xai iya kirana,amma inason ya dandana abinda naji dan haka nayi addu'a tare da kashe wayar nabi lpyr gado.


Washegari ma saida muka gama aikace aikace nida ya ruqayya,nayi wanka nayi breakfast sannan na dauko wayar dan yaran gidan duk sun tafi mkrnt,mubin ne kawai tunda shi bai isa xuwa mkrnt ba kuma shi ba wata hira xamuyi da shi ba.
Data na kunna dan ganin me duniya take ciki,dan ni ban damu da hawa online sosai ba(ba kamar Er baby ba da kullum ana online๐Ÿ˜œ).


Sosai nake jin dadin chatting din kiran ya sadiq ya shigo.har ta katse ban dauka ba saboda nidin mai ajice๐Ÿ˜„,duk da dunbin qaunarsa da kewarsa da nake hakan bazai sa na zubarda ajina na 'ya mace ba.
Daya qara kira ma saida ta kusa katsewa na dauka.vanyi mgn ba shima kuma baiyi ma.munkai tsahon 5mnts a haka dan da niyyata na kashe wayar tunda bashida abin fada.


"Khadija ni kk wulaqantawa koh?"najiyo muryarsa data fi kama data marasa lpy.


Nipa ba wulaqanta ka nake ba"


To mene wannan inba wulaqanci ba?ko kuma raini ne dan kinga ina wasa dake?"


Aa kayi hqr"nace dan jin ya fara mgn da fada fada.


Waye wanda na ganki dashi jiya?"
Saida nayi murmushin mugunta kafin nace.


"wani ne wai sona yake,shine ya biyoni yaga gidanmu wai zai turo a tmbyr masa izini"


Wani dan iska ne kuma a ina yake?baki fada masa ba yanxu xakiyi aure ba?ko kuma baki fada masa akwai wanda yake jiranki ba?wlh wlh khadija ki gaggauta sallamarsa idan ba haka ba kuma.."


Dif!ya kashe wayar.ni dariya ma wallahi ya bani,wannan tmbayiyi kamar yana mini interview?
Sai daga baya tausayinsa ya kamani,gsky ya sadiq masoyi ne na gsky,tun bansan kaina ba yake dakon soyayyata,kuma ya haqura da aure badan wai baya buqata ba Aa sai dan gani ya ingantan rayuwa ta ta hanyar ganin na fara karatu,dan yanxu karatun shine mutum.
Ya sadiq yana taka matsayi kala kala a gurina,wani lkc yazo min a matsayin yaya wanda yakeji da qanwarsa wanda nakan ji dadin hakan koba komai nima naji abinda masa yayye maza sukeji,wani lkcn yakanxo a matsayin masoyi yaita kasheni da kalaman soyayya dan a wannan bangaren gwani ne,wani lkcn yakanxo a matsayin yayana wanda zaimin fada tare da bani umarni shima nakanji dadin hakan dan nasan wani fada da nasihar da yakemin ko nusaiba da take qanwarsa ta haqiqa bayayi mata.
Hakan kan qara masa matsayi da qima a idona,shiyasa ko yaya naga ransa ya baci sai na shiga damuwa musamman ma idan nice silar bacin ran nasa,dan shima ko kadan bayason yaga bacin raina.ya sadiq ko budurwa yayi saiya fada min,nakan tmbyshi ki meyasa yake fadan shine yace shi bayaso zargi ya shigo cikin lamarinmu shiyasa tun kafin naji yake fadamin da bakinsa kuma da sigar da zan fahimci inda ya dosa.
Kai ya sadiq mutum ne wanda ko wace mace take fatan ya xama abokin rayuwarta amma ni qaddarar rayuwa ta nisanta ni dashi,tayi mana katangar a tsakaninmu mai wahalar rushewa๐Ÿ˜ญ๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO....๐Ÿ’™๐Ÿ’™




Na Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’–๐Ÿ’‹




๐Ÿ…ฟ26-๐Ÿ…ฟ30.


A gurguje Haka rayuwa ta cigaba da tapiya inda result dinmu ya fito muka zana jamb nida nusaiba dan alhmdllh result dinmu yayi kyau.
Cikin ikon allah muka nasarar samun admission da taimakon abban su nusaiba,inda zan karanci bangaren law nusaiba kuma bio/chem.
Farin ciki wajen yaya sadiq ba'a mgn nasiha da shawarwari kuwa na shasu kamar shine abbi na.
Cikin nasara muka fara gudanar da lectures dinmu a jami'ar bayero,inda mukayi da ya sadiq xaije wani course na 6months daya dawo xa'akai mgnr aurenmu wajen abba asa rana duk a lkcn dan yace bayaso asa sama da wata biyar.
Haka mukai sallama dashi da tarin nasihohinsa gareni ya tafi ya barni da kewarsa dan har kuka saida nayi.
Sosai lectures suka fara daukan dimi,inda muka maida hankali kan krt ba wasa.
Ya fatima ce ta kirani wai nazo gidanta mijinta yayi tafiya ga dawainiyar yara ga kuma cikin da take dauke dashi.
Haka na tattara na tafi dama kuma gidanta yafi kusa da scul din tunda ita tana rijiyar xaki.
Duk wata dawainiyar yaranta nice nake musu kafin na tapi scuk duk da suma idan suka tafi tun safe sai yamma,amma fitinar shahid sai abinda ta qaru.
Yauma haka yaje ya zazzagen handbag dina a qasa ya dauko handouts dina ya yi min zane a jiki.
Naji haushin abinnan naje tana barandar gidan tana shan iska.


"Yaya kinga yadda shahid ya wuqanta min handout dan allah"


Kinga auta kuje can ku qarata na gaji da shirginku keda shahid,tsoronsa kk ji da baxaki hukunta shi ba?ko kuma idan danki ne haka zaki biye masa kina kai qararsa?"


"Amma yaya kina ganin yadda ya rainani ban isa nayi abuba sai yayi mgn kamar wata sa'arsa"


"Dan allah ni kuje ku gyaleni naji da kaina"tace tana kwanciya.


"Wlh mai rabani da yaron nan sai allah"nace ina komawa cikin gidan.


Bansan fitinar shahid takai haka ba saida naga muna dambe dashi kamar wani sa'a na,ai kuwa zuciya ta deboni na samu nasarar warbar dashi a qasa aka samu akasi goshinsa ya fashe ya kwalla qara,wadda tayi dai dai da qarasowar daddynsa da ya fatima wanda da dukkan alamu dawowarsa kenan,amma da nasan yau xai dawo da daga mkrnt na wuce gidanmu bare na kwashi wannan kayan takaicin.
ko kadan banyi nadamar abinda nayi ba sai danaga jinin da yake fitowa daga goshinsa.


"Hayaty bari muje asibiti ko zamu sami jinin ya tsaya"daddyn nasu ya fada yana wani cin magani.
Ni kuwa nace idanma dan ya ganni a gidansa ko dan najiwa dansa ciwo yake wannan abin to gobe da safe ma xan kama gaba na,yanxunma dan dare yayi ne amma da ba abinda xai hanani tafiya.
Daki na shige dan gaba daya gidan haushi yake bani.
Ban dade da kwanciya ba ya fatima ta shigo.


"Auta badai bacci ba bakici abinci ba?"


Ni na qoshi"


Haba autar ammi ki taso kici ko kadanne,ko kinason ammi tace bana baki abinci?"
Girgixa kai nayi.


"Yawwa to tashi muje kici,sai ki dauko su iman daga falo ki kyautar dasu"
Kadan naci abinci na daukosu dama tunda naxo tare muke kwana,bacci nayi bansan lkcn da yan asibiti suka dawo ba๐Ÿ™
Washegari tun asuba nayi wanka dan inason barin gidan tun kafin mai gidan ya farka daga bacci.
Da yake weekend ne har 9 ina xaman jiran yaya tazo dan tana bangaren mijinta.da yake gidan babba ne gsky kuma an kashe masa kudi iya kudi,dan duk gidan ya fatima yafi na sauran haduwa.
Kiran wayarta nayi a kashe dan haka tea kawai na hada na rubuta letter na ajiye mata a gado nace mata kirana akayi muna da text 10 shiyasa na tafi kuma daga can xan wuce gida.
Daqar na samu abin hawa kasancewar safiya ce kuma unguwar shuru kowa yana cikin gida dan saida nayo tpy mai nisa kafin na samu amma duk ban damuba sbd sa kai ance yafi bauta ciwo.
Ammi batai mamakin ganina ba dan tasan halina,kuma tasan bama jituwa da gidan ya fatima,abbi ne dai yake ta tmby ko lpy na dawo yanxu kamar an koro ni?


"Abbina mafarkinka nayi shine yau da safe nace ni saina xo na ganka"na fada a shagwabe.
Dariya yayi


"Khadijatu bakya gajiya da shirme,kin baro su lpy dai koh?"
Amsa masa nayi na shige daki.
Da ya fatima ta kira kuwa nasha fada wajen ammi nidai bance komai ba tunda nazo gida.


A kwana a tashi babu wuya a wajen allah.
Yau muke saka ran dawowar ya sadiq,amma bansan mai yasa ba yau din banajin dadin jikina ga gabana da yaketa faman faduwa.
Haka na fara shirin xuwa scul ina karanta du addu'ar data xo bakina.
A scul ba haka na yini sukuku,da muka fito a lecture na fara kiran number din ya sadiq dan jin ko wani abu ne ya sameshi.


Hello yanmatanah"naji ya fada hakan ya tabbatar min yau a masoyi yake mgn,dan naga ko jiya da mukai waya sai wani rawar qafa yake waishi angon wata5 ne.


Yaya kun sauka ne?"


Eh mun sauka heartbeat tun dazu amma office na wuce dan akwai wani record da nakeson bayarwa"


Tom saika qarasa gidan nima yanxu tapiya xanyi"


Har kun gama lecture dinne?"


Aa kawai inason xuwa gida ne dan tun safe gaba na yake faduwa"


Subhanallah!kina addu'a dai koh?"


Eh nayi"


To kije gidan anjima zamiyi waya"
Sallama mukayi na kamo hanyar gida.
Ina shigowa layinmu na hango motoci biyu a qofar gidanmu,ga wasu mutane a tsaye dana hango a gefe.
Gaba nane ya tsananta faduwa,tunani kala kala da zullumi sun cika min xuciya.
Banbi takan mazan da suke qofar gidan ba na fada gidan a sukwane.
Mutum na fara cin karo dashi a kwance an lullubeshi da farin gyalle,abbi a tsugunne a gefe yana sharar kwalla sai ya ruqayya itama da take rusar kuka.
Gabana ne ya cigaba da bugawa kamar xai fado,ya ruqayya na nufa ina tmbyrta ina amminah dan banason gargina ya tabbata.
Nuni tayi min da daki ba shiri na fada dan tabbatarwa.
Ammi na zaune akan sallaya tana jan carbi,lokaci lokaci tana share kwalla.


Ammi meya faru?waje ya mutu?"Na tmby ta rarrauniyar xuciya.


"Sai hqr auta yayarku fatima ta rigamu gidan gsky"


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!ya fatima?ya fatima kuma?ya fatimanmu ce ta rasu??
Cak!nunfashina ya tsaya Inda duhu ya fara mamaye idanuna wanda daga lkcn banqara sani meya faru ba kawai dai na bude ido na ganni a gadon asibiti.


Ya zainab ce zaune a gefe na,kana ganinsa xaka gane tarin damuwar dake tare da ita.
A hankali abubuwa suka fara dawo min inda wani kuka yazo min bai daci.


Ya zee da gsk ne?da gsky ya fatima ta rasu?da gsk ta tafi ta barmu baxamu qara ganinta ba?yanxu shikenan...."
Ya xainab ce ta saka hannu ta rufen baki.


Ya isa haka,baki ga halin da kk ciki ba?bakiga tsahon kwana biyun da kk dauka ba numfashi a tare dake ba?ki inason ki qara janyo mana wata damuwar?"kuka ne yaci qarfinta dan dole tayi shiru.nima kukan nake ina jadadda cewa wai ya fatima ta rasu.


Auta yaya ta rasu,yaya ta tafi baxata qara dawowa ba,mutuwa ba qarya bace fatanmu allah ya jiqanta da rahma,duk da tayi mutuwar shahada dan bata kai ga haihuwa ba allah ya karbi abinsa"
Haka muka hadu mukaita rabxar kuka.


"Yaya inasu ammi?"na tmby da dasasshiyar muryata.


"Dukkansu suna gida karbar gaisiwa kinsan yau sadakar uku,amma duk dare suna zuwa duba ki"
Allah mai iko ashe dai da gsk nayi kwana biyun ba motsi,allah kenan mai rayuwa da mutuwa.
Turo qofar da akayi ne yasa muka tsagaita da kukan.nusaiba ce da ya sadiq,wanda shima kallo daya xakayi ka gano yar ramar da yayi.
Da gudu nusaiba tazo ta rungume ni tare da sakin kuka.haka muka hadu ba mai rarrashin wani shidai ya sadiq fita yayi sai gashi sun dawo da doctor.
Dubani yayi tare da rubuta magunguna sannan yayiwa ya sadiq bayanin xasu riqeni xuwa gobe idan sunga jikin da sauqi xasu sallame ni.
Godiya ya sadiq ya masa kafin ya sadiq din ya xauna ya fara mana nasiha mai shiga xuciya.sosai nasiharsa tayi tasiri a xuciyoyinmu,saida ya tabbatar mun samu nutsuwa kafin su bar asibitin.
Da dare su abi sukaxo da su ya aisha amma wai babu ya fatima,allah mai iko.nan ma wani sabon kukan mukasha,Daqar abbi ya shawo kanmu da nasihar yadda da qaddara don hatta ammi ma kukan take.
Sai can dare suka tafi.ya zee ta samu bacci amma ni tunanim rayuwa kawai nake.haka fa rayuwar take yau kananan gobe baka nan.
Tuno ranar da dukkansu sukazo gida muka hadu akaita wasa da raha da kuma shirye shiryen suna idan ta haihu,ashe bama zata haihun ba bare ayi sunan.
A ranar da zasu tafi mijinta yazo daukanta,na rakata ina dauke da iman datayi bacci dansu ya aisha tun yamma suka tafi ita kuma ta zauna tace sai mijinta ya dawo daga aiki xaixo ya daukesu,har na saka iman a mota ina musu bye bye ta jawo kunne na.


Wato kina ganin daddyn shahid bazaki gaida shi ba koh?kewai a rayuwarki bakya yafiya ne?"


Turo baki nayi nace"to bana gaidashi ba"


Baki gaida shi ba na sani kawai dai kin fada ne,kuma zanyi maganinki tunda bakyajin mgn"Tace tana sakin kunne na.


Kiyi hqr kinji sweet yaya"nace ina kamo hannunta.


Idan kinason na hqr sai kin yafewa mijina"


Ganin mijin ya shiga mota yasa banyi mgn ba na tafi ina mata waving da hannu ashe na bankwana nayi mata๐Ÿ˜ญ.
Haka naita tunanin abubuwan da suka faru tare da ita,bansan lkcin da bacci barayo ya sace ni ba.
๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™








Tare da Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹




Gaisuwa da jinjina gareku masoya abin kaunata,musamman yan khayratie's hausa novels allah ya bar xumunci.๐Ÿค๐Ÿค






๐Ÿ…ฟ31-๐Ÿ…ฟ35


Washegari wajan 11 na safe ya sadiq ya dawo asibitin,inda yaje ya karbo takardar discharge kafin ya shigo.


Ina kwana"nace ina satar kallonsa ganin ya tsaya yana kallo na.


Lpy lou,ya jikin?"


Da sauqi"


Ya haqurinmu?"ya kuma tmby.


Kwal kwal idona ya ciko da kwalla.


Kinga ni ba kuka nace kimin ba,ina ya zee din?"


Yanxu ta fita bansan ina taje ba"


Shine take barmin princess dina salon azo a sace min ita?"


Murmushi nayi kawai ina qara satar kallonsa dan ramar dana ga yayi.


Ya sadiq naga ka rame?"


Ba dole ba nernah?kina gadon asibiti rabi rayuwa rabi mutuwa"


Allah sarki ya sadiq,allah ya bani ikon faranta maka tsahon eayuwata"na fada a xcytah dan bana iya sakewa dashi indai mu kadai ne a guri,duk da dadai nasan bazai cutar dani ba,amma idan muna tare da nusaiba hira mukesha sosai.


Khadija kinga yadda allah yake al'amarinsa koh?a yadda na tsara washegarin dana dawo zan tura wajen abbi amma sai wannan rashin ya samemu,kinga dole a jinkirta zuwa lkcn da komai xai dai dai ta"


Allah ya kaimu"nace cikin jin kunya.


Wa yaga khadijan abbi amarya"ya fada da sigar wasa.
Haka yaita jana da hira har ya zee ta dawo muka tattaro muka dawo gida.
Har lkcn muna samun masu xuwa gaisuwa duk da abbi ya hana zaman makoki.
Ina maqale dasu iman dan tausayin yaran nakeji yana ratsa zuciyatah,Allah ka haskaka kabarin ya fatima amiin๐Ÿ˜ญ.


Bayan kwana biyu kowa ya watse dan abbi haka yace su ya aisha su koma gidajensu xaman ya isa haka ita dai ta riga ta tafi ba dawowa zatayi ba.
Tafiyarsu ta karamin kadaici dan su shahida ma wai anxo an daukesu daga gidan kakarsu.


Tsahon sati biyu bana zuwa scul,hakan yasa abbi ya ringa fada dan dole na na shirya na tafi dama nasan ba'a son ran ya sadiq naqi xuwa ba dan bayasan takura ni ne kawai,ga exams da muka kusa farawa.


Yau satin ya fatima 3 da rasuwa.
Ina kwance a daki ina karatun text naji an daga labule,duk a zato na ammi ce amma ga mamaki na naga abbi.
Saurin tashi nayi xaune ina gyara dankwalin kaina tare da yiwa abbi sannu da xuwa ganin yana niyyar shigowa dakin.
Ban gama mamaki ba sai danaga yana zama a gefen gadon.


Abbi ashe ka dawo?daxu na tmby Ammi tace ka fita"


Eh khadijatu na dawo"yace yana kama hannu na.
A hankali na zame na kwanta akan qafarsa kasancewata mai son jiki๐Ÿ˜Š.


Khadija wannan zuwan dan ke nayi shi,ina neman wata alharma ne a wajenki shiyasa na tako da kaina a matsayina na mai nema"


Abbi alfarma kuma?har inada abinda zaka nema a wajena?"Nace ina wasa da yatsun hannunshi.


Eh,fitarnan da nayi naje can wajen sirikan marigayiya fatima ne,kuma a zaman da mukayi mun yanke shawarar ranar asabar mai xuwan nan za'a mayar da auren fatima kanki"


Wata zabura da nayi bansan lkcn da na fado a kan gadon ba.


Abbi kamar ya?ban fahimci me kace ba"Nace duk a rude.


Kinga inaso ki kwantar da hankalinki,muma bawai mun yanke hukunci ne haka kawai ba.bayan fatima ke kadai ce wadda zata iya riqe yaranta da gsky,kuma xaki riqesu kamar kece kk haifesu,koba danni ba khadija ki tausayawa rayuwar yaran nan ki maye musu gurbin mahaifiyarsu"


Wayyo allah na,Allah yasa mafarki nake akan wannan batu,kai ko mafarki nake nasan to yau mummunan mafarki nayi.


Khadija ki min mgn mana,bawai kuka nace kiyi mini ba"na jiyo maganar abbi.


Kuka?dama kuka nakeyi?Wayyo wlh ina ganin na haukace.


Abbi dan Allah ka taimaki rayuwata karka hadini aure da mijin ya fatima,abbi akwai wanda yake sona tsakani da allah dan allah ku tausaya masa"nace ina ja da baya.


A hankali abbi ya kamo ni ya kwantar dani akan qafarsa,bai kuma mgn ba sai daya ga na fara samun nutsuwa.


Khadija kk ce akwai wanda kk so?"


Eh Abbi,wlh ya sadiq yana qaunatah,Mutuwar nan ce ta hana a aiko manya daga gidansu"


Shiru yayi na tsahon lkc kafin ya kira sunana.


Khadija yanxu a matsayi na mahaifinki ashe baxan iya baki umarni kibi ba?a dazu naxo miki a matsayin mai neman alfarma a yanxu kuma ina mai baki umarni ne,inaso ki saka a ranki zuwa ranar asabar zaki bar gidan nan da sunan aure"bai tsaya bi takaina ba ya tureni daga jikinsa ya fice daga dakin.
Daga inda ya tureni nidai haka na kasance a kwance,ban sani ba suma nayi?kai ba suma bace qila mutuwa nayi tunda ance idan mutum ya mutu yana jin abinda mutane suke cewa kamar yadda nima ina iya juyo wayar da abbi yakeyi da mutane cewar ranar asabar akwai daurin auren yar wajensa.


To wai har gani mutum yanayi idan ya mutu??na tmby kaina ganin ammi ta shigo dakin ta riqoni fuskarta da alamar tausayawa daqar nema idan ba kuka tayi ba.


Khadija kiyi hqr kinji?ki yiwa abbinku biyayya insha allah zakiga ribar hakan"


Wai ammi batasan na mutu bane take tayimin mgn?bari dai nayi mata bayanin na mutu suje kawai su binne ni.


Ammi"


Naam khadija kiyi hqr kinji,kiyita addu'a allah yasa haka shiyafi alkhairi"


Wayyo masu karatu wlh na haukace,nashiga uku da gsk na hauka ce.......




Wait a moment....๐Ÿ˜Š๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™






It's me Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
๐Ÿ’™๐Ÿ’™RABON KWADO...๐Ÿ’™๐Ÿ’™




Er mutan ungogo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹






๐Ÿ…ฟ46-๐Ÿ…ฟ50


wai auta yaushe zaki bar wahalar da kanki kibar asarar hawayenki?Abinda kk yiwa kuka ya riga da ya faru,to y not ki samawa zcyrki sauqi ki dauki qaddara"ya aisha tashe ganin na samu damar kuka.


Banyi mgn ba domin nasan duk abinda zan fada mata bazata fahimta ba kunga maganar bata da amfani.


Da yamma ina kwance ina saqa da warwara ya aisha tazo ta zauna a kusa dani.


Ki tashi kije kiyi wanka"
Banyi musu ba na tashi dan ni kaina nasan ina buqatar wanka.


Dana fito

Please Login or Register in order to submit comment