Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusan inna wuro da abdallah ne jigon.


Kwanukan maryam ta kwashe ta kai cikin tukunyar tuwon da aka cikata da ruwa don inna wuro tuni ta hanata wanke wanken dare
ta tattare gun ta nufi soron inda suke ajjiye abun shararsu don ta zubar,soron babu haske don wearing din solar da kayi banda nan don haka bata iya ganinsu sosai,saidai tana ganin tsaiwatsu daga can qofar ficewa a gidan baki daya,muryar indo ta fara ji
''yanzu ke mero idan banda tsaurin ido inake ina wannan balaraben tsabar daukowa kai masifa da kuma jan abinda yafi qarfinka,ins laifin ma ki tsayawa labaran dinki,tunfa kina mitsitsiyarki yake sonki kuma an bashi ke,rashin kudin kayan daki ne ya hana auranku amma da tuni yanzu ai kina da yara''
''babu jan masifa,wallahi indo kada ki dauka wasa nake,da gaske sonsa nake wallahi tun ranar da na fara ganinsa,inason abdullahi sosai wallahi''
''tab,to kuwa kin debo da zafi,daidai ruwa fa daidai qurji,wai shin wannan 'yar indiyar ta gefensa ba matarsa bace,idan kuwa hakane to inake ina hada kai da ita,aradu baki fice irin aikinsu da ake kai musubirni ba,ta gurin gashi ne kawai zaku goga da ita amma ta wuceki mero,kiyi haquri kada ki wahal da kanki''.


tsaki mero ta ja
''bafulata ce kamar ni shima haka,yo to ni ina ruwana da matarsama indai shi yana sona ai shikenan,kuma ni ban taba ganin ma ta,nuna,wani abu ba sai rashin fara'a da take da ita kuma wannan halinta ne,ke koma mebe ita ta jiyo,nidai ina son abdullahi kuma bazan fasa......''
jin taku ya sanya mero yin shiru suka waiwaya da sauri,sai sukayo tairu tauru,maryam ce ke takowa inda suke ta qarasa gaban sharar tayo bismillah ta zuba kana ta juya ba tare da tace musu komai ba,zucoyarta ke mata wani irin suya,duk da qoqarin kwantarwa da kanta hankali da take kan ba son abdallah take ba don me to zata ji zafi don wata tace tana sonshi.



bin maryam suka yi da ido har ta shige cikin gidan,suka dawo da idonsu kan junansu suka kalli juna,indo yace cikin zare ido
''kinga irinta ko๏ผŸyanzu gashi ta ji''cikin son nuna dakiya mero tace
''to baki ga babu abinda ta yi ba,na gaya miki ita fa babu ruwanta''harararta indo tayi
''ashe dai baki da kai mero har yanzu,wace ce zata ce bata kishin mijinta,kina kallon yadda kullum sai anje gudan mai gari rabon fadan kishiyoyi kamar zasu hallaka junansu,bakisan halin irin wadannan matan birnin bane,qila wallahi qyaleki tayi ranar da ta tashi saka ki a maqata babu mai fitar dake,ko kin manta yadda akayi da jummai ita da lantana kan mijinta๏ผŸ''tuno abinda ya faru din ya ruda mero tace
''wallahi hakane fa,ni ai na manta''kama hannun indon tayi qam qam tana kallon cikin gidan
''wallahi bazan koma ba ma cikin gidan,zo mu tafi''ta figeta suka fice gabanta na faduwa saboda tsoron abinda ya faru da lantana kada ya faru da ita,don a yanzun tana nan tana fama da ido daya wanda jummai ta tsiyayar mata.

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Tunda nene ta yiwa malam na hayi maganar su gizago yace ta kwantar da hankalinta,ta riga ai da ta sani fada da aljani babu dadi,cikin kwana daya ya masa 'yan surkullensa ya rufe bakinsa bai kuwa sake dawo musu.

********

dukkansu suka qarewa dakin qwaya daya kallo mai azabar girma wanda aka ginashi da laka da ciyawa irin ginin qauye sosai,dukka suka dubi malam na hayi dake tsaye burgijaja cikin babbar riga da ta wadatu da maqale maqale na kayan sihiri,fuskarnam cike da suma ha hana qarya wanda yayi fiqi fiqi kamar yana barazanar tsone idon daya daga cikinsu,turo baki zahariyya tayi
''gaskiya malam nidai wanan abu yayi min tsauri,ina laifin ma asama min gida mai dan kyau ba wanann kwangon ba cikin wadancan kucakan mutanen da ake kira da mata,daga su har yaransu ni basa min,maraba da dabbobi don wallahi gwara na zauna da karnuka,da in zauna da su''ta qare maganar tana jan tsaki.


malam na hayi ya qara farashin muzuran da yake yi
''su mata na ne ke kuwa ba matata bace,matar aljani zulan anfaini ce,saboda haka babu ruwanki da wani cikin gidan nan,shi kuwa aljani ina ruwansa da wani kyawun giri,kwata kwata ke din ma ba zaki wuce wata biyu ba zakiyi naki gu,idan kuma zaman din din din kike so kuyi to sai a gaya masa,ya dauko miki gida daga dubai yazo ya ajjiye miki cikin gidan nan ki zabi wanda kike so ya maida sauran,ko kuma ya mayar da ke can bangon duniya kuyi zamanku daga ke sai shi''ido ta zaro tana ja da baya
''a'ah,ni bance ba malam kada ka jawomin salalan tsiya''
''ato,shine nima na gani ai''ya fada yana murza hana qaruarsa cikin zuciyarsa cike fal da sha'awarta,musamman idan ya dubi shigar da tayi sai yaji kamar ya janyota ya fara sha'aninsa a lokacin,zuciyarsa ke kwabarsa yabi a hankali,kada kwabarsa tayi ruwa tunda dai nan da jibi komai zai qare.


Cikin sigar lallashi nene tace
''yo banda abun zahariyya ma kwana nawa anyi an gama,ai dama bayan wuya sai dadi''
caraf adnan ya karbe zancen yana yarfa hannuwa
''ehenn,shine fa,to ni Allah na tuba ko kuttu aka ce na shiga na zauna ba shiga zanyi ba,daga fa 'ya'yan bankin sunzo fa sai yadda kaga damar yi'',hara ra zahariyya ta balla masa
''kaga idan ana zance fa ka daina sako kanka,gwara ma macen da kai''har zai hayyaqo,mata nene ta dakatar da shi don dukkansu biyayya suke mata yanzun lallaba ta suke.

๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚

kwana uku tsakani nenen da adnan suka rako zahariyyan gidan malam na hayi a matsayin amaryar aljani zul anfaini,babu abinda aka saka dakin face leda da katifa sai wasu qattin labulaye masu azabar nauyi da kauri wanda malam din ne ya saku su suma a dakin suka tadda shi,wai na aljani zul anfaini ne tanan zai dinga zywa gareta,buta ce kawai sai botikin wanka sai kayan sawarta akwati biyu.


sanda zasu koma ji ta dinga yi kamar ta bisu musamman da ta rakasu qofar gidan taga motarsu ta tashi bayan malam na hayi ya danqa muau 'yan dubu dubu sababbi qar na naira dubu dari uku kudin sadakin zahariyyar inji aljani zul'ainaini,ta dinga binsu da kallo suna keta duhin masara har suka bace mata,ajiyar zuciya ta saki tana jin ba dadi amma data tuna nan da wata biyi komai ya daidaita ta zama wata abar kwatance cikin alumma sai taji hankalinta ya kwanta ta juya cike da qwarin gwiwa ta koma cikin gidan.


gida ne tafkeke mai azabar girma kada ma tsakar gidan nasu yaji labari,ko ina ahimfide yake da jar qasa jazur da ita kuwa,gefe fuda bandakinsu yake mai gajeriyar katanga wadda idan kayi wani wawan tsallen ana iya hangoka,babu mamaki don ita kanta katangar gidan ma tsaf wani dogon mutum din zai kamata ya tsallaketa ba tare da ya taka komai ba,gidan tsakiyar gonaki yake,babu wani gida nan kusa da su su kadaine a gun sai dan gaba kadan bukkar da malam na hayi yake dab da wani rafi hakn ne ma yasa ake ce masa malam na hayi don sai ka hau kwale kwale sanna zaka tsallaka dan qaramin qauyen dake maqotansu inda nan din akwai mutane babu laifi.


dakuna ne rututu a jejjere kuma durqusasau kusan babu dakin,ma da ya kai nata kyua cikinsu sai qwaya daya na malam din dake can gefe guda wanda idan ka kalli dakin shi kadai sai ka dauka ba cikin gidan yake ba,gini ne sosai na zamani don hatta da bangon dakin da yar qaramar baranda da aka yi masa duka tiles ne manne da shi,alatu sosai aka zuba ciki duk da bata ganin ainijin cikin dakin amma kallo daya zaka masa daga waje ka gane hakan.


qofar bandakinsu kaca kaca da qasa da dagwalo sauran kadan ta aheqa amai tayi saurin dauke kanta,yara ne guyin guyin da mata gami da yammata gasunan ko ina tsakar gidan tamkar gidan marayu,kallo suke ta binta da shi kamar mayu manyansu da qana nanau,gefe guda kuwa yara ne zaune cincirondo guda dukakkansu babu mai tufar arziqi dan kamfai ne kawai a jikinsu daidaiku ne masu riga 'yar shar hanci kaca kaca da majina sun zuba mata idanu suna kallonta,daya daga cikin yaran ya taso daga cikin cabalbalin da suke wasa ya sheqo a guje yana mata dariya ya kama gefan rigar material din dake jikinta ruwanmadara take kuwa shatin hannunshi suka fito taya taya,batayi wata wata ba ta tsinkeshi da mari sai ga yaron a qasa warwas ya zube,da gudu wata mace cikin matan dake kallonta ta taho,hannu tasa ta dauke yaran ta janye shi gefe ba tare da tace komai ba,tayi tsammanin jin ihun kuka daga gin yaron saidai ga mamakinta ko uhm baice ba saima miqewa da yayi ya koma gun wasansa,kanta tsaye ta shige dakinta cikin bacin ran kayan da ya bata mata.

***********

tun magariba malam na hayi ya shogo ya gaya mata dokokin zaman aure da aljani zul anfaini,dole dakinta ya dinga kasancewa cikin duhu ana yin sallar magariba har garin Allah ya waye,hakanan duk abinda zata gani kada ta sake tace zatq yi magana ko tambaya a kai idan ba haka ba matsala zata biyo baya da haka ya mata sallama yace ya tafi gun iyalinshi.


wajejan sha daya na dare tana kwance cike da,azabar zafi dq sauro,ga matsanancin duhun da ya mamaye dakin,taja tsaki yafi cikin carbi,addu'a take cikin zuciyarta na bacci yazo ya dauketa kota huta,ta saba kwana cikin hasken qwai da sanyin raba kan tattausan gadonta ta lulluba cikin lafiyayuen bargo,yau sai gata cikin wani irin qadagirin daki,ko qauyensu mahaifinta basu taba marmarin zuwa ba sabida sam bata hada hanya ma da maras shi sai gata yau zata kwana cikin wani daji tsakiyar gonaki''kai neman kudi da wuya yake''ta fada cikin zuciyarta,cikin sa'a kuwa baccin yazo yayi awan gaba da ita.


Saidai ko cikakkiyar awa bata yi da fara baccin ba taji wani irin wari mai gigitarwa na ahirin tsaida fitar numfashinta,a rude ta farka daga baccin saidai nata iya ganin koda tafin hannunta saboda tsananin duhun dakin,tayi yunqurin tashi ta kasa saboda wani uban nauyi da taji samanta tare da wani irin nishi da gurnani,ta riga ta saddaqad aljani,zul anfaini ne ya iso saboda haka bata da wani saufan qarfi na qwatar kanta,haka ta koma ta kwanta daidai.


Tasha azabar da bata taba zaton shan irinta,duk da ba budurci gareta ba amma ko ranar da ta bada budurcinta wa saurayinta bata ji kalar wannnan azabar ba,tun tana ganewa har ta fita hayyacinta,bata farka ba saida hayaniya da haaken rana suka cika idonta
a hankali ta dinga bude idonta,haihuwar uwarta haka ta tsinci kanta,da qyar ta samu ta jawo rigarta ta zura,tun a yau ta fara dana sanin auren aljani zul anfaini,ta jima zaune tana tunanin me ya kamata ma tayi,idanunta suka sauka kan wata baqar leda,maiqon da taga tana yi ya sanyar janyota,kaza ce gasashahiya ciki,ture ledar tayi don bata ko burgeta ba,ganin babu sarki sai Allah donko dan tsakin gidan bata ga ya leqota ba ya sanyata miqewa din ta nemi,bandaki,don hatta da jikinta irin doyin jiya da daddare taji yana yi.



Ta fita kanta tsaye tana dingisawa,tun daga nesa ta hango dogon layi babu babba babu uaro kowa yabi,qofar bandakin suke fuskanta kowannansu da botiki wasu da qwarya wasu da kwatanniya cike da ruwa,bata damu ba ta durfafi qofar bandakin tana da niyyar shigewa,ji tayi an fincikota baya cikin wata iriyar dakakkiyar murya
''ina zakije๏ผŸ''waiwayowa tayi don ganin wanda ya mata wannan cin kashin,mace ce saidai idan baka lura da kyau ba zaka iya kiranta da namiji,a murde take,hakanna a tsaye take qyam,idan banda qirjinta da qudundunanniyar sumar kanta babu abinda zai nuna maka cewa ita maca ce,ba shiri ta hadiye tsiwarta da ta qunso ta sanyaya muryarta don ta fuskanci a banza matar zata dakata
''bandaki zan shiga''wata iriyar ashar da duk duniyancin zahariyya bata taba jin irinsa ba matar ta qundumo kana ta dora
''dan uwarku duka wadan nan da kika gani a gun ba mutane bane,duba har da yaran da,basu wuce shekara biyar ba kowa sai yabi layi,saike wata gundumemiyarki da ke zaki wani taho gandan gandan wai ke zaki shiga bandaki,to sai ki shiga mu gani''inji matar tana muzurai.


Ran zahariyya ya baci,tana ganin kamar ita za'a yiwa haka,tsaki ta ja kana ta juya karo na biyu da niyyar shiga bandakin,bata kai qa ida nufinta ba taji an fincikota an watsar take ta samu masauki cikin tabo da dagwalin dake kwance gaban bandakin,cikin tashin hankali ta dago don ganin wanda ya mata wanann danyan aikin
wata figigiyar matashiyace wadda gaba daya jikinta idan banda fata da jijiya babu komai,sai uban qashi a fuska,kallo daya zaka mata ka tabbatar cewa yunwa ta samu gindin zama a jikinta,tsoro da kunya suka hanata cewa komai haka ta miqe tsamo tsamo ta koma dakinta,dariya taji sun rude da ita muryoyi daban daban babu dadin ji yaransu da manyansu,wani baqinciki da bacin rai take ji ya shaqe,duk yadda takeji da rashin arziqi amma wai har yau za'a samu mai taka ta๏ผŸ,malam kawai take jira ta sauje masa kwanson tsiya,sam bazaiyiwu ta zauna cikin irin wannan qasqancin ba,ai neman kudi ba hauka bane,kuma ita ba matarsa bace bare ta shiga sahun irin rayuwarsu.

๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Kamar kowanne maraice da suke qare shi gaban qoramar bayan gari yauma haka ne,saidai yau kam akwai banbanci domin,kwanaki uku kenan suke wasan buya da mero,koda wasa taqi haduwa da maryam saboda tsoro da kunyarta,sau daya da safe maryam ta fito ta tadda meron zaune bakin rijiya ta zubawa qofar dakin su ido suka hada udo,kallon da maryam ta yi mata yasa ta miqewa cikib hanzari da kame kame ta hau yin wanke wanken da dama shi zatayi ta zauna zaman kallon dakin,idan ta zo da safe ta yiwa inna wuro aikace aikacenta a gurguje take barin gidan duk da yadda har yanzu zuciyarta taqi yadda ta rabu da abdallah,batajin zata iya ci gaba da rashin ganinshin.


Material ne ajikinta mai santsi milk ne da adon manyan fulawoyi ash colour,dinkin bubane da ya saukar mata har qasa tayi rolling har zuwa kafadarta da mayafi cotting ruwan madara,yadine tissue a jikin abdallah light blue dinkin boda gajeriyae riga iya gwiwa,ba qaramin kyau yayi ba cikin yammacin,wani lokacin maryam kanyi mamakin yadda fatar abdallahn ke qara kyau tamkar ba cikin qauye yake ba,ta alaqanta hakan da yadda weather din garin ke da kyau da ni'imtarwa.


Kamar kowanne lokaci garin a lullume yake,a wadace da korayen tsirrai,a hankali suke tafiya,jinta take kamar wadda kasala zata lullube,shiru suke tafiya hakanan a hankali,abdallah na sake nazarin qauyan,shiru hanyar tasu take yau fiye da kullum,babu gilmawar mutane kamar ragowar kwanakin,duk dama ba hanya ce ta jama'a ba.



''haqiqa Allah mai hikima ne baiwa da kuma cikakken iko,babu shakka Allah ne kadai masanin sirruka da boyayyun al'amura,wannan garin ya amshi sunansu babu ko makawa,a koda yaushe na wayi gari,cikin qauyen nan nakanyi duba izuwa tarin ni'imomi da baiwa da Allah ya musu,hakan yake sake sakani,cikin sakankancewa da iko da isa ta ubangiji,nake sake nisa da nutsuwa gun miqa qoqon bara ta agareshi,tabbas na yadda babu makawa Allah na ji kuma akwai lokacin da zaya bude min gaba daya qofofin ni'imarshi''shiru maryam tayi na saurarensa
sassanyar ajiyar zuciya ya saki shima yana kin kasalar na saukar masa.


''maryam''ya kira sunanta cikin wani irinsalo da ya qarasa kashe mata jikinta gaba daya,hakanan taji bakinta ya mata nauyi ta gaza amsawa
''maryam.....sai yausge zaki bawa zuciyarki dama ta bayyaba abinda yake cikinta๏ผŸ,sai yaushe zaki bata dama yaushe zaki bata 'yancinta๏ผŸ''
gaba daya sai ya qarasa qulle mata duk wasu qofofin qwaqwalwarta ta shiga kai kawon nazarin maganarsa,bilhaqqi da gaskiya ya sake tubudata cikin wani duhun ne,meke cikin zuciyar tata da yake tambayarta ta bata 'yancinta a kansa๏ผŸ,bata kai ga warware qullin ba ya sake jefo mata wata tambayar.


''maryam,sona ne maqare cikin zuciyarki,so na ne yake hanaki sukuni duk lokacin da na kadaice da mero,so na ke saka ki cikin yanayi na kasala da mutuwar jiki,me yasa zaki takureshi a muhalli guda ki hana shi fitowa inda ya dace๏ผŸ''ya waiwayo yana dubanta tare da qoqarin kallon qwayar idanunta
bugun zuciyar ta ya sake yawa,tayi gaggaqar cire qwayar idonta daga cikin tasa ta maidata gefe wani abu na taba zuciyarta,me yasa abdallah ke mata haka ne,ko yaushe rauninta yake son gani kuma bata jin zata barshi ya gani din
zuciyarta ke qarfafarta ta qaryata batun abdallah,cikin muryar da ka mata dogon nazaei qwaya tal zaka gano akwai wani abu mai qarfi cikinta tace
''kada ka soma bari zuciyarka ta dora ka akan keken bera,don ko digo babu wani abu mai kama da so cikin zuciyata game da kai,ko ka manta abdur rahim ta so shi kuma ta aura a zatonta๏ผŸ,saboda haka babu so tsakanina da kai kaima ka sani''.


dan guntun murmushi ya saki sannan yace
''irin wanna karsashi da jurumtar na maryamu na dade ina ganinshi cikin idonta tun tana a matsayin kukun abdallah a gidan mami,saidai wani abu guda da bata sani ba,ta dade da makarowa,tun ranar farko da taga abdallah ta fada tarkon sonsa,duk da jarumtar boyewar da take amm is too late don abdallah ba a iya boyemiahi ire iren wanann abubuwan,don ya saba ganinshi cikin idanun 'yan mata daban daban,amma fa wani abu daya da maryam bata sani ba,abdallah shima ya fara sonta ne tun lokacin da ta fara sonshi,sunso juna a rana guda lokaci guda a guri guda a kuma sakanni guda''.


Gaba daya ilahirin jikinta ya kama rawa har ta gaza ci gaba da rura wheelchair din,wanne tonin silili abdallah ke son yi mata,saidai sam na zata bashi dama ya riga zare mata duk wata laka da qwarin gwiwa dake jikinta ba yadda yaga dama,don haka ta ttara sauran dukkan wani karsashi nata
''idanunka da zuciyarka sun maka qarya abdallah,ban taba sonka ban taba sha'awar na qaunaceka ba ko ka manta da bakinka kasha fadan ba kowacce mace ta dace da kaiba๏ผŸbako wacce mace ta cancanci ka sota ba,nasan naso abdur rahim amma ba kai ba kuma bana sonka,bana sonka bana......''
idanunshi a rufe suke yana jin saukar maganarta,sukan zuciyarshi take da wani abu mai kaifi ba tare data sani ba,duk da zuciyarshi na qaryata duk wata magana dake fitowa daga bakinta saidai bai son jin furucin sam,sannu kuma kishin abdur rahim mai qarfi ya fara shigarsa,sanadiyyan katsewar maganarta shine fincikota da yayi ta dire a gabanshi,rashin qwarin jikinta ya sanyata zubewa a gaban nashi.


Murmushi ne kan fuskarsa wanda ko yaushe ke fidda sigar kyawunshi
''banyarda baki son abdallah ba sabida na jima da ci miki alwashin sai kin soni,alhmdlh ban zama looser ba ni nayi nasara,but now ina mai qara tabbatar miki sai son abdallah ya ninku cikin zuciyarki fiye da da,i promise''ya fada yana miqa mata qaramin yatsanshi alamar su qulla,ba tare da jinkiri ba ta miqa masa suka qulle kamar yadda yara keyi,shi ya dagata da kanshi ya kade mata jikinta kana suka ci gaba da tafiya.


suna tafe yana murmushi,raguwar kuzarin jikinta kawai ya isheshi amsar tambayarsa,sai da suka qara mintinan da suke yi akan nada kafin su isa ta ajjiyeshi inda ta saba,qur'aninsa ya ciro gaban aljihunsa don kwana biyu da suke tahowa su kadai da alqur'ani yake tahowa,yana yin tilawa kuwa mai yawa kafin su koma,wucewa tayi gurin da ta saba zama kamar ko yaushe ta zauna.


ta daga idonta take ta hango shanun su baffa da kwana biyu bata ganinsu,murmushi ta saki don sun kwana biyin basu gaisa ba,ciro qafafunta tayi ta karkade jikinta bayan ta miqe ta maida takalmanta ta fara tafiya,daga idonshi yayi a hankali ya bita da kallo,yana lura da yadda ko yaushe idan sunzo idonta na tsallaken rafin bai san meke burgeta ba a gun.


kamar ko wanne lokaci daga baya ta tsaya bata shiga cikin shanun ba sai baffa ne ya isketa,tamkar wadanda suka ahekara tare haka suka dinga hirarsu,ta tambaya kwana biyu bata ganin fitowarsu yace eh mai gida ke fidda zaka cikin dabbobin nasa to sai jiya ya kammala shi yasa sai yau suka fito
ba tare dafa tambaya ba ya ciro wani mazubi mai kyau ya fara tatsar mata madara
''mai gida yace duk sanda ka zo a baka,yana ta tambayarka ma''tayi murmushi tana fadin
''Allah sarki na gode kuwa baffa''ta miqa hannu ta karbi mazubin tayi bismillah ta fara sha
''kisha ahankali idan bai isa ba ma sai a qara miki''taji muryar daga gefanta na gada,ta daga kanta ahankali,mahmud ne yauma cikin shigar kufta,murmushi ta danyi kana ta ja baya tana fadin
''ina wuni''ya amsa mata da ''lafiya lau,tun rannan kuma sai kika bace abunki ban sake ganinki ba''
'๏ผŸeh wlh ta amsa masa a taqaice tana rufe mazubin ta miqawa baffa
''baffa gashi na gode ni zan wuce''
''a'ah,jeki da shi meramu,duk lokacib da kike so kizo da shi sai a dinga zuba miki ciki''godiya ta masa don abun ya mata kyau,dan mazubi ne maikyau irin na fulani
''zaki gudu kenan kam irin na rannan๏ผŸ''ya tambayeta yana dan dada sauri don su jera tare
''a'ah,bani kadaice bace na fada maka,da yayana kuma mijina muke tare''ta fada cikin rashin sakin jiki
dariya ya saka
''wai ni zaki yiwa wayo,don kin fuskanci na yaba ko๏ผŸ''
kai ta girgiza idanunta a qasa
''da gaake ni matar aure ce''
''nima mijin aure ne''ya maida mata amsa cikin maida maganar wasa wasa,ganin da gaske yaqi yarda din ya sata tsayawa da tafiyar da takeyi don sun,kusa da inda abdallah yake bayan ta rage fara'ar fuskarta sosai
''idan baka amince ba muje ka ganshi da idonka,amma ka fara yin gaba tukun yana nan zaune akan kujera idan yaso sai na biyo bayanka''.


kafada ya daga kana yace
''is ok,bari nayi gaban,amma da sharadin idan qarya kike zaki amshi soyayyata''
kada kai tayi kawai ba tare da tace komai ba idanunta suka sauka kan abdallah zaune kan kujerarsa a gabansu,mamakin yadda ya iya kawo kanshi tayi,sai ta dubi kujerar wasu abubuwa guda biyu ta gani gefe da gefe bata taba kula da su ba wanda bisa alamu da su ya tuqa kanshi.


Kallo daya ta yiwa idonshi bata sake marmarun kuma kallonsu ba,ya kalleta ya kalki mahmud sai taga ya danna wani abu,rivearse kujerar tayi da kanta kana ta saita hanya ya soma tafiya sannu a hankali
''ko baki fada ba nasan shine mijinkin,kiyi haquri don Allah,wlh harga Allah ban dauka da gaske kike ba''mahmud ya fada cike da damuwa
a gagguce ta gyada kai bata samu cewa komai ba ta biyo bayan abdallah.





*mrs muhammd ce*๐Ÿ‘‘




๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ
[2:00pm, 9/29/2017] Huguma๐Ÿ‘‘: [11:46am, 9/29/2017] Huguma๐Ÿ‘‘: ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*


5โƒฃ0โƒฃ


๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘‚๐Ÿพ๐Ÿ‘…


*_shin ka/kina lura kuwa 'yar uwa๏ผŸ,kin fuskanci kuwa yadda kwanaki keta zura gudu abinsu๏ผŸ,kinsan me hakan yake nufi a gareka/ki๏ผŸ,tamkar gaya miki suke kifa shirya kina kusantar kabari ne,ki shirya kina kisantar ajalinki,ki shirya kwanakin ki na duniya da aka diba miki na qarewa_*

*_daure ki aikata mai kyau don ki tarar da me kyau,babu yadda za'ayi ki shuka qaya kice inibi kikeson cira,duk fitar numfashinki daya daidai yake da kusantowar ajalinki,yadda idan second guda ta kubuce miki har abda bazata dawo ba haka ajalinki idan yazo daidai da qiftawar ido Allah bazai barki cikin duniya ba,to don me zaki batawa kanki lokaci kan cutar da wani๏ผŸ,don me zaki damu kanki da ababan duniya,duniyar da take wulaqantacciya๏ผŸ,duniyar da Allah yace bata kai qima da darajar da girma daidai da na fukafukin sauro a gurinsa ba,saboda me zaki shagala kin manta ki daina tuna mutuwa,bayan kina da yaqinin tabbas/lallai/babu makawa sai kin muyu kamar yadda kika ga wasu sun mace kema wataran haka ne,komai qararre ne banda zatin Allah,ya ubangijin kowa da komai ya mai rahama da tausayin bayinsa kasa muyi kyakkyawan qarshe,mu mutu muna kan tafarkinka na gaskiya_*
*ALHAMDULILLAHI ALA NI'IMATUL ISLAM*


*_kafin na fara shafin nan ya zama dole na gaisar na kuma miqa godiya ta ga masu aiko da saqonninsu gareni,saqonninku sun ishemin,ina muku fatan alkhairi naji dadi qwarai da addu'o'inku,abinda kuketa roqamin na alkhairi ina fatan Allah ya sanyaku ciki kuma_*

*ummi jos*
*mrs tafida*
*haulat m badamasi*
*Aisha kanyah*
*ummu zainab*
*sis rabi'a*
*jammy jammy zbi group*
*zahra hari zbi group*
*na gode Allah ya bar zumunci da qauna*๐Ÿ™๐Ÿฝ









Cikin kwana goma sha hudu da zahariyya tayi cikin gidan ba qaramar dandana kudarta tayi ba,sauqinta daya malam na hayi ya tsawatarwa iyalin nasa bayan bore da

Please Login or Register in order to submit comment