Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka Fara sani bada magani basa taba barin acuci Wanda nake da niyyar taimaka mishi Dan Haka suka kasa cutar daku




Sannan inason firdausi ki gafarceni kiyafemin tabbas Baki ganeniba Amma ni naganeki dukyadda Kika canza Dole zanganeki domin ke gudan jini nane



Firdausi nine mahaifin ki



Umma firdausi tamike zumbur ta Isa gareshi tabbas tumfitowasu take kallon shi saidai tarasa gane inda tasanshi ashe mahaifin tane Wanda suka rabu tun tana shekara bakwai tunda yasaki mahaifiyar ta


Cikin kuka umma firdausi baba Kaine dama baba ashe zansake ganinka baba ina mama na



Hakimi yayi kuka Mai cin rai yace mahaifiyar ki Allah yayi Mata rasuwa da jimawa


Ainan sabuwar kuka takaru sarki suna tabata hakuri Dole tahakura dama tunda mahaifiyar ta tabar gidan akabarta agurin matar uba muguwa shikenan karshen rabuwarsu da mahaifiyar ta Allah sarki umma firdausi Allah yajikan ta




Anan ka jakanta



Yusrah tace Abba kasan yadda akayi na yanki gashin wa innan azzaluma



Alokacin danake acting amtsayin ameena dakaina NASA musu maganin bacci a ruwa nabasu suka Sha Basu saniba



Aikuwa bacci yadaukesu agurin Dan Haka na yanki gashinsu Haka buhari yaso yaudarata naki amincewa Koda yaje shagon askin nace musu gashin shi nakeso nabasu kudi Mai yawa sukabani


Haka watarana waziri zaitafi gurin bokanshi nayi saurin rigashi tafiya muka hadu ahanya alokacin nacanza duffata


Wani fuskan robber tafitardashi tasaka tace waziri katuna wannan fuskar



Waziri yimike Yana nunata da yatsa Yace kece



Yusrah tayi.murmushi tace kwarai kuwa akan iyayena zan iya sadaukar da Raina Dan Haka Koda naji abinda boka yafada maka nace tosaina Zama maka ciwon Ido



Anan yamusu bayanin komi



Duk matanen dakin sun jinjina ma yusra da kaifin basirar ta


Yusrah tace Abba yanzu wuka da nama agurinki


*******


Mata biyun nan.dasuke gurin tunda akafara magana Basu tofa uffan Sai yanzu wata tsihuwar Mata tace tabbas waziri mugune Haka diyarshi da ya Haifa



Tabbas yaso kasheni Amma Allah baibashi sa.a ba Allah yasa inada Nissan kwana



Yakasheni ban mutuba har ansani akabari nasoma motsi da rabon zan rayu



Wasu mutane sukaga motsina suka dawo suka tononi



Wani kauye suka nufa Dani anan suka kula dani harnasamu lafiya


Koda naji abinda ke faruwa agarin bauchi nace lokaci yayi danza tona mishi asiri Ashe asirin shi yariga ya tonu



Aikuwa guri yadauki salati


Waziri ya kece da dariya yace munafukan banza da wofi kunason kuci mutuncinmu ko to munfi karfinku yakara fashewa da dariya abu kamar wasa hauka fujajan



Maimuna kuwa ai tuni tasoma barkewa da zawo akayi waje da ita


Former Mai martaba yayi addu.a yace ko Haka akabarku kunshiga uku



Bazamu dauki wani matakiba zakuje kuhadu da Allah



Anan maimartaba yamusu ardu.a yass musu albarka
[7/5, 9:17 AM] UMMY KHALEEL: *******


Mai martaba dakanshi yasa aka gyara ma hakimi wajen Zama da matar waziri


Hakama Aisha yanemi iyayenta yayi musu godiya tare da Fahad abokin Yaya sabeer


Khaleel yace gaskiya Aisha Kinsha Mari duk aka tuntsure da dariya


Sarki Yusuf farin ciki ba a misaltawa agurinshi Haka Mai martaba



Yau ranace tafarin ciki Dan Haka yashirya walima Yan uwa da abokan arzi


Bayan anwatse daga walima Mai martaba hada family meeting


Meeting din akan hada auren yusrah da sabeer saikuma


Aisha da Fahad dama already sun hada kansu suna son junansu


Koda Mai martaba yanemi hakan aikuwa iyayen Aisha Dana Fahad sun amince Dan Haka akasa biki Nan da sati biyu



Mai martaba shiyayi komai Kama daga gidan da zasu zauna har kayan da akasa adaki tabbas komi saidai muce alhamdulillah


Aranar da aka daura aure aka hada kayatacciyar walima wanda yatara dumbin jama.a nagida Dana waje



Gida daya suke saidai kowa dansashin sa Amma komai nagidan iri dayane


Karkaso kaga umman sarki Yusuf Baki harkunne bama ita kadaiba duk Wanda yake kaunar su yusrah to aranar suna Taya su farin ciki


Anyi biki anwatse angwaye anrakasu dakin amaren su


Kowanne ya umurci amarya datatsh sugabatar da sallah nafila


Nidai daganan nafita nabarsu Dan banson shiga dakin amarya lol


Da safe yusrah ce na hango kwance jiki. Saber Sai faman shagwaba takeyi shikuwa Sai biye Mata yake



Rayuwarsu gwanin Sha awa


Bayan wata shida sabeer yafito daga dakinshi yusrah ma binshi take tana faman zumbura Baki yace waike lafiya kike ta zumburo Baki Haka



Yusrah tafashe da kuka tace ninace bazanje karatu wajeba anan gida zanyi karatuna



Sabeer yayi murmushi yakara manneta jikinshi yace is okey zanmema miki admission anan ko yusra da murna tace yawwa nawan ta kwace daga jikinshi taruga shima yabi bayanta



Hakama Aisha da sabeer soyayya sukeyo Mai tsafta Mai cike da so da kaunar juna



Bayan shekara wasu Yara na hango mace Dana miji akalla zasu Kai shekara biyar kansu daya suna wasa


Jiyayi namijin yace sister bazakizo kibani ball dinaba yace bros saidai kazo ka kwace da gudu suka kwasa zuwa inda iyayen nasu suke wato Hassan da Hussaina kenan yaran yusrah


Daga kan da zanyi Naga wata beautiful baby itama tazo tatada jikin yusrah ta tana gwaranci yarinyar batafi shekara dayaba cikin nabiyu wato firdausi kenan diyar Aisha Wanda taci sunan umma firdausi ana kiranta danyasmi



Duka da Hassan da Hussaina sukazo suka dauketa suna murna Dan suna matukar kaunar kanwar tasu


*********



Akwana atashi yusrah burinta yacika tazama babbar lawyer Wanda ake alfahari da ita Nan gida da waje



Aisha da Fahad ne suka jero suna takawa cikin so da kaunar juna yusrah da sabeer ganinsu yasa suma suka tashi Dan taryar su yaransu biyu da Yasmin suka zo dagudu suka rungume iyayen nasu




Tammat bihamdul lah



Anan nakawo karsnen wannan short story Mai dauke da wasu darusa Wanda Mai karatu ya fahimta


Nagode masouana da bani lokacinku da kukayi Allah yaba kauna


My besty ummu afan inamiki fatan alheri keda mummy jidda baiwar Allah tare da ummu haneef Allah yabaki lafiya



Sai kinji Ni dauke da sabon novel Dina Mai zuwa




Taku har kullum UMMY KHALEEL



ummykhaleeel@gmail.com
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment