Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana bukatar addu.a inaganin ba ita kadai bace


Mai martaba yace Allah yakyauta tashi muje

Suna fita maimuna takece da dariyar mugunta tace kada kuka gani shekara da shekaru ina fama da yadda zanyi Naga bayanku to yanzu nasamu dama da diyarku zanyi amfani na cutardaku na kashe ku vanzaye


**********


Yusrah ce zaune kan dinning tana cin abincin Fahad yashigo da sallama ko ta amsa mishi


Harkasa ya tsuguna yace gaidata Taki kula shi umma maimuna tafito daga dakinta tace lafiya kaikuma



Fahad yace nazo karbar wankine


Maimuna ta Dalla mishi harara tace fita anan angaya maka ina maimaita kayane dubeshi kazami kawai



Yusrah tace malam kafita inbahakaba zanyi amai


Maimuna tace fita GEEMBIYA Yar sarki tana magana


Da sauri Fahad yafice yabar falon


Wulakanci yariga yasaba danhKa baidameshi ba.

**********

Tunda yusrah tazo batakara taka kafarta inda iyayenta sukeba Dan Haka take cin karenta babu babbaka yanzu tasake da waziri Dan ana iya shawarin yadda za akashe iyayenta agabanta itama tana Basu goyon baya 100% danhaka suka Kara janta ajiki.


Dan yanzu yusrah tazama mara mutunci tazama Mai matukar wulakanta mutane Dan yanzu Bata da abokin da yawuce buhari


Shi buhari ma sonta yakeyi da za a amince mishi da an aura mishi ita Koda shike tunyanzu sunfara saye zuciyarta ma yasan zata amince mishi saidai fa shikanshi yasan ba ajinshi bace ita

Dan tafi karfinshi



Yusrah dakanta takira mummy tasanar Mata halin da ake ciki aikuwa mummy cikin tashin hankali tanemi izini agurin mijinta


Aikuwa da yaso hanata Dan yasan tabbas idan ya Isa gurin bazataji dadin ganin yadda mahaifiyar nata suke ba


Washe gari karfe 9 nasafe a bauchi yayi Mata aikuwa tayi sa a khaleel da Abdul suna tare Dan Haka sukaje dakko ta



Koda suka iso abinda yafara Bata mamaki canzawa dakin mahaifiyar nata batakara tsinkewaba Saida taga firdausi


Aikuwa kuka yaci karfinta Mai martaba yace barta kawai tayi kukan tasamu saukin want abun


Saida tayi Mai isarta sannan tayi shiru


Sarki Yusuf ne yafada Mata komi tundaga farko har kawo yanzu


Mummy tace lallai yusrah inhar abinda tazama kenan to tabbas tacika butulu Kuma ba zanyafe mataba



Mummy da khaleel har dakin maimuna suka nufa

Yusrah tanajin muryarsu tayi kunnen uwar shegu


Maimuna dake wanka a toilet tanajinsu danhaka Taki fitowa


Khaleel ne yace mummy gadakin yusra muje musameta aciki



Aikuwa suna shiga suka tarar makansu abinda yakusan fin karfinsu yusrah ne zaune bakin gado buhari namata tausan kafa aikuwa khaleel Yana Isa wajen yadauketa dammari


Cikin Kara tace Allah ya Isa mugu azzalumi


Mummy sake Baki tayi tana kallon ta tace yusrah kece


Yusra taturo Baki tace dama Baki sanni bace taja dogon tsuka


Mummy hankalinta yatashi khaleel yadakko wani igiyar charge zai tabketa mummy tace kana tabata banyafe makaba


Cikin bacin Rai mummy tajuya khaleel ma yabiye Mata



Koda suka dawo suka sanar danmai martaba abinda ke faruwa Mai martaba yace indai yusra ce kadanfa kuka gani addu.a kawai zamuyi Mata.

********


Satin mummy daya Mai martaba yace takoma gidan mijinta Amma Sam Taki saidai anyi SA.a mijin ya amince Mata tayi jinyar mahaifiyar ta.


Mummy Kam yanzu ibadan yakara karuwa kullum acikin addu.ar neman tsari takeyi dakuma addu.ar Allah yaba mahaifiyar ta lafiya da mayar kwninta



Yusrah ce zaune akan wani kujerar alfarma tana cin Apple kuyanginta da maimuna tanem Mata suna faman yimata fifita



Wayartace tasoma ringing kuyangarta dansauri tadauka takai Mata kunnenta


Tana magana kamar bazatayi ba wato buhari Rabin rantane yakirata Yana tambayar inda take tafada mishi


Aikuwa saigashi a lambun cikin gidan dauke da irin manyan taban masu kudi.


Yusrah fa yanzu life yabude saidai duk iya shegenta Bata yadda tayi wasan banza da buhari domin tana matukar mutunta mutuncin ta


Wazirine yadoko sallam dakin diyar tashi Mai zaigani yusra ce kwance kafar umma.maimuna tana cin chewing gum


Murmushin mugunta yasaki


More comment

More typing


Luv u all


ummykhaleeel@gmail.com
[7/1, 9:27 PM] UMMY KHALEEL: BISMILLAH HIRRAHMANIR RAHIM
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·
πŸ”·
GEEMBIYA YUSRAH (PRENCESS YUSRAH)

WRITTEN BY UMMY KHALEEL

13------14

I dedicated this page to UMMU Farhan comment naki nasani nishadi ina matukar yinki sosai da sosai suksanda zan karanta comment naki nishadi nakeji na daban Allah yabar zumunci yaraya Mana yaranmu bisa farkin. Tsira ameen

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·

Yusrah cikin ladabi da biyayya tagaishe da waziri




Da fara.a ya amsa yace GEEMBIYA YUSRAH Yar sarkin sarakuna kina tare da umman Taki ce


Yusrah tace eh baba ya aiki


Waziri yace lafiya Amma ya jikin ummanki


Yusrah tabata Rai tace nifa ga umma na Nan tanuna maimuna


Waziri yayi murmushi yace aiba asake matuwo suna yusrah


Yusrah tace ninasake just live this aside change the chapter


Maimuna har cikin ranta taji Dadi kwarai Dan tasan yanzu asiri yaci yusrah


Saura umman sarki Yusuf da Mai martaba



Yusrah tace umma na gaskiya inason a nemo min kunyangu Dan Nika gaskiya sarautar nakeji sonake nazama kasai tacciyar mace kamar sauran yaran sarakuna


Maimuna tace indai wannan ne babu matsala karki damu

*******


Aikuwa bayan kwana biyu saiga yanmata manya masu jida kansu aka kawo ma yusrah amatsayin kuyanginta


Yusrah tayaba dasu Dan Haka yanzu takeji dakanta take ganin itama din watace acikin jama.a



Mummy abin Yana cimata tuwo a kwarya idan tatuna cewa yusrah Mai tarbiya itace tazama mara tarbiya Haka Sai taci kukanta tagode Allah


Sallah Kam mummy tanayi sosai sannan akwaita da kokarin nafila Dan Haka tatsaya da addu.a sosai Akan iyayen nata.



Yusrah ce zaune a lambun gidan kuyanginta suna faman Mata fifita dukda iskan bishiyoyin dake kadawa Amma baisa yusrah takallesu tace subari ba saifamar cin ayaba takeyi tana kasaita



Wayartace tasoma ringing ko kallon gurin batayiba kuyangar tace tadauka takara Mata a kunne daidai lokacin Mai jinyar umma firdausi tazo wucewa tagabansu


Yusrah tamata wani banzan kallo tamata alamar tazo dasauri Amina ta iso tace gani ranki shidade


Yusrah tace inason daga yau karnasake ganin ki kingifta tagabana danbanson ganin ki


Amina tace angama ranki shidade tashi kibarnan inji yusrah

Da sauri tatashi tabar gurin takoma inda tafito



Ganin halin da yusrah takoma yasa sabeer shiga tashin hankali Dan Haka shima yadukufa da addu.a Allah yashiryeta


Sarki Yusuf da Mai martaba suna matukar mamakin halin da yusrah tashiga
Yanzuma ko sunhadu a hanya Bata gaiahesu hargarama mahaifin nata takan gaishe shi



Yaukam Mai martaba dakanshi yatura fahad yakira yusrah Dan yayi Mata wa azi


Aikuwa Fahad nazuwa yasameta tana zaune akan wani lallausan kafet tana taunar chewing gum



Harara yadaka mishi da gwala gwalan idonta tuni yadurkushe kasa yace ranki shidade Mai martaba Yana son ganinki



Yusrah ta harareshi tabasar tace kaje kace yazo yasameni banajin zan iya fita



Cikin tashin hankali yace gaskiya ranki shidade bazan iya sanar dashi wannan amsarba yatashi yafice yabar gurin



Wani dogon tsuka taja tare da mikewa dan zuwa Kiran Mai martaba



Koda ta Isa falonshi tasameshi guri tanema tazauna


Kallon shi take up and down tace gani ina sauri


Mai martaba yace yusra Allah ya shiryeki


Yusrah tace kagafa niba abinda yakawoni kenanba mekakirani kacemin



Mai martaba Kama Baki yayi Yana gani ikon Allah


Sarki Yusuf ne yashigo ranshi abace Dan yaji dukwani abinda tafada Dan Haka yace yusrah meke damunki



Yusrah taja dabaya tace Abba kabarni kawai nifa banson takuri tasakai tafice adakin tabarsu su biyu


Kowannen su Saida yazubda hawaye Dan ganin canzawar yusrah



Mai martaba yace muci gaba da addu.a Allah yabasu lafiya yusra tana.bukatar addu.a


Sarki Yusuf yace Allah yabata lafiya

********


Waziri ne tafe cikin wani kasurgumin daji Wanda za aiya Kira da dajin Kare kukanka babu Mai kawo doki


Dajine Wanda ya tanadi miyagun namun dawa



Tafe yake shikanshi yagaji yasan baitaba tafiya irin wannan guriba saidai dilene yanzu yazo Dan yanason karbar sarautar garin bauchi


Bokan da zaije gurinshi ance aikinshi kamar yankar wukane.dan Haka yasa akanema mishi inda yake Dan Haka yazo



Yayi tafiya Mai Nisa baihango ko mutum daya ahanya ba kaiko kukan tsuntsuaye vakaji sosai sabida dajin.cike yake da abin tsoro


Saida ya iso wani gurin katon dutse yahango wata Mata zaune agurin dutsen


Tsoro da fargaba suka dirar mishi Yana tunanin Anya mutum ce kuwa Dan yaji ance bokan Nan Mata basa zuwa gurinshi Sai maza sadaukakku to Amma meyakawo mace Nan toko tafiyace takawota hanyar


Yana cikin tunani har yakaraso inda take


Barkanki dai yafada tadago Kai tace yawwa barka


Yace baiwar Allah meyakawo ki wajen nan


Matar tace kaima meyakawo ka yayi murmushi yace naman duniya


Itama matar tace Nima neman duniya yakawoni gurin Nan Dan Haka mujera tare mukara wajen boka


Cikin jindadi yace kekuwa wani bukatace takawoki wannan wajen matar tace idanmun karasa wajen zakaji yace shikenan Allah yasa mukarasa lafiya



Matar tace daina Kiran Allah Dan inda zakaje bakasan Allah ba dakasanshi dabazakazo ba danhaka karkasake



Suna cikin tafiya suka hadu da wani kasurgumin kumurci dasauri matar taja baya tace kashemana wannan macijin



Waziri yace bazan iyaba barshi kawai muwuce


Aikuwa Haka suka wuce abinsu



Suna Isa inda bokan yake sukaji wani hajijiya da iska tataso



Matar cikin tsoro tasoma ja da baya yace karki matsa Koda da taku dayane Dan yanzu zamu maidaki tsuntsuwa



Cikin tsoro tace to natsaya shikuwa waziri yace nikumafa




Dariya yaji an kyakyata yace zamu maidaka tabarmar sarkin da kakawo Mana aiki akanshi



Cikin tsoro yatsaya cak



Wani iska sukaga ya tsaya cak agabansu



Yace dukkurufe idanunku


Gabaki dayansu suka rufe


Ba afi minti dayaba yace kubude idanunku


Aikuwa ganin mummunanar halittar bokan saura kiris matar tasaki ihu



Yakece da dariya yace ke jarumace tunda Kika iya isowa Nan gurina ihunki bazaimin komiba



Yakalli waziri yace Kai meke tafe dakai ina neman Karin bayani Amma kafin Nan barin indanyi sharhi akan abinda ketafe dakai




Boka yace sokake Mai martaba da sarki Mai ci ayanzu akashesu dakuma diyarshi ajiluyamata Kai tazama Sai abinda kukayi da ita ko



Waziri yace hakane



Boka yace to abune Mai sauki Amma samun abunda za ahada maganin dashi shike da wahala Amma shima Mai saukine

Waziri yace inajinka ya boka



Boka ya kalleshi ya kece da dariya yace yarsa yusrah tazama taku danhaka da ita zakuyi amfani Dan ganin kukawar da wa innan mutane


Sabida Haka zanfada maka abinda make bukata kakawo Mana kokuma mubaka kaje kahada dakanka




Waziri yace ina sauraranka boka


Boka yace inason asamomin gashin fulani firdausi na kanta da gashin sarki Yusuf ahadasu waje daya hakama na umman Yusuf da Mai martaba Suma ahadasu waje daya


Sannan kasamu buhari yaron da kuke rikewa amatsayin danku wato Maci amanar sarki kubashi yaje yaba yusrah takona


Dazarar takona gashin da hanunta to iyayenta sungama.rayuwa kenan adoron kasa



Waziri yace ga maganin bawahala Amma samun gashinsu shine Mai wahala



Wani garin magani yabasu yace ga wannan dashi za ahada da gashin nasu akone



Bayan yagama da waziri yace ke bazan amsa bukatarkiba yanzu Amma kikoma Nan da wata daya kidawo.dan zanyi tafiya bazan dawoba Sai Nan da wata daya zanje yawon bincike



Aikuwa matar bataso hakaba Amma bayadda ta iya Dan Taji anacewa bokan mabaya magana biyu Dan Haka tamike tafara tafiya cikin rashin kwarin gwiwa.


Tofa Wai shin waziri zaiyi nasaran aikata wannan bakin muguntar kuwa



Kubiyoni UMMY KHALEEL danjin yadda zata Kaya



Luv you all members of GEEMBIYA YUSRAH



Much love to your sweet comment


Meet me at

ummykhaleeel@gmail.com
[7/3, 4:52 PM] UMMY KHALEEL: BISMILLAH HIRRAHMANIR RAHIM
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·
πŸ”·
GEEMBIYA YUSRAH (PRENCESS YUSRAH)

WRITTEN BY UMMY KHALEEL

15-------20

Page dedicated to all members of GEEMBIYA YUSRAH fans group in matukar JINDADIN kulawarku ga novel Dina in alfahari da comment naku tnx u so much

Keep it up


URS UMMY KHALEELπŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Aminace Mai kula da umma firdausi zaune Sai rusar kuka takeyi forhaka kawai take matukar tausaya ma umma firdausi da mahaifiyar sarki Yusuf


Lallai lamarin gidan abin dubawane


Fahad ne rike da katon almakashi dake yanka fulwar gidan


Ya iso gareta yace meyasa kike Kuma


Amina tace wallahi tausayin wannan bayin Allah nakeji wallahi akwai tuggu da aka kulla da ace inada yadda zanyi danayi Dan su samu lafiya


Fahad yanemi guri ya zauna yace komai zaiyi daidai kikwantar da hankalinki



Amina ta kalleshi da mamaki tace kamar Yaya



Fahad yace zanyi wani Abu akai

Ameena tace shikenan Allah yataimaka suka yace ameen



Fahad ne ketafaman aikin banruwanshi ma flowers din gida


Jinmagana kasa kasane yasashi Kara nutsuwa domin jin maganar



Wazirene yake waya yace ai boko wancan maganin anriga anyi Kuma Naga nasara Dan yazu da matar da mahaifiyar maimartaba duksuna kwance gaba dayansu babu lafiya Rai ahanun Allah

Sabida Haka yanzu bana tasu sonake Naga karshen wa innan mutanen wato maimartaba da danshi


Dan Haka sainaga bayansu




*******


Wanenen waziri?


Waziri shine amintaccen sarkin Abdul azeez tun suna Yara tunkafin Mai martaba yasan zaikarbi mulki


Suntaso tare cikinso da kaunar juna


Saidai shi waziri tunsuna yaro yake da mugun ciwon Nan maicinye ayyukan Lada wato hassada


Asalin sunan waziri kasimu


Dan alokacin suna Yara baya tabason yaga Wanda suke tare dashi sunwuce shi akomi dazaran kuwa kasamu Abu shibai samuba saiyasa kyashi da hassada



Saidai duk hassadar tashi baya taba nunawa yanamaka musamman Abdul azeez dayake tunyana yaro Allah yadaura mishi farin jinin jama.a danhaka bayan rasuwar mahaifin shi aka nadashi sarauta



Aikuwa waziri kasim kamar yakashe kanshi Dan bakin ciki saidai Bai nunama abokin nashiba yazage anyi bikin sarauta dashi kaikace babu komi azuciyar shi



Matar Abdul azeez kawace ko ince aminiya ga matar waziri


Waziri da matarshi Allah yabasu aihuwar Diya mace aikuwa waziri bakinciki kamar yakash kanshi tunbaya nunawa haryafito fili yasanar da matarshi hauwa.u shifa yafison a Haifa mishi namiji


Jinhka hauwa.u tasanar da aminiyarta halin da ake ciki


Kawarta HAJARA tabata shawar wari akan tayi hakuri Insha Allah zata haifi namijin



Aranar suna akasa ma yarinya maimuna Wanda tunda tataso halinta irin na ubantane sak babu abinda tabari nashi



Watarana maimuna suna wasa da yaran makotan su want yaro yazo wucewa yace ke Yar wazirin sarki tsohonki yadawo daga fada ne


Aikuwa maimuna tace kuturin uba ubanane kake Kira wazirin sarki


Aiko tabishi yagudu


Koda mahaifin nata yadawo tasanar mishi yayi bakin ciki kwarai dagaske Dan Haka yakudiri niyyar Sai yayi mulki kotahalin Kaka



Aikuwa maimuna jinbayanin baban nata yasata murna


Hauwa u tace gaskiya abinda kikeyi baidaceba kaidai kasan basarauta kagadaba bare kace saikayi mulki kuma ai maimartaba Yana da magaji kaga bakai ba mulki



Maimuna tace wallahi kedai mama akwai hassada kema idan babana yazama sarki kinzama sarauniya nikuma GEEMBIYA Dan wallahi na tsani yarshin Nan sadeeya


Waziri yayi dariya yace ina alfahari da samunki amatsayin Diya da farko nayi bakin cikin aihuwar Diya mace Amma yanzu Naga alama ke Zaki sharemin hawaye na Zaki ciremin kitse awuta



Maimuna tace kaidai kwantar da hankali babana.


Hauwa.u tace Allah ya shiryeku nidai baruwana azancenku waziri yace wannan damuwarki Yar hassada kawai



Watarana hauwa.u tana dakinta Taji waziri Yana waya batasan Koda wayeba Amma taji Yana cewa kawai kuje kusheke shi kawai yafi banason awayi gari yatashi dannumfashi



Tunda taji wannan maganar hankalinta yatashi saidai batafitoba gudun karya zargi Taji abinda yake Fadi


Jitayi yace kutabbata kinkasheshi Dan Dole nahau sarauta banson ganin sarki Abdul azeez da yaronshi araye



Cikin tashin hankali tafito tace mekake nufi akashe Mai martaba da danshi maisuka maka akan mulki


Waziri yajuyo ranshi bace yace ke bakisanni bako kafin tayi magana ya bigeta tafadi kan tiles jaryayya aikuwa yadakko wani zani yadaureta tana tafaman mutsutstaukuwa akasa so yake yakasheta



Saida yaga Bata motsi kafin yadauke yakaita kan gadon ta yakwantar kamar Mai bacci



Da asuban fari yafita yalekata yakira jama.a gidanshi ya sanar musu rasuwar matarshi


Aikuwa maimuna tayi kuka Mai martaba shiyayi Mata salla


Akakaita gidanta nagaskiya


*********

Bayan.kwana arba.in maimuna tazama itakadai agidan babanta mahaifiyar su sadeeya taso abata maimuna tarike Amma waziri yaki domin akwai wani buri dayake son yacimma kanshi tayi tayi Amma yace yafison su zauna tare da diyartashi domin tana debe mishi kewa Dole tahakura tabarmishi diyarshi



Aikuwa koda maimuna takara wayo Sai dabi.un sadeeya yasoma Bata haushi mutane kaman ba yayan sarautaba komai suce addini danhKa sukaci gaba da kulle kullen makircin su da mahaifin ta hartakai maimuna takai aure yanemi sarki dayabashi damar hada maimuna da Yusuf aure dukda Yusuf kwata kwata shekara biyu yaba maimuna bawani girmanta yayi ba


Tunda dukyadda yaso yakashe sarki hakan baiyuwuba


*********


Cigaban labari


Fahad ne yasami Mai martaba yanason yaje garinsu duba iyayenshi


Maimartaba yabashi izinin zuwa tare da bashi guzuri Mai yasa Fahad yaki karba Amma Mai martaba yace kasan dai niba abokin wasanka bane sabida Haka kakarba Fahad yakarba yayi godiya



Sabeer ne zaune da mummy suna tattaunawa yadda zasuyi kokarin nema ma bayin Allah Nan magani



Yusrah tashigo cikin falo Amina tagani tana fama da umma firdausi Kashi tayi tana goge Mata



Yusrah ta yatsina fuska zata fita mummy tace Baki da hankali ko yusrah yakamata ki farga kikoma daidai kikula da iyayenki daidai lokacin ameena tagama idonta cike da hawaye sabeer ne yayi sallama yashigo falon shima hankalinshi atashe


Amina tana zubda kwalla tabar dakin dasauri sabeer yamaida kallonshi ga yusrah yace ke kifadawo hankalinki


Yusrah tace kaga sabeer dakata banson dogon surutu kakula


Baki yasaki Yana kallonta yace sabeer tofa



Hanu yadaga zaikai mata Mari yusrah tace kana tabani wallahi zanrama Danni ba jakar ka bace



Mummy tace rabu da ita Allah yashiryeta tace ameen


Ganin zasu dameta tace mummy nifa zanfita inason nakoma karatu fa Dan ankai one week dakomawa school danhaka Nazo sallaman ku



Sabeer yace fice kibamu guri tunkafin Raina yabaci na tattakaki anan


Tace banyi dakaiba malam


Mummy tace Allah yashiryeki yusrah

********


Aranar da yusrah zata koma karatu ko abban ta Bata sallama ba bare tadubo taga jikin umman ta yayake



Rike take da posa ahanunta tafito nenab taga waziri suna magana da umma maimuna harzata wuce saikuma ta juyo tace Amma dai lafiya ko


Umma maimuna tace hmmm inafa lafiya GEEMBIYA YUSRAH



Yusra tanemi guri tazauna tace meke faruwa



Maimuna Tama yusrah bayanin cewa ai ansamo maganin da za ayi ma ummanki da umman Mai martaba magani Dan susamu lafiya



Yusrah tatashi tace what's

Kunsan dai mutanen Nan basa gabana yanzu ko suwarke ko karsu warke nothing concerned me so me I don't have care on them



Umma maimuna murna yakamata lallai asiri yayi tasiri akan yusrah sungode Allah



Umma maimuna tace karkiyi Haka yusrah akwai abinda nakeso ki fahimta koda sunsamu lafiya bazaki koma gurinsuba Kuma bamasu takura Miki sabida Haka ki amince kikarbi maganin Nan ki aiwatar da aikinki Dan samun lafiyan su



Yusrah Taki amincewa Saida buhari dake gefe tunda ake magana bauce komiba Sai yanzu yace haba sweet heart ki amince kiyi wannan aikin domin ance Sai diyar da suka Haifa ta cikinsu ce zata yi wannan aikin Dan asiri aka musu



Yusrah tace ok nothing but I would do Dan kuntakura nine



Duksuka ji Dadi yusrah tace yanzu kunsa nakoma baya akaratuna yaushe kukeson afara aikin



Waziri yace ko yaune Dan zanyi alfahari dake yusrah



Yusrah tace no Sai Nan da.wata daya domin zanje school akwana abubuwan danakeson gabatarwa Amma karku damu Nan da four weeka I would be with you



Bahaka sukasoba Amma sun amince Dan gani suke yanzu komai yazo karshe




Aminace zaune agaban sarki Yusuf saifaman ravsar kuka takeyi yayi yayi tafada mishi meke damunta Amma Taki


Ganin yusrah yasa tamike dagudu zata bargurin yusra tace zonan karki barnan


Amina tadawo tazauna Sai faman sheshshekar kuka takeyi yusrah tanemi guri tazauna tace Abba varka da warhaka



Cikin mamaki yakalleta yace yusrah mekika dauki duniya


Yusra tayi murmushi tace Abba gurin zama yace dakyau



Yusrah tace Abba zankoma makaranta ina bukatar kudi agurinka yanzu zanwuce



Abba yace yusrah Baki da hankali ne kina ganin halin da ake ciki acikin gidan Nan Amma Baki damuba kiduba kiga mahaifiyar ki yadda take Rai ahanun Allah amma kice Zaki tafi kibarta awannan halin Baki tunanin gobe yusrah


Wannan baiwar Allah itace kedawainiya da mahaifiyar ki itada Yaya sadeeya gatawa mahaifiyar duksu suke dawainiya da ita nabiyata kudi Taki karba tace tanayi Dan Allah ne itama kenan daba aifanta sukayiba tana kula dasu bare ke



Yusrah tace Abba idan nadawo zankula dasu Ni yanzu karatu NASA agaba


Abba ranshi abace yace to bazan bada ko sisiba kije kinemi masu yimiki inasu uwartaki da Kika canza



Tatashi zata tafi Amina takama kafan Abba tace kayi hakuri kavata Allah yabata sa.a abban



Yace Amina yarinyarnan ta lalace dasauri Amina tace karkafadi Haka Abba zata shiryu Insha Allah addu.a zaka Mata



Yusra Kama tabar gurin tatafi abinta

**********

Amina ita taci gaba da kula da umma firdausi itakuma mummy tana kula da mahaifiyar ta daddy baya sati baizoba Allah sarki mutumin arziki



Sabeer Kam tuni yafara Jin kaunar Amina acikin ranshi Dan tana birgeshi sosai yadda take kula da umma kamar diyar cikinta Dan Haka soyayya yakeyi Mata a boye



Mummy tace waini yaushe su Abdul zasu dawone da khaleel sabeer yace sunkusa dawowa Insha Allah tace Allah yadawo dasu lafiya



Akwana atashi satin yusrah biyu da tafiya ba abinda yadameta



Yanzu burinta tadawo ta aiwatar da aikinda su waziri sukasata


Aminace yau kawai jitayi tana danjin nishadi cikin lambun cikin gidan ta Isa sabeer ta hango Yana ways itakuwa kokari take ta balli wani mangoro dukda tsayinta Amma takasa balla Sai tsalle takeyi



Har sabeer yagama wayar yajuyo ya kalleta tana tafaman tsalle Dan ballab mangwaro


Shikuwa sabeer binta yake da kallon sha.awa yarinyar tana birgeshi sosai inama ta amince adaura musu aure saidai yasan zaiyi wuya ta amince da auren shi


Ahankali yakaro cikin tafiyarshi ta manyan maza masu jida kansu aikuwa daidai lokacin Amina tayi want tsalle Wanda saura kiris tafadi Sai jinta tayi ajikin mutum anrungumeta



Dasauri tasoma kwatar jikinta sabeer Kam yamanta duniyar dayake Dan lokaci guda yaji wani irin feeling Nan da Nan yasaketa yakori shaidan Amina Kam kunya ya addabeta zata juya kenan yariko hanunta yace koma kizauna muyi magana Amina taruga da gudu yabita da kallo murmushi yasake kawai jinshi yake cikin nishadi

*******

Sabeer dakanshi yasami daddy yasanar mihsi Dan Allah yanason anema minshi auren ameena Dan shi Yana sonta


Daddy yayi mamaki kwarai yace yusrah fa sabeer yace God forbid I can't marry her wallahi



Daddy yace baka Isaba sabeer yarinyar da tuntana karama kace kanaaonta Sai yanzu zakace baka sonta


Akan wani dalili sabeer yace daddy yusrah has changed now she don't have the qualities of being a wife to innocent man



Daddy yace shot up I don't want to hear this word yusrah she's your blood anything she be you must married her



Sabeer ya saukar da kanshi kasa yace understand me dad



Daddy yatashi yabar wurin Dan sabeer yabata mishi Rai yasan idan har sabeer ya auri yusrah Dole shizaiga darajarta akan wani daba asanshuba dukda halin yusrah data canza



Sabeer ne kwance akan lafiyayyen gadon shi Yana tunano childhood life dinsu da yusrah but now she was changed all her qualities behaviors to negative



Yau yusrah tacika sati hudu da tafiyarta Dan Haka tun safe su waziri suka dameta dakira tace tana hanya su saurareta Nan da awa buyu




Khaleel ne zaune agaban umma saifaman kuka yakeyi kamar want karamin yaro umma Kam ba um ba um um Bata bacci kullum Ido abude


Tunda khaleel yadawo shike dawainiya da umma firdausi shida Amina sabida Haka shakuwa Mai kyau yashiga tsakanin su


Saidai Koda khaleel yaji halin da yusrah tacanza yace zaiyi maganinta atunaninshi zaihukuntata saidai baisan yusrah tawuce tunaninshi ba



Gidane yacika da mutane maimuna tatara kawayenta Yan bariki irinta za akarbi GEEMBIYA YUSRAH


Abba Kam yanzu bashi da bakin magana komai yagani nashi Ido



Khaleel ne zaune a lambun cikin gidan Yana zaune yaga inda za afara


Aikuwa motocine masu masifar kyau Lambar motar dauke take da GEEMBIYA YUSRAH 1 har zuwa 10 wato motocin ta kenan


Cikin damuwa yace bari dai yaga Mai zai faru Abdul Rashid yagani yafito daga cikin motar as body guard din yusrah yabude Mata kofa khaleel yace what's Yaya Abdul security for this young girl


Mikewa yayi tsaye ganin wacce tafito a motar yaji gabanshi yafadi Ras Ras



Kamar zai karaso inda suke saikuma yafasa yatsaya Yana kallon ikon Allah



Koda mutanen kowa yafito yusrah tace karkowa yabiyota su tsaya idan tana da bukatar ganin wani daga cikinsu zata nemesu awaya


Danhaka kowanne yakoma mota tana isowa bakin kofa sukayi Karo da khaleel kallon mamaki takemai tace oh Young Man daga ina



Khaleel Rai vace yace nonsense are you senseless


Yusrah takalleshi ta Dalla mishi harara zata shige yayi saukrin fincikota saidai lokacin Abdul ya iso gurin yace bros she deserved it just live her yusrah taja dogon tsuka tayi wucewarta




Keep tsaye dakin umma maimuna tanufa da sallamar ta


Amsa Mata sukayi cike da mamaki


Tofa kubiyoni abaya yusrah tadawo


Shin me zai faru



More comment


More typing



ummykhaleeel@gmail.com
[7/3, 6:25 PM] UMMY KHALEEL: BISMILLAH HIRRAHMANIR RAHIM
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·
πŸ”·
GEEMBIYA YUSRAH (PRENCESS YUSRAH)

WRITTEN BY UMMY KHALEEL

15-------20
β˜€ FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATION β˜€


β˜€ FCWAβ˜€

Home of qualities and trusted writers of the nation





Page dedicated to all members of GEEMBIYA YUSRAH fans group in

Please Login or Register in order to submit comment