Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya gurin

Ameena tace Abba inason nayi magana dakai


Abba yace to ameena inajinki


Ameena tace sirri ne Abba


Sarki Yusuf yamike tsaye yanuna Mata hanya akan suje



Adakin shi suka tsaya


Ameena tadurkusa harkasa tace ranka shidade inason Amin izinin zuwa gida duba iyayena



Maimartaba yace shine damuwanki


Ameena tace eh yace shikenan karki damu zansa akaiki



Ameena tace kayi hakuri Abba nafison tafiya dakaina


Baimata musu VA ya amince saidai yabata kudi masu yawa takarba dan yin guzuri



Koda tasami Fahad tasanar mishi tafiyanta Amma bawai garin nasu zatajeba kawai zataje tanemi bishiyar dalbejiya Wanda za asami kauchi



Aikuwa tare suka shirya tafiyar tun cikin dare Fahad ya shirya Haka ma ameena


Mummy tayi kewar ameena Dan yarinyar tana debe Mata kewa saita tuna lokaci yusrah tana yusrah Mai biyayya hawaye yazubo Mata


Mummy tace Dan Allah ameena karki Dade kidawo Kinga zuwanki yasa firdausi tadansami dama dama akan da



Ameena tace kimin addu.a mummy Allah yabani sa ar samo abinda nake nema



Mummy tace ameen ameena zanrika yimiki addu.a



Ameena takoma da kallonta kan umma Mai zata gani hawaye ne ke zuba a idanunta


Ameena ta rungumeta tace umma Zaki samu lafiya insha Allah wands suka Miki Haka keda umman Mai martaba asirin kansu zaikona ameena kuka yaci karfinta



Mummy kallon ikon Allah kawai takeyi wanna shakuwarsu tayi yawa Aiko itatahaifi ameena dolene tayi alfahari da ita amatsayin yarinya


Mummy mamakin hawayen idon umma yakamata first tunda tafara ciwo kenan


Ameena tashare mata hawayen da hanunta tamike Dan tafiya Dan batason umma ta sanyayar Mata da gwiwa


Misalin karfe Tara nasafe ameena tayi Shirin tafiya

********

Yusrah ce zaune adakin ummanta tana Mata hira dukda dai tasan umman nata ba amsawa zatayi ba


Tana hawaye tace umma kinkusa warkewa saidai nikam bazaki sameni amatsayin diya ba nariga nazama yarinyar umma maimuna da waziri



Khaleel dake falonshi yanajinta yafito a harzuke yace kitashi kifice adakin Nan yusrah kafin nabata Miki Rai


Yusrah tadago Kai takalleshi tace mamanka ko mamana


Khaleel ya Dalla Mata harara Wanda yasa hanjin cikinta kadawa tamike zata fita


Hartakai bakin kifa yakira sunanta yusrah


Tajuyo takalleshi yace karnasake ganinki adakin Nan


Yusrah tafice batare da tace komiba


******

Ameena ce da Fahad suke tafiya a acikin motar haya



Ameena takalli Fahad tace to Wai yanzu ina zamu Fara dosane


Fahad yace akwai wani kauye anan hanyar bauchi Wai shi katsinawa muje wannan kauyen akwai daji agabasnhi nasan bazamu rasa samun itaciyar ba



Ameena tace shikenan Allah yasa mudace


Fahad yace Wai ya akayi kikasan kauche ne



Ameena tace Hira naji waziri da umma maimuna sunayi lokacin nafito daga dakin maimuna nagama shara naji Yana cewa ai maimuna wannan ciwo nasu fulani firdausi babu Wanda yasan maganinshi saimu


Kinga kenan bazasu taba samun lafiyaba kenan


Shine maimuna tace ammafa yakamata kasanar Dani maganin Dan savuda Nan gaba ko rayuwa zata canza


Shine waziri yayi murmushi yace Mata maganin ciwon ba Mai wahala vane iyaka anemo itacen kauchi Wanda akasaro Bai busheba aba yusrah taba iyayen nata susha tashafa musu da dakanta Dan duk asirin da sukayi Babu Mai warwareshi Sai da sa hanun yusrah acikin maganin kafin komai ya karye


Dan Haka Haka suke murna yusrah tariga tazama tasu sunsan ko sunbata bazata basuba



Haka asirin dasukaje sukayi yusrah itace zatayi komi akai harsukai zuwa ga mutuwar su


Fahad yace to yanzu yakike ganin zamuyi da yusrah


Ameena tace karka damu kabarmin ahanuna yace shikenan



Sun Isa katsinawa sunsami hakimin kauyen suka sanar mishi abinda ke tafe dasu



Hakimi yace karku damu ai kauci baida wahalar samu Dan Yana magunguna da dama


Fahad yace Yanzu a tawani guri zamu Sami kauchin


Hakimi yace za asamu Amma Sai Nan da Rana ita jiya sabida ranar ne kasuwa Kuma masu kawo sassake suna kawowa su sayar Dan abin Yana da matukar tsada


Ameena tace Yaya Fahad bazan iya jira sati tazagayo ba idan ka amince kawai a nuna Mana bishiyar dazami iya Samu mucire Dan wallahi rayuwar su umma Yana cikin hadari acikin Yan kwanakin Nan


Hakimi yace ke yarinya kinsan bishiyar da za asami kauci Sai kina da guru da laya Dan akwai manyan aljanu akai gurin ba gurin zuwan mace bane Dan ko namiji ma saiwanda yashirya



Ameena tace inhar wannan hanyar itace hanyar ajalina nashirya mudai rokonmu kamana kwatancen bishiyar



Haka kawai hakimi yaji yarinyar ta birgeshi sadaukakkiya kenan ko ba tajeba tanuna jarumta Dan Haka yace muje nakaiku inda bishiyar take ina tare daku


Hakimi yashiga yayi ma iyalonshi sallama aikuww matar ta hau ta dire akan bazata jeba shikuwa hakimi yace baiga abinda zaihanashi zuwaba ai taimako akazo nema



Matar hakimi tace tabdi yaukaine da taimako a lallai fa Abu yayi kyau

Baitsaya yaji abinda zata Kara Fadi ba yace mujenku




Ahanya suna tafiya ameena tace malam Dan Allah ya bishiyar Nan take



Malam yace bishiyace Mai cike da hadari babba Amma Insha Allah bazamu wahalaba


Shiyasa ma itacen ke tsada Babu kasa da dubu dari biyu ahakama busashshe bare kukuma kunce danyen kauchin kukeso


Fahad yace gaskiyane danye mukeso



Suna tafe suna Hira har lokacin sallan azahar tayi suka nemi Dan Rafi sukayi alwala suka gabatar da sallar



Kafin sukaci gaba da tafiya



Sunyi tafiya Mai Nisa ameena taga wani katon maciji cikin wani ciyawa aitasa ihu ta rungume Fahad


Hakimi yace lafiya tanuna mishi inda macijin yake aikuwa sukayi Ido hudu


Hakimi dashike irin mutanen. Da dinnan ne Kuma yaga jiya yaga yau kallo daya yayi ma macijin yagane ba macijin gaskiya bane


Hakimi yace bawan Allah idan turoka akayi kamana hakuri shikuwa Fahad yatsaya kallon ikon Allah ameena Kam takasa sake hada Ido da macijin



Gani kawai sukayi yashige daji abinshi Sai alokacin tadawo hankalinta


Hakimi yace tabbas wannan macijin akwai Wanda yake nema


Ameena tace meyasa kace Haka



Hakeemi yace zanmiki bayani Nan gaba

***********



Sunyi tafiya Mai Nisa suka hangi wani bishiyar dalbejiya aikuwa sukayi sa.a bishiyar tsihuwar bishiya ce



Hakimi yace tabbas wannan bishiyar akwai kauchi saidai yadda za ahau a karyo shine babban matsalar



Ankuwa Fahad da yusrah suka tsaya kawai kallon bishiyar Dan bishiyar kanta abin tsoro ne da fargaba



Fahad yace zanhau insha Allah zan sakko lafiya



Ameena tace Yaya namanta banfada makaba maganin Nan ance yusrah akeso tasamo da kanta idan ba ita ta karyo ba to yazamana hanun macece yataba maganin


Saidai sharadi maganin inhar watace daban tasami maganin tofa bazasu warke kwata kwata ba saidai asamu sassauci kadan



Hakimi yayi murmushi yace kenan ke Zaki hau



Ameena tace inhar hakan zaizama karshen rayuwata zanhau Dan ganin bayin Allah Nan sunsamu lafiya


Fahad Kam jarumtar ameena yake gani shikanshi yayi niyyar hawa Amma maganin Yana da sharruda saidai ko bakomi shima zaihau bishiyar su ballo tare shinma tayaya ameena zata iya hawa wannan bishiyar



Ameena ta dumfari bishiyar addu.oi ne kawai abakinta dakeyi da mamamkinsu sukaga ameena tatsaya cak inda take



Fahad zai Isa gareta tayi saurin juyowa ta kalleshi alamar karya karaso jiyayi kirjinshi yabuga Ras ganin lokaci guda ameena yanayin ta ya sauya shima Sai yakama addu.a kawai hakeemi manaddu.ar yakeyi Dan tabbas ba lallai ameena tadawo da raiba



Aikuwa rsayawan da ameena tayi jitayi ankarade gurin da ihu Amma dukda Haka Bata daina dumfarar wajenba hakeemi da Fahad Basu San abinda ake cikiba Dan Haka sukaci gaba da addu.a



Kubiyoni abaya danjin yadda zata Kaya


Luv you



ummykhaleeel@gmail.com
[7/5, 9:18 AM] UMMY KHALEEL: [7/5, 7:16 AM] UMMY KHALEEL: BISMILLAH HIRRAHMANIR RAHIM
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·πŸ”·
πŸ”·πŸ”·
πŸ”·
GEEMBIYA YUSRAH
(PRENCESS YUSRAH)

WRITTEN BY UMMY KHALEEL

31------40

β˜€ FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATION β˜€

FCWA

β˜€ home of qualities and trusted writers of the nationβ˜€


I dedicated this page to my lovers members of GEEMBIYA YUSRAH include

Sister UMMU AFAN
Firdausi
Halimatu sadiya
Sley PRENCESS
Hajara
Maman 3 babies
Mum eishat
Maryam sunusi senato

Dama Wanda ban Kira sunansu ba masu comment ina matukar alfahari daku Kuna karfafamin gwiwa akan wannan novel din

Naso naba kowacce page Amma Kuma ganin hakan bazai kaiba yasa nayi amfani da wannan dogon page

Allah yasaka muku da alkhairi Wanda ban ambaci sunansu ba Suma Insha Allah next zan ambatosu kuma Allah yasaka muku da alheri

Taku UMMY KHALEELπŸ˜˜πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—

Cikin ikon Allah ameena taso hawa wannan bishiyar Mai cike da tsoro Fahad Kam mamakin ameena yakeji Amma lallai wannan yarinyar tacika sadaukakkiya ace ko tsoro bataji yayi imanin da ace namiji shine makaryin asirin Nan da zaiyi kokarin ganin yayaimaka Mata Amma addu a ma zaikai gareta

Hartakai tsakiyar bishiyar taji kamar ana jijjigata saidai ina zuciyarta tariga tabushe either life or death tasadaukar kawai


Tunda taji bishiyar nanjijjiga tuni tacigaba da addu.a can Kuma taji komi ya tsaya cak kamar daukewar iska



Tundaga lokacin takasa gane a inda take



Fahad da hakimi ganin ameena sukayi tana sakkowa saidai gaba daya yanayinta ya sauya sunkasa gane Mata kamanninta ma sauya sukayi


Sundumfarota tamusu alamar su tsaya Dan Haka sukaja suka tsaya cak


Magana sukaji Amma ba muryar ameena ba Dan Haka sukasoma addu.o I acikin zuciyar su


Gani kawai sukayi tafadi kasa sumammiya gefenta Kuma kauchin da ake bukatane


Tuni farin ciki yarufe Hakimi da Fahad


Karasawa sukayi Dan taimakonta anan suka ga kamannin ameena yadawo



Fahad yasoma Mata addu.a cikin ikon Allah tamike kamar ba abinda ya sameta murmushi tasakar musu


Fahad yataimaka Mata tatashi sukadau hanyar komawa saidai dare yayi sosai


Ameena tana Basu LABARIN abinda yafaru Fahad yamatukar jinjina Mata lallai tacika sadaukakkiya



Sunyi tafiya Mai Nisa hakimi yace gaskiya yarinya kincika Yar halak kema Allah yabaki masu yimiki



Ameena tace ameen baba


Guri suka nema sukayi taimMa suka gabatar da sallar magriba da isha.i dukda dai basusan meye time ba Amma sunsan anyi magriba da Isha Dan Haka suka gabatar



Sai alokacin ameena tasoma Jin yunwa gashi dajin bakomi saima abubuwan tsoro dasuke haduwa dashi lokaci guda ameena tasoma Jin amai



Aikuwa Nan take tasoma kwarara amai Fahad yatsorata yace lafiya ameena



Ameena takama cikinta tana kuka tace cikina kemin ciwo



Wani bishiyar mangoro yagani aikuwa baidamu da abinda zaisameshiba yaje ya Fara tsinko Mata mangoro



Jiyayi kamar wani Abu nataba mishi hanu aikuwa Jan hanunshi danzaiyi yaga wani katon maciji ya harde mishi hanu



Hakimi ya kwalla ma Kira


Cikin sauri hakimi da ameena suka Isa gurin


Ganin abunda yake faruwa hakimi yayi saurin yima macijin magana Dan dama hakimi lokacin kuruciyar shi yayi wasa da macizai Dan Haka yasan macijin gaskiya yasan na akasin Haka



Cikin ikon Allah macijin yace kuntsallake rijiya da baya



Ameena tsoro yacikata danjin maganar maciji mehakan kenufi



Kafi kace wani Abu macijin ya bace bat


Sai alokacin ameena tatuna Wanda tagani a yayin tatiyarsu


Tabbas shine bawaniba


**********


Basu suka iso cikin kauyen katsinawa ba Sai misalin karfe shida na asuba Dan ahanya sukayi sallah



Koda suka iso cikin kauyen suka nemi ruwa suka zuba wannan itaciyar kauchi Dan ance Sai yajika na kwana uku kafin suba marasa lafiyan



Washe gari Fahad da ameena suka shirya komawa garin bauchi gidan sarauta Mai adalci da tafiyar dashi tafarkin addinin musulunci



Gudun Kar again tafiyar su tare take Fahad yace ameena kifara Isa nizannemi wani gurin nazauna gobe Insha Allah zankaraso da safe


Ameena tace shikenan


********


Koda tadawo mummy tayi murnar ganinta hakama Abba da former Mai martaba Haka kawai sukejin kaunar yarinyar acikin ransu


Bayan tahuta ne ameena takira Mai martaba da sarki Yusuf dama mummy


Ameena tamusu bayanin maganin Amma ance Dole Sai yusrah ce zata bada maganin da hanunta domin sauran asirin da ita aka kammala



Sarki da murnar shi yace ameena Allah yamiki albarka barin Kira yusrah tazo ta aiwatar da hakan Allah yasa ta shiryu



Aikuwa da.murnar shi yanemi yusrah dake zaune a lambun gidan tana faman waya



Da murna ya Isa gurin yariko hanunta Kai tsaye dakinshi suka wuce



Koda suka Isa yusrah tana ganin ameena ta Dalla Mata harara tace wallahi Baki Isa namiki wannan aikinba



Dama nagane abinda kike nufi Amma kinci uwar Karya



Yusrah takalli Mai martaba tace agaskiya Abba inhar nice zanba umma da ummanka magani tofa saidai Kar abasu



Mai martaba dakanshi yadaga hanu zaikai Mata Mari



MUMMY tace rabuda ita



Ameena cikin fushi tamike tanufa dakin umma Wanda ayanzu tare suke da umman Mai martaba da umman yusrah


Tana shiga tatura dakin tasa key ta kulle Dan batason abiyota bare ayi yinkurin hanata Basu maganin



Aikuwa kamar tasani ta kulle Mai martaba nakiranta Amma ina Taki kulasu aikuwa umma yusrah tafara bude ma Baki Saida tayi adduo.i sosai kafin tabasu maganin


Mezata gani aikuwa daga umma yusrah har umman Mai martaba sukasoma bige bige



Ameena Sai faman addu.a take tana kuka



Maimartaba yace tabude Amma ina Taki Sai kuka takeyi Fahad ne yashigo gidan


Ganin abinda ke faruwa yasa shi tambayar lafiya


Mai martaba yabashi labarin abindake faruwa


Fahad yace ameena kibude Amma ina kukane yaci karfinta



Jitayi umma da umman Mai martaba suna wani irin ihu Wanda ya karade gurin harsu dake falo suna Jin irin karar dagani karar bana lafiya bane



Anfi kamar minti talatin ahaka kafin gurin yayi tsit



Ameena tanemi guri tazauna tana kuka lallai anzalinci wa innan bayin Allah tabbas kaji tsoron Allah kaji tsoron mutum


Mummy ce tace Dan ameena ki bude aikuwa ameena tace wallahi bazan budeba sainaga umma suntashi lafiya kafin inkuwa kukaki kuka takuramin wallahi zan kashe kaina



Yusrah tace kibude dan Allah natuba


Dukansu suka juyo suna kallon yusra itama sutake kallo



Ameena Kam ganin za atakura Mata yasa tasharesu tacigaba da yin damuwar ta



Abu kamar wasa anfi awa uku ahaka umma ko motsi basayi abin Kuma Sai yafara ba ameena tsoro can Kuma saita tuna ance Sai anmusu magani kamarna kwana uku kafin komai yakona normal Dan Haka hankalinta ya kwanta


Wasa gaske Saida aka Kira sallan azahar kafin ameena tafito sutasamu atsaye cirko cirko



Aikuwa gaba dayansu suka duru cikin dakin


Ameena Kam wucewa tayi abinta

**********

Gani sukayi umma ko motsi basayi Dan Haka suke tsammani toko sun rasune



Yusrah tayi murmushi tace alhamdulillah abinda nakeso yafaru Dan Haka saikuyi murna daga yau cuta takare


Ankuwa khaleel da yajuyo tamanj zabga Mata wani uban Mari Saida taga wuta



Yusrah tayi wani uban Kara wanda yasa umma dagowa can ummanta datasa Kai ajikin ummanta tana kuka


Mummy tace kayi nafarko kayi na karshe yusra addu.a take bukata


Mai martaba ne yasoma tabbatarwa Basu rasuba Dan Haka yayi hamdala kowa yajuyo yamaida hankalinshi kansu daidai Kuma motsin ba sosaiba
[7/5, 8:50 AM] UMMY KHALEEL: Dan Haka hankalinssu yadan kwanta kowa yanufi inda zai nufa Dan gabatar da sallar azahar



Ameena ce zaune a lambun gidan tana tataman saka da warwara taji andafa bayanta wazata gani sabeer ne


Murmushi tasakar mishi tace Yaya sabeer kadawo

Yadaga Kai alamar eh tace sannu da dawowa yaushe kashigo yace dazun Nan ya ayyuka tace alhamdulillah



Bayna kwana uku da faruwar Haka kullum ameena saitaba umma da umman Mai martaba magani


Aranar na ukun ne yusrah tasami umma maimuna da waziri tace kuzo muje yau mukashe mutanen nan agabansu



Waziri yace aidama agabasu zamu Kona gashin su tunda daka magani mukace musu zamuyi



Yusrah takece da dariyar mugunta tace gaskiya Mai martaba kabirgeni wato waziri takira da Mai martaba


Aikuwa jiyayi kanshi ya fasu yace shiyasa nakesonki



Maimuna tace aiyakamata muyi kokari muje dannagaji da ganinsu araye



Waziri yace oh waike yusrah waya fada Miki cewa maganin kashe su Mai martaba ne



Yusrah tayi murmushi tace na yadda daku ku baku yadda daniba



Waziri kunya takamashi yace kimana aikin gafara



Yusrah tace kawucenan mijina to be aikuwa maimuna take Taji wani haushi yanaddabeta yanzu yusrah takusan Zama matar sarki kenan



Buhari yashigo da murna yace ku albishirin ku



Waziri yace goro


Yace Yanzu nafito daga sashin sarki Mata biyun Nan sunmutu kurmus



Waziri yace Kai gaske ko wasa yace muje kugani



Aikuwa suna Isa sukaji gurin haya haya masu kuka nayi masu salati nayi


Mai martaba da sarki Yusuf ba abinda sukeyi Sai salati


Ameena Kam taksa fitowa Mai falo din kuka kawai takeyi Mai cin rai



*********

Falon yacika da mutane haddama Wanda ban sansuba suncika falon Amma anyi anyi da amina tabude dakin adauki gawar danzuwa ayi musu sutura Amma Taki



Ga mutane afalon Mai martaba da sarki Yusuf waziri da maimuna saifaman kukan munafurci sukeyi ga sabeer da Abdul Rashid khaleel mummy dasu daddy hakeemi da Fahad Sai wasu nata biyu ba Wanda yasansu acikin su saidai Babu yusrah acikinsu



Mai martaba yace ameena kiyi ma Allah ki bude dakin Nan



Ameena tace inharkunason nabude muku dakin Nan Sai kun Nemo min yusrah kuma banson kowa yafita adakin Nan sai abban mu shikadai zaije yakira yusrah



Aikuwa Abba jiki na Bari kamar ba sarkiba yamike yafice ya kulle dakin



Kai tsaye motarshi ya hau dakanshi yake driving Karo nafarko da yasoma tuki da kanshi kenan



Kai tsaye sashin maimuna yanufa anan yaga yusrah sanye da katon hijab hanunta rike da wani bakin leda




Yusrah tana ganin Abba tayi saurin Jada baya



Abba ranshi abace yace wuce muje meye ahanunki



Yusrah tace muje inda kakeso muje Abba zanmaka bayani



Aikuwa tana tafe Yana binya abaya



Har gurin motar suka Isa tabude tashiga shima yashiga



Koda suka iso yayi parking yafito yusrah ma tafito yace muje


Da mamakinshi saiyaga tacire hijabinta ta jefar takunce dankwalin kanta ta daura


Abba yace lafiya yusrah tayi murmushi tace muje Abba


********

Aikuwa da sallama suka shigo


MUMMY tace to kibude Mana kofa ameena ga yusrah tazo



Ameena tace yusrah


Yusrah ta amsa na am


Ameena tace alhamdulillah


Tatashi takaraso bakin kofa tabude kofar saidai tace batason kowa ya dumfarota inhar da bude kofar



Dan Haka suka ce sun amince


Aikuwa tana budewa tafito falo takara har inda yusrah take ta Yi murmushi sukayi shaking hand



Aisai kallo yakoma kansu har anmanta da gawa



Yusrah da ameena suka koma tsakiyar dakin inda kowa zai iya kallonsu



Ameena tace Yaya Fahad BISMILLAH Yaya sabeer kaima bisimillah


Aikuwa suka tashi


Mai martaba yace banson rainin hankali

Ameena tacire plastic face din


Mezasuyi aikuwa mutanen dakin suka Mike zumbur especially sarki da Mai martaba mamaki yakamasu Haka


Basu Kara karayaba Saida sukaga yusrah tacire nata plastic face din sabeer ma yacire nashi hakama Fahad



Basu Kara tsinkewa ba Saida suka ga umman sarki Yusuf da umman GEEMBIYA YUSRAH sunfito cikin shiga ta alfarma kamar Basu ke da ciwo ba Wanda akai tafama shekara da shekaru ba



Sarki Yusuf da murna yaje ya rungume su Yana kuka hakama mai martaba tsaban farin ciki khaleel da abdul Kam mamaki yahansu aiwatar da komi


Khaleel yace dama duk wannan abindake faruwa plan ne lallai mutanen Nan sunci abasu award


Mai martaba dakanshi yazaunar Dadi


Wayyo Allah waziri da maimuna da buhari hankalinssu yatashi aituni maimuna zufa yasoma yanko Mata Haka ma waziri da buhari


Waziri yace Allah katsine ma munafukai Amma acikin zuciyar shi

**********

Yusrah ta asali tace Abba na namaka laifi ko mummy Mai martaba duknamuku laifiko


Murmushi suka saksr Mata Mai cike da kauna


Yusrah tazo ta rungume abban ta tana kuka ameena ma kikan takeyi hanunta rike da leda



Sabeer tausayin su yakeji hakama Fahad


Saida yusrah tayi kuka Mai isanta kafin tayi shiru


Tatashi Ido a kumbure yusrah tace waziri da maimuna Allah ya Isa tsakani na daku kuncuce iyayena kuncuci umma na da kakata Allah saiya saka musu Kuma kusani asirinku ya tonu



Dama ance inzaka Gina Ramin mugunta kaginashi daidai Kai Amma kun Gina Wanda yafi karfinku



Yusrah tace aminiyata Miko ladar hanunki



Ansha kasar yusrah wacce tayi amfani da face din yusra tatashi takawo Mata ledan


Yusrah ta zazzago abinda yake ciki layune dakuma Killin leda Mai dauke da gashin da ake bukata



Yusrah takalli abban ta tace Abba wannan gashinkane da na umma Tamika mishi yabude tabbas kuwa hakane mamaki yakamashi


Bai ankaraba yaji takara cewa abban wannan ma gashin Kane Dana matarka shima Tamika mishi


Tunaninsu ya akayi suka samu gashin su



Wani leda tafitar shima gashin ne aciki tace wannan Kuma gashin wa innan azzaluman ne dasuka cutarmin da iyaye



Takalli waziri da maimuna da buhari Wanda gaba daya hankalinssu baya jikinsu



Sannan taciro wani laya da garin magani tace



Abba umma Mai martaba dakuma umman abbanta


Tace wannan maganin da kuke gani anbani ne Akan nayi kokarin na hadashi da gashinku nakone


Idan harna konesu to tabbas kingama Shan iskar duniya


Anyi asirin da ba Mai iya warwareshi Sai Allah sannan Kuma Ni inzama sila


Inhar bani nanemo wa innan maganinva to bayadda za ayi su umma susarke sukoma kamar da



To alhamdulillah Allah yakawo Mana komi cikin sauki



Yusrah taci gaba dacewa Abba inbaku mantaba nataba cemuku zandawo Amma kuyi hakuri da halin da zancanza



Alokacin kawai nafada ne Amma bansan me zan aiwatarba sabida


Watarana nazo hutu natafi ingaishe da wannan makirar matar wato maimuna


Sai naji suna kulle kullen yadda za ayi akasheku Dan wannan tsohon muna fukin ya hau mulki



Koda naji maganar sai hankalina yatashi alokacin kamar zan juya nakoma Amma saina fasa sabida wasu kwararan dalili Wanda Yaya sabeer yake koyar Dani wato tauheed


Danagama saursrsnsu nakoma lambu nazauna nabasu kamar minti 30 kafin nashigo gidan da murna na rungume wannan munafukar matar



Ahaka kullum burina nasan abinyi Amma nakasa sanin komi Dan Haka kullum sainayi salla da addu.oi Akan Allah yakaremin iyayena



Ahaka harlokcin komawata kano yayi nakoma Amma kullum a cikin tunanin ku nake saidai Yaya sabeer yariga yakoyar Dani tauheed Dan Haka nakara amincewa da cewan Babu Wanda ya Isa yacutar da bawa batare da yaddan ubangijiba



Ahaka zucciyata take tafiya kullum Dan Haka nadogara da Allah

Watarana inajin daddy Yana waya Yana tambayar jikin ummana da umman ka Koda natamvayeshi saiyace Wai ummana zazzabi kedamunta Amma da sauki Dan Haka na hakura Amma alokacin kullum acikin muggan mafarkai nake


********

Yusrah taci gaba dacewa tunda nagama secondary nake ta planning yadda zancimma burina gurin ganin nakawar da sharrin da ake son kullawa awannan masarautar Mai tarin albarka


Kai tsaye abokin shawarana nanema wato Yaya sabeer nasanar mishi abinda akeciki


Tare muka zauna muka shirya planning yadda zamu samu motona ma wa innan makiran asiri ta wannan hanyar da na bullo muku



Yusrah tanuna Aisha tace Abba wannan qawa tace wacce mukayi secondary da ita tun daga jss one tasan komi nawa nasan komi nata Dan Haka takuduri niyyar taimaka min da ita Mike shawara hakama Yaya sabeer da amininshi



Dan Haka Koda nsamu makatanta a kasar waje bakaratun yakainiba Yaya sabeer yanema min wani malamin da yakoyar Dani addu.oi da yadda zan fuskanci makiya sukasa gane a irin suffar da nazo musu dashi


Dan Haka namakda hankali na ga abinda naje koya Haka Kuma alhamdulillah nayi sa.a sosai



Innagama wannan training din na dumfaro gida anan nasoma aiwatar da duk Shiri na


Dukwani Abu da kukaga nakeyi dama nariga na tsara shi ko ince muntsara



Abba sabeer tare dashi mukaje neman maganin kauci alokacin da naji munafukin Nan Yana fada ma munafukarnan wato waziri da maimuna


Nanne na umurci Aisha wacce take acting a matsayina takulamin daku



Kuma alhamdulillah tamin yadda nakeso Dan Haka komai namu take tafiya



Haka Yaya sabeer dayasa fuskan abokinshi shiya taimaka gurin wasu abubuwa da dama Haka abokin nashi yajiyo Mana surruka da dama Wanda takai ga yanzu muncinma burinmu



Alhamdulillah Abba komi yayi daidai komi yatafi yadda akeso



Abba dakaina nahau bishiyar dalbejiya Dan ganin iyayenmu sunsamu lafiya



Anan yusrah tasanar dashi yadda tasami bishiya da irin hadarin da tafada



Yusrah tace Abba Koda nayi nisa da Fara hawa bishiyar harnakai tsakiyar wani aljani yace tabbas kincika sadau kakkiya akan iyayenki Dan Haka zan taimakeki


Banganshi ba kawai alokacin naji komi nawa yacanza SAINAJI kamar baniba


Adaidai lokacin da zan karyi itacen Sai naji anbugi hanuna ansake bugu naji zafi natuna cewa iyayena suna wahala Basu mutuba Amma suna Jin jiki Dan Haka nakara Kai hanu sainaji abun laushi aikuwa ina sakkowa bansan yadda hankalinta yayiba



Sai alokacin sabeer wato Fahad alokacin yace gaskiya ne kamanninki suncanza yusrah alokacin da Kika dumfari bishiyar hakama dakika sakko kinyi doguwar Suma kamanninki alokacin suncanza nida wannan bawan Allah wato hakimi mukaitamiki addu.a cikin ikon Allah Kika samu sauki Kika dawo normal yusrah



Hakimi tunda akafara maganar saifaman hawaye yakeyi Dan Wanda aka rasa hawayen meye


Yayi gyaran murya yace tabbas yusrah kinhadu da maciji Haka saber macijin da ya nade maka hanu tabbas ba asalin maciji bane turosu akayi gareku



Yusrah tun alokacin dakuka zo gidana na ji kaunarku araina Dan Haka nakuduri aniyar taimaka muku



Hakimi ya kalli sabeer yace tabbas sabeer kacika Dan halak Dan uwa ga yusrah Dan kayi jarumta kwarai



Hakimi yaci gaba dacewa macijin da kuka gani anturoshi ne Akan yakasheku Amma tafiyata daku bazasu tana iya cutar dakuba domin tun ina yaro mutanen boye kefamn bina tun suna wahalar Dani har

Please Login or Register in order to submit comment