Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadai ɗan ɗago ya kalli Anuwar ɗin ya zuba masa harara ya ɗauke kansa. Sai da suka gama dariyarsu sannan ya sake kallonsa fuska babu wasa. “Kai baka da kunya ko......?” “A'a yayanmu nifa wlhy gaskiya na faɗa, yanzu dan ALLAH little zataji daɗine idan aka haifota ta iskeni babu aure, ita dai ai nasan tanason iske kawunta a dattijonsa ko”. Kai kawai Jay ya girgiza ya sake ɗauke kansa, dan indai shaƙiyancine akazo wajen Anuwar kowa ya shafama kansa lafiya, duk masifarsa kuresa yake shima har yagaza cewa komai.
     Umm-Anum da itama ke dariya yanzun tace, “To ni miye nawa, aiga mai maka auren nan a gabanka” tai maganar tana nuna Jay. Tasowa yay ya tsuguna a gaban Jay ɗin yana wani marairaice fuska. “Yayanmu dan ALLAH ka aurar dani kar a haifi little ina a ƙasa” yay maganar cikin harshen nasara da haɗawa da ƴar hausar daya fara kowa wajen Nabeelah”. Kunnensa Jay ya kama ya murɗa da ƙarfi, aiko a take yahau roƙo daban haƙuri. su Bily kuma namasa dariya.
     Cak ta tsaya daga dariyar tata jin bayanta ya riƙe, ta shiga yamutsa fuska tanason fiskewa amma haka
[2/17, 3:01 AM] +234 703 966 0069: sa. Kallon juna muke cike da shauƙi babu mai ko ƙiftawa, sai da naji bakinsa cikin nawa na dawo hayyacina da sauke nannauyar ajiyar zuciya, son tureaa nake amma yaƙi bada damar hakan, na rinƙa dukan bayansa amma bai barniba saida yayi san ransa sannan ya sakeni ya miƙe yana dariya damin gwalo. “Dama abinda ya kawoka kenan ai” na faɗa iana ɓata fuska kamar zanyi kuka. Gwalo yaymin dai-dai zai fita yace, “Eh naji ɗin”. 
       Fariya sosai nayi ina girgiza kai, na jawo ɗiyata na rungume ina sumbatarta dajin kamar na haɗiyeta na huta dan ɗunbin son da nake mata.

BAYAN WASU SHEKARU.

              Yarane kusan uku keta wasan basket ball a madaidaicin filin wasa dake a cikin wani ƙaton gida mai ɓangarori kusan huɗu. ina tsaye a wajen kusan mintuna huɗu saiga mata da miji sun fito daga ɗayan ɓangare na gidan, ba kowa bane face Anuwar da Nabeelah, suma suna sanye ga j.c. ihu yaran suka fara, biyu na kiran Abbah! Abbah! Abbah. Biyu na kiran Mamma! Mamma! Mamma!! Cikin ɗaga hannu irin na jinjina da ɗokin isowar abokin wasa. Anuwar yaja ƴan team ɗinsa, Little Bee, da ƙaninta na biyu Abdul-aziz suna kiransa (Awwab). Nabeelah kuma taja nata ƴan team, ƙanwar Little bee mai bimata Maryam suna kiranta (Khairiyya) sai yaron su Anuwar ɗin mai sunan Jawaad, suna kiransa (Khalifa). Wasansu suka fara cike da nishaɗi, basufi mintuna talatin da farawarba sukaji horn. Maigadi dake kallonsu daga gate yay saurin zuwa ya buɗe. Farar mota tas ta shigo gidan wadda Bily ke mazaunin driver cikin kayan aiki, Jay na gefenta shima sanye da suit yanata faman danne-danne a laptop.
      Da gudu yaran suka nufi motar suna faɗin, Abie! Miemaa! oyoyo. Bily dake murmushi ta kalli Jay shima ya kalleta, kafin su maida idanunsu ga yaran nasu dake tunkarosu. Awwab da Khairiyya suka nufi sashen da bily take suka buɗe mata, Little Bee da Khalifa kuma Jay suka buɗemawa. A tare suka fito fuskarsu ɗauke da murmushi. Jay ya ɗaga khalifa tare da sumbatar kumatumsa, shima yaron ya sumbaci Jay ɗin yana dariya da faɗin, “Abie i love you”. “I love you too second Jawaad” ya faɗa yana lakace masa hanci, kafin ya duƙa ya sumbaci Little bee ƴar kimanin shekaru goma itama. “Little BeeJay ɗina”. Fuskarta washe da murmushi sak irin na Bily tace, “Sweet Abie na i love you” tai maganar da sumbatar hannunsa itama. Ta matsa jikinsa ya rungumeta ta gefen hannun damarsa, na haggun kuma yana ɗauke da khalifa.
     Acanma dai Awwab da khairiyya suna maƙale da Bily, saida suka gama ɗokin ganinta sannan suka dawo wajen Abie, ya sumbacesu suma a kumatu kamar yanda yayma su Khalifa. Kafin su Anuwar su ƙaraso suna musu barka da dawowa.
     Cikin tsokana bily tace, “Iyayen da basa girma da shiriritar ƴaƴansu”. Dariya Anuwar da Nabeelah sukayi, Jay dake murmushi shima yace, “Karki ja mana yanda muka dawo a gajiyanen yanzu su tara mana ciwon kai suda ƴaƴansu, zomu gudu muje mu hutama ranmu princess”. Cikin dariya Anuwar yace, “Idanma kun gudu binku zamuyi, dan yau a falonka aka haɗa dinner. Idanu Jay ya zaro sosai. sai kuma ya ɓata fuska yana kallon Bily cike da langaɓe kai. “Miemaa kinajifa, nidai ALLAH ban yardaba hutawa zanyi”. Kafin bily ta bada amsa yaran suka shiga ihu da tsalle suna faɗin suma basu yardaba a falon Abie zasuyi dinner yau”.
       Ƙwafa Jay yay yana kallon Nabeelah, “Auta kece kika haɗamin wannan aikin ko, maganar gaskiya ayi hutu na tarkataku ku tafi Saudia wajen Ummuna muma muɗan huce gajiya da matata a gidanga. A waje dambe da ɓarayi a gida dambe da iyayen yara da yaransu”.
    Sosai Nabeelah da Anuwar ke dariya, Nabeelah tace, “ALLAH babu ruwana, Abban Little ne”. “Kai ko?”. Jay ya faɗa yana kama kunnensa. “ALLAH da zafi Yayanmu” Anuwar ya faɗa cikin marairaicewa yana riƙe hannun Jay. Yaran suma duk sai suka marairaice suna faɗin, “Sorry Abie Abbanmu yanajin zafi sosai”.
     Dariya Bily takeyi. Jay dake murmushi ma ya saki kunnen Anuwar ya kama hannun matarsa suka shige dan anfara kiran sallar magrba. Kayansu yaran suka kwasa daga mota tare da tsarabar da aka yo musu sukabi bayansu. Anuwar da Nabeelah ma suka nufi ɓangarensu dansu watsa ruwa  tu fito.✍😭🙏🏻

ALHAMDU
[2/17, 3:02 AM] +234 703 966 0069: LILLAHI ALA KULLI HALIN.

Na godema UBANGIJIN al'arshi daya bani ikon kammala wannan littafi daya jani dogon zango, kuskure. dana tafka a cikinsa ALLAH ka yafeni, abinda nayi dai-dai ALLAH ya haɗamu a ladan daku masoya da mukai tafiyar tare.

Nagode, nagode, nagode irin trillions trillions trillions ɗinan da haɗin kai da ɗunbin soyayyar da kuka nunamin akan wannan littafi. Alkairin ALLAH da rahamarsa su tabbata a gareku a duk inda kuke.

Duk wanda na ɓatama rai a yayin rubuta wannan Littafin ya gafarceni dan ALLAH, nima kuma na yafema duk wanda ya ɓatamin😭🙏🏻😍😍😍😘😘.

inajin kewarku tun yanzu, sai dai kuma nasan insha ALLAH zamu haɗu a ZAFAFA 2021🤗.

Masoya na Telegram, Wattpad, Facebook, WhatsApp dama duk wata manhaja da wannan littafi ya leƙa ina muku fatan alkairi da sake miƙa godiya a gareku.

Zakuga ba'a sake kawo maganar Jazuga da gidan ƴan lesbians ba. Haka rayuwa take, wani yakan shigo rayuwarkane bisa ZAREN ƘADDARA bawai sai kaga wani abu daga gareaaba daga baya, mutane da yawa sukan shigo rayuwarmu su taka rawa, walau alkairi ko sharri, daga baya kuma saisu ɓace mana ɓat komu mu ɓace musu. Alka gafarta mana😭🙏🏻.

Sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR 2021, karku bari a baku labari, dan aumafa sunzo da ɗunbin sabon salo mai birgewa ta musamman, bazance muku komaiba akai sai mun fara sakin ɗanɗanon free pages😋 zaku tabbatar da hakan. Masoya ku garzaya kar a baku labari, dan idan babuku muma babu mu ai😪🚶🏻.

Taku Bilyn Abdull ce🤗.

Insha ALLAH bayan sallah sannan an gama zafafa zamu sake dasa free book mai daɗi😉💃🏻😍😍😍

Ina fatan yanzu kowa ya fahimci ƙaddarar jini a cikin jini da zai zama jini🤗.

Shahudah, Bilkisu, sun haɗu akan son abu guda, Jawaad, wanda kuma ya kasance jininsune su duka. Ga kuma

Ya rabbi ka gafartama iyayenmu damu baki ɗaya🙏🏻😭

      
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment