Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu nasarar cafko wannan mayen idon dake neman saukar masa da gajiya. Karaf kuwa idanunsa suka sauka akanta, shima ƙirjinsa ya motsa alamar harbawar zuciyarsa. Tabbas yaji a ransa itace ke kallonsa, amma a mamakinsa sam idanunta da hankalinta basa kansa, karon farko da miskilancin yarinyarnan ya motsa zuciyarsa, tun ganinsa da ita na farko a airport ya fahimci miskilace ta bugawa a jarida, kasancewar ALLAH ya azurtashi da ilimin karantar hallayyar ɗan adam cikin lokaci ƙanƙani, zuwa yanzu mamakin ganinta yabar ransa, dan ya kula akwai alaƙa tsakaninta da Qaseem.......
      “Hello...hello...” Da Jabeer keta ambatane ya sakashi dawowa hayyacinsa, dan tuni ya saki wayar da suke ya kama sabgar bilkisu, abinda bayayi sam a rayuwarsa (wato shiga abinda bai shafesa ba), yaja siririn tsaki yana murza goshinsa da hannunsa daya ciro daga cikin aljihu.
      Dai-dai lokacin da Bilkisu ta buɗe gaban mota ta shiga ta zauna, dan Mom harta shige baya itama.
         Wani irin harɗaɗɗen numfashi ya sauke har Jabeer na tambayarsa “ko lafiya?”.
      Gutun tsaki yaja yana yanke wayar batare daya bashi amsaba, yakuma jan wani tsakin har sau biyu yana takaicin kansa da shiga hurumin da ba nasaba.

___________________________

      Washe gari ban biyosuba, dan inama barci suka fice, babu wanda yace a tasoni, nima koda na tashi kuku ke sanarmin sun tafi banji komaiba a raina saima daɗi, tunda nasan zuwana bazai ƙara komaiba koya hana, hasalima banason gamuwa da Dodona.
        Bayan na karya ɗaki na koma nai wanka, nai shiri cikin doguwar riga ta atanfa data samu zaunannen ɗinki, bawata kwalliya naiba, nasaka turare sama-sama na fito bayan na yafa ƙarmin gyale.
     Kai tsaye gate na nufa wajen baba maigadi dake zaune shida mai bayin filawar gidan suna hira, suna ganina suka shiga gaisheni cikin girmamawa, sam banason hakan da sukemin, dan kuwa niba kowa bace a gidan face maicin alfarma, sannan duk sun girmeni, baba maigadi ma a haife ya haifeni, shima mai bayin fulawar kobai haifi kamata ba nasan yanada manyan ƴaƴa.....
       “Hajiya fita zakiyine?”.
Baba mai gadi ya katsemin tunanina, kaina na girgiza masa ina murmushi. “A'a baba ba fita zanyiba, hasalima wajenka nazo muyi magana idan ban takura makaba dan ALLAH”.
      Da sauri yace, “Haba wace takura kuma” yay maganar yana miƙewa da sauri, babu jimawa sai gashi da farar kujera, ajiyemin yay gefensu alamar na zauna, mai bayin fulawa kuwa yay mana sallama akan zaije gida yakai cefane.

          Sake gaisawa mukai da baba maigadi, yay min ta'aziyyar rasuwar da akayi, nako amsa masa tare da tambayar lafiyar iyalansa, bayan amsamin da yay muka ɗanyi shiru, tunani nake ta ina zan fara abinda ya kawoni garesa?. Zuwa wasu ƴan mintuna sai dabara ta faɗomin, nai murmushi ina sake maida hankalina ga

reshi da kunna voice recorder dan na samu damar kwashe dukkan abinda zamu tattauna nayi nazari a tsanake a kansu.
       “Uhm... Baba dan ALLAH niko wata tambayace dani?”.
     Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “ALLAH Yasa na sani hajiya”.
     Murmushi naɗan masa, nace, “Insha ALLAHU inada tabbacin kama sani ɗin”.
       Baice komaiba sai hankalinsa daya maido kaina baki ɗaya, nima sai na sake nutsuwa sosai.
       “Baba dan ALLAH ko zaka iya tuna ranar da abinnan ya faru da Amina a gidannan da wanda ba'asan ko waneneba?”.
          A bazata maganar tazo masa, dan haka kawai saiya hau tari babu shiri. A rikice na shiga masa sannu, na jawo ruwan dana fito dashi daga ciki na miƙa masa da sauri bayan na ɓalle murfin, amsa yay har hannunsa na rawa ya kafa goran a baki ya ɓaɓɓaka, saida yasha kusan rabi kafin ya sauke, idanunsa harsun kaɗa sunyi jajur, sai naji tausayinsa ya kamani, koda ya dawo dai-dai shiru nai ban sake masa tambayarba har tsawon wasu mintuna.
      Na sake jeho masa tambayar a karo na biyu, yanzunkam a mamakinawa shiru yay bai tanka minba, sai dai yanata ƴan kalle-kalle tamkar mai tsoron a ganmu ko wani ya jimu. Jin bashi da niyyar bani amsa ya sakani kallonsa, a karo na uku na sake maimaita masa tambayar da sigar kwantar da kai.........
      “Ɗi!! Ɗi!!! Ɗi!!...” mukaji horn ɗin mota daga waje, hakanne ya sakashi tashi da sauri ya nufi gate ɗin, na tabbatar dama hanyar da zai gudu yake nema, sai kawai na samu kaina da ƙura masa idanu ganin yanda har yanzu jikinsa ke mazarin rawa.
        Hancin motar Dad ne ya danno kai cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya ina miƙewa tsaye, saboda tsayawar da driver yayi a saitin da nake zaune, shi kuma Dad ya sauke glass ɗin ɓangarensa yana mani murmushi.
      Nima murmushin nake masa ina miƙewa na nufesa, da hannu yaymin nuni nazo, dole nabi motar da direba yaja zuwa ciki inda zaiyi fakin.

        Tare da Dad muka shige cikin falo yana tambayata miyyasa banbi su Mom ba can gida?, cikin girmamawa na bashi amsa akan sun wucene ina barci lokacin. Nayi zaton zaiyi faɗa, amma sai naji kawai yay ƙaramar dariya. Mun yada zango a falon ƙasa, ya bani Umarnin naje nasa kuku ya haɗa masa abinci mara nauyi yunwa ya keji, ya fita bai karyabane.
      Koda naje kicin ɗin sai ban fitoba na zauna mukayi abu mai sauƙi wa Dad ɗin ni da kuku, dan zuwa yanzunkam Alhmdllh hannuna yay masifar faɗawa akan girki kala-kala na zamani, na gargajiya kuwa dama bani da matsala a kansa, innata tarigada tayi min wannan horon tun ban gama fahimtar muhimmancin girki ga ɗiya mace ba.
      Bayan mun kammala nice da kaina na kawoma Dad, lokacin yana waya, na ɗora tiren bisa tebir ɗin tsakkiyar falon na jasa gabansa, buɗe masa komai nayi tare da tsiyaya masa ruwa a kofi sannan na koma gefe na zauna, a haka ya faracin abincin yana cigaba da wayarsa data jashi tsayin lokaci, sai yazam yanacin abincinne kawai a shiririce. Dan harya kammala wayar baici ko kashi ɗayaba bisa uku, ya ajiye wayar yana maido hankalinsa gareni, “Taso muci mana ɗiyata”.
      “Lah Dad nakane, ni ban daɗema da karyawaba fa”.
    Cike da kulawa yacemin, “Da gaske?”.
      Na langaɓe kai gefe ina ɗagawa alamar eh. Murmushi yayi ya cigaba dacin abincinasa yana mani hirar data bani mamaki, dan kuwa akan kasuwancinsane ya ɗakkomin hira, yana faɗamin alkairi da kullum kamfaninsa ke samu da yanda kuɗaɗe ke shigo masa babu ƙaƙƙautawa. Banda masha ALLAH da ALLAH ya ƙara sanya albarka babu abinda nake iya cewa, danni kam dai ban fahimci dalilin mani labarinba, tunda a ganina ai sirrinsane wannan, ko a cikin ƴaƴa kuwa a ganina sai wanda ka aminta da amanarsa.
    Kamar kuwa ya karanci mike raina, sai cewa yay, “Kinji inata baki labarin abinda bai shafekiba ko?”.
     Murmushin yaƙe naɗanyi ina gyaɗa kaina, shima ya murmusa yana mai kai cokalin romon farfesun daya ɗobo a bakinsa.
        “Karkiji komai a ranki Bilkisu, na yarda da kene kawai shiyyasa, dan na fahimci keɗin yarinyace mai hankali da tarin nutsuwa, sannan sam baki da yawan surutu, waɗanan halayyar taki na ƙaramin ƙaunarki sosai”.
     Murmushi yanzunkam nayi har haƙorana na bayyana

, nace, “Nagode Daddy”.
     Ƙaramar dariya yay yana miƙewa bayan ya ajiye kofin da yasha ruwa, “Kinga bara naje naɗan kwanta na huta, zuwa yamma saimu tafi gidan rasuwar muma”.
    Kaina na jinjina masa kawai, dan nima tuni nake buƙatar keɓancewa, inason yin nazari akan halinda mai gadi ya shiga akan tambayar danai masa ɗazun kafin zuwansu Dad daya gaza amsa mani.

         Koda Yammar bamuje ko inaba, dan banga Dad ba sai bayan la'asar lokacin da yah Salim ke dawowa gidan. Harare-hararen da yaketayine ya sakani tashi na barmusu falon na koma ɗaki.

★..★...:::::...★..★

           Washe gari litinin kowa yasan tushen aiki, hakanne ya sakani shiri tun a farar safiya, lokacin dana fito babu wanda ya fito a mutanen gidan, tea kawai nasha driver ya ɗaukeni zuwa station ɗinmu kamar yanda a yanzu da Yah Qaseem bayanan kullum shine ke kaini.

        Nayi mamakin rashin ganinsa yauma a office, bayan nasan ya dawo, daga baya sai nayi tunanin kodan dai rasuwarcan ne da bansan minene alaƙarsa da mamacinba, dan har yanzu ina mamakin ganinsa a gidan su Mom ɗin, dukda wani sashe na zuciyata na rayamin shima ɗan uwansune ƙila sunje gaisuwane.
    Daga haka ban daɗaba ban ragaba har lokacin tashi yayi muka tashi.
         Tare muka tafi a motar Ummie, dan ita Dadyn ta ya bata mota ƴar ƙarama tun fara aikinmu, tun tafiyar Yah Qaseem sai yazam direba na kawoni da safe, ita kuma mutafi tare idan mun tashi sai ta ajiyeni gida ta wuce nasu gidan.
       Kiran da Nazifa tai minne a waya muke amsawa tare da Ummie dake tuƙi, dan a amsa kuwwa (Hans free)na saka wayar yanda itama zataji, munzo dai-dai shataletalen (roundabout) ɗin da zamu ɗauki hanyar gida danja (traffic light) ta tsaidamu, sai kwasar dariyar labarin da Nazifa ke bamu mukeyi.
     Kusan minti goma muna a haka, saina fahimci sam motocin basa motsawa ma, buɗe motar nai na leƙa, hayaniyar mutane sosai ke tashi, dan motocin dake tahowa a dukkannin titinan huɗune suka cure waje guda, watama ta mugun bugama wata, sun saka jami'i mai bada hannu a tsakkiya sunata zabga masa masifa. Mamaki ya sake kamani, nadai dawo na zauna, mun cigaba da hira kusan ta minti ɗaya nadai sake jin abin bai zaunamin a raiba, dan wannan go slow ɗin yafi kama da wanda aka haɗa da gangan, gashi motoci sai sake taruwa sukeyi titin na sake cinkushewa. Ummie na bama Nazifa amsa ni kuma na maida kallona ga mirror ɗin waje, har yanzu dai babu alamar motsin motocin a dukkanin titinan huɗu da suka raba kansu, sai naɗan kalli Ummie ina yamutsa fuska, dan na lura har yanzu ita bama ta fahimci halin da ake cikiba.
       “Ummie akwai matsalafa, tabbas wannan cinkosan  haɗashi akayi akan sani”.
       Da sauri ta katse wayar tana cema Nazifa muna zuwa.
      Kashe motar tai duk muka fita a hanzarce, tabbas an haɗashine da gayya, hakkanne ya sakamu fara ƴan dube-dube muna kutsawa tsakanin motoci domin san isa ainahin wajen da danjar take.
     Gaba ɗaya wajen ya hargitse, sai hayaniya ke sake tashi, duk yanda mai bada hannun keson dai-daita komai hakan ya gagara, ga waɗanda motarsu ta gogi junama sun fara faɗa na shirin danbe. babu yanda za'ai muyi magana muma wani ya sauraremu, dan abin yafi karfinmu.
     Kalle-kalle na maida hankalina wajenyi sosai kozan samo bakin zaren,
Idona ya kasa barin wata baƙar mota mai baƙin gilashi {tinted glass}, na wuceta yafi sau uku ina sake dawowa gareta, dan sai buga azababben horn mai motar yake nason a bashi hanya ya wuce tamkar shi kaɗaine yafi kowa buƙatar titin kosan tafiya.
       Glass ɗin na ƙwanƙwasa, dan na tabbata koma wanene a ciki shi yana kallon na waje ai, ba'a saukeba na sake bugawa, dan haka kawai nakejin wata irin jarumta da ƙarfin zuciya da bansan daga ina tazo minba........
       A fusace aka bugo mirfin motar ya bugeni, kafin na dawo daga jin zafin da nayi kawai naji ƙarar harbin bindiga har sau biyu.
     Take wajen ya hargitse da ihu, nima na toshe kunnena ina mai duƙewa ƙasa, mutane sai fita suke daga mota suna gudu, masu dabara kuma na kwanciya a ƙasa, tuni jama'ar dasuka taru suna hayaniya kowa ya kama gabansa, wasu sai son jan ababen hawansu baya suke suna k

omawa da baya-baya domin ƙoƙarin barin wajen.
       Cikin tunanin da yazomin daga UBANGIJINA ya sani fahimtar akwai matsala.
        Murfin motar da bai gama buɗuwaba aka ziro hannu ahaka aka ƙara wani harbin na kalla, da ƙafa na turashi ya bigi motar, hakan yasaka hannun da yay harbin ya matse sosai, ƙara ya saki yana sakin bindigar itama ta faɗi ƙasa.
      Jan motar sukai da wani irin ƙarfi, dukda motsocin dake gabansu bila adadin, tuni wajen ya sake ruɗewa, jikake garraaam!! Kaccaam!! Na haɗewar motoci, wata na bugar wata, gilasai sai fashewa suke famanyi, waɗanda suke a motocin basu fitaba sunata ihu na firgita.
     Saura kaɗan su takemin ƙafa, nai azamar sunkuyawa na ɗauki bindigarsa data faɗi, banyi zato ko tsammanin zan iya abinda nake yunƙuriba, amma cikin amincin UBANGIJI koda na harba sai harsashin ya sauka akan tayar motar ta baya.
     Tangal-tangal motar ta fara, hakan kuma ya sake hargitse wajen da ihun mutane. Kuma harbin ɗayar tayar nayi, hakan ya saka motocin dake gefenta, sukuma suka bigi fitilar dake a tsakkiyar titi ta tsaya cak.
          Gaba ɗayansu suka fito kuma lokaci ɗaya, dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya, gaba ɗayansu bindigace a hannayensu, hatta da wanda na bugama hannu da ƙofa na ɗauka tashi yana tare da wata, hannunsa dana buga sai faman jale-jale yake tabbacin na jimasa ciwo.......
         Da ƙarfi naji an fisgi hannuna, dai-dai shigar ihun Ummie cikin kunnena tana faɗin “Bily!!! harsashi!!”..................✍🏻


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 3

...............Shuuuu yazo ya wuce sai jikin glass ɗin wata motar bus.
Saurin kallon wanda ke riƙe da hannuna nayi, gabana yay masifar faɗuwa saboda cin karo da nai da fuskar da ban taɓa tunanin gani a wajenba ko tsammani, ya sake fisgar min hannu muka duƙe bayan wata mota saboda tahowar wasu harsasan huɗu kanmu.
Cikin matuƙar fusata ya girgizamin hannu yana faɗin, “K shashasha ki dawo hankalinki!!”.
Yanda yay maganar da wata firgitacciyar muryace ta dawo dani duniyar mutane, amma hatta da kunnuwana da sun doɗe baki ɗaya ko ƙarar harbin banaji.
Ya jefamin wata bindigar a jiki, cikin zafin nama na cafeta.
Sosai Jawaad yaji mamakin salon na bilkisu, sai dai babu wannan lokacin a garesa yanzun, dan haka ya maida hankalinsa akan abinda ke gabasu.
Wajen ya sake hargitsewa da musayar wutar harbe-harbe, kowa burinsa ya kare kansa, mutane kam bamuda tabbacin halin da suke ciki a yanzu.
Bazan iya tantance muku halin dana tsinci kainaba a ciki a wannan lokacin, amma ni kaina nasan na zama jaruma mai ban al'ajabi..
Kowa ya jigatu a wajennan. Bagamu jami'an tsaronba baga ƴan ta'addaba, balle kuma jama'ar gari da suka fimu shiga ruɗani da tashin hankali. Sai dai abin farin cikin shine mutum biyune suka haɗu da tsautsayin harbi a farar hula, ɗaya a ƙafa ɗaya a hannu, amma Alhmdllh babu wanda ya rasa ransa sai a cikin ƴan ta'addar da aka harba a ƙirji. Mun sami nasarar cafkesu baki ɗaya, su biyarne, ɗaya ya mutu, ɗaya naji masa ciwo a hannu, sai raunika da sauran suka samu da wasu a cikinmu harda ni da gilashin wata mota ya yanka a hannu.
Wannan shine karon farko dana taɓajin mummunan rauni makamancin haka a rayuwata, sai dai lokacin dana jisa ruɗani baisa na maida hankaliba dukda inajin wani masifaffen zafi da raɗaɗi na ratsani, a cikin ƴan uwana kuma babu wanda ya lura sai da ƙura ta lafa, zuwa sannan na zubar da jini sosai, harma takai ina ganin jiri a idanuna, dama gashi inajin yunwa sosai. Rose da hankalinta ya fara kaiwa kainace ta iso gareni da hanzari, dan tuni hayaniyar mutane data ababen hawa data cika wajen ta fara yima kunnuwana nisa, duhu ya fara mamaye idanuna, hakama numfashina sai tattarewa yake waje guda yana dunƙulewa a cikin ƙirjina, abinda kawai zan iya tunawa shine taroni da tai na faɗa jikinta, daga haka ban sake fahimtar komaiba daga duniyar mutane.
★★..::..★..::..★..::..★★
A hankali nake buɗe idanuna da sukaimin masifar nauyi, naɗan motsa kaɗan ina cije leɓe kafin na samu nasarar buɗe ido da ƙyau. ‘Asibiti kuma?’ na ambata a hankali ina waige-waige da kallon ɗakin dana buɗe ido na ganni cikin bazata. A saman hannuna dake naɗe da bandegi na sauke ganina, sai yanzune abinda ya faru yake ƙoƙarin dawomin a zuciya, a hasashena zan iya cewa jiya kenan abin ya faru, dan yanzu dai ranace ƙwanyar na fahimta, idan kuma ban mantaba ƙurar jiya ta tashine da yammaci har zuwa duhun mangariba, kenan a cikin asibiti na kwana?.
Bani da amsar tambayar tawa, kamar yanda babu alamun akwai mai amsa mani ita a kusa, dan babu kowa a ɗakin sai ni kaɗai.
Na ɗauki tsawon wasu mintuna da bazan iya ƙididdige yawansuba sallamar Ummie ta riski kunnuwana, nakai dubana gareta yayinda take ajiye madaidaicin kwandon data shigo dashi a hannu,
“Bily ashe kin tashi ma?”
Tai maganar tana matsowa daf dani. tare da taɓa hannuna da naji ciwon. murmushi nai mata, kafin na buɗe baki a hankali ina bata amsa da “eh”. Zama tai a kujerar gaban gadon, tana murmushi, tace, “Kai Alhmdllh, bily kin bala'in rikitamu jiya, wlhy mun zata bazaki sake buɗe ido ki ganmu ba”. Da tsagwaron mamaki nace, “Miyasa?”. Tai ƙaramar dariya tana miƙewa, “karki damu zan baki labarin komai, yanzu dai bara na kira Doctor danya dubaki, daganan kici abinci ko, dan tun kiran sallar farko na tashi domin na haɗa miki shi”. Kaina kawai na iya rausayarwa gefe ina binta da murmushi, tare da tarin ƙaunar da nake jinmu tamkar jini guda.
Ba'a ɗauki wani dogon lokaciba Doctor yazo, yaymin tanbayoyi kafin ya bama Ummie Umarni akan ta taimakamin nayi wanka ga bayi nan, idan na kammala naci abinci nasha magani, zuwa yamma ƙilama su sallameni tunda sunga komai normal.
Da taimakon Ummie na sakko a gadon, sai yanzune na kuma fahimtar a ɗaki na musamman nake, kuma ni kaɗaice a ciki, na kalli ledar jini dake rataye a ƙarfe cikin mamaki, Ummie data lura saita bani amsa da faɗin, “Ke aka ƙaramawa, dan sanda muka iso jininki ya zuba da yawa, amma Doctor yace babu wata damuwa a hakan, idan an ƙara miki zai amfaneki, idan kuma ba'a ƙaraba bazaki cutuba, sai dai boss ya dage akan a ƙara miki jinin dole, anbuƙaci gwada su oga Hafiz koza'a samu na ɗaya a cikinsu yay dai-dai da naki, amma sai boss ya hana a gwada kowa, a cewarsa jininsa yana rukunin da zai iya bama kowa, dan haka a ɗeba nashi, kowa yasha mamakin furucinsa, amma bawan ALLAHN nan ya fuske abinsa, babu ma wanda ya samu ƙofar kawo masa wargin tambayar dalilin hakan, daga ƙarshe dai jininsa aka ɗiba aka saka miki.......”
Lokaci ɗaya nai masifar zabura da zaro idanuna waje, har ina bige hannuna mai ciwo, hakan ya sakani cije lip ɗina na ƙasa kafin nace, “Jininsa fa kikace?”.
Sosai ta ƙyalƙyale da dariya, “Wlhy karkiji wasa, jinin Boss ne ke gauraye da naki suna aiki a kowacce kafar jijiyarki a halin yanzu”.
“Na shiga uku ni Bilkisu” nai maganar ciki yanayin ta ƙaremin. Dariya Ummie ta cigaba dayi, dan na lura sam bata fahimci tashin hankalin da nake a cikiba da gaske, ban sake iya maganaba har taimin rakkiya cikin toilet ɗin ɗakin dake tsaf babu datti, ga ruwan ɗumi ta haɗa mani kuma.
A cikin dabaru nake wankan gudun karna jiƙa hannun dake naɗe da bandeji, sai dai zuciyata sam bata tare da hankalina, sai faman juya maganar sakamin jinin Boss da Ummie tace anyi nakeyi, haka kawai naji hawaye masu ɗumi suna sauka bisa kumatuna, bansan na mineneba, sannan bansan dalilin zubar tasuba, sai dai wani gefe na zuciyata na danganta saukarsu da ganin kamar bankai matsayin da za'ace jinin wannan bawa ya gaurayu da nawaba, da kuma zaka tambayeni dalilin faɗar haka a lokacin bazan iya cewa komaiba balle yin fashin baƙi. Haka dai na kammala na fito, da taimakon Ummie na kimtsa cikin kayan da tazomin dasu, ta shafa min mai harda ƴar hoda fara ta sakamin dan karna zauna fuska na ƙyalli, na zauna a saman gadon jingine da filo ita kuma ta haɗamin tea, tare da zubamin farfesun kan rago daketa ƙamshin kayan yaji.
“Ummie ƴan gidanmu kuwa sun sani?”.
Sai da ta miƙamin tea ɗin kafin tace, “Eh, tun jiya da daddare sukazo ai, Daddy, Mom sai Aamilah da Shahudah da Salim, lokacin bakisan inda hankalinki yakeba, anama ƙara miki jinin ne”.
Kaina na gyaɗa mata sannan na amshi kofin, cikin suɓucewar harshe nace, “Sanda sukazo Boss na nan?”.
Tsareni tai da kallon tuhuma, ni kuma na basar cikin kauda mata shakkun dake neman yin ƙutse a ranta, fahimtar hakanne ya sakata daidaita yanayinta itama, tace, “A'a sun tafi lokaci harsu Oga Aliyu, ni kaɗaice kawai, saboda nima Daddy ne yace na jirashi shida Mami zasuzo su dubaki saisu tafi dani, tunda Doctor yace basa buƙatar kowa ya zauna dake”.
Bansan miyasaba sai kawai naji zuciyata tamin daɗi da rashin haɗuwar tasu, na cigaba da shan tea ɗin a hankali, Ummie ce ta kuma maido hankalina gareta da faɗin,
“Ammafa kin bala'in burgeni jiya wlhy Bily, wai dama baki da tsoro ashe?”.
Murmushi nayi kaɗan ina lumshe idanuna tare da muskuta zamana yanda zanji daɗi sosai, “Ummie ba tsorone banda shiba, wani lokacin tsoro da kansa yana jin tsoron mai tsoronsa, sai dai ba kowacce ƙwarin gwiwa ke fahimtar da hakanba, a duk lokacin da kikejin tsoron abu to kawai ki tunkareshi koda kina tunanin zaki halaka ne, ina mai tabbatar miki shi wannan abin tsoron shine zai koma tsoronki, da gaske daga jiya na ƙarajin ƙarfin gwiwar yima ƙasata aiki bakin rai bakin fama , alƙawarin danai da izinin ALLAH bazata tashi a banzaba, daga yanzu zan cigaba da tunkarar kowanne irin abin tsoro daka iya tsoratar da al'ummar ƙasata koda zai sakani fuskantar ƙalubale, bani da kowa sai kaina Ummie, akwai irina da yawa a faɗin duniya, waɗanda sukafini shiga gararin rayuwa da buƙatar jin ɗumin duniya a dalilin rashin majingina ta iyaye, wadda mutuwa ta nisantasu, kokuma iyayen na raye ƙaddara ta nisantasu, sai dai ita duniyar ta juya musu nata bayan saboda bata buƙatar nasu ɗumin, waɗanda kuma keda kusanci da duniyar suna hantararsu saboda basu da buƙatar taimakonsu koda da nuna tausayawane, irina da sukasan wannan zafinne kawai yakamata ace suna iya tunawa dasu da waiwayensu a lokacin da suka sami damar ƙutsawa jikin duniya ta ƙarfin tsiya. Na shiga aikinnan ne domin ALLAH, zanyi hidima wa ƙasata domin ita ƙasata ce, zan rungumi marayu irina domin ƴan uwanane, zan kare haƙƙin ƴan ƙasata domin suɗin ahalinane, nabar kallon allon tsoro a gabana a yanzun, allon jajircewa kawai nake burin cinmawa insha ALLAHU, abokan tafiya kawai nake buƙata, waɗanda basai naje farautarsuba, da kansu nakeso suzo gareni, hakkane kawai zaisa na tabbatar da sun cika sharuɗɗan abokan gwagwarmaya dai-dai da yaƙar tsorona, jiya ta wuce, yanzu a yau muke, abi mafi muhimmanci shine mu fiskanci gobanmu idan muna cikin masu rabon gani”.
Sosai Ummie keta faman jinjina kai da dogon bayanina da bani da tabbacin zai zama abin fahimta ga kowa har ita kanta, wani zai iya kallonsa ta fuskar ƙuruciya, wani yace rashin hankali na mata, wani yace wauta ta mara gata, wani yace zaƙewa ta ƴaƴa mata masu san nuna daidaita kafaɗunsu da maza, hakan bazai dameniba a duk yanda fahimtarka ta baka, abinda na sani kawai zuciya sirrin mai ita kawai takeji, duk bin diddigin ma'abocin kusanci koya kasa kunnuwa bazaiji komaiba sai bugawarta, idan kuwa har mun yarda gaibu sunanta gaibu, to yazama tilas muyi imani da hankali koda bama ganinsa a zahiri saita yaƙini kawai.
“Maganganunki irin na mutanene masu himma bilkisu, sannan masu duba gabansu mizatazo dashi, bawai yau ɗinsu kawaiba, da jiyansu data shuɗe ta zama tarihi, tun haɗuwata dake ta farko na fahimci kinada wata baiwa ɓoyayya da bakowa ALLAH ya bama ilhamar hasasotaba, daga lokacin kuma da muka kasance ma'abota kusanci na tabbatar da zamu ribantu da junanmu, sai dai taki ribar da zamu samu saita ɗara tamu muhimmanci da amfani a garemu, k.......”
“Sam ban gamsu da bayanankiba Ummie” na faɗa cikin ɗaga mata hannu saboda yanda ta kwararo zance.
“Miyasa kikace haka Bily?”.
“Banason faɗa kice na maida hannun agogo baya, mubar zancen kawai watarana ma ƙarasa, mizai hana kije wajen Doctor kimasa maganar ya sallamemu haka, banason zaman asibiti a rayuwata”.
kafin Ummie ta samu damar yin magana aka turo ƙofar aka shigo da sallama, Dad ne, hakanne ya sakani faɗaɗa murmushi akan

Please Login or Register in order to submit comment