Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
     Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
     Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss, murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa tsakanin...........
          Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da ɗakuna biyu a ciki.
      Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake kasheni taketa sakarmin.
           Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita. Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana, sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama, murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango kaina da ita kanta.
 

        Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace, ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata, zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku zama huɗu bayan ke”.
         Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.

            Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi, aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana koyamin

girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
     Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
        Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara hankalina gareta baki ɗaya.


____________________________

           A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen, koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.

       A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya dace..............✍


Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane wlhy🤦🏻😑😓.
[12/29/2020, 1:33 PM] HASNA✍🏻: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO



Bilyn Abdull 📚:
Page 38


..................Shagulgulan biki sun cigaba da gudana a washe gari tamkar yanda aka tsara, su Ummah babba sunyi yinin biki suma matsayin iyayen ango, kafin zuwa la'asar su ɗunguma zuwa masarauta domin halartar walima da gimbiya ta shirya itama. Walima kam ta ƙayatar fiye da zato, amarya tasha ƙyau cikin shadda pink mai duhu. Inda malamai magada annabawa suka gudanar da wa'azi mai kashe jiki da ɓargo, bilkisu kam dai ansha kuka, idanu sun ƙara girma. Tun su Zuhrah dake zaune kusa da ita suna mata dariya har dai suka koma lallashinta suma suna sharar hawayen dan jikinsu duk sai yay sanyi ƙalau. An tashine gab da magriba, dan haka kowa yana yin salla shirin tafiya dinner ya fara. Amarya ma wanka aka sakata ta shiga.
Gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, tunani da fargaba duk sun cika zuciyata, yau ni Bilkisu nice za'a ɗauka akai gidan boss matsayin matarsa ta aure, aure ba yawo ba, idan naje shike nan natafi din din din, duk da nasan ba sonsa nakeba, shima kuma bason nawa ya keba na ɗaura ɗammarar masa biyyayya insha ALLAH, zanyi haƙuri tamkar yanda kowa ke faɗamin zaman aure haƙurine, zanyi biyayya a garesa matsayinsa na mijina shugabana, zanyi aiki da dukkan dabarun Umm-Anum da gambiya suka ɗorani akai domin samun zaman lafiya a gidana koda ace bazai soni ba. tausayinsa nakeji har cikin raina yanzun, dan a daren jiya munyi zama na musamman da Ummu inda muka tattauna game da kamanninsa da Anuwar harma da Umm-Anum ta abubuwa da dama. Ta tabbatar min nice ya dace nai wannan aikin na bincikar abinda ya shafesa ko tanan zasu iya fahimtar idan akwai alaƙar da duk muke zargi dan kamannin sun wuce kama akwai dangantakar jini dole, bansan komai na abinda ya shafi family nasa ba, sai ɗan abinda ba'a rasaba shima iyakarsa daga wajen su Mom ne da da rashin jituwa tsakaninsa da Yah Qaseem, amma a raina nima tunda muka haɗu da Umm-Anum nakeji abubuwa da dama nazomin a rai game da shi......... Da wannan tunane-tunanen na tsaftace jikina na fito, kasancewar ba salla zanyiba zaman min kwalliya akayi.
Tun ina jiyo hayaniyar ƙawayena dake ɗakin su Amaturrahman suna shiryawa har naji tsit, alamar dai sun fice dan zuwa yanzu har anyi sallar isha'i. Basan yaya zan musalta muku irin ƙyawun da nayiba yauma, amma na bama kowa damar ya hasasoni cikin zuciyarsa, kwalliyata ta yau ta kasance harda alƙyabar da Mommah ta bani matsayin ƙyautarta, basai an faɗaba, a gani da ido kaɗai ya isa amsa ga mai kallo cewar an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi da darajar gaske. Suna cikin gyaramin alƙyabbar da santin ƙyawun da nayi aunty Samha ta shigo.
“Wow, masha ALLAH amaryar ƙamshi” ta faɗa tana rungumeni, ta ɗagoni tana kallona da cigaba da faɗin, “Wannan ai saiki rikita angon yace an fasa dinner ɗin”. Dariya waɗanda sukaimin kwalliyar sukayi, ni dai kaina a ƙasa ban yarda na kalleta bama dan tasa naji kunya, gashi kukane keta ƙoƙarin tasomin ina dannewa. Itace ta kama hannuna muka fice, ganin ba'a kaini wajen Ummu ba sai nayi tunanin za'a sake dawo dani nan kenan, ƙilama sai gobe idan ALLAH ya kaimu. A take naji farin ciki ya wani lulluɓeni. Ko ina ƙwanyar yake da haske a masarauta shiyyasa koda muka fito dukda kaina a ƙasa yake ina kallon inda muka nufa.
Mun tsaya dai-dai motar da na hango Oga Jabeer jingine yana waya tun fitowarmu, yana sanye da shadda ƴar ubansu ruwan madara. Yana ganin mun ƙaraso ya ajiye wayar yana murmushi da faɗin, “Aunty Samha aini da har ina shirin bin bayanku, dan naga baƙwa son bamu amaryarnan kamar”.
Murmushi tayi mai sauti tana gyaramin hular alƙyabar, “To gaskiya badan munasoba zamu baku, dan bamu gaji da ɗiyarmu ba, amma yaya muka iya, wannan shine girman”. Oga Jabeer na ƴar dariya ya buɗe ƙofar motar da cewa, “Aure yaƙin mata”. Tace, “Har mazan ma”.
Daddaɗan ƙamshin turarensa da na sani daine ya fara tarbata da sallama, na shaƙa na lumshe idanu ina ƙoƙarin dai-daita bugun zuciyata da kalato yawun da zan jiƙa maƙoshina da ya bushe, sai da na zauna da ƙyau Mah-mah ta gyaramin alƙyabar sannan na tsinkayi muryarsa yana gaisheta cike da mutun tawa, sai da suka gama gaisuwar s

annan Oga Jabeer ya rufe motar ya shigo shima, itama motar da zasu tafi a ciki ta nufa ta shiga.
“Ina yini?”. Na faɗa a hankali har banyi zaton zaima jini ba. Shiru banji ya amsaba, kuma tabbas inaji a jikina idonsa a kaina suke, dan ina jinsu har cikin ɓargona. kaɗan juya na kalli sashen da yake dan in tabbatar da bai jinin ba kokuwa ƴan wulaƙancinne a kusa.....
Ina ɗagowa idanuna na shigewa cikin nasa, saurin maida kaina ƙasa nai ina ɗan ƙunƙuni a cikin raina batare da nasan bakina naɗan motsawaba ashe, ‘mutum babu abinda ya iya sai kallo, har sai an hango maka muni’.
Jawaad dake kallon yanda bakinta dake ta shining na ɗan lipstick ɗin da aka sanya mata ya lumshe idanu a hankali yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, maida kansa yay jikin sit ya kwantar yana maijin takaicin yarda da yay da zuwan wannan dinner ɗin banzar, yanzufa kowa sai yaga wannan ƙyawun da tai ko?. Ware idanunsa ya sakeyi a kanta yana binta da wani irin sassanyar kallo, gaba ɗaya ƙamshin turarenta ya saukarma gaɓɓansa da kasala.........
“Ehhgy egeehhmm!”. Jabeer yay gyaran murya. Haɗe fuska jay yayi ya balla masa harara tare da ɗauke kansa ya maida gefe bai dai ce komaiba. Jabeer ya haɗiye dariyar dake cinsa daƙyar sannan ya tada motar suka fice.

Shiru motar tayi bakajin motsin komai sai na ac da ƙamshin turarukanmu, tunda na gaida Oga Jabeer nima ban sake ko ɗaga kai na kalli inda sukeba, dodon nawa kam tun gaisuwarsa da aunty Samha ban sakejin ya firta komai ba shima, anata kiran wayarsama yayi kunnen uwar shegu tamkar ba yaji ana kiran. Mintuna ƙalilan muka iso wajen taron, inda muka taras da abokansa dasu Ummie tsaitsaye alamar isowarmu suke jira.
Jabeer da yay fakin ya juyo ya kalli Jay. “ku zama cikin shiri boss, bara na musu magana”. Kai kawai ya ɗaga masa, shi kuma ya fice. Kusan sakanni ashirin da fitar Oga Jabeer babu wanda ya motsa a cikinmu daga ni har shi, inata ɗan juya zoben yatsana ne dan gaba ɗaya a takure nakejin zaman namu kusa da juna.
“Bana son rawa” na tsinkayi muryarsa ƙasa-ƙasa saitin kunnena, da sauri na juya garesa dan a bazata maganar tazomin. A karo na biyu muka sake haɗa ido, sai dai yanzun duk yanda naso janye nawa kamar ɗazun hakan ya gagara, kallo yakemin irin na tsakkiyar idonnan tamkar zai haɗiyeni dasu, bazan iya jurewa ba, amma na kasa janyewa dan tamkar yamin ɗaurin goro ne da mayun idanun nasa da a yau suke farare tas babu sirkin ja alamar dai baya tattare da ɓacin rai. Da ƙyar na samu nai ƙoƙarin yin ƙasa da kaina zuciyata na wani tsitstsinkewa tare da jinin jikina. Amma a bazata saijin tattausan hannunsa nai ya taro haɓata ya sake ɗago fuskar, tuni zuciyata ta sake wani zallo tamjar zata faso ƙirji ta fito, Farfar na farayi da idanuna da suka cika taf da ƙwalla lokacin da ya matso da fuskarsa daf da tawa har munajin saukar numfashin juna, lumshe idanun kawai nayi ganin bani da wata mafita kuma, ya kawo bakinsa daf da nawa.
Yanda jikina ke tsuma zai tabbatar maka a matsanancin tsoro nake da yanayin, tsigar jikina duk ta miƙe.
Jay dake kallon yanda bily ta rikice ya saki lallausan murmushi tare da goga hancinsa kan nata, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Matsoraciya kawai, darajar matata tafi ƙarfin nayi kissing ɗinta anan wajen yariya, hakan bazai taɓa yuwuba sai a fadata insha ALLAH. badan girman alƙawari ba da bazan taɓa bari ki shiga wajen nanba, ni kaɗai yafi cancanta na shaida wannan ƙyawu naki a cikin gidana. Ina ƙara maimaita miki bana son rawa”. Ya ƙare maganar da ɗaura yatsansa babba saman lips ɗina ya kwashe ɗan lipstick ɗin da aka samin.
Wata irin kunya naji ta lulluɓeni mai haɗe da tsoro da ɗan haushin gogen lipstick da yayi, nai ƙasa da kaina ina ɗan kumbura da faɗin, “Toni nama iya rawan ne ma.........”
Saukar ɗalli kawai naji a saman laɓɓana mai azabar zafin, na ɗago idanuna da suka cika da ƙwalla a kansa. sassanyan murmushin mugunta ya sakarmin har dimples ɗinsa duka biyu na loɓawa, ya ɗage kafaɗunsa yana ɗage gira ɗaya da taɓe baki alamar ni naja.
Kafin wani ya ƙara magana a ciki

nmu akai knocking glass ɗin motar, sauke gilas ɗin yayi, oga Hafiz ne yay masa magana akan mu fito. Banji amsar da ya bashiba, baice min komaiba nima ya fice, ina ƙoƙarin gyara alƙyabata nima na fita naji an buɗe ƙofar ɓangarena, na ɗago dan ganin wanene muka haɗa ido ashe shine ya zagayo tanan, hannunsa na dama ya miƙomin yana wani ɓata fuska da kallona ƙasa-ƙasa, a kunyace na ɗora nawa ya taimakamin na fita nima, hannunsa na haggu yasa yaja hular alƙyabar ya sake rufemin fuska da ƙyau.
Ina jiyo wani cikin baƙin abokansa na faɗin, “Sarakin kishi muma ba kalla zamuyiba ai bar wahalar rurrufe mata fuska”. banji ya bashi amsaba sai dariyar da sauran sukayi. Inajin irin zafin da nakeji a duk lokacin da ya raɓu jikina, sai dai yau kaɗan nakejinsa cikin amincin ALLAH, dan haka nai jarumtar daurewa tamkar banajin komai ina addu'a cikin raina har muka shige abokansa da ƙawayena na biye damu a baya cikin ƙyaƙyƙyawan tsari babu wata hayaniya.
Muna shiga da aunty Batool dake ƙofar tsaye tana jiranmu muka fara cin karo, ta shiga feso mana wani farin abu mai ƙyalƙyali da ƙamshi, masu hotuna kuwa nata ƙyalla mu.

Sauran mutanen duk suka miƙe idanun kowa na kan amarya da ango dake cike da birgewa, yayinda ƴanmatan family ɗin su Jay sukejin zafi a zukatansu dajin takaicin bilkisu da tazo daga sama tai musu wuf da shi, sai irinsu Rose da kallo ɗaya zakai musu ka hango tsagwaron kishi da tsanar bilkisun a cikin idanunsu. MC kuwa na zubama amarya da ango kirari. yayinda Ali jita ya sake gyara maƙogwaron nan nasa na zinari ya fara baitocin girma ga amaryar ƙamshi bilkisu mai gadon zinari cikin waƙarsa mai taken Bilkisu gimbiya.

(Bara naɗan raira muku kaɗan saura wani yace ban iyaba😣😚. lol)

🎸🎸🎶🎶BILKEESU zan faɗa dan ALLAH, mata ku bani dama duka.
bilkisu gimbiya.
BILKEESU mai gadon zinari waƙarki ta fita haka.🎸🎶🎶
BILKEESU sai gani sai nuni, kowa ya tabbata duka.🎸🎸🎸🎺🎺
BILKEESU gimbiya an baki, mata su dakata duka.🎸🎸🎺
BILKEESU sanya alƙyabar ki kaya mayalwata haka.🎸
Bilkisu gimbiya.
BILKEESU za'a yiwa fada, ai mata fifita haka. 🎸
Jita kaja muje nai waƙar Bilkisu masu girma haka.🎸
Mata ku rausaya Ali jita nine na baku dama haka🎸🎶🎶
Komai yanada rana a gane dama tanada dama haka, Bilkisu gimbiya.
Giwa ki rausaya BILKEESU ALLAH ya ƙara baiwa haka.🎸🎷🎷
Komai yaje ya dawo BILKEESU ku za'a tabbatarwa haka🎸
Ganga irin ta girma a miki waccan a mata garwa haka.🎸
BILKEESU za'a baiwa Number komai daren daɗewa duka


Please Login or Register in order to submit comment