Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake gudu dai ta tabbata, jawoni yay zai maida ya sake kwantarwa nace, “takwas fa ta wuce boss”. Buɗe idanunsa yayi yana ɓata fuska, da alama ba haka ya soba. Da ƙyar ya iya tashi muka shiga wanka tare, a gaggauce mukai muka fito, batare da mun tsaya neman abinci ba muka shirya, tea ɗin dana haɗa manama cayay muje masha a mota, shi dai maigadi ya miƙa masa nasa tare da kuɗi akan ya sayo bread mun makara yau. A motar kuwa muka sha tea ɗin abin dariya da tausayi (lol😂😜). Aiko yau ina rakasa office na fito dan ban kammala aikin jiyaba nima, a ƙofar office ɗin naci karo da rose, ko kallonta banyiba nai gaba abina, harna sauka ƙasa ina jiyo idanunta dake yawo a jikina, nidai ban fasa neman tsarin ALLAH da ga sharrinta ba harna ɓace abina.
  
     Kusan sha biyu da wasu mintuna ya kirani akan idan anfito salla nazo na samesa. Amsa masa

nai da to ana idarwa kuwa can na nufa, shi kaɗaine a office ɗin yanata ayyuka, duk da da alama shima yanzu ya shigo ɗin, ban zaunaba har sai da ya bani izinin zama. Tasowa yay daga kujerarsa ya dawo ɗayar dake kallon wadda na zauna, ya kamo hannayena cikin nasa yana mai tsareni da idanunsa nan masu takurani. “Miemaa na amince kije gidan Alhaji kokino, amma da sharaɗi”. Cike da ɗoki nace, “Minene shaɗarin?”. “Sharaɗin shine kwana ɗaya kacal da yini biyu zakiyi, idan yayi tsaurine kikai biyu, sannan tare zamuyi aikin dan bazan taɓa barinki ki shiga wannan aikin mai haɗari ke kaɗai ba”. Rungumesa nai saboda jin daɗi, hannu biyu ya amsheni yana murmushi, nace, “Na yarda da duka sharaɗin, ALLAH ya bamu sa'a da nasara”. Yace, “Amin Beejay, yanzu zaki tashi Sadiq ya kaiki gida kiɗan shirya, shine zai kaiki inda zaku haɗu da baba, sai ya ƙarasa da ke”. “Wow da wuri haka?, insha ALLAHU zaka sameni fiye da yanda kai tunani, kaida kaitamin addu'a boss ɗinmu abin alfaharinmu”. Ɓata fuska yay cikin wasa yace, “ke da wa?”. Ganin yanda yay da fuska ya sakani ƙyaƙyƙyawa da dariya, “Ni kaɗai mana, sai su oga Jabeer ”. Hararata yay, “K nifa kibarma kirana da wani boss na gaji da ji”. Kunya naji sosai, dan haka na ɓoye fuskata a ƙirjinsa ina dariya.

★★★★

       Duk yanda muka tsara hakance ta kasance, bayan sallar la'asar muka isa gidan Alhaji kokino, cikin shiri nake irin na ainahin garorin yaran nan na ƙauye da ko karatu basu taɓa samu ba, ga matarsa kam mun samu tarbar mutuntawa, ƴaƴan gidanne dai sai a hankali, dan gaba ɗaya halayensu baimin ba, sai wani famar min kallon banza suke, musamman mai son boss ɗin nan. Shiru nai na maƙure jikin kuje alamar tsorata ta baƙunta. Baba mai gadi da suka gama gaisawa da hajiya ya juyo ya kalleni, “K Larai! Baki iya gaisuwa bane? nifa banason wannan ɗabi'ar banzar kin sani”. Muryata na rawa nace, “Ina wuni hajiya, mun sameku lahiya?”. Dariya yaran suka bushe da ita duka falon, irin wai ƙauyancina ne ya basu dariyar. Ita dai hajiyar Murmushi tayi tana cigaba da kallona, tace, “Lafiya lau Larai, yasu mamar taku?”. “Lahiya lumi suke aradu hajiya, tace tana gaiheki”. Saboda dariya har ƙasa suke faɗuwa daga saman kujerun. A raina nace, ‘Wawaye kawai’.
      Baba ne da yake ɗan murmushi shima yace, “Hajiya dama tazo daga ƙauye ne can anguwar tudun birji wajen ƴar uwar mahaifiyarta, to saita iske wai sunje suna ko ina, kuma sai jibi zasu dawo, shine nace data koma kuma ai wahala goma da ashirin tazo nan saita kwana idan suka dawo sai taje, ALLAH yasa dai ban wuce gona da iriba?”. “A'a Malam baka wuceba kam, ai kaga anyi zuminci tunda dama kaƙi kawo mana iyalanka shekara da shekaru, ni nagode sosai da wannan ziyara”. “Nima nagode hajiya, bara na koma bakin aiki to ga tanan”.
      Ganin zai fita nai ƙwalƙwal da idanuna alamar kuka, “Kaka anan zaka barni?”. Juyowa yay da ɗan faɗa yana min daƙƙuwa, “Kinci gidanku Larai, nanɗin cin mutane ake bare kice za'a cinyeki? To idan hakan bai mikiba tashi ki kama hanyar ƙauye idan su Rakkiyar sun dawo sai ki dawo”. Baki na tura ina maƙe kafaɗa, “Ni alkur'an a'a”. “Ke kuma kika sani ja'ira kawai” ya faɗa yana ƙarasa ficewarsa. Yana fita suka fara jana da hira wai na basu labarin garinmu, nasan sosuke kawai su ringajin yanda nake magana suna dariya. Abinci aka kawomin, inaci ina basu labari kamar wata sakara, suko sai kwasar dariya sukeyi da zagina a kaikaice.
        
              Haka na maida kaina ƴar cali-calin ƙarfi da yaji a gidan Alhaji kokino, sannan aiki duk dana gani zan tashi nayi kamar bansan ciwon kaina ba, bansan inajin kewar mijina ba sai da dare yayi nazo zan kwanta a tabarmar ɗakin masu aiki, hakan bai dameni ba, dan wannan ba sabo bane a gareni, kewar tasace dai kawai naji, sai tunani nake yanzu koshi mi yakeyi? Oho.

★★★★

         Yanda Bily ke cikin kewa a gidan Alhaji kokino haka Jawaad yake a gidansa, tun da ya dawo daga wajen aiki duk sai yaga gidan yay masa wani faɗi da baƙi, yay zaune a babban falo yanata kallon sashenta, da ƙyar ya iya tashi yaje yay salla, koda ya dawo yaga zuciyarsa na ƙara ƙuntata sai ya fice daga gidan zuwa gidansu A

mina, baisan yawan zuwa gidan dan kar a fahimci akwai wani abu duk da yasan Dad baya a garin, sannan ma ƴan gidan hankalinsu baya aƙwance saboda rashin ganin Shahudah, shiko akan hakan yamaƙi zuwa ko family house ɗinsu tunda suka dawo, ya kuma kashe wayar da kowa zai iya samunsa.
     A gidan su Amina ya ɗan rage kewa,  maman yara tace ya kwantar da hankalinsa tanaji a ranta insha ALLAH bilkisu zata iya, dan a zuwan da sukayi jiya ta fahimci tana da hankali da wayo. Kai kawai Jawaad shi dai ya ɗaga, zuwa tara ya baro gidan, rasa mizaiyi yayi, haka dai ya koma gidan ransa duk a jagule. Tea kawai yasha yay shirin barci ya kwanta a ɗakinta, jin zuciyarsa ta sake ƙuntata ya ɗauki waya akan bara ya kirata ko muryarta yaji, sai da yaji switch up sannan ya tuna cewar bama ta tafi da waya ba. Tsaki ya buga yana jefar da wayar a kan gadon, waishi mima yasa ya barta taje ne?. haka yayta takaicinsa hardai daga ƙarshe ya sake ɗaukar wayar, Anuwar ya kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka cike da ɗoki. Wannan kiran Anuwar shine ya rage masa kewar Bilkisu a ransa, sunsha hira sosai dai sai kusan ɗaya da rabi na dare sukai sallama, sai kawai yayo alwala ya hau salloli ma. Sai kusan uku ya kwanta sai barci.

WASHE GARI

        Washe gari ma haka na tashi cikin ƴan aikin nan duk abinda sukeyi dani akayisa, babu wanda yace nabari a gidan, saima faɗa suke wai nafi masu aikin iya aiki. Nidai bance komaiba, sai lokacin da hajiya ke faɗa akan mai gyara mata ɗaki batayi da ƙyau ba, idan bazata iyaba a canja da wata. Murmushi nayi domin wata damace ni a gareni hakan, dan haka nai caraf nace ni bara na gyara mata yau. “A'a Larai, daga zuwa sai kita aiki? Aiba haka akeyiba”. “Lah hajiya karki damu, yo mufa mun saba alkur'an, dafa a ƙauyene da yanzu inacan ina sirhe, yo ni ina zan iya da wanga lalaci naku na mutan burni hajiya, ke dai bani aiki kiga aikin mata aradun ALLAH yanzu na ƙalƙale miki ɗaki ko fadar mai garin garinmu bata nuna masa fita ba”. Sunata dariyarsu niko na fuske abuna.
       Zagewa nai naima ɗakin gyara na sosai, sai gashi hajiya na santi ita da yaran nata, aiko ranar na aikatu, dan ɗakunansu sukaita sakani na gyara musu suma yaran, duk da na gaji haka na daure dan fatana nidai a ƙarshe a turani ɗakin mai gidan, amma sai naji tsit. Washe gari babu wanda ya sakani wani aiki, har yamma, abin duk ya dameni inata addu'a da fatan samun hanyar da zan shiga ɗakin, dan a yinin da nai jiya na aiki nazarin gidan naitayi da hanyoyin cikinsa. Kusan ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a can baya ni da ɗaya daga masu aikin gidan sai ga hajiya ta fito, sannu duk mukai mata da gaisheta dan duk yau ban gantaba bata yini a gida ba. Tace, “Larai Please zoki min wani ɗan aiki nan na dawo a makare”. “To” nace ina miƙewa, wani irin farin ciki ya kamani ganin mun nufi sama, inda nake da tabbacin turakar mai gidance anan. Fasalta muku yanda tsarin yakema ɓata lokacine, kowa ta ƙiyasta tsaruwarsa kawai. Kallona tai tana ɗan murmushi, “Larai nan zaki gyaramin, babu wata mai aiki dake shigowa ni nake gyarawa, to naje saloon da gyaran jiki sai yanzu na dawo gashi lokaci ya ƙure, kuma Alhaji nanda takwas na dare zai iso yayi tafiyane, na yarda da kene saboda kinada nutsuwa, dan ALLAH ki gyara komai ƙal kinji, ni kuma zanje mu ɗaura masa abinci”.
       Farin cikin da ke cin raina na danne, na amsa mata da “Insha ALLAH hajiya zaki samu fiye da yanda kikeso” “Yauwa ƴar albarka nakuwa gode, bara na turo miki Laila ta tayaki. Ɗaf ɗokina ya gudu, kamar zanyi magana sai kuma nai shiru harta fice. aikin na fara ina tunanin yanda abin zai kasance, dan insha ALLAHU bazan fita daga ɗakin nanba yau sai da abun nan.
     Laila ɗaya daga cikin yaran gidan ta shigo ko sallama babu, bataimin magana ba ta nema waje ta kwanta a cikin kujera tana danna waya, nima bance da ita komaiba na cigaba da aikin, tsaf na kammala falon na saka fresheners dana gani da turaren wuta, sannan na nufi bedroom ɗin. Ƙaton gaske ne shima kuma ya haɗu, sai dai gadon irin gajere ɗin nanne wanda babu yanda za'ai ka iya leƙa ƙarƙashin gado balle harka jawo abu. Wucewa nai toilet ina ƙullawa da kwancewa a raina

, gabana sai faɗuwa yake amma inata addu'a. Bayan na gama sai na ɗan fito falon dan naga mi laila keyi. Tsaye na taddata ta tashi, ta kalleni tana faɗin, “Nazo na baki bedsheet ko?”. Kaina na ɗaga mata alamar eh. Tare muka koma cikin ɗakin, ta buɗe haɗaɗiyar Wadrobe ɗin ta ciro zanin gado mai ƙyau ta ajiyemin a ledarsa. Murmushi kawai nai mata, a raina ina addu'ar ALLAH yasa ta fita, sai kawai naga ta ɗane sofa ta kwanta. Kaina na dafe ina cije leɓe, wannan itace damar da nake da ita ta ƙarshe, gashi kuma tana neman kufcemin. Jiki a sanyaye na fara yaye zanin gadon dake a gadon, na ajiyesa gefe suma filolin na fara cire rigarsu, harna gama na saka na wanda ta fiddomin, na ɗauki zanin gadon na fara shimfiɗawa, ina gab da gamawa akai kiran wayarta, gani nai ta tashi tana murmushi, ta kalle ni tana faɗin, “Larai banda aikin mugunta fa, ki tabbatar komai tsaf bara na amsa waya”. Kaina na ɗaga mata ina murmushi, ta zare keys ɗin duka drawer ɗin ɗakin ta fita da su, bakina na taɓe dan inda take bama tsaron ni bashine abin harina ba. Wata ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin ƙarar rufe ƙofa alamar tama fita daga falon. Ban ɓata lokaciba na yaye zanin gadon gaba ɗaya jikina na rawa, katifar na kama na ɗaga, bana ganin abinda ke ƙasan gadon saboda an saka kwali bisa katakon shimfiɗar gadon, maida katifar nai na ɗan fito falo na sake lalleƙawa, ganin babu kowa nai azamar dawowa na sake ɗagawa, shima kwalin ɗagashi nai, addu'a naketa yi a raina nidai, ina ɗaga kwalin wani hayaƙi ya taso ya bulemin ido, tari na farayi kamar zan mutu, na saka hannu na toshe bakina dan kar wani ya jiyoni, saurin maida katifar nai saboda jin kamar motsin tafiya, na cigaba da ƙoƙarin gyara gadon kamar dama shi nakeyi, hajiyace ta shigo, ɗagowa nai naimata murmushi, itama dai fuskarta da murmushin take faɗin, “Kai sannu da ƙoƙari larai, falon yayi ƙyau kuwa, an wanko bayi ko?”. “Eh na wanke hajiya, yanzu nan zan ƙarasa kawai”. “Yauwa to sannu da aiki kinji, ina Lailan?”. “Yanzun nan tafita inaga abu zata ɗakko”. “Okay to bara naje mu cigaba da namu aikin muma, dama dan naga yaya aikin ke tafiyane shiyyasa”.
    Ficewa tai, ni kuma na sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu na buɗe lokaci guda, hannuna dafe da ƙirjina. Yanzu kam a fili na fara karatun alkur'ani mai girma cikin suratul baƙara, na sake ɗaga katifar da kwalin, baƙin maciji na gani kwance idanunsa jajur, sai tukunyar ƙasa a gefensa an ƙulle bakinta da jan ƙyale. UBANGIJI mai rahama da ƙari, sai ya sakamin dakiyar zuciya da ganin nasa, nama cigaba da karatuna ina sake danne al'ajabi na, baya ya ringa ja daga gaban tukunyar, ganin haka sai na cigaba da karatun nima, sai kawai naga ya sulala ya shige wani rami a jikin bangon wanda bansan tayaya aka ƙirƙiresa ba. Cikin rawar jiki na ɗauka tukunyar na fiddo, ina cigaba da addu'a, sai dai ƙirjina wani irin mahaikacin bugawa ya keyi tamakar zuciyata zata faso ta fito, maida kwalin da katifar nayi, na fito falo da tukunyar jikina har yanzu rawa yake, sai da na leƙa falon ƙasa na tabbatar babu kowa sai tv kawai dake magana sannan na fito cikin sanɗa, addu'a nake jikina kuma na wani irin tsumar rawa, ina ficewa a falon naji muryar cikin masu aikin na faɗin, “wanene ya fita?”. Innalillahi na faɗa ina ƙara sauri, baba maigadi yana hangoni ya taso, na tsaya bayan wata mota inata waige-waige, isowa yayi gareni cikin sassarfa, na miƙa masa tukunyar ina magana da rawar murya matuƙa, “Baba, ka kirashi yazo ya amsa yanzun, bara naje na ƙarasa aikin da aka sani karsu fahimci wani abu”. Kansa ya ɗagamin kawai, na juya da gudu na koma, nai saurin daidaita yanayina lokacin dana shiga falon, hajiya na iske tsaye, ta zubamin ido cike da kallon tuhuma. “Keda kike aiki a sama mi kuma ya sakko dake ƙasa larai?”. Da ƙyar na iya ƙaƙalo yawu na haɗiye ina murmushin ƙarfin hali, “Hajiya wani yana na gani ta tagan ɗakin (Window) shine fa na zagaya dan na share sai naga ashe da nisa ta waje”. Dariya naga ta tuntsure dashi tana girgiza kanta, “Banda abinki larai ba a sama kikeba? Ki barsa akwai yaron dake sharewa zaizo ya share ranar weekend”. Kaina na ɗaga mata, ta juya kicin ɗi

n ni kuna na nufi saman benen ina godema ALLAH da ya rufamin asiri. Sai dai jikinafa har yanzu wani irin tsuma yakeyi, ga Masifaffen ciwon kai da alokaci ɗaya ya saukarmin. Haka na daure na koma ɗakin, canma na iske laila tsaye tana ƙarema ɗakin kallo, da masifa ta hauni akan ina naje? Kenanma tana fita nima na fita tunda ga shi nan ko gadon ban kammala gyarawa ba. Haƙuri na bata duk da zamuyi sa'anni da ita, na faɗa mata kamar yanda naima hajiya bayanin share yana. Tsaki taja min tana faɗin, “Malama kiyi sauri ki gama inada wajen zuwa”. Kaina na ɗaga mata kawai a sanyaye na hau gyaran gadon, yanzunkam tsaye tayi a kaina harna kammala aikin, hakan bai dameniba tunda naci nasara, na saka turaren wuta muka fito tare ina dafe kai saboda ciwon da yakemin.

★★★★★

         Jawaad na tsaka da aiki a office, sai dai rabin hankalinsa duk yana ga Bilkisu, tunda ta tafi basuyi ko waya ba, sai dai baba na faɗa masa tana cikin ƙoshin lafiya ya cigaba da mata addu'ar nasara. Wayarsa da tai ring ya duba, ganin baba ne yay saurin ɗagawa babu ɓata lokaci. Ko gaisuwa baba bai jira sunyiba yace, “Duk inda kake ka taho nan yanzun, yarinyarnan ƴar albarka tayi nasarar ɗakko tukunyarnan gata a hannuna ma”. Zaram Jawaad ya miƙe tare da wancakalar da takardun gabansa, bai saurari ɗaukar komaiba ya fice, key ɗin motar ya amsa a hannun Sadiq yace ya zauna ya jirashi dan da kansa zai tuƙa motar.
     Gudu yake na tashin hankali kamar titin nasane shi kaɗai, tsabar karya samu cinkoso ma sai ya ringabi ta wasu hanyiyin daban yana ratsema duk titin da yasan zai iske go-slow. Acan bayan layin suka haɗu da baba maigadi daya fito daga gidan akan yaje salla, da yake anata kiraye-kirayen sallar magriba ne. Miƙa masa kawai yayi batare da sun tsaya doguwar magana ba, “Maza kaje ka fasata Jawaad, karka tsaya ɓata lokaci”. “To baba, amma matata fa?”. “Kaje itama zan fiddota yanzu dana koma, dan tabbas akwai haɗari babba Alhaji ƙarfe takwas zai sauka ƙasarnan, duk inda yake a halin yanzun kuma nasan yaji a jikinsa an ɗauka tukunyar nan.............✍



ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[1/22, 9:04 AM] HASNA✍🏻: Page 55

.................“Baba bazan iya barin anguwarnan ba sai da ita”. “Bazai yuwuba Jawaad, kaje itama insha ALLAH lafiya zata fito, dana koma yanzu zan fiddotane itama”. “Baba kaima fa bazai yuwu ka zaunaba, dan zamanka akwai haɗari Sadiq zaizo ya ɗaukeku tare, kaje ka haɗa duk wani abunka mai muhimmanci”. “To shikenan ɗana, ALLAH yay maka albarka sai ya zo”.
             

CIKIN JIRGI

           Tun ɗaga gadon farko da Bilkisu tayi jikin Alhaji kokino ya bashi, to amma yasan akwai mai tsaron wajen koma waye tsautsayi ya kaisa sai dai gawarsa. Sai dai kuma ƙarfin gwiwarsa ta sare lokacin da yaga zoben dake a hannunsa yana canja kala zuwa baƙi, gabansa yay matuƙar faɗuwa, gashi babu damar kiran waya, a take komai nasa ya fara kwancewa lokacin da zobe tsafinsu ya shiga hasko masa abinda bilkisu keyi, sai dai ALLAH ya hanashi ganin fuskarta sam sai duhun inuwarta kawai yake gani harta ɗauki tukunyar data ɗauki tsawon shekaru a jiye babu wani mahaluki da ko yatsansa ya taɓa taɓata, sai maman yara da idanunta suka gani itama kuma saida ya sakata tai nadamar hakan, tanama can cikin nadamar ma (Masu karatu Alhaji kokino fa baisan yanzu maman yara bata wajen yaransa ba, dan randa ƴarsa ta saka masa maganin barci koda ya farka a washe gari har an maida masa wayoyinsa, babu wata kuma alama da Jawaad ya bari dazai iya zarga, shikuma da yasan babu wani mahaluki da zai iya masa makamancin haka sai bai kawo komai a ransaba, a washe garin ya bar ƙasar batare da yayi waya da yaransa akan komaiba. ALLAH kuma ya hana shaiɗanun dake taimaka musu fahimtar komai balle shugaban nasu na dodon tsafi damar sanar masa.
         Gaba ɗaya ya jiƙe da uwar zufa sharkaf kamar ana masa wanka da ruwan zafi, jiyake tamkar ya rikito jirgin ƙasa dan tsabagen tashin hankalin da yake a ciki, gashi sauransu kusan awa ɗaya da rabi kafin ma su sauka. Lallai wannan ko wanene a cikin gidansa sai ya ƙarar da dukan ahalinsa bama shi kaɗaiba.
          Jawaad kam kai tsaye gidan Alhaji babba ya nufa, sun fito masallaci kenan sai ganin Jawaad ɗin yayi ya fito a mota, sai dai yanayinsa yay masifar ɗaga hankalinsa. Tambayoyi ya shiga jera masa, Jay dai bai amsa masa ko gudaba a ciki ba, “Baba wannan ba lokacin amsa tambayoyi bane”. Ya faɗa yana nufar cikin gidan da tukunyar a hannunsa dan da duk a wajen gate suke inda Jawaad ɗin ya faka motarsa. Alhaji babba da ciwon ƙafa ya matsamawa a kwanakin nan ga yawan mafarke-mafarke da faɗuwar gaba da yake yawanyi yabi bayan Jawaad jiki a sanyaye, iskesa yay tsaye tacan bayan ɗakunansu ya ɗaga tukunyar zai fasa bakinsa ɗauke da addu'a. “Kai wai minene kake haka? sai kace wani matsafi?”. Jikake “Tassss!” Jawaad ya buga tukunya da ƙasa.
       Fashewarta tayi dai-dai da faruwar abu uku a zahiri, biyu a ɓoye.

       Na farko shine saukar jirgin da alhaji kokino ke a ciki bisa ƙasa. Na biyu mummunar faɗuwar gaba ga duk masu alaƙa da tukunyar, na uku faɗuwar Umm-Anum dake a kicin tana dafama Abbu shayi da yake a gidanta yake yau. Na baɗinin kuwa daga can fadar shaiɗancinsu ya faru.
        Wasu irin mugayen layune manya-manya guda uku a ciki, sai ƙananun allurai da wasu irin abubuwan surkulle da baisan minene ba shima, sai ruwan kuwa da suke ciki na jini ne sai wani uban wari ya keyi maiban tashin hankali, Alhaji Babba ya waro idanu waje jikinsa na rawa da toshe hancinsa da hannu yace, “Muhammad minene wannan? A ina ka samoshi ni Nuhu?”. Taga-taga Jawaad yay zai faɗi idanunsa a matuƙar jazur, Alhaji babba yay saurin riƙosa. Atare suka sauke ajiyar zuciya, da sauri Jawaad ya zare hanunsa daga na Alhaji babba ya nufi cikin gidan, hankalin Alhaji babba sake tashi yayi, ya kalli tukunyar da kayan ciki ya kalli hanyar da Jawaad yabi, ya juya zai bishi sai gashi ya fito ɗauke da ashana da gallon ɗin fetur na Genretor. Akan kayan ya zuba ya ƙyasta musu wuta. A take gidan ya ɗauki wani irin mahaukacin ƙauri mara daɗin shaƙa, sai ƙananun motsi kamar ana guje-guje, suka hau waige-waige suna dafe kunnuwansu da hannu da sauri, sai kuma aka fasa kuka da wata irin murya mara daɗin saurare. Ana ƙwalla kiran sallar isha'i gidan kuma yay tsitt dan masallacin idan aka kira salla kakanji tamkar a cikin gidan akeyi tsabar kusancin da suke dashi. Jagwab Jawaad ya zauna a ɗan dakalin da aka shuka fulawoyin gidan, ya dafe kansa yana karanto hasbinallahu wani'imal wakil. Sai kuma ya miƙe zumbur saboda tunawa da bilkisu da baba, lallai duk inda Alhaji kokino yake yanzu jirginsu ya isa sauka ƙasarnan. “Baba ina zuwa ya faɗa yana nufar gate cikin zafin nama. Sake binsa da kallo Alhaji babba yayi harya fice.
      Jay ya buɗe mota zai shiga saiga drivern gidan Ummah babba ya kawo Batool, baiko kallesu ba duk da ɗaga masa hannu da takeyi ya buɗe motarsa ya shiga tare da yin reverse yabar anguwar da mahaukacin gudu kamar zai tashi sama.

★★★★

          Tun ina ɗaukar ciwon kai wasa har ya fara neman fin ƙarfina, dan idanuna sun fara rufewa bana ganin abu da ƙyau, innalillahi wainna'ilairraji'un naketa ambata da sauran addu'oi. A wannan halin lariya ta shigo ta sameni ɗaya daga masu akin gidan. “Larai kije inji hajiya”. Gabana ne ya faɗi, dan a tunanina kodai ta gane wani abune?.
      A babban falo na iskesa tsuggune ita kuma tana daga tsaye da hijjab jikinta alamar salla tayi, “Haba dai baba, ai bai kamata ace a darennan zata wuceba, gashi bamu tanadar mata komai ba, kacema wanda yazo ɗaukar nata yayi haƙuri sai da safe sai ya dawo su tafi”. Baba da gabansa ke faɗuwa yace, “To hajiya banƙi ta takiba, amma da anyi haƙuri sun tafin dai babu damuwa, idan ta gama kwanakinta a can ɗin saita dawo nan ta ƙara miki kwana ɗaya daga nan saita wuce”. Shiru tai kamar bazata amsaba, sai kuma tace, “To shikenan na amince da wannan shawarar taka, bara na basu ko kuɗin motane, amma dan ALLAH fa kartaƙi dawowa”. “Insha ALLAHU zata dawo Hajiya”. Kallona tai da ɗan murmushi, “To larai kije ki ɗakko kayanki anzo ɗaukarkine”. Kaina na ɗaga kamar banason tafiyar jikina a sanyaye, ta nufi sashenta ni kuma na nufi ɗakin da aka saukeni na ƴan aiki, ƴar bakko ɗin kayana na ɗakko na fito bayan nama sauran sallama, kaina ne kemin ciwo sosai, dauriya kawai nakeyi.
     Dubu biyar hajiya ta bani, nai mata godiya da cewar ai zan dawo na sake mata kwana biyu kafin na tafi, da haka mukai sallama. Muna fitowa daga cikin gidan ana yin horn a ƙofar gate. Wani irin Masifaffen  faɗuwa gabana yay, shi kansa baba mai gadi a take ya diririce, saurin nunamin ɗakinsa yay yace na shiga ciki, shi kuma yaje ya buɗe gate ɗin.
     Drivern Alhaji kokino ya danno kan motar da sauri, kamar yanda baba ya saba duk sanda ya shigo

Please Login or Register in order to submit comment