Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya fara gani a yau karan farko na rayuwarsa, Anum tazo kusa dashi ta tsugunna itama tana ɗaura hannunta akan na Anuwar dake riƙe dana Alhaji babba. Jawaad dai yana kallonsu, sai dai bazaka taɓa fahimtar yanayinsa ba, kamilar fuskarsa ta shanye komai.
      A hakanli Alhaji babba yaɗan motsa hannunsa dake riƙe a cikin na Umm-Anum, saurin ɗagowa tai tana kallon hannun, ya sake motsashi a karo na biyu tare da kansa. tsitt ɗakin yay duk suka zuba masa ido. Sake motsawa yay fiye dana farko, sai kuma ya buɗe idanunsa a hankali ya sake maidawa ya rufe saboda nauyin da sukai masa, sake buɗewar yayi a karo na biyu, dishi-dishi ya fara hango Jawaad dake tsaye daga can ƙofar ɗakin yana facing nashi, ya ɗan kafesa da kallo tamkar dai yanason gano wanene?. takowa Jay yay a hankali zuwa gaban gadon, ya tsaya kusa da Umm-Anum tare da ɗan ranƙwafawa yanama Alhaji babba murmushi, hannu ya saka da kansa ya cire masa na'urar da aka saka masa. cikin magana a hankali yace, “Tsoho mairan ƙarfe!”.
     Karan farko Alhaji babba yay wani ɗan murmushi kaɗan da sake motsa hannunsa sai ya jisu duka biyu an riƙe. “Babah!” Umm-Anum ta kira sunansa cikin sanyin murya. Cikin wata irin faɗuwar gaba Alhaji babba ya juya saitin inda yaji muryar da bazai taɓa mantawaba a rayuwarsa, to kodai mafarki yakeyine har yanzun? Ya ayyana a ransa yana ware idanu akan Umm-Anum dake kallonsa tana murmushi da hawaye.
       Ya mata kallon kusan minti ɗaya kafin ya sake juyowa ya kalli Jay, sai kuma ya kalli Anuwar da Anum, ya sake maidawa ya kalli Ummah ƙarama da babba da Batool, Bilkisu da Nabeelah, cike da ƙarfin hali ya yunƙura zai tashi zaune dan ba'a ƙaramin ruɗani ya tsinci kansaba. Saurin riƙesa Jay yayi yana girgiza masa kai. Alhaji babba ya kalesa cikin muryar dake nuna bashi da lafiya yace, “Jawaad mafarkin dana sabane ko? Yo inba mafarkiba a ina nikam zanga mahaifiyarka ido da ido irin haka? Dan ALLAH kaga karka tadani a barcin nan barni nayi tayi ko ALLAH zaisa itama Rahmah da Maryam da Amina da Adamu zasuzo gareni duk mu haɗu anan”.
          “Baba ba mafarki ka ke ba, Bilkisun ka ce a gaske gabanka, nice na dawo gareku, ni ce ban mutuba baba”. Umm-Anum ta faɗa tana rushewa da kuka. Ai yanzunkam babuma wanda yaga sanda Alhaji babba ya tashi dingangan zaune yana riƙo hannun Umm-Anum cikin nasa duka, jikinsa sai rawa yakeyi, hannunsa ya ɗaura saman idonsa ya murza, ya kai kuma kan fuskarta ya shafa. Tabbas ba mafarki yakeba Bilkisun sa ce a gabansa, bilkisun daya rasa kusan shekaru ashirin dashida, bilkisun daya fidda rai da gani a wannan duniyar dukda yana tsananin ƙwaɗayin hakan. “Bilkisu dama kina raye?”. ya faɗa da tsananin rawar murya.
         “Ina raye baba, ganima ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwarmu, na godema UBANGIJINA daya saka ka kasance mai tsahon ran da zan dawo na tadda, da ace na dawo baka raye bazan taɓa daina yima mutanen nan munanan addu'oi ba har randa numfashina zai yanke”. Fashewa Alhaji babba yay da kuka, ya kamo kan Umm-Anum ya ɗaura saman cinyarsa ya rungume yana sake fashewa da kuka mai ban tausayi da tsuma rai.

             Da ƙyar Jay da Doctor suka samu damar lallashin Umm-Anum da Alhaji babba, harma dasu Ummah dasu Bilkisu, sai dai fa Alhaji babba ya tubure akan ya warke a sallamesa ya tafi gida, anyi lallashin duniya yace sam baisan wannanba wlhy shifa bazai kwana a asibitin nanba koma mi za'ayi.
     Ganin ya rikice musu harda hawaye Jay yace Doctor ya basu sallama kawai, sai su sami likitan dazai dinga zuwa gida yana dubashi babu damuwa. badan Doctor yasoba ya basu sallama.
       Jay da Anuwar ne suka kama Alhaji babba aka kaisa har mota, yayinda itama Ummah ƙarama ke riƙe da Bilkisu da keta dauriya da ƙarfafa jikinta dukda batajin daɗinsa sam, sai dai ƙasan ranta wani irin farin ciki takeyi da barin asibitin da zasuyi. Motar ta musu kaɗan, dan haka suka shiga ta Aliyu da suka iso asibitin babu jimawa suma dan an ƙaro jami'an tsaro cikin asibitin saboda mutane dake neman kawo ruɗani, acewarsu sunason suga gawawwakin da waɗanda aka samo da rai ko akwai ƴan uwansu a cikinsu.
     Jay bai bisuba, cikin asibitin ya sake komawa inda Qaseem da Salman ke tare da Mom wadda ta farfaɗo amma sun mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta ya hau sosai, Doctor ma yace badan ALLAH ya taƙaita mata wahalaba irin wannan faɗuwar da tayi zai iya sakawa ta kamu da paralysis. Sai da suka ɗanyi magana da Qaseem da shi kansa idan da za'a bashi gadon an taimakesa sannan Jay ya fito. Daya fito ɗinma wajen su Jabeer ya tsaya sukai magana sannan ya amshi key ɗin mashin ɗin ɗaya daga cikin jami'insu yabi bayan su Alhaji Babba.

_____________________
Dr Tayyeb Hospital
_________________________

                Shahudah dai suma tai a wajen, sai da cikin ƴan matan family ɗin wata tai ƙarfin halin shafa mata ruwa sannan ta kawo numfashi, hakama matar Uncle Nasir ita sai dama aka bata gado, ƴaƴansa nata kuka maiban tausayi da saka zukatan mai kallonsu rauni. Kosu Uncle Sulaiman sai da suka share hawaye dan tsananin tashin hankali. A yanzun kam sun fahimci zaman asibitin sam bazai yuwu a garesuba, dan haka suka tattara inasu-inasu suka nufi gida, dan anma hana kowa shiga wajen Mama Badiyya dama, ba'ason ai mata wata hayaniya ko kaɗan.
          Sun iso gida suka iske waɗanda suka bari anan cikin matsanancin tashin hankali suma, ciki harda Mama Atika da tafi kowa shiga ruɗani ganin halin da babba ɗanta yake a ciki da surukinta, tayi bala'in yin wujiga-wujiga da ita tamkar wata taɓaɓɓiya, dan sai surutai take, fitsari kuwa ba'a magana, tayisa a zane sau babu adadadi batare da tasan yanama zuba ba. Sai da ƴan asibiti suka isone suka fargar da ita halin da take ciki.
       Tabbas bayyana irin kalar ruɗanin da wannan ahali suke ciki ɓata lokacine, sai dai na bama kowa gari ya ƙiyasta a ransa. Gashi an turo jami'an tsaro sun zagaye sashen Uncle Nasir ɗin babu mai shiga kamar yanda akaima gidan Dad shima.
   
_______________________

             Ba ahalinsu Jawaad ne kawai a cikin ruɗaniba, duk ahalin dake da nasaba da waɗanan mutane yau hankalinsu baya tare da tunaninsu, anje kuma duk an zagaye gidajensu da jami'an tsaron sintiri, babu mai shiga babu mai fita. Waɗanda suka tsinci kansu a wani hali kuwa sai dai likitoci ake tura musu cikin gidajen suna dubasu.
     Sosai ƙasarma gaba ɗaya take a hargitse bawai jihar da abin ya faru kawaiba, idan ka buɗe tv da redio babu wani magana saita wannan tashin hankali daya faru. Masu jaje nayi masu ALLAH wadai nayi, waɗanda suka jima suna zarginsu kuwa suka shiga maimaita ai dama a rina. Ƴan uwansu masu mu'amula dasu da suka rasa wasu mutanensu da suka rasu ta wasu hanyoyin tuni suka fara yayibo hujjoji da zarge-zarge suna ɗora musu (Kusan ɗan Adam kamar jira yake🤦🏻, abinda ma ba haka yakeba sai ya maidasa hakan🙄🚶🏻😏).
             Masu ƙara gishi da magi a teburan masu shayi da gidajen suna da biki kuwa harda faɗin wai tukunya tukunya aka ringa fiddowa na farfesun mutane da gasashshen nama daga gidan😂, jini kuwa drom-drom sai kace wani mangyaɗa🤣. Aifa nayi ya samu a bakunan ƴan bani na iya, kowa burinsa ace shine ya fara kawo labarin🤒.

___________________________________
ƘARAMAR HUKUMAR GWANSU
_________________________________

                Gidane madaidaici mai ƙyau, dan kuwa ko'ina na cikinsa mulmule yake da suminti, sannan an shafesa da fenti ruwan madara da ganye mai haske, ƙal yake da shara sai ƙyalli fasassun tiles ɗin da aka saka a tsakar gidan yake da ɗaukar ido. Yarone da zai iya kaiwa shekara uku ke barci kwance a ƙaramar katifa ta yara a tsakar gidan babu riga jikinsa saboda yanayin zafi, sai wani da bazai wuce shekara shida ba tsaye jikin ƙofar fita daga soron gidan yanata kumburi alamar wani abun akai masa.
      Matashiyar mace da bazata gaza shekaru ashirin da huku ba ta fito daga matsakaicin kicin ɗin dake tsakar gidan ɗauke da tukunya alamar abinci ta kwashe, bayanta goye da jaririya ƙyaƙyƙyawa tanata barcinta hankali kwance. Tunkuyar ta ajiye inda alamu suka nuna wajen wanke-wanke ne tana mai harar yaron dake laɓe jikin ƙofar. “Wlhy kabari na kamaka a gidannan Fharhan sai na maka dukan da ko ubanka ba ganeka zaiyiba, karkazo ka ɗauki abincin su Innata ka kakai musu tunda ni na aikeka gidan su Musbahun har aka dakeka”.
     Sake tura baki yayi gaba yana share ƴar ƙwallarsa, “To Umma ni kije ki amsomin ball ɗina, inaba hakaba ni bazankai abincinba kuma”. “Karka kai dan ALLAH kaga yanda zan kirɓa namanka a gidan nan mara mutunci..........”
          “Yaya?! yaya?! dai”. Da gudu yaron da aka kira da Fharhan ya nufi mai maganar daya shigo yana faɗin, “Oyoyo Abbanmu”. Buɗe masa hannayensa yay ya shige jikinsa, ya ɗagashi sama yana dariya da faɗin, “Babana duk faɗan da nai maka akan yima Umma laifi bakajiba ko?”. Yaron ya ɓata fuska yana kallon Umman tasa dake tsaye tanama mijin nata kallon mamaki, yace mata wannan satin bazaizo weekend ba, amma kuma sai gashi a bazata da yamma liƙis. “Abbamu buguna zatai fa”. “Laifi kamata ai ko?”. Girgiza kai yaron yayi, kafin yayi magana ta matso inda suke ta ɗauka leda viva daya ajiye ƙasa lokacin da zai ɗauki Fharhan. “Sannu da zuwa”. Tafaɗa har yau da mamaki tattare da ita. Murmushi yay mata, yasa ɗayan hannunsa ya shafa kan yarinyar dake goye a bayanta. “Mai gadon zinarina barci akeyi?”. “Ai tunda naimata wanka ta ɓingire, irin wannan zuwan bazata haka”. Murmushi yayi batare da ya bata amsaba ya ida shiga gidan yana faɗin, “Banga na hannun damar Inna ba?”. “Gashi can yana barci”. Ta bashi amsa da nuna masa inda ɗayan yaron ke barci. Sauke Fharhan yay ya kama hannunsa suka nufesa, saida ya shafa kan yaronsa sannan ya zauna gefen tabarmar da aka ɗaura katifar. Itama ledar ta ajiye taje ta kawo masa ruwan sha. Sai da ta ajiye sannan ta sake kallon Fharhan, “Kazo ka kaima su Inna abinci karka bari na sake maimaita maka wlhy Fharhan ”. Baki ya tura zaiyi magana Abbansa ya hararesa, “Kanason na ɓata maka rai ko?” da sauri yaron ya girgiza masa kai, “Ɗauka abincin ka wuce, ka faɗama Inna muma muna nan zuwa gidan”. Da mamaki ta kallesa, sai dai bata iya cewa komaiba har Fharhan ya ɗauka kular abincin su inna ya fice daga gidan.
        “Amma daga dawowarka kake.....” katseta yay da faɗin, “Firdausi babban al'amarine ya kawoni gida, zo kiga abinda na gano”. Babu musu ta nufesa, ya ɗago daga danna wayar da ya keyi ya miƙa mata wayar yana faɗin, “Ko zaki iya gane wannan?”. Da saurinta ta amshi wayar, hoton da taci karo da shi ta tsatstsare da idanu, kusan mintuna uku tana kallonsa cike da nazari ko ƙyaftawa batayi, da sauri ta zabura tana zaro idanu waje da ɗora hannunta saman baki, “Abban Fharhan wlhy kamar Bilkisu fa”. “Kama ko itace?” “Wlhy bana ko tantama Bilkisu ce wannan, ko wane irin canjawa zatayi a rayuwa bazan gaza ganeta ba, dan ALLAH ina ka samo mana Bilkisu? Bayan shekarun da muka ɗauka cikin nemanta babu ko labarinta”. Tai maganar tana zama kusa da shi cike da zumuɗi. “Nima yau na ganta Firdausi, a media naci karo da hoton yana yawo a dalilin abinda ya faru, tana cikin tawagar jami'an tsaron da suka nuna bajinta wajen kamo miyagun mutanen nan yan cultism, kinganta anan tare da mijinta ranar aurensu, shima jami'in tsarone”. “A...ab... Abban Fharhan wai kana nufin Bilkisun ce ta zama jami'ar tsaro kuma tai aure?”. “Wlhy kuwa haka na gani, auren nasu bai wuce wata huɗu ba akace, amma watanta kusan biyu kenan da tarewa, shiyyasa nake faɗa miki ki ringa ɗan shiga yanar gizon nan amma kinƙi, koba komai zaki san abubuwa da yawa da duniya ke ciki, yanzu hakama bakisan abinda ke faruwa a ƙasarba yau ɗin?”. “A'a na sani, dan ɗazun su Luba sunzomin barka kasan sanda na haihu tana Niger, to shine suke labarin, hakan yasa na buɗe redio anan naji komai”. Murmushi yayi ya sake miƙa mata wayarsa dake ɗauke da hoton Bilkisu da Jawaad a ranar dinner ɗinsu lokacin da suke wasan bindiga. Sosai Firdausi ta saku wani ihun farin ciki, ta rungume mijinta tana mai fashewa da kuka, “Wlhy itace Abban Fharhan, ashe zan sake ganin bily a duniyarnan. Abban Fharhan dan ALLAH muje gidan baba, wlhy nasan zaifi kowa farin ciki a yau, bashi da wani buri daya wuce gamo da Bilkisu, wannan shine burinsa, da fatansa a kullum”.
       Babu musu ya amince, ta ɗakko mayafi da kayan da za'a sakama Abbas dake barci, shibe ya amsa ya saka masa, ita kuma ta shiga da kayansa ɗaki ta kulle ƙofar, ta kullo kicin da ɗakin da suke saka kayan abinci da tarkace, ɗaukar Abbas daketa barcinsa yay a kafaɗa suka fice a gidan, saida ta kulle sannan suka ɗauki hanyar gidan Baba a ƙafa da yake babu nisa sosai.

                Sun iske Fharhan nata bama inna labarin abinda akai masa a gidan su musbahu abokinsa kuma maƙwaftansu, tanata lallashinsa ita kuma. Sai dai shigowar su firdausi yasata maida hankali a kansu, Abban Fharhan ya kwantar da Abbas a gefen tabarmar da suke sannan suka zauna suna gaisheta.
       “Wai dama kazo garin Muktar?”. “A'a inna, zuwana kenan”. “To, shine kuma kuka taho nan? Lafiya dai ko?”. “Alhmdllh inna sai alkairi”. “To masha ALLAH, ai haka akeson ji”.
       Kamar yanda ya nunama firdausi hoto haka ya nunama Inna itama, kwatankwacin ruɗanin da Firdausi ta shiga innama haka ta tsinci kanta a ciki, da sauri ta shiga ƙwalama Baba dake ɗakinsa kira. Fitowa yay da ɗan hanzari dan dama bai jima da shigaba wanka ya fito yake kimtsawa dan dawowarsa kenan daga kasuwar ƙauye da yake zuwa yanzun yana sana'ar kayan miyarsa.
        Shikam ai ganin Bilkisu sai ya rikice fiye da zatoma, musamman dayaga hotunan waɗanda su Bilkisun suka kama, ya share ƙwallar data taru masa a cikin ido yana faɗin, “ALLAH mai iko, ALLAH mai hikima buwayi gagara misali. Muktar kayi haƙuri, dolene zuwa gobe mu koma birni tare da kai kuwa”.
       “Baba har dani dan ALLAH”. Firdausi ta faɗa tana share ƙwalla. Inna tace, “Wlhy nima kam ba'a barina baya, dolene naje ganin ɗiyata”. Itama muryarta da rauni a ciki tai maganar.
     A take babu wani ɓata lokaci suka yanke hukuncin tafiya birni gobe idan ALLAH ya kaimu koda kuwa idan sunje Alhaji lado da Jazuga zasu salwantar da rayuwar tasu kamar yanda suka faɗa musu a baya.

____________________________

               Tunda muka baro asibitin saina samu ƴar nutsuwa, dan yanzu banajin aman sam, sai dai kawai rashin ƙwarin jiki da damuwar dake cike taf da ƙirjina harma da ruɗani, ganin duk abinda ya faru nake tamkar a mafarki zan farka zuwa anjima naji ba hakaba.
         Mun yada zango a gidan Alhaji babba, inda muka iskesa zagaye da jami'an tsaro har yanzun, dan ba'a basu izinin barin gidanba. Aliyu na ajiyemu ya juya da cewar zaije ya nemo mana abincin da zamuci.
          Kasancewar magriba tayi ba zama mukayiba, da yake bayan ɗakin Alhaji babba akwai isasun ɗakuna a gidan sai kowa ya samu wajen shiga a wadace, ni dai sakani Ummah ƙarama tayi nai wanka da ruwa mai ɗumi, kamar yanda Anuwar ya taimakama Alhaji babba shima yay wanka dan ya ƙara samun ƙwarin jikinsa.
        Bani da wasu kaya a gidan dan haka na rasa yaya zanyi, saina maida na jikina na fito, salloli ake bina tun daga zuhur har mgriba da akeyi yanzun, gashi kayan jikina bana tunaninma zasuyi salla.
    Ina cikin wannan hasashen Anum ta shigo ɗauke da leda, ajiyewa tai a saman gadon tana murmushi, “Ga kaya yayanmu ya kawo miki”. Kallonta nai da sauri, mamaki sosai a fuskata, “Yazo gidan ne?”. Kanta ta jinjina min, “Yazo yanzun nan shi da abokan nan nasa na wajen bikinku, amma sun fita massallaci, Ummah tace ki saka kiyi salla kizo kici abinci”. Kai kawai na iya jinjina mata, na miƙe nayi duk yanda tace, ina saka kaya ina kallon cikina dake a shafe tamkar babu kayan ciki ma, amma a haka ake maganar akwai ɗan mutum a ciki. Bansan murmushi ya suɓuce minba, na ɗaura hannuna akan cikin naɗan shafa.

              Lokacin dana kammala rama sallolin dake kaina anata kiran sallar isha'i, dan haka na gabatar itama. ban fitaba, na kwanta a saman gadon ƙafafuna a ƙasa fuskata na kallon silin ɗin ɗakin, idanuna a lumshe suke, yayinda hannayena duka buyu ke cikin rigata ina shafa cikina, ni kaɗai nasan mi nakeji a lokacin, ina farin cikin samun ƙaruwar da ALLAH kaɗai ke wadata bayinsa da ita, gefe kuma inajin ɗacin tsintar wanda zuciyata take girmama da daratawa bayan iyayen firdausi fiye da kowa a duniya cikin mummunan hali. Tabbas da ace wanine yazomin da wannan labarin akan Dad bazan taɓa gaskatashiba koda kuwa ace Mijina ne, sai dai kash, nice da idanuna na gansa, da kunnuwana na jisa, ba'a cikin mafarkiba ko magagin barci, ba'a labari daga bakin wani ba. Haɗiye ɗacin daya tokare maƙoshina nayi daƙyar ina buɗe lumsassun idanuna jin ƙamshin turaren dana fi ƙauna fiye da kowanne a duniya a yanzun.
        Jay daya jima da shigowa yana ƙare mata kallo harya gaji ya ƙaraso inda take ya durƙusa a bakin gadon. A hankali ya kwantar da kansa saman cikinta bayan ya janye hanayenta, ya lumshe idanunsa dake cike da nauyin damuwa dana gajiya.
           “Kin bayyana a ranar da tarihi bazai taɓa mantawa da itaba Little Beejay, rana mai cike da ruɗani kala-kala da ban al'ajab, ina roƙon ALLAH ya raya mana ke cikin aminci, ALLAH yasa ki zama hasken idaniyarmu da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) baki ɗaya, kizama madubi mai haska addinin musulinci a kowace irin nahiya, kizama jaruma irin Mamanki.....”
          Murmushi ya suɓucemin babu shiri saboda jin sambatun da yakeyi, hannuna nakai saman kansa na fara shafawa a hankali ina sake faɗaɗa murmushi na, shi kaɗai ya ragemin yanzu a duniya sai gudan jininmu dake a cikin ciki, muryata da ɗan rawa nace, “Nidai insha ALLAH Little Jay ne”.
       “Tab, yarinya ban yardaba”. Ya faɗa yana ɗaga kansa da sauri da hawowa saman gadon ya zauna, yunƙurawa nai zan tashi ya riƙeni, maidoni yay jikinsa ya kwantar dani saman ƙirjinsa. Sai da na shaƙi ƙamshinsa na lumshe idanu sannan na buɗesu a kan fuskarsa ma'abociya kamala da kamewa ina murmushi. Shima murmushi yay min kaɗan yana kafeni da jajayen idanunsa, ya duƙo da fuskarsa dai-dai tawa ya sumbaci goshina da laɓɓana. Sake lumshe idanu nayi da kai hannuna saman kumatunsa ina shafawa a hankali har zuwa bayan kunnensa. “Thanks you Sweet Love” na faɗa a can ƙasan maƙoshi batare dana san shauƙi ya kwasheniba nai suɓutar bakin. Idanu ya ɗan waro alamar mamaki, cikin sarƙewar halshe yace, “Mi ki ka ce?!”. Cusa kaina nai a ƙirjinsa wani masifan kunya na lulluɓeni, ya ɗago fuskata da sauri yana faɗin, “Please Miemaa sake faɗa naji”. Ƙara ɓoye fuskar nayi da ƙyau. “Pleaseeeeeeee”. Ya faɗa a wani irin yanayin daya saka tsigar jikina tashi na sake ƙanƙamesa. “Sweet Love” na sake faɗa a hankali. “Oh my God, wannan rana ta musamman ce a gareni” ya faɗa da sake ƙanƙameni yay baya muka faɗa saman gadon ina jikinsa. “Lilly kinzo da tarin sauyi” ya sake faɗa yana shafa cikina da lalubar bakina ya haɗe da nasa.
       Karan farko a rayuwata dana fara maida masa murtanin abinda ya kemin kaina tsaye babu wani kunya kojin ɗar, a take ya haukacemin jikinsa sai tsuma yakeyi, munyi nisan kiwo sosai dan da gaske neman kaiwa inda yafi ƙauna yake nemanyi, ALLAH ya ceceni a bazata akai knocking ƙofar ɗakin.
        Nice na fara ƙoƙarin zare jikina daga garesa a wale, amma duk da haka ƙoƙarin maidoni ya keyi, na sake ja baya sosai ina sauke tagwayen numfashi da sauri-sauri da gyara rigata, sake knocking ɗin akayi, sai dai narasa ta yanda zan amsa, dan inhar nayi magana sai angane halin da nake a ciki, gashi kuma bansan wanene ba. Juyawa nai na kallesa, yana kwance a yanda na barsa idanunsa a rumtse yana sauke nasa numfashin shima, nasan tabbas yanajin buga ƙofar da akeyi, amma ya share abinsa hankali kwance. Yunƙurawa nai zan miƙe naje na buɗe yay saurin riƙo hannuna, sake juyawa nai na kallesa, yanzu kam ya tashi zaune, ya zaunar dani saman cinyarsa sannan yay gyaran murya batare da ya kalleniba. Daga wajen Nabeelah tace, “Yayanmu ance kufito aci abinci”. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, shikuma yace, “Uhhum”. Daga haka bai sake maganaba, Nabeelah ma haka saita bar wajen kasancewar tasan halin kayanta.
     Kallon juna mukayi, yaɗan kaɗamin idanunsa da suka ƙanƙance yana cika bakinsa da iska ya furzar. Bance komaiba na maida kaina na duƙar. Shima bai sake cewarba ya ɗagani daga cinyar tasa bayan ya shafa cikina. Matsawa nayi gefe ganin na samu ya sakeni, batare da yace dani komaiba ya nufi bayi.
     Ƙarar ruwa kawai na jiyo alamar wankama ya keyi kenan, na ɗan dafe kaina ina jinjina kaina, tunanin kar aga bamu fitoba ai zaton wani abunne ya sakani saka hijjab ɗina na fita ni, idan ya fito ya iskeni a can.

         Tunda na fito suketa jeramin sannu, Umm-Anum ta kamo hannuna ta zaunar a kusa da ita. Ɗan kallon Alhaji babba dake gefenta nayi na gaishesa, ya amsamin da kulawa tare da sakamin albarka da doguwar addu'a akan namijin ƙoƙarin da muka nuna a jejin can dan a cewarsa yanzu ya ga komai a labaran dare da suke sake maimaitawa. Kasa cewa komai nayi nidai, na juya na gaida Umm-Anum itama dasu Ummah babba, sai Yaya Anuwar da Aunty Batool da Aunty Haneefa, Aunty Saudah da sukazo suma babu jimawa, Anum da Nabeelah kuma na basu hannu mukai musabaha.
      Babu wanda ya tambayeni boss har aka fara zuba abinci a babban faranti kamar yanda Alhaji babba ya buƙata, muna shirin fara ci sai gashi ya fito sanye da kayan daya haɗo cikin nawa da Anum ta kaimin ɗazun. Ɗan kallonsa nayi ya zubamin harara, na ɗauke kaina ina haɗiye murmushin dake neman suɓucemin. Zama yay tsakkiyar Anuwar da Ummah ƙarama, shima yay bismilla kamar kowa ya saka hannu.

              Muna gab da kammala cin abincin wayarsa ta shiga vibration, da farko kalla yay zai ɗauke kansa, sai kuma ya ɗauka wayar da ɗan zafin nama yana ja baya daga gaban abincin, babu wanda yasan mi aka faɗa masa ya mike da ɗan hanzarinsa yana faɗin, “Zanje office, na manta shaf munada meeting wlhy”.
       “Meeting a daren nan Muhammad?”. Alhaji babba ya faɗa yana kallonsa.
          “To ya zamuyi baba? Akan case ɗin mutanen nanne, kasan manyan ƙasar sunyi caa akan batun, gefe kuma al'ummar ƙasar suma da zafi-zafi suke buƙatar suga hukuncin da za'a yanke, gashi a kuma a dalilin faruwar al'amarin allura na neman tono garma”.
       Murmushi Alhaji babba yayi yana faɗin, “Garmuna ma, dan ta wuce guda ɗaya. ALLAH ya bada nasarar ƙulla alkairi to, amma shiga ɗaki ka ɗakko magani kasha, wannan kan naka daga gani ciwo yakeyi”.
      Baiyi musu ba ya nufi ɗakin Alhaji babban ya ɗakko maganin, ruwa ya ɗauka a inda muke yasha sannan yay mana sallama ya fice. Muka rakashi da addu'a

Please Login or Register in order to submit comment