Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bilkisu gimbiya
BILKEESU sannu mata irin na zamanin ɗebe kewa duka.🎸🎸
Kinsha aradu kinsha yasin, kin samu arziƙi duka.🎸🎷🎸🎷
Kin tsallakema tarkon maƙiya, ga ɗan abin biki haka.🎸
Kinzam sarauniya a cikin mata bar munafuka haka.
Bilkisu gimbiya🎸
Ga zamani da daɗi wannan al'amarinkine duka🎸🎸🎸
Tsarki na zuciya bilkisu ya baki ɗaukaka haka.
Kinsa kara a hanya BILKEESU wazata tsallakane🎸
Komai kina tunani Bilkisu baƙya abu daka haka🎸
Bilkisu gimbiya
Ga ilimi da halin girma, ALLAH ya ɗaukaka haka.........🎸🎷🎸🎷🎸🎺🎺🎺🎺

(Kunema sauran kuji na gaji😂😜)

“Mawaƙin nan dolene yaci ƙyautar mota”. Oga Aliyu dake bayanmu shida matarsa ya faɗa yana ƴar dariya.
Murmushi naga boss yayi a hankali lokacin da yake kama kafaɗuna yana zaunar da ni a ɗaya daga kujerar guda biyu da aka tanada danmu. Ni kaina waƙar tamin daɗi sosai, hakan ya sakani sakin murmushi da banyi niyyaba. Jay yaɗan lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta sannan ya zauna a nashi mazaunin shima.

Babu ɓata lokaci aka fara gudanar da abinda ya tara mutane, an buɗe taro da addu'a kafin ai kiran Ummie tazo ta bada tarihin amarya a taƙaice, Hafiz ma ya bada tarihin ango tare da ɗorawa da shaƙiyancin randa suka fara gane Jawaad ya kamu da son amaryar tasa. Yanda yake faɗar wajen dole ya saka mutane dariya, masu baƙin ciki kuwa suka shiga zuba tsaki suna haɗiyar zuciya. Bily kanta sai da ta murmusa dukda tasan ba haka bane tunda ita

dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido, dan shima kallonta yake ƙasa-ƙasa idanu a narke.
Cike da salo ya wani ɗagemin girarsa ɗaya, maida kaina nai ƙasa zuciyata na motsawa. Ban sake gigin kallon sashen da yakeba nima na maida hankalina ga kallon mawaƙa da suketa baje fasaharsu cikin daɗaɗan waƙoƙi da duk an raira baitocinsune da sunayenmu. Umar m shariff, Ado gwanja, Nura m inuwa, Naziru Ahmad, Hamisu breaker, Isa ayagi, Abdul D one, kai abunfa ba'a magana, ƴan uwa da ƙawaye da abokan ango nata casar rawa, duk yanda mc keta magiya da roƙon amarya da ango su fito filin rawa ya hanani ko motsi, duk wanda ke buƙatar mana liƙi sai daifa yazo nan inda muke zaune ya liƙa mana ɗin, amma ko sau ɗaya bamu shiga filin rawarba.
Lokacin da Anum da Nabeelah suka hawo domin yima su Jay liƙi ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayiba, itama ɗin dai sai da ta ɗora hannunta a ƙirji alamar gaban nata faɗuwar ya keyi, dama tun sanda su bilkisu suka shigo saida gabanta ya faɗi, jikinta a sanyaye ta liƙa masa kuɗin shi da bilyn suka sauka ko jin surutun da Nabeelah keyi bataiba. Duk bilkisu na kula da yanayin da boss da Anum ɗin suka shiga, dan harta sauka yana binta da kallone.
Tun ɗazun nake wuwwula idanu ko zanga Yah Anuwar, haka kawai nakeji a raina bana son su haɗu da boss yanzu anan, to bammaga su Abdur-raheem bama. Da hannu na yafito Anum, ta taso zuwa gareni. Cikin magana ƙasa-ƙasa nace, “Ina Yah Anuwar?”. Tace, “Tab aishi bayason bidi'a, da wahala idan zaizo wajen nan, amma bakiga yanda mijinki ke kama da Yah Anuwar ba? Nifa dana kallesa gabana sai ya faɗi wlhy bilkisu”. Murmushi na mata da cewa, “Karki damu zamuyi magana amma ba anan ba”. Kanta ta ɗagamin ta koma wajen zamanta. Ina kallon irin kallon tuhumar da boss kemin nai kamar ban ganiba, dan rashin zuwar Anuwat ɗin yasa naji hankalina ya kwanta.
An buƙaci mu fito domin yanka cake. Ganin bai motsaba nima nai zamana, Ina jiyo fitar guntun tsakinsa alamar bayason yi, ni kaina bason nakeba, dan duk a takure nake matuƙa. Sai da Jabeer yazo yayta roƙonsa da ƙyar ya amince muka miƙe zuwa gaban cake ɗin da yay masifar ƙyau.
Mun yanka cake tamkar yanda tsarin yake, ni na fara cira ɗan guntu da zan saka masa a baki cike da jin matsananciyar kunya, dan da ƙyar na iya control ɗin tsumar da jikina keyi nakai hannuna bakinsa, hannun nawa ya riƙe shima muka saka masa gaba ɗaya wanda na ciroɗin kasancewar ɗan ƙaramine a baki. Ina ƙoƙarin janye hannun ya maidashi cikin bakinsa ya tsotse yatsun biyu dana ɗauki cake ɗin dasu suka ɗan ɓaci kaɗan. tafi hall ɗin ya ɗauka. Jinai tamkar na nutse dan kunya.
Shi kam Maimakon ya ciro ya bani kamar yanda nai masa sai ya lakato ya samin a saman hanci kawai dan wulaƙanci, ban gama fita daga takaicin salon nasaba naji saukar numfashinsa kan fuskata, kafin na sami damar magana ya lashe wanda ya lakatamin ɗin da bakinsa. tafin yanzun kam har yafi na ɗazu, dan yanzu harda waƙar Ali jita aka sake saki ta Bilkisu gimbiya. Ƙasa nai niyyar duƙewa dan kunya yay azamar riƙoni jikinsa, sai kawai na ɗora kaina saman ƙirjinsa ina sakin murmushin jin kunya, shima ya ɗaura hannunsa ɗaya saman bayana yana ɗan bubbugawa.
Da ƙyar mc ya samu hayaniyar ta lafa, zamu koma wajen zamanmu aka dakatar damu. Jabeer ya fara bayani kamar haka....
“To jama'a kowa sai ya buɗe idanu domin dai zamuga wasan manya ne, kunsan daga amaryar har angon jarumaine a filin daga”. Ya nuna bindigu guda biyu dake saman wani table duk an buɗesu, “Kuna dai ganin bindiga guda biyu ajiye ko? To munason ango da amarya su haɗasu cikin minti ɗaya yanda suke, wanda ya fara gamawa yana da ƙyauta ta musamman”.
Ni abinma dariya ya bani, hakan yasa naɗan murmusa, batare da tunanin zanyi nasaraba muka ƙarasa, sai da oga Jabeer ya irga uku sannan duk muka fara ƙoƙarin haɗawar cikin hanzari, ina kammalawa nai saurin ɗagowa na nunasa da bindigar fuskata a ɗaure, dai-dai da shima ya nunani data hannunsa fusakarsa babu wasa. .
Wani irin ihu hall ɗin ya ɗauka da tafi. Murmushi ya saki tare da tanƙwa

ɓe hannuna bindigar tai ƙasa ya caɓe cikin hannunsa, nai ƙasa da kaina ina murmushin nima dan naji kunya.
Duk da kusan tare muka gama ni aka bama ƙyautar dai dan nina fara nunasa da bindigar, wajen zamanmu muka koma, muna zama mc ya fara sanar da babban saƙo daga ƙannen ango na musamman Princes, sunce a basu wannan filin su kaɗai, dan ga waƙa ta musamman daga garesu da suka tanada domin amarya da ango. tsit hall ɗin yayi kowa ya buɗe kunne yaji ya kuma ga waɗanan ƙannen ango na musman da kowa ke ƙyautata zaton ƴaƴane daga masarauta.
Matasan samari masu ji da jini a jika da wautar ƙuruciya, Abdul-Raheem, Abdur-rahman, Ameen, suka miƙe, dan da gaske Anuwar bai zoba (su ustazu🤐 lol). sunsha ƙyau harsun gaji cikin shadda kalar sararin samaniya, kansu tsaye mazaunin ango da amarya suka nufa, yayinda Hamisu breaker ya miƙe ya fara raira musu waƙar........
Ashe da rai yake sanki jaruma bada zuciyatai ba, komai ruwa da iska akanki jay baza ya daina kewa ba, tunda dai ya samu zarrar samunki baza ya tanka kowaba, shi baiga mai hararaba, balle ya waiwaya baya. Indai a kankine zaya jure wahalar zuwa garin nisa, da an taɓaki ajirasa danko tilas yazo ya ɗau fansa..........

(Man kaina ya tsiyaye dole mukoma wajen breaker ya ƙarisa🚶🏻😫)

Breaker na fara raira waka sukuma suka farke ƴan dubu-dubu suka fara zubama Jay da bily liƙi, gaba ɗaya hall ɗin ya yamutse da hayaniya, masu ɗaukar video nayi a waya masu hotuna nayi, masu yima breaker liƙi nayi masu yima ango da amarya dasu Abdur-raheem nayi. Daga hakafa aka tafi casun ƙarshe.
Alhmdllh taro ya tashi lafiya kowa cikin farin ciki, anci ansha kowa yayi haniƙan banda amarya da ango, dan ko ruwa bily batasha a wajen nanba har aka tashi, haka shima Jay ɗin.

★★★★★

Ana tashi aka fice dani daga wajen, ganin mun barsa acan ba'a mota ɗaya zamu tafiba kuma farin ciki ya kamani, dan nazata dai masarauta za'a maidani. Sai dai ana sakani mota naji suna faɗin daga nan gidan amarya za'a nufa, idan anje ana kaita mutane su fito dan ba zama za'aiba dare yayi shabiyu saura.
A take zuciyata ta shiga tsitstsinkewa, hawaye suka fara gudu a kumatuna, dan nama manta da wata kwalliyar fuskata, ALLAH bansan wannan shirin suka shirya ba, duk zatona sai gobe idan ALLAH ya kaimu ganin bamuyi sallama da Ummu ba a masarauta. Tun ina kuka a hankali har ya bayyana fili. Lallashina Mah-mah take tayi da sakemin nasiha ƙasa-ƙasa har muka isa, dazan fita a motarma sai da ta sakani nai addu'a, hakama da zan saka ƙafata a falon, kaina lulluɓe yake da alƙyabba banajin komai sai ƙamshin fenta da ya haɗe dana turare dana sabon kaya ya bada yanayi na musamman.

An miƙa amarya Bilkisu ɗakin mijinta, inda basu wani ɓata lokaciba dan basufi mintuna ashirinba aka saka kowa ya fita ya shiga mota, dama wasu sun wuce gida daga wajen dinner, acewarsu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sazo suga gidan amarya da ƙyau.
Cikin mintuna ƙalilan gidan yay tsit, motocin duk sun juya, Aunty Batool kawai aka bari, itama zata ɗan zaunane kar abar Bilkisu ita kaɗai kafin Jay ya shigo. Bayi ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙamshi tazo ta tada bily da har yanzu take kuka. “Kukan ya isa haka amarsu, tashi ki daure ki watsa ruwa dan wannan kukan naki nasan ya ɓata kwalliyar”. Ban musa mataba dan inada buƙatar yin wankan kasancewar a yanayin da nake ciki. Alƙyabar ta taimakamin na cire kawai ta fita ta barni, ban zauna jan jikiba dan tace nai sauri boss zai iya shigowa koda yaushe, bai kuma dace ya iskeni a haka ba. Wanka na shiga nayo sauri-sauri na kimtsa jikina na fito, harta kwashe kayan dana cire ta ajiye min riga da zani na atanfa. Shiryawa nai a gurguje, ina kammala saka kayan tana shigowa. Tace, “Yauwa kinga ai hakan yafi, bara aɗan gyara fuskar”. Bance komaiba nidai taɗan shafamin fauda da lipsgloss a baki kaɗan sai turarurruka data fesheni dasu ta bani babban gyale na yafa tare da sake feshe ɗakin da Air Fresheners masu daɗin ƙamshi.
Inda ta zaunar dani ta matso tana murmushi, “To Amarsu angonki ya shigo, bara naje hasu Aliyu can na jirana zasu

saukeni a gida, mu kwana lafiya ALLAH ya huta gajiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, nace, “Aunty Batool dan ALLAH ki kwana anan mana, kingafa dare yayi”. Murmushi tayi tana riƙe haɓa, “Inani ina kwana gidan amarya, kinga nayi nan”. Hawaye masu ɗumi ne suka sake gangaromin, na zame na kwanta inayin kayana dan jinake ma duk haushin kowa nakeji, ni banason auren a maidani gidan Dad kawai na cigaba da zamana hankalina kwance.


__________________________

Lokacin da shagali ke gudana a gidan Dad tashin hankali suke fuskanta, dan kuwa dai Salman ne ya gano hotunan biki na yawo a yanar gizo waɗanda ke wajen dinner nata ɗorawa, kunsan mutane da waya a hannu tamkar abu na cizonsune idan suka gani, tun fara dinner ɗin suketa ɗakar hotuna suna ɗorawa wasuma harda videos. Aiko Salman yaci karo da su, shigowa gida yay ya kunna tv dan son ganin wainar da ake toyawa a wajen kasancwwar babu wanda yaje a cikinsu Momy ta hana. Yana zama Aamilah na fitowa, zama tayi suna kallo tare da zagin Bilkisu da Jawaad, hayaniyarsu ta saka Shahudah dake kwance a ɗaki zazzaɓi ya rufe fitowa, aiko tai mummunan gani, dan kuwa dai-dai wajen da Jay ya lashe cake ɗinan daya saka a hancin Bilkisu taci karo dashi, idan ba kallon tsaf kaima wajenba zaka ɗauka kissing ɗin Bilkisu ya keyi. Ƙara kawai ta ƙwalla ta yanke jiki ta faɗi.
Duk kanta sukayi da ihu har Momy Da Dad dake sakkowa daga sama. Girgizawar duniya da sakama Shahudah ruwa taƙi koda motsi, a take hankalinsu ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi suka kwasheta zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta. Har zuwa yanzun dai babu wani bayanin farfaɗowarta kuma.............🤦🏻✍



Duk wanda suka kirani jiya ban ɗagaba suyi haƙuri, ngd sosai kuma da addu'oinku gareni na samu lafiya🤦🏻.


ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
[1/1, 9:21 PM] HASNA✍🏻: Page 39

.................Tsaye kawai Jawaad daya shigo yay yana kallon Bilkisu da keta faman shashashar kuka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa. Sai ya tuna da randa aka kai masa Shahudah, cikin kayan barci ya shiga ya sameta zaune hankalinta a kwance tana buga game a waya, amma ita jiba duk da ba daga ainahin iyayenta aka rabotaba ta kasa barin kuka. Idanunsa ya lumshe a hankali da ƙara sauke ajiyar zuciya. Ya cire hular da babbar rigan, daga shi sai wando da ƴar cikin da iyakarta rafin cinyarsa. Ƙarasawa yay gaban gadon ya zauna kusa da ita, dauriya kawai yake dan kansa ciwo yake masa shima, hannunta ya kamo batare da yayi magana ba.
            Gaba na ne ya faɗi dan banji motsin shigowar kowa ba, gyalen dana rufe har fuskata da shi nai saurin janyewa dan naji tsoro, ya murza hannuna dake cikin nashi yana faɗin, “Tashi zaune, K baƙya gajiya da kukane?”. Yay maganar da kamoni sosai ya miƙar. Koda na tashi zaunen ban yarda na kallesa ba, ya sake murza hannuna da har yanzu yake a cikin nashin. Idanuna naɗan rumtse ina ƙoƙarin danne abinda nakeji.
          Jay dake kallonta ya girgiza kansa kawai tare da kai hannu ya janye gyalen data rufe fuska “Jiba yanda wannan kukan ya saka miki zazzaɓi, amma bazaki tausayima kankiba ki barsa haka, indai danni akeyi a ya isa haka na yafe”. Kamar jira take yay magana wasu hawayen suka sake zubowa sharrr. Kai Jawaad ya dafe kawai yana lumshe ido da sake buɗewa a kanta, shi kukan natama ya fara bashi dariya, sudai mata a duniya suyi kuka shine jin daɗinsu, ya sauke numfashi kaɗan  yana ƙoƙarin danne dariyarsa. “Tashi muje kici abinci kisha magani sai mu dawo ki cigaba da kukan kamar ƙyafi samun ruwan hawayen sosai ai”. Mamakin maganarsa yasa na ɗago na kallesa. Yace, “To miye na kallon nawa? Ba daɗi kukan yake miki ba?”. Ɓata fuska nayi nasa hannu na goge hawayen. Bai sake cewa komaiba ya miƙar dani tsaye, kunyace ta kamani nai azamar ɗaukar gyalena daya zame zan maida, amma sai ya riƙe, yana nunamin hanya alamar muje. Cikin rawar murya nai magana a karo na farko tun shigiwarsa, “To ka bani gyalen”. Matsowa yay gab dani sosai, hakan yasa naja baya idanuna na sake tara ƙwalla, Hannuna kawai ya kama batare da ya bani gyalenba bai kuma cemin komaiba muka fito falo.
       Dukda kaina a ƙasa yake nasan falon nan ya haɗu, ga wani ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi a cikinsa. Cikin kujera ya zaunar dani shima ya zauna kusa dani, ya buɗe filet ɗin dake akan centre table ɗin falon, ƙamshi mai daɗi ya daki hancina, kajine guda biyu da suka sami gashi mai ƙyau da tsafta. Yace, “Kici abinci kisha magani jikinki yayi zafi da yawa”. “Nifa na ƙoshi”. Na faɗa murya na rawa. Banza yaymin ya ɗebo naman da hannunsa ya kawo min a baki. matsar da fuskata nai ina girgiza kaina da sake faɗin, “ALLAH da gaske nake na ƙoshi”.
     Shiru yay na wasu sakanni baice komaiba yana kallona, kafin ya ajiye wanda ya ɗebo ɗin ya matsoni sosai, Hannunsa kawai naji saman haɓata ya ɗago fuskata, muryarsa babu alamar wasa yace, “Iyayi zakimin danma kinga zan baki kazan ƙyauta, ALLAH garama kici da arziƙi, bar ganin period kikeyi inada hanyoyin da zan sakaki kukan da kike sha'awar yi mai dalili, idan kuma kinji ƙarya kar kici na nuna miki ainahin kalata da baki saniba”. Tunda ya fara maganar idona ya cika da ƙwalla, na fara ƙyaƙyƙyaftasu.
       Fuska Jawaad ya haɗe sosai, dan ya kula sai ya buɗe mata wuta zasu dai-daita, a ɗan kausashe yace, “Miemaa!”. Da sauri na ɗago na kallesa jin yanda ya kira sunan a daƙile. Ya tsatstsareni da idanunsa dake tattare da ɗumbin gajiya, duk yanda naso janye nawa ya hanani. “Na miki kama da abin wasanki?”. Kaina na girgiza masa da sauri. “Inhar kika bari waɗanan hawayen suka zubo ALLAH saikin gane kurenki”.
         “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nima bada sona suke zubowa ba, wani irin tsoro nakeji a raina, saina dinga ganin kamar gilmawar inuwa kuma idanuna, sannan a ƙasan zuciyata wani irin zafi nakeji, kamin addu'a a cikin ruwa”. Kafeta yay kawai da idanu na wasu sakanni, ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa yana jawota jikinsa ya rungume. “Ki daure kinji, ki dinga ƙarfafa zuciy
[1/2, 1:07 PM] HASNA✍🏻: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 40
...............Sosai Nabeelah ta waro idanunta da suka cika da hawaye tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, “ALLAH yayanmu ni babu abinda zan faɗa, dan ALLAH kayi haƙuri”.
“Kinsan ALLAH idan kika bari harna miƙe kanki sai jikinki yay masifar yin tsami”. Yay maganar muryarsa babu alamun wasa. A mamakina sai naga Nabeelah ta fashe da kuka tana ɗanja baya, na kallesa da nufin bashi haƙuri duk da nima a tsoracen nake sai na ga ya miƙe, ai kafinma nace wani abu sai hango Nabeelah nai ta kwasa da gudu ta fice. Yanda yaja birki tare da riƙe ƙugu yana kallontane ya sakani kasa danne dariyata, hannu nasaka na toshe bakina tare da saurin kauda idanuna ganin ya kalloni.
Jawaad yay ƙwafa yanabin Bilkisu da kallo, “Ke kuma dariyan na miye to?”. Kallonsa nai da sauri ina ƙoƙarin haɗiye kayata amma na kasan, dan fuskata kawai zaka kalla kasan dariyar taƙi haɗiyu wa, harar daya ballo mince tasa nai niyyar barin masa falon naje nai dariyata a ciki. Caraf naji an cafkomin hannu da faɗin, “Dariya ko? To bara na huce a kanki”. Tsaf na haɗiye dariyar na koma zare idanu, cikin marairaice fuska nace, “Nifa ba dariya nayiba”. “To mi kikayi?”. Yay maganar da tsatstsareni da mayun idanunsa. Sosai kunya ta lulluɓeni nai ƙasa da kaina ina ɗan waige-waige, nima na Nabeelah nake tsarawa na fece kawai. Kamar ya fahimci abinda nake tsarawa a raina yace, “Kema guduwar zakiyi? Itama ɗin ba ƙyaleta naiba zan sameta har gida sai naci ƙaniyarta na gasa mata baki tunda ita magananniyace”. Murmushin da ban shiryaba ne ya suɓucemin, nace, “Yi haƙuri to niba baƙuwar zafi bace wlhy”. Kafin yace wani abu wayarsa ta shiga ring, kallon wayar duk mukai da mamaki, da alama ma anan ya mantata ta kwana ko?, hannuna dake cikin nasa na janye na ɗakko masa wayar da rabinta ya shige ƙasan filon kujera. Ban tsaya kallon ko wanene ba na kawo masa cikin.
Amsa yayi yana zama, ni kuma na juya na ɗauki basket ɗin da Nabeelah ta kawo wanda ko ba'a faɗaba kasan breakfast ne a ciki. Harna nufi D/table naji ya kirayi sunana, juyowa nai ina amsawa da “Na'am”. Dai-dai zai saka wayar a kunnensa alamar wancan kiran ya katse shi ya sake kira. Yace, “Kawomin tea, karki saka suga da yawa”. Da “to” na amsa kawai na ƙarisa na ajiye basket ɗin saman dani. Kicin ɗin na nufa ina ɗan murmushi da yaba ƙoƙari da sadaukarwa irin ta waɗanan bayin ALLAH, babu dangin iya babu na baba suka kashemin waɗanan kuɗin? Ba ƙaramin mutsuwar tsaye naiba da ganin yanda kicin ɗinan yay mugu-mugun haɗuwa, ni balki ɗiyar baba makaho ce da wannan gidan matsayin matar cikinsa? Sai kawai naji ƙwalla sun cikamin idanu, na shiga maimaita kalomin Alhmdllh a zuciyata ina hawayen zuci. Fasalta muku yanda kicin ɗinan yake ai ɓata lokacine, abin mamaki da al'ajab harda kayan abinci da malam bahaushe ke kira da gara, dai-dai da magi wannan sakarai an ajiye min shi. Sai dai kuma babu kayan tea ɗin da yace na haɗa masa, iya dubana banga koda lipton ba sai kayan ƙamshi kawai da abinda ba a rasaba, komawa nai da niyyar faɗa masa ban ganiba amma na iske yana waya da ransa a ɓace. “Uncle Please ka ƙyalesu ni babu abinda zanzo na musu, ina ƙoƙarin danne duk abinda suke son takalata dashi kawai amma na kula neman kaini maƙura sukeyi akan shirmensu”. Yaɗanyi shiru alamar saurare, hakan yasa na juya zan koma dan na bashi damar gamawa amma sai naji takunsa a bayana, baimin maganaba yazo ya wuceni, ganin hakan yasani bin bayansa, drawer saitin fridge ya buɗe ya nunamin. Kaina na jinjina masa na ida shiga ciki shi kuma ya fice yana cigaba da wayarsa. Bani da matsala da kayan ƙamshi dan duk gasunan a robobi harma da ganyan shayi masu daɗi da Umm-Aban dama tace zata haɗa min saboda ta lura inason shayi. Tukunya na ciro da dama an fiddata a kwalinta na ɗauraye na zuba duk abinda zan buƙata na ɗora saman gas da dama an haɗashi shima. Komawa nai na ɗauki plate da flask da kofi na ɗaurayesu tsaf, cikin mintuna ƙalilan na kammala na fito da komai na ajiye a dani ɗin, sannan na koma na ɗakko tea ɗin dana haɗa a kofi na ɗaura saman ƙaramin tire na kai masa falon dan har yanzu wayar yakeyi. Yanda yake kallona harna ajiye tiren a centre table duk sai naji na takura, nuni yaymin da in bashi, ɗauka nai na miƙa masa, ya ɗan lumshemin idanu alamar “thanks”. Bance komaiba nabar wajen dan sonake nai wanka.
Saida na gyara gadon yay tsaf sannan na shiga wankan, wanka nai haɗe da wankan tsarki dan mai jar motama ya ɗauke tunkan azhar ɗin da nake hasashen, zaton babu mai shigominne ya sakani fitowa daga ni sai guntun towel ga gashi a jiƙe, sai dai inata ƙoƙarin tsanesa da ƙaramin towel dake a hannuna. Ina ƙarasawa gaban mirror yana shigowa da sallama ciki-ciki alamar ransa a ɓace yake har yanzun, saida naji tamkar na ƙwala ihu, na ɗan wawwaiga banga wani abu dazan iya ja na rufe jikina da shiba, haƙura nai kawai na ɗan ɗago na kallesa cikin dauriya ina faɗin, “Nazo na baka abincin ɗinne?”. Shirun da naji yayi bai amsaba yasa na ɗago kaina na dubesa, idanunsa nakan gashina ko ƙyaftawa bayayi. Sake maimaita masa tambayar nayi. Ya janye idonun nasa da juyawa zai fita yana faɗin, “Ki gama nima zanyi wankan ne”. Binsa kawai nayi da kallo dan na lura ransa a ɓace yake, ‘Komi akai masa kuma?’ na faɗa a fili batare da inada mai bani amsata ba. Gudun karya sake shigomin yasa nai shiri a gaggauce cikin sket da riga na shadda orange color. Ni kaina nasan sunyimin ƙyau dan kamar an haliccesune a jikina sunmin ɗam dan telan ya iya ɗinki, kaina nakeson busarwa amma abin haushi babu wuta, a haka na gyarashi bayan na tsanesa sosai babu ruwa, ɗauresa

Please Login or Register in order to submit comment