Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Habiba a sama musu abinda za suci kamin mu dawo zan shawo kan shi Ahmad d'in insha Allah."

Godiya suka yima malam Mamuda kamar zasu yi mai sujjada sabida farin ciki, a haka duk suka yi alwala suka fice, itako Maman kitchen ta shige domin ganin ta dafa abu me sauki wanda zasu ci......










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

40

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*D*uk iyakar lallashin malam Mamuda gurin Ahmad daya yiyafiyar amma ta gagara domin, bayan dawowar su daga masallaci sunci sun koshi kowan ne baki awashe Ahmad ya yunkura zai tashi malam Mamuda ya hanashi tare da bashi hakurin da suketa fama dashi, idanun shi sunyi jawur sosai yake kallon yayyen mahaifin nashi da kannenshi d'aya bayan d'aya kamin yace da kyar.

"Na yafe musu duk abinda sukai min ammafa babu ruwana da huld'a dasu domin ina jin tsoran in sake dasu su cutar damu kamar yadda sukai sanadin d'an uwansu."

Ganin ya bar d'akin yasa malam Mamuda kallonsu tare da cewa,

"Kuyi hakuri insh Allah zai sakko kunsan yaro da rikon abu dole sai a hankali zai manta."

Itama matma hakurin dai ta basu tare da musu alkawarin zuwa su su duka garin domin sada zumunci.

***

"Ya Ahmad gaskiya be kamata kai musu haka ba naji baba nata fad'a dan Allah kai musu hakuri su duka ka yafe musu, kaga sun tuba zaka sami ladan yafiya kaji kaji..?!"

Murmishi yayi tare da rungumota jikin shi ya fara shafar cikinta wanda yake ashafe kamin yace,

"Nima na yafe musu baby kawai dai haushin su na keji wallahi na kasa manta abinda suka yi mana, oya haa bakin ki amshi abincin idan kinci da yawa to zan fita yawo dake anjima da yamma."

Baki ta bud'e da sauri a hankali ya dinga bata yana janta da hira hartaci da yawa ba tare da tasani ba, sai da ta kammala sannan ya kwashe kayan ya mayar kitchen ya dawo kusa da ita ya zauna.

"Sannu kaji mijin Khadija, Allah yabar mu tare ya k'ara mana hakurin juna.."

"Amin Dijama ta 'yar albarka ke kad'ai kike iyawa dani Allah yayi miki albarka."

"Amin my Dr ai kaine duk ka koya min ka raineni akan duk yadda kake so na kasan ce Khadija love you so much."

Da sauri ya kankameta a jikinshi tare da furta,

"Ahmad love's you so so very much..."

***

Ahmad da kanshi yayi tunanin fara azumi domin samun sauk'in rayuwar shi data khadijan shi, sai dai lokuta da dama adaddafe yake kai azumin sabida dama yunwa takan kwantar da sha'awa ammafa da kaci ka koshi zata iya tasowa.

Hakan yasa idan yana yi baya zuwa gida sai gaf da magriba sabida ko kwalliyarta ya gani sai taji abu ya fito mai amma idan gaf da magriba be zai koma yayi sallah a masallacin kofar gida sannan ta shiga ciki da haka yake samu ya saurarawa Khadija dama Zainab tunda ta tafi ba'a biyo sahuba shima bebiba tunda ta nuna mai bazata iya maiba.

*Bayan wata bakwai*
Cikin ikon Allah rayuwa ke juyawa wataran da dad'i wataran asami aka sin hakan. a bangaren su Ahmad sun cigaba da zumunci da 'yan uwansu suna matukar girmama Ahmad d'in domin yana kokarin ganin ya manta da komai daya faru abaya dan ya kyautata musu, sannan sukan ziyar ce su akai-akai domin temakon su shi yasa suke mishi kallon babban mutun ballantana da Allah yayi mishi arziki dai-dai bakin gwargwado.

A bangarenshi da khadija kuwa sai dai ace alhamdulillah domin cikinta harya shiga watan na haihuwa tana matukar samun kulawa fiye da duk yanda zan misalta muku musamman wajan mijinta ya d'auketa da matukar muhimmanci arayuwar shi ko washh ta furta to yanzu hankalin shi zai tashi, kullum cikin lallashi da bata labarin kaunar shi gareta ya keyi abinda ranta keso shi suke mata, domin samun surkai irinsu Mama zai yi wahala bata tab'a cewa babana meyasa kaima khadija abu kazaba ni bakai min ba? A'a sai dai kullun cikin tuna mishi take khadija taimaka halacci babana kadda kai mata butulci tayima iyayenta biyayyar zama dakai tunbaka da hankali sabida haka kadda ka cutar da ita, sannan ka dinga saurara mata da bukatarka sabida cikin jikinta kadda ka yadda ka koya mata gudunka kadinga tausaya mata domin tana bukatar hakan. kullun Mama bata barcin kirki kusan kwana take yi akan sallaya tana rokama khadija saukin haihuwa da zuri'a d'ayyaba.

Shin iyaye mata surukai munayin hakan kuwa?
nasan da yawa amsar itace a'a sabida haka kadda mu manta duk abinda kaima d'an wani to tabbas yananan zuwa kan naka. in kai me kyau zaka gani haka in kai sab'anin hakan shima zaka gani Allah yasa Mu dace, idan mun dace Mu dafe abunmu....

****

"Babyna zan fita babu abinda kike bukata?"

Tulelen cikinta ta shafa kamin tace,

"Honey yayana kadan d'ebe min kewa mana kota minti talatin ce ina bukace da kai naga kwana biyu baka san yi kuma ni wallahi ina..ina so."

Zama yayi gefenta tare da damke hannayenta cikin nashi yanajin wani irin mugun sonta na ratsa sassan jikinshi murya can k'asa kamin yace,

"Ayy sorry babyna ina jin tausayin kine shi yasa nake hakura amma tunda kinaso bari muyi sannan na tafi asibiti but babu inda kemiki ciwo yanzu ko..?!"

"Ni dai babu sai ciwon buk'atar mijina itace kawai take damuna."

Yana jin haka yayi saurin zame takalmin k'afarshi dama me neman yin kuka ne sai aka jefeshi da kashin awaki kunga kuwa sai yi.

Kusan da dabara ya samu biyan bukata sabida girman cikin yau kwana uku kenan ta lura ko bacci baya yi sosai kuma abinda ke damun shi kenan shi yasa tayi mishi wannan dabarar dan yasamu sakewa koda kuwa ita da babyn zasu takura.

Saida ya temaka mata tayi wanka sannan shima yayi ya sake kintsa jikin shi yayi mata sallama yana ta faman sa mata albarka zuciyar shi wasai a haka ya fita.

****

"Wayyo Allah na...!"

Cewa khadija wadda taji mararta ta isheta da tsinkulawa. da kyar ta kai hannu kan wayarta ta kira Maman kamin ta ajiye wayar Maman ta shigo.

"Sannu..sannu khadija oh ikon Allah kamar ana jiran babana ya bar gidan? kodai shine ya dameki?"

Banza tayiwa Manan ita dai hannu kawai take yarfewa ganin haihuwar tariga tazone yasa Maman gyara mata wajan zama cikin yardar Allah ko minti arba'in ba tayi ba saiga yaronta d'irkeke gundumeme kato tabarkalla Masha Allah, kuma daga ganin shi lafiyayye ne ko dan ihun daya cika musu kunne dashi.

Nan da nan jikin Mama ko ina rawa yake sabida murna ta rungume jaririn da jinin shi a jikinta da komai tana addu'a kamin tafara gyara shi ta na d'eshi ta koma kan khadija wacce tuni barcin dad'i ya fara d'ibarta.

Goge mata jikinta tayi sannan ta kamata ta maida ita gado sabida tasamu isasshen hutu sabida anaso idan kika haihu akalla kisami awa hud'u a kwance kamin wanka ya biyo baya sabida yin wankan da wuri shine ya kan kawo bugun jini da sauran su.

Zama tayi ta goge yaron nan tas! sannan tasa ka mishi kayan sanyi ta zuba mishi ido babu inda yaron ya baro uban shi sai bud'e idanun shi yake yi yana rufewa jitayi wasu hawaye sun zubo mata tace,

"Oh yanzu da basu yi mishi aure ba kila can za'a tsiyayar da yaron nan kila ma a kawo mata shi ya zamto itace zata raini d'an da bana halak ba da hannunta, amma yanzu murna take ji take tamkar ta suma danjin dad'i.

Godiya ta dinga jerama lillahi kamin ta rab'ashi gefen Maman shi wacce tuni tai barci, tashi tayi tafara gyaran wurin cikin kanknin lokaci d'akin ya d'auki kamshi kamin tayi waje da kanta ta d'auraye kayan ta shanya sannan ta d'orama khadijan ruwan tea wanda yaji kayan yaji saida ta had'a komai har kunun waken soya tayi mata sabida ruwan nono yazo sannan ta d'ora musu ruwan wanka domin daga mejego har jaririn ba aso daga haihuwa asamusu ruwan zafi ajiki hutunsu akafi bukata bawai wankan ba.

*****

kiranshi na hud'u kenan sannan yaji an d'aga sallama tayi mishi kamin tace,

"Honey yayana ya aikin naka?"

"Lafiya lau babyna ya kike ya ajiyata?ina fatan duk lafiya kuke ko?!"

"Lafiya lau muke wallahi ga Mama zaku yi waya."

Maman ta mik'awa saida ya gaishe ta sannan tace mai,

"Dama zance idan zaka taho gida kad'an taho da kaji zan bama khadijan sabida jikinta."

"Ok toh Mama zan taho dasu ai yau karfe hudu zan dawo insha Allahu."

"Allah yasa toh."

"Amin Mama bye."


Maman khadija ce da Maman Ahmad zaune sunata hirarsu ko wanne fuska awashe anyi jika, jariri ya fara kuka Mama tayi saurin d'aukar shi ta koma wajan khadijan tace,

"Kinga yaron nan bazai yi wani barcin kirki ba in bajin nono yayi abakin shi ba kallifa yanda ya keta wawure-wawure kiba shi yaja hakanan ai nonon yazo yanzu."

Cikin shagwab'a khadijan tace,

"Mama kaddafa yayi min da zafi?!"

"Keni ban san shirme bashi yasha ni zai kashemin dodon kunne."

Ita dai Maman khadija na gefe tana dariya, Maman ta samu ta nuna mata yanda zata bashi aiko da sauri caraf ya cafke da karfin shi ya fara zuka ihu khadijan ta saka tare da furta.

"Wayyo Allah nono na Mama."

Saida ya saki sannan Maman ta amshe shi tuni yayi bacci itako khadija hadda hawayenta wai da zafi. mutane nata shigo musu barka domin tuni Aminu ya gama zagaye mutune da suma sunyi sabon baby.

Da la'asar ya nufo gidan yanajin ya gaji sosai sai dai har yanzu farin cikin da khadijar ta shayar dashi da sanyin safiyar yau be sake shiba dan haka nan yake murmushi shi kadai tun a cikin asibiti.

Yana faka motar ya kwaso ledojin daya taho dasu ya nufi cikin gidan, yayi mamaki da yaji mata nata mishi barka da arziki, kayan ya zube cikin kitchen ya nufi d'akin khadijan,
aiko zaune ya taddata da k'aton jariri ahannu tana kukan bashi nono shi kuma yana kukan sai yasha.

Da sassarfa ya isa garesu sam be lura da matan dake cikin d'akin ba ciki kuwa hadda Maman tashi. d'aya bayan d'aya suka bar d'akin ganin yanda malam Amadu ya rungume iyalin shi yana jin wani farin ciki na ratsa zuciyar shi,

"Allah yayi miki albarka babyna Allah yayi miki sakayya da Aljanna yanda kike faranta min kema Allah yafaran tamiki ashe kinajin ciwo da safe amma kika sani dole na dameki ko?gashinan kinja na zunguro shi, nagode sosai yanzu kukan me kike yi shima yana taya ki ha?"

"Amin honey yaya na wai dole sai yasha nono kuma ko d'azu saida naba shi wallahi akwai zafi."

Bin yaron da kallo yayi yaga sai lasar bakin shi yake yana son saka hannu abaki, murmushi yayi kamin ya share mata hawayen yace,

"Kin gafa kina kuka yana kallonki kadda kisa ya raina kifa bashi kad'an yasha saimu gaisa dashi dan kar ya min kuka."
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

42

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)


*B*ayan kwana biyu masu jego sunyi shar abinsu basu da wata damuwa sabida irin kulawar da suke samu daga gurin duka side din, abba sai k'ara washewa ya keyi da wayau tubarkalla Mama bata da aiki saina kallon abba tare dayi mishi rawa ita dai Allah ya jarabce ta dason yaron wanda har bata iya boyewa.

AMINU kam kullum sai anyi daga dashi domin soya keyi ya dinga goyashi itako Mama taki yarda khadija ko babu ruwanta daya ce bani take mika mishi haka Maman zatai tamata fad'a amma bazai hana gobema taba shiba dan tana ganin bayan uban yaron to Aminu ne na biyu.

Malam Amadu kuwa tuni ya fara tsanewa atsaye duk da cewa kullum yanzu azumi yake yini dashi amma dakyar yake barci sabida kewar matar shi.

Zaune yake cikin ofis d'inshi yau tun safe babu abinda ya tsinana gashi yanzu har anfara kiran sallar azahar a wasu masallatan, wayar shi ya lalubo kamin ya dan na mata kira, cikin shagwab'a ya furta,

"Babyna..!"

Murmushi tayi kamin tace "uhumm yayana ya aikin?"

"Na kasa baby wallahi yau jinake kamar zan halaka Mama ta daina jin tausayina wai har yanzu baki fara sallah ba?"

Tunowa tayi da fad'an Mama dan haka da sauri tace mai,

"Eh ban fara ba, amma dai yau baka azumin ne?!"

"Inayi baby ya zanyi."

"Ayya toh shike nan dama cewa zanyi kai sauri ka dawo yanzu kamin Mama ta dawo ko ragewa sai kayi, tunda kuma kana azumin shike nan.."

Ai tuni ya mike tsaye tare da furta,

"Ashe batanan amma kikaki gayamin tun safe? bari inzo ganinan."

Dariya ta fara yi mai bayan ta ajiye wayar, zuwa yanzu mijin nata ya daina bata mamaki sai dai tausayi, sannan kullum adduarta gareshi shine Allah ya dauwamar da hankalin shi a kanta ya kauda idanunshi daga kallon matan banza ballema harya kaiga ta yawa.

Jikinta ta gyara da turaruka sannan ta tsaya jiran shi tana addu'ar Allah yasa kar Mama ta dawo da wuri. aiko sai gashi yau ko takan abba bebiba wata irin wawar runguma yayi mata akirjin shi kamin ya fara sunsunarta da lasarta, jikinshi harwata tsuma ya keyi yana cewa,

"Babyna yaushe rabon da ko rungumarki nayi Mama ta hana komai wallahi na kusa mutuwa da kyar nake daurewa, dan Allah da abun ya d'auke kimin magana ko sau d'aya ne nayi batare da sanin maman ba kinji matata?!"

Sumarshi take shafa ahankali cikin lallashi kamin tace,

"Kayi hakuri kaji kayiwa Mama biyaya nima ka tayani yi mata abinda take so."

Bak'aramar murza ta shaba a hannunshi ba sannan ya samu ya rage damuwar shi, Allah ya temaketa harya gama bired'ed'en shi hankalin shi be kai wajan abinba dan tasan da saiya gane ta sami tsarki ita kuma tana tsoran kar Mama ta gane tayi mata kallon wani abun.

kwance yayi agadon yana sauke nunfashi, har lokacin idanunshi alumshe yake kuma hannunshi na saman kirjinta yana cigaba da shafarta,

"Uhm! honey ya Ahmad to ka tashi ka shirya jikinka kamin Mama ta dawo ta taddaka kasan fad'a zatayi kuma sai ta gane sannan ya maganar azuminka yana nan?!"

Dariya yayi kamin yace,

"Ai kema kin san yabi ruwa na yau babyna amma dai zanyi gobe insha Allahu ai na rage zafi."

Itama dariyar tayi kamin tace,

"To yaza kai da girkin da zatayi maa anjima?"

Janta yayi jikin shi yaci gaba da tsotsar lips d'inta idanunshi arufe tsawon lokaci domin harta farajin zafi sai dai batasan ta katse shi domin samun nustwarshi itace tata.

Motsin yaron ya kwaceta dan haka da sauri ya tashi ya fara goge jikin shi ita kuma ta nufi abba dake son fara kuka.

Wucewa yayi d'akinsu yana fad'in,

"Sorry bari inyo wanka yaron baban shi sai nazo in d'aukeka kajiko?"

Tana bawa yaron nono shi kuma ya shigo ya canza kaya sai kamshi ya keyi, ganin irin kallon da take mishi yasa shi zama gefenta yace,

"Baby na can zamiki ne?!"

"A'a dadyn abba kawai dai naga kaimin kyaune sosai ina fatan zaka kauda idanunka daga kallon haramun?!"

Abba ya amsa a hannunta kamin yace,

"Ki tayani addu'a babyna insha Allah zan kiyaye nagode da kulawarki gareni Allah yayi miki albarka."

"Amin."

Wasa ya fara yima yaron kamar wani babba shiko yaro ya zubama fuskar baban shi ido.

"Kaga nidai kawoshi ka tafi kadda Mama ta dawo tayi tunanin ko wani abun kadawo mawa."

Yana mika mata yaron Mama na shigowa domin tunda ta hango motarshi taji hankalinta ya tashi, sannu da zuwa sukai mata ciki-ciki ta amsa tare da jefama Ahmad din wani kallon tuhuma,
kauda kashi yayi ga barin kallonta kamin yace,

"Mama ashe unguwa kikaje yanzu na shigo khadija ke gayamin gidan hassan naje shine nace bari na biyo daga nan in gaya miki hadda d'an-wake zakimin na bud'a baki sabida na rabu dacin shi wallahi."

Washe baki Maman tayi kamin tace,

"Au to shike nan yasu hassan d'in ai tun safe nafita dawowata kenan."

"Toh sannu rikeshi baby in wuce sai na dawo."


Kallon tausayi Maman tabishi dashi kamin ta maido kallonta gun khadija tana murmushi tace,

"Ashe yanzu shima ya dawo?!"

"Eh Mama shigowar shi kenan sai ya dauki abba toh kema sai gashi kin shigo kamar tafiyar ku d'aya."

"A'a ni yanzu na shigo Allah ya dawo dashi lafiya."

"Amin Mama."


Irin gyaran da Mama takema khadija ya sanya tuni itama tafara adduar Allah yasa Mama taje unguwa kosun samu su sake da juna dan ta tsumu iya tsumuwa, sai dai ina Mama ta tsare ta rantse sai anyi arba'in cas.

"Please Mama na kiji tausayi na tunda tayi kwanaki 40 din kibarni da ita wallahi kamar zan mutu nakeji ki tausaya min Mama dan Allah ki cetoni daga fad'awa halaka kamar yadda kika cetoni tun kafin nakai haka girma.."

"Oh ni na bani babana nadai koma abokiyar wasanka kawai, yo in ba haka ba niza ka samu da wannan maganar?!"

"To Mama ya zanyi kefa mahaifiya tace amma kin hanani ganin khadija bani da nutswa idan na gaza hakuri na dauko wani zunubin wallahi hadda laifinki ciki Mama please, yanzu bakya sona kin daina damuwa dani baki san ya nake kwana ba haba Mama ni nefa Ahmad d'inki babanki d'anki wanda kikafi so a duniya."

Tashi tayi tabar mishi d'akin cike da jin nauyin maganar shi, aiko shima afusace ya bar gidan yana cewa,

"Yaukam bazai yiwu ba wannan wahalallen barcin da nake yi ba dani ba, babu wani lemon tsamin da zanshi...."












*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

41

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*H*ararar yaron tayi kamin ta saka mishi nonon cikin bakin shi, dafe kafad'unta Ahmad yayi ganin yanda take kankame jikinta kamar ma so take ta kwace abinta.

Yaron yaci gaba dajan abincin shi har sai da ya saki dan kanshi sannan Ahmad d'in ya d'auke shi daga jikin ta ya rungumeshi yana ta sakin murmushi, kallon yaron ya keyi sosai ganin irin kamar da yaron yayi dashi, Allah nagode maka da kamin wannan kyautar, Allah nagode maka da arzikin da kamin ka bani dama in cigaba da gode maka."

Rungumo khadijan yayi tare da shafar kirjinta wa inda suke cike taf da alama ruwan nonon yariga ya samu, kwab'e mishi hannu tayi tana hararar shi.

"Allah ya baki aljanna matata ina fatan Allah ya barmun ke babyna kin isheni zaman duniya dana kiyama wallahi nagode nana khadijana..."

Murmushi kawai tayi tare da jawo ledar balangun da babanta ya aiko mata dashi d'azu sai faman kamshi yake.

Kusan tare suka cinye naman har lokacin yaron na hannun abban shi, shiko Ahmad tuni ya sami abin kallo gani ya keyi kamar banashi bane jiyake kamar za'a ce bani ba naka bane, ko yaji ana tashinshi daga bacci yasan mafarki ne amma yaji shiru sai mamakin kanshi yake wai shike da wannan zuk'ek'en yaron.

"Oh ikon Allah babana ka fita mana mutane nason shigowa amma sabida Allah kazo kayi zamanka a ciki ko kunya."

Kallonta yayi da kyawawana idanun shi kamin yace,

"Mama ganin su fa na keyi, kuma so nake muje asibiti yanzu a duba su."

"Amma dai ai ka bari suyi wanka ko? tunda shi yaron ance so d'aya ya wadatar dashi."

Cikin shagwab'a khadija tace,

"Mama waini bake zakimin wankan ba to waye zai min?"

"Haba khadija nace miki gwaggonki zatayi miki amma sai tambayata kike yi tun d'azu."

Idanun shi awaje yake kallonsu kamin yace,

"Haba Mama wai kina nufin baby tubewa zata yi wata taga jikin ta bayan ni?!"

Harararshi tayi sam idanunshi sun rufe kamin tace,

"Kai tafi can, nifa ban san hauka gwaggonta ta tace wata? to eh ita zata yi mata."

Grgiza kanshi yayi kamin yace,

"Ahh no gaskiya Mama gaskiya ban yarda ba wallahi kuma ban amince ba indai ke baza kiyi mata ba to gaskiya sai dai kibari ni nayi mata ko kuma a hakura da wankan, ya za ayi kowa sai yaga jikinta dan Allah haba-haba.."

Batai mamakiba domin tuni tagane irin masifar kishin shi akan khadijan amma batai tunanin abin ya kai haka ba. Kai ta girgiza kamin tace,

"Allah ya shiryaka to."

Sannan tabar musu d'akin.

Shi kam juyawa yayi wajan khadija yana tambayarta,

"Babyna babu inda kemiki ciwo ko?!"

Kallonshi tayi sannan ta kalli yaron dake hannun shi tace,

"Laah ya Ahmad wallahi da kai yake kama ka gani kuwa?"

Murmushi yayi tare da kashemata ido d'aya yace,

"Yoo yarinya angaya miki ni d'in na wasa ne ko matsalata ai tasa yaron yayo kama dani, tambayarki nayi fa ina kemiki ciwo?"

"Jikina be min ciwo amma dai ina jin zafi awajan abuna."

Kwantar da yaron yayi kamin yajata can karshen d'akin saman gado yace,

"Kwanta in gani ko kinsami kari ne."

Bata yi mishi gadda maba domin tana jin zafin wajen sosai daurewa kawai take yi. cikin nutsuwa ya dubata yaga tasamu amma dai beda yawa befi aimata d'inki d'aya ba kuma daga waje ne, shafarta ya fara yi bayan ya gama dubawa musamman kirjinta da sun riga sun gama tsokane mishi idanu, ganin yana neman fita hayyacin shi ne ya sata fara tureshi daga jikinta sabida tasan bata da abin bashi sannan tasan shi wasan ninnan bawani yi mishi suke ba shi dai kawai yajishi in.

"Nashiga uku ni Habi babana uban me kuke yi cikin kuryar d'aki kuma daga haihuwa yau sakaran wofi kawai...? zaka fito ko saina ci maka mutunci yanzun nan?"

Zaro idanuwa yayi yana kallon khadija saida ya dai data nutsuwar shi sannan ya fito yanata murmushi tare da shafar sumarshi yace,

"Kai Mama bafa wani abu zanyi ba dubata kawai nayi yanzuma idan kin yi mata wankan zanje da ita sai nayi mata d'inki tukunna ta denaji ciwon."

Harararshi tayi kamin tace,

"To naji zoka fice waje dan Allah kabarta ta huta haba mana kadai. san yanda haihuwa take yarinya nason hutu amma ka like da wanne kakeso taji?"

Hakuri ya bata tare da sumbatar yaron shi agoshi sannan ya bar d'akin bako kunya shi yanzu har wata fitsara-fitsara yakeji sabida ya girna ya zama Abba.

***

Kullum gidan nan cike yake da mutane Ahmad sam be cikin sukuni domin idan yabar gidan tun safe to be kuma dawowa sai dare sabida mutane. sosai yayi kokarin ganin yayima khadija da yaron shi bajinta domin akwati uku yayima khadijan sannan yayi ma yaron akwati d'aya sabida shi yaron kullum cikin samun kaya ya keyi daga abokanan shi da dangi kowa ya naso yaga yayima Ahmad din wani abu da zaiji dad'i.

Sun bawa mutane mamaki domin kuwa kowa yayi tunanin zai sakama yaron sunan mahaifin shi ranar sunan sai kawai sukaji an sakama yaro suna MAHMOUD, wato sunan malam Mamuda mahaifin khadija sai dai sun saka mishi suna na alkunya wato Abba.

Har hawayen dad'i malam Mamuda yayi lokacin daya ji sunan yaron yayi farin ciki tare da godema Allah, sannan ya shiga har gidan yayima Mama godiya sai dai itama godiya take mishi hadda hawaye yayinda ta tuna irin halaccin dayayi musu a cikin rayuwar su.


BAYAN SUNA:-

"Mama inaga abarta anan kawai d'akinta zaifi tunda baba yak'i yadda ta koma can d'in kuma mani sai naga dama nan da can d'in ai duk d'aya ne ko?!"

Wani kallon banza tai mishi kamin tace,

"Babana ban san meyasa yanzu ka rainani ba wallahi, so kake yi in bar maka yarinyar mutane kasani jin kunya wataran? kaddafa ka kamanta nice mahaifiyarka na sanka ciki dabai dan haka bazan bar khadija a d'akin taba zata dawo nan d'akina kai kuma ka zauna ana kun data gama wanka saita dawo d'akinta idan tagama zaga dangi amma gaskiya bazan yadda da zamanku tare ba sabida inajin tsoran halinka babana..."

Hakuri ya bata tare da barin d'akin cikin sanyin jiki. zaune ya taddata tana bawa yaron nono shima jikinta ya shige har wani ajiyar zuciya ya sauke kamin ya fara d'an shafarta sama-sama yana jin wata irin masifar kewarta jiyake kamar yayita tsala ihu ko za afahimci abinda ya keji cikin jikinshi.

Daga shi har ita nisa suka yi,sai dai sukaji ihun yaron ashe Ahmad dinne ya kwace nonon daga bakin shi ba tare da sanin lokacin da yayi hakan ba wato shi ya maye gurbin yaron, dariya suka saka tare bayan yai saurin maidama yaron nonon cikin bakin shi.

Dariya suke yi sosai musamman khadija da harwani nuna Ahmad din ta keyi da yatsa, saida Mama ta leko sannan sukai fargai-fargai dasu tace,

"Kukan me abba keyi haka?!"

Shiru su kayi kowan ne ya sadda kanshi k'asa, hararar Ahmad d'in tayi kamin tace hala yau ba zaka fita ba ne ko?!"

Mikewa yayi ya shige ciki saida ya shirya ya fito, Maman tabashi hanya ya fice sannan taje

Please Login or Register in order to submit comment