Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magani da sunan shi na mata domin babu komai cikinsu sai cutarwa kinga akwai wanda malamai suke badawa wanda amfani dashi bata ne, sannan ko wane kalar magani zaki sha indai baki da biyayya ko gyaran jikinki da iya kwanciyar auren to tabbas babu wani tasiri da maganin zaiyi a zuciyar mijinki.

Yanzu fa babu kalar kashin dabbar da za ace beyin maganin mata wannan wace irin masiface yanzu kusan komaima magani ne wannan ai musibace sannan babu abinda suke sawa sai mutuwar aure, malamai nata tambaya meyakesa mutuwar aure tayi yawa awan nan zamani musamman a arewacin Nigeria, to ba komai bane face maganin mata, domin wani maganin daga randakikai amfani dashi shike nan zaki kashe ainihin ta jikinki kinga kenan mijinki bazai kuma jin dad'in kiba. dan haka ki d'aure ki kuma jurema wa innan kawai sun isheki zaman duniya domin kadda garin neman k'iba ki nemo rama duk da nasan mijinki mabukaci ne sosai amma ina so kadda hakan ya jaki inda zaki kai kanki ki baro."

Cikin matsanan tacciyar kunya khadija ta sadda kanta k'asa tare da yima Maman godiya domin ko rannan da taje gidan wani suna taga an baje dilarsu anata fad'in amfaninsu saida ta siyo kala biyu har tana tunanin idan tasami kud'i zata je ta siyo wasu ashe ashe hakan abun yake.

Ganin khadijan tayi zugudum da ita yasa Maman tace,

"Karfa ki damu baki da wata matsala indai zaki dinga cin kayan marmari kuma kin rike wannan sirrin to zaki godemin nan gaba, tashi kije ga girkin can koya k'arasa."

A hankali Khadija ta mik'e ta wuce kitchen tana jin kaunar surukar tata duk da tasan d'anta take wa tanadi.

*****

A gajiye ya shigo gidan sai dai yanayin arba da gimbiyar tashi yaji ya watstsake saima wani irin shauk'inta daya taso mishi a lokacin.

Sai da ya gaishe da Maman sannan ya wuce d'akin su yana Alla Alla ta biyo shi amma tak'i sabida Kunyar Mama.


BAYAN ISHA'I:-

"Mama dama wani tunani nayi shine nace bari nayi miki bayani sai naji menene shawararki akai."

"Akwai wasu kud'i masu yawa da suke mallakina shine na canza mota sabida zirga-zirga yanzu kuma ina so mukoma gidan wani abokina daya gina amma be tare ba sai insa abaje wannan acanza na zamani zuwa gaba kuma sai in gyara na baba (malam Mamuda) sai kuma afara temakama dangi, amma me kika gani ke?!"

Murmushin jin dad'i tayi kamin tace,

"Amma dai kayi tunani me kyau wallahi Allah yayi maka albarka ya kara bud'i ina fatan dai na kane bawai bashin banki bane??!"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai Mama."

Itama dariyar tayi kamin tace,

"Aah to ai da gaskiya ta haka fa mutane suke yi yanzu kawai suje suciwo bashin banki sabida shirme sai daga baya kuma azo ana wallahi tallahi."

Dariya yayi yace "a'a Mama na wane kuma insha Allah bazan tab'a ciwo wa kaina bashin kowa ba."

"Allah yasa toh..!"

Yace "Amin."

****
Kan cinyarta ya zauna dan tsokana aiko tasaka ihu tare da k'iran "wayyo cinyoyina." Dariya yayi kamin yace "kai amma dai kekam anyi raguwa yo babyna ina naga wani nauyin da zaki min ihu?"

Ture shi tayi daga jikinta kamin tace "au haka ma zaka minko Allah ya kaimu wajan kwanciya lafiya zaka san nice raguwa."

Cikin dariya ya fara fad'in "wayyo Allah babyna bakece raguwaba nine nan ke kam ai nashaida ki jarumace ki rufamin asiri kadda jinina ya hau abani gado kija surutun al'uma ace Dr Ahmad a kwance sabida huran matar sh..."

Tayi saurin rufe mai baki da nata tana yi mai cakulkuli...









*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/14, 2:41 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

37

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)


_Wannan shafin nakune domin naga kuna jin dad'in labarin nan *DR AHMAD*, toh gashi kuyi yadda kuke so dashi_.

*Sister Ag*💕
*Sis Safara'u murtala*
*Real mai dambu*
*Ummumuhammad*
*Miss Marok'i*
*Khairat up*
Da k'awata ta kaina
*Sis Shafa'@t Omar*



*"K*inga wannan abun khadija, toh ba komai bane face kanunfari sai mazarkwaila da zuma, kinga abu ukun nan na rantse da Allah wanda ya halicceni kenan babu wata d'iya mace da zata kama wa innan abubuwan batare da ta mallaki mijin taba. Temakon da zata d'ora dashi biyu ne shine iya kwanciya da biyayya shikenan zaki iya zama da kowane irin namiji komai taurin kanshi da miskilancin shi kuwa, sabida mu lokacin mu duk babu irin wad'an nan kayan haukan da ake saidawar yanzu sai 'yan dubaru wanda bazasu taba cutar dake ba balle lafiyarki. kinga ZUMA! ita kadai ta isheki k'arin ni'ima ga KANUNFARI shima haka sannan kamshi zai zauna ajikinki musamman baki da kasanki sai MAZARKWAILA, kin dai san ita rakece sabida haka zanyi miki nasiha daki kiyayi kanki da duk wani nau'in na magani da sunan shi na mata domin babu komai cikinsu sai cutarwa kinga akwai wanda malamai suke badawa wanda amfani dashi b'ata ne, sannan ko wane kalar magani zakisha indai baki da biyayya ko gyaran jikinki da iya kwanciyar auren to tabbas babu wani tasiri da maganin zai yi.

YANZU fa babu kalar kashin dabbar da baza ace beyin maganin mata wannan wace irin masiface? yanzu kusan komaima magani ne wannan ai musibace sannan babu abinda suke sawa sai mutuwar aure, malamai nata tambaya meya kesa mutuwar aure tai yawa awannan zamani musamman a arewacin Nigeria, toh bako mai bane face maganin mata domin wani maganin daga randaki kai amfani dashi shikenan zaki kashe ainihin ta jikinki kinga kenan mijinki bazai kuma jin dad'in kiba dan haka ki daure ki kuma jurema wa innan kawai sun isheki zaman duniya domin kadda garin neman kiba ki nemo rama duk da nasan mijinki mabukaci ne sosai amma inaso kadda hakan yajaki inda zaki kai kanki ki baro."

Cikin wata matsanan tacciyar kunya khadija ta sadda kanta k'asa tare da yima Maman godiya domin ko rannan da taje gidan wani suna taga an baje dilarsu anata fad'in amfaninsu saida ta siyo kala biyu har tana tunanin idan tasamu kud'i zataje ta siyo wasu ashe-ashe haka abun yake.

Ganin khadijan tayi zugudum da ita yasa Maman tace,

"Karfa ki damu baki da wata matsala in dai zaki dinga cin kayan marmari kuma ki rike wannan sirrin toh zaki gode min nan gaba, tashi kije ga girkin can koya k'arasa."

Tashi Khadija tayi cikin jin kunya ta fita har tanajin tuntub'e da kifar d'akin...

*****

A gajiye ya shigo gidan sai dai yana yin arba da gimbiyar tashi yaji ya watstsake sai wani irin shauk'i daya taso mishi alokacin.

Sai da ya gaishe da Mama sannan ya wuce d'akin su ganin itama ta shige tana mai dariya.


BAYAN ISHA'I

"Mama dama wani wani tunani nayi shine nace bari nai miki bayani sai naji menene shawararki akai,

Akwai wasu kud'i masu yawa da suke mallakina shine na canza mota sabida zirga-zirga yanzu kuma ina so mukoma gidan wani abokina daya gina amma be tareba sai insa abaje wannan acanza na zamani zuwa gaba kuma sai in gyara na baba(malam Mamuda) sai kuma a fara temakama dangi, amma me kika gani?"

Murmushin jin dad'i tayi kamin tace,

"Amma dai kayi tunani me kyau wallahi Allah yayi maka albarka yakara bud'i ina fatan dai naka ne bawai bashin banki bane kaje ka d'akko?"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai Mama?!"

Itama dariyar tayi kamin tace,

"Ah to aida gaskiyata hakafa mutane suke yi yanzu kawai suje su ciwo bashin banki sabida shirme sai daga baya kuma azo ana wallahi tallahi."

Yace,

"A'ah Mama wallahi nawa ne halak malak kidena saka ran Zan d'aggo abinda yafi karfina."

"Toh Allah ya kyauta ya kuma tabbatar maka da alkairi babana."

"Amin Mama na."

Daga nan ya fita ya koma d'akin su,

Kan cinyarta ya zauna dan tsokana aiko tasakar mishi ihu tare da kiran,

"Wayyo Allah cinyoyi na.!"

Dariya yayi kamin yace,

"Kai sharri kayan mata, amma dai kekam anyi raguwa yoo babyna ina naga wani nauyin da zaki min wannan ihu?"

Tureshi tayi daga jikinta kamin tace,

"Uhmm'ehm au hakama zaka minko? Allah ya kaimu wajan kwanciya lafiya zaka san nice raguwa."

Cikin dariya ya fara fad'in,

"Wayyo Allah ni Ahmad marayan Allah, babyna ba kece raguwaba nine nan mugun rago kekam ai na shaida ki jarumace ki rufamin asiri kadda jinina ya hau abani gado a asibiti kisa a gano abinda yasani kwanciya.."

"Ah'ah Allah dai ya kaimu kuma in gaya maka na tsumu zakasha mamaki.."

"Habba my Dijama kema kinsan indai akanki ne ni mugun ragone kuma dole shashasha wa..."

Bata bari ya k'arasa ba tayi saurin zura harshanta cikin bakinshi dayake ta faman motsawa daga nan wasan ya canza salo....













*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/14, 2:41 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

38

*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by Dota *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)




*G*anin yabi bayanta zugui-zugui yana gyara sumar kanshi yasa ta jan tunga tana kallonshi cikin mamaki ta shagwab'e tace,

"Ahh! towai bina zaka yine?!"

Komawa yayi da baya kamar wani soko ya zauna yana shafar siririn kwantaccen gashin bakinshi zuwa gemunshi yana mata murmishi yace.

"Ahh! khadija tawa, tona zauna ki ajemin fitsarin cikin wannan murfin in kin gama sai kimin magana shi kenan...?!"

Ajemishi tayi kamin ta mike a hankali jikinta duk ciwo ya keyi jita keyi kamar anyi mata dukan tsiya a jikinta.

Har saida ta zauna gefen katifarsu sannan ya zaro pregnancy test strip d'in (abin gano ciki) ya shige toilet din ya tsoma a ciki, cikin mintunan da basu shige uku ba saiga shi Dr Ahmad yaga positive ya fito a jiki rad'o-rad'o ma'ana akwai hamdala ya fara cikin zuciyar shi kamin ya jefar da abin ya fito waje bakin shi har kunne sabida murna sam ya kasa rufe bakin shi.

Hannuwanta ya kama dukan su ya rike yana kallon cikin idanunta yace,

"Allah yayi miki albarka babyna ina fatan Allah ya baki farin ciki fiye da yanda kike farantamin na gode sosai tabbas ked'in matace ta rufin asiri abar sona tun kafin nakai haka."

Jikin shi kawai ta shige tare da lafewa tana sauke numfashi.

"Uhumm babyna me zakici na siyo miki ko nayi miki ko me kikeso?!"

Yatsina fuska tayi kamin tace,

"Yaya au *Mai ni* bakina babu dad'i nifa bammajin yunwar kwad'ayi kawai nakeji kuma bansan kome nake so ba."

Dariya yayi cikin sauk'i jin saban sunan da ta kirashi dashi kamin yace,

"Ahh babban magana kenan to kiyi hakuri kidai tuno me kike so ko??!"

"Babana! babana!! kufito mana inga jikin gashinan ma waje ana sallama dakai haba kun shiga duk kunyi shiru...!"

Cewar Mama wacce hankalinta yak'i kwanciya tunda taji yace khadija nata amai.

Saurin d'agata yayi daga jikin shi kamin ya temaka mata ta mike suka fita yana rike da ita saida ya zaunar da ita kusa da Maman sannan ya fita wajen inda ake sallamar.

"Sannu khadija me kike so yanzu?"

Cikin alamun sonyin kuka tace,

"Mama nima ban san menake soba, kawai dai banajin dad'in jikina ne."

"Ayya sannu kinji ko zakici tuwo?"

"A'a Mama ina son dai cin shashshaka da yaji da manja harda kayan miya."

Babu kyashi bare ganda kijin haushi cikin murna Maman ta mike kamin tace,

"Alhamdulillah bari nai miki kamin dare yayi sosai ai na iya."

Nan da nan Mama ta hau aiki ta riga ta gano aikin d'anta ne yake son nuna riba (ciki), kafin wani lokacin har ta kammala duk Khadija na zaune suna hira jefi-jefi.

Kayan da suka kintsa waje d'aya wasu matasa suka shigo suka kwashe shima be sami zama ba dan haka binsu yayi zuwa ainahin gidan su domin so yake gobe tun safe su tare a cikin sa.

Ita kuwa khadija tanaci tana bad'a yaji wajan har wajan tara kenan na dare a haka ya taddasu d'akin Maman, murmushi yayi kamin yace,

"Aminu auntyn ka kake tayawa kwad'ayi kenan koh?"

Aminu dariya yayi kamin yace,

"Yaya akwai dad'i fa sosai."

Kallon khadijan yayi kamin yace,

"Toh baby kid'an rage shan yajin kadda kirjinki yayi miki zafi."

Ko kallonshi bata yiba saida ta cinye abinta tas! sannan tasha ruwa tayi gyatsa sannan ta kalli Mama tace,

"Mama saida safe."

Mikewa yayi zai bi bayanta Maman tayi saurin dakatar dashi,

"Dan Allah babana banda wauta kaga bata da lafiya daurewa kawai take yi kaji?!"

Sunkuyar da kanshi k'asa yayi kamin yace,

"To mama insha Allah zan kiyaye, saida safe."

Sallama suka yi sannan yafita daga d'akin cike da mamakin Mama wai yayi hakuri toh wajanwa zashi bayan zainab ta gujeshi khadijan kawai gare shi dan haka sai hakuri kawai. Tuni tajima da hayewa gado dan haka ruwa kawai ya watsa kamin ya dawo kusa da ita ya kwanta yaso yayi wani bin cike amma ya kasa sabida gajiyar dayaji yayi sai dai ya rab'a jikinta ya kwanta tare da rungumeta, ya kai tunanin shi nesa sannan ya barta harya samu yai barcin shima ba tare da wani abun ya had'a suba.

****

Cikin yardar Allah suka koma gidan su a washe gari, sai dai kuma tunda ranar suka rasa kan khadijan sabida masifar laulayi komi taci sai tayi amanshi babu wani kuzari ajikinta kusan duk dare sai ya sakamata drip dashi suke kwana ga matsananciyar bukatarta data addabe shi domin tsawon kwana biyar kenan rabonshi da ita sai dai yasan a yanda take in dai ba k'arasata zai yiba to be kamata ya dame taba dan ita kanta yanzu ta tsani tagama ya rab'eta.

Agogon hannun shi ya kuma kallo laoakcin tara saura na safe har lokacin basu fita ba sabida tunda suka tashi take mai kuka ita tagaji da cikin bata so tunda wuya ake sha, duk ya gigice yama rasa yanda zai yi da ita Allah ma ya temake shi yau asabar.

"Kai Aminu maza jeka ka gano min yayanku har yanzu basu fito ba ko lafiya?"

Yajima tsaye yana sallama sannan Ahmad d:in yace mishi "shigo aminu."

Saida ya gaishe shi sannan yace,

"Mama ce tace inzo in gano ku lafiya taji shiru"

Wani miyau Ahmad ya had'iye kamin yace,

"Jeka ka gamu nan zuwa."

Aminu na fita ya zauna kusa da Mama cikin zumud'i yace mata,

"Mama aunty khadija ce naga tana kuka yanzu wallahi."

Cewar aminu wanda yaba Maman amsa bayan ya koma gareta.

A tsakar gidan suka had'e da Maman domin tuni ta rud'e ta nufosu, cikin damuwa yace,

"Wallahi Mama gata nan kuka kawai ta keyi tunda ta tashi na rasa yadda zanyi da ita."

Yayi maganar yana yatsina fuska cikin jimamin halin da duk suke ciki daga shi har ita.....






*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[3/14, 2:42 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

39

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by Dota *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*I*nnalillahi haba khadijatu toh kuma menene na kuka? kiyi hakuri kinji dama haka ne kowa ce mace da kalar yadda take yin natq laulayin, kiyi shiru kinji ina ke miki ciwo yanzu?"

"Mama babu inda kemin ciwo, kawai dai banijin dad'i ne."

"Toh Allah ya baki lafiya ai kuma yanzu ke dajin dai-dai sai dai idan Allah ya saukeki lafiya sannu."

A bincin su aminu ya jera musu kamin ya fice gidan su khadija sabida sam be san zaman gidan sabida babu abokan wasa amma gidan su khadija akwai.

Cin karo ya kusa yi da ita tafito daga toilet daga ita sai karamin tawul wanda iyakar shi cinyoyinta had'iyar miyau yayi jikake k'uttt kamin ya nufeta yana murmushi mai cike da ma'anoni daban-daban ya sakalata jikin shi tare da cewa,

"Babyna kin k'ara kyau da cika wallahi cikin nan yayi matukar yi miki kyau."

k'okarin zame jikinta ta keyi daga jikin shi shi kuma tuni ya fara sunsunarta yana lumshe idanuwa sabida kamshin sabulun da tayi amfani dashi, daurewa tayi ta biye mishi sabida tasan yayi hakurima sabida yanda yake da zalama tasan sam beda hakuri amma gashi yayi wajan kwana biyar sabida rashin lafiyar da tayi.

Kusan babu kalar shirmen da bemata ba sabida tsabar gigicewar da yayi, jiyayi kamar ranar ya fara saninta sabida irin samun nutsuwar da yayi akanta jikinta yayi zam-zam ta k'ara armashi har ya kasa gane farkon yinshi da na yanzu.

Cikin sanyin murya ya fara mata magana yayin da hannun shi ke cigaba da yawo ajikinta,

"Babyna kin gaji ko?"

"Uhumm..!"

Kawai ta iya cewa sabida gajiyar da tayi.

Ganin tayi shiru yasa shi cigaba da lalubarta da alama sake yi zai yi sabida ba karamin dad'i yajiba yanzu saima ji yayi kamar ya tsokano ma kanshi buk'atarta.

Cigaba da murzarta yayi har saida yaji ta sakar mishi kukan ta gaji sannan ya saura mata tare da rungumeta ajikin shi yana d'an jijjigata jikin shi saida yaga tayi lamo tana sauke nunfashi sannan ya tashi a hankali yana cewa,

"Bari in had'a mana ruwan wanka kinji ko..?!"

Tare suka yo wankan su har lokacin bebar lakud'ar jikinta ba ita ko kasala sai dai kawai tabishi da manyan idanuwan ta farare kal.

****

Sun jima tsaye kofar gidan suna jiran ganin yaron da zasu aika cikin gidan domin sam basu yadda da cewa wai wannan gidan nasu Ahmad bane, domin cikin suma akwai wa in da basu yarda da cewa Ahmad d'in likita bane.

Cikin ikon Allah saiga malam Mamuda zai shiga gidan domin tunda suka tare bezo yayi musu Allah ya sanya alkhairi ba, shine yaga yau tunda asabar ce yasan duk suna gida bari yaje.

Saida sukai kallon-kallon tsakaninsu kamin malam Mamudan ya mika musu hannu sukai musabaha domin shi yaga basu da niyyar bashi hannun da alama dai mamaki ne ya kusa kashe su.

"Kushigo mana kuzo mushiga ai sunanan ciki yau hutun karshen mako har Dr d'in ma nasan yana nan ciki."

Cikin sanyin jiki suka bi bayan shi, yayin da idanunsu keta yawo acikin gidan domin ba wata k'arya aka tsaraba agidan ammafa bak'aramin kyau yayi ba musamman da har yanzu yake kamshin sabon fenti.

Zaune suka taddasu d'akin Maman Ahmad na kusa da Maman shi yayin da khadija ke kwance acinyar Maman Ahmad d'in na mata matsar kafafu ita kuma Maman nata shafar gashin kanta tuni ita tayi barcinta sukuma hira kawai suke abunsu bazaka tab'a gane cewar suruka akewa wannan gatan ba.

"Sannu da zuwa Ahmad d'in da Maman kema malam Mamuda kamin idanun su ya sauka akan wa inda ke bayan shi.

Fuskar Maman babu wata damuwa sai dai tuni ta Ahmad ta canza dan haka komawa yayi kawai ya zauna tare da gyarama khadijan kafafunta wa inda ya sauke daga jikin shi yanzu.

Malam salisu ne ya fara magana cikin alhini da karayar zuciya yace,

"Dama mun zone domin muyi zumunci tunda kun yaddar damu sai kace ba jinin kuba."

Wani mugun kallon takaici Ahmad yayi mishi kamin yace cikin gadara,

"Ahh zumuncifa kace malam? kanaso kuyi shari'a da zumunci a gaban Allah kenan tunda har zaka iya zuwa wajan mu da sunan wai zumunci, koda yake kila ka manta irin korar dabbobin da kukai mana tare da yanke duk wata alaka datake tsakanin mu? kamanta ranar da ka dinga kiranmu da shegu karnuka kuma lalatattu dan kawai munje sada zumunci daku? ka manta ranar da kace mu d'auka bamu da sauran dangi acikin garin charanci sabida kun ruga kun ya femu? kun manta ranar da kuka tasani nida kanina kuka dinga tsine mana albarka da zagin cin mutunci ga mahafiyar mu kuma a gaban idanun mu?

Kamanta ranar da kake furta cewa kune kuka kashe mana mahaifi kuma kani agareku sabida kawai beyi muku d'in kunan daya saba mukuba?

Kun manta kace duk ranar da muka sake waiwayar charanci lallai sai kunyi sanadin ajalina musamman ni danake babba?
a hakan kuke tunanin zamu kuma waiwayarku harmu sada zumuncin?"

Ckin matukar sanyin murya ya furta,

"Ina yawan zuwa charanci ba tare da sanin kuba haka ma Mama sabida inaso inga ko zuciyarku ta sauya kunfara son mu, sai dai kash! kullum baku da aiki saina binmu da mugun kalaima na b'atanci da lalacewa, idan ban manta ba ko wata hudu da suka shige ankama yaronku musa yayima wata yarinya ciki, me kace a ranar? cewa kayi inama me sunan babane aka samu da laifin nan.
sabida haka kunga wannan ya nuna musu malam Mamuda wanda ya zabga tagumin mamaki da tsoran halin mutanen ya hanashi ko motsin kirki, Ahmad yaci gaba, to wannan shine uba agaremu nida k'anina bamu da kowa saishi shine ya tsaya mana haihuwar mune kawai beyi ba sannan daga karshe kun san gatan da yayi min wanda Ku kuka kekashe kuka kasa yimin? nasan baku saniba to wannan d'iyarshi ce ya aura min kamar yadda kukemin fatan inyima yaran mutane ciki to hakan be faruba sabida ya bani d'iyar shi tun kamin ta mallaki hankalin kanta, yanzu haka cikina ne na halal a cikin jikinta kuma ban tab'a shaye-shaye ba kamar yadda kuke min fata, ni _AHMAD BANI DA SAURAN WATA ALAKA DAKU_, dan haka kuyi gaggawar barin gidan nan kamin in had'aku da hukuma."

"Kai Ahmad gidan ku, nace kajiko gidan ku, nace iyayen naka zaka kai ga hukuma dan iya shege to inji kafara kaga yanda zanyi dakai..."

Cewar malam Mamuda da yayi karfin halin yin maganar, itako Mama ai kuka kawai take yi sabida jitai komai ya dawo mata sabo sannan bata tab'a tunanin shi Ahmad d'in ya rike abubuwan da suka faruba a baya ba.

Ahmad da takaici ya kusa kashewa share kwallar idanunshi yayi kamin d'auki khadija cak! daketa barcinta yasab'ata akafad'a yabar d'akin, gaba d"aya suka bishi da idanu domin har yanzu anrasa wanda zai kuma tankawa cikin su, saima sheshshekar kukan Maman dake tashi kadan-kadan cikin dakin.

Sunjima cikin shiru kamin sufara bata hakuri daya-bayan daya, tare da neman gafararta data yaranta duk da cewa sunga rashin sauki dagashi gurin *DR.AHMAD* d'in amma dai suna so ta yafe musu.

Malam salisu ne ya d'ora da cewa,

"Tabbas muncika azzalumai Habiba domin tun tasowar iro muke cutar dashi sai gashi duk da abinda muke mushi hakan besa Allah ya tabar da shiba sai ma yayi mishi d'aukaka sama damu, muna cikin wani hali munsan cewa alhakin kune yake bibiyarmu kuduba irin gidan da kuke ciki babu abunda kuka rasa, muko kullum cikin tashin hankali muke sabida yanzu tun a duniya Allah kefara sakayya dan Allah kuya femana kuyi mana afuwa tabbas masu hali irin namu nanan sunada yawa a duniya, munafatan Allah ya shirya su tunkamin lokaci ya kuremusu kamar yadda muka sami kanmu aciki kuyi hakuri Habiba muntub'a wallahi harga Allah kuma bazamu kuma aikata wani abuba makamancin wannan domin munga ishara."

Saida malam Mamuda yasa baki sannan tace ta yafe, aiko sukai ta godiya tare da cewa zasu kawo iyalansu domin suka waje.


MALAM Mamuda ne ya fara magana cikin farin ciki domin tabbas yajima yana fatan zuwan wannan ranar yacce,

"Tabbas mun godewa Allah daya nuna mana wannan lokaci munafatan Allah ya kuma kare zumuncin shi, gaskiya nayi farin ciki sosai wallahi na tabbata malam ibrahim shima zai yi farin ciki duk da yake kwance cikin k'abari Allah yaji kanshi yayi mai rahma."

Gaba d'aya suka amsa amin cikin jimami.

Malam Mamuda ya d'ora da cewa,

"Tabbas mutane da dama sukan aikata kuskure batare da tunanin kuskurene ba misali zaka sami yaron wani kaita zagi tare da aibatashi da munanan kalamai sai-dai sani ne da ba muyi ba amma a duk lokacin da kai hakan to tabbas mala'iku sukan maido da wa'innan muyagun kalaman ne akan iyalinka, shi yasa sai kaga kaima acikin iyalinka kasami me irin wannan halin koma fiye,

Haka kuma idan kayima iyalan wani kyakykyawan addu'a to tabbas saita sami naka iyalin sabida haka yaka mata mu kula sannan mudaina kullatar marayu domin dayawansu Allah baya tabar dasu kuma tabbas wataran sai kaci arzikinsu Allah yasa mugane.

Sannan ina iyaye masu tsatstsauran ra'ayi akan yaran su? kanada yaro namiji kuma baligi cikakken mabukaci amma ku hanashi aure harsai ya gama karatu ya sami aiki kuma ya gina gida yasai mota tsawon wannan lokacin kasan iyakar zunubin daya kwasarma kanshi? to karka manta kuma iyayenshi akwai naku kason na zunubin domin laifin kune duk wani abu da zai aikata
.
Yima yara k'ana nu fyad'e ya yawaita sabida haka aure da iyaye suke yi sabida wani buri nasu nada ban, yarinya zata nuna tana son aure amma iyaye suk'i yi mata sai tasami me kud'i ko kuma sai tayi zurfin karatu wannan kuskureni domin sha'awa babu abinda baza tasa mutun ya aika taba, misali yanzu shi Ahmad me yarasa?
Babu, itace amsar anyi mishi aure alokacin da ya bukata kuma gashi yayi karatun shi hankali kwance, yanzu inda ba ayi mishi ba mun san iyakar yaran da zai lalata? bamu saniba dan haka yaka mata mu iyaye mu kula tunkamin ranar da Allah zai tirkemu da tambayar yaya muka tafiyar da amanar daya bamu.

Bari muje sallah

Please Login or Register in order to submit comment