Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inbaka gantaba har rasuwa zaka iya yi."

Dariya Ahmad d'in yayi kamin yace "kome zaka fad'i ka fad'a wallahi amma yau a bayan matata zan kwana tunda mungama exam din nan mezanjira toh...!"

Cike da shakuwa suka rabu lokacin misalin sha biyu na rana. Da yaji ya zauna cikin mota daram sannan ya lalubi wayarshi yakira gida, lokacin wayar na hannun Mama ita kuma khadija ta tafi kitso wajan Mamanta. Bayan sun gaisa yake shaida mata gashinan tafe insha Allah kuma d'an wake ya keso aiyi mishi na fulawa.

Cikin murna Maman ta bishi da addu'ar sauka lafiya domin sunyi masifar kewar shi.

"Aminu! Aminu!! kai fito mana."

Cewar Mama bakinta har kunne, sabida tsabar murna.

"Yauwa Aminu na ruga wajan aunty khadija kace ta taho gida idan angama kitson ga mijinta nan bisa hanya ya taho."

Yana fita ita kuma taci gaba da gyare gyaren gidan domin Ahmad sam beson kazanta duk da itama Maman irin matan nanne masu tsafta to amma ahaka sai yaga kamar bemishi ba shi yasa lokacin da yana gidan ya gwammace yayi share-sharen shi da kanshi.


"Mama ki daina d'ura min wannan tsumin wallahi wani lokacin marata har murd'awa take yi kuma nasan zumar ciki kesani jin hakan."

Maman khadija tayi dariya kamin tace "a'a khadija kadda kiyima zuma sharri domin zuma bata da wata illa ajikin mutum saima gyarashi da take yi kedai kawai wani abun ke damun ki, kumafa gata nake miki domin nasan duk ranar da mijinki yadawo to zaki gayama garin ku, shiyasa nake miki tallafi amatsayina na mahaifiyarki."

Duk saida suka mike ganin yanda Aminu ya shigo da gudu yana haki Mama tace,

"kai amma dai Aminu Allah ya shiryeka walahi kamar wanda aka jeho daga sama?"

Cewar Maman khadijan daketa zare idanu domin bak'a ramin tsoro tajiba. saida yayi dariya sannan yace "aunty Mama tace idan angama kitson kiyi sauri kitaho ga mijinki nan bisa hanya ya taho."

Tsalle d'aya tayi ta isa wajan hijabin ta kamin tafara dariyar murna "wayyo Allah na ya Ahmad zai dawo." Maman ta kalleta da murmushi kamin tace "ah lallai khadija ko irin kunyar nan ma babu?"

Dariya tayi kamin tayi mata sallama.

Da zumud'i tayi sallama kamin tace "Mama sanu da gida ashe ya ahmad yau zai dawo?" "eh yanzu ba dad'ewa ya kirani yake gaya min shine nace bari na aika miki koda abinda zaki yi kisanshi da kakale kakalen tsiya, "babu wani datti dakina mama amma dai bari ingani sainazo na tayaki aikin.

Cikin kankanin loaci takalkale ko ina sannan tasaka turaren wuta me dad'in kamshi,.

Koda da ta fita tuni har Maman tagama komai saura dakan yaji dan haka tana dakawa itama tashige d'aki domin yin sallar azahar domin tuni biyuna rana ta wuce.


Saida tai wanka sannan ta d'auro alwala bayan tagama sallarta ta zauna ta tsara kwalliyarta duk da cewa bata yi wata me yawa ba amma tayi kyau sosai cikin riga da siket na atanfa kamshi kawai jikinta keyi gashi anyi asa'a domin kanta yasha kitso.


Suna zaune suna cin abinci yayi sallama cikin gidan. Aminu ya han kad'e kwanon d'an waken shi ya cacumi yayan shi yana ihun murna. D'agashi samayayi yana dariya kamin yace "wai gaskiya kayi nauyi Aminu."

Zama yayi sannan suka gaisa da Maman kamin khadijan ta gashe shi, binta yayi da wani mayen kallo domin gaba d'aya gani yayi kamar sauya mishi ita aka yi.

Bejima ba ya basu tsarabarsu kamin yayi alwala ya fice masallaci domin tuni anfara kiran la'asar.

"Khadija ga abincin shi ki wuce mishi dashi d'aki sannan ki aje mishi ruwan wanka, kinga idan yayi wankan yaci ya koshi sai ya kwanta ya huta ni sai managa duk ya rame."

khadija tace "eh gasiya ya rame Mama kuma saiya kara haske.

Saida ta gama shirya mishi abincin sanan ta had'a ruwan wankan sannanta d'aura alwalarta ta la'asar.

Tun kamin ta idasa sallar ya shigo kai tsaye bakin gadon su ya zauna tare da zuba mata ido.










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[2/26, 9:30 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

25

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO.....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*S*hiru tayi mishi tare da cigaba dacin abincinta sai da taji ta koshi sannan ta kalle shi. murmushi ya sakar mata kamin yace

"khadija tawa ni kadai."

Tashi tayi tayi waje yayin da shima yabita yana dariya, koda ya koma d'aki kiranta yayi tayi har saida Maman tagaji tace wa Khadija,

"Tashi kije khadija inba haka ba bazai bari mu huta ba kita hakuri kinji.?!"

Cikin sanyin jiki ta nufi d'akin, Ahmad d'in ya fara gundurarta sam be son zaman lafiya. Rungume ta yayi ajikin shi zuwa gado, fuskarta atamke sabida tasan sauran zancen.

Ahmad yana cikin jerin maza masu matukar son kasan cewa da mace koda yaushe, shi yasa yanzu daya dawo dinnan ya kejin kamar ya cinyeta domin har yanzu bejishi ya dawo dai-dai ba sabida yanda ya tara bukatar da matukar yawa, duk da cewa ya san yana matukar takurata sai dai bashi da yanda zai yi.


Yinin ranar cikin d'aki sukayi shi sai dai inza shi masallaci yake fitowa itako khadija sam babu lokacin fitowama wajanta, jitake kamar tagudu tabar gidan sabida wahalar da takesha a hannun shi.

Bayan sallar isha'i dasu kaje d'akin Maman cin abinci ko zaman kirki bata iyawa, tsoro ya kama Maman kadda ya lahanta musu yarinya tabani. sosai taci abinci kamin ta haye kijerar Maman tayi kwanciyarta kamin wani lokaci kuwa tayi bacci.

Kallonshi tayi tare da kankance idanu kamin tace,

"Babana naga alamar baka da hankali ko?
baka tunanin kaje kaji mata ciwo, sabida Allah duk irin hakurin yarinyar nan soka keyi dole saika kureta kallifa yau ko zaman kirki bata iyawa to wallahi ka kiyaye ni, na gaya maka tunda kai baka san zuruba, tashi kabani waje."

Cikin jin nauyi ya bar d'akin shi kanshi yasan be kyauta ba domin d'azu da kyar ya samu tayi tsarki sabida zafin da wajan kemata.
gaba d'aya ficewa yayi daga gidan.


Lokacin daya dawo gidan sai yayi sa'a Maman na bayi dan haka kai tsaye d'akin ta ya wuce tare da rungumar khadija wadda keta baccinta cak ya kokarta ya sab'eta.

A gado ya shinfid'eta sannan ya koma ya rufe d'akin, jallabiya kawai ya saka yarab'a gefenta ya kwanta tare da rungumuta cikin shi.


Duk wani hutu da ahmad yazo kusan akan khdijan ya kare domin tuni ta fita hayyacinta duk irin fad'an da Maman keyi da nasiha harta gaji tasa ka mishi ido saida yayi sati uku sannan ya koma school.

Khadija kam har rawar murna tayi ita kanta Maman ba k'aramar murna tayi ba daya tafi. su khadija sun shiga aji biyu yayin da komai yaci gaba da tafiya yanda ake bukata tana samun kulawa sosai wajan Mama haka iyayenta nan da nan ta dawo hayyacinta ta murmure.


Ahmad kuwa ba k'aramin yaki da zuciyar shi yayi ba kamin ya saba da rashin khadijan sai dai kullun suna waya karatu ya keyi sosai da sosai domin burin shi kenan kuma yana son ganin ya tallafama mahaifiyar shi ganin yanda tajajir ce mishi a rayuwa.










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[2/26, 9:30 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

24

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*T*are suka shafa addu'ar sannan ta kalleshi tace, "sannu da zuwa ya Ahmad ya karatu ya hanya?"

Hannuwan shi ya mik'a mata tare da langab'ar da kanshi gefe guda. a hankali ta shige cikin jikin shi, tare suka sauke ajiyan zuciya kamin ya kuma matseta ajikin shi yana sauke numfa shi, jiyake yi kamar bashiba sabida yanda yayi kewarta.

Cikin sanyin murya yake furta "nayi kewarki khadija wallahi kullum sai nayi mafarkinki ashe kin kara girma ko ina na jikinki ya kuma bud'ewa da fatan kinyi murna da ganina?"

Murmushi kawai tayi mashi domin zuciyarta cike take da tsoran abinda yake nufi. Sunsunar wuyanta ya fara yana lumshe idanu yayin da yake kai hannun shi ko ina na jikinta, tanajin jikin shi ya fara kyarma tayi kokarin zame jikinta tare da ce mishi,

"Muje kaci abinci kadda ya sandare."

Tuni idanunshi sun kankance, a hankali yabi bayanta suka koma falon a baki tabashi sabida tsabar sangarta jinshi ya keyi kamar sabon haihuwa duk ci d'aya saiya sude mata yatsu tas sannan ta kuma debowa gaba d'aya ya gama shagala tun wajan cin abincin da kyar tasamu yayi wankan, ko mai be shafa ba yajata gado jikin shi har rawa yake wajan cire mata riga, masha Allah ya furta ganin yanda kirjinta ya bashi sha'awa tuni ya liketa a jikinshi kamar an lik'a mata cingum, murzarta yayi sosai ba tare daya nemi hakkin shiba, wannan tana jin dare akayi mata.


Sai kusan magriba sannan ya kyaleta tasamu sukunin fitowa waje lokacin tuni Mama tanata kwasar tuwonta.

"khadija! khadija!"

Turo bakinta ta yi tana yin kunkuni, Maman ta kalleta kamin tace "khadija me yasa hakane mijinki nata kiranki amma kinyi shiru wallahi babu ruwana."

Xikin shagwab'a tace "To Mama yanzu mafa da kyar ya bari nayi sallar isha'i ni wallahi nagaji kirjina ma ciwo ya keyi min."

Cikin lallashi Maman tace "haba khadija kidin ga hakuri mana kibashi lokacinki sabida Allah yaushe rabon shi da gida? kuma ya dawo amma harkin fara maganar kin gaji to wallahi kisama ranki hakuri da juriya domin mijinki ba hakuri gareshi ba, kuma dai dole gunki kadai zai iya bankad'e sirrin shi garama kiyi hakuri kita shi niban masan zaman me kike minba nan tunda kinci kin koshi."

Bakinta a dane ta tashi tafice, tana fita taji yayi sama da ita, ashe dama yana tsaye kunyar Maman ta hanashi shiga cikin d'akin. Kai tsaye gado ya direta yana murmushi, itako tsabar tsoro jitake kamar ta tsala ihu.

Rungumarta yayi yana shafarta aiko jikinta ya kama kyarma cikin muryar kuka tace "dan Allah kadda ka kasheni." cikin jin tausayin ta yace "bazan yi miki irin na watannin baya ba amma idan kinsaki jikinki dani fa."

********

Karad'in Aminu ya tashe shi daga daddad'an barcin da ya keyi, mika yayi a hankali tare da cire khadijan daga jikin shi, fuskarta ya kalla duk busassun hawaye murmushi yayi kamin yace "rigimam miya kawai."

Shiryawa yayi cikin farar jallabiya ya nufi d'akin Maman, saida suka gaisa sannan ya fara karyawa kunun tsamiya yau tayi da alala. yana ci suna hira inda take cewa "babana bawata matsalako sai naga dukka rame?"

"Babu wata matsala wallahi kewarku kawai kedamuna kuma kinga ga karatun ya fara mikawa."

"Toh Allah ya temaka suma su khadija ina ga daga wannnn hutun zasu shiga aji biyu.."

"Eh haka ne kam, Aminu yana karatun sosai ko Mama?!"

"Yana yi sosai kam aika san beda wasa."

khadija ce tayi sallama ta shiga cikin shirinta cikin doguwar riga ta kanti, babanta ya siyo matasu da yawa daya je kano.
Maman kawai ta gaida ta jawo abin karinta domin wata almirar yunwa takeji sosai. Tunda tashigo d'akin ya fita nutsuwar shi musamman kamshin dake tashi ajikinta, Maman tana kallan shi ita mamakin Ahmad d'i yake bata, oh zamani sai kaga yaro kamar besan komaiba amma sai kaga ba hakaba.

Tana d'ago kanta suka had'a ido harara ta wurga mishi hadda murgud'a baki. dariya yayi kamin yace "Mama d'iyar ki na hararata fa."

Tashi tayi ma tabar musu d'akin tana dariya, dawowa yayi kusa da ita tare da yimata rad'a akunne "kisauri kici ki koshi muje ki sallameni."

Ya idasa maganar yana murzar gashin kanshi tare da yin wani makirin murmush.










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[2/26, 9:30 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

26

*NA MANAN KHADIJA*🙇‍♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)


*BAYAN SHEKARA UKU*

Tafiya sannu sannu kwana nesa, haka dai hausawa suka ce, wannan batu haka yake.

Cikin sa'a bayan sun kammala karatu da sati d'aya federal government ta biyawa mutum biyar karatu zuwa k'asar waje Allah yayi kuma harda Ahmad a cikin su, farin ciki da murna kuwa ba'a cewa komai domin yaji dad'i yasan zai k'ara samun ingantaccen sani akan aikin shi da kuma san cika burinshi na zama cikakken likita ya dinga jin ana kiran shi da *DR AHMAD* mijin Nana Khadija.

Cikin tsananin murna da jin dad'i ya shirya kayanshi suka yi sallama da abokinshi kuma aminin shi Hamza ya wuce tasha ya hau mota sai gida, yasan tabbas zasu ji dad'i gabaki d'ayan su ta yadda suke matukar son ganin ci gaban shi.

Bayan ya sauka yaje gida ba k'aramin murna sukayi ba, Khadija kam murnarta harda d'ar-d'ar dan tasan Yaya Ahmad d'inta babu kawaici bare tausayi ita kullum addu'arta Allah ya yaye mai wannan yawan bukatar yasa idan yana karatu ya gano abinda zai sha ya rage wannan sha'anin dan kam ita tana wahala dan ma Allah yayi mata lud'ufi bata bushewa da saitafi shan wahala.

Saida yayi kwana biyu sannan ya shirya ya tafi gurin Mama akan bayanin tafiyar shi dan dama cewa yayi sai ya huta zai fad'a musu. Sai da ya gama kwarara bayani yaji Mama tace,

"Babana katashi kabani wuri wallahi zan sab'a maka yanda baka tab'a tunaniba akan maganar nan, nadai gaya maka." cikin sanyin jiki ya tashi ya bar d'akin kai tsaye gidan malam Mamuda ya wuce, aiko yayi sa'a domin azauren gidan ya gamu dashi yana niyyar barin gidan.

"To toh malam Amadu ne tafe yanzu shigo to ai da fita zanyi d'azu Aminu kece min ka dawo ina fatan lafiya?"

Cewar malam Mamuda dake ta washe baki cikin jin dad'in ganin Ahmad d'in.

Bayan sun gaisa ne, malam Mamuda ya d'ora da cewa "ya na ganka duk a hargitse ne lafiya dai ko?"

Cikin raunin murya Ahmad ya fara magana, "baba dama kasan tun kwanaki da muka gama jarabawa mun samu munyi piratical to yanzu na samu sa'a ina cikin wa inda gwamnati da d'auki nauyin karatunsu zuwa k'asar waje inda zan samu in fito a cikin manyan kwararrun likitoci shine mama taki tun awaya nayi mata bayani amma taki yauna dawo d'in befi saura sati ayi tafiyar ba amma taki nikuma inaso tunda dai cigaba ne."

"Ashsha ashsha gaskiya abu beyi dad'i ba ita habiba me zaisa tayi haka tashi muje gidan kaji insha Allah zaka yo wannan karatun ai cigaba ne abunda wasu ke nema..."

fuska ta kuma had'ewa ganin sun shigo tare tasan maganar kenan. malam Mamuda yayi dariya kamin yace "kima saki fuskarki wallahi domin kin san baki da gaskiya."

Zama yayi kamin itama ta zauna Ahmad ya rab'a gefen malam Mamuda d'in ya zauna.

"Yanzu sabida Allah habiba kin kyauta kenan yaro ya samu cigaba amma kina nema kimishi bakin ciki?yo bakin ciki mana in ba haka ba mutane nawa ke neman tafiya inda yake so sabida Allah shine shi Allah ya temake shi ya dubi maraicin shi yaba shi zaki hana shi tafiya?"

Cikin damuwa tace "A'a malam nifa ba haka nake nufiba, nigani nayi ya zauna nan yayi karatunshi yafi kwanciyar hankali kasan dai yanda tarbiyya tayi wuya kana ta yaroma ya ya aka kare balle yatafi wata uwa duniya."

"Toh ke habiba banda abinki ai ko ina Allah ne ke tsarewa bawai dabarar muba, kedai kawai kibishi da addu'a sannan ki kyautata mishi zato insha Allah babu wata matsala da kike tunani. kai kuma sai ka kiyaye kayi abinda ya kaika kawai ka dawo kadai gani mahaifiyarka bawani so take ba dan haka dan Allah kadda ka dawo mana da wani sabon abun."

Cikin jin dad'i Ahmad yace "insha Allahu zan ki yaye baba."

*****

"Mama sannu da gida na dawo."

"Yauwa khadija sannu da dawo wa ya makarantar?"

"lafiya lau Mama."

'Daki ta nufa tuni ta yaki ce hijabin sabida zafi. Da gudu ta yadda jakar tare dayin tsalle ta makalkale Ahmad dake tsaye yana neman kayan da zai saka. juyowa yayi tare da yin dariya cikin jin dad'i tace

"Yaushe ka dawo ya ahmad kuma fa sam baka gaya minba gashi da safe munyi waya da kai."

K'arasawa yayi da ita gado yana karemata kallo gaba d'aya ta canza domin tafara zama budurwa kyakykyawar surar jikinta ta fito. zama yayi a gado kamin ya d'orata saman cinyar shi yana warware tufkar data yima gashinta.

Tashi tayi ta shige toilet domin watsama jikinta ruwa sannan ta fito d'aure da alwalar sallar azahar. kwance ta ganshi yanda ta barshi murmushi kawai tayi tare da canza kaya ta kabbara sallah. kamin ta gama Mama ta aiko mata da abincin ta dan haka yana kwancen nan taci ta koshi sai dai kusan hakalinta nakan shi mamakin girman shi take yi domin gani take yi kamar sauya shi akayi.

Kamar yadda shima ana shi b'angaren ya keta mamakin yanda ta koma saidai yana cikin godiya ga Allah daya bashi ita amatsayin mata.

"Babyna zomu gaisa mana baki ga ko kaya na kasa sawaba tunda kika shigo?"

Dariya tayi tare da hayewa jikin shi saida numfashin shi ya kusa d'aukewa lokacin da yacire rigar jikinta nan da nan ya rud'e ya fara mata sambatu "oh baby na kin girma da yawa yaushe kika koma haka?! i missing you baby."

Kamin wani lokaci Ahmad ya koma sambatun kauna😃. babu wanda ya kumajin duriyar su sai wayewar gari da khadijan tafito cikin shirin makarnta a tsitsaye suga gaisa tare da karyawa domin takusa makara.

Cikin satin ya gama duk wani shirin shi dan haka lokacin da tafiyar ta tashi tayi sai ya tafi bayan jan kunne da nasiha kala-kala daya sha daga bakin iyayen shi musamman Mama wadda kasashen waje bawani yi mata suka yiba. Daga haka ta wuce ya tafi suna tayi mai fatan alkairi..








*MAMAN KHADIJA*🙇‍♀
[2/26, 9:35 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

27

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)





*R*ayuwa takan juya a hankali-a hankali komai ke tafiya wataran da dad'i wataran babu dad'i sai dai dole mu amsheta duk yadda tazo mana.

*BAYAN SHEKARA HUDU*:- Matashin saurayi ne zaune cikin turawa yana duba wayar shi kyakykyawa ne sosai domin kuwa farar fata kawai turawan dake tare dashi zasu nunamai amma fa badai zallar kyawu ba. sallama yayi musu tare da shigewa cikin d'akin da yake mallakin shi tun zuwan shi kasar amatsayin sa ns d'alibi.

Alwalar sallar magriba ya d'aura, saida ya gabatar da sallar, yana zaune har lokacin isha'i ya shiga ya d'orata sannan ya haye gado kewar gida ce ta ishe shi ya gaji da zaman fatan shi guda d'aya ne su idasa gama jarabawar nan ya koma k'asarshi ta haihuwa.

Wayar shice tayi ring kamar bazai d'au kaba sannan ya d'aga ba tare daya ce komai ba. Saida ta sauke a jiyar zuciya kamin tace "haba Ahmad me yasa baka jin tausayina kullum kokarin ka ganin kasani cikin tashin hankali kake wallahi ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba a cikinta ba dan Allah kayar da ka aureni koda baka sona wallahi zan iya zama da kai...."

Saida ya wani tab'e bakin shi kamin yace "zainab nifa bawai son kine bana yiba na gaya miki inada mata ko?"

Cikin sanyin jiki tace "eh ka gaya min."

Yace "to kinga bazan b'oye miki ba sannan ni maraya ne bani da mahaifi dagani sai mahaifiyata da kanina sai kuma matata, muba wasu masu kud'i bane hasalima bamu da komai sai rufin asiri kekuma d'iyar me kud'i ce amma in kinga zaki iya to babu matsala....!!"

Wani miyau ta had'iye kamin tace "ina sonka sosai Ahmad zan iya hakura da komai in dai zan sameka." Murmushi yayi kamin yace "ina cikin jinsin maza masu tsananin bukatuwa Zainab shima kin amince zaki aureni a haka?"

Jimmm tayi kamin tace "karka damu na amince in dai zaka aure ni zan jure maka."

"Kin yarda babu wani shagalin biki da za ayi idan mun tashi aure? domin bani da kud'in da zanyi su...."

"Na amince ahmad."

"Toho shikenan ki kwanta kiyi baccin ki gobe zamu had'u a school."

Sallama suka yi kowa ya kashe Ahmad na tunanin yadda Khadija zata ji idan taji cewar zai k'ara aure..

Cike da farin ciki ta kwanta yayin da shi kuma ya fad'a duniyar tunani, yasan kam zainab babbar yarinya ce domin iyayenta masu kud'i ne sosai a cikin garin funtuwa, itama karatu ne ya kawota k'asar kamar yadda yazo, Ahmad yana son babbar mace daga baya-bayan nan musamman yanda yake ganin surar ita zainab d'in tana da komai na cikakakkiyar budurwa tafi khadijan shi girma nesa ba kusa ba duk da cewa shekaru biyu da suka shige yaje gida kuma yaga yanda khadijan nashi tayi girma sai dai yana da burin ya kuma yin wani auren da gumin shi idan ya sami dama ya auri 'yar boko wayayya mai ji da kanta, sai gashi zainab ta shigo cikin rayuwar shi, kusan babu kalar hantara da kyarar da bai nuna mata ba amma ta nace mishi, sai gashi daga baya har yana kulata kuma bugu da kari shine yana matukar son ganin yaranshi shima, yayi mamakin da khadijan shi sam bata sami ciki ba har yanzu domin ko al'ada ta keyi to ranar data gama a ranar yake kusantarta dan kawai yaji ta samu ciki sai dai shiru kakeji wannan dalilin ya sanya tsoro ya d'arsu a cikin zuciyar shi na kodai beda lafiyane sai dai zuwan shi k'asar nan yasashi ganin wani likita ya gaya mishi lafiyan shi kalau sai dai in matar ta shice bata da lafiya, daga lokacin Ahmad ya fara d'aura d'amarar k'aro aure koda Allah zaisa yaga yaran shi.

Juyawa yayi ya kuma juyawa tare da gyara kwanciyar shi, wayar shi ya laluba tare da kiran number khadija, sai dai harta gama ringing amma bata d'auka ba dole ya hakura yayi barcin shi.

******

A bangaren khadija kuwa ta girma sosai domin a yanzu tanada kusan shekaru goma sha shidda, duk wani kyawunta da dirin jikinta ya gama fitowa bata da wata matsala ta iya komai na kula da miji gamida zaman gidan auren kusan ta haddace komai daya kamata ace tasani, domin Mamanta da Maman mijinta suna matukar kula da duk wani motsinta, tana zuwa islamiyya ta matan aure da ahmad d'in yasa mahaifinta yasa kata, sannan tana zuwa ta bokonta tunda gashi har sun shiga ss3 an zama 'yan mata. tana son mijinta fiye da yanda zan yi muku bayani domin Ahmad abin sone yana da kula sosai musamman akan abinda ya keso, kusan duk dare suna tare dashi a waya, kullun burinta taganta jikin mijinta tayi kewarshi sosai da sosai a b'angare guda kuma ga mugun kishin shi da take yi fatanta kawai kada Allah yasa ko magana da mata ya din gayi.
kullum lissafin ranar dawor shi take yi, kaika ce bitar karatu take yi..









*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
[2/26, 9:35 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

29

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀

Edit by *Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



Leb'unan shi ya lashe tare dabin khadijan da lumsassun idanun shi wadda ke tsaye tana ciro mishi kayan da zai saka idan yayi wankan cikin sanyin murya tace,

"Ya Ahmad ga ruwan can na had'a maka."

Mikewa yayi ya isa jikinta tare da rungumeta ya fara sunsunar gashin kanta da wuyanta hannu wanshi kuwa tuni sun jima da fara yawo ajikin ta muryar shi a shak'e yake furta "babyna kin girma da yawa kin zama babbar yarinya ki gaya min meye sirrin?"

Dariya tayi tare da zame jikinta daga nashi tace "kai mafa kayi girma tunda harka fini kalli furkarka ga saje ga gemo, sannan kakusa ninkani tsawo ma, kuma ji kirjinka kamar me koyon karfi komai na jikinka ya kara girma da yawa..."

Dariya kawai yayi tare da kwab'e kayan shi ya shige bayin ita kuma ta kwashe kayan tare da gyara wajan.

koda ya fito tuni harta gama shirya mishi abinci acikin falonsu,

Please Login or Register in order to submit comment