Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naji duk na tsane shi musamman dana sami cikin nan ga laulayi ga lalurarshi da wanne zanji?!"

Dariya khadijan tayi kamin tace,

"Zan baki shawara guda d'aya kacal fatima, shawarar itace kimaida kayan marmari abincinki sannan ki dirfafi dafa zuma da mazarkwaila da kanunfari kinasha insha Allah zakiji wani lokacin da kankima kinaso, nikam bana huld'a da duk wani abu mesunan maganin mata amma nasan nafi karfin wulakanci ga mijina wallahi dan haka kikama mijinki tunkamin ya fara gajiya da gardamar da kike mishi yafara hango na waje inbe auroba ya bisu watarana. kinga ni yanzu bani da wata damuwa kullum cikin godema Allah nake da iyayena domin sunyi min babban gata..."

"Hakane wallahi nagode sosai khadija insha Allahu ni kuma zanyi amfani da duk shawararki na gode da tarayyarmu Allah ya raya mana Abba ya barmu tare da aminci."

"Kai ga mayen mijinki nan yazo khadija.."

Cewar fatima wadda ke nuna mata Ahmad daya faka motarshi daga nesa dasu.

Rungumarta yayi jikin shi tare da sunbatar goshinta sannan ya d'aga ma fatima hannu, tana like jikin shi ya bud'e mata motar saida ya zaunar da ita sannan yaza gaya ya shiga shima sukai gida babu ruwanshi da yawan mutanan dake kallonsu.

Bayan shekara biyu

Rayuwa tayi mawa in nan bayin Allah dad'i hankalin su kwace masu dana sani sunyi danasanin su damma Allah ya temake su sunyi kamin kasa ta rufe idanunsu, Abba ya girma sosai ga surutu kamar redio haka ga wayo sannan ga khadija da wani cikin, kullum cikin godema Allah suke domin babu abinda suka rasa ya rufamusu asiri lokacin da mutane suka so tona musu shi yasa ake son ka zab'i rufin asirin Allah bana mutum ba.

Dama dai ita rayuwa haka take yanda ka dauketa haka take zuwar maka inka kyautata niyyarka sai Allah ya cika maka inko kayi sabinin haka sai Allah ya barka da shaid'an ya taya ka jan ragamar zuciyarka Allah ya karemu daga sharrin zuciya amin.


_Duka-duka anan na kawo karshen wannan labari nawa me suna *DR.AHMAD*, Ina fatan inda nayi dai-dai Allah ya bani lada inda kuma nayi kuskure Allah ya gafarta min domin d'an Adam munsan kullun cikin aikata zunubi muke sai dai Allah ya ya femana Albarkar soyayyar shi da ANNABIN RAHMA (s.a,w)._

*SHARHI*

JIGON LABARIN DR. AHMAD SHINE.
Babban dalilina na kawo wannan labari shine, domin yiwa iyayen mu tuni akan amanar da Allah ya bamu, domin awannan zamanin ana yawan samun wannan matsalar, zaka ga k'aramin yaro da matsanciyar sha'awa amma babu kula daga iyayenshi har shi, shi yasa yanzu fyade da zinace-zinace suka yawaita.

Yaro zai nuna yana son aure amma iyaye su hana sai suce wai wani duka nawa yake da zaice aure zai yi? Kunsan dalilinshi na cewa aure zai yi? Idan baki saniba ke uwa kai uba kuna damar zaunar dashi ya sanar muku kuji sai ku magance mishi idan ba haka ba zakuji kunyar duniya kuje lahira ma kuma ku karb'i sakamako.

An yi a kusa dani nagani ganin idona inda iyaye suka hana yaronsu aure yanada shekaru 27 suka ce sai ya gama karatu yazo yayi suka ce sai ya sami aiki ya gina gida, kundai san yanzu samun aiki a Nigeria yanda yake be samu ba tsawon lokaci, 'yan mata biyu yayi ma ciki sannan ya gudu yabar iyayen kunga wa gari ya waya sunyi dana sani lokacin da babu amfani. Toh akwai iyaye da yawa masu wannan burin dan haka gara mu gyara tunkamin lokaci ya kure mana domin bako wane yaro bane zai yi tunanin tsare kanshi daga halaka ba kamar Ahmad, suna ganin da suyi azumi gara suyi zina da hannuwansu ko subi wata hanyar mummuna kanacan kana cewa wane yaron kirki babu ruwan shi kaza-kaza baki san me yake aikatawa a waje ko a d'aki ba, Allah ka shirya mana zuria ka tsare manasu.

Sannan sai ZAINAB,
Ta shigo gidan Ahmad amatsayin kishiyar khadija, to wannan wata kaddara ce da zata iya fad'awa akanki a kaina, mata da yawa bama san kishiya sam sai dai muna mantawa da rubutaccen Al'amari daga Allah wanda idan mijinki aure goma zai yi toh fa sai fa yayi shi ko kina raye ko kina mace duk kwalliyarki duk kyawunki duk dirinki duk nutsuwarki duk biyayyarki idan Allah yayi toh sai kin samu abokiyar zama.

Sannan wani shirme domin wannan dole akira shi da shirme da yawan mu zamu taso gidan mu muga mahaifinmu da mata biyu uku hudu, kilama da wayanki ya saki wata ya auro wata kintaso a irin wannan gidan sannan kizo kice waike bakisan kishiya kuma bazaki yarda da ita ba, wannan wane irin tunani ne? BABU kalar surutun da banjiba daga mutane lokacin da Ahmad ya auri zainab nayi mamaki sosai wallahi domin na san akwai babban aiki a gaban mu matukar haka tafiyar zata kasance, akwai ma wadda naji tace ita book in dai da kishiya bata karan tashi to me yayi zafi haka? zaman duniya ne bawai na kiya maba shekaru kalilan kike jira k'asa ta rufe idanun kifa A haka zamuje ma Allah da mummunan k'uduri ga 'yan uwan mu? Kuma wata kilama mahaifiyarka a ta biyu tazo ku itace ma ta hudu kuma ta shiga har aka haifeki amma ke kin hana wata ta shigo kuma idan 'ya'yanki duk mata ne kuma duk masu zuwa gurinsu suna da aure gashi suma na gidan sunce baza'ayi musu kishiya ba ki gyamin ya zakiyi da yaranki kuma suna son aure? Muyi tunani muyi ma kanmu adalci da hallaci dan Allah.


SANNAN SURUKAI:-
Da yawan mu yanzu bamu son auren wanda iyayen shi ke a raye musamman uwa mace, menene ya jawo haka?

Amsar itace mugun hali na zalinci sa ido da kuma wulakanci da wasu surukai suke gwadawa matan 'ya'yan su, kada mu manta daga lokacin da yaronki yayi aure tofa duk wani hakkin wannan mata tashi ya bar wajan iyayenta ya koma kanshi kinga hana warki yayi mata wani abu ko kyautatawa kamar kin sashi sab'ama Allah ne dan haka ki saurari hukuncinki wajan Allah domin shine ya tsara komai tun kamin zuwanki.

kudu ba kuga yanda Maman Ahmad ta rike khadija wanda daga karshe saida khadijan ta koma bata son Maman taje konan da can sabida son da take mata. kowace uwa tagari nasan baza taso akunta tama na taba tofa tunda bakiso kema kadda kifara yima d'an wani.

MALAM MAMUDA:-
Malam Mamuda yayi halacci kuma yarike amanar makota sannan ya fara ganin saka mako tun a duniya.

Eh mana tunda gashi Ahmad ya d'auke mishi dawainiyar komai sabida halaccin dayayi mishi kamin yaje wajan Allah yasamu saka mako me kyau domin yayi aiki me kyau na toshe wata kafa ta b'arna, sannan matar shi taba shi goyan baya inda ta toshe kunnuwanta daga dukkan wani gulmace-gulmace da mutane suka yita jifanta dashi.

GA KHADIJ KUMA:-
Khadija itace tauraruwar labarin dan Allah banda cigaba akwai wani na kasu data samu a rayuwarta? amsar itace babu taga ranar biyyayya dan kuwa gashinan tana karatunta tana da mijinta na nunawa sa'a sannan ga albarkar aure da Allah yaba su, kaddafa mu manta da yawa akwai iyayen mu da akaima aure tun basu da wayan kirki kuma suka zauna qalau, amma yanzu sai yarinya tayi shekaru akalla 20 kuma kuji iyayenta na maganar bata isa aureba toma idan zina batai yawaba meye zai yi yawa? abarshi a kunaso tayi karatu! karatu bawani illa bane dan tayi amma me ku aurar da ita sannan taje makarantar shifa aure daraja ne dashi wa innan igiyoyin da suka hau kanta sai kuga sanadin ta tasamu nutsuwar yin komai.

*DR.AHMAD*
Gaba d'aya labarin na shine mutane nata maganar jarabarshi tacika yawa, to wallahi kunji na rantse akwai mazan da suka fishi tsananin buk'ata kuma sunada yawa sosai acikin maza. sabida haka ni banga wani abun mamakiba dajin labarin Ahmad ke dai kawai amatsayin ki na mace kiyi addu'ar Allah ya baki miji dai-dai da yanayin bukatarki harda masu cewa wallahi babu masu irin wannan yawan buk'atar toh kuje da rantsuwarku amma mudena saurin rantsuwa akan abinda bamuda sani akai.

*ANAN NI MAMAN KHADIJA nake muku fatan Alkhairi ina fatan zaku tayani da addu'ar Allah yasa na haihuwa lafiya na gode sosai.*


*TO YOU HAJJA CE my hajja, Dota hajja nagode sosai da temakonki gareni domin kece me gyaran kusan dukkan kurakuran da ake samu a ciki da kuma rubutun, toh kundai san mace me ciki😃sai a slow na gode sosai may God bless you and jikata ihsan.*

_Sai kuma ke! Na gode da kulawarki da adduarki gareni Mamana ta kaina Maijidda musa Allah ya barmu tare._

*KUNGIYATA ABIN ALFAHARINA HASKE WRITER'S ASSO*
Allah ya kareku ya k'ara muku basira da hangen nesa Maman Khady na yinku Allah yabarmu tare

_Ummi Aisha, phatymah Zarah, Hajja ce, khaleesat hydar, miss Xoxo, billy galadanci, Aisha d/sabo, safiyya Huguma, Asmy b Aliyu, Afrah bhai, Faxyfation, Nana diso, Feedohm, Nuceeyluv, Ayusher Muhd Allah ya kara had'e kanmu_🤝








*MAMAN KHADIJA*🙇🏻‍♀
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment