Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yayi wonka da ruwa mai sanyi sannan yaji jikinsa ya yi masa daɗi.
Da sauri ya fito ya fara shirin zuwa masallacin masarautar don har sun fara kiran assalatu.

Bayan sun idar da sallan acan ya yi zamansa don gabatar da azkar da sauran addu'o'in da yake gabatarwa a dai-dai lokacin, sai da gari ya yi washe sannan ya dawo ya wuce falonsa kai tsaye.

Da hantsi ya fito daga falon. Cikin shigarsa ta yau da kullum.
A nan ya taradda su ita da Ummi suna zaune.
Da alamun Ummi nata lallashinta akan ta yi breakfast ne.

Tsayuwa ya ɗan yi gefensu tare da cewa.
"Ummi yunwa".
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Dama yanzu nakeso Aysha taci, sai ta kai maka nakan."

A hankali ya ɗan yi taku biyu zuwa uku, ya kana ya zauna bisa kujerar dake fuskantar tasu.
Ido ya ɗan zuba mata, tare da jingina kansa jikin kujera.
Cike da wani irin mayataccen shauƙi.

Ita kuwa Aysha yatsun sawunshi ta zubawa ido, tare da shaƙan ƙamshin turaren jikinshi dan tun da ya shigo daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika wajen har sai da Aysha ta lumshe ido, Allah ma ya sani tana masifar son ƙamshin turarensa.

Idonshi ya ɗan buɗe tare da ƙanƙancesu kana ya tsira mata su yana kallonta, a nutse sai kuma yayi wani gajeren.
Murmushi cikin nutsuwa da jera kalami yace.
"Me zai sa ace ba za a ci abincin safe ba? bayan kuma shi ya fi kowanne amfani a jikin ɗan adam?".
Kallon shi ta yi tare da kwaɓe fuska kana ta ɗan tura bakinta tare da fara magana ƙasa-ƙasa can cikin maƙoshinta.
"Dama ba dole kace haka ba, tunda kai ne sanadiyyar ciwon, kuma ba ajikinka yake ba." Ummi dake gefenta ta jita sarai duk da ba kalmomin duka ta ji ba amma tasan abinda take nufi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer lumshe ido ya kumayi tare da sauke sassayan numfashi kana ya buɗe idon ya zubasu kan bakinta.
Kallon bakinta yayi ba tare da ta gama haɗe lips ɗintaba yace.
"Kika ce kin yi yajin cin abinci?".
Ya faɗa da zolaya duk da ba halinsa ba ne, ba kuma ɗabi'arsa bane.
Shima kanshi bai san ya aka yi zuciyarsa ta raya masa faɗin hakanba.
Lips ɗinsa ya ɗan laso da harshensa lokacin da yaji tana cewa.
"Uhmm ni ba haka na ce ba."
Gyara zamansa ya yi yana mata wani irin kallo mai cike da fassara, kallon nasa ne ya sa mata mutuwar jiki da kasala, don sai da ta ji wani iri a jikinta sabida wani irin kallone mai tsada da masifar ratsa jiki da zuciya.
Shi kuwa cikin tsareta da idon yace.
"Uhumm to muna jinki Aaaaishhh!".
Kiran sunanta da yayi da wata siga haka ya sa ta ɗago kai ta zuba mishi ido.
Sai kuma ta kauda kanta da sauri tare da sauƙe numfashi,
kwarjininsa ne ya cika mata ido sai wani Murmushi mai tsada da yake mata.
Cikin narkekkiyar murya tace.
"Cewa na yi na ƙoshi."
Ta ƙarashe mgnar tana kauda kai aranta tana jinjina kwarjini da haiba irin ta shi.

"Yarinyar goye a ke yiwa dole ta ci abinci fa, ko kema sai Ummin ta goyaki zaki ci? Tunda naga nima mancewa sani takeyi sai ke".
Dariya Ummi tayi tace. "Idan zata ci sai na goyata".
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai ƙasa tana nanata zancensa wai agoyata.
"Yi haƙuri ki ci abincin kin ji." ta kuma jin muryarsa a bazata.

Janyo flask ɗin yayi gabanta,
flask ɗin ta ɗan kalla tana jujjuya kwayar idanunta, cikin ranta take jin kwarjininsa ke yi mata barazana da ta ji shakkarsa, ban da haka ba zata iya shan da ruwan zafi acikinta ba sabida ɗazu da sassafe Ummi ta sata cin sauran naman ji data ɗumama mata.
Sama-sama a haka ta ci abincin da ɗan yawa duk da bata so cinsa ba.

Tana gamawa Ummi ta kwashe kayan kwanukan, shi kuma Sheikh ya wuce falonsa.

Yana shiga Jamil ya shigo, shi da Juwairiyya, zama suka yi suna hira Ummi ce ta ɗan kalli gefen da Aysha ke zaune tare da cewa.
"Yauwa Aysha tashi ki kaiwa Sheykh abincinsa".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummi bawa Jamil ya kai mishi".
Sai kuma ta kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil ɗauki ka kai mishi".
Ta ƙare mgnar tana ɓoye ainihin tsoron sake shiga inda yake da takejin.
Murmushi Ummi tayi dan ta ganota, tray'n ta miƙawa Jamil dake cewa.
"Ummi kawo dai in kai dan ke".
Murmushi sukayi, kana shi kuma ya kai mishi sannan ya fiti.
ba su daɗe ba Yah Ja'afar ya shigo shi ma ya zauna kusa da Jamil nan suka ɗan ci gaba da hirarsu

Haka dai sukayi wunin wannan.
Ranar cikin farin ciki suka yini don anan falon suka ci abinci dukansu.


Da daddare ba yanda Ummi ba ta yi da Shatu ba akan ta kaiwa Sheikh abinci ta ƙi, sai da kanta ta kai masa.
Don Aysha tsoron zuwa ɓangarensa take, saboda har yanzun tana jin jiki.

Washegari ma da safe Ummin ce ta bawa Jamil ya kai masa, don fir Aysha ta ƙi zuwa.

Bayan yayi wanka ya fito, ya shafa mai ya kimtsa cikin wani tattausan yafi boyel mai taushi da kyau, Sky blue ne sai aikin da akayi mishi da farin zare sosai yayi kyau sai ƙamshi yake zubawa.

A haka ya fito falonshi
breakfast ɗinsa Wanda yana kimtsawa ya jiyo muryar Jamil ɗin na ce masa ga breakfast ɗinka Hamma Jabeer.

Zama yayi bisa kujera, yana mai mgnar zuci. "Rabon Aiiish da side ɗinna tun shekaran da safe yau kwana biyu kenan ana na uku rabon data shigo nan". Murmushi mai yelwa yayi wanda bai san dalilinsa ba.
"Uwar raki da tsoro".
Ya faɗi a fili lokacin da ya fito babban falon ba kowa a falon haka yasa ya wuce yana girgiza kai ya wuce dan sauri yake Asibitinshi zaije.


Bayan ya shiga asibitin ɗaki ɗaki ya bi duk marasa lafiyan ciki suna gaisawa tare da basu taimako na musamman yana duba lfyarsu wanda dama hakan al'adarsa ce kyautawa marasa lafiya, bayan ya gama da shiga ɗakunan suna binsa da addu'o'in nasara da lfy a rayuwarsa.

Ya wuce office ɗinsa don duba outpatient, lumshe ido yayi bayan ya zauna kan kujerar,
Miƙa ya ɗanyi a hankali tare da yin salati.
Gaba ɗaya yanayi shi ya sauya.
Tun jiya yake jinsa cikin wani irin matsi.
Yau kuma tunda gari ya waye yake jin wani abu na fusgarsa a hankali yake dannewa zamansa waje ɗaya ya ji abun na ƙoƙarin son bijire masa, patient ne ya shigo, ya duba sa cikin kulawa tare da ɗaukan dukkan bayanansa ya rubuta masa magani ya fice, kwantar da kansa yayi jikin kujerar haɗe da lumshe idunsa da suka ƙanƙance saboda wani irin feelings yake ji na bin sassan jikinsa a haka ya duba dukkan patient ɗin sai gab da magriba ya bar asibitin saboda hadari da ya fara haɗuwa alamar za a yi ruwan sama.

Direct masarautar Joɗa wuce.
Yana shiga cikin masarautar kai tsaye Masallaci ya wuce don yana shiga cikin farfajiyar gidan aka kira salla.

Bai fito daga masallacin ba, sai da aka yi sallan isha'i sannan ya fito ya nufi gida.

Sosai yake jin wani irin masifeffen feelings mai shegen fitina yana bibiyar sasan jikinsa gaba ɗaya, a haka ya shigo falon, su Jalal na biye dashi a baya.

Ba a falon Ummi na ɗalinta hakama Aysha.

Wuce Side ɗinsa yayi.

Su kuwa su Jalal abincindu suka ɗauka suka tafi Side ɗinsu sabida jin yayyafi ya fara sauka tare da wata iriyar sassayar iska mai sanyi daɗi mai ratsa jiki.

A Dinning area ya nufa.
cikin kasala da gajiya da yunwa ya zauna.
Abinci ya ɗan zuba kana ya fara ci yana mai matse cinyoyinsa yana mgnar zuci.
"To shi wannan me yake buƙata ne da zai hanani zaman lfy, ina dalilin da zakayi ta tashi tsaye, uwar me kakeso kayi".
Sai kuma ya ɗan sha ruwan sanyi tare daci gaba da mgnar zuci.
"To ita wannan uwar tsoron ma ni rabon da ita kwana biyu, na lura tsoron zuwa nan ɗin ma takeyi."
Mitssssss ya ɗan ja dogon tsaki tare da tafin hannunshi ya dafe kanshi.
Yau gaba daya sha'awarta ta cika shi don har sai da ya ji Jabeer ɗinshi tana harbawa da cekiyar neman aminiyarta.

A hankali ya miƙe ya bar wurin.
A kasalance sabida ua fara jin zazzaɓin nan na ƙoƙarin da yanzu kullum yake kwana dashi yana bin jikinsa, da sauri ya nemo paracetamol yasha.

Sai dai abin mamaki ba abinda yayi masa don ji yayi kamar ma ƙara ciwon aka yi jingina ya yi da kujerar yana sakin ajiyar zuciya tare da tambayar kansa meyasa ne? Meke damuna?".
Yau dare na huɗu kenan Kullum da zazzaɓi yake kwana a jikinsa, asuban fari yayi lfy, sai kuma wani daren. cikin sanyi yace.
"Ya zama dole inyiwa kaina medical checkup".
Don zazzaɓin na da zafin gaske, saboda ya fara jin ya yi loosing appatite, da ƙyar ya samu ya yi bacci don abubuwan sun haɗun masa goma da ashirin ga zazzaɓi ga azabebben Feelings mai fitinarwa.

Tun asuba ya tashi bayan zazzaɓin ya sauka, cike da kuzari da kuma tarin Feelings ya shirya ya wuce masallaci yana danne kanshi.

Yau yini akayi zurr ana tsuga ruwa kamar da bakin kwarya sai gab magriba ya ɗauke.
zuwa dare garin yayi luffff gwanin sha'awa sai iska mai sanyi da ɗan karen daɗi dake kaɗawa tare da ƙamshin ƙasa, yanayin garin yayi daɗi ko ina lib gwanin ban sha'awa da birgewa.

Bai shigo ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye side ɗinsa ya shige yana jinjina yau kwanansa uku rabon da ya sa Shatu cikin idonsa gaba ɗaya ta mai da shi dodo ta ƙi yarda su haɗu, ko abinci ne sai dai Ummi ko Jamil su kawo masa ga tsananin jarababbiyar sha'awarta da take fusgarsa yau kwana biyu, da ƙyar ya iya cin abincin yana jin alamomin bayyanar nataccen zazzaɓin da yake duk dare wanda baya jin magani ya kuma rasa meye sanadinsa ga kuma wannan mayataccen Feelings dake hanashi nitsuwa.

Zubawa sarautar Allah ido ya yi, yana jira yaga wai ko zata zo kuwa saboda yau kwana nawa rabon da su haɗu.

Wuce su da ya yi a falo suna hira ya kuma ce Ummi ta bata zam-zam ta kawo mishi yasa ya yi tunanin ko zata zo.

Shiru-shiru har goma da rabi hakan yasa ya miƙe ya fito falon ya tarar da su suna hira ita da Ummin, jikinsa sanyaye alamun zazzaɓin ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi zam-zam ɗinfa".
Juyowa Ummi tayi cikin kula tace.
"Aysha baki kai bane?".
Kanta a sunkuye tace.
"Na kai mana yana kan Dinning table ɗin ka na ajiye".
Juyowa yayi ya ɗan zuba mata ido,
sai kuma ya jinjina kai ya juya ya koma cikin falonsa .
yana lallaɓa kansa don sha'awarta na ta fusgarsa musamman sautin dariyarta da ya ji tana yi, sai da Jabeer ɗinsa ta harba da masifar ƙarfi.


Ƙarfe sha daya da minti goma ya kara komawa falon ya tarar da su har da Jamil da Jalal, da Ummin suna hira sosai, haushi ya kama shi, haka nan yaji sun nashi haushi, kamar ya rufesu da duka.
Don dariyar da suke yi cikin hirar ya sa ya ɗan tunzira yana jin kamar ma da shi suke, hakan yasa ya fito da sauri cikin faɗa yace.
"Jamil meye ya hanaka bacci ka zo ka tasa mutane a gaba da surutu kamar lalataccen Radio?".
Gyada kai Jamil ya yi tare da cewa.
"Eh yanzu zan tafi, Ummi ce ta faɗa mana mana, in munci dai zamu tafi."
Sai kuma yayi magana ƙasa-ƙasa.
"Yau kuma waya taɓo Sheykh alaramma akarmakallu, Hamma Jabeer naga masifa da fushi yakeji."
Bai ji mai ya ce ba, amma yaga dukansu sun kuma yin dariya ƙasa-ƙasa a hankali, miƙewa Jamil ya miƙe tare cewa.
"Asha bacci lafiya Sheikh Hamma Jabeer".
Ya wuce ba tare da Sheikh ɗin ya sake magana ba, don shi ma daki ya koma, saboda yaga Ummin ita ko motsi bata yi ba daga inda take a zaune shima Jalal moƙewa yayi yabi bayan Jamil dake fita yana dariya.

Suna fita Aysha ta ɗan juyo, ta fuskanci Ummi da kyau kana da gyara zamanta.
Numfashin ta ɗan fidda a hankali, sannan ta juya kanta ta ɗan kalli corridor'n shiga falon Sheykh.
Ummi kuwa ido ta zuba mata ganin yadda take waige-waige da alamun mgna mai mahimmanci takeson suyi.
Cikin nitsuwa da yin ƙasa da murya tace.
"Ayyah Ummi dan Allah zan tambayeki wani abun dake damuna, dan Allah Ummi ki gaya min gskyr meke faruwa a masarautar Joɗa".
Woni dogon numfashi Ummi ta sauƙe tare da cewa.
"In sha Allahu zan gaya miki gskyar da na sani a masarautar Joɗa, sai dai ina sirrine shi bazan faɗa miki sittin wasuba".
Cikin sanyi ta ƙara matsowa gaban Ummi kai ta ronƙofar bisa kafaɗunta kana cikin sanyi tace.
"Ummi koda sirrin Yah Sheykh ne baza ki gaya minba?".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To ai shi sirrinsa naki ne?".
Cikin jin kunya da daɗi tace.
"To dan Allah Ummi wai me Yah Sheykh yayiwa Gimbiya Saudatu ne? Meyasa bata sonshi? Meyasa su Bappa Nasiru basa sonshi? Meyasa baya shiri da Mom Imaran? Waye Gimbiya Samira amaryar Abba".

Dogon numfashi Ummi ta fesar tare da gyara zamanta ta ɗan jingina bayanta da jikin kujera, cikin sanyi tace.
"Tambayoyin ai duka amsarsu ɗaya ne!".
Da sauri tace.
"To Ummi gaya min sai muje tambaya ta biyu?".

Fuskantar Aysha tayi da kyau kana a hankali tace.
"Kwanakin baya can munyi makami ciyar wannan hirar.
Babu wani abu da Sheykh yayiwa kowa na masarautar Joɗa, domin wannan ƙiyayyar da suke nuna mishi ta samu asaline tun yana yaro".

Da sauri Aysha tace.
"To tun yana yaro kuma haka kawai kenan suka tsaneshi?".
Kai Ummi ta jujjuya mata tare da cewa.
"A a ƙiyayyar da dalilin zaɓin tambarine".
Cike da kaɗuwa Aysha tace.
"Menene zaɓin tambarin?".
Cikin yin ƙasa da murya Ummi tace.
"Bisa al'adar masarautun gargajiya na Hausa Fulani, dole har kwanan gobe suna da al'adu ko wacce masarauta da al'adarta, sai dai mafiya yawan masarautun al'adar tambarin ɗaya ce.
In kinji ance tambari wani kayan kiɗane da babu shi a ko ina sai gijen manyan masarautu. A bisa al'adar masarautar Joɗa bawai sarkine ke ko mutanen gari kance wane ne zai gaji sarauta ko wanene zaiyi mikinba. Duk ranar bikin salla ana fito da kakaki da al'gaita mabusar masarauta da kuma tambari a ajiye a tsakiyar faɗa, gaban sarki. Kana duk ƴaƴan sarki da jikokinsa da makusantasa maza, zasu hallara a fada, inda kowa zaije gaban sarki ya gaishesa, to muddin akwai nasibin gadar sarauta, a jikin mutun kana isa gaban sarki, kakaki da al'gaita nan zasu fara bisa kansu da kansu.
In kuma kaine zaka gaji mulki daga hannun shi wannan sarkin na wannan lokaci to tambarin masarautar zaiyi ta kaɗa kanshi da kashi,. Duk sanda ka isa kusa dashi, in ka wuce zai bari in ka dawo zaici gaba da yi.
Wannan al'adace tun ta zamanin jahiliya, kuma har yanzu wasu masarautun sunayi, to Amman masarautar Joɗa tun a kan Sheykh aka bar wannan al'adar tun yanada shekara uku a duniya, da akaje fada gaisuwar salla da yazo gaban Lamiɗo sai tambari yayi ta kaɗa kanshi kana kakaki da al'gaita sukayi ta busa kansu.
Tofa wannan shine musabbabin ƙiyayyar da yake fuskanta har ya shafi mahaifiyarshi mahaifinshi yayanshi da ƙannenshi, sabida duk mutanen masarauta sun gani a gabansu abin ya faru".
Ɗan tsagaitawa tayi kana a hankali tace.
"Kinji amsar tambayoyinka duka".
Da sauri Ummi ta kalli Aysha jin ta jefo mata tammayar.
"Ummi Waye Mamansu Yah Sheykh ina Mamansu Yah Sheykh meya sameta".
Jikin sauri Ummi ta miƙe tare da cewa.
"Hajia Mama ce".
Da sauri Aysha tace.
"Kiyi haƙuri Ummi ki gaya min gsky".
Juyawa Ummi tayi ta nufi falonsu tare da cewa.
"Je ki tambayi mijinki shi yafi cancanta ki tambaya bani ba".
Tana faɗin haka ta wuce ɗakinta.

Jiki a mace Aysha ta miƙa ta nufi ɗakinta cikin tsananin gaskata tunaninta na ba Hajia Mamace mahaifiyarsu Yah Sheykh ba.

Kai tsaye Bathroom ta shige,
Brosh tayi sannan tayi wonka da ruwan ɗumi sosai, kana tayi al'wala.

Tana fitowa ta shafa mai tare da shefe jikinta da humranta mai ɗan karen sanyi da daɗin shaƙa.

Wata tattausar rigar bacci wacce iya karta cinya ta saka tare da pant ɗinta da hularta, rigar pink guava color cr mak taushi.

A hankali tayi hamma tare da salati, ba tare daya kashe wutan ɗakinba ta juya ta hau kan gadonta ta kwanta ta bawa kofar shigowa tasa hannunta zata jawo blanket kenan taji wayarta na ringing da sauri tasa hannu ta ɗauka ganin Rafi'a ce, haka yasa bata rufe jikin nataba.
Murmushi Rafi'a tayi tare da cewa.
"Ina son kiranki Ina jin tsoro kada oga yana kusa".
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
"To baya kusa, muyi hirarmu".
Cikin shaƙuwarsu Rafi'a tace.
"A a kai ba wata hira zamuyi ba, zan dai gaya miki cewa, gwamnatin tarayya ta nemi malaman jami'o'i da su zauna wata ƙil zasu sasanta mu koma makaranta".
Cikin jin daɗi tace.
"Kai Alhamdulillah Allah yasa a sasanta nima gobe zan kira Umaymah in gaya mata".

Cikin sauri Rafi'a tace.
"Allah ya kaimu, Ni saida safe tashi ki tafi wurin mijinki".
Da sauri tace.
"Ke da Allah baya nanne tsaya muyi hirarmu".
Cikin wasa Rafi'a tace.
"To da sauƙi tsoro nake kar in shiga lokacin sa ai".
Dariya tayi kana sukaci gaba da hira.


Shi kuwa Yah Sheykh ya kasa zaune ya kasa tsaye, yanzu karo na biyu kenan ya shiga Bathroom ya watsa ruwan sanyi.
Sabida a zatonshi ko har yanzu suna falo da Ummi sabida ya leƙa ɗazu ya gansu duk da baijin me suke cewaba.

Yana watsa ruwan ya fito jikinsa ya ɗan tsane kana ya shafa OudKareem dake cikin saman dreesing mirror'n.
Wasu riga da wondo masu taushi red color and white
yasa wondon iya guiwa ne rigar kuma mai guntun hannune sai dai tana da hula rigar.
sa hular yayi a kanshi, kana ya feffesa turaren.

A hankali ya ya kuma fitowa ganin sun hada ido da Ummi wacce lokacin ne ta miƙa zata tafi.
da sauri ya ɗan wayance ya koma falo yana jin kasala, da sha'awa, zama ya yi kan kujera, ya jingina da ita tare da lumshe ido, hancinsa na zuko masa ƙamshin ƙasa mai daɗi, kunnensa na jiyo sautin kukan tsuntsaye mai daɗi, yanayin ya ƙara sakar masa da jiki kasala mai ƙarfi ta rufeshi wannen yasa bai sake leƙawaba, har suka watse, har yaje tai wonka.

Ido a lumsh miƙe da sauri.
Ƙarfe ɗaya na dare dai-dai agogon wayarshi ta nuna mishi.
Hannunshi na hagu yasa ya damƙi kan Jabeer ɗin sa daketa harbawa, da miƙewa tsaye.
"Hehyyyyyy". Ya fidda wani wani dogon sauti tare da komawa zaune yana taune lips ɗinsa ido ya zubawa Jabeer ɗin nasa data miƙe tayi sama ba alamun sassauci.
Don izuwa yanzu ya fara jin mararsa ta yi nauyi, cikin tafiya da sassarfa, ya fito falon wani dogon ajiyan zuciya ya sauƙe ganin basa nan kuma ko ina shiru alamun sunayi bacci.
Da sauri yaje ya rufe kofar babban falon tare da addu'a, kana ya kashe duk kayan wutan falon, ya wuce falon Aysha.
A hankali yake taku wai sabida kada Ummi ta jishi.
Saɗab-saɗab yake ɗaya ƙafafushi.
Har ya isa kofar bedroom ɗin Aysha, hannunshi yasa a hankali ya murɗa handil ɗin, ajiyan zuciya ya kuma sauƙewa jin ɗakin a buɗe ne.
Ga kuma wani masifeffen ƙamshi daya shaƙa.
Ƙamshin turaren da take amfani da shi idan zata kwanta, ƙamshin ya kara hautsuna masa tunani.
Can ya hangota bisa gadon, tana riƙe da waya ta bawa kofar shigowa baya,
sai dariya takeyi, sam bataji motsin buɗe ƙofar ba bare shigowarsa.

Cibiyoyin ta ya zubawa ido sabida a bayyane suke a fili.
Dogon numfashi yana tare da ƙarasawa kusa da ita a hankali, ya hau bisa gadon tare dasa hannun sa ya rug......






By
*GARKUWAR FULANI*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment