Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taita kiranki ashe kina bacci ne".
Cikin nitsuwa tace.
"To Aunty yanzu kuwa, ngd matuƙa".
Cikin jin daɗi Aunty Hafsat tace.
"Allah ya muku al'barka ya baku zaman lafiya.
In Sha Allah zamuzo auren Haroon zaki gammu mu ganki".

"Amin Amin. Aunty Allah ya kaimu lokacin ya kawoku lfy".
Tace kana sukayi sallama.

Daga nan suka shiga kitchen.
Jamil kuwa tuni yaje yayiwa wani mai musu aikin gidansu.
Yasa ya nemi irin wannan tayis ɗin. Yace gobe da safe misalin sha ɗaya zaizo ya ɗauke shi.

Washe gari da safe.
Misalin karfe tara, Sheykh ya fito cikin shiga ta al'farma, yau ba al'kyabba a jikinshi riga da wondone sai malum-malum gariya mai kyau.
Getzner ce mai masifar kyau Brownish red color mai ɗan karen kyau da sheƙi, gariyar tasha aiki mai ɗan karen kyau da zaren surfani mai sheƙin piash color.
Hular kanshi da red and piash color, takalmin shi kuwa fatar ta kifa kalar red ɗin.
Yayi kyau sosai ya kafa hular nan cas a kanshi. Kekyawan suman kanshi ya konto gefe da gefe da ƙeyarshi sai sheƙi da ƙelli yakeyi.
Sajenshi ya kwanta lib, gashin girarsa dana gemunshi ɗan cas dashi misalin kamu ɗaya, sai sheƙi suke zubawa.
Ɗan madai-daicin bakinshi mai jajayen laɓɓa sai sheƙi sukeyi.
Yar ƙaramar jakar na'urar System ya riƙe a hannunshi, sai wani ƙamshi mai daɗin ji yake fiddawa, ɗan farin siririn Glass irin na manyan Doctors ya manna a fuskarshi kana ya fito.

A falonshi ya sameta, tana jera mishi breakfast.
Ganin zai wucene ta ɗan biyoshi a hankali ya zama suna tafe a jere.
Cikin kallon suman ƙeyarshi tace.
"You are breakfast is ready".
Bai kulata ba yaci gaba da tafiya.
Ita kuma ƙeyanshi ta mannawa harara.
A haka suka fito.
Ya sallami Ummi da Jamil da tunda suka karya bai tafiba.
Da sauri Jamil yabi bayanshi yana cewa.
"Uhum Dakta sai yaushe zaka dawo ne?".
Juyowa yayi ya kalli Jamil sai kuma yace.
"Kanada matsala ne?".
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da cewa.
"No. I'm very fine".
yayi mgnar yana jijjiga jikinsa.
Kai ya kaɗa ya juya zai fita,
Da sauri Jamil ya kuma tambayarsa.
"Dakta yaushe zai dawone".
Cikin tsuke fuskarsa yace.
"Ban sani ba".
Daga nan ya fita, shi kuwa Jamil tsalle yayi tare da cewa.
"Yesss, Dakta Allah ya kiyaye hanya, a wuni lfy a asibiti".

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Yi maza to ka ɗauki shi".
To yace kana ya miƙe ya fita.
Sanin cewa yanzu Sheykh yana sashin Hajia Mama ne.

Haka yasa ya rigashi fita.

Ummi kuwa miƙewa tayi taje ta rufe ƙofar sabida bata son wani yazo ya shigo.
Kiran Jamil tayi a waya tace in sun isoma ya kirata a wayane zata buɗe mishi.

Tana katse kiran ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta tana ce mata.
"Yauwa to Ummi muje mu fara aikin kafin ya iso mun kusa cimma aikin."

Cikin mamaki tace.
"A a keda kikace sai an matsar da gadonshi sannan aikin tono ai bazamu iyaba. Dole sai mazan".
Cikin muryar da har yau Ummi ta kasa banbance shi da asalin muryarta tace.
"A a ba matsala Ummi muje zamu iya".
Ta ƙarishe mgnar tana yin gaba, ganin hakane yasa Ummi Binta a baya.
A hankali suka shiga falon.
Tana mai cewa Ummi.
"A nan ma an mishi wani aikin amman shi bai shiga jikinsa ba, sabida yanada Garkuwar addu'o'in da yakeyi yau da kullum.
Shiyasa duk sabbin sihirurruka basa shigarsa.
Sai dai waɗanda akayi mishi tun bai gama girma ba."
To kawai Ummi ke ce mata sabida jin kamar muryarta na canza mata.

A haka ta kuma nuna mata wani wurin.

Tare da cewa.
"Uhumm Ya Jafar suke nema, su maida majanunin kan bola sai kuma sharrinsu ya zame mishi al'khairi,
Tsawon shekaru baya mgn sai ambaton Allah. Bashi ba zunibi sai tarin lada da yake samu na karatun al'ƙur'ani da ya zame mishi abokin hira.

To ita kuma me take nema a duniya da zata cutar da baiwar Allah da ahlinta duka haka.
In banda lalaci da son duniya na miji ya lalace da bin matsafa yana sawa ana sabauta ɗan uwanshi da yayanshi."
Ita dai Ummi binta takeyi da ido da ƙafa har suka isa bedroom ɗin shi.

Ɗan lungun da ɗaya Bedside drower'n take ta shiga.
Kana ta kalli Ummi fuska a juye tace.
"Naɗe min carpet ɗin nan.
To Ummi tace da sauri ta fara naɗe carpet ɗin.
Bayan ta janyeshi da kyar ne, ita kuma Shatu.
A hankali tasa hannun damanta bisa jikin gadon ba tare da ta ɓallashi ba ko, ta cire wani abu a jikinshi ba, ta yunƙura ta tura gadon tare da cewa.
"Bismillahirahamanirahim".
Da sauri Ummi taja da baya cike da mamaki da tsoron ganin yadda take tura tamfatsetsen gadon mai ɗirkekiyar katifa da ko tura katifar kawai aikine.

Guuuuuuh haka sautin tura gadon yake badawa.

Saida ta turashi har jikin Waldurob.
Kana ta tsaya a tsakiyar inda gadon yake kafin ta turashi.
Dai-dai lokacin kiran Jamil ya shigo wayarta.

Da sauri taje ta buɗe mushi.

Kana suka shigo,. A falon suka bar Ɗalha mai tayis,
kana Jamil ya amshi kayan aikin yabi bayan Ummi yana cewa.
"Yauwa ɗalha ɗan jirani bari inzo mu isa kaga wurin".

To ɗalha yace kana ya fara cin abincin da Ummi ta saka mishi.

Suna shiga suka maida ƙofar falon suka rufe.

A inda Ummi ta barta a han suka sameta.
Da sauri ta miƙawa Jamil hannun tare da cewa.
"Bani gudumar da ma'ɓamɓarin."
Cikin sauri ya iso tare da ajiye ɗan buhun ya fito da gudumar da Maɓamɓarin yana mai mamakin yadda aka tura gadon yace.
"Bari Aunty Shatu nuna min ina zan fasa".
Da sauri tace a a, ku ɗan matsa gefe, musamman ma kai koma can".
Ta nuna mishi gefe.
Sake mata gudumar yayi jin ta fizgeshi.
A hankali ya tashi sabida cewa da tayi ya tashi.
Ido suka zuba mata, ita kuwa, gudumar tasa ta rinƙa buga tayis ɗin dake wurin saida ta fasa uku lafiyeyyu.
Kana ta ture fasassun tasa maɓamɓari tana ɓalle sauran, saida ta ciresu kab.
Sannan ta fara fasa fulon simintin dake ƙasan.
Da mamaki Ummi ke kallon wurin sabida tasan babu wani fulo da akayi kafin asa tayis ɗin.
Fasashi tayi kana ta fara caccaka ƙasan wurin da matonin, tanayi yana fito da ƙasa.

Shiru sukayi ganin ramin yayi zurfi kuma ba komai.

A haka taci gaba da tono tana kuma faɗaɗa ramin ta ƙasa.

Wani irin zabura Jamil da Ummi sukayi lokacin da suka ga wani baƙin hayaƙi yana fitowa cikin ramin.

Ita kuwa Shatu da sauri tasa hannun damanta taci gaba da tonon.
Tare da yin mgna da sauri tace.
"Jamilu buɗe windows da sauri hayaƙin nan ya fita".
Cikin rawan jiki yace to.
Kana ya fara buɗe wa da sauri sabida, hayaƙin ya fara cika ɗakin.

Yana buɗe windows ɗin kuwa hayaƙin ya fara fita.
Tonon taci gaba dayi tare da cewa.
"Inama da akwai wani yardajjen mu a kusa, bayan ku biyun nan da yabi hayaƙin nan zaigane mana ina zai shiga cikin sashukan mutanen gidannan shaidar aiki ya koma kan wanda ya yishi."
Da sauri Jamil yace.
"To ko in fitane inbi hayaƙin".
Cikin sauri tace.
"A a kada ka fita ku tsaya kaida Ummi."

Numfashi suka fara sauƙewa, a hankali lokacin da sukaga duk hayaƙin ya gama fita.
Sai kuma suka fara takowa suna zuwa inda take ganin yadda hannunta dake cikin ramin yake karkarwa.
Ga wata zufa dake keto mata kamar da bakin kwarya.
Wani marfin tukunyar ƙasa ta ɗago.
Kana a hankali ta ɗago tukunyar.
Ta ajiyeta gefe kana ta koma ta jingina tana mai jan numfashin.
Cikin sauri Ummi taje ta kunna sauran wutan ɗakin duka, ya zama kamar farin wata.

Jamil ne ya fara leƙa cikin tukunyar.
Da sauri yace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummi zo ki gani".
Ya ƙarishe mgnar yana sunkuyowa da kai hannunshi zai kama tukunyar ƙasan cikin sauri da ƙarfi Shatu ta buge hannunshi da hannunta na hagu tare da cewa.
"Jininka ɗaya da Yah Sheykh in ka taɓa duk abun zai iya dawowa jikinka."

Ta ƙarishe mgnar da ɗago hannun ta na dama tasa a ciki.
Tukunyar da sauri ta rumtse idanunta sabida wani irin masifeffen tsikara da taji an mata a hannunta.

A can ƙasar Cameroon kuwa cikin Rugar Duno dake, kusa da Rugar Malam Babayo.
Ba'ana ne zaune bisa buzun aikinshi.
Da kasko a gabanshi yana kallon cikin kaskon gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi cikin tashin hankali da fargaba yace.
"A'a A a Mata kada ki taɓa, baki amince na baki mgnin kariyar tonar sihiriba, iya ganin idan a zuba sihiri a abinci yake na shayar dake shi nanma a bisa dole baki saniba.
Kada ki taɓa zai cutar dake".
Ya ƙarishe mgnar hawaye na zubo mishi, Allah ya sani baya son abinda zai cutar da Shatu ko kaɗan.

Ita kuwa Shatu a hankali ta fara fito da wasu irin tabka-tabkan layu wanda aka liƙesu da yadin al'kyabba daga gani kasan na Sheykh ne sabida shi ɗaya kesa irinsu a masarautar Joɗa tun yana ɗan yaro matashinsa.
Wani dogon ajiyan zuciya taja tare da fizgo wani dogon maciji a cikin tukunyar ƙasar.
Da sauri Ummi taja da baya, shi kuwa Jamil sai leƙowa yakeyi.

A dai-dai lokacin kuma Sheykh dake cikin Office dinshi na cikin Genaral Hospital Ɓadawaya shi ɗaya, dan yau ba mutane sosai dudu mutun biyar ne kuma ya gama dubasu ya musu komai, yana zaune ko za'a turo wasu.
Wani irin zabura yayi ya miƙe tsaye da ƙarfi tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Sai kuma ya sunkuyo yana kallon yadda babbar yatsarshi ta ƙafar dama wacce zanen maci ke kanta take rawa kar-kar.
Da sauri ya juya ya nufi bathroom ɗin cikin Office dinshi.
Cikin sauri ya zare malum-malum ɗin jikinshi juyowa yayi ya ajiyeta saman kujerarshi.
Kana da sauri ya nufi Bathroom sabida yadda yakejin ana fizgo wani abu kamar jijiya a jikinshi tun daga saman cikinsa kusa da ƙirjinsa, har zuwa kan ɗan yatsarshi.
Da sauri ya cire rigarshi da snglet ɗin, da ido yabi zanen dake jikinshi wanda samanshi zanen kan macijine.
Gaba ɗaya jikinshi rawa ya farayi tamkar mazari.
Duk wata jijiya dake jikinsa saida ta tashi tsaye.
Cikin tashin hankali yake ambaton sunayen Allah da duk addu'o'in da sukazo bakinsa.
Hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi data miƙe tayi wani irin harbawa da masifar ƙarfi, riƙeta yayi da kyau jin yadda take tashi tana kumbura da cika tana tsawo tamkar zata faso boxes ɗin shi ta fito woje.
Wannan shine babban tashin hankalinshi dan tsawon shekaru kusan ashirin bai sake ji ko ganin bnnarshi ta miƙe kamar hakaba sai yau.
Karkarwa duk jikinshi keyi, hatta jijiyoyin kanshi dana damatsan hannunshi tasowa sukayi ruɗu-ruɗu jijiyar goshinsa har harbawa takeyi".
Innalillahi wa innailaihi rajiun yaketa maimaitawa, yanajin kamar ana jan jijiyoyin jikinsa.
A haka ya maida kayanshi kana ya fito.
Sai dai bai samu damar maida gariyar ba, zama kawai yayi bisa kujerar yana rawan sanyi.

A haka abokinshi Dr Arabi ya shigo ya sameshi cikin mamakin ganin yadda yake karkarwa yace.
"Dakta Jabeer lfy kuwa meya sameka".
Cikin muryar alamun zazzaɓi yace.
"Zazzaɓi ne Arabi. Sanyi nakeji".
Da sauri ya iso inda yake taimaka mishi yayi ya saka mishi gariyar.
Kana ya kamoshi ya kawoshi bisa tattausan kujerar 3 str dadake cikin Office ɗin ya kwantar dashi.
Aunashi yayi tare da kiran wata Nurse ya gaya mata magungunan da zata amsa musu a Pharmacyn nasu, cewa Dr Jabeer ba lfy.
Ai lokacin ɗaya sai gata da manyan likitoci har uku.
Cikin tarin kulawa, suka fara dubashi ganin yana gab da fita haiyacinsa ne, yasa suka mishi allurar bacci.
Da sauri Dr Arabi kuma ya kira, Jalal ya sanar mishi.
Jalal kuwa dake falon Hajia Mama ba tare da ya gaya mata ba ya miƙe da sauri ya fita.
Tana tambayarshi lfy.
Yace lfy sabida baison tayar mata da hankali.
A bakin ƙofar fita ya haɗu da Ya Affan da sauri ya kamo hanunshi suka juya yana cewa.
"Ya Affan Hamma Jabeer ba lfy, yana Genaral Hospital Ɓadawaya, yanzu Yayan abokina Umar Dr Arabi abokinshi ya kirani ya gaya min yace baida lfy sosai fa".
Ai da sauri Affan ya fara lalubo car key dake cikin al'jihunsa cikin kiɗima da tashin hankali yace.
"Muje, muje da sauri mu tafi a maidashi Valli Hospital yafi kwararrun likitoci".
Kusan a tare suka shiga motar Affan suka tafi.

Kafin suje kuwa tuni bacci ya ɗauke shi, an ɗaura mishi ruwa da allurai.
Sauran Doctors ɗin sun fita.
Sai Dr Arabi da yake zaune gabanshi.
Da sauri Affan yasa hannun shi ya taɓa jikinshi tamkar wuta.
Jalal kuma yatsarshi daketa karkarwa yake kallo tare da rauni a fuskarshi yace.
"Yah Arabi meya sameshi ne?".
Cikin sanyi Dr Arabi yace.
"To wlh nima shigowa kawai nayi na sameshi yanata karkarwa, yace min zazzaɓi yakeji sanyi na damunshi.
Na kira Nurse ta kawo min injections and drip kafin muyi mishi allurar ma tuni ya kusa suma, abun yafa bani tsoro.
Amman Alhamdulillah kunga yanzu kuma da sauƙi".
Ajiyan zuciya sukayi kana suka zauna a nan, ba tare da sun gayawa kowa ba.


A can masarautar Joɗa kuwa.
Cikin tarin firgici da al'ajabi Jamil da Ummi ke kallon Shatu.
Data fizgo macijin da ƙarfi cikin tukunyar.
wurgar dashi tayi a ƙasa sai gashi yayi wutsul-wutsul sau biyu, shike nan ya mutu."
Mazargin mondo ta fitar da kuma hula wanda duk na Sheykh ne.
Cikin murya mai rauni tace.
"Yanzu Jamil zaka iya taɓasu.
Haɗasu kaje in akwai inda zaka wurgar dasu ka wurgar dasu, ka fasa tulun.
Kada ka binne macijin ya bushe akeso.
Ummi ɗauki Hular Yah Sheykh da zariyarshi a wonkesu.

Da sauri Jamil yace.
"Eh akwai inda zan wurgar dasu".
Nan ya tattare macijin da da layun ya saka cikin tulun ya fita.
Key ɗin ƙofar baya ya ɗauka ya buɗe ya tafi cikin Garden ɗin.
Tafiya yayi sosai saida yaje can cikin dajin ya fasa tulun macijin da layun suka watse kana ya juyo ya dawo ba tare da ko waiwaya ba sabida tsoro.


Ita kuwa Ummi bathroom ɗin shi ta shiga a take ta wonkesu kana ta fito dasu.
Cikin sanyi Shatu tace.
"Wai hannuna Ummi yi sauri ki wonko gero ki kawo min ruwan tsarin."

Da sauri Ummi ta fita.
Murmushi tayi ganin Ɗalha mai gyaran tayis yaci yayi haniƙan yana kallon tv.
Cikin sauri tace.
"Yi haƙuri dan Allah Ɗalha muna tattare ɗakin ne da yake tayis ɗin ƙasan gadone ya fashe".
Cikin shan iskar yace.
"Ba komai Ummi".
To tace kana taje ta wonke gero, sannan ta fito da ruwan tsarin tazo.
Tana zuwa ta bawa Shatu cikin ramin ta watsa ruwan.
Kana ta fara tura ƙasar da kuma fashesshe-fashesshen tayis da fulo ɗin tanayi tana yayyafa ruwan.

Dai-dai lokacin Jamil kuma ya shigo.

Ganin yadda hannunta yaketa karkarwane yasa ya tayata tura ƙasar saida suka gyara komai fes kamar ba fasawan ganganci akayiba.
Kana ta miƙe tare dasa hannun hagunta ta riƙo na damanta tana cewa.
"Shima Yah Sheykh dole zaiji wani abu a jikinshi duk inada yake".
Sai kuma tayi shiru tare da rumtse idanunta tace.
"Wash hannuna".
Cikin sauri Ummi tace.
"Sannu hannun ya gaji ko".
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A haka suka fito falon. Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa.

Shi kuwa Jamil yayiwa Ɗalha jagoro,
Suka shiga suka gyara wurin da aka fasa ɗin fes.
Kana Ummi ta share wurin ta goge, sannan suka tura gadon suka maidashi.

Nanma ta ƙara gyara ɗakin Jamil kuwa ya ɗauki Ɗalha ya maidashi wurin aikinshi.

Ummi na gamawa taja ƙofar ta rufe tana al'ajabin wannan abu da ta gani da idonta.
Kitchen ta wuce ta ɗaura musu Lunch tana kiran Umaymah ta gaya mata duk abinda ya faru.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi kan Sheykh ya auro ba fulatar daji sun fara tabbata.
Ya Allah kasa abinda zai faru a sanadin shigowar Shatu masarautar Joɗa ne kake nunamin a mafarkaina".
Umaymah ta faɗi lokacin da Ummi ta mata bayanin abinda ya faru.
"Amin Amin, Ummi tace kana ta katse kiran jin muryar Aunty Juwairiyya da Hibba."

Umaymah kuwa da sauri ta kira Lamiɗo ta gaya mishi abinda ya faru.
Murmushi yayi irin nasu na manyan sarakuna yace.
"Alhamdulillah warakafa nan shigowa masarautar Joɗa baki ɗayanmu zamu rabu da mugun iri a cikinmu, kada ki gayawa kowa Khadijatu kinji ko".
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
"In sha Allah kuwa ko Jadda bazan gaya mishi ba".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Masha Allah, Allah ya miki al'barka Khadijatu da ace duk ƴan uwa haka suke riƙe ƴaƴan yar uwarsu da zumunci ya ƙara ƙarfi kin musu abinda mahaifiyarsu bazata iya musuba".
Amin Amin tace kana ya katse kiran.

A cikin ɗakin Shatu kuwa.
Wani irin...!






By
*GARKUWAR FULANI*Ya ruggumeta da kyau a jikinshi.
Jinyadda taketa fizge-fizgen zata kwance kanta.
Wani irin tsuma jikinshi ya rinƙayi can cikin naman jikinshi yake jin tsuman.

A hankali ya manna kanta, kan faffaɗan ƙirjinshi,
hannunta mai ciwon data ɗaura a tsakiyar kan natane ya zubawa ido.

Sosai hannun yayi jazir sai kelli yaki, alamun kumburin da yayi.
A hankali yasa hannunshin ya tallabo hannun.
Wani irin ihu tasaka da ƙarfi.
Sai dai bai bari ihun ya fito daga bakinta ba, yayi maza ya rufe mata baki da tattausan tafin hannunshi yana ta mai-maita.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Tabbas da in ya barta ta kurma ihun shike nan ta tabbata zautacciya,
yin ihun da take son yi dai-dai yake da sihirin ya gama shiga jikinta ya ratsa zai kuma haukatata.
Shiru tayi tana zazzare idanunta da hawaye ke zuba babu ƙaƙƙautawa, shi kuwa Sheykh a hankali ya janye hannun nata data aza a kai ya tallabeshi da tafin hannunshi.
Sannan ya manna ƙirjinshi da nata ƙirjin da kyau.
Har suna iya juyo bugun zuciyar juna.
Sunkuyo da kanshi yayi tsakanin kafaɗarta da wuyatan

Bakinshi ya saita cikin kunnenta.
Hure gashin daya baje kan kunnen yayi ya matsa,
sannan ya kawo bakinshi gab da kunnenta har tattausan lips ɗinshi na taɓa tattausan kunnenta.

Lumshe idonshi yayi tare da gyara tsayuwar nasu da kyau.
Ita kuma sai fiffizgewa take sonshi jikinta duk yana karkarwa ga zufar dake tsiyayo mata.

Hannunta dake cikin hannunshi ya kalla yadda yaketa rawa, gashi zafi jau kamar wuta.

A hankali yayi gyaran murya tare da yin bisimilla.
Cikin ɗan-ɗaga sauti ya fara karanta Suratul Baqra cikin kunnenta cikin fidda harrufan da karsashin yadda zai ratsa kunnuwanta.

Yanashi yana cire tafin hannunshi dake bakinta,
wani irin manna kanta tayi da ƙirjinsa,
ta lumshe idonta wasu hawaye masu ɗumi suka fara kwaranya.
hannunta na hagu dake da lfyar tasa bisa kafaɗanshi ta zagayo wuyanshi da kyau.

Shi kuma hannunshi da ya janye daga kan bakinta ya maida kan ƙugunta ya ruggumeta tsam a jikinshi.

A haka yaci gaba da karatu, in yazo wasu ayoyin yakan maimaita karshensu kafin ya kuma kama forkon na gaba.

A hankali ta fara sauƙe wasu tagwayen numfarfashi, ji takeyi azaba da raɗaɗin yana ɗan lafawa.
*Al'farma Annabi da Alqur'ani kenan.*
A hankali ta daina duk fizge-fizgen ta dawo sai kukan da takeyi mai sauti amman sautin a hankali ne.

Kuka take sosai ganin hakane, ya gyara tsayuwar tasu.
Kana ya tallabo kanta ya kalleta.
A hankali ya girgiza kanshi tare da jawota suka nufi bakin gado.
Yana cewa.
"Uhummm baku samu wurin zamaba a kanta in Sha Allah bazamu zauna inuwa ɗaya dani da kuba, zaku bar jikinta."

Ajiyeta yayi kan gadon kana shima ya hau ya zauna.
da sauri ya riƙo hannunta da take son maidashi tsakiyar kanta ɗin.

Karatu ya fara yanayi yana ɗan hura mata sassanyan iskan bakinshi.
Tub, tub, tub, haka yake ɗanyi tare da fesa iskar, kana ya zuba mata ido cikin idanunta.
A hankali tayi ƙasa da kanta.

Shi kuwa haɗe fuska yayi tare da cewa.
"Ɗago ki kalleni mana".
Kai ta girgiza alamun a a.
Shikuwa hannunshi ɗaya yasa ya tallabo haɓarta, dan ta kalleshi da sauri ta rumtse idanunta.
Cikin kausasa murya yace.
"Buɗe idon ki kalleni!".
A hankali ta buɗi baki cikin irin Muryar da yaji tayi mgna kwanaki dashi tace.
"Bazan iyaba, kunyarka nakeji!".
Watsa mata wani kallo yayi tare da cewa.
"Ƙarya ne, bakiji kunyan Allah'n daya haliccemu ya halicceku ya kuma yi mana iyaka a tsakaninmu ya hanaku cutar damu, ta hanyar mazonsa ya ƙaiyade muku dukkan motsinku, ya hanaku cutar da bani Adam.
Duk bakiji kunyarsu ba, kika shiga jikin yarinya ƙarama, kina sata yin wasu abun da ba halinta ba,
bakiji tsoron Allah daya hanakuba.
Bakiji kunyar iyayenta ba, kina cutar musu da ɗiyarsu sai ni?".
Cikin sanyi murya cike da alamun tsufa, tace.
"Ni bana cutar da ita, Ni ba muguwa bace, ban taɓata cutar da ita ko wani nataba duk tsawon shekarun da nake tare da ita".
Da sauri cikin faɗa yace.
"To meyasa zaki shiga jikinta".
A hankali cikin zubda hawaye tace.
"Ni tun tana jaririya nake jikinta, kuma ni makaran gadone na ahlinsu daga wurin kakarta mahaifiyar mahaifinta".
Da sauri yace.
"Rufe min baki, makaran gado,
Ku kuɗine ko wata kadara ce, ku cikin kadarorin da Allah (S.W.A) ya lissafa cikin jerin jadawalin abinda za'a gada?.
Ko dan kinga ina binki a hankali ne yasa zakiyi min zancen banza na mutanen banza".
A hankali tace.
"Jikana ka kontar da hankalinka muyi mgna".
A fusace yace.
"Waye jikan naki, kina Jinnu ina bani Adam ta ina na zama jikanki.
An ƙi a kontar da hankali tsohuwa dake kinzo kin liƙewa yarinya kina ƙoƙarin sata tana yaye suturar jikinta tana shirin yin ihu.
Ko baki san cewa matar aure bace, baki san daraja da kimar dake cikin aure bako?".
Cikin fushi itama tace.
"Ni bani nasata yarda kallabin kanta ba, zafin ciwo da takeji ne ya gigitata yasata yarda kalkabinta.
Sannan batun ihu da kakeyi kuwa.
Aikin da mugayen Masarautar Joɗa sukayi data taɓane yake shiga jikinta.
Ni kuwa na zone sanadin karatun Rugyan da kayi ta mata, amman duk wancan abun da takeyi ni bana kusa ma.
Kuma ni ba mai cutarwa bace.
Batun darajar aure kuma na fika sani.
Kai kama tsaya inda takene bare ka raya auren ka tabbatar da ita matarka ce kai mijinta ne?.
Kasa sabgogi a gabanka, kana sane da magautanka sun saka a tsakiya kayi, burus dasu, suna neman rabaka da rayuwarka.
Ita kuma dole in taimaketa sannan dama Aysha in dai bata da lfy ko zazzaɓi ne tana kuka haka ciwonta yake."
Cikin haɗe fuska yace.
"Eh wato da ban ƙonaki bane, kikemin baki ko. T taimako bana son taimakonki ki fitamin a jikin matata, bana so, zakisa tayi ihu ta fita tsakiyar masarauta bayan kin san inada magautan to meyasa zaki nemin abinda zaisa magautana farin ciki.
Tai mako kuma bama so, muda mukeda ubangijin taliƙai wanda yasan zahiri da baɗinin shi yake taimaka min, ba tare da yasa mana ciwon kai ko fita haiyaci ko kukaba dan haka fice min a jikin matata".
Murmushi tayi tare da jinjina kai kana tace.
"Matarka kuma yau".
A hatsale yace.
"A a matarki ce, in ba matata ba?."
Sai kuma yayi bisimilla zai fara karatu da sauri tace.
"Tsaya Muhammad Jabeer ɗan Habibullah jikan Nuruddee, Bubayero, Joɗa, Sule Usmanu jinin sarki Muhammad Bello, ni bazanyi faɗa da kaiba kafi ƙarfin haka duk da ni ba cutar daku nakeyi ba. Naga ranka ya ɓaci ina jinin.
Wai matarka kace ko?".
Wani irin kallo yayi mata tare da ɗago hannun shi zai shararamata mari yana cewa.
"Wai ne ma ko?".
Da sauri tayi murmushi tare da cewa.
"Kamar gibtawar ido zan gudu jikinta, ka kwaɗa marin a kanta".
Ai fa a kufule ya kai marin.
Hannunshi na isa fuskarta tana yin atishawa.
Zafin marin ya sauƙa kan fuskarta cikin azaba ta ɓare baki tare dasa kuka tana mai shafa haɓarta ido na zubda hawaye a gigice idonta na ganin duhu sabida zafin marin bata gama dawowa haiyacinta ba murya na rawa tace.
"Wayyo Allah na me nayi maka zaka mareni, ka barni inji da ciwo ɗaya mana".
Hararanta yayi tare da miƙewa ya sauƙa gadon yana cewa.
"Mutun jiki duk al'janu, sai hegen bakin rashin kunya mutun in ba lfy bazaiyi addu'a ba sai kuka".

Ya ƙarishe mgnar da juyawa ya nufi falo.

Ita kuwa Aysha wani irin bacci ne yayi awon gaba da ita,
tana mai jin zafin hannun ya ɗan lafa sai kuma raɗaɗin marin.

A can falon kuwa, wayar Aysha ne dake hannun Hibba yayi ringi.
Bappa am.
Shine sunan da ta gani a rubuce.
Da sauri ta nunawa Ummi shi tare da cewa.
"Ummi ana kiranta".
A hankali tace ki ɗaga.
Kai ta gyaɗa tare da amsa kiran ta kara wayar a kunnenta.

Cikin nitsuwa tace.
"Wa alaikassalam". Sai kuma tace.
"A a Bappa ba Aysha bace.
Hibba ce, Aunty Ayshan tana ɗakin Hamma Jabeer".
Cikin dattaku Bappa yace.
"To Hibba ya jikin nata?".
A hankali tace.
"Bappa hannunta kam yana ciwo sosai, ya kumbura yayi ja, in an taɓashi zafi kamar wuta, bata iya bacci".
Da sauri tayi shiru ganin Ummi na girgiza mata kai alamu.
Ta daina faɗa mishi hankalinsa zai tashi.
Ila kuwa hakane, cikin tashin hankali da kiɗima yace.
"Yanzu kai mata wayar maza, kai mata inji muryarta".
A hankali ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi wai in Kai mata wayar".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Jekiyi sallama ki kai wayar".

To tace kana ta juya ta nufi falonshi.
Tana jin Bappa na cewa.
Yi sauri".
A falo ta samu Hamma Jabeer ɗin cikin sanyi tace.
"Hamma Jabeer gashi Bappa am, na son yin mgna da Aunty Aysha".
Hannunshi ya miƙa ya amshi wayar ba tare da yace komaiba.
Ganin kiran bai yanke bane.
Yasa ya zubawa number ido cike da mamaki ganin code number ɗin bana ƙasar Nigeria bane, na ƙasar Cameroon ne.
a hankali ya kai wayar kunnenshi tare

Please Login or Register in order to submit comment