Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ƙarshen shekara yake samu yazo ya koma, zaman canada ya yi masa daɗi yana ta karatunsa, ga wata irin shaƙuwa tsakaninsa da ƴar anty laila.
Mijin anty laila yana ta jaddada mata, shifa idan Yasir ya kammala karatun sa, a nan zai samu aiki su cigaba da zamansu, sannan kuma da ya kammala karatun ya bashi anam.


Ƴan mazan mama, gidaje uku suka saya, a jikin nasu, suka faɗaɗawa mama shi, dan cewa tayi dan Allah yayi musu arziki ba zata bar unguwar nan ba, tana fatan suma su ci albarkacin ruma da ƴan uwanta.


Hakan ya sa suka gyara layin, aka yi masa kwalta da kwalbati, aka sassaka sola, wannan ya shiga da abun alkhairinsa wannan ya fita.


Mummy ta koma tamkar mushe da rai, saboda wari, kuma tana ji tana gani, gida ya koma hannun ammi, ta malleke komai da take ta ƙoƙarin hana faruwar hakan.
Ba tare da ƙyashi ba, ammi ta din ga nemawa ruƙayya magani, ta ce in dai tana raye ba zata bari ɗan marigayi galadima ya wulakanta ba.


Adam ya sauyawa ruma gida, manyan motocin take ja, da ƙananun shekarunta sai ta birgeka, saboda har a lokacin ba ta haɗa shekara ashirin ba, ta saka ya ɗaukko mata ɗan mai unguwa mai hanata shiga lambu sata, yake kai Sabir makaranta ana biyansa kuɗi mai yawa.


Adam ya ɗauke mata komai, dan haka kuɗin kasuwancin ta a sama suke, sai dai tayi ta kyauta kasancewar ta mai kyauta ce.
Ba ƙaramin girmama rumaisa suke yi ba, saboda rawar ganin da taka a rayuwar Adam, dan shi kansa duk wani abu da zai taɓa mutuncinta, ko tayar mata da hankali fito na fito yake da shi.


Ƴan unguwarsu ruma har murna suke su ga danƙareriyar mota a ƙofar gida, sun san akwai kaɓakin alkhairi ranar.


Hajiya Lubabatu ce ta fara mutuwa, ba tayi arba'in ma Mummy ta bita, ammi ta ji mutuwar nan ba kaɗan ba, hakan ya sa ta ce duk ta yafe musu, kuma ta rungumi Fauziyya da ruƙayya ta cigaba da riƙo, baba uwani a can garin su mahaifinta aka ganota, Cancer ya kama mata ƙafafuwa ita ma, babu kuɗin da za ayi mata aiki, ammi ba ta yi shawara da wani ba ma, ta tura sidi aka biya kuɗi, aka cire mata ƙafafuwan ta saya mata keken guragu tare da bata jarin sana'a.


Rumaisa kafin ta gama makaranta sai da ta haifi ƴan maza biyu, ta din ga Addu'a "Allah kar ka sa na yi irin ta mama na haifi ƙanwar maza, ba zan iya ba" takawa ya din ga yi mata dariya ya ce ashe kina sane ki ke tsiyata ku.


Idan ta tuna wasu rashin hankalin da tayi a baya, ta ji kamar ta yi wa kanta duka, babban abun da ya bata mamaki, bai wuce duk shekarun nan takawa yana ajiye da wasiƙar da ta rubuta masa, na cewar ya taɓa mata nono, yayi ta tsokanarta yana dariya.


Samha kuwa rayuwa ta juya mata baya, dan abun da Jamil ya aikata, da wanda tayi ita ma, ya zame mata baƙin fenti, aka rasa mai aurenta, duk gayu da ƙwalisar samarin duk suka watse.


Runaisa ba ta bar harkarta ta zane-zane ba, dan har rubuce-rubuce take yi, kamar wasa ta zama popular manyan mutane suke sayen zane-zanenta.


Cikin ikon Allah rumaisa ta zama criminal lawyer, sunanta ya shahara sosai, ga ta lawyer, ƙwararriya wurin zane-zane da rubuce-rubuce, kuma ƴar kasuwa.
A duk lokacin da aka yi hira da ita, ta kan ja hankalin mutane a kan cewa a duk lokacin da aka samu ɗa mara ji kamarta a cikin al'umma, kar a tsangwame shi, a ja shi a jiki a duba wace irin baiwa Allah ya yi masa a dafa masa a kanta, saboda Allah baya halittar abun da ba shi da amfani. Kamar dai ita da tun a tasowarta ko makaranta ba ta so saboda rashin jin ta, amma cikin ikon Allah a yanzu, ilimi na addini da na zamani sai dai ta koyar da wani bisa jagoranci da jajircewar mahaifiyarta yayyenta da kuma mijinta ta zama abun da ta zama a yanzu.








TAMMAT BI HAMDILLAH!!!




GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TAIKAI MAI KOWA MAI KOMAI, DA YA BANI IKON FARA RUBUTUN NAN YA BANI ARON RAI DA LAFIYA NA KAMMALA SHI. ALLAH YA SANYA A AMFANA DA DARUSSAN DA KE CIKI, AKASIN HAKA KUMA ALLAH YA YAFE MANA.


SAƘON GAISUWA TA MUSSAMAN, UWAR KIRKI UWAR ALJANNA UWA TA TA KAINA, MALAMA NAFISU ADAMU, DA MUKA FARA TARE HAR NA KALLAMA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MIKI HAR GADON BACCINKI.




GODIYA TA MUSAMMAN GA ƳAN UWANA.
ZEE KUMURYA NIMCY LUV, TARE DA SAURAN MARUBUTA MAIMOON, MARYAM MAI ƘOSAI ANTY ZEETY, KUNA DA YAWA GASKIYA DUK INA JI DA KU DAI.


BAN MANTA DA KU BA, MUTANEN DA SUKA BANI TALLACE TALLACENKU
MAMAN MEENAT COLLECTION
MAMAN KHADIJAH MAI SABAYAR ƳAN GAYU TARE DA MAMAN ILHAM KUN GA DAI YADDA SUKA KANKARO RUMA A GIDAN AURENTA, KAR A GAJI DA CIGABA DA PATRONIZING KAYANSU, TESTED AND TRUSTED RUMA TA YI AMFANI DA SU KUN GANI.


WAƊANDA SUKA YI SUPPORTING ƊINA, WURIN SAYEN LITTAFINA, ƳAN NORMAL GROUP, SPECIAL DA AKE TURAWA TA PC, ƳAN AREWABOOKS DUK INA GODIYA, DA SUPPORTING ƊINA ALLAH YA ƘARO MUKU ARZIKI DA BUƊI MARA YANKEWA.


WAƊANDA SUKA DIN GA FITAR MINI TARE DA KARANTAWA, BA TARE DA KUN SAYA BA, DA WANDA SUKA YI MINI AMFANI DA SHI WATA SIGAR BA TARE DA IZININA BA, INA YI MUKU TUNI DA ALLAH BAYA YAFE HAKKIN WANI A KAN WANI, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA.
0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK.




DOMIN GYARA SHARHI, KO SHAWARA ƘOFATA A BUƊE TAKE.
SAI MUN SA
08081012143


Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu.
Silar haɗuwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba"


Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji.
Wannan wayar na ɗauke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haɗa mota da ƴan bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta ɗauka, ciki har da jakar bullet mai ɗauke da wasu lambobi, da sunan SMOKE.
A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara.
Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan.


Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta'adda.


Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba.


Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce".


Ɗiff ɗakin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna".


Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna".


Rumaisa ta ɗora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta.


Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan.


Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi.


Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya....


"Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna"


Wambai ya ɗagawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?".


"Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha.


Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah"


Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa.


Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment"


Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta.


Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka ɗauki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka ɗauki gawar.


A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi.


A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faɗuwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin.


Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba.


Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin ƴan uwanta maza muka yi aikin nan.
Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking ɗin ta, haka zalika ɗan uwanta Yasir yayi tracking ɗin ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result ɗin sa, ni ma ina da nawa da police suka yi"


Wani daga cikin ƴan sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne".


"Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami'an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami'an tsaro.
Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin.


Maganar ina ƙoƙarin ɓata zumunci ta hanyar haɗa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daɗe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar ɗaya daga cikin ma'aikatana, na naɗi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki".


Adam ya tashi jiki a matuƙar sanyaye, ya ɗauki excuse ya fita amsa waya.


Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na.


A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faɗi abubuwan da suka shafi ɓangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa.


Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raɗaɗi, saboda abun duniya yana ciki ɗaya da aisha, ubansu ɗaya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ƙoƙarin sanyawa a ɗora zargi a kan Adam, Adam ɗin da ya kasance abokinsa ɗan uwansa da suka tashi tare.


Kuka matar turaki take yi, ta ce "Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa".


Bashir ya ce "Hajiya sai dai ki yi haƙuri, domin kuwa jami'anmu sun riga sun kama shi ma"


Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce "In faɗi me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faɗa da kanku?"


Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce "Dole ka cigaba da zama a hannun 'yan sanda su kammala bincike"


Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba ɗaya falon ya hargitse da hayaniya.


Rumaisa ta ce "Babban roƙon da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaɗai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba".


Bashir ya ce "Haka ne, amma ban taɓa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba"






Adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da ƴan team ɗin ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaɗai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu ɗaukar maka matakin suna cikin SMOKE.
ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, Ɓangaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ƙasar nan.
Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaɓar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa.
Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaɗai ka yi nasarar gano suwaye, ɗan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin ɗauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu ɗaya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al'amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da ɗanka, dan kuwa ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil.
Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku" ya katse wayar.


Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.


Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?"


Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba, Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment