Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ta fuskanci komai ba.


Takawa ya ƙaraso ya karɓi kayan hannun matar, ya yi signing ya ce mata ya gode.


"Wai ni ya aka yi ka saka aka kawo abinci, naga ba wanda ka kira a waya"


Ya ce "Ai na so matar nan ta zane ki, kawai kin saka mata a gaba, kina ta mata surutun banza da hausa, bayan ba ganewa take yi ba".


Ta ce "Mhmm, nima fa kamar da a makarantar mu, bana gane komai, kamar dai ni da matar nan, ni babban abun da nake ganewa, a bani kuɗin makaranta na sai goriba, ko manɗo na yi tsokana da surutu na dawo gida".


"Yanzu fa?"


"Ina ganewa, anty laila ke koya mini sosai, kuma zaka ga result ɗina"


Suka karya, yana yi mata mitar, dukan da tayi masa cikin dare. Dariya ta din ga yi masa, ta ce "Ai dama na gaya maka, Innalillahi ni fa sai da aka yi mini aure na daina fitsarin kwance, musamman idan ana sanyi, in ji fitsarin ya matseni, sai in yi mafarkin gani ina fitsari a banɗaki, wallahi ina tashi zan ga nayi a kwance"


"Yanzun ma waye ya sani ko kuna abun ki?"


Ta ce "Haba papa, lokacin fa ina yarinya ne fa nake baka labari"


"To yanzun girma ki ka yi, ko da yake an fara girma fa, mantawa nake yi" Saboda kar ya zauna ya fara tsokanar ta, ya sanya ta tashi ta tafi window tana leƙawa.


Can ya ji ta ce "Innalillahi"
Ya ɗago ya ce "Lafiya?"


"Papa ina ka kawo mu nan? Nan ai duk ƴan iska ne leƙo ka ga fa"


Ya ƙarasa ya tsaya a bayanta, wasu mata take nuna masa, sun sha matsatsun kaya, marabarsu da tsirara kaɗan ne, sai kaiwa suke suna komowa.


Ya ce "Sun yi kyau tubarkallah" ba shiri ta kalle shi ta ce "Me ka ce?".


"Na ce sun yi kyau"


Haɗe rai ta yi ta ce "Amma dai ka san haram ne ko?".


Adam ya ce "Ke fa ki ka nuna mini" janyo window tayi ta rufe tana huci.


Ya fara ƙoƙarin ture ta ya sake buɗewa ya ce "Matsa ban gama gani ba"


Rumaisa ta haɗe rai ta ce "Wallahi ba zan matsa ba"


Yayi murmushi dama abun da yake so kenan, ya ce "Yanzu da cewa na yi, ki saka irin kayan, cewa zaki yi ke ba ƴar iska ba ce, tunda na ga na bati, ai sai ki barni na kalla ko?"


Tayi shiru tana kallon sa. "Ko zaki saka?" Yayi maganar yana tsareta da ido, sai dai tayi shiru bata bashi amsa ba.


Ya ce "Ke ba ƴar iska ba ce ko? Laila ba ta gaya miki babu kunya tsakanina da ke ba?"


Shiru tayi tana tunani, tabbas laila ta gaya mata, kuma usy ma ya gaya mata, kenan da gaske suke mata?.


A hankali ya ce "Shikenan, laifina ne" ya juya ya bar wurin.


"Zan saka" ta furta kamar tayi zunubi.


Ya tsaya ya waiwayo ya ce "Are you serious?" Ta jinjina masa kai alamar eh, dan har ga Allah saboda kar ya cigaba da kallon waɗancan matan ya sanya ta ce zata saka, kuma bata son kishiya.


Ya ce "To mu je in anjima mu sayo, zaki saka?"


"Eh amma zaka daina kallonsu?".


"To me zai saka na kallesu? Ai na san ba kyau, in dai zaki saka ba zan sake ba"


Murmushi yayi yana kallon baby face ɗin ta, ta faɗa ne kawai saboda kishi.


Ya ce "To shikenan, in anjima zamu je, saura sai mun dawo ki ce baki san zance ba"


Wuni suka yi tare, ya bata damar yin surutunta son ranta, ba tare da nuna mata ya gaji, ko ya ƙosa ba, suka sha dariyarsu tare ta bashi labaran ta lokacin tana gida, salla ce kawai ta din ga fitar da shi.


Da zai fita sallar magariba ya ce mata "Mimi, ki zauna karki fita ko ina, idan na idar da salla zan je meeting ba daɗewa zan yi ba, zan dawo in sha Allah"


"Wai ni zaka bari a ɗakin nan nikaɗai?"


"Eh, ba daɗewa zan yi ba"


"Wallahi tsoro nake ji, haka kurum a yankani, idan ka tafi sai dai ka tarar da ni a bakin titi, ko na ɗaukko rigima da sai an koromu daga wurin nan. Ko kuma in jiraka a wurin shigowar nan, kuma ka bani system ɗin ka da wayarka ɗaya nayi game har ka dawo".


"Salon ki goge mini wani abun, idan ki ka goge mini abubuwana, sai na kai ki prison, zan baki amma a ɗaki zaki zauna".


Rumaisa ta basar ta ce "Prison ai sai marasa gaskiya, dan Allah kar ka barni a nan papa, da gaske tsoro nake ji fa" tayi maganar cikin shagwaɓa.


Yayi ajiyar zuciya ya ce "Bari na je nayi sallar sai mu tafi".


Da misalin ƙarfe takwas da mintuna biyar na dare, takawa yayi parking a gaban harabar wata plaza, ya sanya rumaisa a gaba, suka shiga.


Wani irin katafaren office ne, ƙato mai kyan gaske.


A can suka tarar da bashir ma, ruma ta ce "Yaya bashir, ya aka yi ka zo nan?"


Ya ce "Ɗazu na shigo ni, ai ya ce mini tun jiya ku ka zo"


Suka gaggaisa da mutanen wurin, sai dai ruma ta raɓe a kusa da adam, saboda duk sai ta takura, ita kaɗai ce mace a cikinsu.


"Adam wannan kuma fa?" Cewar ɗaya daga cikin su, da ya tsare rumaisa da ido.


Barrister sa'ad ya ce "Madam ɗin sa ce".


Ya ce "Masha Allah, amma me zata yi a nan, harkar aiki ce fa"


Adam ya ce "Ba zata hanamu aikinmu ba, mu fara kawai barrister meye a ƙasa?"


Barrister sa'ad ya ce "Eh to, harƙallar fasa bututun man fetur, da kullum ake yi wa ƴan ƙasa ƙarya da ita, Dss sun kama mutum uku shekaranjiya a delta, bayan sanarwar da hukumar matatar mai ta fitar cewa, man da ake samarwa a Nigeria yayi ƙarancin da kuɗin da yake kawowa ƙasa ba zai wadaceta ba, sai an ciyo bashi, sai dai mutanen sun ce SMOKE suke yi wa aiki, an sake su ba tare da kowa ya san an yi bama, Salim ne yake gaya mini"


Takawa ya ce "SMOKE again?"


Bashir ya ce "Adam, shirye-shirye fa sun yi nisa, wakili zai tsayar da ɗan sa Khalifa takarar ɗan majalisa, kuma ka san jam'iyyar tana da ƙarfin da ko da ƙarfin tuwo zasu ƙwata su bashi, mecece makomar al'ummar da mutumin banza zai jagoranta?"


"Ba wannan ba, cire sunanka da ga jerin jami'an da za a ƙarawa matsayi bayan dawowa daga ƙaro karatu, yafi ɓata mini rai".


Takawa ya ce "Ba matsayin nake buƙata ba, goyon baya ta yadda zamu yi ƙarfin da zamu iya ƙalubalantar kowa. Akwai buƙatar lawyoyin cikinmu, ƴan siyasa da sauran hukumomi masu son yin aiki domin ƙasarmu ta gyaru, ace sun ƙara yawa".


"Adadin mutanen ka adadin matsalarka, adadin yadda sirrinka zai din ga fita, aikin yana tarwatsewa, ayi ta haɗaku rigima da zargin juna"


Tsit suka yi suna kallonta, shi takawa a wurinsa ba abun mamaki bane ba, jin kalaman hangen nesa a bakin ruma idan ta ga dama, dan na shirirtarta sun fi yawa.


Ya ce "Silent mimi, meeting fa nake yi".


"Daga bayar da shawara?"


Takawa ya ce "Idan ki ka kuma magana ba zan sake fita da ke ba"


Barrister sa'ad ya ce "Adam, allow her please, gaskiya fa ta faɗa"


Takawa ya ce "Rabu da ita, yanzu dai sa'ad, zan yi magana da salim, ya sake bin diddigin samo mana hujja da tabattar da abun da ya faɗa, zamu sanar wa da mutane.
Sannan ɓangaren media, su musbahu, dole su cigaba da tattaunawa da masana tare da fahimtar da mutane illar ciyo wannan bashi, dan ba ƙasa ake ginawa ba, kansu suke azurtawa, na rasa wani asarraren ne ya zauna ya samar da dokar yi wa ƴan majalisa da tsofaffin gwamnoni hidima da kuɗin al'umma, wace irin ƙasa ce haka, a mulke ka a gasa ka, kuma a ranto kuɗi a bawa wanda ya zalunce ka ace ka biya, abubuwan nan sun fara isata, muna tufka ta gaba ta baya na warwarewa".


"Wannan faɗar fa da ka ce ayi ta gayawa mutane, ƙara musu takaici ku ke yi, maganin abun yakamata ku yi musu, tayaya za a zo ace mini wane ya ɗauki kayana, mutane na kallonsa babu wanda yayi yinƙurin hana shi, balle a karɓa mini kayana, kuma azo ana bani labari, kamar haka ne fa papa"


Bashir ne ya tafawa rumaisa, ya ce "Kai, rumaisa kina da brain irin sosai ɗin nan, takawa yakamata kayi mata special adviser a tafiyar nan. Amma rumaisa mun koma maganar mu ta farko, domin iya kama ɓarawon da yayi miki sata, dole wataƙila mutane na buƙatar ƙarfi da yawa, dan wataƙila ɓarawon ba ɗaya bane ba, sun ɓuya da yawa da muggan makamai"


"Sai ku yi musu dabara, ta hanyar yi musu tarko, ku kama wakilin nasu, idan kuka cigaba da zuba ido ana yi mini sata, idan nawa kayan suka ƙare kan naku zasu dawo, kuma bayan sun gama idan suka rasa abun sata, ku zasu fara kamawa suna sayarwa, ana ciniki ku kamar dai yadda ake fataucin dabbobi, ayi ta ciniki kamar an kama bayi, kamar dai yadda aka sace ni, da ni da anty aisha".


Maganganu rumaisa ta saƙa musu cikin hikima, da sai da ta sanya su cikin nazari, adam ya ce "Ina ga mu tashi haka, zamu biya wani wurin ne da ita, zamu haɗu gobe in Allah ya kaimu "


Barrister sa'ad ya ce "Allah ya kaimu, amma lallai muna buƙatar ƙwaƙwalwa irin t madam a tafiyar nan".


A ransa ya ce 'Baku san butsancinta ba, sai tayi muku wani shirmen zaku gane baku da wayo'.


Adam kansa har wani ciwo yake, yana ta tunanin maganganun ta, ita kuwa ko a jikinta, har suka isa masaukinsu.


Kamar yayi mata magana a kan maganganun da tayi, amma ya shareta, dan da yayi zata fara wahalar da shi.


Kwanansu uku a Abuja, ya kaita yayi mata sayayya, ya kashe kuɗ sosai, banda tsarabar da ya yi mata da zai dawo, banda uban kayan lefenta da haryanzu wani abun ma bata taɓa ba, ga shirin bikin iman nan ma yana ta hidima.


Suna tafe a hanya tana kallonsa, ba ƙaramin tausayinsa take ji ba yanzu, gaba ɗaya yadda ta tsammaci halinsa ba haka yake ba, duk da dai mafaɗaci ne mai zuciya, amma a zamansu ta tanƙwara shi ta ƙarfin tsiya ya tanƙwaru, dan shi kansa ya san ko bai durƙusa mata a kan gwiwoyinsa a zahiri ba, a baɗini yayi.


Tana ta ɗaɗɗaga kayan da ya saya mata tana murna, wasu kayan tana tunanin anya zata iya sawa kuwa, duk da anty laila ta koya mata saka ƙanan kaya, amma wasu kayan sun yi watsewa da yawa.


Yana zaune a kan gado yayi shiru, yana zancen zuci, rumaisa ta buɗe akwatinsu, ta fito da pencils ɗin ta na zane, ta ɗaukko cardboard paper, ta zube su a kan ƙaramin Centre table, da cleaner da duk abun da take buƙata.


Ta tashi ta nufi takawa, ta riƙo hannunsa ta ce "Taso muyi zane papa"


Ya ƙwace hannunsa ya ce "Leave me, am not in mood"


Ta ce "Gaskiya ni ba zaka zauna kayi mini shiru ba, ka taso".


Ya ɗaukko wayarsa ya ajiye mata, ya ce "Gata nan je ki kiyi hirar da ita".


"I want de encrypted the portrait i gave you 6months ago".


A hankali ya juyo yana kallonta, ta jinjina masa kai ta ce "Taso"


Tashi yayi a hankali ya biyo ta, suka zauna a tsakiyar ɗakin.


Ta fara da zana farin wata, irin a daren goma sha huɗu.


Yayi shiru ya nutsu yana kallon ikon Allah, sannu a hankali ta yi zane iri ɗaya sak da wanda ta bashi, sai dai a wannan karon da alamomi da bayanai yadda zai gane.


Ta zana kanta a zaune a cikin daren a daji, ga masu garkuwa da su riƙe da bindigogi, sai ta zana wata hanya, ta rubuta unknown distance. Tayi alamar yadda sautin ababen hawa ke kaiwa suna komowa a nesa da wurin, duk da yanayin wurin babu alamar abun hawa zai iya bi.


Ta kalleshi ta ce "Papa meye ma'adanai?"


Ya ce "Resources, albarkatun da Allah ya ajiye a cikin ƙasa, da ƙasa ke amfani da su, a sayar ko a sarrafa dan al'ummar ƙasa su mora"


Ta ce "Ok"


Sai ta koma kan zanen ƴan ta'addan, ta nuna ɗaya yayi magana ya ce "Ga mutanen SMOKE can suna aiki"


Ɗaya kuma ta yi alamar ya ce "Ƴan wahala, coustom sun gama gyara musu hanya, da sun je za su wuce"


Ta koma wajen da tayi alamar sauti na tasowa ta ce "Unknown resources"


Ta ce "zasu iya kasancewa ma'adanai ne kawai? Ko kuma akwai wani abu bayan ma'adanan da suke ɗauka. Ka tambayi uncle bashir, a ina ya tsinto ni, ba zan ce takamaimai in da ya ganmu nan ne aka sace mu ba, amma daga nan zuwa in da aka ɗaukemu, kwana uku nayi ina tafiya, sannan duk wanda aka kama a wurin da ma'adanan nan suke, sun san suwaye SMOKE!"


Jiki a sanyaye ya ɗauki zanen yana dubawa, rumaisa ta sake cewa "Nayi maka wannan bayanin ne, saboda naga you are curious about it. Amma still SMOKE ɗin na da nasaba da sace anty aisha, dan ita ba dan a karɓi kuɗin fansa aka kawota ba, dan a koyawa mijinta darasin da har abada ba zai manta ba aka kawota, ku kula sosai wannan aikin SMOKE ne. Shi ne abun da aka ce lokacin da aka kawota.
Papa idan har babu wanda ya san anty aisha ta dawo daga kai sai ita, dole-dole akwai na kusa da ita da ya sani, aka haɗa baki da shi, ko ta gayawa wani kai baka sani ba, ko kuma ka ƙara tsananta bincike a kan yaronka da aka kashe wanda shi ya tafi kai ta garin nasu"


Tamkar rumaisa ta zare masa lakar jikinsa, gaba ɗaya in da ya dasa hasashen binciken sa daban, abun da rumaisa kuma ta gaya masa dabanz to meye manufar ƙin yi masa wannan bayanan tun da wuri?.


"Mimi meyasa duk baki yi mini wannan bayanin ba tuntuni, ki ka bari nake ta wahala?".


"Saboda baka buƙatarsa a lokacin da ka neme shi, yanzu ka mayar da hankali ka san suwaye SMOKE ɗin dai. Saura kuma ka je ka gayawa wannan abokan aikin naka, dan ka fiye yadda da mutane da yawa, yaya bashir kawai zaka gayawa, idan ba haka ba zan sake gaya maka komai ba"


Daga haka ta tashi ta bar shi da tufka da warwara.


Gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa da walwala, kwanyar rumaisa ba duk kai ba, rashin jin ta kawai mutane ke iya gani, amma ba kowa ke iya ganin baiwar da Allah ya yi mata ba.


Ita dai hankalinta kwance ta kwanta baccinta, amma adam bacci ya gagare shi, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya kasa kwanciya yayi bacci, yama rasa me zai yi.


Yayi alwala, ya tayar da salla, yayi ta addu'a.


Har ya hau kan gadon zai kwanta, ya buɗe ya shiga kallon hotunan aisha.


Ya kashe system ɗin ya kwanta, rumaisa duk tana kallonsa.


"Papa"


"Mimi".


"Ka kwantar da hankalinka dan Allah, zaka yi nasara, sai dai kar ka sanya ran ko komai ya bayyana zaka samu adalci yadda ka ke tsammani"


Bai ce komai ba, ya juya ya rungumeta sosai a jikinsa, yana ta jejjera numfashi.


"You are brave papa".


"Yanzu kin yadda ba sakaci ne ya sanya ina jami'in tsaro na kasa karɓo Aisha ba?".


Ta ce "Faɗa fa nake dan na baka haushi kawai, anty aisha ta gaya mini kai mutum ne mai yi wa iyalinsa hidima sosai"


Riƙe kunneta yayi ya ce "Daɗin me ki ke ji, idan kin ɓata mini rai ne?"


"Daɗin da ka ke ji idan kana tsokanata" ta bashi amsa.


Ya ce "Yauwwa kin tuna mini ma, bari in ɗora daga in da na tsaya, my mimi ƴan mata, budurwata ta kaina".


Ƙoƙarin ƙwacewa take daga jikinsa, sai dai abu kamar wasa, Adam ya mayar da rumaisa cikakkiyar matarsa.


Wanda shi kansa abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, kenan matsalar ta sa a cikin gidansa take kenan?.


Bayan gama jero sunayen ƴan gidansu, har da kiran ƙawayenta, banda cizonsa da ta din ga yi, kamar ƴar damusa.


Bayan shuɗewar wani lokaci, ya laluba ya ɗau wayarsa, ya kunna fitila ya haska fuskar rumaisa, da ta haɗa yawu da majina, da hawaye sai jan majina take yi tana kuka.


"Amarsu ta ango, finally budurwata ta zama matata, wannan cizo kamar damusa mimi" ɓare baki tayi, ta cigaba da kuka, tana wallahi sai na faɗa.


"Wa zaki gayawa? Ammi ko mama?".


"Kowa na duniyar nan, kuma sai na rubuta kowa ya gani, kamar yadda na taɓa yi maka"


Ya yi dariya mai isar sa, kashe murya yana kwaikwayon ta ya ce "Yaya usy, mai sunan baba. Ai ko shi mai sunan baban, bai isa hana ni karɓar sadakina ba. Inyee ni dakata ma, nawa na baki sadaki? Ciko zan yi ko wani abu zaki rago mini?"


Ta ɗora hannu a ka, tana cigaba da kuka har da ta shiga uku ta lalace, shi kuma ya sakata a gaba, yana ta tuntsira dariya, bai taɓa ganin karaya ƙarara da miƙa wuya a wurin rumaisa ba sai yau.


Ya ce "Dan Allah ki goge wannan majinar mana, ƙazama, kin bayar da mata gaskiya" ya janyo ta yana goge mata hawayen fuskarta.


Buge hannunsa tayi ta ce "Wallahi yaya usy ne ya janyo mini, ya ce duk abun da ka yi mini ba haram ba ne, idan ban yadda ba zaka yi mini kishiya da shi da anty laila, suka ɗorani a hanyar da bata kamata ba".


"Au zuwa ki ka yi ki ka gaya masa nayi miki wani abu?".


Ta ce "Eh, duk abun da ka yi mini faɗa nake yi, wallahi Allah ya....." Sai kuma tayi shiru.


"Allah ya isa, Usman ɗin ki ke yi wa Allah ya isa"


Ta girgiza kai. Ya ce "Ni?"


"Ni ban maka Allah ya isa ba"


Ya sake juyo da ita ya ce "Oyaa say thank you".


"Thank you for what?" Tayi maganar tana mamakin rainin hankalin da yake mata.


"Thank you for everything i did, faɗi"


"Wallahi ba zan faɗa ba"


"Ok, naga alamar bakin ki bai mutu ba, am equal to you".


"Na shiga uku, na gode Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata"


Yayi murmushi ya ce "Kowa ya tuba dan wuya ba lada, ya cikata" ya sauka ya nufi toilet.


Har ya fito tana zaune a takure, jikinta sai tsuma yake yi, tana ta tunanin ya ma za ta yi ne.
Abun gaba ɗaya ta rasa a wani muhallin za ta saka shi, anty laila dama tuntuni tayi mata bayani, usman ma duk da ba kai tsaye ya gaya mata ba, amma yayi mata bayani, amma ita dai sam abun ya zarce tunaninta.


Kamar zai tsayar da taxi ya ce "Sss" ta ɗago ta kalleshi.


"Zo"


Tayi shiru tana kallon sa.


"Magana fa nake" a hankali ta tashi tana raɓe-raɓe.


"Auren kenan mimi, ki daina hararata kamar zaki kai mini duka, ki shiga toilet ki yi wanka, kamar yadda ki ke na period, sai dai wannan akwai banbancin niyya".


Karatun ajin su yasir ne ya faɗo mata, sai yanzu ta gane ina karatun ya dosa, a wancan lokacin kanta a doɗe yake. To idan haramun ne ai ba za a koyar a makaranta ba, duk da haka ai mama ba ta ce mini haka ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita.


A haka ta gama abun da za ta yi ta fito, sai dai still ba ta daina kuka ba.


"Haba mimi, hawayen zai ƙare fa, is ok ya isa haka, zo in canza miki kayan sai ki kwanata ki yi bacci".


Ta girgiza kai ta ce "Ni ba na so"


Ta canza kayanta, ta kwanta a ƙasa, wai ba zata sake kwana a kan gadon ba.


Ya tayar da salla, sai da tayi bacci, sannan ya ɗauke ta ya mayar kan gadon.


"Allah kai ka san dalilin da ya sanya ka ɗauki Aisha, ina tsaka da ƙaunarta, ka bani rumaisa, kuma ita ma ka sanya mini son ta, Ubangiji Allah ka jagorance ni a al'amarin nan, ya sanya ta zame mini sanyin idaniya, kuma ka bani ikon kula da ita" yayi Addu'a murya ƙasa ƙasa, ya shfa kanta yayi murmushi ya ce "Ni na cancanci in ƙara sadaki mimi"


Su da zasu yi kwanaki biyar, abu kamar wasa adam yayi burus da komawarsu, ya addabi rumaisa da sai da tayi dana sanin biyo shi, kuma ya hanata waya da kowa, ammi tana mita ta ce tana son ganin rumaisa suna shirin biki, ga sabir yana ta rigima shi mimi.
Adam yayi mursisi ya ce aiki ne ya riƙe shi zasu dawo.


Tayi kukan, tayi rashin kunyar, tayi tsiwar amma babu wadda tayi tasiri, adam yayi burus da ita.


Yau suna kwance da safe, tana jin yana waya da laila, laila tana tambayarsa rumaisa, ya ce bacci take.


"Wai takawa ba zaka dawo da yarinyar nan ba?"


"Honeymoon muke" ya bata amsa.


"Ni ka ke gayawa haka, lallai baka da kunya, dan Allah a dawo mana da ita, wallahi we are missing her".


Wata shida na barku tare da ita, dan haka a ƙyaleni.


"Anty laila" rumaisa ta yi maganar kamar za ta yi kuka.


"Na'am mimi, ya kike?"


"Dan Allah ki saka baki ya dawo da ni gida, na gaji" tayi maganar tana kuka.


Katse kiran yayi, ya harareta ya ce "Da gaske faɗa musun zaki yi abun da nake miki? Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana, kuma Allah ya tsinewa mai tona asirin aurensa, sirri ne mimi ba a faɗa".


"Ni wallahi a gida ba a ce mini haka ba"


"Amma laila ta gaya miki ai, kuma Usman ma haka, amma tun da haka ne shikenan, ina ga kawai wani auren zan yi"


Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*


*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon

Please Login or Register in order to submit comment