Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
๐Ÿ’”_*DEPRESSION*_๐Ÿ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 15*











Acan adamawa kuwa ummace keta faman Kiran numbar doctor ak fadama Amma Ina Bata shiga, Nan d'anan hankalin ta ya tashi ta sake kallon sumayya, itama sumayya kallon ta tayi Tace "Wai umma yauma babu sa a shikkenan inaga yadaina Kira ,to ko ya mutu ne?" "N'a ci uwarki a gurinnan ubanwa ya kasheshi insha Allahu ma yanan araye Bai mutu ba ,sokike kifada abakin mala iku narasa Wanda zai bani kudade, itama shegiyar yarinyar Nan ciremata kayannan tun da Bai daga ba, Kuma wallahi akanta Zan huce, Ni za asa asarar kudi, kigani fa Har naira dubu biyu na cire n'a sayawa yarinyar nan Kaya d'uk dan ya gani ya ji dadi ya turamin wasu kudin Amma yaki kunna wayar sa" umma ta fada lokacin da take damko Amnaa tana janta har ta cire mata Kayan, sannan ta SHIGA dala Mata duka kamar ita ce ta Hana Abeed din daga wayar, Allah sarki Amnaa ta dage sai zunduma ihu take, ",shegiyar yarinya Gama kukanki Babu Mai ceton ki wallahi uban nakima saura kiriss n'a hallakashi Har lahira" "innalillahi a,a umma sokike kimai damu marayu Dan Allah karki Soma indai akan wannan yarinyar ne gwara ita ta mutu" dallacan shashasha wazaki rainawa wayo mai uban naki ya tsinana Miki ,harda zakice min ke kar ya mutu ,to saina kasheshi din saime" umma tayi tsaki ta tashi tare da sakin amnaa a kasa, jikuke kwalla ta bugu da bango take tasake chanyarewa da kuka kanta ya kumbura.


*Faransa*


Tun da Abba ya sake zubewa a jikin bangon Bai motsa ba Haka ma momy tana zaune tana faman aikin kuka, Gaba ki daya ma ta manta da Zaid a cikin gida Yana baxcy Sabi da tsananin tashin hankali.


Doctor ne ya Soma Takoma in da suke bayan awa biyu da kawo su fu ad, Abba dai ganin yadda likitan yake tun Karo in da suke yasa ya tabbatar da cewa su Abeed ko sun mutune ko sun ta shi, Dan Haka da sauri ya nufi in da yake yace "doctor! Doctor!! Ya jikin nasu sun farka ko, Dan Allah kada ka fadamin mummunan labari sonake n'a san suna raye, kada kacemin sun mutu"


"Amm ka kwantar da hankalin ka alhaji indai yaran Kane cikin ikon allah yatashi kafadin su ,saรฏ dai muce alhamdulillah allah ta Kara mana lafiya baki daya, amma saรฏ dai alhaji akwai wata matsala guda daya, "matsala kuma tame?" Abba ya fad'a Yana zaro manya manyan idanuwan sa waje, "no ka kwantar da hankalin ka yar karamar matsala ce a yanzu, nan gabane nake tunanin zata iya zama babbar matsala" "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Doctor matsalar me?"

"Yaran ka duk da bansan mai yake daminsu ba ,Amma dai babban ya Dade Yana fama da damuwa a zuciyarsa Kuma muddum ba a daina yimasa abin da zai sashi a depression ba zuciyar sa tana gab da bugawa ,Dan ayanzu ma sai dai kuyi hakuri ya kamu da ciwan zuciyar" baya abba yayi tare da dafe kirji ya saki kuka Mai ban tausayi Yana girgiza Kai yana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Shikkenan wallahi duk laifi nane, duk abin da ya faru da shi nine silah"


Cikin kulawa da nuna dumuwa akai doctor yashiga lallaba Abba Yana Dan bashi Baki da llabawa Yana cewa "kayi hakuri alhaji ,komai kagani jarrabawa ce daga allah , to ka kaddara ma wanan ciwo da ta samu danka jarabawa ce daga allah kayi hakuri ka fawwala wa allah ,ciwan zuciya da ya Kama Abeed hakan baya n'a nufin cewa mutuwa zaiyi ba, a,a bazai mutu ba saรฏ lokacin sa yayi " "innalillahi wa'inna ilaihirraju un doctor bazaka gane ba, bazaka gane abin da nake nufi ba, Ni kadai nasan abin da nake ji game da abin da yasamu yaranna wallahi nasan komai ne akaso dari n'a wanan abin kaso 99 nine Sana di , doctor kada ka cemin shima fu ad din ya kamu da ciwan zuciya ,Dan Allah ka fadamin wani abin da zaisa zuciyata bazata sakรฉ karaya ba" abba ta ciga ba da kuka har da majina.


Shiru doctor ya danyi kamin daga bisani yace "tabbas ba irin wanan maganar Zan fadamaka ba ,sai dai shima fu ad shigen irin abin da na fad'a akan Abeed Zan sanar maka, domin ayan Zu idan tausayin ka ya hanani fad'a maka ,to fa na cuce ka domin ciwan zai coga ba ne da addabar zuciyar yaronka shiyasa gwara n'a sauke hakkina n'a sanar maka ,ko Babu komai zaka dauki mataki akai "

Shiru Abba yayi ya tsaya da kukan da yake ,can Kuma sai yace "shikkenan doctor Ina sauraron ka ,ko Babu komai nayar da da Allah shine Mai tsara komai ,Kuma shine Mai dorawa bawa duk kan abin da kaga ta sameshi domin ya jarraba shi yaga yadda zai dauki jarabawar".




"Haka ne alhaji ,wanan kwarin guywata dana gani a tattare dakai ba karamin burgeni yayi ba, irin ku akeso acikin duniyar nan masu karbar kaddara hannu bibbiyu mai kyau ko Mara kyau, yau wa yanzu bayan na fad'a maka sai ka biyoni kaga jikin nasu KO?"


"Oh Tom shikkenan Babu damuwa muje Amma Dan Allah doctor kada ka Bari mai dakina taji wanan batun, nasan idan taji hankalin ta bazai taba kwanci yaba kataimaka"

"Shikkenan alhaji insha allah bazan Bari ta sani ba ,muje ki!"


Tafiya suka Soma yi zuwa dakin Abeed dake farko kafin su karasa abba ta kalli likitan yace "yauwa yanzu kam n'a dan dawo hayyaci n'a ,fadamin shi Fu ad din Mai yake damunsa?"

"Uhm"

Doctor ya danyi murmushi n karfin hali kafin daga bisani yace "ba komai bane kusan irin ciwan su daya da yayan sa Abeed ,saรฏ dai shi baikai na Abeed ba, ban bancin anan shine Abeed ko ayaushe zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu tun da shi ciwan zuciya ya kamashi, shikuma Fu ad ciwan Bai kamashi ba ,sai dai Yana bara zanar kamasa sabi da damuwar da ya sa azuciyar sa, so ya kamata a ce kun kiyaye damuwar sa da duk wani abu da zai Bata Masa Rai" Jin wannan kashai din na doctor da yayi Masa yasa Abba yaji zuciyar sa ta Soma bugu ,tunanin rugimar fu, ad yake Yi yasan muddum idan Fu ad ya tashi dolene sai ya nemi wannan littafin domin ya karasa Karan tawa, zuciyar Abba cike da farga ba yace "nashiga uku wallahi tun da fu, ad ya San akwai abin da ake boye Masa nasan Babu mahalukin da zai Hana shi karasa karanta littafinnan, Kash maiyasa ma na nuna Masa inda book din yake, Gaba kidaya n'a sha,AFA namanta da duk wani abu da ya faru ,nayi tunanin Abeed kawai Zan batawa Rai Sabi da girman abin da nayi Masa, ashe Nima har Dani aceki innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Ta furta tare da bude kofar d'akin ya shiga,



๐Ÿ’”_____*DEPRESSION*_____๐Ÿ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*๐Ÿ’”
*#JURIYA*๐Ÿ’”
*#SOYAYYA*๐Ÿ’”
*#DAMUWA*๐Ÿ’”
*#HAKURI*๐Ÿ’”
*#YAFIYA*๐Ÿ’”
*#KYRA*๐Ÿ’”


*Chapter 16*

TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ๐Ÿ’ช๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
๐Ÿ’”_*DEPRESSION*_๐Ÿ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 16*







Jiki Babu kwari Abba ya hango Abeed kwance idanunsa a lumshe sai zub da hawaye yake, da kamar ya fita, sai Kuma yayi karfin hali ya karasa ,kujera ya janyo zai zauna ya tsinkayo muryar Abeed Yana cewa "kada ka zauna abbanmu , bai ka mata ace ka zauna a gurin mutumin da baka so ba," jin maganar Abba yayi kamar saukar aradu bakinsa har rawa yake wajen cewa "Babana haba Abeed Ni nace maka bana sonka Taya za ai uba yace baya son dansa " "uhm abbanmu kenan ,lokacin yin wanan maganar ta wuce kama ta yayi ace iyanzu Kana gida Kana farincikin yanko likkafanin bonne mu, burinka ya cika Abba kayi sanadiyyar sa zuciyata kamu wa da ciwo, kasa rayuwa ta acikin masifa ,akullum laifina kawai kake gani baka ganin laifin zarah baka ganin laifin ka Ni kawai ka tsana idan Zara 'yar kace ta sunna nima d'an Kane abbanmu komai ya faru Abba Kaine ka fara lalalta komai shiyasa Allah ya nuna maka ishara akan Hakan mu" "no Babana kadai na fadan Haka indai wanan matsalar ce kasa aranka n'a hakura Kuma zamu dawo kamar da ,Zan kula da rayuwar ka" " uhm abbanmu kenan Babu lokaci, lokaci ya ruga da ya wuce ,karike kulawarka bana bukata ,lokaci ya wuce Kuma kasan Abba ance lokaci baya jira, albishir daya zanmaka shine ,idan Fu ad ya tashi Zan bashi Wanan littafin ya karanta iya karfin sa Har lokacin da zai Gane abin da kuke boye Masa" "nashiga uku Abeed kada Kai Haka, Dan Allah bana son rasa Fu ad ,wanan littafin zai iya sanadiyyar sa zuciyar sa ta buga ya mutu ya bar duniya, Dan Allah ka taimaka kaji" "abba walalhi Babu abin da zai Hana na bashi littafin Nan ya karanta , da bakason ya San komai ka dauki book din ka bashi ,daman nasani Haka zata faru, kuma ga ranar tazo ,abbanmu kayi hakuri kaddarace ga kudi ga mulki da sarauta Babu abin da baka hada ba, komai Allah ya baka , Amma ya dauke maka kwanciyar hankali da nutsuwa, depression babbar matsalace ga Dan Adam, Kuma ba kowa bane asalin damuwa sai Kai Abba Ni kawai dorawa nayi" kuka Abba ya fashe dashi gami da mikewa jiki Babu kwari ya fita.



Abba Yana fita Abeed ya runtse ido tare da furzar da iska daga bakinsa, ya lumshe Ido, Yana zub da hawaye yace "uhm abbanmu kenan ,Allah ya fitar da mu daga wanan jarrabawar Ni ayanzu nasan tawa tarugata kare " daga Haka Kuma ya Kara sakin murmushin karfin hali ya daga idonsa sama Yana kallon silif.


Abba kuwa bayan ya fita gurin doctor ya koma yace "doctor ka kaini dakin da Fu ad take" Babu musu doctor ya shige Gaba Abba ya bishi a baya Har zuwa d'akin da Fu ad yake, tura kofar yayi ya Shiga shikuma doctor ya dawo office dinsa, kaitsaye Abba Shiga yayi ,a zaune ya samu fu ad ya hada Kai da gywa idanun Nan nasa sun kada sunyi jajur, jiki a sanyaye Abba ya karasa bakin gadon ya zauna, shiru ya danyi baice komai ba ,Haka shima fu ad Bai d'ago ba Kuma Bai Masa magana ba, har tsawan yan dak'iku ,can Kuma sai Abba ya dauki hannunsa ya Dora akan hanun Fu ad kana ya d'ago sa, yanayin yanda yq ganshi ne yasa Abba ya tsorata ,zuciyar sa ta SHIGA bugu bakinsa ya kasa furta komai ,ya bude Baki zaiyi magana Fu ad ya daga Masa hannu Ade da cewa "abbanmu Kar ka cemin komai ,banason n'a kara magana da Kai Har sai ka bani labarin abin da ya faru abaya, yanayin yadda Naga kuna boyemin Abu ya tabbatar min da cewa akwai abin da yafaru wan da ba kwasan nasani, Abba na rokeka Dan Allah ka dakko min wanna littafin kada ka Bari zuciya ta ta buga bansan komai Akan Haka ba, Allah aba kaba namutu Sana din damuwa Akan Haka, bazan taba ya femuku ba koma menene ake boyemin" saurin dagowa abba yayi arazabe yace "ta sallam fu ad Mai yayi zafi Haka ? Dan Allah kada ka fadi Haka ,sanan n'a rokeka ka hakura da sanin wanan labarin ,rashin sanin labarin shine alkairi a gareka" "wallahi Abba maganar Nan da ka fada Takara samin kaunar karanta wanan littafin KO abani littafin kokuma n'a kashe kaina " turo kofar sukaji anyi tare da cewa "ba saรฏ ka kashe kanka ba fu ad ka kwantar da hankalin ka indai har Akan wanan littafin ne zaka karanta shi" Abeed ya fad'a lokacin da take karasowa gabansu, sanan ya zuya ya kalli abbansu yace "abbbanmu Kaine wan da ka fara buga wasan ,Kaine wan da ka fara Toni wanan sirrin da ace baka bashi littafin Nan haryanzu hankalin ku a kwance ,meyasa ba zaka bar wanan gabar iya Ni ba ? Dolene Ni saika kunta tamin, ai aikin Gama yariga da ya Gama dolene Fu ad ya San komai Babu yadda ka iya da kaddara, Fu ad ka shirya karanta littafin nan yanzu ?" Abeed ya fad'a ya na kuka, gyd'a Kai fu ad yayi Yana kallon sa, "Tom shikkenan hakan ya tabbatar min kanason cigaba da karantawa ,kataso mutafi gida nabaka littafin" murmushi Fu ad yayi yace " dagaske Yaya zaka bani?" "Dagaske nake Fu ad taso mutafi" yafada tare da juyawa shima fu ad ya Mike daker ya bi bayansa, abbama tashi yayi jiki Babu kwari ya bi bayansu har suka karasa inda momy take a zaune tana kukan zuci, mamaki ne ta kamata ganin yadda su Fu ad suka fito ,Abba ta kalla Tace "abbanmu Yana ga sun fito Kuma?" "Uhm taso mutafi gida ammi nakara maganar acan" daga Haka suka fita zuwa parking space ko sallama basuyiwa doctor ba suka tafi gida.



BAYAN sun koma gida Abeed ne ta Shiga dakinsa ya dakko wanan littafin , juyowar da zaiyi yaga Abbansu ya marairaice kamar zaiyi kuka ,ga idonan nasa ya kada yayi jajur, Allah sarki tsabar tashin hankalin da yake ciki fuskarsa har ta fad'a,

Muryarsa ya tausasa yace "Babana kada Kai Haka Dan Allah, masu sunan ka akwaisu da jin magana kuma kaima nasan Kana jin maganata sosai ban San maiyasa zuwa yanzu zuciyarka ta kekashe kake tsallake magana ta, Abeeddeen ka taimaka rokarka nake amatsayina na mahaifinka kada kace zaka aikata Haka , wallahi tashin hankalin Gaba saiyafi nayanzu zafi da kunci, fu ad Bai San yayanku yasid ba baisan maiya fitar da shi daga gidanan ba, Haka zalika baisan maiyasa tsawan lokaci da Kai da abdulmajeed bakwa gida ba, yanzu gashi Abjeed ya sake tafiya ga zarah tatafi kaima so kake narasa ku?" "Uhm abbanmu ai bansan Rashi kariga da kayi shi karasa Yaya yasid ma ballan tana Fu ad, ai karka damu nine wan da zanfi Jin Babu dadi idan nasashi, to Kuma Nima din saura kadan abba kasa zuciyata ta buga" Yana gama fadar Haka ya ratsa ta kusa da Abba ya huce batare da ya jira abin da abbansu zaice ba.


K'asa ya sakko dauke da littafin a hannunsa Yana zuwa ya samu Adeena a zaune da Zaid sai ammi ta zabga tagumi ,gefe Kuma Fu ad ne zaune Yana aikin da ta Saba wato tunanin Mai zaifaru dashi Nan Gaba, mikewa yayi ganin Abeed ya dakko littafin ,Yana tsaye har ya karaso ya Mika Masa, jikin Fu ad da hannunsa na rawa ya amsa Yana kallon cikin idon Abeed din, tabbas ya hango tsoro da fargaba da tsananin tashin hankali acikin idanun yayan nasa, Abeed Bai ce komai ba ya juya sama, ammi kuwa zarw Ido tayi tana kallon littafin dake hannun Fu ad, da sauri ta hau sama ,d'akin Abeed ta nufa, Bata sameshi ba, sai dai Abba dake zaune kamar macacce, sai ka kula sosai sannan zaka fahimci idon sa a bude yake, ganin Haka yasa ammi ta zube a gurin sharaf tana kallon mijin nata cike da tausayawa, hannun ta takai kan kafadar abba Yana rawa ta bude Baki zatayi magana sai ta kasa, kawai itama ta saki kuka Mai ban tausayi, suna zaune a gurin na tsawan lokaci suna kuka, har Abeed ya zo shigowa d'akin ya kasa Sabi da kukan da yaji sunayi, gani yake kamar idan ya shigo zuciyarsa zata karye ya amso littafin Nan, Babu yadda ya iya Haka yaja kafarsa daga kofar dakin ya bar gurin.



Ammi ce ta d'ago ta kalli abba Tace "abbanmu komai ya faru Kaine kaja ,yanzu ga shinan wagari ya waya, Ni wallahi har tsoron fadawa duniya irin wannan babbar kazantar da ta faru nake, yanzu mezaka fad'a musu eh, sai da na fad'a maka akwai lokaci komai Daren dadewa sai abin da muke biyewa ya bayyana ko da ace Fu ad Bai tono ba Dole Adeena sai ta tono komai , innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Munshiga uku" "uhm Ammi kidaina cewa kin SHIGA uku Baki shiga ukuba nine Wanda nashiga uku " "uhm ba Kai kadai ba Abeeddeen ma Yana ciki da ace yasid ya nanan komai zaifi saituwa Amma Kash ya tafi ya barmu bamusan duniyar da ya shiga ba ,Haka itama Zara,u ,yanzu kenan yazamuyu?" "Babu abin da zamuyi da ya wuce mu fawwwalawa Allah muga abin da zai faru Nan Gaba".




Fu ad kuwa daki ya shiga ya turo kofa , ya cire rigarsa, ko wanka Bai ba Sabi da cin gudu yake yaga abin da yake ciki, shiyasa ma Bai bu ta kan abinci ba ya hau kan gado tare da bude shafin da ya tsaya yaci Gaba da karatu kamar Haka.......




ALHAMDULILLAH

DUKA DUKA ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN DEPRESSION BOOK 1 SAI MUN HADU A BOOK 2 IDAN ALLAH YA BANI TSAWAN RAI DA NISAN KWANA BOOK 2 AND 3 NERA 700# BABU TSADA GADUK WAN DA YAYI SHIRIN BIYA YAMIN MAGANA.


BOOK 2 AND 3 700# ONLY NO 09166764540

HAFSAT UMAR DANGORO


Duk Wanda ya karanta batare da ya biyani hakkina ba ALLAH YA ISA BAN YAFE BA Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment