Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
๐Ÿ’”_*DEPRESSION*_๐Ÿ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 8*




Tom Bayan oga tanimu ya bawa zaid kayan da zai Kai Tasha,shima ya shirya suka tafi tare, a cikin motarsa sai da oga tanimu ya ga anzo daidai Tasha Sanan ya sauke Zaid ya shiga ciki, duk inda zai huce sai masu gadin alhaji sun tsai dashi sun cajeshi ,ledar hannunsa ce kawai basu amsa ba Sabi da sunyi waya da alhaji yace Aiken sane, sai da zaid ya karasa gate din da zai sadashi da alhaji wani matashim saurayi ya fito daga cikin motar ya tsaya a bakin gate din ,har zaidu ya huce ya dawo dashi yace "kai zo Nan" da sauri Zaid ya tsaya Yana tuno kashai din da oga atiku yayi Masa sai kawai ya cigaba da tafiya, shikuwa wanan matashin saurayin ganin Haka yasa ya bi Zaid da sauri ya rukosa, yace "Kai Ina zaka ? Wane ya Aiko ka" a lokaci daya ya jefowa Zaid wadanan tambayoyin Dan Haka kuwa Zaid ya Yi shiru yakasa cewa uffan, can Kuma sai wannan saurayin ya karbi ledar dake hannun Zaid ya kwance ,Mai zai gani sai ga kayan maye da kwayiyi n'a bugawa, zare Ido yayi yace "Kai waya Aiko ka? Wa akace ka kawowa wadannan kayan?" Yana magana Yana dakawa zaid tsawa, shidai zaidu shiru yayi Yana kallon saurayin cike da furgici a kan fuskarsa



Zaune yake cikin mota mai kimanin nera billion dubu dari da saba,in ,Yana zaunene ya jingina bayansa a baya ,ma,ana mazaunin mai zaman banza ba mazaunin dreba ba, kekkewan dattijon da a kalla zaiyi kimanin shekara 68 a duniya, farine tass Kai Kana kallon wannan dattijon kasan ya jima Yana Jin dadi a duniya Dan har yanzu da sauran karfinsa a jikinsa, konnen sa ne ya tsinkayo Masa tsawar da saurayin yake dakawa Zaid ,dasauri ya tsintse idonsa tare da cewa "Kash aiki ya lalace, da sauki ma tun da Fu,ad ne, mikewa yayi da sauri ya zuro kafarsa wajen motar ya Soma takawa har ya karasa in da suke, zaro Ido yayi ganin yadda ma,aikatan nasa suka Dora bindigun su a kan d'an karamin yaro kamar zaid, a fusace yace "Kai fu,ad menรฉ hakan?" "Uhm barka da fitowa abbanmu daman yaron nanne muka kamashi da kwaya " "to sai me Ina ruwanku da kwayar da take hannun sa "


"Am sorry abbanmu Amma dai Bai kamata ba wannan yaron yazama Dole mutafi dashi idan muka barshi anan zai girma a Haka kuma ya Bata rayuwar wasu yaran" "no ku barshi ya tafi" "abbanmu doka ce Kuma zatayi aiki akai muje mota muyi magana" "ina zamu Babu inda zani kusake shi" "tom shikkenan zamu sakeshi Amma muje mota muyi magana" gyd'a Kai kwai abba yayi ya koma cikin mota fu,ad ya bishi a baya, suna Shiga fu,ad ya Kamo hannun sa tare da tausasa murya yace " Abbanmu! Ina sane da cewa wadannan kwayoyin Kaine kasaka a kawo maka ,kawai na basar ne dan bana son wani yafahim ci babban mutum kamar Abban mu Yana aikata irin wannan ,haba Abba kainefa wadan da mutane da dama suke koyi da halayyar ka dan Allah kayi hakuri n'a rokeka ka daina irin Wannan abin, nasani bai kamata ace nine wan da Zan sameka na fad'a maka Haka ba Amma Abbanmu Ina so kada kayi la,akari da cewa Ni karamin 'dan Kane Kuma Mara shekaru dayawa ,duk da bani da shekaru Ina da hankali da hangen nesa Dan Allah Abba amatsayina na Dan karamin Dan ka narokeka kadaina ,inajin Babu dadi Abba da ba Haka kakemin ba kamanta yadda ka raineni wallahi abba inda ka kara shan wadannan abubuwan wannan karan nima sha,zanyi bazan sanarwa da yaya Abjeed ko Yaya Abeed ba " zaro Ido Abba yayi yace "

"Ana da hankali kuwa Fu,ad ,Ni kake fadawa kaima zaka Sha kwaya ? Bana so kada ka Soma dan Allah , indai Akan wadannan abubuwan ne nadai n'a Sha, Daman damuwa ce nake ragewa da ita" "haba abbanmu Wai har yaushene wannan damuwar taka zata kau, zuwa tsawan shekara nawa run Ina karami nake kallonka da damuwa a fuskar ka Har yau narasa lokacin dazaka daina damuwa ka hakura mana yaya bazata taba dawowa ba Tun da Har zuwa wannan lokacin Bata dawoba" "a,a Fu,ad zata dawo komai Daren dadewa zata nemeni, duk da cewar banine na haifeta ba Amma a cikin jinina da zuciyata nake jin ta ,damuwar rashin ta ta hanani sukuni tsawan shekaru da dama ban San yaushene Zan sake saka ta a cikin idanuna ba,har yanzu ban cire rai ba indarai da rabo zata dawo gareni kafin numfashina na karshe ya kare" ya karasa maganar Yana share kwallar da tacika Masa Ido take kokarin sakkowa.


Kukan da Fu,ad yake rikewa ne yakasa rukuwa saรฏ da ya zubo , Sabi da tsananin tausayin Abban su da ace Yana da damar da zai iya dawo Masa da farin cikin sa da ya rasa a baya tabbas zaiyi hakan ,Amma Babu dama dukiya da murlki da sarauta da iko baza su taba iya mai do Masa da shi ba sai dai wani ikon Allah, jiki a sanyaye Fu,ad yace "abbanmu to Mai zai Hana ka dauki yaronnan ka ceceshi daga wannan halin da ake kokarin saka sa a kai ka rikesa Tun da Naga baiyi nisa a harkar ba, ko hakan zai sa shaye shayen da kadade kanayi Allah ya dubeka ya yafemaka, Mai bima ta dalilin Haka allah ta dawo da yaya zaraah" "a,a fu,ad baza a Yi haka ba ba Haka mukayi da wadannan mutanen ba ,idan nace Zan dauke musu yaro naci amanar su kawai abin da nakeso da Kai ka sakรฉ shi yatafi" "a,a abbanmu Babu wani alkawari da ka karya daga gani wannan yaron Babu abin da yasani Dan Allah ka taimakesa ,da ace suna da wata dangan taka da yaron bazai guduba ,Abba Yana ganin na Kama yaron wan da ya kawosa ya gudu ,Kuma da d'an uwansune ai ba zasu yadda su sashi a wannan had'arin ba kayi tunani Abba"



"Eh Kuma fa hakane tabbas nayadda kaidin Mai basira ne shikkenan kaje ka d'aukeshi kushiga motar da kazo a ciki saรฏ mutafi dashi gida, inyaso gobe saรฏ muhuce kasar mu dashi" " wayyo allah dadi abbanmu nagode sosai" fu,ad ya fad'a jikin Abban nasu ya rungume, "oh nifa kaga abin da take hadani da Kai fu,ad har abada bazaka taba girma ba ,yanzu sabi da shashanci menรฉ n'a fadowa kaina Kai ko kunya ma bakaji saika karyani ,idan ka karyani ka huta ai" "hhh abbanmu kenan ballema bazan taba karya kaba kamanta nine auta Taya Zan girma anki ayimin Kani" yayi maganar a shagwabe , "to ai gashinan kasamu magajinka sai abar Masa ciyar " "uhm Abba Wai har yazama danka Kai ammafa nayi farinciki Allah ya Kara lafiya Abban mu" "ameen thumma Ameen Fu,adu na" "a,a fa Abba Ni kadaina cemin Fu,adu ga sunana Mai dadi zaka na cemin Fu,adu"

"Ikon Allah to Mai kakeso nace maka?" "Fu,ad zaka ce " "Tom shikkenan fu,ad yanzu nayi daidai" "eh yauwa ko kaifa yanzu kam kayi daidai" yafara Yana zuro kafarsa wajen motar tare da yiwa abbansa sallama ya koma gurin da yabar Zaid da ma,aikatan su. Yana karasawa yace "am Abba yace kusake shi " Babu musu suka matsar da bindigun su daga kan zaid , sankuyawa fu,ad yayi yace "Yaya sunka?" "Za za Zaid" ya fad'a daker , wanan abin da Fu,ad yaji yasa zuciyarsa ta karayin rauni Bai San sanda kawalla ta Shiga zubo Masa ba a zuciyar sa yace "Allah sarki bawan Allah mebi ma maraya ne" afili kuma yace "kanina zaka bini?" Saurin girgiza Kai zaid yayi alamar a,a "maiyasa kabiyoni mutafi bazan cutar da kaiba " kuka Zaid ya saki Yana son yace wani abu Amma ya kasa fad'a sai da ker ya iya cewa "Yaya mujahid" ganin Zaid Yana kokarin Bata musu lokaci hakan yasa fu,ad ya dageshi tsam ya saka shi acikin mota shima ya Shiga sanan ragowar ma,aikatan suma suka shiga suka Soma tafiya motocin suna fita a jerea jere.


๐Ÿ’”_____*DEPRESSION*_____๐Ÿ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*๐Ÿ’”
*#JURIYA*๐Ÿ’”
*#SOYAYYA*๐Ÿ’”
*#DAMUWA*๐Ÿ’”
*#HAKURI*๐Ÿ’”
*#YAFIYA*๐Ÿ’”
*#KYRA*๐Ÿ’”


*Chapter 9*

TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ๐Ÿ’ช๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
๐Ÿ’”_*DEPRESSION*_๐Ÿ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 9*




Har gumi oga atiku yake wajen tukin motar da ker ya iya saita kansa ya dawo gida ,Yana shiga a tsai tsaye ya tadda su mujahid suna jiran dawowar sa, shi kuwa mujahid Babu abin da yake dubawa sai bayan oga ko zaiga bullowar Zaid Amma shiru hakan yasa jikinsa yayi sanyi idonsa ya kada yayi jajur bakinsa ya Soma rawa daker ya iya bude Baki yace "oga Ina Zaid...... Kar dai kacemin zaid ya mutu ? Oga kamin magana Mana Ina zaid yake naga kuntafi tare Kuma ka dawo Kai kadai han kalin ka kaima a tashe Naga sai gumi kake Dan Allah kayi min bayani karka cemin sunkama Zaid ko ya mutu, "oga atikunw yayi Masa shiru kawai ya tsaya ya zuba Ido yana kallonsa cikin ikon Allah ganin yadda lokaci daya yanayin mujahid ya canza kamar ba mujahid din da yasani ba yarasa dalilin da yasa ya damu da wanan Zaid din" mujahid ne yakara cewa a Karo na biyu "oga Ina Zaid?".......


"Zaid kake tambaya ta bama zaka Yi hamdala Dana dawo araye ba sai dai wasu tambayoyi da kakemin kamar zaka da keni" ziki Babu kwari mujahid ya karaso inda oga atiku ya tsaya tare da Kura Masa Ido Yana karantar yanayin sa ,Can Kuma sai yace "Dole na tambaye ka Ina Zaid Sabi da tare kuka tafi ,Dan Allah ka fadamin ina ka kaishi zaid amana ce shi a gareni " "au to amana? Waya baka amanar ko kwalta ce ta baka amanar Dan nasan a titi ka tsinto shi, Wai yanzu mujahid har Ni oganka kake kallon tsabar idona kana min wad'anan tambayoyin kamar wani sa,an ka, to zaidu Yana hannun su sun Kama shi sai Mai ,zaka iya barina yanzu na sarara haba tambaya tun da nadawo kakemin ita Ina laifin kace nadawo lafiya wato Zaid kawai kasani to Ina ga zuwa yanzu zaid ya Dade da zama macacce " "innalillahi wa'inna ilaihirraju un!" Mujahid ya fada Wade da dafa Kai ya d'ago idanun sa cike da hawaye tab a ciki yace "yanzu oga ka kyauta kenan mai ka aikata Haka , innalillahi wa'inna ilaihirraju un saรฏ da nace kabari ZAN Kai zaidu yarone baisan komai ba Amma ka d'รขge shi zai Kai yanzu gashinan abin da kajanyo shikkenan Daman haka kake so burinka ya cika ka kashe Zaid ,nasan dama' tun da nazo da shi ba sonshi kake ba ,to hankalin ka ya kwanta kakashe Zaid Allah sarki bawan Allah bashi da kowa sai Allah yanzu ka rabashi da duniya ta hanyar gurba tacciyar sana,ar ka , shikkenan Babu komai kamar yadda ka kashe Zaid Nima wata Rana zaka min Haka domin Nima ba Dan uwanka bane kaganni ne ka taimakeni ,n'a gode da taimakon da kayi mini allah ya saka da alkairi Amma kasani zama dakai ya kare "daga Haka mujahid ya Mike tare da goge hawayen Dake zuba a kuncinsa ,sannan ya Yi hanyar fita, abokinan sa wadan da suka dad'e suna yiwa oga atiku aiki ne suka Shiga tsayar da shi suna bashi hakuri Amma mujahid ya ki tsayawa ya ciga ba da tafiya tare da cewa0 "Kuna Allah ya ganar da ku kamar yadda nagane wannan hanyar da muke bi ba Mai kyau bace nabar ku lafiya" dai dai lokacin da ya fice daga gidan.


"Kallan me kuke? Kuma idan zaku bishi ban hana kuba zaku iya tafiya, Daman shi Haka d'an Adam yake ka dakko shi daga Rana ka saka shi a inuwa daga baya ya butul ce maka, jibi sabi da wannan d'an jaririn yaron yayimin Haka shekara sama da 12 ina tare da mujahid saรฏ gashi yaro karami Wan da ko shekara daya basuyi tare ba ya butul cemin akan shi" "Nima gaskiya oga nayi mamakin abin da mujahid ya aikata ban San maiyasa yake kaunar yaronan ba muma lokaci guda mukaga soyayya Mai karfi ta shiga tsakaninsa da Zaid" "mtstwww Kai Kuma Ali akwai ka da muna furci to Ina ruwanka kasan yaro akwai saurin Shiga rai dadin da dawa kuma Zaid abin tausayi ne allah idan yaronan Yana magana wataran har kuka yake sani" haushine ya Kama oga atiku a fusace yace "okay tausayi ko to kaima zaka iya bin mujahid Dan da alama Kai ma wataran zaka iya cin Amana ta kamar yadda yayi min ,Amma kusani Baku tsira ba sannan bakuci nulus ba duk inda kuka shiga a fadin duniyar Nan saina Nemo KU na kashek",


"Oga kusa fa?" Ali yafada tare da zaro Ido "eh kusa ai duk wan da nazauna dashi musamman mujahid yariga da yasan sirrina tun da yaci amanata zai iya kaini Kara gurin hukuma Akan harkalla ta ,Dan Haka ya zama Dole na kwar da su" yan Gama fadar Haka Bai jira abin da Ali zai ce ba ya shige cikin gidan da sauri.





Acan gidan su Amnaa kuwa zainab n'a komawa gida tashiga sanarwa da sumayya abin da yafaru a asbiti, sosai tayi mamakin yadda mahaifiyar ta tazage taringa sharara karya, Amma Kuma saita danne Tace "to umma Kuma doctor Yana da kudi Haka Amma kika Bari mukayi saki na safe?" "Dallacan shashasha waya fadamiki Ni zainabu zanga su Naga Rashi bama ki da hankali, to Bari kiji har katinsa yabani zamuringa waya "to waya Kuma umma? Kinmanta ke matar aurece?' "mestwwww banza to saime Allah Zan iya kashe aurena Dan na auri wannan likitan ke bikiga kayau ba kamar shiyay kansa ni ina tunani ma wannan doctor din jinsin larabawa ne " "Kai umma kikashe auranki fa kikace daman Har akwai wani Dan Adam da zai rudeki ki iya kashe aurenan ki nasan duk kyau na doctor din Bai Kai Abban muba" "a uzubillahi daina fad'a Babu hadima Abban me tab mutumin da duk ya tsufa kyan da ya dushashe ,ammafa duk da Haka bazan kashe aurena ba Zan zauna acikin gidannan kodan Naga bayan wannan tsinanniyar yarinyar ,yan Zu abin da nakeso Dake Zan had'aki da wannan likitan domin ki Sato Mana zuciyar sa kingane" "Kai umma ni fa idan bai min ba bazan kulaki shiba" "shashasha akwai hotonsa a jikin katin kallifa " ta d'akko katin tare da nuna Mata sannan taci gaba da cewa "ni uwarki ma nagani n'a rude ballan tana ke duk wani qualitรฉs da ake nema a jikin namiji wannan likitan ya hadasu" "woww umma ammafa ya had'u wallahi Ina sonki ummana jibeshi fa Ni tun da nake ban taba ganin namiji Mai kyau kamar wannan ba umma ya sunan shi?" "Eto Nan fa daya sunan shine ban sani ba Amma duba katin baza a rasa sunan sa ajikiba" kallon katin sumayya taciga ba dayi tana karantawa anan ta ga sunsa a jiki,



"Woww ummana yanayin sa yanayin dadin sunan sa wallahi sunan yadace dashi" "ke dalla gafara Can, yasunan nashi?" Sunan sa doctor *ABEED AK FADAMA*. "Kai AK FADAMA?" Wannan sunan Aina nakejin sa ?" Tabbas n'a gane wannan mutumin shine wan da akaf fadin nahiyar Nan yafi kowanne attajiri yawan dukiya da yawan gwalagwalai hatta kofofin gidan sa ance na gold ne " "n'a gold umma?" Sumayya tayi tambayar had'e da zaro ido, "eh n'a gold aike mun warke wallahi yanzu abin da za ayi kisan yadda Zaki ki sace zuciyar doctor ABEED " "tab umma ba Dole ba" Bata Gama rufe bakiba sukaji amnaa ta chanyare da ihu alamar yunwa takeji ,Nan take zainab da sumayya sukayi tsaki "shegiyar yarinyar Nan kukan Mai takiyi Haka mestwwww" "a,a dai umma kisamu ki dauketa yanzu Sabi da Abba yakusa dawowa Dan wallahi zai iya ganewa " "hakane Amma wallahi kafin na dauketa saina zaneta "umma tatafi da sauri tashiga dukan d'uwawun amnaa da hannu itakuwa yarinyar ta dage sai kuka take abin tausayi , nikuwa marubuciyar nace idan karasa mahaifiya kayi kuka Dan karasa wani bangare na jikinka.





๐Ÿ’”_____*DEPRESSION*_____๐Ÿ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*๐Ÿ’”
*#JURIYA*๐Ÿ’”
*#SOYAYYA*๐Ÿ’”
*#DAMUWA*๐Ÿ’”
*#HAKURI*๐Ÿ’”
*#YAFIYA*๐Ÿ’”
*#KYRA*๐Ÿ’”


*Chapter 10*

TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ๐Ÿ’ช๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
๐Ÿ’”_*DEPRESSION*_๐Ÿ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 10*






*A.k FADAMA EXCITED*

Tun da su Fu,ad suke tafiya Zaid ya damesu da kuka har ya gaji yayi bacci a kirjin Fu,ad har suka karasa katafaren excited din ak fadama Dake cikin garin adamawa, babban gate din da aka Gina shi da zallar gold Mai tsada a ka wangale musu suka Shiga, excited din dake dauke da manya man yan gidaje na alfarma, daya daga cikin part din suka nufa, a daidai parking space din da yake wajen part din suka tsaya sukayi parking, Fu,ad ne ya fito dauke da Zaid a hannunsa da alama bayan kukan da yaci bacci ya samu yayi, takawa ya somayi har yakara sa bakin kofa ta farko wadda Tun kan ya karasa ta bude kanta da kanta, shiga yayi sukuma masu gadin abba n'a biye da abba abaya shima yazo ya Shiga, a babban falon gidan'suka zauna Abba ya bawa masu bagin sa umarni da su matsa Babu musu suka fita daga cikin part din Gaba daya, basu jima da fita ba Abba ya ji wayar sa na Kara, cikin nutsuwa ya sa hannu ya dauki wayar Dan ganin wayake kiransa a wannan lokacin, number faransa ce kuma Kiran daga cikin family dinsa ne dan yaga number ,dayawa yayi a nutse yace


"Assalamualaikum" "ameen wa, alaikumussalam" aka amsa cikin wata sanya yayyiyar murya Mai dadin gaske, "abbana! Ko ba a fad'a Masa ba yasan wanan muryar wanene acikin yaransa sanan ya Gane wan da yake magana Dan Babu wan da yake kiransa da irin wanan sunan sai shi, kafcikin yaransa kowa in ya tashi Haka yake cewa Abban mu, shi kadai ne yake kiransa da abbana.

Murmushi Abba ya saka yace "karamin su babban su, kan lafiya ?" "Yar dariya yayi yace "Kai abbana a she zaka ganeni wallahi nazata bazaka ganeni ba Dan muryata na sauya bakaji ba?" "Uhm Abjeed kenan ko Ina bacci najiyo sautin muryarka saina Gane kaine" "to abbana meyasa?" "Sabi da muryar ka ta fita da ban ,muryar ka ki wata macen albarka dan dadi" "uhm uhm Kai abba dan Allah kadaina yabona sai kasa naji nidin wani hadaddene" "ah to da fa bawani yabo gaskiya bake fad'a Abjeed Dina ,kasan ma mene kuwa ?" "A,a Abbana sai ka fada?" "Uhm n'a zaga kasashe da dama Har yanzu Banga mutumin da ya Yi ko kwata na kyawun kaba " zaro Ido Abjeed yayi yace "Kai abbana shikkenan dai abar Zan cenan yaushe zaka dawo?" "Gobe insha allah ka dawone ai nayi tunanin Kana Dubaรฏ " "a,a Abbana nayi kewarka ne shiyasa n'a dawo kuma Daman Ina farincikin dawowar Yaya Abeed shiyasa nadawo" "au aveed din ya dawo ne ?" "Eh abba yaya Abeed ya dawo sai dai kamar baiyi farincikin dawowa taba" "to meyasa Mai kagani?" "Abbana kaima kasani ai Sabi da Ina hanashi tunani Mana yanzuma kaganshi can Yana fama da tunani" ",uhm bansan meyasa Abeed yakeso ya illata kansa Sabi da zarah ba Ni kaina mahaifinsa na hakura ballanta na Kuma shi da yayi silar wargatsa mata rayuwa, "shikkenan barni dashi Zan dawo gobe insha allah" ",Tom shikkenan abba saรฏ ka dawo amma wannan abin kadaina" "mai kake tambaya ta Haka?" "Kasani abbana" " uhma karaminsu babbansu Kai ko to na daina Shan komai " "uhm abbana kenan shikkenan Zan ganema idan ma baka daina shaba " "tom shikkenan bye" "uhmm uhm Abbana kagaji Dani kenan?" "A,a ni n'a isa ingaji da king" "to naji har da wani cemin king wato cin hanci za a bani to bai isheni ba ka fadamin wani abu" "Kai oh ni dan gidan innata wato yaronan ka rainani da yawa saรฏ kace wata budurwar ka duk lokacin da zamuyi waya saรฏ kasa nace maka i love you , to wallahi kakiyayeni" "hhhh abbana gashinan ka fada to Nima I love you too baby boy" kitt ya katse wayar batare da ya jira abin da Abba zai ce ba,

"Kajini da yaran zamani wai ni ne baby boy ? Hmm abba yayi kwafa ya juyo in da yaji ana dariya kasa_kasa yace "to Kai Kuma fa wa kakewa dariya?" Abba ya fad'a tare da hade girar sama da ta kasa" Fu,ad ne yace " wallahi abbanmu da Kai da yaya Abjeed Idan kuna wani abun saรฏ kace abokanai ko Yaya da Kani" "uhm Fu,ad kenan ban San meyasa ba Abjeed ya Mai Dani kamar wani kakansa Ni Ina tunanin ma Anya dannan ba a can asbiti aka canza min shiba " dariya ce ta kubucewa fu,ad besan lokacin da yace "abbanmu Anya kuwa yakamata ayi bien cike dan duk kanmu yaya Abjeed ya fimu kyau da komai Allah na tuba ayi mutum kamar aljani" "kull fu,ad kafa na sake jin irin wannan maganar abakin ka Ni ma da Wasa nake Abjeed danane na sunna Kuma mahaifiyar ku itace mahaifiyar sa" yayi maganar ransa a bace,

"Abbanmu! abbanmu dan Allah kayi hakuri nima dawasa nake ,abbanmu Wai Ni naji kamar Yaya Abjeed Yana cewa Yaya Abeed ya dawo Kuma har yanzu Bai canza

Please Login or Register in order to submit comment