Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba Ido ki Sha kallo zai du a satinan mahaifin sa Zai koreshi da kansa" "to umma ko fadamin Mana Taya kenan kinsan yadda Abba take son zaidu kuwa shi kadaine fa namiji acikin mu?" " An jima da daddare Zan turoshi d'akin ku ki kasance cikin shiri ai kin dai Gane abin da nake nufi ko?" "Kan bala'i wallahi na gane ai kuwa Babu makawa mukayi Shirin Nan sai Abba ya koreshi Kinga sai musamu damar cin uwar yarinyar Nan " "ai dolema na hallaka jaririyar Nan ko Dan Sabi da akwatin gold dinnan" "akwatin gold Kuna ta me?" " Bakisan komai ba 'yanan Zan Baki labari Nan gaba kadan" "Tom shikkenan umma Bari n'a je n'a fara shiri".


*After one week*

Bayan sati d'aya da haihuwar yarinyar Abban su ya Yi sadaka wan da yayi daidai da kwanan mahaifiyar yarinyar a makabarta yau tacika bakwai Kuma yau ne suna Dan Haka ba ayi wani taro ba kawai ya yanka ragone na suna kamar yadda kowacce yarinya ko yaro idan yazo duniya ake yanka Masa, Haka itama aka yanka Mata katon rago sannan mahaifinta ya rada mata suna Mai dadi da ma,ana *FATIMA* wato sunan mahaifiyar ta ya mayar Mata Amma ana Kiran ta da *AMNAA* Masha Allah Allah ya Raya bisa sunnar annabi Muhammad (s.a.w)


Acan gida kuwa lokacin da zainab ta samu labarin sunan da Aka mayar wa da jaririyar saΓ― taji aduniya ta kara tsanar yarinyar domin gani take kamar fateema ce ta dawo "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Wannan Wace iriyar masifa ce ya tabbata dai sainayi kishi da wannan yarinyar to wallahi ba a isaba " "haba umma ki kwantar da hankalin ki Mana sokike Abba yagane kina bakinciki da zuwan amnaa duniya ,Allah idan kika cigaba da wannan mitar sai kin batamana shirinmu Gaba daya dan Allah kiyi shiru ki daina wannan abin, mai akai akai wata jaririya amnaa yarinyar da ko sati biyu batai ba bamuma da tabbacin zata Kai gobe dan Allah ki kwantar da hankalin ki mu fara gamawa da Wan da muke tsammanin zai iya rayuwa yazama wani a duniya" "ke dallacan rufemun baki shashasha kawai ,yau n'a tabbatar da baki da hankali uban wa yasan Zan Kai gobe ,ke kanki yanzu kina surutun nan Zaki iya mutuwa bama amnaa ba ,dan kina ganinta 'yar karama shine kike tunanin bazata rayuwa to kema daga Haka n'a haifeki kika girma Haka, saΓ― kiga zaidu ya mutu amnaa Bata mutu ba shashasha kawai " "to umma hakane abin da ma tab kenan kinsan da Haka kike cewa Kuma Zaki kasheta ba kya tsoron kema ki mutu?" ",Ke kinga dan n'a fada Miki Haka bashine zaisa kice Zan mutu yanzu ba ,ajikina na kejin bayanzu Zan mutu ba ,ke meyasa jahilace ne nakaiki islamiya dankiyi ilimi amma bakisan komai ba kin ki zama saΓ― kita zama da jahilcin ki ai ni fita ki bani guri ,ku ki shirya ayau sai zaidu ya bar gidannan" batare da sumayya ta ce komai ba ta futa ta bar dakin . Tana fita munira ta shigo idanuwan ta cike fal da hawaye ta tsaya tana kallon mahaifiyar tasu, "ke dalla lafiya kikazo kika sani agaba Haka zakiyi kuka bana son shashanci fa" "umma yanzu abin da kuke shiryawa kenan naji komai dan Allah umma Kar kuyi Haka zaidu Bai San komai ba sai maraici bashi da wayan da zai iya zama shikadai yayi rayuwwa Dan Allah kar kusa Abba ya koreshi" "to uwata ah nace sannu uwarmu ko nace sannu sahabiya uwar tausayi to Bari kiji idan har naji zancenan agun wani kema sainaci ubanki wallahi sai kin gwammace bani ce mahaifiyar kiba,ki fice ki bani guri tun kafin naci ubanki a gidannan muna fukar banza muna fukar hofi ke ala dole mai imani" sum sum munira ta fuce daga d'akin tana goge kwalla.


*Tom misalin karfe 12 na dare kowa yayi bacci a gidan ba kyajin ihun komai sai na tsuntsaye ,zainab ce tsugune a gaban zaidu tana bugunsa da hannu ,shikuwa zaidu cikin baccinsa yaji ana tashin sa dan Haka ya fara bude Ido Yana kallon ta dishi_dishi can Kuma sai ya fara ganinta tarau ,cikin voice dinsa Mai ban wahala yasoma kinkina Yana cewa ummmmmm um umm umma! "Kai da dalla rufemin baki banason ka 'batamin lokaci da wannan maganar taka haba sai muyi minti 5 kafin kace umma Ni tashi ka biyoni" Babu musu zaidu ya tashi ya biyo bayanta batare da sanin cutar da shi zatai ba, sai da suka zo daidai d'akin su sumayya sannan ta tsayar da shi cikin rada Tace "kana jina ko Maza kaje aunty sumayya tana kiranka Kuma duk abin da tacemaka kayi idan bakayi ba wallahi saina yankaka kajini?" "Sauri zaro Ido waje yayi ya Kura Mata Ido "au tsareni Kai da kallo bakaji abin da na ce makaba" "saurin d'aga Kai yayi ya bude baki zai ce to ,ta dakatar dashi da sauri "Kai Ni bana son jin amsarka sokake ka batamin lokaci Maza SHIGA" Babu musu zaidu ya shiga d'akin Yana dube dube Dan ya kunna kwai sai Kuma yaji an rufe kofar d'akin an saka sakata, sannan an kurma ihu "wayyo taimako umma ! Umma ki taimaka min wayyo abba! Abba!! Kuna Ina Wayyo " Abba wan da ke kwance a kan gadonsa amnaa n'a kan kirjinsa ya ajiyeta a kan gadon ya sakko da sauri yafito Yana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Sumayya lafiya" ganin zainab da yayi a bakin kofar itama yasoma tambayar ta Yana cewa "lafiya?" "Ina fa lafiya nima bansan mai yake faruwa ba Ina kwance najiyo ihunta , malan kayi wani abu akai" .





πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 4*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 4*



Munira da ke kwance ko runtsawa batayi ba Sabi da a gaban idonta sumayya tagama shirya komai sannan akan idonta zaidu ya shigo gashi Bata da yadda zata iya taimaka Masa, Dan Haka ta Kara kudin dunewa tacigaba da kukan ta ,har sai da taji muryar Abban su Yana cewa "Wai babu wan da zai iya bude kofar ne?" SaΓ― lokacin ta Mike ta karaso gaban kofar ta zare sakatar, da sauri abba ya shigo ya kunna kwai yadda yaga sumayya be yasa ya runtse ido "subahanallahi "sumayya Ina rigarki Mai yasameki Haka? Zainab ce tayi saurin karasawa ta d'akko Zani ta rufeta ,sannan abba ya bude idonsa karaf akan zaidu Wanda ke zaune a gefan shimfidar su ya takure guri daya sai muzurai yake, "Kai zaidu maiya kawoka Nan taso maza zonan, abba ya Kamo hannunsa, "abba wallahi bazan Yar daba Dan uwar yaronan Ni da,ar sace daman Ashe yaje an koya masa iskanci ban sani ba, akanme ina bacci zaina shafani " "zafaki kuma wannan dan yaron sumayya kiji tsoron Allah "zainab ta fada kamar batasan komai ba, "n'a rantse da Allah umma da gaske nake kinsan kaf gidan Nan Babu wan da ya kaini son zaidu bazan taba iya yimasa sharriba Amma abin da zai sakamin dashi kenan Allah na tsani yaronan , indai Abba Bai dauki mataki ba yau d'inan Zan varmuku gidan Nan.


"Tsaya waini ban fahimci abin da kuke nufi ba Maine ya faru?"

"Ah lallai malan yanzu baka ga abin da ya faruba ya tabbata fateema ta maka asiri shiyasa baka ganin laifin yaranta ko kadan?"

"Ke zainab ki san abin da bakin ki zai dinga fadi Akan ta idan ban da rashin hankali baiwar allahn ko wata daya batayi da rasuwa ba kudin ga fadin irin wannan magan ganun akanta ,Ina Miki kallon Mai hankali Ashe Babu hankalin ki barni nayi magana da yarana bana so na sake jin bakin ki akai" ya fad'a Yana huci.

"Iyye ah Dole wato n'a barka kayi magana da yaranka Tun da Ni an Dada maka atishawa nayi na haifosu ,wallahi in dai Akan su sumayya ne baka da ikon da zaka hanani magana sannan baka da ikon dazaka hanani Kare hakkin yarana, shi dai zaidun naji shi ba 'dana bane tun da Haka kakeson na ce To kaje shi bazan sake magana akan shiba Amma wallahi muddum zancen Nan ya tabbata gaskiya sai dai ka za'ba ko zaidu ko mu"

Juyawa tayi ta kalli munira wadda hawaye yabi ya wankemata fuska tsabar tsananin tausayin zaidu da ya cika Mata zuciya tana ji tana gani ga gaskiya Amma Babu damar fad'a,. "Ke kukan uban me kike ke kuma ko kema ya shafa kine shashasha kawai" "uuhm Babu komai umma kawai Ina hango rayuwarnan yadda ta zama abin ban Al,ajabi" "to Dan uwarki da Baki hango abin Al,ajabin ba sai da wannan abin ya faru ko da bakisan duniyar ta lalace ba sai da kika kalli fuskata?" "Uhm umma wallahi tausayin ku nakeji" "tausayin mu ?" Tausayin mu to kima daina ji huce ki bani guri tunkan na har Baki"


"Kinga zainab ya Isa Haka sumayya! Zonan"


Kara sowa sumayya tayi ta zauna idonta ya kumbura suntum hanci duk majina sai shashshekar kukan karya take.

Abbane ya kalle ta ya ce "sumayya ! Sumayya!! Sumayya!!! Nakira sunanki sau uku sumayya kiji tsoron Allah kitina Zaki mutu ki tadda allah kuma kisa azuciyarki a yanzu idan mutuwa tazo Miki Zaki iya mutuwa ina da tabbacin cewa kin San alkalami ya hau kanki a yanzu ,idan har kikayiwa yaronnan kazafi Allah saiya hukunta ki Kuma hukunci Mai tsanani Dan Haka kiji tsoron Allah ki fadamin gaskiya sumayya".

Jikin sumayya Gaba ki daya yayi sanyi saΓ― taji kamar ta ce karya takeyi ,to Amma idan tau Haka ta zubar da mutuncin ta dana mahaifiyar ta ,sabi da Haka yasa sumayya tayi karfin halin cewa "abba hakika ban taba tunanin irin wannan halin daga zaidu ba saka makon irin kekkewar tarbiyyar da kabamu duk da kasan cewar sa yaro karami ya ayka ta min abin da bazan iya yare Masa ba da farko nayi tunanin babban mutum ne dana bude Ido Naga zaidu ban Yar da shi bane sai da na sake murza idona Dan tabbatar wa ,wallahi Abba idan har nayiwa zaidu sharri Allah ya saka Masa cikin gaggawa, haba Abba kayi tunani Akan Haka Mai zaisa nayi Masa sharri ko Babu komai d'an ,uwanane kuma nasan idan nayi masa sharri Dole Zan mutu na tadda Allah ga shinan ka tam bayeshi".

"Ban gane atam Baye shi ba wannan Mai zai iya cewa ban da a 'batawa mutane lokaci yanzu kafin ya Fadi kalma daya sai gari ya waye gwara kawai amasa hukunci tun da dai anzan baza kiyi Masa sharri ba" cewar umma Dake zaune a gyfe tana kallon yadda sumayya ta dage tana fadin karya kamar gaske.


" A,a har yanzu bakisan Mata ba zainab bana tunanin wannan d'an karamin yaron zai iya aikata abin da kukace amma Bari naji ta ba kinsa" "zaid! Zaid !! d'ago ka kalleni kaji ko" dagowa zai du yayi ya kurawa mahaifin nasa ido cikin farga ba da rashin sanin abin da zaice.

Cikin nutsuwa ya Soma yimasa magana Yana cewa "zaid shin da gaske ne ka Shiga dakin yayarka sumayya kuka abin da Tace kayi mata kay?" ,"Haba malan wannan ai ba adalci bane yaza ai kadinga Masa irin wannan tambayar Kai ma kasan gaskiya sai karinga takewa" "Kinga zainab ya isheki Haka kibari kamar yadda namata magana a nutse shima nayi Masa"

"Zaidu kabani amsa hakane?" "Ah ahh an abb abb abba wallllllllll walla wallahi ba Haka bane "
"Dalla Can rufe Mana Baki shashasha kafin kayi magana daya saika Bata Mana Rai ka bude baki kayi magana ko yanzu jikinka ya gaya maka"

Habawa nan take cikin sa ya Murda jikake kulululu ya hadiye wani masifaffen yawu lokaci guda ya tuno da gargadin umma da Tace duk abin da sumayya Tace tace to idan ba Haka ba sai ta yanka shi Kuma ta yanka jaririyar su, "Kai zaidu magana fa nake maka shin dagaske ne anyi Haka ?",Abba ya Kara jefo Masa wata tambayar a Karo na biyu.

"Eh ehhh eh abbbba da da dagaske ne an anyi Haka ?"



"Innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! innalillahi wa'inna ilaihirraju un !! Innalillahi wa'inna ilaihirraju un !!! Nashiga uku zaidu innalillahi wa'inna ilaihirraju un !!!! Abba ya fashe da kuka ,itama sumayya kuka ta sake fashewa dashi tana cewa "wallahi Abba in dai baka koreshi ba Ni saina kashe kaina Sabi da duk lokacin da na ga fuskar yaronan Dole abin zaina dawomin Kuma zanji ciwo ace kanine Dan iska kuma abba wallahi idan ka barshi baka Kore shiba zai zauna ne ta Bata rayuwar mutane Har da yaran ma kwafta tun da yanzu Yana yaro ma yayi Haka balle kuma ya girma Nan Gaba saiya zanyo mana masifa " "hakama bazata faruba dolene ya bar gidannan bazai yuwu na zauna dashi a Haka ba" "uhm kokai fa wallahi idan ka barshi nan gaba yar wani zaiyiwa ciki shikkenan kaga saΓ― ya Bata maka suna ya Bata sunan gidan Nan sannan ya Bata rayuwar su yadda bamai Sha,awar zuwa neman auren "yayanka "

"Ki ma daina fad'ar Haka dolene na koreshi ayanzu Amma ban taba tunanin Haka daga gurin zaidu ba iya tarbiyya na bashi hakama mahaifiyar sa"

Kuka zaidu ya saka ya Soma cewa "abbbbbba ab Dan allla allah...." Bai karasa maganar ba yaji saukar wani gigitaccen mari a kuncin sa "uban me kuma zaka cin ?yimin shiru naji da bakin cikin daka kunsamin"

"Hmm to yanzu Mai ake jira ya d'ebo kayansa ya bargidan Nan" "a,a zainab yanzu darene abari sai da safe sai ya tafi" "wlh baza a bari sai da safe ba yanzu zai tafi" tatashi a fusace ta shiga d'akin su ta d'ebo kayansa a cikin bakko ta hurga Masa, "tashi ka huce kafita" mikewa zaidu yayi abin tausayi Yana kuka Yana Jan numfashi har da majina, "kukan me ka tsaya yi tashi" ta kama hannunsa ta tunkudashi saΓ― gashi ya Fadi kasa Nan take bakinsa ya fashe jini ya Soma wanke Masa Baki, saurin runtse ido abba yayi ya Mike ya shiga daki domin baya son ganin zaidu a damuwa kawai Babu yadda ya iya ne sunfi karfinsa dan Haka ya zauna a bakin gado ya saki kuka kamar karamin yaro ,yasan yanzu idan yace bazai Kori zaidu ba zasu iya kaishi Kara mebi ma a yankewa zaidu hukunci na shekaru a gidan yari to da wanan abin gwara ya koreshi din.

Munira Dake gefe a tsaye ta karaso da sauri ta durkusa gaban umman tasu tashiga rokonta "Dan girman Allah umma kada kiyi Haka kiyi hakuri Dan Allah kada ki koreshi kiji tsoron Allah, zaidu Babu abin da ya aikata muku Shidin kawai karamin yarone Bai San komai ba sai kadaici da damuwa bashi da kowa sai mu yanzu idan kika koreshi Ina zaune?" Bashi da inda zaije bashi da wayon da zai iya neman abinci yaci sokike ya wulakan ta BAYAN Yana da iyaye ,ko so kuke kusa shi ya Rika bin layi Yana bara dan neman abin da zaifi?" Umma kada ku gurbata rayuwar sa dan Allah ,Yana da tarbiyya Yana da addini daidai gwargwado kada kiyi sanadiyyar fadawar sa gurbatacciyar hanya , dan Allah kiji tausayin sa kada ki koreshi".


Kafa tasa ta harbe ta da kafa ta Soma surfa bala'i "munira zanci... Hmmm da ace ba a gida n'a haifeki ba wallahi da saina ce canzamin ke a Kai ,ni duk yarona indai ta Sha nonona Babu dugon imani a zuciyar sa amma ke bansan uban wa kikayo ba Naga alamar sai na fara Saba Miki tukunna Zaki daina min shishshigi a lamurana ,wallahi muddum kika Kara magana akan zaidu saina tsine Miki albarka shashasha kawai"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Zaki tsinemin fa kikace umma ni Zaki tsinewa?"

"Eh tsinemiki zanyi huce ki ban guri"


"Kai kuma tashi tunkafin na karkasheka anan" tayi maganar tana daga zaidu ta ja hannun sa zuwa waje, me gadi Tace ya bude Mata gate Babu musu ya bud'e Mata ta tura zaidu waje sanan ta hurga Masa jakar kayansa.

Juyowa tayi ta kalli Mai gadin Tace "sauran Kuma Naga ka taimake shi abakin aikin ka" tajuya ta koma cikin gidan.

Tsayawa yayi maigadin Yana kallon ikon allah Can Kuma sai ya mayar da gate din ya rufe ya saka sakata a zuciyar sa yace "Allah sarki rayuwa idan ba mahaifiyar ka agida sai yadda kagani gashi wanan yaron mahaifiyar sa ko sati uku Bata cika da rasuwa ba Amma jibi ,Allah ya kyauta" ya koma kan kujera ya zauna.



Cikin tsakiyar dare misalin karfe 4 hadiri ya hado Ganga Ganga yayi bakikkirin saΓ― waljiya ake gari yanata kara, Can Kuma sai ga wani ruwa Mai karfin gaske ya sakko shahhhh kamar da bakin kwarya sosai , Mai gadi dake zaune a waje ya Mike ya Shiga dakinsa ya kwanta can Kuma sai yaji bazai iya kwanciya ba Yana da tabbacin zaidu Bai bar kofar gidanan ba Dan Haka ya Mike cikin sauri ya bude gate aikuwa can ya hangoshi ya takure guri daya sai rawar d'ari yake ruwa ya jikeshi jakaf, "yaro" dasauri zaudu ya dago ya a kallonsa, "zonan kaji" Babu musu zaidu ya taso d'auke da kayansa a hannunsa ya shigo, maigadin ya Kama hannun sa ya kaishi dakinsa, sanan shima ya Shiga,.


πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 5*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 5*








Acan cikin gidan kuwa Abba ya kasa bacci yarasa Mai take Masa dadi sai faman juyi yake Yana tunanin halin da 'dansa namiji tilo guda d'aya yake ciki ,ji yake ajikinsa duk inda zaidu yake a yanzu baya cikin koshin lafiya, zaune ya Mike ya kalli zainab yace "yanzu Ina zaidu yanufa gashi ana ruwa karfa yakamu da zazzabi " "to sai mai?" Mu ina ruwan mu Kai kadamu kanka " "uhm zainab Dole n'a damu wlh damuwa tazama Dole hankalina bazai kwanta Bari naje n'a duba ko Yana waje" "kaje ka duba kuma?" "Eh dubawa zanyi idan nayi Haka allah saiya kamani" Yana Gama fadar Haka ya fice waje" sauri ya shiga Yi har ya karasa bakin gate din ya zare sakata ya leka ko Ina Amma yanemi zaidu sama ko kasa ya rasa, jiki a sanyaye Babu kwari ya juyo karaf suka hada ido da Mai gadi yace " alhaji lafiya wani abun kake nema ne ?" "Am uhm dan Allah bakaga inda zaidu yayi ba" tinani mai gadin ya somayi da kamar ya ce Masa gashi a dakinsa sai yaji tsoron Kar nemansa yake sukara dukansa Sabi da Bai tafi ba koma gudin tsoron Kar ya rasa aikinsa yasa yace " gaskiya Banga zaidu ba"

"Oh good innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Shikkenan bansan kuma yazanyi ba " ya fad'a tare da sauri komawa cikin gidan,

Sai da Mai gadin ta dan tsaya kafin ya koma cikin d'akin sa ,cikin sauri ya janyo zaid ya shiga cire masa jikankun Kayan ya lullube sa ganin yadda yake rawar sanyi, "sannu zaid kaji ,zaka ci abinci?" "Ehhhh ZAN Zan ci" "Tom shikkenan tashi Kaci" mai gadin ya dakko Masa ragowar abincin Daren da da yaci ya rage, sosai zaidu ya shiga cin abincin har ya cinye Tass sanan ya kwanta ya Soma bacci, Allah sarki rabon sa da komawa bacci Tun da zainab tazo ta tashesa.



Acan cikin gidan kuwa bayan ya Abba ya koma zainab ta shiga tambayer sa "shin kaga zaidun?" "Uhm wallahi ban ganshi ba na duba duk inda ya kamata Amma ban ga Zaid ba ,ban San Mai yasa ba jinake kamar wani abu Yana faruwa dashi ,yanzu Ina yaje wazai rikeshi awane Hali yake bansani ba kawai mudai min yanke hukunci cikin fishi ga abin da ya ja Mana" "ban gane hukunci cikin fishi ba malan nufinka kenan da ansani anbar shi llai ma wato Sabi da ba Fatima ya so ya lallata ba ko?" "Kinga zainab ya isheki ki barni naji da abin da yake damuna karki karamin wani ciwan kan dan Allah" ..

"Okay d'akin ma ai saΓ― n'a barmaka Tun da ciwan kai Zan Dora maka" ta karasa maganar tare da ficewa d'akin su sumayya.




Tana shiga ta sameta a zaune ta zabga ta gumi ta kasa komawa bacci ,gefan ta ta samu ta zauna ta ce "sumayya lafiya kuwa naganki a Haka ?" "Uhm umma tunani nake Ni sai nake gani kamar abin da mukayi bamu kyau ta ba hukuncin da akayiwa Zaid ya Yi tsauri jikina duk yayi sanyi ban San maiyasa nakejin na aikata wani babban zunubi arayuwa ta ba umma mufita mu nemosa Dan Allah" "afita anemosa to bazan jeba shashasha kewai maiyasa Baki da hankali ne Ina ruwanki da halin da zai Shiga ,to Bari kiji na fad'a Miki idan ma kina mafar kin fadawa malan karyane abin da yafaru sharrine kika Masa to ki daina Dan wallahi bayan korar mu da zaiyi inya sani har Kotu saiya Kai karar mu an yanke Mana hukunci ,yanzu kuwa idan kikayi shiru zamu kashe AMNAA sanan mu yi amfani da wan can dukiyar" "wace dukiyar Kuma umma?" "Shashasha wancan dutsen gold din na cikin akwatin can da fateema ta bani kafin ta rasu" " okay na gane yanzu dai umma Ina son ba koma school gobe Kuma kinsan Abba Bai biya kudinnan ba" "oky ai Babu damuwa Allah ya kaimu goben Ameen" "ameen umma".



Washe Gari da safe karfe 6 Mai gadi ya tashi zaidu saga bacci ,ya sauya Masa Kayan jikinsa sannan ya gyra Masa bakkon kayansa yace "tom zaid na maka iya taimakon da Zan iya maka yanzu abin da nakeso ka tashi ka tafi Tun kafin wani a cikin gidannan yasan kana dakinnan ,kaga idan akasan kana cikin dakinnan korata zasuyi kayi hakuri kaji bayan wuya sai dadi, duk halin da zaka tsinci kanka aciki kada ka cutar da wani ko kace zaka dauki kayan wani haramun ne kaji" sannan nayi niyar taimakon ka Amma Babu Dana iyalina ba anan garin suke zaune ba

Please Login or Register in order to submit comment