Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da na kaika gida na Amma Babu ko Mai na Allah basa karewa a duniya kaje Allah zai taimaka maka" batare da Zaid ya ce masa komai ba ya goge hawayen idonsa ya Mike sannan ya dauki bakkon sa da ta so fin karfin sa dan ta masa nauyi ,ya Soma tafiya ,har ya Kai bakin kofar d'akin ya juyo ya kalli baba Mai gadi yace " naaa na na na nagoooooo de" daga Haka ya fita ya zare sakatar gate din ya fita, tun da ya fita ya Soma tafiya Bai San in da zai nufa ba har sai da yayi nisa da gidan su sosai zai Sha kwana sannan ya juyo ya kalli gidan ya kurawa gate din gidan Ido ,kana ya Shiga lungun ya ciga ba da tafiya a kasa Babu Mai taima kon sa, duk in da ya huce kowa sai ya d'ago ya kallesa Amma Babu Mai cewa uffan Akan Haka, har ya fita bakin titi, Wasa Wasa zaid yayi tafiya mai nisa har ya soma jigata Sabi da yunwa da ta Soma tambayar cikin sa, Tun da bai ci abincin safe ba gashi lokacin har karfe 11am tayi ,Amma duk da Haka Bai daina tafiya ba sai da karfinsa ya kare Kat sannan ya samu guri a kasa ya kwanta ya Dora kansa a kan bakkonsa, duk wan da zai huce saΓ― ya kalleshi Babu wan da ya kulashi balle ya taimaka Masa , wani yarone matashi bazai huce shekara 17 a duniya ba yazo hucewa jikinsa kaca kaca rigar sa kuwa duk a yage ,da alama Yana Shan wahala a duniya ,har ya huce inda Zaid yake ya dawo , a ga bansa ya tsuguna yace "yaro lafiya ?" "Kai lafiya ka kwanta anan?" Zaid dai Sabi da yunwa ta ci tacinyesa baya iya ko magana Dan Haka ya bi wannan matasha da Ido ,Yana rike ciki idonsa na zubda hawaye, ganin Haka yasa wannan yaron ya Gane abin da ke damun sa bakomai bane face yunwa , da sauri ya Mike ya karasa gurin wata Mata Mai sai da abinci a gefe ya Mika kudi ta bashi abin ci ta dawo gurin zaid yace "tashi kaji yaro Kaci "mikewa zaidu ya kasa Yi Sabi da ya jigata ,ganin Haka yasa wannan saurayin ya dagoshi yashiga bashi abincin Yana ci Har ya Soma dawowa hayyacin sa, saΓ― da Zaid ya cinye abincin tas kafin ya bud'e Baki yace "naaaa na na nagoooooo de" hawaye masu zafine suka cika idanuwan wannan saurayin ganin yadda Zaid yake magana da ker yasa ya fahimci Yana cikin tashin hankali ,yasan Babu Mai tsayawa ya saurari maganarsa balle ya taimaka Masa da wani abu sa bida kafin ya Fadi kalma daya sai an Bata lokaci, Dan Haka yayi Sha,awar ya taimaka Masa ,kallon zaidu ya sake Yi wan da shima zaid kallon sa take , "yaro zaka bini?" saurin d'aga masa Kai zaid yayi Har da Dan murmushin sa, "Tom shikkenan gama hutawa saΓ― mutafi a Can gaba kad'an gidan ogana yake Nima ka ganni maraya ne kamar Kai bani da kowa shiya taimake ni kuma nasan kaima zai taimaka maka" murmushi zaid ya Kara Masa can Kuma sai yace "mutafi ka huta?" "Ehh eh naaaannn n'a huuuuuu ta" Mika Masa hannu saurayin yayi yace to muje ko "ya dagoshi sannan ya karbi bakkon kayan suka Soma tafiya ...




*Bayan wata buyu*


"zonan shalele na" tayi maganar tare da mik'a mata hannu, nok'e wuya tayi gami da k'ara k'an k'ame mahaifin nata cike da furgici, "uhm malan kaga Taki zuwa,kizo kinji maza zoki karbi Madara" Takara Kiran 'yar k'aramar yarinyar a Karo na biyu, murmushi malan yayi ya Mike tsaye yace "Ni Zan fita ga tanan Dan Allah ki kula da ita kinji" "Tom shikkenan honey sai ka dawo" ta fad'a tare da d'aukar AMNAA da bazata huce wata biyu a duniya ba, kuka AMNAA ta somayi tana zillo ajikita, ganin Haka yasa malan ya dawo ya na cewa "Wai Ni zainab Mai yasa yarinyar Nan Bata son zuwa gurinki n'a rasa dalili?" "Uhm malan kenan ni kaina mamaki nake Bari sumayya ta dawo ko munira nasan zata yadda da su musamman munira" "okay tom shikkenan sai na dawo Dan Allah ki kula da ita" "insha allah" Tace sanan malan ya fita.



πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 6*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 6*







Baifi minti 5 da fita ba ta dungurar da AMNAA a k'asa tare da dungure mata Kai Tace "shashasha,wato ka ajiye baiwarka mai kular maka da yarinyar ",tana maganar tana kallon yarinyar tana zare mata ido, "ubanki zakici wallahi sainayi ajalin ki indai nice ba yafi sonki Akan sauran 'yan,uwan ki ba, takarasa maganar tare da d'aukar ta da hannu d'aya ta ajiyeta a waje, ajiyeta keda wuya ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, aikuwa yarinyar ta chanyare da ihu tana kuka tana faman Mika hannu tazo ta dauketa ,Amma Ina Sabi da tsabar mugunta saima ta sake turo kofa ...


Allah sarki wannan baiwar Allan da bataji ba Bata gani ba batasan komai a duniya ba sai soyayyar mahaifinta da kiyayyar zainab , yarinyar da har yanzu batasan wacece mahaifiyar taba ,kallon zainab take a matsayin itace jigon rayuwata ,

Sallamar su munira ce ta dawo da zainab daga gengedin da tafara ,jin yadda taji munira ta zabga uban salati ta na ihu "innalillahi wa'inna ilaihirraju un mun Shiga uku! Umma kin kasheta umma!! Kina Ina umma zokiga Amnaa" ta durkusa ta dauketa a San k'ame ko motsi Babu a jikin yarinyar Sabi da yadda ruwan ya shanye jikinta Gaba daya Har fuskarta , "amnaa! manaa!! Ta shiga Kiran sunan ta tana jijiga ta ,dai dai lokacin da umma ta fito daga d'aki Tace "lafiya kike min Kara aka Sabi da Baki da hankali daga dawiwar ki" "umma ! Umma kalli ki duba kigani Dan Allah ,jibi yarinyar Nan umma yanzu har tsanar da kukewa amnaa takai Haka?" "Dallacan rufemun Baki uban mai nayi mata Har da zakice n'a tsaneta ,ke indai baki min. Sharriba bakya jin dadi?" "Umma Naga alamar bakisan Mai kika aikata ba to kin kashe ta Bata motsi umm kin kashe amnaa" "what namai?" Na kasheta kikace uban me nayi Mata da har Zan kashe ta?" Ta sa hannu ta finciko hannun yarinyar kwalli daya wai zata dauketa take taji hannun yayi Kara ji kake kass "na shiga uku innalillahi wa'inna ilaihirraju un!! Umma kin karya ta wallahi kin balla mata hannu " hannu zainba ta dora Aka tashiga juyi a gurin tana salati da salallami tana zufa ruwa ake a lokacin Amma ita gumine ya Soma zubo mata, "shikkenan munira zamana yakare a gidannan saganan Kuma sai gidan yari nashiga uku sai kicemin ta duri ruwa da yawa ai da bazan nata wannan daukan ba ,bani ita muje asibiti ko Bata mutu ba " "a,a umma wlh bazan Baki ita ba nasan halinki sai ki karasa ta ,indai asbiti ne Zan kaita da kaina" "eyee sannu uwar tausayi jikar Anna bawa to wallahi ba kin tafi kaita asbitin ba ,Sora naji wannan maganar a gurin abbanku ,idan kika sake naji wannnan maganar hmm saina miki abin da yafi wan da nayiwa amnaa saina Miki tsanar da saikin gwammace allah bai halicceki a cikin wannan gidan ba" "shikkenan umma bazan fada ba amma dan Allah kiyi hakuri ki bani kudi natafi kinsan baza a dubata kyau taba Dole sai na bada kudi" "to bazan bayar ba nace bazan bayar ba indai da kudina za a dubata Allah sai dai ta mutu" "umma ta mutu fa kikace?" Dan Allah umma Taya akai kika Bari shaid'an yaci galaba a kanki Mai yasa ? Ni dain nasan a da mahaifiyata ba Haka take ba wallahi umma kin canza ,ki Tai aka ki bani ita na kaita asbiti umma kada ta mutu" "rufemin Baki Ni cewa nayi Miki ban San hanyar asbitin ba "umma tayi tsaki ta dauki hijabi ta fice kamar wata tsohuwar mahaukayi ya, tana tafe tana salati kamar wata Mara gaskiya Tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Nashiga uku yanzu idan Malan yazo mai ZAN ce masa ?" Dai dai lokacin da ta Isa bakin titi ta tsare Mai adaidai ta "hajiya Ina Zan kaiki?" " Please Nan Gaba kadan asbiti Zani nawa Zan baka?" "Dari biyar " "haba bawan Allah dari biyar Kuma?" "Kinga baba ruwa fa akeyi idan yamiki ki shigo idan Bai Miki ba Bay tafiya ta" "shikkenan muje Amma ban da Ina tsoron kada wannnan yarinyar ta mutu ban je asbiti ba da wallahi sisita bazan kashe ba a kafa ZAN tafi" ta karasa maganar tare da Shiga a saidai ta, BAYAN ta zauna a cikin Zuciyar ta ta ce "Wallahi muna dawowa saΓ― n'a daki d'ari biyar d'ita dan ba uwar kice ta bani kudin ba" "am baiwar Allah anzo fa kina can kina tunani" "okay tom n'a gode " ta zaro daribiyar ta Mika mm asa tashi ga asbitin a guje.



*Zaid kasan Mai nake so da Kai?" "Aaaaa,a "ya fad'a tare da tsirawa mujahid Ido, "Ina son duk abin da oga atiku ya baka kafin ka Kai kafara sanar mun, Sabi da a kwai gurare masu hatsari da ake Kai Kaya Kuma a samu akasi "yan sanda suzo kame ta gurin, ya kamata ka d'inga kulawa kaji, Ina tausaya maka ne su baza su duba Kai yaro bane wallahi kulleka zasuyi " daga masa Kai zaid yayi tare da cewa "to too Amma Dan Dan al alllah zaka kaini a bani ma ma magani magana ta ta dawooooooo dai dai?" Murmushi mujahid yayi gami da kallon sa ta shafa masa Kai yace "kar ka damu kanina insha allah idan Har nasamu kudi Zan kaika domin Nima bana jin dadin ganin ka a Haka magana Tana maka wahala ,kada da hakuri kaji" "uhm uhm yau yau she zaka kaiiiiiii Ni na na na ga Amnaa?" "Uhm Allah sarki d'an uwa mai dadi kada ka damu insha allah zaka sakΓ© ganin 'yar,uwarka hakan da ta faru bayana nufin kara bu da ita n'a Har aba da ba, insha Allahu bazasu cutar maka da kanwarka ba zata rayu Kuma watara na zaka ganta" ya na magana Yana kallonsa cike da tausaya wa, wayar shi ce ta shiga ruri ,cikin hanzari ya d'aga tare da karawa a kunne yace "yanka yadade barka da wanan lokacin" "barka ina zaid?" Oga gashinan muna tare wani abun ne ya faru?" "A,a akwai wata harkalla da zamu buga ne ina son Zan bashi aiki yanzu zai kaiwa Kaya tasha" "Kai oga Tasha fa kace za su iya kamashi wallahi kasan basa da kirki" "a,a baza su Kama shi ba ai shi karamin yaro ne bazasu fahimci komai a Kai ba ,kuma ma idan sun Kama shi mu Ina ruwan mu badai ya biya mana bukatar mu ba" "a,a oga dan Allah a Can za wanan abin idan ba damuwa ni Bari n'a zo n'a amsa n'a Kai" "Kai baka da hankali wan da za a kaiwa kayanan shahararren Mai dukiya ne kowa ya san shi a kasarnan idan Aka samu matsala Koda d'aya ce sai an kamamu" "ah to indai Haka ne oga ai Babu wani abu Dan sun Kama Ni , bakaji Mai kace ba kowa ya sanshi kaga kuwa zai iya belin mu " "hmm shifa ba Yana Kar bar kayanan Nan da sanan 'yayan sa ki wani nasa ba a,a Babu wan da ya sani ,Idan Kuma muka Bari wani daga cikin ahalinsa ya Ankara tamu ta kare , shiyasa na ce a aika Zaid ya Kai Babu wan da zai fahimta," "hmm oga bazaka gane ba gwara Ni idan an Kama Ni nasan tayadda Zan kwaci kaina shikuwa fa baisan yazai ba ga maganar sa Bata fita kamar ta kowa kaga kuwa akai matsala" "Kai mujahid Ina maka magana Kana mayar mun to Bari na fito na fad'a maka yadda zaka gane, idan wanan mutumin yazo kasar nan Tun daga farkon Tasha har izuwa filin jirgi masu gadin sa ne da masu take masa baya ga uban rundunar sojoji da suke a gurin ,Kai Kana da hankali zaka Kai kan ka gurin sokake ka mutu " zaro ido mujahid yayi yace "tofa yanzu kenan ta za a Yi?" "Kawai ka turomin Zaid ya Kai Masa , katse waya kaga alhaji ya na sake kirana" 'kitt mujahid ya ktse gami da kallon Zaid yace "Ina fatan dai kaji duk abin da muka tattauna da oga ko" batare da yayi magana ba ya daga Masa Kai idonsa cike fal da kwalla, ganin Haka yasa jikin mujahid yayi sanyi sai yaji kamar ya karbi kayan ya Kai da kansa, can Kuna sai ya dafa kafadar Zaid ya janyosa jikinsa yace "Zaid ka kwantar da hankalin ka kaji insha allah Babu abin da zai faru da Kai kaji ,nasan Mai kake tunani Amnaa ko ?" Karka damu insha Allahu zaka je ka dawo lafiya kuma zaka rayu da kanwarka cikin ikon allah" Yana magana ya na jijjiga bayan Zaid alamar rarrashi.

πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 7*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWAπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAIπŸ’ͺ🏻WRITER'S ASSOCIATIONπŸ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ƘasΖ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
πŸ’”_*DEPRESSION*_πŸ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 7*





Tana Shiga asbitin ta shiga Kiran likitocin asbitin a gigice " doctor ! Doctor's!! " Suma likitocin a tsorace suka fito ganin yadda take kwada musu Kira kamar wadda zata tashi sama, "lafiya baiwar Allah" wani likita ya fad'a fitowar sa kenan, Mika Masa Amnaa tayi wadda ke sankame cikin zani, "baiwar Allah lafiya ya Zaki kawo Mana gawa kice muduba ta Anya kina da hankali kuwa?" "Gawa kuma wallahi ba gawa bace da ran ta Dan Allah ku taimake ni" "kinga baiwar Allah ki kwantar da hankalin ki Naga gaba daya a rub'e kike ,wanan yarinyar da kika kawomin ta riga da ta mutu Babu wani sauran Rai a jikinta" "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ta mutu dan Allah doctor ka duba ta walalhi Bata mutu ba da ranta mai yasa zaku yanke wanan hukunci Haka ku gawada duba lafiyar ta zaku tabbatar da abin da n'a en fada maku kawai fa ruwa ne ta dan daketa ,shine har zakuce ta mutu Dan Allah ku taimaka wallahi idan mijina yazo yaji wanan abu kasheni zaiyi" "Kinga baiwar Allah kada fa ki daga Mana hankali mu Ina ruwan mu da wani mijin ki da wayasa ki barta ruwan ya dake ta sakacin ku na mata lokacin da take a cikin ruwan ke kina Ina Sabi da tsabar rashin sanin darajar haihuwa" "Dan girman Allah doctor Ni dai katai makeni komai zakace saika fadamin daga baya amma ni yanzu ka tausaya min, wanan dada 'bata lokacin da akeyi wajan Yin magana shima saΓ― yasa ko Bata mutu ba ta mutu dan Allah ka taimaka please" "ke Kinga bafa Zan taba yarinyar Nan ba salon ta karasa a gurina ki d'ebo min hukuma kice na kashe Miki yarinya to bazan iya ba ,Zaki iya tafiya" "idan kana son iyayen kan ka taimake ni. Dan girman allah" "uhm shikkenan to jira Ni anan "ya juya ya Soma tafiya zuwa cikin asbitin, daki daya ya shiga wan da shine daya daga cikin d'akunan da ake ajiye yara wadan da suka kusa mutuwa ko suka mutu, a kan gado ya Dora ta sannan ya zuba Mata Ido Yana kallon ta cike da nazarin a bin da ke damun ta, hannun sa ya saka guda daya a kan cikinta sannan ya shiga anfani da yatsun sa guda daya Yana d'an d'Anna kirjinta zuwa cikinta ,ba a dauki wasu 'yan mintina ba saΓ― ga ruwa Yana fitowa daga cikin bakinta Har da hancin ta, da sauri doctor ya zaro Ido cikin kidima yace "subahanallahi" wannan ruwa Haka garin ya akai Haka?" Yana magana Yana danna wa har ruwan ya daina fita daga bakinta ,can Kuma baiwar Allah taja wani dogon numfashi ta Soma bude idonta, saΓ― kuma ta canyara da ihu Daman kuka take abin ya faru ,ganin Haka yasa ta cigaba da kukanta tana Mika Masa hannu alamar ya dauketa duk a tunanin ta a lokacin acikin ruwa take ,Gaba kidaya tabi ta furgice ,Babu yadda doctor ya gudun Kar ta shid'e yasa ya saka hannu ya dauketa yashiga jijjigata Yana Dan babbuga bayanta, can Kuma sai yaji shiru alamar tayi bacci, hakan yasa yayi gan dala ya Mai da ita Daman gadon ya fita waje gurin zainab,


Yana zuwa gaban ta a fusace yace "kina da hankali kuwa Anya ma wannan yarinyar kece kika haifeta?" Kasheta kikeso kiyi ko?" "A,a doctor wallahi 'yatace Kuma kasan yadda uwa takeji akan danta bazan taba iya kashe wannan yarinyar ba Ina son ta to Mai zaisa na kasheta?" Karya kike da ace yarkicr baza ki barta a waje ke kishiga daki ba, da alama mahaifiyar ta kishiyar kice ko?" "Haba likita yazaka d'inga Bina da wadannan munanen kalmomin Akan Yaya Mai kasani akai na" tana magana Tana kuka "Ina da miji Amma kamar Banda miji kullum cikin kuka nake da kuncin rayuwa yanzu takai ta kawo ma abin cin da zamuci ga garar mu yake balle kuma gurin zama , yau Watan mijina daya da guduwa ya barni Babu Kira Babu message kullum cikin bin gida Jen masu kudi nake Ina atai nakamin , yauma abin da ya faru kenan nashiga makotan mu domin su taimaka min kafin n'a dawo Ashe ita ta rarrafo ta fito waje shine nazo na sameta acikin ruwa tsulum_tsulum ruwa ya shanye ta har wuya , wayyoo Allah na bansan Mai zanyi ba bani da kowa bani da Mai taimako na uhm uhm uhm" kukan zainab ya tsanan ta kamar gaske, shikuwa doctor Nan take jikinsa yayi sanyi idanuwan sa duk suka cika da kwalla ,murya a sanyaye ya kalle ta yace "kiyi hakuri kinji wallahi nayi Miki mummunar fahimta ne shiyasa Amma kiyi hakuri kinji Kuma inssha Allah Zan taimaka Miki da wasu kudade kafin ki tafi kinji" "to doctor nagode kwarai da gaske Amma da kabar shi bana son na dora maka nauyi " "a,a ai bake kika rokeni ba nine nayi niyyar na taimaka muku ,tom shikkenan doctor nagode Allah ya saka maka da alkairi ya biyaka da gidan aljanna ,yanzu Ina ita Amnaa take da dukkan alamu wani abu ya faru da ita shiyasa kafito kanamin fad'a" ta yi maganar tana Jan majina hade da rausayar da murya ,Wai dan ya kara jin tausayin ta, "uhm Kar ki damu dama' nazata kina sanene kika Mata Haka da ace an Kara wasu yan dak'iku kafin ki kawota zata iya mutuwa alokacin sai Kuma Allah yayi da sauran kwanan ta a Gaba ,yanzu tasamu bacci Zaki iya shiga ki ganta Allah ya Kara lafiya sai a kula" "insha allah doctor Zan kula yanzu ina ne dakin" ta tambaye shi yayi Mata nuni da hannu, hanyar d'akin ta nufa ta bude kofar a hankula sannan tashiga ,karasawa tayi bakin gadon ta Yi tsaye a kan ta, Can kuma ta tabe Baki Tace "shegiya wato Ni Ina can Ina zabga karya danna fitar da kaina Ashe ke kinan kina aikin sharara bacci ,dama kin mutu ai shashasha"ta fada tare da Kai hannu zata dungure mata Kai saΓ― ga doctor ya shigo, da sauri ta Shiga shafamata Kai tana cewa "wayyo Allah yarinya ta yanzu da kin tafi kin barni shikkenan bani sauran wani wan da Zan gani naji dadi ,Kai Allah na gide maka da ka rayamin amnaa ta" "uhm gaskiya ne alamu sun nuna kina kaunar 'yarnan Taki Kuma gata kekykewa Ni har da zance kibani ita nayi rainonta?" "Ni wallahi da Haka zata faru Dana fi kowa farinciki" tafada a zuciyar ta a fili kuma Tace" uhm ai doctor yadda nake son Amnaa bazan iya bada kyau tar taba ban sani ba dai ko ban Gaba, amma doctor Kai da ga gani ma ko aure baka da shi balle Har na dau yata n'a baka to waye zaiyi rainon kenan?" "Uhm Ni na fad'a Miki ai ninan da kike gani raino gadon gidan mune duk da bani da aure ki bani ita kiga yadda Zan nuna Mata gata" "tab Ni da banason taji dadi kodai dai da sa,a dayane shine zakace na baka ita taga gata "afili Kuma tace uhm a,a dai doctor kabarni da yarinyata hakan ma na gode" "Tom shikkenan nidai daman aikine ya kawoni kasarnan Kuna agobe nake Shirin komawa kasarmu ga Katina idan Kuna bukatar wani abu sai ku tuntubeni ta wannan number " to doctor Aina kake kenan ?" Uhm kowa nawa Yana kasar faransa iyayena Dan Gina yayan Nina Kuma dama' abin da ya kawoni adamawa na kammala shi Dan Haka gobe zan koma Dan Allah mama sai adada kulawa kinji" Baki zainab ta sake budewa ta saki kuka Tace "yaro tun da nake Babu wan da yata'ba kirana da maman sa kowa kallon wulakan tacciya talaka yakemin ,amma saΓ― gashi yau nasamu da Wan da ya girmamani ngd sosai yaro " "ah haba idan bama girmama manya da wad'an da suka girnemu ai bamucika ginin Abban muba inason kisa a raki kinsamu da Wanda zai tallafa Miki ,akullum mahaifin mu Yana ce mana duk wata MacΓ© komai kan kwantar ta kada musake mu wulakan tata Sabi da watarana itama uwace Dan Haka kema a yanzu kinzama mahaifiya a gareni ,yanzu Ni Zan tafi Allah ya Bata lafiya ga wannan sai kusayi wasu abubuwan da Baku da shi" ,ya Mika nata bandirr din kudade guda uku sannan ya juya ya fita, Baki da hanci ta saka tana mamaki wannan kudade Haka to shi wannan d'an gidan wane tab da alama Watan tafiyata Hajji ya Kama ,lallai wannan yarinyar tazo da 'kashin arziki Amma fa hakan bazai Hana naki cin ubanki ba ,nadai hakura ki danyi wasu 'yan shekaru a duniya kafin Nan Nima na samu abin da n'a samu a gurinsa inya so saina kasheki....





πŸ’”_____*DEPRESSION*_____πŸ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*πŸ’”
*#JURIYA*πŸ’”
*#SOYAYYA*πŸ’”
*#DAMUWA*πŸ’”
*#HAKURI*πŸ’”
*#YAFIYA*πŸ’”
*#KYRA*πŸ’”


*Chapter 8*

TO😌 TO😌 TO😌πŸ’ͺπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ DA KARFIN

Please Login or Register in order to submit comment