Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannu a daidai kan idonsa taba gwale idon wai ala Dole saรฏ ya tashi,


Bude Ido yayi Rai a bace kamar Daren mutuwa ya zabga tsaki ya kalleta yace "Adeena menรฉ Haka ? "Kaii Adeena kuma? "Uhm sorry Mommy lafiya sokike ki kashe Dan Baki " "a,a ni ba so nake ba ganinai kowa zai fito yayi Hira Amma ban da Kai Kai kullum kana cikin daki nayi nayi kana fitowa kaki, kumama Tai abbanmu zai dawo Amma Kai ko farinciki ma bakayi, jiya ka dawo gidannan inata murna dana ta dawo Ashe kace murna ta koma ciki duk kasa jikina yayi sanyi kullum Kai damuwa Haka ake" ido ya Kura Mata sosai Yana kallonta kamar ba itace take zaro wadannan zantukan ba, Yana mamakin yadda yarinya karama take zama tana zaro wadannan zantukan, "mommy Wai keko kike wannan zancen?" "Ban fahimta ba da waye Naga mu biyune a cikin d'akin" "uhm ai kawai Naga kin fage sai Dada kikemin ,to Allah ya huci zuciyar mother yanzun Nan Zan tashi ai bansan yau Abbanmu zai dawo ba shiyasa kikaga ko shiryawa banyi ba" "to yanzu kasani ai sai katashi ka fara shiri nima yanzu wanka zanje nayi Nay kwalliya dan Kar ammi tafi Ni yin kyau " " to Adeena yau Kuma keda ammin naki ?" "To ai dukana tayi kumama yau bazan shiga dakinta na dakko kayaba sai dai ka fita ka sayomin sabo " "haba mommy sabon Kaya Kuma ki tausayamun nagaji bazan iya tafiya ba Allah kiyi hakuri kishiga d'akin ammi ki dakko kayanki" "tab Ni fa bazanje ba nayi ritaya nida shiga d'akin ammi sai nayi sati guda kumama duk abin ta yau idan Abbanmu ya dawo kwana nane ba nataba" zaro Ido Abeed yayi tare da ruke Baki yace "kwananki Kuma kedawa zaku kwanta din?" "Ni da mijina abbanmu Mana?" "Ah lallai mommy kin debota da zafi lallai kina son ammi tayi kulikulin kubura da ke tab ah lallai" "uhm wa abbanmu yananan zata dakeni tab kaga Ni katashi ka sayomin kafin ka dawo nayi wanka a nan dakin ,dan yau bazan SHIGA dakin Ammi ba " tayi maganar tana turo Baki "shikkenan gimbiyata ai ba sai kinyi kuka ba duk yadda kika ce Haka za,ayi" Yana Gama fadar Haka ya saka rigarsa jallabiya blue ya fito falo, anan ya samu Abjeed a zaune ya kishingida da bayan kujerar ya lumshe Ido Babu abin da yake damunsa gashin idonnan nashi kuwa ya sakko Gaba daya ya rufe Masa kasan Ido Zara Zara abin dai gwanin Sha,awa Dole abbansu yace shi har yanzu Bai ga namiji Mai kyau irin Abjeed ba,


" Am Abdul majeed! Dan Allah idan ba wani abun kake ba tashi na Dan aike ka" bude ido yayi a hankula cikin nutsuwa yake kalllonsa Dan ya San Babu Mai fad'a Masa irin wannan sunan sai shi, kallonsa yayi yace "na d'aka kafito kenan?" "Kaga Ni ba wannan nakeson jiba idan zakaje to idan kuma bazakaje ba natafi da kaina" "bazai jeba tafi da kanka Babu wan da ya hanaka" ammi ta fada lokacin da take karasonwa cikin falon "ammi kanina ne fa ban Isa na aikesa ba?" "Ni Kuma mahaifiyar kace ban Isa na baka humarni ka jiba?"

"Allah ya huci zuciyar ki ammi zanje da kaina kamar yadda kike so" Bai sake kallon inda Abjeed ya keba ya fice daga part din, Kai tsaye parking space ya nufa ya shiga mota zai fara tuki,wayarsa ta shiga ruri ,rainsa Bai soba haka ya dauki wayar ya Kara a kunnensa "Assalamualaikum" ya furta a takaice "am Abeeddeen Abban ku nake nema yanan kuwa Dan na Kira wayarsa naji Bai daga ba" "uhm wallahi abbanmu bayanan Amma ban sani ba dai ko Yana hanya shiyasa Bai daga ba, yau nake tunanin zai dawo" "okay Allah ya dawo da shi lafiya Daman maganar aurenku da haleema ne naji shiru nikuma sonake n'a aurar da yarinya ta " "uhm abba indai wannan maganar ce aini ma zan iya baka amsa ba sai Abbanmu ya dawo ba ,kawai kayi Mata auren dama' Ni ban shirya aure yanzu ba kuyi hakuri,"lallai ma yaronnan kacika dan duniya wato baka shirya aure ba ,irin ga gold dinan ana bibiyar ka Har kasamu bakin wulakanci, to wallahi ka kiyayeni aikin banza ni gangancine yasa ZAN baka auren 'yata " Bai jira abin da Abeed zai ce ba ya katse wayar kitt.


Allah sarki abeeed kifa kansa yayi a kan sitiyarin motar ya saki kuka n'a rashin dalilin mai yake damunsa Gaba daya ta rasa duk wani farinciki ,komai Yamada zafi rayuwarsa gaba daya tazama a bin tausayi yasan ba komai bane face sakayya kamaryadda damuwarasa ta illata zarah a baya shima gashi zuciyar sa tana son bugawa sabi da tunanin da kunci, jiyayi an rabashi ta baya ,saurin d'ago wa yayi Yana kallonsa a zuciyar sa kuma yace "daman bai rufe kofar motar nan ba" afili kuma saรฏ yace "Abjeed ! Lafiya ?" "Yaya wai maiyake faruwa ne maiyake damunka narasa mai yaje faruwa dakai ni fa da ba Haka nasan yayana ba ,amma jibeka yanzu duk dรฉpression ya maka yawa ,ita wadda kake domin ta mebi ma yanzu Bata Raye Dan Allah Yaya ka daina tunanin nan, sannan ina son kaje ka roki yafiyar abbana zai yafe maka nasani sabi da abbana Yana da hakuri nasan girman zunubin da ka aikata bai zama lallai ya goge cikin sauki ba ,Amma ai an dade dolene abbana ya manta wasu daga ciki ka daure Dan uwana dan Allah, bana jin dadin ina ganinka cikin damuwa ,kwana biyu Adeena datake yarinya karama itama ta Soma damuwa Akan yadda kake rayuwarka a gidannan sokake ta tsinci kanta a yanayin da kake ciki?" "Uhm Abjeed bazaka gane ba bakasan komai ba Kai yarone har yanzu , kaje kawai Zan fita" "a,a Yaya wallahi bazan barka ka fita a irin wannan yanayin ba , koma mainene ka kawo n'a sayo maka" "a,a Abjeed kabarshi bakaji abin da Ammi Tace ba bazaka ba" "uhm Ammi ai ba sabi da haka Tace baza niba itama tagaji da halinkane na ko in kula shiyasa takeso ka dan taka da kanka kaima sabi da zaman dakin shima wani ciwanne haba ayi mutum kamar wani sakago, yanzu dai idan ma baza ka bani nasayo maka ba mutafi tare" Babu yarda Abeed ya iya ya Soma tuka mota Har baki gate Mai gadi ya wangale musu gete suka fita,




Wani karamin store suka shiga , Kaya masu kyau suka kwasowa Adeena sosai sannan suka buya kudin suka fita zuwa mota, BAYAN sun saka kayan a ciki ne suma suka shiga motar suka Soma tafiya cikin nutsuwa har suka karasa cikin warabar gidan su, bude musu gate Mai gadi yayi suka shiga ciki ,bayan sun Yi parking suka fito dauke da kayan a hannun su suka shiga cikin gidan , Basu tadda kowa a falon ba Dan Haka Abjeed ya shige bedroom dinsa shima Abeed ya shiga nasa bedroom din dauke da kayan Adeena a hannunsa,


A zaune ya sameta ta Yi wanka hadda saka janbaki da jagira, abin gwanin ban dariya Sabi da kwalliyar ma Bata iyaba , Jan bakin duk ya hauro fuskarta , Abeed da ya shigo da dariya zaiyi sai Kuma ya fasa Sabi da yasan halin darunta "awwwwn kinganki kuwa ko turawa albarka" "Allah dagaske kake uncle?" ",Uhm dagaske mana ga kayanma n'a sayo Miki kiyi sauri kisa Abba ya karaso Dan yanzu ammi ta tafi airport " kuka ta saka ta Soma daru harda burgima Wai yaza ace ammi taje taro Abba ita Kuma a barta a gida, da sauri Abeed ya katseta da cewa "ya Isa mommy Zaki Bata kwalliyar sokike ya dawo yaga bakiyi kyau ba? To albishirinki ammi batayi kwalliya ba ta tafi Kinga kafin ta dawo ke kinyi walliyarki ko? "Eh hakane ta washe Baki tana dariya shima dariyar ya Soma Yi, Dan shi Babu abin da ya bashi dariya kamar janbakin da ta lafta har saman hakoranta ,Wai duk a tunanin ta ita ta kure kyau.


Doguwar riga ya Bata fara Mai ratsin ado Baki da pink sai dankwalin rigar baki, Yana Bata ya fita yace "to Ina jiranki a falo natafi taro abbanmu" to Tace Masa kawai ya fita.

Bai Dade da zama a falon ba sai jin jiniya yayi ta ko Ina da karar shigowar motoci ,wannan abin ya tabbatar Masa abbansu ne yadawo ,nan take Abeed ya ji jikinsa yayi sanyi Haka kurum yaji jikinsa na Bari kamar nazari, kokarin saita kansa yayi ganin Adeena ta fito daga d'aki da gudu ,hakan yayi daidai da shigowar Abba falon ,a guje ta fad'a jikin sa Yana murna tana cewa "oyoyo abbanmu " shima murna yashiga yi da murmushi Yana cewa "oyoyo amaryata, kinyi kyau fa" "Allah abbanmu nayi kyau ? Tana magana Tana watsawa ammi harara , sannan ta cigaba da cewa "abbanmu Amma ai nafi ammi yin kyau ko" "ah haba Wana zai hada kinfita kyau itafa ta tsufa" dariya Adeena tashiga yimata har da kwalo , Abjeed da ya fito daga dakinsa shima rungume Abba yayi Yana dariya Yana cewa "I miss you baby boy" Rai Abba ya hade tare da cewa "ka Soma ko?' "u uhm uhm shikkenan bazance maka baby boy ba to naji muje kaci abinci ka huta ko" "tom shikkenan muje" "a,a Abbana bakaga Yaya Abeed bane tun dazu yaketa maka sannu da zuwa baka amsa ba" "oh Ashe Daman da mutum a falon aini ban ganshi ba" Nan take jikin Abeed tasakeyin sanyi ,Amma duk da Haka baiyi kasa a guywa ba yasake cewa "abbanmu sannu da zuwa" "banza yayi Masa tare da watsa masa harara ya huce ,har yaje bakin kofa yace "waye Abban naka ? Metsamtssss Abba yayi tsaki ya huce ciki.


Wannan abin da abbba yayi yakarasa jikin ammi da Abjeed da duk mutanen gurin yayi sanyi musamman ma Adeena da take tsananin son uncle dinta batason ganin damuwarsa,

Shikuwa abeef idanunsa ne suka kawo kwalla saura kadan su zubo yayi saurin tarewa da hannunsa ya saki murmushin karfin hali ya kalli Adeena wadda tayi tsugune a gabansa yace "Mommy yanaga kin tsaya bakibi angon naki ba?" "Uncle meyasa kake kuka? Abbane ko kayi hakuri kaji uncle " murmushi ya sake sakar Mata yace "mommy Mai kikagani ba kuka nake ba " uhm Allah uncle kuka kake , uncle Wai maiyasa abbanmu yake maka Haka sainaga kamar baya sonka" "uhm Adeena ki daina fad'ar Haka abbanmu Yana sona "ya karasa maganar ragowar hawayen cikin idonsa suka Soma gangarowa da sauri ya Mike ya nufi dakinsa ,Yana shiga ya fada kan bed ya fashe da kuka .


Ammi dake tsaye batasan dan da ta zauna a kujera ta Soma rera kuka kamar wata karamar yarinya, Adeena dake zaune inda yatafi ya bb arta duk sai taji tana jin haushin abba Sabi da yasa sahibinta kuma rabin ranta kuka,.


Acan cikin dakin kuma Abjeed ne ke biye da abba Har yasamu guri ya zauna,BAYAN Abba ya zauna be Abjeed ya kalleshi yace "abbana !

"Naam karamin su babban su" "uhm abbana abin da Kai yanzu banji dadin Saba ,sai Naga kamar Bai kamata ace har zuwa yanzu kana jin haushin Yaya Abeed ba yakamata ace ka yafe Masa"

"Uhm Abjeed kenan bakasan komai ba har zuwa yanzu Kai yaro ne a lokacin da komai ya faru baka gama sanin mecece rayuwa ba shiyasa kake kallon abin da nayiwa Dan uwanka a matsayin ba daidai ba, ba Kai ba nima inajin Babu da di Akan abin da nake Masa sai dai bazan iya jurewa ba dolene sai na nuna Masa kuskurensa"


"A,a fa abbana kuskure dayane yaruga da yayishi Kuma Abu yaruga da ya shude yazama tarihi ya kamata kaima ka manta yazama tarihi a zuciyarka ,yanzu fa ace Yaya Abeed ya kwanta ya mutu wuta zai shiga kasan meyasa Abba sai bida kaki ka yafemasa fishin iyaye Akan da Yana matukar tasiri a gurin yaro Dan Allah Kai ka yafe Masa Kai zafin yayi masa yawa ga naka gaba zarah"


"Uhm nasani Abjeed ko da ace na yafe Masa ita Kuma Adeena fa?"


"Oh my God"

Abbana Adeena batasan komai ba ita kanta yarinyar tanajin Babu dadi akan abin da kakeyi Masa yakamata ka fahimta abbana ,ni yanzu Zan koma gurin Yaya Abeed ko Zan iya samun wasu kalmomin a bakina da zai sa ya ji dadi idan na fada mas_a"

Shi dai Abba Bai ce komai ba har Abjeed ya fita sai dai magan ganun da yayi Masa Gaba daya sun Gama kashe Masa jiki .

๐Ÿ’”_____*DEPRESSION*_____๐Ÿ’”
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*๐Ÿ’”
*#JURIYA*๐Ÿ’”
*#SOYAYYA*๐Ÿ’”
*#DAMUWA*๐Ÿ’”
*#HAKURI*๐Ÿ’”
*#YAFIYA*๐Ÿ’”
*#KYRA*๐Ÿ’”


*Chapter 12*

TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ TO๐Ÿ˜Œ๐Ÿ’ช๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ



๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
๐Ÿ’”_*DEPRESSION*_๐Ÿ’”
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 12*




************


"Ammi ! "Naam fu ad" "ammi bakiyi murnar dawowa ta bane? "Haba fu ad Ni na Isa Mai kayimin da Zan ce banyi murnar dawowar ka ba, kuma abin farincikin ma har da kyautar da da ka kawomin " dariya fu ad yayi yace "ammi yanzu dai gashinan Zan barshi a gurinki Ni Zan shiga ciki na Dan huta kafin yamma Zan fito "


"Okay tom shikkenan sai ka fito"

Fu ad Yana shiga d'akin kayansa ya zazzage ya dakko littafin Nan ,sai da ya tabbatar Babu wan da yake ganinsa sannan ya tura kofar dakin sa tare da saka mukulli ya rufe, ya koma cikin bedroom dinsa, riga kawai ya cire ya kwanta a kan gadon wanka yakeso yayi amma zumudi da matsuwar san karanta littafin ya hanashi yin komai, numfashi ya danja kana ya sauke ajiyar zuciya yabude feji na biyu ya Soma karatu kamar Haka........



"Acikin ak fadama akwai wani guri wan da abbanmu ne kadai yasan gurin saรฏ ita ,ananne inda masifa ta Soma afkamin tsakani n'a da ita , yau kamar kullum Ina zaune a dakina ina danna waya, saรฏ ga Kira ya shigo dauke da bakuwar number, da kamar bazan dauka ba sai kuma wata zuciyar tacemin ka dauka mana kasani ko damuwa ce, daya zuciyar kuma Tace "a,a karka dauka mebi irin matan nanne masu bibiyarka suna kaunar ka" ban bi ta wanna zuciyar ba sai na daga,ta shin farko abin da ya tsayarmin da tunanin da nake a lokacin dai dai lokacin da sautin gudun zuciyata ya karu jin wanan dadda dar muryar "Assalamualaikum" Baki na harrawa yake wajen cewa "wa, alaikumussalam" "Ina wuni yaya? Kwakwalwata ce ta sakรฉ kullewa jin yadda yarinyar ta kirani da yayanta sai Kuma na sake shiru Ina sauraron abin da zata ce n'a gaba, "Yaya baka ganeni ba" to alokacin gaskiya ban gane taba domin Ni ba mazauni bane ko a gida sai dai na kalleta ta kalleni Babu abin da ya taba hadani da ita, shiyasa ban dauki murya ba, a hankula na bude Baki nace "a,a ban gane koba gaskiya" "uhm uhm Yaya zarah cefa " "zarah Kuma wacece zarah Kuma?" Wanan tambayar da nayi Mata yasa ta k'atse wayarta Dan ita a tunanin ta ta zata sonta nake kamar yadda itama take Sona, sai yau ta fahimci ita kadai take haukanta,

Katse wayar da tayi Ashe kuka ta fashe dashi lokaci guda har da majina, wayarta ta janyo a hankula ta danna Kiran kawarta jalila ,bugu biyu jalila ta daga muryarta na magagin bacci Tace "zarah lafiya Naga kiranki yanzu?"


"Wayyo Allah na jalila nashi ga uku na afka tarkon da Babu Mai iya tsamoni sai Allah jalila ki taimakeni" "nashiga uku zarah Mai yake damunki Haka kukafa naji kinayi kodai yayan nakine?" "Uhm jalila shine Mana Ni Ina ta haukana Ashe shi baya sona ni kadai nake haukana yanzu yazanyi nashiga uku" zarah ta sake fashewa da kuka kamar wata karamar yarinya.


"To ke shi da bakin ki yace baya sonki ,haba zarah ne zai ganki yace baya sonki ,saรฏ dai in bashi da zuciya a kirjinsa ,ke ko macece ta ganki ai sai tayi dagaske zata iya dauke kanta daga gareki, ki kwantar da hankalin ki Dan Allah indai shine kisa aranki shima Yana sonki, yanzu ki samu kiyi bacci kinji"

"Uhm uhm dan Allah jalila ki taimaka kada ki kashe walalhi tsoro nakeji dan Allah" tana maganar tana shashshekar kuka, "to yanzu zarah idan ban kashe ba yakike so nayi ,na farko dai Ni ba iya ciremiki son shi zanyi daga zuciyar ki ba nabiyi Kuma Ni ba iya tararsa zanyi na sanar Masa ba ki daiyi tunani Dan wallahi idan kika cigaba da sa damuwa a ranki zuciyarki zata iyayi bindaga"

"Uhm shikkenan jalila a tinanina ke kad'aice wacce Zan iya kawowa kukana naji sanyi a Raina domin Ina tunanin Zaki iya faran tamin da kalamar masu dadi, Ashe ba Haka bane " tana Gama fadar Haka ta k'atse wayar tare da d'ago wayar a hannunta tashiga kallon hoton Abeed tana zubda hawaye masu zafi,

******


Bayan ta kashe wayar Kira na shiga domin son sanin wacece wadda take kirana Dan kokad'an ban kawo wannan zaran bace nayi tunanin watace daban a waje, a Daren ne n'a fahimci irin soyayyar da yarinyar take nunamin,

Misalin karfe 3 na dare zarah takasa Koda runtsawa Sabi da tunani na koya ta kwanta ta rufe idonta nine dai wan da take gani, hakan yasa ta kasa jurewa ta dauki wayarta ta turamin massage Akan na fito lambu Zan San kowace a wannan Daren, sannan ta Kara da cewa idan kuwa ban fito ba Dole zata kashe kanta ta huta.

A lokacin da message din ya shigo wayata nayi tunanin cewa message din mTN ne saina ga Ashe wannan bakuwar number ce, dan Haka nashiga karantawa ,abin da zai baku mamaki shine ,yadda jikina ya hau tsima Sabi da tunanin yadda za ai ace mutum ya ce kafito karfe 3 n'a dare ,so a lokacin nayi tunanin cewa aljana ce kawai nayi gamo ba mutum bace, dan Haka nashiga yin addu,oi duk wadda tazo bakina, can Kuma sai naji nafara daina jin tsoron da nakeji, take tinanina ya Soma dawowa, namike zumbur na nufi hanyar fita ko riga Babu dagani sai gajeran wando, cikin sanda na karasa lambun abbanmu Danni banma taba shigaba duk da dewata a gidan ban taba sanin akwai wani lambu a gidan ba sai yau,
.

Ina karasawa can na hangota ta kifa Kai hannunta Kuma wukace Mai kaifin gaske, addu,a na sakeyi sannan na Soma takawa zuwa kusa da ita cikin jarumta da fargaba,har na Kai inda take a tsugune, batare da nace Mata uffan ba nayi tsaye a kanta, jin Haka yasa ta d'ago ta kalleni idanun ta sun rune sunyi jajawur kamar garwashi fuskar Nan Tata tayi ja ta kumbura Sabi da kuka, bakina na sarkewa nace "Kai zarah meya sameki Haka? Wai kece Daman? "Kuka tasake fashemin da shi a lokacin tare da fadowa kirjina tana cigaba da kukan, sai lokacin na gane yadda akejin juciya na bugawa sosai idan soyakai so , hannuna ta janyo daddai saitin zuciyar ta Tace "Yaya kaji yadda zuciyata zata buga ko" "ya Salam "ya furzar da iska daga bakin sa yace "zarah meyasa kike fadar Haka zuciyarki bazata taba bugawa ba in dai a kainane"

"A,a Yaya kada kace haka wallahi tana gab da bugawa saura kadan muddum baka Soni ba" "uhm zarah kenan waya fada Miki ni bana sonki, nima ai Ina sonki Zara,una" "to Amma Yaya kabarni Ina Shan wahala kasan tsawan shekarun da aka dauka inata dakon siyayyarka , Ada nayi tunanin hakura zanyi Yaya" "ki hakura Kuma akanme Zaki hakura bayan Ina sonki" "uhm bazaka gane ba Yaya kafi karfina ta ko Ina a Koda yaushe idan kasamu wadda ta fini zaka iya barina ka koma gurinta" "Zara,u ! Kenan nima ina sonki kuma abin da kike tunani bazai taba faruwa ba insha Allahu" "uhm Yaya i love you" to Yaya ya kayi shiru kace wani abun Mana?" "I kiss you " "kana so ne ?" "Uhm indai za aimin ai ina so" "tab to Ni Yaya komai kakeso indai Ina dashi Zan maka" "tom shikkenan yanzu dai Bari nayi kiss din , ko "uhm uhm ba yanzu ba Yaya sai munyi aure" tana gama fadar Haka ta cire jikinta daga nasa tayi cikin gida da gudu zuciyarta cike fal da farinciki, ni kuwa tsayawa nayi kamar wani sakago ina tunanin yadda Zan iya koyawa zuciyata soyayyarta batare da na wahalar da ita ba".


Jin wannan maganar da Abeed ya fad'a yasa Fu,ad rufe littafin tare da gige zufar da ya hada bakinsa na rawa yace" innalillahi wa'inna ilaihirraju un kenan dama baya son ta ya amsa kenan mezai faru? Ya bude littafin zai cigaba da karantawa yaji ana kwankwasa d'akin basa, tsaki yayi ya Mike duk da baisan wanene ba amma dai ya Bata Masa Rai arasa San da za azo a takura Masa sai lokacin da yake karanta wannan littafin,


Mikewa yayi ya karasa bakin kofar ,"wane? "Uncle Fu ad nice" "kewa? "Ni Adeena abbanmu yace idan ka gama abin da kake kazo kuci abinci" "okay Tom shikkenan kicewa abba ganinan zuwa " "Tom Uncle sai ka fito" bai ce mata komai ba ya juya saman gadonsa yayi shiru Yana son ya ciga ba da karanta littafin Amma Kuma Yana tsoron ya cigaba da karatun abba yaga baizo ba yasake aikowa, magana yasoma Yi shikadai Yana cewa "to Amma idan na cigaba da karatun a ai banyi laifi ba ,tun da abbanmu yace nagama abin da nake.

Kwanciya yayi ya sake dakko littafin ya bude shafi na biyar ya ciga ba da karatun sa daga inda ya tsaya .....


********

Ban San Mai yasa yarinyar Nan ta nemi shigowa rayuwa taba,Ni dai har zuwa wannan lokacin Ina tsaye a inda tatafi ta barni ,a tsarin rayuwata bana da bajed din na auri wata a ahalin mu , Sabi da Ni nasan kaina bazan iya adalci ba ,domin zuciyata daban take da ta sauran mutane ,amma Kuma sainayi kokari na bar abin a zuciyata na Soma takawa zuwa part dinmu, a lokacin da na Shiga falo kafin ba bude kofata sai da nayi duba zuwa kofar d'akin ta ,a take tausayinta ya shiga zuciyata ,Sabi da yadda Naga tana zubar da hawaye a kaina ,babban kato barar da na tafka a rayuwa ta kenan tausayi ,ko da so daya ban taba Jin son zarah a Raina ba ,Amma Kuma lokacin da na Yi tozali da ita sai naji Gaba kidaya tausayinta ya mamayemin zuciya, abin da zai Baku mamaki Ni Abeed har yanzu ban fara sonta ba ,Sabi da Ni kyaun mace ko muryar ta baya taba rudani, a yanzuma da kukaga

Please Login or Register in order to submit comment