Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su hud'u suka yi min fyad'e wanda sanardiyar haka tun ranan bana magana dan bana ma hayyaci kafin su kashe ni police suka zo jin karar motan police yasa su guduwa suka barni cikin jini


Makotan mu ne ya taimake ni kasancewar dama bani da kowa sai zainab dan dama mu marayu ne


Malam musa ne ya kaini kauyen su ya bani kulawa har na samu lafiya amma bana magana


Wata d'aya da suka wuce Allah yayi wa malam musa rasuwa shine nace bari na shigo gari niman RAYHAN shine ranan nan a cikin gari naga a nuna shari'ar ki a TV tundaga ranar nace sai nimo ki dan ke kad'ai ne zaki iya hukunta Abida"


Kasa magana tayi dan kuka da yaci karfinta,rungume ta IKLAS tayi itama kukan takeyi cikin kuka tace"yi shiru inshaallah zan sa kotu tayiwa ke da zainab da nuratu adalci ita kuma Abida sai ta fuskanci hukunci dai-dai da abinda ta aikata wanan alkawari ne"


Ummi ko kuka tausayin zaliha takeyi tace"wanan wani irin hasabibiya ce?"


Islam tace"anty karki raga mata"


Kallon zaliha IKLAS tayi tace"yanzu ina kwalbar alurar da videon?"


Zaliha tace"yana pause d'in na kafin inyi accident,amma tunda na farfado banga pause d'inba"


Da sauri Islam tace"yana wajena Abba ya bani in ajiye"


IKLAS tace"je ki d'auko"da gudu taje ta d'auko,suna bud'ewa sai ga kwalbar da memory card


Kallon Islam tayi tace"d'auko mana laptop"


Suna saka memory card suka shiga video nan suka kalli komai da ya faru Ranan


IKLAS tace"........
































Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.


Dedicated to my fans


πŸ…Ώ6⃣7⃣&6⃣8⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Abida tace"dolene ma in kashe IKLAS"


Mugu yace"angama masoyiyata yau zan aikata lahira"


Tace"ah ah ba yanzu ba,so nike a sato mun ita,saboda bana so ta halalci zaman kotu,kaga inba ganta ba za ayi wasi da maganar,mu kuma bayan anyi wasi da maganan sai mu kashe ta"


Mugu yace"haka yayi,yanzu yaushene zaman kotun?"


Tace"nan da sati d'aya wato Monday 6-7-2019"


Yace"toh gobe zan sato ta"


Tace"na yarda da kai"


Washe gari minal ta kira IKLAS a waya dake kwance zazzabi tace "hello IKLAS kina kina?"


Da k'yar ta amsa da eh


Minal tace"ki zo ki same ni a asibiti yanzu angama bincike akan alurar da inda take aiki a jikin d'an adam lab attendant d'in mu zai miki bayani"


Tace"toh gani nan zuwa"


Da k'yar ta mike dai-dai nan RAYHAN ya fito daga bayi yana ganin ta tsaye yace"ya dai wiffy jikin ne"


Tace"da sauki"


Yace"toh yaya ne dear"


Kasa magana tayi dan miyau ne cike a bakin ta,san da ta je ta subar ta dawo


Tace"wallahi minal ne ta kirani in same ta asibiti akan magana binciken nan"


Yace"ba inda zaki dube ki fa baki da ishashen lafiya kike maganan zuwa wani wuri,akan wani banzan shari'a,nifa hankalina bai kwanta ba akan wanan abun"


Rufe me baki tayi tace"mijina bana son mu maimaita wanan maganan addu'a ka nike da bukata"


Yace"toh ai shikenan"


Tace"muje kayi min wanka toh"


Yace"ke ma kinsan in muka shiga sai na latsa dan wallahy bazan iya ganin ki ba kaya ba in hakura"


Tace"toh muje kayi inda kake so"


Dariya yayi yace"yarinyar nan na lura kwana biyu kin fiya jaraba"


Bayan awa d'aya RAYHAN ya shirya IKLAS cikin riga da zani atampa hijab yasa mata yace"muje in sauke ki"


A bakin asibiti RAYHAN ya sauke IKLAS yace"in kin gama ki kirani zan zo in d'auke ki"


Tace"toh"har zata fita ya rungumeta sosai tace"lafiya?"


Yace"wiffy wallahi gabana na fad'iwa ji nake kamar wani abu zai faru"


Tace"ka yawaita fad'i inalillahi wa ina ilahi rajiun,insha Allah komai zai zo da sauki"


Yace"nagode baby"murmushi tayi ta fita a motar sanda yagan shigarta asibiti ya bar guri cike da damuwa


IKLAS na shi direct office d'in minal tashiga


Minal tace" sannu da zuwa"


IKLAS tace"yauwa ya shirin biki"


Minal tace"lafiya"


IKLAS tace"minal muje waje warin asibitin nan na damu na"


Dariya tayi tace"hmmm ki kamu kenan"zaro ido IKLAS tayi tace"dame fa?"




Minal tace"ciki mana"


Tace"habadai sati biyu kawai zaki wani ce ciki ne dani"


Minal tace" ko ki yarda ko karki yarda ciki ne dake"


IKLAS tace"Allah ya kawu" tashi sukayi suka je lab nan lab attendant yayi mata bayani tare da bata result d'in,


Minal ne ta ansa suka fito office d'in minal suka koma


IKLAS tace"bari in kira shi yazo ya d'auke ki"


Kiran RAYHAN tayi tace"hello mijina kazo na gama"


Yace"sorry wiffy baki sun mun yawa a office ki bani nan da awa biyu"


Tace"no ba zan iya jira ba zazzabi nike ji ka bari kawai minal ta sauke ni"


Yace"toh sai na dawo ki lula da kanki"


Tace"toh"


Kallon minal tayi tace"minal sauke ni gida"


Minal tace"toh dama zan biya unguwar Ku in anshi d'inki"


Tashi sukayi suka bar office d'in




Minal na drivin suna fira minal tace"kin gan ni da shirme na manta da result d'inna a office"


IKLAS ta bud'e baki zata yi magana kawai sai ga wata mota ta shiga gaban su babu b'ata lokaci suka fito da IKLAS suka wurga ta mota sai ihu takeyi


Cikin tashin hankali ta fita a mota tana niman taimako


Cikin rudewa ta Ciro wayar ta ta kira Abdul ta fad'a me"


Yace"what ai na kike yanzu"


Kiran RAYHAN tayi ta fad'a me halin da ake Viki


RAYHAN dake tsaye yana bayani a mitin zama yayi kasa nan da nan ya fara zufa"


Abba da daddy suka kalli juna daddy ne ya karasa inda yake yace"son lafiya meke faruwa ne haka"


Kallon daddy yayi cikin rudewa yace"daddy sun sace mun ita wallahi sun tafi da IKLAS"


Daddy cikin rashin fahimta yace"su waye kuma saboda me?"




Yace"abida ne wallahi Abba dan Allah ka taimake ni"




Abu kamar wasa har akayi kwana biyar ba a gan IKLAS ba yan sanda ma suyi cigiya shiru Wanda sanadiyar haka aka kama Abida amma duk horo da akayi mata ansa d'aya ce batasan inda IKLAS take ba


RAYHAN ko abinci baya ci ko magana ba yayi said dai ya zauna kamar sabon kamu yayi ta magana yana cewa miyasa zaki yi mun haka?ki taimaka ki dawo gareni matata"


A yau a kayi kwana shida da b'atan IKLAS kuma gone ne shari'a,bikin minal kuma saura kwana shida,amm ba Wanda ya bi kan bikin


Zaliha ma kullum cikin kuka tace"da na sani da ban zo ba,laifi na ne wallahi"


Mamy ko hawan jinin ta San da ya tashi dan yanzu haka tana kwance a asibiti


Minal ne zaune tana tunani tace"dole ne IKLAS taje kotu gobe amma kafin haka ta faru dole nayi tunani irin nasu"


Mahmud ne ya fad'o mata a rai tace"yes shi kad'ai ne zai taimaka min tunda yanzu ya shiryu kuma nasan zai San inda take dan dashi aka had'a baki akayi mata sharri a Lagos


Tashi tayi ta d'au wayar ta bata fi


Bayan awa d'aya sai ga minal na magana da Mahmud


Tace"..........














Maman
, noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share


[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we the best among the rest.




πŸ…Ώ6⃣9⃣&7⃣0⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Minal ta kalli Mahmud dake zaune a wheel chair tace" an fa sace IKLAS"


Yace"what garin yaya?"


Nan ta kwashe komai ta fad'a me


Yace"wanan gaskiya ne dan abida ita kashe nuratu"


Minal tace"toh ya zayi yanzu"


Yace"bari in kira mai yin bincike yazo shi zai gaya mana mafita dan dolene IKLAS taje kotu gobe"


Bangaren IKLAS kuwa sun d'aure ta a wani daki da k'yar suke bata abinci tana ci ga zazzabi da ke damun ta"


Tunanin ta d'aya shine wani hali mijin ta ke ciki da tasan bashi da juriya abu kad'an ke sashi kuka a tace"Allah sarki mijina"


Bayan awa biyu yaron Mahmud mai bincike yazo


Mahmud yace"an gano inda aka kaita?"


Yace"eh mai gida tana bayan gari"


Minal tace"toh miye mafita kenan ko mu sanar da yan sands"


Yace"ah'ah bana jin haka mafitane domin ina zargin akwai d'an sanda mai yi musu aiki zai iya sanar da su kuma haka zai iya sa su kashe ta"


Mahmud yace"toh miye mafita ne?"


Yace"mafita d'aya ne a had'a baki da d'aya daga cikin su in akwai Wanda ka yarda dashi"


Mahmud yace"akwai"


Da sauri minal tace"waya?"


Yace"babsy"waya rshi ya d'auko ya kira shi yace"babsy ya dai "


Babsy yace"lafiya oga ka guje mu"


Mahmud ya mu hadu a guest house d'ina yanzu amma ban son kowa ya sani"


Yace"toh gani nan tahowa"


Bayan minti talatin babsy ya taho,nan dai suka gaya mai komai


Babsy yace"nawa za a bani"


Mahmud ya bashi cheque yace" ka cika ko nawa kake so kud'i ba Matsala bane"




Karba yayi yace"mafita d'aya ne"


Minal tace"muna jinka"


Yace"shine ki maye gurbin ya gobe ni zan San inda zanyi infito da ita ke kuka ki zauna a madadin ta dan ta samu zuwa kotu"


Mahmud yace"no baza mu sa ta a had'ari ba"


Babsy yace"toh gaskiya babu wata mafita sai wanan"


Minal tace"zan iya"


Mahmud yace"no kiyi tunani aure ki saura kwana shida"


Tace"mahmud IKLAS na bukatar taimako dan ciki ne da ita gashi ba lafiya da kagan halin da mijinta ke ciki da ka tausaya me"


Mahmud yace"ya kamata ki sanar da mijin kin"


Tace"no in na sanar da shi ba zai bari in je"


Kallonta babsy yayi yace"gobe kifito karfe 9:am




Haka kuwa akayi gari na wayewa minal ta shirya ta fita titi babsy ya dauketa zubawa su mugu maganin barci a abin sha,sai barci suke,


Suna isa suka tarar dasu suna barci a hankali babsy ya bude d'akin da IKLAS take


IKLAS na ganin minal tana so tayi magana babsy ya yasar shi a baki shhhhhhhhh




Shiru tayi da Sauri ya kwace ta yace"koyi sauri Ku canja kayar jikin Ku"fita yayi ya basu wuri cikin mintu biya suka sauya kayar su


IKLAS tace"minal me kike yi a nan"


Minal tace"ba lokacin bayani,kije ki tsayawa mutanen da aka zalunta a kotu saura minti 40 a zauna


Tace"ba in zani in da gaske ne mu gudu tare mana tunda sunyi barci"


Minal tace"da mun gudu zasu kashe zaliha dan tun jiya ba ganta ba kije ba lokaci"


Babsy ne ya shigo yace"muje in raka ki akwai mota a waje da zai kaiki kotu Islam zata same ki a kotu da kaya"


Kallon minal tayi tace"toh ita ya zayi da ita?"


Yace"da angama shari'a zan samo hanya kubutar da ita,Allah yasa karsu gane bake bane dan insu gane akwai matsala, amma minal bazan d'aure ki sosai ba incase in an samu matsala ki kare kanji,in kun ji shiru bayan shari"'a Ku zo da yan sands"




Rungumeta Minal tayi tace"in na mutu ki ce wa Abdul da iyaye na su yafe mun"


Kuka IKLAS tayi tace"gaskiya bazan iya barin ki a nan ba"


Babsy yace "mu je ba lokaci" da k'yar Minal tayi da IKLAS ta bi babsy


'Bangare RAYHAN ko














Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah




🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ7⃣1⃣&7⃣2⃣


Bismillahir Ramanir Rahim


'Bangaren RAYHAN ko sai abin da ya karu dan wuni yake yi yana kira sunan IKLAS nawal ma sai kuka take


Misallin karfe 9:40 IKLAS ta isa kotu sai dai bata da karfin jiki


Tana fitowa a kotu Islam ta karaso ta rungumeta


IKLAS tace"in mijina yake?"


Tace"yana gida ba lafiya"


Tace"kira shi ki ce ina nan"


Mahmud ne yayi gyran murya,sai a sanan ta lura dashi


Fad'iwar gaba had'e da mamaki ne ya kamata na ganin shi a keken guragu


Yace"ya jikin?"ko kallonshi batayi ba yace"ya kamata ki je ki shirya shari'a saura minti goma"


Kallon Islam tayi tace" meya had'a ki da wanan"


Murmushi Islam tayi ta bata labarin komai


Cikin jin kuya da nadama mahmud ya kalleta yace"ki yafe mun nasan nayi miki ba dai dai ba,kuma nayi miki alkawari ceto rayuwar minal yanzu ma nasa aje a nimo zaliha"


Tace"na yafe ma,Islam kirashi please"kiran RAYHAN Islam tayi ta fad'a me IKLAS na kotu


Ai da sauri ya tashi dan dama yana zaune ne a kasa yace"Allah nagode ma yace"ai babu shari'a da zatayi bana son in rasa ki kema"


A gurguje ta shirya cikin kayarta na lauyoyi


Ta fito tana shiga dai-dai alkali na cewa ina lauyan mai kara?"


Dariya Abida tayi a ranta tace"ai tana nan naure"


Jin muryan IKLAS tayi tace"gani ya mai shari'a"


Ai nan take gaban ta ya fad'i kallon Mahmud tayi ya sakar mata murmushi


IKLAS na shigowa bada dadewa ba yaron Mahmud ya shigo da zaliha


Ai abida na ganin zaliha hakalin ta ya tashi


Tashi IKLAS tayi zatayi magana kwai sai taji muryar Abida


Tace"na ansa laifi na na kashe nuratu da zainab"


Kallonta alkali yayi ya tambaye ta sau uku tace"eh ta aikaita laifinta"


Nan dai alkali yayi gyran murya yace"Abida nasir ta amsa lai fin kissa wato kashe nuratu da zainab bisa wanan dalili wanan kotu ma adalci ta Yankewa Abida nasir hukunci kisa ta hanyar rataya"




Kukar nadama ta fashe dashi dai-dai nan RAYHAN da abdul suka shigo shigo


Nan police suka tafi da Abida


Da gudu RAYHAN ya zo ya rungumeta itama rungume shi tayi domin dama anga zamar kotu


Abokin Mahmud ne ya karaso dashi kusa dasu


Kallonsu IKLAS tayi tace"ina minal?"


Abdul yace wata minal?"


Shima RAYHAN kallonta yayi nan dai kwashe komai ta sanar da su cikin tashin hankali Abdul yace"ina ne wajen?"


Mahmud yace"bari a sanar da yan sanda"


Kafin suyi.magana Abdul ya tafi ya barsu da gudu RAYHAN ya bishi itama IKLAS da Islam binsu sukayi Wanda da k'yar take tafiya


Mahmud shi kad'ai aka barshi dan ya aiki yaronshi wake


Har da zaliha ta fara tafiya sai ta juyo ta kalleshi dawowa tayi ta taimaka me suka fito


'Bangaren Mugu ko kiranshi aka yi aka sanar dashi an yanke wa Abida hukuncin kisa ta hanya rataya


Yace"what?ta ya haka ta faru?"


Police d'in yace"ai barrister IKLAS ta zo kotu kuma abida da kanta ta ansa laifinta"


Yace"ban gane ta zo kotu"


Tashi yayi yaje d'akin da suka boye IKLAS dan tun safe bai ba leka ba"


Yana shiga yaga minal zaune,karasawa yayi ya d'aga mata fuska ganin fuskar minal yace"nasan wanan aikin babsy ne"


Fita yayi ya kalli babsy cikin rashin gaskiya babsy yace"oga ya dai?"


Ba tare da yayi magana ba ya halbe shi a kafa yace" ni zaka yaudara gashi sanadiyar ka an kashe mun masoyiya"


Kallonshi tayi yace"ku kuna gidan nan dasu a ciki"


Suka ce"toh oga"


Bude gas suka yi suna fita suka sa ashana,nan take gidan ya fara konewa


Abdul ne yana tuki kamar zai tashi sama dan shi bai jira yan sanda ba


Su IKLAS ne a police station RAYHAN yace"he gida ki jira mu kinga baki da lafiya ko"


Tace"ni bazan iya ba muje tare sanadiyata minal ke cikin wanan halin"


Ba dan ya so ba yace"toh muje"mota d'aya suka shiga da Islam,yan sanda kuma nabin su a baya"


Suna isa suka tarar da Abdul zaune a kasa idanun shi sun yi jajur,ga gidan ya kone kurumus


IKLAS ta fashe da kuka tace"wallahi nan ne gidan Allah yasa basu kasheta ba"


A fusace Abdul yace"ba abinda ya sameta"


Yan sands suka ce"......




































Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟




🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ7⃣3⃣&7⃣4⃣


Bismillahir Rahmani Rahim


Yanda suka CE"bari mu kira fire service a kashe wutan"ba tare da b'ata lokaci ba sai ga fire service sun iso


Bayan sun kashe wuta,suka shiga cikin gidan da kone kurmus


Shigarsu da minti ashiri sai gashi sun fito da gawa


IKLAS na ganin gawa saki wani mugun kara dan duk a zaton ta minal ne


Tace"shikenan sun kashe minal"


A zabure Abdul ya tashi yace"ke kiwa mutane shiru minal bata mutu ba"


Kafin fire service suyi magana IKLAS ta dafe ciki tana ihu,jinine ya fara bin kafarta


Cikin tashin hankali RAYHAN ya saki Abdaul dan dama ya rike tun kan fire service sun zo,dan cewa yayi shiga zaiyi shima wutan ya kashe


Zuwa yayi ya rike ta yace"wiffy menene?"


Tace"cikina,mutuwa zanyi ka taimake ni"da Sauri ya sakata mota ya zaga ya zauna,ko ta kan Islam bai bi ba dake faman cewa"yaya jira ni"


Direct asibiti ya kaita,da sauri Dr suka fara aikin su sai dai cikin ya riga ya zube


Kallon Abdul police sukayi d'aya daga cikin su yace" mun duba ko ina bamu gan gawarta ba sai na wanan"


Islam ta fashe da kuka tace"kila ta kone kena kurumu........"maganan ta makale ne sakamakon mari da Abdul yayi mata


Yace"wallahi in kika kuskura kika kara cewa minal ta mutu sai na hallaka ki"


Cikin b'acin rai ya shiga mota ya ja kamar zai tashi sama yana tuki yana magana yana cewa"minal meyasa kika yi mun haka?miyasa baki nimi shawarata ba?please ki dawo ko masifa ne kiyi mun ki taimaki rayuwata bazan iya rayuwa babu ke ba"


Parking yayi a gefen titi ya samu gefen titi ya zauna gindi wani bishiya'


RAYHAN ne gaban Dr yace"Dr ya ake ciki ne yanzu?"


Dr yace"jikin da sauki sai dai tayi b'ari cikin ya zube sakamako wani abu da ta ji ko gani ya firgita ta kuma tana zama da yunwa kamar kuma bata samun barcin kirki"


RAYHAN a ranshi yace"dama tana da ciki ne?no wonder"a fili kuma yace"eh dr hakane"


Cikin damuwa yace"Dr zan iya ganin ta?"


Yace"eh amma kar a tashe ta"


Yana fitowa ya kira ummi da mamy ya fad'a musu halin da ake ciki


Shiga d'akin yayi ya ganta kwance kamar mai barci hawaye nabin kunne ta


Zuwa yayi ya kwanta kusa da ita ya shafa cikin ta


Tana jin shi kusa da ita ga kuma hanun shi a cikin ta ai sai ta saki kuka mai cin rai


Juyo da ita yayi suna fuskarta juna sai dai idon ta rufe


Yace"wiffy bude idon ki kalle ni" babu musu ta bude


Yace"meyasa kike kuka?kina so nima nayi ne?" Girgiza kanta yayi alamun a'a


Yace"kema ki san bani da wuyan kuka,iam too emotional balle nagan ki kina kuka zuciyata zafi take yi"


Kuka ta fashe da shi yace"ya salam,toh menene"


Cikin kuka tace"baby mun ya tafi ya barmu"


Rungumeta yayi yace"karki damu wiffy Allah zai bamu wani,Allah bai nufi zaizo duniya ba,da kin samu wani zan baki wani kema kinsan bana wasa"ai batasan sanda dariya ya subuce mata ba


Kashe mata ido yayi yace"da kin farfado zan fara aiki"


Kallonshi tayi ta kara fashewa da kuka tace"ina minal ta mutu ko"


Yace"a'aba a tabbatar ba dan babu alamun gawanta a nan,yanzu ma zan je in same abdul "


Suna cikin magana ummi ta turo kofa da sauri ya mike ganin mamy tare da ita


Bayan sun gaisa yayi wa mamy ya jiki ummi tace"yariyar nan ta cuce mu,yanzu ya magana minal"


Yace"yanzu wurin Abdul zan je kuma yan sanda sunyi nasara kama mugu da yaranshi"


Yana fita ya kira Abdul yace"ina kake"jin shiru ya sake cewa hello"karshe ma Abdul ya sinke kiran


Sultan ne zaune a asibitin bye-bye pass yace"bari in kira Abdul"


Kiran Abdul yayi yace"hello!hello kana jina"


Abdul yace"uhrmmm"


Sultan yace"Abdul ka fad'awa kawayen amare ba zan samu zuwa yau ba ina asibiti da nake zuwa naga wata gefen titi a sume shine na taimaka mata yanzu ina asibiti amma da ta farfado zan shigo"


Jin shiru yasa yace"hello kana jina?"


Yace"eh"


Sultan yace"tana ji murya ka haka?"


Abdul yace"ba a ga minal ba"


Sultan yace"ban gane ba"nan ya kwashe komai ya fad'a mashi


Sultan yace"toh ko ta mutu ne"


Abdul yace"no ina ji a jiki na minal na raye"


Kallon minal dake kwance a gadon asibiti sultan yayi a ransh yace"ko dai ita ne?bari ta farfado in tambayeta"




Abu kamar wasa anyi kwana uku ba gan minal,cikin kwana uku nan Abdul ya rame yayi baki,umma minal ko kullum cikin kuka


IKLAS ko tashiga tashin hankali sosai,Mahmud yace"laifi nane dana bari ta je dan yanzu sun bala'in shakuwa da zaliha


Yau likita ya sallami IKLAS a asibiti suka dawo gida


'Bangaren sultan ko misallin karfe 4:pm tana zaune a kujera minal ta farka


Tana farkawa tace.....


















Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ7⃣5⃣&7⃣6⃣


Bismillahi Rahmanir Rahim


Minal na farfadowa ta fara kallon wuri,sultan ma kallonta yake


Tace"ina nike?"


Yace"a gefen titi na gan ki a sume,na kawo ki asibiti yau kwanan ki uku"


Zaro ido tayi a hankali ta fara tuna komai da ya faru


Yace"bari in kira likita"


Likita na zuwa ya duba ta allura yayi mata ya fita


Kallonta sultan yayi yace"ki kira gida a san halin da kike ciki"


Tace"ba waya hanun na"


Yace"kin san noba wani a kanki?"


Tace"eh"waya ya ciro yace"kira inji"


Nan ta fara kiran noban Abdul,yana dialling ya ga sunan Abdul ya fito kallonta yayi


Yace"minal ko?"


Cikin mamaki tace"eh ya akayi kasan suna na ne?"


Yace"ai ni cousin brother Abdul ne bikin Ku ma zani na gan ki,nine Wanda kawaye ke jira"


Tace"sultan ko"


Cigaba yayi da kiran Abdul amma yaki d'agawa


Abdul da ke kwance ba lafiya ya duba wayar yana ganin sunan sultan yace"wanan sarkin surutu,zai dame ni"


Sultan yace"bai d'aga ba"


Tace"toh kira wanan,kiran noba ummata tayi sai dai shima har ya katse bata d'auka ba"


Yace"shima ba a d'aga ba"


Na IKLAS ta bashi amma noban be je ba"


Tace"please kira wanan na karshen inba sai in hakura"


Islam dake zaune kusa da IKLAS tun dawowan su daga hospital IKLAS ke kuka tana kiran sunan minal Islam itama zaliha kuka takeyi tana cewa"laifi nane"


Islam zatayi magana wayarta yayi kara tana d'agawa sultan yayi ajiyar zuciya


Tace"hello!"jire wayar yayi a kunne ya kalla ya kuma maidaw


Yace"hello"itako Islam sanda ta dafe kirjin ta dan wani bugu zuciyarta ya farayi da Sauri


Mikawa minal wayar yayi dan haka kawai yaji baya da kuzarin magana da ita


Minal tace"hello"Islam na jin muryarta ta mike tsaye tace"minal dama kina raye?"


IKLAS na jin an kira sunan minal ta kwace wayar batayi magana ba ta saki kuka




Minal tace"meya same ki sunyi miki wani abune"


IKLAS tace"please karki kara tafiya ki barni nayi kewar ki,Abdul kamar zaiyi hauka yanzu ma fushi yake da kowa"


Minal ma hawayen takeyi tace"ku zo ku d'auke ni ina asibiti"


Da sauri IKLAS ta saka hijabi Islam tace"ina zaki ke da baki da lafiya"


Kafin tayi magana RAYHAN ya sauko yace"meke faruwa ne?kuma ina zaki?"


Tace"minal ta kira wai tana asibiti"


Yace"alhamdullilah bari inki kira Abdul mu had'u a asibiti"


Sanda ya kira Abdul sau biyu bai d'auka ba a a na ukun ya d'aga


Yace"kai baban soyyaya ai sai ka tashi muje mu d'auko minal a asibiti daga yau zaman takaba ya kare"


Da sauri Abdul ya mike yace"da gaske an ganta?"


Yace"eh yanzu ta kira Islam wai sun kira ka baka d'aga ba"wani uban yayi,Wanda RAYHAN ya cire wayar a kunna yace"kar a fasa mun kunne"


Kiran ummi Abdul yayi ya gaya mata an gan minal


Cikin murna tace"toh sai kun dawo"kicin ta shiga ta fara had'a abincin mai lafiya dan ba karya tana ji da minal kasancewar ita kad'ai ta Haifa


Lokaci d'aya suka isa asibiti RAYHAN yace"har ka iso"


Abdul yace"ba dole ba"


Suna shiga IKLAS ta ruga da gudu ta rungume minal


Abun mamaki ina sanmani ganin Abdul yana farin ciki sai na gan ya tamke fuska kamar Wanda bai tab'a dariya ba"


RAYHAN ko gaisawa yayi da sultan


Islam ko ta rakube a gefe d ya dan wani irin kallo da sultan keyi mata


Abdul na karasowa kusa da minal ya..........












Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah






🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writer,we are the best among the rest.




πŸ…Ώ7⃣7⃣&7⃣8⃣


Bismillahir Ramanir Rahim


Yana karasowa ya sinka mata lafiyyayen mari,rike wurin tayi tana hawaye


Yace"me kike tunani?bakiyi tunanin halin da zan shiga ba ko umma ki,ki san irin tashin hankalin dana shiga"


Cikin kuka da zafin marin da yayi mata tace"yi hakuri naga babu lokaci ne kuma ina tausayin IKLAS dan na lura a lokacin tana da ciki shiyasa"


Yace"ni na hanaki taimako ta ne?amma miyasa

Please Login or Register in order to submit comment