Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

ο»ΏπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah




🌟GORGEOUS WRITERS FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.


Dedicated to my fans


πŸ…Ώ1⃣&2⃣


Bismillahir rahmanir rahim


"IKLAS!lKLAS!!IKLAS!!!" buga table minal tayi ganin ta kira ta sau uku bata jiba dan tayi nisa cikin tunani wanda inda sabo ta saba ganin ta haka


A firgice ta kalleta tace"lafiya kike kira na haka?har kin saurata ni"


Minal tace"ai sai ki tashi mu tafi gida an tashi islammiyar ai"


Tashi tayi ta dauki jakar ta tace"muje toh yar bakin ciki kullum sai ina tunanin masoyina zaki wani zo kiyi ta damuna"


Minal tace"lallai IKLAS anyi wahalliya ke yanzu bazaki shafawa kanki lafiya ki daina wahalar da kanki ba?be ma san kina yi ba,ke ma baki san shi ba muryashi kawai kike ji amma kin hana kanki sukuni saboda wanda be san da zaman ki ba,wallahi ki yiwa kanki fad'a waya san ma ko yana da mata"


Kallonta IKLAS tayi tace" wallahi ko matan shi uku nine cikon na hudu wallahi zan iya aure shi ya rigada ya sace zuciyata tun ranar farko da nafara jin muryashi a radio alheri fm na kamu da son shi kuma ina jin dad'in inda yake bama masoya shawara a daddalin masoya wallahi bana jin zan iya cire soyayya R M D,a zuciyata dan ya rigada ya zama jinin jikina"ta kare maganan tana hawaye


Minal tace"ikon Allah,toh Allah ya kyauta"


Tafiya suke suna hira wanda rabe maganar R M D ne


Rabi tace"inda zaki bi shawara na da kin hakura da wanan makauniyar soyyaya ki fara kula mahmud naga shima yana son ki"


IKLAS tace"Allah ya kiyaye na auri d'an iska wanda baya kamun kai da bin mata,gaskiya minal in kina son muci gaba da zumunci pls ki daina kawo min maganan mahmud"


Minal tace"Allah ya baki hakuri"


Dai-dai nan suka kawo kofan gidansu minal


Minal tace"sai mun had'u gobe kenan ko?"


Ko kallonta batayi ba ta yi tafiyar ta,ta bar minal tsaya da baki bude


Minal tace"IKLAS ba a son gaskiya yanzu haka fushi tayi"


IKLAS na shiga cikin gidasu wow!!!nace ganin kyau da tsaruwa gidan direct part din mamy ta shiga ta gaishe ta


Cikin kulawa mamy tace"oh har kin dawo?


Tace"eh mamy sannu da gida,mamy daddy ya dawo ne ko?"


Mamy tace"a'a be dawo ba"


Toh bari inje ciki in yi wanka da sallah mangaruba kafin ya dawo"


Hadeddiya bedroom d'inta ta shiga wanda aka yiwa decoration da komai orange colour


Wanka tayi hade da alwala tafito gown ta saka da hijabi ta gabatar da sallah mangaruba


Bayan ta idar kawanta maryam ta tura kofa tace"ki zo in ji daddy muyi dinner"


Tashi tayi tana murna ta fito tana saukowa direct dinning taje ta zauna


tace"daddy nayi fushi da kai baka dawo da wuri ba"tayi maganan cikin shagwaba


Daddy yace"yi hakuri yar baba wallahy na tsaya wani meeting ne nida alhaji Mohammed shiyasa na dade"toro baki tayi tace "gaskiya ni nayi fushi da kai"


Mamy tace "gaskiya alhaji ka daina shagwaba yarinyar na,ka tuna fa macece kuma wata rana aure zatayi"


Ko kula mamy beyi ba yace"yar baba na zo miki da wata kyauta kuma nasan da kin gani zaki yafe mun laifi na"


Dariya tayi tace"menene Abba?"sabon radio ya ciro a leda


Yace"gashi latest ne nasan zaki ji dadin jin labarai da shi tana kama ko wace tasha"dan shi a tunanin shi labarai take ji da radio


Ihu murna ta saka tace"nagode abba na Allah ya barmun kai"


Yace"amin"


Maryam ko kallonsu take cikin takaici ta girgiza kai


Abincin sukaci bayan sun gama mai aiki tayi clearing table


IKLAS ko d'akinta ta koma ta kunna radio tsaki tayi ganin ba fara daddalin masoya ba


Missalin karfe 7:40pm ya gama shirin shi na zuwa FM dan 8:pm yake fara program


Islam ne ta shigo d'akin dai-dai yana saka wani abu abaki,ko miye ohoπŸ™„


Islam tace"yaya wai dole ne sai ka saka wanan abun a baki in zaka FM ne?"


Dariya yayi yace"bazaki gane bane ai bana son abba ya gane nine R M D shiyasa nike basaja wanan abun da kike gani shike canja min murya"


Tace"gaskiya kayi dabara"


Kallonta yayi yace"ki kula da nawal"


Tana idar da sallah mangaruba ta kunna radio dai-dai nan aka fara daddalin masoya


Ji nayi ance a radio"asalamu alaikum masu saurare barkan mu da sake saduwa a wanan filin na daddalin masoya


Kamar inda kuka sani sunana R M D kamar inda muka saba yanzu zamu bude hotlines dan sauraren matsololin ku na soyyaya"


Lumshe ido tayi ta bude da Sauri ta d'auki waya tayi dialling number


Hello!hello!!hello!!!shiru tayi sai lumshe ido takeyi


Gajiya yayi yace"as usual first caller d'in basa magana"


Haka ta cigaba da jin FM har barci yayi awon gaba da ita




Washe gari








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.


Dedicate to Nana Khadija


πŸ…Ώ3⃣&4⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim


Washe gari misalin 7:am IKLAS ne cikin atampa Riga da skirt tayi bala'in yin kyau sai a sanan na kare mata kallo




IKLAS karshe ne wajen kyau dan in ba kasan asalin ta ba ka d'auka balarabiya ce


Fara ce sol ga ta da suma da hanci mai sini sai maidaidaicin baki tana da hips da boobs ba over ba da flat tummy tana da kiba madaidaici dan baza a kira ta siririya ba tana da tsayi dan baza a kira ta gajeruwa ba


Tana gama shiryawa ta fito ta samesu daddy a dinning maryam cikin secondary school unifoam


Daddy na ganinta yace"yar baba har kin shirya?"


Toro baki tayi tace"eh Abba gashi har yanzu ba a dawo mun da mota ba,gaskiya daddy ya kamata a canja mun mota wanan ta fara bani Matsala"


Yace"inshaallah allahu inda kika ce haka za a yi"


Kallon su mamy tayi tace"haba du-du wata nawa da canja mata mota ko wata biyar beyi ba shine kake maganar canja mata mota,wallahi alhaji gaba zaka duba dan bamu San hanun da zata Shiga ba tun da macece kuma aure zata yi"


Cikin halin ko in kula yace"karki damu,ina ce damuwar ki mijin da daza ta aura ne?toh ni zan mata mijin irin mijin da bazata wahala ba"


Murmushi IKLAS tayi tace"tanks dad


Itako maryam ko kallon su bata yi ba abincin ta take ci hankali kwance


IKLAS na gama cin abinci tace"Abba na gama zan tafi makaranta sai nadawo"


Yace"toh tsaya in sauke ki mana daga nan in tafi office"


Tace"toh dad"


Mamy ta yiwa sallama suka bar falon


Suna kaiwa gate d'in makaranta IKLAS ta fita a mota tana yiwa Abba


Yace"karfe nawa zaki gama lecture Nazi na d'auke ki?


Tace"no karka damu dad zan dawo a mota amira"


Yace"ok"


Sanda ta gan tafiyar shi ta juya tayi cikin makaranta


Tana shiga wani saurayi ya duro a mota sai gaban ta


Wani wawan kallo tayime kafin tace"mahmud ka fita harka ta wai me yasa ka fiya naci ne?


Yace"wallahi bazan fita ba in kin ga haka ta faru toh mutuwa nayi ko ke kika mutu amma muddin dukan mu biyu muna da rai toh wallahi baki isa ki auri wani ba"


Tsaki tayi ta ratsa shi tayi tafiyar ta aji ta barshi tsaye


Bayan ta gama lectures ta fito sai niman minal take amma bata gan ta ba can ta hango wata yar aji su tambayar ta tayi nan take sanar da ita minal bata zo ba yau


Tsaki tayi tace"bari in je in shiga taxi"


Gefen titi ta tsaya sai ga wani zukekiyar mota tazo ta pesa mata ruwan gaban ta kasancewar a damina ake


Cikin b'acin rai ta kalli motan dan duo ya b'ata mata kaya sai ta gan yayi parking gaban gate


Ai da Sauri ta karasa wajen shi ta buga glass da kamar beze fito ba sai kawai yafito da gongoni climax a hanun


Wow!!!nace ganin kyaun shi dogo ne yana da kiba amma ba sosai ba shi ba baki shi ba fari he is just perfect sai dai abin da baza a ratsa ba kasancewar mutum tara yake be kai goma ba


Tace"Malam wanan wani irin wulakanci ne"


Kallon ta yayi sama da kasa ya wasa mata climax din hanun shi ba tare da yayi magana ba


Cikin kuna rai tace"ya ishe ka haka mugu azalumi wanda ba san darajar d'an adam ba"


Idon ta ne ya hango mata wasu budurwa da saurayi suna cin abinci a wani gindin bishiya da exotic babban gora a gaban su ba tare da bata lokaci ba taje gaban su ko magana bata yi ba ta d'auke kwalin exotic


Dagudu ta zo gaban shi ta kwara me ai sai mutanen wajen suka fara yi me dariya bata tsaya wata-wata ta ruga a guje tana maida numfashi


Cikin b'acin rai ya koma mota tare da alwashi din inda ya gan ta sai ya ci mata mutunci


Wacece IKLAS?


IKLAS umar faruk cikeken sunan ta ya' ce ga alhaji umar faruk mai gwal cikaken bafulatani Adamawa zama ne ya da kasuwanci ya kawo su Niger state dan yana da shagunan gulagulai a cikin kasuwan minna


su biyu iyayen su suka haifa daga ita sai kawanta maryam hajiya balkisu ita ce mahaifiyar su


IKLAS ta taso ne cikin gata most especially wajen mahaifinta wanda ya shgwab'a ta kasancewar sanda suka yi shekara goma kafin su sami haihuwarta bayan ita kuma sanda sukai shekara tara kafin su samu haihuwar maryam


IKLAS yariya ce me matukar sanyi da son jama'a duk da gatan da take samu wajen iyayenta besa ta sangarce ba,ga ladabi da biyyaya


Wanda a yanzu tana final year a jami'a tana karanta law ita kuma maryam secondary school ss (1)


IKLAS tana da shekara ashirin da hudu a duniya maryam kuma sha biyar


A shekaru uku da suka wuce ne IKLAS ta kamu da soyyaya wani mai gabatar da shirin dandaalin masoya a gidan radio Alheri FM wanda ba wanda yasan da zance sai babban aminiyarta minal




Dan koshi wanda takeyi so be ma San da ita ba


Bata taba ganin shi ba muryar shi kawai take ji dan ji take yi in ba ta aure shi ba zata iya rasa rainta


Gefe d'aya kuma Mahmud d'an senator ne rikeke d'an iska noba d'aya Mahmud bashi da tarbiyya ko kad'an tunda ya had'a ido da IKLAS ya sha alwashi ko ta halin ka'ka sai ya aureta in kuma be samu ya aureta ba sai ya d'and'ani zuman ta ko ta karfi ne lokaci kawai yake jira


Cigaban labari








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITER FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ5⃣&6⃣


Bimillahi Rahmani Rahim


Mota ya shiga ya zauna ran shi na kuna dan tunda yake ba taba wulakanta shi ba sai yau


Islam ne ta shigo motar tana dariya tace"yaya har ka iso?"


Kallonta yayi rai b'ece yace"bani son surutu"


Shiru tayi dan ta sorata da yanayin shi


"Bagaren IKLAS kuwa tana isa gida tayi sallah ta kunna radio


A fili tace"wai shi R M D baya program ne sai da dadadare I miss his voice"tsaki tayi ta kwanta barci yayi awan gaba da ita cike da kewar muryar R M D kasancewar yau alhamis babu islamiya


Misalin karfe 6:30 na yamma daddy ya shigo falon da sallama


Mamy ta amsa tace" Abba yara sannu da zuwa,ruwa taba shi yasha


Bayan ya gama shan ruwan


Ya kalle mamy da ke tsaye yace"balkisu zauna zamuyi magana ne"


Zama tayi tace"toh ina ji Abba yara"


Yace"dama akan maganar yariyar nan ne IKLAS na yanke hukunci had'a ta aure da d'an amini na alhaji Mohammed wato RAYHAN inshaallahu nan da sati biyar za a yi bikin nasan kafin lokacin ta gama jarabawa ta tunda befi sati uku su gama ba"


Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah ya sanya albarka Abba yara"


Yace"amin ina yar baba take ne?"


Mamy tace"ta na d'aki tana barci"


Yace"amma na fad'a miki ki daina bari yaran nan suna barci har mangrib ko"


Tace"yi hakuri yanzu zan tashe ta maryam na baya tana wanki a machine


Bayan mamy ta tashe ta tace"ki zo daddy ki na niman ki"


Da Sauri ta tashi ta shiga bathroom tayi brush ta sauko ta zauna kusa da shi sai shagwab'a take zuba me


Kallonta yayi yace"IKLAS"


Da sauri ta kalleshi dan in taji ya kira sunan ta toh magana mai muhimmanci ne


Tace"na'am daddy na"


Yace"wani alfarma nike nima a gun ki nasan ki da biyyaya ina fatan wanan karon ma zakiyi mun biyyaya da kika saba"


Tace"daddy inshaallahu zan kasance mai biyyaya a ko wani lokaci ka wuci alfarma ka nimi alfarma a guna umarni kawai zaka bani"


Yace"toh madallah yar baba na yanke auren ki nan da wata biyar da d'an amini na RAYHAN"


Ji maganan kamar saukan guduma cikin dakiya tace"Allah ya tabbatar ma na da alheri"


Cikin jin dadi daddy yace"Allah ya miki albarka,inda kika yi mana biyyaya Allah ya baki zuri'a da zasu yi miki biyyaya,Allah yasa ki gama da duniya lafiya"


Tace"amin daddy bari inje inyi sallah mangrib"


Yace"toh yar baba"


Tana shiga d'akinta ta kwanta ta saki wani kuka mai cin rai surutai take tanacewa"shikenan an rabani da kai R M D meyasa daddy zai yi mun haka?"kuka take sosai daga karshe zazzabi mai zafi yayi mata mugun kamu


RAYHAN ne gaban iyayen shi Abba ya kalleshi


yace"Rayhan na ya na yanke aure ka nan da sati biyar"


Zaiyi magana Abba yayi saurin katse shi da cewa "umurni ne ba shawaran ka na niman ba"


Cikin jin dadi ummi tace"gaskiya nayi far in cikin wanan magana na kosa yaron nan yayi aure ko nawal ta samu soyyayar uwa, da dadin uwa data ratsa tun tana jinjira"


RAYHAN ko ji yake kamar yasa hanun a kai yayi ta ihu


A zuciyar shi yace"gaski da sake bana jin zan iya zama da mace bayan Nuratu,matata d'aya ce a duniya kuma Allah ya amshi rayuwarta


Bayan ita babu Wanda ya isa in ba shi wanan mtsayi"


Wanene RAYHAN


RAYHAN Mohammed D'ahiru cikaken sunan shi


Sunan mahaifinshi Alhaji Mohammed D'ahiru mai dala cikaken bahaushe ne d'an garin kano amma yana za a naija state yana kasuwanci canji dala(dollars)
Rayhan su biyu ne a wajen iyayen su Rayhan ne na farko sa Islam wanda a yanzu shekaran shi talatin da biyar ita kuma Islam ashirin da uku


Alhaji Mohammed yana da kamfonuni daban daban shi da alhaji umar babban amini shi wato daddy IKLAS dan ba iya kasuwanci suka tsaya ba


Rahyan ya taso yana matukan sha'awar aikin media dan haka yaso karanta mass com tare da abokin shi Abdul amma Abba shi yace be yarda ba sai sai sai ya karanta business administration dan kula da kasuwancin shi


Haka kuwa akayi bayan ya gama karatu a oxford university ya dawo Nigeria ya fara kula da kamfani abban shi


A na cikin haka ne ya had'u da wata ma'aikaciyar gidan radio mai gabatar da daddalin masoya


Bayan hud'uwan su da watani ya gabatar da ita a matsayin Wanda zai aura amma da k'yar Abba ya yadda wai shi na son ma'aikaciya


Sai dai inta amince zata ajiye aikin ta itako nuratu tace bata yarda ba dan ba dan kudi take aiki ba tana yi ne dan passion


Karshe dai Rayhan da ya ga alaman ba yadda Abba zaiyi ba it's kuma nuratu ta ki yarda da shading Abba shi


Sai kawai yace"su yi plan shi ya yarda bayan auren shi zata iya cigaba da aikin ta amma boye tunda ba gida d'aya za su zauna ba


Bayan bikin su nuratu ta cigaba da aikin ta amma ta canja sunan da take gabatarwa a daddalin zuwa R M D wato RAYHAN Mohammed D'ahiru


Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa ba karami son juna suke na har Allah ya bawa nuratu ciki


Bayan wata tara da samun cikin ta ranan wata talata da safe nuratu ta tashi da nakuda RAYHAN ya kaita asibiti


Suna zuwa suka tarar da Dr ABIDA ce a duty tsohuwan budurwan RAYHAN ne run suna oxford amma saboda bata da kamun kai yace ba zai iya aurenta ba


Dr Abida yar shekara talatin da d'aya a duniya kuwa ta sha alwasin in bata samu RAYHAN ba babu Wanda zai.same shi kuma zata iya kashe koma wacece da ta auri RAYHAN hmmm


Amma sai ta nuna me ana tare


Tana ganin RAYHAN ya shigo da nuratu tayi dariya mugunta tace"ban taba tunani komai zai zo mun da sauki haka ba


Fitowa tayi tace"RAYHAN ya kayi ne"kallonta yayi yace"wallahi matata ta ke nakuda tana cikin labour room


Tace"subhanallah bari in shiga in duba ta karka damu inshaallahu zata sauna lafiya


Bayan awa biyu ta fito da baby tace"ta haifi baby girl"


Murna a wajen RAYHAN kamar yayi rawa nan ya kira ummi ya Samar da ita


Kallon Abida yayi yace"toh ya nuratu take"


Tace"lafiya lau yanzu ma zan sallame Ku"


Bayan ta sallame su da kwana uku Allah yayi wa nuratu rasuwa


RAYHAN yayi kuka ya gaji ummi ne ta raine nasal Wanda yanzu shekaranta biyar kuma ga wayau bata da buri da yawuce daddy ta yayi aure dan ta samu mummy


Shiko RAYHAN mace inba nuratu ba to bata kai ya kalleta ba


Bayan ratsuwar nuratu da shekara biyu RAYHAN ya bude gidan radio alhari FM Wanda Abdul abokin shi ke kula da shi


Shikuma yana gabatar da shirin daddalin masoya da sunan da nuratu ke amfani dashi wato R M D amma na Wanda ya sani sai Islam
Kuma yana da kamfononi daban daban


Cigaban labari








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ7⃣&8⃣


Tashi RAYHAN yayi cike da tashin hankali ya shiga bedroom d'in shi ya kwanta


A fili yace"duk mace da ta yar da ta aureni tashiga uku dan sai na wulakanta ta irin wulakanci da sai ta nimi in sake ta da kanta wallahi


Islam ne ta shigo d'aki tace"yaya baza ka je FM bane yau?"


Tashi yayi yace"bari inje it will cheer me up iam in worry,


Ciro wanan abun yayi na baki ya saka


Islam tace"yaya wallahi muryar ka yafi dadi in baka saka wanan abun bakin ba,why not kayi ta using natural voice d'in ka sai kafi samun fans"


Zaro ido yayi yace"ke kin manta da halin Abba ne?in ya gane nike program d'in daddalin masoya hmmm sai na gane shayi ruwane"


Tace"yaya ka hakura mana tunda abba baya so"


Yace"wallahi sister ba zan iya ba abin da ya rage mun nike tuna nuratu kenan dan in ina yi sai naji kamar ina tare da ita ne"


"Bangaren IKLAS kuwa zazzabi ya mata mugun kamu yanzu ma da k'yar tayi tsalla isha'i ta jawo radio ta tafara sauraren daddalin masoya yau ma kamar kullum batayi magana ba har ya gaji ya yanke call d'in haka ta cigaba da ji FM har barci yayi gaba da ita


Washe gari ta shirya ta sauko sai dai bata da walwala


A makaranta ta had'u da minal tana ganin ta,ta rungume ta ta fashe da kuka


Minal tace"IKLAS me aka miki kike kuka haka?"


IKLAS tace"minal zan auri wani ba R M D ba,minal daddy yayi mun miji ji nake kamar zan mutu"


Tsaki minal tayi tace"ai yayi mun dai-dai dan ko yace ki fito da R M D ba sanin shi kikayi ba balle ya aure ki,ni naji kamar ance yana da mata dan ance shekaru biyar da suka wuce mace ne ke program d'in kuma mutane ke zargi Matan shi ne"


Kuka IKLAS ta sake tace"may be ba zai soni ba tunda yana da mata"


Minal tace"IKLAS ki dage da addu'a ki daure kiyi wa iyayen ki addu'a inshaallahu zaki ga dai-dai"


Bayan sati uku IKLAS ta gama jarabawan ta kuma biki ya rage sati biyu amma har yanzu basu had'u da ango ba ko waya be taba kiran ta ba"


Abba ne zaune a palour yace"Islam kira mun RAYHAN"


Bayan tafiyar ta sai gashi sun dawo tare


Zama yayi Abba yace"ya kamata Kaje gidan su yariyar nan Ku fahimci juna"


Gaban shine ya fadi dan shi gaskiya baya tunani zai iya zuwa gidan ko wace mace ba da sunan zance"


Abba ne ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya fad'a


Yace"da kai nike magana"


Yace"inshaallah gobe zani"


Abba yace"toh"


Nawal tace"dad nima zani wajen new mummy d'ina"


Hararar ta yayi yace je ki shirya muje kasuwa siyar teddy"


Tsalle tayi tace"toh daddy"


Ummi tace"Ku siyo mun irin wanan atampa kelle ta basu"


Minal ne zaune a falo mamy tana cewa"IKLAS yi sauri muje mu fito da anko dibi biki saura sati biyu amma a ce ba anko friends sai kira na suke"


Mamy tace"kema dai kye fad'i"


Minal tace"suma angon ina nan ina jiran su sai na ci musu tara for coming late"


Hijabi IKLAS ta saka tace"muje" ba dan ta so ba


Wani babban shago zanuwa suka shiga


Minal sai tsurutu take tana duba kaya


Itako IKLAS zama tayi a kujera tana fuskanta kofan shago


RAYHAN ne a wani shago yana tambayar su ko suna da zanin da ummi tace su siyo mata
A ka ce babu tsaki yayi yace"ummi ma sai tayi ta ma mutum aiken mata"


Kallon d'aya daga bodyguard din shi yayi dan sometimes kan yi yawo da su amma not always ya bashi kellen zani


Yace"je shagon can ka tambayo ko za a samu"yayi mishi nuni da shagon da su IKLAS ke ciki


Yana tsaye sai ga wani me yiwa Abba aiki a shagon su na cikin kasuwa tsayawa sukayi suna fira


Be lura da nawal bata kusa dasu ba sai fira su suke hankali kwance


IKLAS ne ta hango wata karamar yariya machine na son ya kwashe ta da gudu ta fito ta tureta suka fad'i tare kasancewar shagon na gab da titi


Yariyar ta gurje a hanun jini na fita


Mai machine ko sai mita ya kayi yana cewa"sai Ku kawo yara kasuwa baza Ku kula da su ba salon Ku jawowa mutane magana"dan shi a zaton shi yariyar tare suke da IKLAS




Tashi tayi ta d'auke ta,ta rungume tana cewa"ina maman ki?da wa kuke ne"




Nawal ko rungume ta tayi ko magana ba tayi dan ta tsorata sosai


IKLAS tace"muje in siya miki big teddy"tayi haka ne dan yariyar ta sake da ita sanan daga baya ta tambaye ta Inda zata sami maman ta


Barin gaban shago suka yi zuwa wani shagon teddy




Juyowa RAYHAN yayi ya kalli d'ayan bodyguard d'in yace"ina nawal"


Zare ido yayi yace"d'azu fa tana nan"


RAYHAN yace"what? kaji sakarai wallahi in wani abu ya sami nawal bazan yafe ma ba"


Niman nawal suka fara yi abu kamar wasa sai da suka kai awa biyu suna niman ta


dan bayan sun shiga shagon teddy nawal ta hango wani shago da ake sayar da kayar wasan yara


Tace sai IKLAS ta siya mata babu musu suka shiga sai jido mata takeyi amma da ta fara tambayar ta gidan su ko maman ta sai ta fashe da kuma


RAYHAN ko gajiya yayi da nimar ta ya sanar da yan sanda cikin kasuwa










Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ9⃣&1⃣0⃣


IKLAS ko gajiya tayi da ita, ta zaunar da ita shagon wata mai abinci,abinci ta siye mata ta fara feeding nata


Minal ma gajiya tayi da nimar IKLAS gashi in ta kira ta bata d'agawa tace"wai ina ta shiga ne"


Sai daga baya

Please Login or Register in order to submit comment