Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani had’add’en suit mai tsadar gaske.


Anutse ya saka boxer da singlet d’insa, kana cikin dan hanzarin kada ya makara ya shirya kansa cikin suit din nasa, mai kalan army green wanda yayi matukar yi masa kyau.


Cikar haibar kwalliyan nasa ya sake fitowa ne kuma, musamman daya saka takalmin sau ciki army green, da kuma agogon kamfanin Rolex ahannunsa.


Briefcase da kuma wayarsa ya d’auka, cikin takunsa na alfarma ya fita zuwa falon.


Dai-dai lokacin ne kuma delivery ya kawo masa ordern abincin da yayi.


Karb’an abincin yayi, tare da komawa Cikin falon ya zauna.


Bud’e ledan yayi tare da ciro takeaway d’aya ya bud’e, Kallon abincin dake cikin takeway din yayi, kana ahankali kuma ya d’ago da kansa ya kalli kofar d’akin nata.


Idanunsa ya dan zubawa kofar domin baiga alaman cewa an bud’eta ba, na yan wasu mintuna ya kalli kofar, lokaci daya kuma ya dauke kansa, tare da daukan spoon ya soma d’an tsakalan abincin dake gabansa.


Kwata kwata kuma bai wuce loma 4 yayi ba, ya ture takeway din gefe saboda har yanzu bawai yana wani jin dadin bakinsa bane Chocolate din daya ɗebo ya fara gutsara yana taunawa a hankali saida yaji ya ɗa koshi kana yaja ledan maganibsa.


Bayan yasha maganinsa ne kuma ya mik’e tsaye, still ya kuma Kallon kofar dakin nata, kamar wani wanda ke tsammatan wani abu, dai-dai lokacin kuma wayarsa dake cikin aljihunsa ta soma k’ara.


Zaro wayar daga cikin aljihun nasa yayi, Ganin da yayi sunan Abbansa na yawo akan screen din wayarne kuma ya sashi, picking call din tare da kara wayar akan kunnensa, cikin dan yanayin girmamawa yace.


“Assalamu Alaikum Abba Ina kwana.”


Daga can b’angaren Abba dake zaune akusa da Mamy, Jin muryar Rayyern din wasai ne ya sashi, Dan fadada murmushi kana cikin kulawa yace.


“Wa’alaikassalam, lafiya kalau Rayyern ya jikin naka?”


“Alhamdulillah Abba naji sauki sosai, Dan yanzu haka ma wajen aiki zan tafi.”


Rayyern din ya fada yana me janye idanunsa daga Kallon kofar dakin Jannart din.


Abba kuwa Ajiyar zuciya ya sauke, saboda ko daga sautin muryar Rayyern din, kasan Masha Allah yaji sauki.


Cikin jin dadin hakan kuwa yace.
“Masha Allah haka akeso ai, Allah ya kara maka lafiya, amma kada ka manta da shan magunguna akan lokaci, ina Jannart fatan tana lafiya?”


Idanunsa ya dan lumshe ahankali, kuma cikin sanyin murya yace.


“Lafiyanta kalau.”


Kai Abban ya girgiza kana cikin gamsuwa yace.


“masha Allah to adawo lafiya amma Rayyern ka kula da kanka sosai, ka daina sakaci akan cin abinci da kuma shan magani.”


“To Abba.”
Rayyern din ya fad’a atsanake, jin Abban ya kashe wayanne kuma, yasa shima ya zare wayar akan kunnensa, tare da maida ita cikin aljihun rigarsa.
Gudun kada ya makara ne kuma yasanyashi, d’aukan Briefcase d’insa ya fice daga cikin falon.


Koda ya fito waje motarsa ya shiga, cikin dan hanzari yayi mata key, tare da cillata kan titi kaitsaye ya nufi, babban hotel din da acikinsa zasuyi lecture din yau.




10:00 pm


Ahankali ta bud’e murfin kofar dakin nata ta fito, saidai kuma daddad’an k’amshin turarensa da ya gauraya da numfashinta ne, ya sata lumshe ido tare da shak’an wani sabon numfashi.


Ahankali kuma ta bud’e Idanunta tare da soma k’arewa falon kallo, wanda komai na cikinsa tsab tsab yake.


Idanunta da suka sauk’a akan ledodin takeaway din dake kan table ne, ya sata karasowa cikin falon.


Sanin da tayi kuma cewar Rayyern din baya gidanne, yasa ta nemi waje anan cikin falon ta zauna, batare da ta damu da irin shigar dake jikinta ba.


Ahankali ta jawo ledodin takeaway din, abunda taga yayi mata ta d’anci kad’an, bayan ta kammala cin abincinne kuma, ta koma ta kwanta tare da lumshe Idanunta, tana me sauraran wak’an film din Kalho Naho, dake tashi acikin babban tv’n dake falon.


Azahirin gaskiya wakan take saurare, saidai kuma amma abunda ke cikin zuciyarta daban yake, domin gaba daya tunaninta ya tafi ne izuwa ga rayuwarta.


Sau da yawan lokaci takan ji ta wata ta daban acikin wannan duniyar, takanji kanta amatsayin wata halitta wacce bata da gata, halittar da rayuwar ta ta kasance tamkar haja a kasuwa, ko kuma kwallo ta yanda kowa ke bugata yanda yake so.


Tabbas tasan k’addara na iya zuwarwa bawa, ayanda bai tsammata ba, amma ita tata k’addarar akullum da salon wasa da rayuwa take zuwar mata.


Kamar dai yanzu da take rayuwa awata duniyar ta daban, wanda babu iyayenta akusa da ita.


Ada ta fuskanci takura kad’aici da kuma tsangawa ma, awajen Yah Junaid, takanyi kuka sosai aduk sanda Junaid ya musgunawa rayuwarta, haka kuma takanyi takaici da mamaki aduk sanda, yayi yunkurin kusanto da kansa gareta, ta sani cewar shidin Yayanta ne na jini, amma har yau tambayar da takeyi wa kanta shine, Meyasa Junaid din da ya kasance dan uwa agareta, ke kokarin keta haddinta akoda yaushe?


Ajiyar zuciya ta Dan sauke ahankali, cikin sanyi kuma tasa hannu ta sharce hawayen, daya gangaro ta gefen fuskarta.


Sakamakon tunawa da tayi cewar, ayanzu wata kalan rayuwa takeyi daban, cikin kuma k’addarar da ta d’aukota daga gidansu, ta raba ta da Mahaifinta, da kuma y’an uwanta.


K’addarar da ta kawota wannnan k’asar da take ganinta amatsayin sabuwar duniya.


Numfashi ta kuma fesarwa, tare da gyara kwanciyarta akan kujeran, ahankali ta kuma lumshe Idanunta.


Tana kwance ahaka da tunani kala kala, acikin zuciyarta bacci b’arawo ya d’auketa.


Acan b’angaren Rayyern kuwa tun 8:00 pm suke lecture, basu ne suka fito ba sai 1:00 am, nanma breaktime ne da suka samu, domin bayan sunci abinci zasu sake komawa wani lecture din.


Kasancewar kuma akwai musulmai da dama, acikinsu ne yasa sukayi amfani da breaktime din sukayi Sallan azahar, bayan sun idar da sallan azahar dinne kuma, suka wuce cafe dan cin abinci.


Shidai bai wani ci abincin sosai ba, sai drinks kawai da yasha kan Chocolate ɗinsa da yaci.


Kasancewar kuma agefen cafe din akwai, wani sasanyan furanni da swimming pool ne, yasa ko ina dake wajen ya d’auki sanyi, daga inda su Rayyern din ke zaune kuma, suna iya jiyo koke koken tsuntsayen dake shawagi awajen.


Saboda daddad’an sanyin dake ratsa sa ne, kuma yasa shi d’an lumshe idanunsa ahankali.


Wani irin yanayi yakejin kansa aciki, ma’ana yanayi mai kama da shauk’i, akaro na farko kuma acikin rayuwarsa daya fara tunanin wata mace.


“Naan! Naanu!!”


Ya maimaita sunan da take kiransa dashi, Yayinda acikin kunnuwansa kuwa, yakejin tamkar sautin muryar nata ne keyi masa gizo.


Idanunsa dake alumshe kuwa, salon shagwab’arta suke hasko masa, musamman yanda takeyi Idan tana magana, Ahankali yake ganin lips dinta na motsawa, Idan acikin fushi take kuwa, to lips din nata take turowa gaba, then saita dan karyar da wuyanta gefe.


Sassanyar Ajiyar zuciya ya sauke, ahankali kuma yake sauraran sautin bugun zuciyarsa dake tafiya kadan kadan, batare da ya ankara ko sanin abunda yakeyi ba, kuwa yaji heart din nasa tayi sanyi sosai.
Take kuma wani bakon yanayi mai kama da farinciki, ya ziyarcesa.


D’an bud’e idanunsa yayi Ahankali, ya saukesu akan wasu kyawawan tsuntsaye dake shawagi asaman wasu fararen furanni wani yalwataccen murmushi ya subce masa.


“Rayyern.”
Dr. Sulaiman dake zaune agefensa ya kira sunansa, fuskarsa d’auke da mamaki saboda, wannan ne karo na farko aduk rayuwarsu, daya taba ganin Rayyern din ya nutsu yana tunani, wanda da’alama kuma abu mai mahimmanci yake tunawa.


Jin sautin muryar Dr. Sulaiman acikin kunnuwansa ne, yasa shi juyowa batare kuma daya kalli Dr Sulaiman dinba yace.


“What happened?”


Idanu Dr. Sulaiman din ya zuba masa, saidai duk yanda yaso karantar yanayin Rayyern din bazai iya ba, saboda Miskiline na k’arshe, Dan kuwa gashi yanzu yanzun ya sanja mood din fuskarsa.


“What Happened?”
Rayyern din ya sake tambayar Dr. Sulaiman.


Jin hakanne kuma yasa Dr. Sulaiman girgiza kansa, cikin kuma kawar da tunanin dake ransa yace.


“No dama naga lokacin komawa lecture yayi ne.”


Agogon dake daure atsintsiyar hannunsa ya duba, Ganin lokaci na tafiya ne ya sashi mikewa, batare kuma daya jira su Dr. Sulaiman din ba yayi gaba.


Kaitsaye hall din nasu duk suka koma, tare da ci gaba dayin lecture.


Kamar kullum haka yau dinma 5:30 am dai-dai suka tashi daga lecture din, kasancewar kuma hazo ya bayyana agarin da kuma sanyi mai tsanani, shiyasa basu wani tsaya ba anatashi kowa ya kama hanyar masaukinsa.


Ahanyarsa ta dawowan ne kuma ya tsaya yayi musu takeaway, kamar dai yanda ya saba yi musu akowacce rana.


Cikin ikon Allah kuma yana isowa gida, aka fara yi musu ruwan dusan k’ank’ara.


Koda ya shigo cikin falon rigar suit d’insa da dusan k’ank’aran ya sauka akai ya cire, tare da ajiye ta akan kujera, Ahankali kuma yake karewa falon kallo.


Sauke idanunsa da yayi akan hulan Jannart din, dake yashe ak’asan carpet ne kuma, yasa shi fahimtar cewa ta d’an zauna afalon.


K’ofar d’akinta dake arufe gam ya kalla, kana cikin dan hanzari ya wuce d’akinsa, bayan ya ajiye ledan takeway din anan cikin falon.


Koda ya shiga bedroom kayan dake jikinsa ya rage, tare da daura towel akan waist d’insa, kaitsaye ya wuce bathroom yayi wanka had’e da d’auro alwala.


Koda ya fito daga toilet din har 6:20 tayi.


Ruwan dake jikinsa ya dan goggoge, bayan ya shafa mai ajikin nasa ne kuma, ya karasa gaban drawer’n sa, tare da ciro kayan da zai saka.


Kasancewar kuma ana sanyi sosai ne, ya sa shi saka wani dogon wandon jeans mai kauri, tare da long sleeve t shirt kana kuma ya daura babban sweater akan shigar tasa.


Bayan ya kammala kimtsa Kannasa ne kuma, ya d’auki key din motarsa ya fice.


Duk da cewar kuma har yanzu ba’a gama ruwan dusan kankaran ba, haka ya fita ya shiga mota zuwa masallaci, domin dama su y’an garin sun saba da irin yanayin.


Bayan an idar da sallan ne kuma ya zauna acikin masallacin, har saida akayi sallan Isha.


Wanda zuwa lokacin kuma sosai garin ya sake yin sanyi.
Hakanne ma yasa bai wani tsawaita addu’a ba ya nufo hanyar dawowa gida.


Duk da kuma cewar shidin yana cikin mota, amma hakan bai hanashi jin fitinannen sanyin dake tashi acikin garin ba.


Koda ya iso gida ko gama dai-dai-ta parking baiyi ba, da Dan sassarfa ya fito ya shige cikin falon.


Ajiyar zuciya ya dan sauke, kana ahankali kuma ya sauke idanunsa akan ledodin daya kawo, wanda suke nan kamar yanda ya ajiyesu, saboda babu alaman an tab’a.


Idanun nasa ya daga tare dakai dubansa izuwa kofarta.


Tsaida idanunsa akan kofar yayi baya ko kyaftawa, Yayinda shi kansa ya rasa me yake kallo, da tsammani.


Saidai kuma har acikin zuciyarsa abu d’aya yakeson sani, shine rashin cin abincin da baiga tayi ba, wanda baisan dalili ba, cause kullum Idan ya kawo abincin kafun ya dawo daga masallaci yake Ganin taci nata.


Numfashi ya fesar kana ahankali kuma ya dauke idanunsa daga Kallon kofar nata, batare kuma daya waiwayi abincin ba shima, kaitsaye ya wuce d’akinsa.


Koda ya shiga cikin dakin sweater din nasa ya cire, bayan ya rage hasken wuta ne kuma, ya koma ya kwanta akan lallausan gadonsa.




Kamar yanda yake kwance akan gadon nasa kuwa, haka itama Jannart ke kwance, Yayinda ta kanannad’e Kanta acikin blanket.
Saboda sanyin da akeyi ne kuma yasa, tunda yamma da ta shigo cikin dakin bata sake fita ba.


Ko yanzu ma batajin zata fita saboda batajin yunwa, kasancewar taci abinci da rana sannan tasha fruits salat.


Atana kwancen kuma wayarta ce ke rike ahannunta, tana Dan latsawa, game takeyi wanda da’alama kuma tana Jin dadin game din sosai.


Kasancewar ana sanyi sosai ne kuma, yasa tana rik’e da wayan ahaka har bacci ya dauketa batare da ta shirya masa ba.


*Rayyern.*


Ajiyar zuciya mai k’arfi ya kuma sauk’ewa akaro na barkatai, kana cikin dan yanayin kasalan da yakejin kansa aciki ya lumshe idanunsa.


Ahankali yakejin mood d’insa na sanjawa, ga kuma tsikar jikinsa da yakejin yana tashi.


Sannu ahankali kuma idanunsa dake lumshe, suka soma yi masa imagining nata, wanda hakan yasa take duk wata gab’a dake jikinsa ta amsa.


Ahankali yake tuno moment dinsu, da kuma yanda ta saka hannunta akan saman mararsa tana shafawa, Yayinda yan yatsun hannu, da kuma dumin tafin hannun nata ke ratsa cikin Dick d’in sa.


Da sauri ya bud’e idanunsa, saboda wani irin zubawa da yaji tsikar jikinsa nayi ya rasa wannan wanne irin masifeffen tunani ne da ki barinsa ya huta domin kusan kullum sai ya tuna wannan yanayin.


Daga gefe guda kuwa ga numfashinsa, da yakejin yana kokarin kwacewa, wanda hakan yasa awahalce ya fusgo numfashin nasa.


Saidai kuma jin yanda mararsa ke motsawa ne, ya sashi saurin d’aura hannunsa, ya danne saman marar.


“Yah Salam.”


Ya fad’i haka yana me rumtse idanunsa, tare da cizon lips d’insa, saboda dick d’insa dake amsawa.


Domin haka yakejin tamkar yanzu ne abun ke faruwa, dalilin hakanne kuma yasa shi, soma motsa hannunsa dake kan saman marar nasa.


Ahankali yake shafawa tare da maida idanunsa ya lumshe.


Almost 17mn
Ya soma sauke wani irin
Breath mai kama da sexual erection sound, duk da ba masturbation yayi ba, amma sai yaji numfashinsa na fusga kaman zai kwace, Yayinda duk jikinsa kuwa ya d’auki rawa da karkarwa.


Alaman tafiyan hannunta akan saman marar tasa kawai yakeji, da sauri ya juya tare da kifa kansa acikin pillow.


Numfar fashi ya dinga saukewa akai akai, yana ahaka har bacci ya daukesa.


*Washegari*


Duk yau din haka ya tashi yana jin jikinsa wani iri, kasancewar Sam wannan moment din ya kasa barin cikin Brain d’insa.


Ahaka dai ya shirya ya wuce wajen lecture, bayan ya saka ankawo abinci kamar kowacce rana.


Still yauma bai wani ci abincin sosai ba magani kawai yasha ya kama hanyarsa ya tafi.


Jin alamun fitansa ne kuma yasa Jannart fitowa falon, abincin daya rage ta dauka taci, bayan ta tattare wajenne kuma ta dawo ta kunna kallo.


Haka dai tayi ta zama ita kadai, ba ita takoma d’akinta ba kuma har saida aka soma kiraye kirayen sallan magriba.


Shikuwa Rayyern ranan bai dawo gidan ba, saida yayi sallan Isha, still da takeaway ya dawo, bayan yaci nasa abincin ne kuma ya wuce d’akinsa.


Kasancewar yau din ya gaji sosai shiyasa, yana kwanciya bacci ya daukesa.


Jannart kuwa sai wajajen 9 ta fito taci abincin, bayan ta kammala kuma itama ta koma d’akinta.


*** **


*After 5days*
Da sannu rayuwa ta koma musu irin Wacce sukeyi Ada, saboda tun ranan da ya shigo dakin nata, acikinsu babu wanda ya sake Ganin Dan uwansa har zuwa yau.
Sai dai akwai gagarun banbanci domin a yanzu wuni yakeyi tunaninta kamar zai zautar dashi, taurin kai kuma da kafiya ya hanashi yin mubaya'a.


Saidai akowacce rana yana ajiye mata abinci, kamar yanda ta saba kuwa takan ci abincin, sauran ragowan kuwa sai ta kaishi kitchine.




Kasancewar kuma ranan yau ta kasance, Wednesday shiyasa su Rayyern din suka tashi da wuri.


Bayan ya biya restaurant ya saya musu abinci ne kuma, kaitsaye ya dawo gidan.


Yana shiga bedroom d’insa kuwa kiran Mamynsa na shigowa.


Adan kasalance ya d’aga wayar, kana cikin shagwab’a yace.


“Mamy barka da yamma.”


“Yauwa Rayyern barka dai ya jikin naka? duk dama naji Jananrt tace min yanzu kam ka warware.”


Mamyn ta fad’i haka cikin sakin rai, da kuma nuna kulawa agaresa.


Shikuwa jin abunda Mamyn ta fad’ane ya sashi, narkewa kamar karamin yaro yace.


“Mamy nifa nayi sauki sosai, Ina Ramadan da Baba Maud’o, Allah Mamy nayi kewar Baba Maud’o sosai, duk da cewar muna waya amma sai nakejin kewarsa sosai.”


Ajiyar zuciya Mamyn ta sauke, cikin kuma danne abunda ke cikin zuciyarta tace.


“Baba Maud’o yana lafiya Rayyern, wato mu baka kewar ganinmu sai shi ko.”


Murmushi ya d’anyi, kana Cikin kwantar da murya yace.


“A'a ba haka nake nufi ba Mamy.”


Itama Mamyn Murmushi tayi, Cikin kulawa kuma tace.


“Ka huta gajiya zamuyi waya anjima, dama na kira na sakejin ya lafiyar jikin naka ne.”


Kansa ya dan jinjina tare da cewa.
“To Mamy.”
Jin ta kashe wayarne kuma yasa shi. Dan lumshe ido, abayyane kuma cikin sanyin murya da alamun kamar fushi da shagaɓa yace.


“Almost 6days kenan bata ganni ba kuma bata nemeni ba, amma wai har ta iya fadawa kowa cewar na samu lafiya, bayan ko zuwa dubani ma batayi like tana fushi dani, kuma ni dai nasan ba abinda na mata, shagwab’abb’iya da wani d’an k’aramin bakinta awajen,."
Numfashi ya ɗan fesar tare da lumsh ido a fili yace.
“Now da zan kwanta ciwo sai tafi kowa rudewa a duniya, she’s saying Naan! Hamma Naanu!! Please Naan karka mutu, Dan Allah Naan ka bude idanunka, wayyo Allah Ka taimakeni Naanuna!!!.”


Ya kare maganan cikin kwaikwayon maganan Jannart din.
Saboda har yanzu tana yi masa gizo acikin idanunsa.
Murmushi yayi shi dayansa.
Ahankali ya ajiye wayar tasa tare da wucewa toilet kaitsaye.


Jannart kuwa Acan d’akinta zaune take agaban dressing mirror, Yayinda jikinta ke sanye da bathrobe da alama kuma fitowarta daga wanka kenan.


Duk da cewar kuma ta gama kimtsa kanta, amma bata saka kaya ba.
Yar karamar wayarsa dake hannunta ta soma jujjuyawa, Yayinda acikin ranta take tunanin kiran Aunty Fauziya, saboda ba kadan ba tayi kewar matar.


Wayarta kiran iphone ta dauka tare da kunnawa, ta kwafi numbern Aunty Fauziyan, acikin karamar wayar tasa tare kuma dayin dialing call din.


Aunty fauziya dake zaune kuwa, Ganin kira ya shigo wayanta ne ya sata, duba screen din wayar new number , kuma ta k’asar Russia da ta ganine yasa, atakeyi tayi tunanin ko Jannart ne, hakan yasa ta d’aga da sauri, tare da kara wayan akan kunnenta.


Jannart dake zaune kuwa jin Aunty Fauziyan tayi picking call dinne, yasa tayi murmushi cikin sakin rai tace.


“Nayi kewarku sosai My Aunty.”


Murmushi itama Aunty Fauziyan tayi, cikin kuma jin dadin kiranta da Jannart din tayi tace.


“Wallahi Jannart muma munyi kewarki sosai, ya kuke keda mijin naki ya Mascow?”


“Alhamdulillah Aunty, duk muna lafiya yasu twins, da kuma mutanen wajen aiki, Allah duk nayi kewarsu inajin kaman na dawo.”


Jannart din ta fadi haka cikin sanyin murya.


Hakanne ko yasa Aunty Fauziyan sakin murmushi, cike da kulawa kuma tace.


“Haba Jannart keda kike tare da mijinki, Ina ke Ina wani kewar abokanan aiki, ai ki manta da wasu abokanan aiki kawai ki saurari mijinki, Kodai yanzun ma yana kusa ne?”


Kai ta d’an girgiza cikin sanyin murya kuma tace.


“A’a baya kusa, ya fita tun safe, amma bansani ba ko ya dawo.”


Ta kare maganan in don’t care manner, wanda hakan ke nuna kwata kwata batasan, kula da dawowarsa ko kuma fitansa ba.


“Jannart.”
Aunty Fauziyan D Sulaiman ta kira sunanta cikin yanayin mamaki, kana bata jira ta amsa ta ba tace.


“Bakisan lokacin dawowan mijinki ba Jannart Why, Kodai kun samu matsala dashi ne?”


Shiru Jannart din tayi tare kuma da sunkuyar da kanta k’asa, saboda batasan me zata fad’awa Aunty Fauziyan ba.


“Jannart tambayanki nake ba kodai kun samu miss understanding ne, tell me karki damu saboda akowanni zaman aure, ana samun irin haka Dan haka karki boyemin komai.”


Ajiyar zuciya ta d’an sauke jin hakanne kuma ya sata, langwabar dakai cikin sanyin murya tace.


“A’a My Aunty ba fad’a mukayi ba, nida yau kwana na 6 ban sashi a idanuna ba tayaya zamuyi fad’a, Allah Aunty ba muyi fad’a ba.”


Baki Aunty Fauziya ta sake, cikin kuma mamakin abunda Jannart din ta fad’a tace.


“Subahanallah, Haba Jannart ya zaki wofantar da mijinki haka, har tsawon kwana 6 batare da kinsan halin da yake ciki ba? kinsan me hakan da kika aikata yake nufi kuwa? you mean bakya kulawa da mijinki why, Meyasa Jannart bayan kuma kinsan yana da hakki akanki, Koda ace anyi auren naku ne acikin wani irin yanayi, amma shidin mijinki ne kuma yana da hakki akanki, Kodai bakisan da hakan ba?”.


Aunty Fauziyan ta tambaya cikin dan yanayin damuwa.


Jannart kuwa Kanta ta sadda k’asa, tare da soma wasa da hannunta, cikin sanyin murya tace.


“To ni Aunty....”


“To keme Jannart baki da wani excuse din da zaki bani, indai akan kulawa da mijinki ne, Meyasa zaki bari rayuwar aurenku ta zama haka? Wallahi ba haka ake rayuwar aure ba Jannart, mijinki mijinki ne ako ya yake, sannan shine komai naki ahalin yanzu, babu kuma wanda ya fisa kusan ci dake, haka kuma Aljannarki tana karkashin kafarsa, To meyasa kikeson yin wasa da damarki?”


Shiru Jannart din tayi saboda, bata da wani kalma da zata fada, wanda Aunty Fauziyan zata fahimta.


Aunty Fauziya kuwa sanin halin Jannart din, na sanyin rai da tayi ne yasa ta cigaba da cewa.


“Baki kyauta ba Jannart, Sam bai dace ba ace kin bar mijinki, har tsawon 6days babu kulawarki, kenan babu wani hakkinsa ko daya dake kanki, da kika sauke, na farko bakya zuwa Koda gaishesa ne, balle kuma ki dafa masa abinci ki basa yaci, kuma yau koda ace shi yayi miki laifi, kece akasansa saboda haka wajibi ne, ki basa hakuri kodan neman zaman lafiya, sannan duk wata macen kirki bata raba muhalli da Mijinta Jannart, bakyau Mace ta kauracewa mijinta, domin yin hakan kan jawo mata tsinuwa awajen mala’ikun Allah, me yasa to ke kikeson kasancewa a haka? Jannart miji fa ya wuce wasa, matsayinsa yana da girma sosai, kinyi ilimin boko dana addini ɗan dai-dai, kinsan komai kanki awaye yake, Meyasa bazaki zauna ki kula da mijinki ba, bacin kinsan cewar ak’asan da kuke, babu wani naku ku kad’ai kuke rayuwa, wanda kuma dole kuna da buk’atar kulawan juna, Dan Allah Jannart ki kula da mijinki kinji.”


Aunty Fauziyan ta k’are maganan cikin tausasawa, saboda tasani dole wani abun sai ta hanyar tausasawa ne, Jannart din zata fahimta, domin ba komaine za ace mutum ya sani ba, more especially kamar ita Jannart da ta taso, babu takamammen wanda zai kula da ita, babu wanda zai nusar da ita ya koya mata yanda ake zaman aure.


“Jannart.”
Aunty Fauziyan ta kuma kiran sunanta akaro na uku.


Asanyaye Jannart din ta amsa mata, kana cikin dan raunin murya tace.


“Naji Aunty Insha Allah zan kiyaye.”


Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, tare da kara sassauta muryarta, kana cikin son bata karfin guiwa tace.


“Duk da nasan bawai auren soyayya kukayi ba Jannart, amma ki sani kulawa yana da matukar muhimmaci, sannan kyuatatawa na jawo soyayya, Koda kuwa ga makiyinka ne idan ka kyautata masa, sai yaji dadi aransa Koda kuwa bazai bud’e baki ya fada ba, balle kuma ace mijinki na aure, shine wanda ya kamata ace kin kyautatawa fiye da kowa, ki duba irin mijin da Allah ya baki Jannart, bawai gama garin miji bane, mijine irin na nunawa sa’a, karki damu Koda ace shi bai baki kulawa ba, domin kece zaki nuna masa hakan, kece zaki fara har shima ya dauka, please Jannart ki kula da mijinki dan Allah, saboda ayanzu baki da wanda ya fishi, kar na sakejin haka cewar kinbar mijinki babu kulawa, bakisan ci da shansa ba, bakisan ki sauke masa hakkinsa dake kanki ba, ki gyara karki sakeyin haka saboda miji ba abun wofantarwa bane.”


Idanunta da suka ciko da hawaye ta d’an lumshe, Ahankali kuma Cikin sanyin murya tace.


“Kiyi hakuri Aunty Fauziya Insha Allah zan gyara.”


Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauk’e, tare da cewa.


“Shikenan yanzu kije ki kula da mijinki, sannan ako da yaushe ki kasance mai yawan ado, duk da nasanki da son ado, amma dole zan kara nana ta miki, Jannart ki kula da mijiki sosai, sannan kibar duk abunda kikeyi yanzu kije garesa, saboda na tabbatar cewa shima yana da buk’atar ki, Koda kuwa bazai bayyana hakan ba na sani tabbas yana bukatar ki kusa dashi yana kuma son ganinki Koda bai faɗa mikiba, nasan yana mararin ganinki akusa dashi, ajiye wayan ki tafi maza.”


Aunty Fauziyan ta kare maganan cikin serious.


“To.”
Jannart din tace tare da zare wayan akunnenta, ahankali ta Dan murza Idanunta wanda suke dauke da hawaye.


Cikin sanyin yanayi da kuma mutuwar da jikinta yayi, ta karasa gaban drawern ta.


Wani doguwar riga marar nauyi ta ciro, tare da zurasa ajikinta, kasancewar kuma rigar bata da wadataccen fadi ne, yasa duk wani surar jikinta bayyana.
Musamman breast dinta wanda suka tashi suka tsaya, tamkar zasu tsone idon mai kallonsu.


Bayan ta zura rigar ajikinta ne kuma, ta saka hulan sanyi mai dan kauri akanta, tare da daukan wani boyfriend jacket marar nauyi ta daura akan kayan nata, saboda ayanda surar jikinta ya bayyana sosai, kunya bazai barta taje garesa ahaka ba.


Bayan ta fesa turaren oud ajikinta ne kuma, ta zura wasu takalma masu laushi ak’afafunta.


Babban wayar nata ta d’auka, Cikin nutsuwa da kuma tarin fad’uwar gaban da takeji, ta bud’e kofar dakin nata ta fice.


Yayinda acikin zuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment