Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fareeda da kanta tashirya ni cikin wata super wax ligt ash da ratsin baki sai akasaka mun wata datsetsiyar alkyabba dark ash, da adon silver duk yanda akaso da na tsaida hawaye na kasawa nayi, duk inda tashin hankali yake da fargaba ranarnan akaina ya kare, ganin cewar kowa yakasa fahimtar illar wannan rayuwar da suke sonayi da "Uncle justice".


A nacewa nafito na rungume maman fareeda ga gam jinake lumfashina tamkar zao yanke, da kyar aka baban bareni jikinta yaya mariya tajani zuwa dakin ummu salma, zuwa nayi na dora kaina saman jikinta atunanina kozata turemun kaine, amma ga mamaki na first time in history naji tafara shafa kaina tace kiyi biyayayy yar gidan Asiya, maman ki mai kirkice, tashi kuje Allah yayi muku albarka.


Wani kukan nake mai narka zuciya, haka yaya mariya tajani bamuje wurin Abba ba sanin cewar yana tareda dayan uwansa suna gidansu samie.


Gidan babansu samie munsa mesa da dukka yan gidansu Abba wa azi sukayim,un sosai akan yanda nayima iyayena biyayyay ban yimusu musuba yace kwarai Abbanki ke alfahari da hakan sannan yamani kyautar set din sarkar zinari duk da bawata maigirma bace sosai, amma tanada kyau da tsari kirar dubai,


Bayan nan kuma sai mukabiya gidan wasu kakan nina haka wasu daga yan uwan su Abba sai kuma fada ba a wuce dani direct ba muka sauka.




*Idan kinada hali kibiyani Wannan littafin nakidine kibiya Hafsat Abu akar sadeeq first bank 3195366407*


*xxxvi*




A cikin fada kuwa munduka munkai gaisuwa wa mai martaba, duk abun nan da ake yaya mariya narike dani. duk mutanen da ke cikin fada kuwa nata saka mun albarka.


A'nbude taro da sallatin annabi, mai martaba shima yasakama auren albarka, tare da yin doguwar Addu'a kuma yace shekaranjiya da jiya da yau, duk yasa anje gidan anyimun saukar karatun alqurani bakwai sau bakwai, har kwana ukku.


D'uk aka dauki kabbara daga nan cikin gida muka wuce muka fara shiga dakin fulani karama, ta tarbemu da dammamiyar fura ta asalin katsinawa da dambun naman sa, karshe mukayi masauki dakin fulani babba.


N'i sai lokcin ma nasan dacewar wai da akwai hidimar daza ayi welcome to the family suma da suka shirya, wan da za,ayi yamxu anan gidan.


A'nan cikin kuryar dakin hajiya mukayi sallar isha,I tukunna aka maidani tsohon dakin Aunty Raheema Aunty Aunty mamie ce tace kiyi hakuri kidaina kukan nan yar gidan yaya Aseeya banida yanda zanyi dole tasa nadaurema raina nahakura da zubar hawayen ba don na daina na zuciba.




Yaya mariya ce tashigo da wani maganin tsugunno, takalli Aunty mamie tace mata suna son garwashi, tuni kuwa Aunty mamie tabugama uwar madafi wata tsohuwar mai aikin gidan da akayiwa sarautar uwar madafin, saboda kula dashige da fichen madafin gargajiya da cimar gargajiyar.


T'afadi mata baifi mintuna huduba sai gashi.


To tashi yar gidan Aseeya kihada da wananna dama barin sa nayi har sai ranar da za,a kaiki tukunnah tundashi sau daya ake turarashi ashekara. Ni wallahi Al amarin Ya'ya mariya zuwa yanxu kam har mamaki da tsoro yake bani, to duk fadan nata kuma inna tunaninta yake haba wannan abubu wanda take inna ma amfanin su haba ba halin nayi gaddama dole nayi yanda tace.


I'nna gama turaren mai make up wata daban ce ba wadda tayimun na gidanmu ba, tashigo. dan juyawa tayi kafin takuma juyowa takalli Aunty uwani tace gadukkan alamu ke kanwar sace Angon ce koh ta Aunty uwanie tace yayarsa dai. maii make up din tace oh sorry dayake basanin sa nayi yiba inna son ne naji yanayin mijin nata domin asan kallar kwalliyar da za a dora mata.


S'hiru dukka sukayi dan murmushi tayi tace baku gane ba kwalliya ranar kai amarya tanada ban banchi data event wannan tambayar damu ke zaibamu dammar sanin abunda zamuyi da zai kara armashin wannan ranar, misali wani zaki ganshi mai sanyi saboda haka zamuyiwa amarya kwalliya maisanyi maras hayaniya.

A'yayin da wani kuma zakigan samai zafi shima kuma mukanyi wa amarya kwalliya mai zafi wato heavy make up!


(to make the night hot)πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


Munayi ne dai depending on the nature of the groom.period!.πŸ’¦πŸ«§


Aunty mamie tanachin abinci tace to ayanayin zamansa dai da marigayiyah duk alamu sun nuna cewa mai zafine shidin, saboda haka yimata ita mai zafin, domin kam mijin nata mai zafinne! jawad kam ai dukkan alamu sun nunacewa lafiyaye ne, cewar Aunty baby dukkan su kuma suka kwashe da dariya.


Runtse idona kawai nayi ni yar gidan maman fareeda, a halin yanxu da so samune da ba anbunda nafiso fiye da nagnni gida saman ciyar maman fareeda, oh ni wannan family sam bata ido, idan dai wurin biyan bukatar dan uwansu ne.😒




N'ikuwa bansan sanda kukana yafito filiba sai yanxu wani irin tsoro da fargaba yakamani, tunawa danayi shifa "Uncle justice" yafadimani ya karbi aurena da hannu biyu, barin da. dashima yakejin auren kamar bama zaiyi yiba, so akwai yiyuwar wannan rayuwar kwanciyar aure tashiga tsakanin mu kenan.


F'uskar kowa dakin dauke da murmushi, suka hau rarrarshina.
matar nan ce wadda take yimun gyaran jiki Tazo tatsaya saman kaina tana rarashina har akasamu nayi shiru.


Domin niduk kusan yanxu kowa ma haushi yakeba ni, tayanda kirikiri kowa yaki fahimta ta kuma da gayya sukaki su fahimceni din.




Make up tayimun heavy abunda yake heavy sosai, koomai yafito ram, lip dina sunsha lips glow sosai bayan red lipstick din daya sha, tukunna a
kashirya ni cikin wani tsadeden material purple mai haske wato lilac, fitted gown har ja take a kasa, ko inna nata walwali yake, tagyra gashina tayi parkin dinshi tsakiya, sai wata lafaya silver color, da tasaka mun sai zallar sarkar diamond tacikin lefena maidan fadi round neck da akasaka mun akalla kudinta zasu tasarma million biyar, sai munduwa mai daya hade da agogo dan siriri fari sai kowane yatsan tsakiya da aka sakama dan sirrin zobuna, kowane hannu guda biyu biyu.


Mark πŸ‘‰you!


Yes you! πŸ€“ba acikima amarya kayan yari masu yarbatsau dayawa, idan za,a kaita su akasari anfison sirara it looks more sexy then the heavy ones.


Haka kuma wani lokaci suna dan dagula lissafin miji ko surika cizonshi.


Aka daura mun da daurin dankwalin zara buhari gashina tabaya yasauka sosai yana shining, aka turarani gaba da baya dawani mayen turaren rushi mai sanyin gaske, tukunna kowa yafita, aka barni nikadai adakin.inna dai zaune atsakiyar dakin saman kujerar da na zauna akagama daura dan kwalin kaina akasa banji shigo warsa ba kamar yanda nayi zurfi cikin tunani sam banjii fitar suba.



G'anin mutum kawai nayi yatsugunno gabana, aikuwa gabana yayi wata irin tsinkewa, jinayi tamkar zai fado, dole tasa na rintse idona, banyi tsammanin ganinsa ba, nadauka sai dai muhadu achan gidan ne.


Y'ana sanye cikin danyar sahdda dark Purple da takara fitar da hasken fatar sa, sai alkabba dark ash! daya dora, sai rawanin da akayi masa simple but amazing,


Yayi kau sosai dashigar kallarshi tafarar fata tadace da kalar alkabbar sa, kallo daya nayima shi, nadukar da kaina, baiyi magana ba nima kuma banyi ba, ban kuma sake dogowa nakalle saba, kaina n akasa,


Ido kawai yazuba mun yaci gaba da nachin kallona, dama yasaba wannan kowa yasani, hallittar sa ce yawan kallon so sanin hakan baisa ni har yanxu na saba ba, ga kallon kurillah kusan mintuna bakwai muna ahaka, dan kwan kwasa kofar akayi jekadiya ce tashigo, bayan tarusuna tayi gaisuwa tareda kirari, tukunnah tace ranka dade mai babbban daki tace afadima ku kukadai akejira.


B'ata tafiba tadai rakube jikin kofa baiyi Magana ba gyada mata kai kawai yayi hannun sa yasa yalalubo hannunah dake harde dajuna, cikin lafayar yariko shi a hankali kamar wanda ke talalayar kwai, yami kar dani tsaye.


J'ikina narawa jinhaka yadan dakata har na dan natsu kafafuwana da suke sanye cikin silver high hill da digo digon baki suka kafu kan kasa, tukunna yajani muka fara taku ahankali, Allah kadai yasan irin dauriyar dana ke rike kukuna danayi, idan da inna da halin ihuma ba kuka kawai ba danayi, Aayayin da jekadiya tabiyo bayan mu tana ran gada mana guda, gudar dake kara birkita natsuwata.




*Idan kinada hali kibiyani typing akwai wahala Hafsat Abubakar sadeeq first bank. 3195366407*






*xxxvii*






L'okacin da muka fita harabar gidan, naga yanda tacika dankam da jama,a, daga bayana kuma ga jekadiya na dada birkita lissafina, da tasan illar da gudar nan kemani a tsakiyar kaina da kirjina, da wata killa ta taimakeni tabari.


A'i tuni naji kafafuna sunfara harhar dewa, alokaci daya kuma inna kokarin kwace hannuna, dake harde dana "Uncle justice" amma yaki sakina.


H'aba ni lissafina duk yadagulema wallahi. Allah gani gareka. kawai nakefadi araina wurin yawani masifar tsaruwa, iyya tsaruwa, dama ni arayuwata inna son decoration din waje fiye dana cikin hall.

A'ntsara wurin sosai kowane kusurwa rukuni rukuni, akafidda mai martaba anfitar masa da nashi bangaren da jama'ar sa wadanda suka hada da manya manyan malamai, da limaman gari da saurn hakkimai,


S'ai kusa dasu mahaifina da dangin sa abokanai da sauran makota, dakuma wasu tsirarun maza yan uwan mahaifiya ta su ukku dasuka zo daga zamfara, sadeeq ma da Asalam duk suna wurin, sai kuma wani bangaren da yahada duka iyyalen gidan mai martaba.


Saina kawaye da abokanan arziki saina Ummu salma itama da dangin ta kusur warsu da ban, wanda da kyar akasamu tazo saida akace mata toh diya bata Asiya bace tatace idan bata zonba. sannan tazo din.


D'ama ita maman fareeda tace sam komai za,ayida ita, daga cikin sha anin buki nan ya daya tamkar da dubu, achan daga gefe wani wurin ne da bayada girma amaimakon asakarmashi rumfa tent kamar mazaunin kowa, ah ah wannan wata yar bukka ce akayi ta gazebo, sai kujerun ta da dan karamin table da aka kawata da flowers da yadin row silk ash mai ratsin purple, nan naga mun dosa.innaga ganin dai lura da "Uncle justice" yayi bama kawa kafafuwa na hardeni zasuyi nazube, yasa dole sai yabani support dan saida yadan jingina ni da jikinsa.


H'akan yasa jikina yakarayin sanyi sosai, da kyar nake daga kafa idona arufe bansan inda nake daga kafaba, inna mayarwa ba, nidai kawai inna tafene da dan jagora!

G'anin duk dahaka da gaske zubewa zanyi yasa "Uncle justice" yadan duko ta saitin kunnainah yace mun relax Reedah duk masoyan mu ne yau atare da mu,


Hakan daya fadi mani yasa naji wani dan kuzari kadan na hakwace jikina, baiyi musuba yasakeni amma hannuna nacikin nashi.
A'haka dai har muka zauna malam Ahamad sulaiman ne yabude taro da doguwar adddu,a ga ma aurantan, tareda karanta wasu ayoyi kadan daga cikin alqur ani mai girma.

Sai malam Aminu yammawa, wan da yayi bayanin hakin mata akan mijinta, sai kuma malam kabeer gombe dayayi akan hakkin miji akan matarsa, da irin azabar da akatana darma matan da basayuin baiyyayar aure, saikuma malam Aminu daurawa dayayi bayani akana yanda iyaye zasu tarbiyantar dayaran su tayanda zasu zamo masu ya'ya nagari.


K'odon kasarmu tazauna lafiya, daganan sai waziri yayi jawabin godiya ga wadanda suka amsa gaiyata, sai kuma majidadin mai martaba shima dayayi jawabin godiya ga Abbana, na irin karamchi da mutumchin dayanuna, tareda gabartar masa da takardun wani katon fili a dutinma road daga masaurata,


S'ai sarkin gida dayayi bayanin murna da maraba ga gimbiya fareeda nashigowa cikin wannan zuria, sai kuma dan takaitatacen jawabin godiya daga mai martaba, shima da fatar Alheri sai kautar dalleliyar mota kirara camery 2022 da albashi daya yanka duk wata na naira dubu dari biyu zuga ga yarshi fareeda.

S'annan aka mayarda abun Magana ga Abba da ya bukaci hakan inda shima yayi godiya kwari kuma yayi addu,a sosai, da sanya alheri ga auren dafatar samun zaman lafiya. jin muryar Abba sam ban san sanda, da kuka mai sauti ya kucce munba, harda shesheka, innajan hanci ido kawai "Uncle justice" yakura mani daga farko yana mun Magana a hankali, ammani sam bamanajin abunda yakecewa, ganin kamar dukkam hankalina yanaga jawabin mahaifina.


D'aga nan zaune inna hango yanda su khaitrat da Asalam suma suke share hawaye, saddeq ne kawai baiyai ba.


D'agashi sai bayanin ababansu samie, inda yace shida danginsa sunyima "Uncle justice" kautar gona dake hanyar dan musa.

S'annan malam Mansur sokoto yarufe Toron da addu,a, mataan duka parlor suka dawo akachi akasha, ayayinda duka tawagaar mazan suka shiga chamber mai martaba, suma sukaci suka sha, tukunnah nidai inna zaune kuryar dakin Fulani babba makale da maman fareeda.


Fulani karamace tazo tayi kiran maman fareeda zata salami manyan kawayen ta tafita kuma bata jima da fitaba saiga fulani karama ta sake dawowa tace mai martaba yace afito atafi dare nayi sosai, jin haka yasa naji dukjikina yadauki wani tsam tsam yana yami yami, hawayen danake ta faman dannewa saboda gudun shigar damuwa maman fareeda, suka samu hanyar sauka ba kyakkyautawa.


Tashin hankali sukuwa su zeena samie khausar khalsoom sai ma ganganu suke kasa kasa, hannun khalsoom na janyo na rike gam, kwannan nan zakibar wannan kukan kowa yasan "Uncle justice" romio ne hajiya, idan dai gameda soyayyaya ne,


T'uni Yaya Mariya tayimun jagopra zuwa palor inda Fulani babba agabanta aka zaunar dani, tayimuna fatar alheri tareda bani kautar naira dubu dari biyar, da turare sai itama fulani karama tabani kautar naira dubu dari biyu, sai kwalla daya ta danbun nama da ta dakuwa da kuma ta aya maigishiri.


Nidai khlsoom tunda kune yan kai Amarya dan Allah kuwutomun da AyarπŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…




A parlon waje muka hadu da maman fareeda, sai faman matse kwallah take, kuka take sosai tanayima Allah godiya da irin mutanen daya hadata zama dasu masu karamchi da dukkan alheri, irin yanda mai marta ba yake yabon Abba tanajin kaf lillahi surukkan gidan nan bawan da yakeso da yabo tamkar mijinta, daya cikin mazaje .


T'ayi zurfi batasan da shigowar muba saida taji salatin Fulani karama tana fadin ke kuwa maman fareeda munata naimanki kiyi ban kwana da yarki bamu gankiba sai alokacin tadawo cikin hayyacccinta nikuma jin an ambachi sunanta yasa nasaki hannuna dake hannun yaya mariya da sauri cikkin sasarfa naje gareta.
A yayinda itama cikin sassarfar ta iso gareni, dukkanmu lokaci daya muka sauke ajiyar zuciya da zuciya daya matar nan kemani son yanda uwa keson danta haka nima da zuciya daya nake mata son uwa da ya.




R'ungume nakeda ita kuka sosai nake jinake tamkar rayuwata tazo karshe ne, wai yau nice amatsayin matar "Uncle justice" gani har za akaini gidan sa ni fareeda "Uncle justice" mijin Auntie raheema, matar dana tashi da sonta, ta ke amsa wani matsayi mai girma a rayuwa ta.


Bata yanda ba ayiba arabani da jikin maman fareeda amma naki sakinta, nariketa gagam kukan ma yaki fitowa sosai, alokaci daya kuma zazzabin danakeji inna daurewa ya kara tsanna ta ajikina, inna ji alokacin da za a auna jininah wata kila za asamu yahaura dari biyar.


G'anin haka yasa akace to ita uwar amaryar tajani ta kaini mota da kanta, ahaka makale da juna muka fita zuwa harabar gidan, duk su Abba da tawagar su mai martaba na tsaye amma duk dahaka kinayi narabu da jikinta. nawuce mutafi tamkar yanda ake Umur tata, sai wani haki nake tamkar zanshide, Abbane yazo wurin mu yasaka hannu, ya cironi daga jikin maman fareeda, yakira "uncle justice" dake chan kusa da ban garensa tareda P.A dinsa da oderly,


D'uk abunda ke faruwa yana kallo, tsaye yake yajingina jikin pillar sashen nasa, ya raungume hannayen sa duk biyu kiransa Abba yayi, yana zuwa yamika masa hannuna cikin nasa yace jawad ga matar ka kuwuce gida dare yayi.*DIE* πŸ™†β€β™€οΈ


D'uk kabara aka dauka a wurin anan take shima yajuya yashige cikin gida.




*Idan kinada hali kibiyani typing akwai wahala, Hafsat Abubakar sadeeq first bank 3195366407*


*xxxviii*






A'hankali "Unlce justice" aya tsugunna kasa gaban Abba, kuma tunda har a lokacin hannun mu nahade dole tasa nima na tsugunna, mubiyu tsugunne gaban Abban.


"Unce justice" yana ta faman yima Abba godiya,
to tashi tashi Abba yasa ka hannu dukkan mu mubiyun ya mikar damu tsaye, amma ni saina kasa tashi tuni dauriya ta ta kare. daga nan tsugunnen na yibaya zan fadi, Abba ne yayi saurin taroni na dawo saman kirjin sa.


Da ido yayima "Uncle justice" nuni daya kamani mutafi ba kunya kuwa yadaukeni ina a bridel style, lilac din rigar material din naja da kasa, haka kuma da wani sashe na alkabbar da aka saka mun saman adon kayana da zamufito baka wulik da ratsin kallar rowan makubba.


Ni yau naga rayuwa, dole tasa na runtse idanuna duk wurin kuwa akadauki ihu da sowa, da hargagi,
ayayinda hadda su maman fareeda da abba suke tsaye suma suna binmu da kallo kamar yanda kowa yabimu da kallon daga ciki harda haddiman gidan.


J'ikin wurin sabuwar motarsa kirar jeep din sa, sabuwa dal campany B.M.W 2022 yasakani, sannan yazagaya yashiga, a hankali yake jan motar har muka fito daga harabar gidan, kamar yanda a hankali nima nakejin zazzabi na nakaruwa, kuma still ni idona akulle suke, jin mun tasarma kofar wani gida naji jikina yayimun wani irin mugun zafi ga wata fitinan niyar faduwar gaba jin jikina nake har wani tsam tsam yake saboda fargaba.


G'aban wani Matashin sabon jinin massion gida muka tsaya! get din gidan katon gaske baki waluk ayayinda harabar gidan takeda painty ash wato kallar rowan toka.


N'adanji sanyi sanyi araina ganin cewar gidan da Aunty Raheema ta zauna niba a nan zan zauna ba. bawai domin tsaruwar wannan dinba yasa naji dan dama dama, ah ah sam wannan din dai ba zaidinga tunomun da abuuwa ne sosai game da Rayuwar mu da Aunty Raheema.


A'hankali get din ke budewa mushiga ciki bayan anbude mana secound get din, tundashi na farkon da remote yake aiki,


Y'a tasayar da motar amma bai fitoba, mun danyi shiru ne na misalin mintuna biyar, tukunna yabude motar yafito yakuma zagayon ta side dina yabudemun. ban fito ba banma nuna alamun naji abude dinba ballanta na nayi yinkurin fitowar
araina kuma tunani nake waini meyasa ne komai nawa yana banbam tuwa ne dana sauran mutane ne.
M'unje saudiya ne da sunan jinyar Aunty Raheema, amma cikin sati biyu chakal sai gani nadawo da igiyar auren mijin Aunty Raheemar😰 ya Allah.


H'aka kuma kowa yasani a al'ada dangine, yan uwa da abokan arzikine suke kai amarya dakinta, amma ni gani nabuge da zuwa gidan aurena dagani sai mijina.


B'ayan rakiya a haka yafitodani daga cikin motar shiga nan fita chan bude nan shiganan fita chan har naji yadireni saman wani sanyayyar gado mai kamshi da taushin katifa, dakin sai kamshin turaren wuta mai sanyi gidan yakeyi da kamshin sabon penty.


Ga jiya sosai da zzaazabi zazazabi suka tasarmun amai na dimga yunkurin yi, dagudu naruga nashiga kewaye, yana rike dani har nagama, zuwa lokacin shima yafara shiga damuwa, yafara blaming kanshi da meyasa yayi saurin amsar auren, so easily haka.


Da sai yabari har sai komai yalafa yanaimi ra ayin yarinyar, mana any way he believes cewar komai yana tafiyane da destiny!


W'ayar Dr naseer yakira mijin Dr safiya b liman, suna hanyar komawa ne gida, daga gidan mai martaba. kasan cewar shi nasser maahaifinsa abokin wasan su mai martaba ne, kwararren likitan zuciyane, da kuma matar tasa Dr Safiya B Liman wadda ta kasance likitar mata wato gynea palor suka tsaya shida naseer, ita kuma dr safiyya tawuto daki saboda yawan kukan danayi da kuma rashi cin abincin kirki, sai kuma Fargaba yasa jikina yayi weak sosai.


Allurai taha da tayi mun sai Karin ruwa da tasa mun wanda shima saboda yanda taga nayi yaushi da yawane shiyasa, ta hada mun ruwa masu dan zafi nadan watsa nashirya cikin wasu kayan barci riga da wando silk ne duk sunbi jikina figure 8 dina ya haska sosai acikinsu nidai takaina nake ban wani damuna ba da kalar kayan da tabani, kawai nakarba nasaka sai dataga nasamu barci tukunna ta gyara saitin rowan tafita.


A palor kuma shawar warine naseer yake tabama Uncle justice, na idan so samu ne to karya fadamun har sai nasamu natsuwa da shi kuma nasamu natsuwa da gidan da aure.

Tafito tareda yima Uncle justice bayanin cewar bawata matsala bace stress ne, da tension, ga enxiety duk suka hadu suka saukar mata da zazzabi, sai kuma tace masa idan rowan sun kare yatada ita tacire tasamu barci yanxu.


S'ai bayan da yaraka su tukunna yadawo ya dubani sannan ya wuce da kinsa yayi wanka yashiryaa cikin kayan barci pjamus farar kal masu toch of blue kitchen yanufa ya hado tea mai kauri da zafi ya dauko yankakkun fruits da holandiya yaso yahadamun daffafiyar madara da zumar danake sha, amma bai iyyaba, shifa kusan shekara yake bai shiga kitchen ba sai idan dole ce takama irin hakan.


Tea din yasha da fruit zuwa lokacin shabiyu tayi yatashi yafara nafil fili duk zaman tafiya sai ya lekkoni yagani kona tashi kokuma gudun kar nadanne hannun, ko rowan sukare. sai kusan biyu da shabiyar tukun nah yagama sallar, wadda kusan duk dare sai yayita idan yagama kuma yakan bata dogon lokaci mai tsawo yana yiwa Aunty Raheema addu,an dafatar samun rahamar ubangiji da yiwa yaransa da kuma rayuwar auren da zaifara daga yau.


R'uwan baikare ba sai kusan karfe hudu tashi yayi tareda kunnna fitilar gefen gado tukunna yakama hannunah yana cire Karin rowan, wurin cire allurara ne yasa nadan farka, saboda dan zafi danaji yafara shigata, shiru duk da nafar ka amma ko kwakkwaran motsi banyi ba, kusan nama rage speed din lumfashi na, domin kokadan bana son yasan nafar ka. tashi yayi yadauko tray din dazu tukunna yahau saman gadon sosai yana shirin daukarta yabata holandiyar tasha soyake tasakama cikinta wani abu kafin gari yawaye, haba zubur nayi saurin tashi zaune.


B'atare da na kalle shiba tadai dukar da kanta kasa dan side murmushi yayi ganin cewar kenan tafarka tundazu, cup kawai yadauka ya tsiyaya madarar holandiya, yacikashi yakai ya mannashi saman lips dinta shiru shi baiyi magana ba baice ta shaba kuma bai janye kofin ba yadai kafeta da idanuwan sa dan dago idona nayi kadan nasaci kallon sa, ni din yake kallo hakan yasa idanunmu suka garwaya cikin najuna, ganin ya kureni da kallon nan nasa na kasa kasa ga iduwannna nasa manya dasu hakan yasa yayimani kwarjini sosai fiye da kowane lokaci.


Hakan yasa a dole nafara kurba ahankali hankli, yanata bani har nasha dayawa nakoshi iya koshi, amma bazan iya magana ba ko nanumasa hakan ba sam.


Kaifin idanunsa da nachin su yasa adole naciga ba dasha din, saida yagadama dan kansa tukunna ayajanye kofin ya dauko fork yafara bani fruits din amma apple kawai da water melon yake bani nadan sha dayawa, tukunna nadan dago tasachi kallon sa innada bukatar shiga toilet hakan yasa tadan dago takalleshi amma sam takasa yimasa Magana kwarjinishi nayau datake gani shimfide afuskarsa yashaa ban bam dana kullum.




H'ar saaida Allah yataimake ni yasauka daga saman gadon hakan yasa nasamu sukunin sauka.


N'ima duk jikinna yasaki sam banida wani kuzari, jina nake tamkar saman isaka, amma haka nadaure cikin dan sauri nashige toilet din, nadaiji kaifin idanun "Uncle justice" akaina inna shiga toilet din saida nadan jinginna jikin kofar toilet din inna sauke lumfashi ahankali tareda lumshe ido ya illahi kawai

Please Login or Register in order to submit comment