Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za'a baka"na sami labarin har yanzun baka fara Aiki ba, shima zaka iya kamun takardun naka mu gani za'a kai inda Atake za'a daukeka Aiki "yanzun kasamun contact naka! ya fad'a yana sakin wani shegen murmushin rainin wayo"sbd Aganinsa dole Dr darma ya Ajiye zafin kai tunda yaga kud'i..... mik'ewa tsaye yayi Anutse yana koma sakin wani k'aramin murmushi "wanda yadaki zuciyar Mr mahuta dake zaune yana kallonsa da son jin ta bakinsa"gab dashi ya iso murmushin dake saman fuskarsa na dishewa"saida ya kallesa sama da k'asa kafin ya girgiza kansa Ido cikin Ido cikin iya tsara laffuzzan mgn yace" *wanda Ake d'auka ba komai bane sauda yawa wata ran shine ke zama komai" harma ya Amfani wanda ke ganin yafi k'arfin ya nemi ya masa wani Amfani* naji inada gadarar, kamar yadda kace"saidai Ina godiya ga Allah da yayini A talaka bamai dukiyar da zaiyi fahari ko tunk'aho itaba"iya Abinda na. sani da talaka dame kud'i duk Allah ne yayisu"fatan dacewa kamai muke nema"zancan Ahyaan dakake mgn ! Kaifa namiji ne? to meye zai Hana kayi Amfani da kanka wajen shayo kanta harta Amince maka?"Ina so kasani kud'i! basu bane komai" ka rik'e kud'inka bana buk'ata "iya Abinda na sani duk me jin kansa da nuna shi wanine tofa Agaban bainar jama'a yake gadararsa bawai ya tsaya yayita Abayan fage ba"idan har ka gama mgn dani Ina buk'atar na k'ara gaba"ban damu da matsayinka ko dukiyarka ba ,ko kuma zaka saka acutar dani"Abinda kawai na sani.....kai! kasan ko shi waye ne kake k'ok'arin gaya masa mgn?"cewar wani k'ato d'aya shigo ya tsintsi maganar Dr darma"saidai mahuta beso ya dakatar da shiba, yaso ya barsa yakai Aya "ya lura zafin kan yaron da izzarsa me girma ne"Amma daidai yake dashi....Dr darma kuwa murmushin takaici yayi yana nufar k'aton abazata yamasa wata wawar cakuma yana fad'in waye shi bayan *Ibrahim Abubakar mahuta*? Haihuwar sa Akayi kamar kowa ko kuwa daga sama yafad'o ne??"ya fad'a cikin zafin zuciya yana ingizashi da masifar k'arfi,ya daki bango"Atake wasu katti su ukku suka fito da manyan makamai Ahannunsu zasu nufesa"hannu guda Mr mahuta ya d'aga musu Alamar su bari"kafin ya mik'e tsaye sbd Al'amarin yaron ya fara bashi tsoro" yana ganin ba ta haka yaka mata yabiyo masa ba"Amma saiya basar ya kalli mutum biyu yana fad'in ku maidashi gida"daga haka ya d'auki ledar kud'in yabar parlourn.....kafin Dr darma ya juyo yaji wani k'yalle saman fuskarsa sun rufe masa Ido dashi "beyi mgn ba yana dai tsaye suka jashi suka fita suka shige mota...... k'arfe sha d'aya saura suka yi parking bakin titi basu shigo cikin layin suba"bece komai ba da suka janye k'yallen,kamar yadda suma basu maca komai ba, sai fitowa kawai da yayi daga cikin nafef d'in yana jan tsaki "ko Ajikinsa da Abinda Mr mahuta yayi na sakawa a d'akkosa"saidai zai nuna masa cewa raina kama kaga gayya"da wannan tunanin ya zaro wayarsa yaga 20 miss call"bema tsaya dubawa yaga kona waye, time kawai ya duba"jikinsa na bashi y'an gidan sune ke kiran sa"yaja tsaki yana nufar layin nasu da yayi tsit duk gidajen Anguwar suna a rufe ,sai d'aid'ai k'un motoci dake wucewa da mashina"tun daga nesa ya hango daddy da Abba da khaleel tsaye bakin get d'in shiga *gida biyu* suna mgn..... d'an huci ya furzan daga bakinsa"yana fad'in daidai nake dakai wlh mahuta tunda ka had'a wasanka dani"haka kawai sbd wani banza za'a tayarwa da iyayena hankali"ya fad'a Afili cikin yana yin jin b'acin rai yana tattaro nutsuwa da dakiya ya yafama kansa"cikin tausayin iyayen nasu ya iso gabansu....nurah! Ina kaje haka baka dawo gida da wuri ba, Anata kiranka ta waya baka d'auka ba??cewar Abba suna binsa da kallo....sunkuyar dakai k'asa yayi yana tunanin Abinda zai fad'a musu sbd su yadda"kasancewar be saba yin k'arya ba"kuma baya jin zai iya sanar musu Ainahin gaskiyar Abinda ya faru...wai bada kai Ake mgn bane?"cewar daddy Ad'an tsawace"kuyi hak'uri Abba Ina gidansu wani Abokinah k'anwarsa ce ta k'one "shine na tsaya na kula da ita da Abinda ya dace"wayarma tana silent yanzun me nafef ya saukeni"Ajiyar zuciya suka saki tare da fad'in Allah ya kyauta"daga haka suka wuce ciki"Dr darma ya rufe get d'in gidan ya nufi k'ofar d'akinsa yana tunanin Abinda yaga Mubarak nayi d'azun"da hanzari ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo ya kunnah haske ya nufi bath room "Agaggauce ya d'auro Alwallah ya fito ya kabbara sallar isha'i,bayan ya idar yayi shafa'i da wuturi "wajen k'arfe 11:30 pm ya fito daga cikin d'akin sanye da fara k'ar d'in jallabiya ya nufi inda yaga mubarak d'azun yaduk'a yana binnewa"k'arfen dake hannunsa ya saka yafara hak'o wajen.....k'irjinsa yayi wani irin bugu sbd ganin wasu layu had'e da Allurai da gefen zani da mayafi an yanka an daure"cike da mamaki da Al'ajabi ya d'aukesu ya Ajiye gefe ya maida ginar tsab ya rufe,kafin ya d'auki tarkacen layun yanufi d'aki dasu"dukda kasancewarsa masanin Abubuwa masu yawa yanada ilimi Akansu"Amma beyi gigin bincikaba ya barsu zuwa safe zaije wajen malaminsa daya koyar dashi Abinciki me layun suka k'unsa?"ransa yafi bashi kodai Ahyaan ko mama ummah tayima Asiri,shine ta bama Mubarak ya binne Acikin gidan"yaja wani kakkauran tsaki had'e da furzan da wani irin zazzafan huci daga bakinsa yana taunar lips nasa kamar zai hudasu"ya lashi takobin muddin harda Ahyaan Acikin wannan sihirin wanda yayi shi ya jama kansa"da wannan tunanin bacci yayi Awon gaba dashi ba tare da yama shiryama baccin ba.....washe gari misalin k'arfe 2:38 pm"Ahyaan na zaune kan kujerah y'ar tsugunno Atsakar gidan gaban tape tana wanke inner wears d'inta cikin roba"sanye take da plate d'in takalmi fashion pink colour masu taushin gaske"sunyi matuk'ar k'ara k'awata kyawun k'afar tata"yayinda da take sanye da doguwar riga ta Atamfa da hula navy blue tayi goshi style "fuskarta ba make up Amma tayi Shar da ita sai zuba k'amshi me kashe jiki takeyi"duka lips nata na cikin bakinta "tana pasin k'ofar shigowa tsakar gidan"mamy bata jima da fitaba wajen sunan k'anwar daddy"daga ita sai hamzavne Agidan"shi yana d'aki yana kallo"gaba d'aya cikin nishad'i take sbd tun safe Abba dazai fita ya Amshi takardunta ya tafi dasu"tana jiran dawowarsa"duka yau kwananta biyu da dawowa KT Amma bataje ko inaba in aka cire fitarsu ta jiya da Dr darma"har gidansu Khairiyyah taso taje yau mamy tace ta bari sai gobe Friday....k'amshin turarukan Dr darma masu kashe gangar jiki da zuciya suka fara rige rigen kaima kokafin hancinta ziyara ,kafin ta d'ago kanta har taji Amon jarumar muryansa me dad'in sauti na ratso kunnuwanta yana yin sallama "shi kuwa yana shigowa idanunsa Akanta suka fara sauka"sai Akayi sa'a ta d'an kallesa ta zabga masa wata uwar harara sbd tuna Abinda yamata jiya"kallon second 2 ta masa ta tab'e baki had'e da d'auke kanta"sanye yake da k'ananun kaya da p cap da takalmi sawu ciki"wanda sukayi shige da gogonsa da p cap d'insa "hannayensa na rik'e da ledoji guda biyu"fuskarsa ta d'an fad'a sbd Azumin daya tashi dashi"saidai ya k'ara haske"karan hancinsa yad'an fito"lips nasa sun k'ara yin jaa"directly inda take yak'ara so Aransa yaji dad'in ganin ta rufe gashin kanta"sosai yaji tausayinta dalilin binciken da aka masa d'azun akan layun dayaga Mubarak na binnewa"ita bata damu da rayuwar kowaba tana hidimar gabanta Amma wasu najin zafinta"ya Ayyana Aransa.......tsaye yayi gefenta in low voice ya furta"ba sannu da zuwa sai harara da za'a Aiko mun da ita *Amun dago* ? k'in tankashi tayi sai kuma ta dinga b'abb'aka dariya "ya tab'e baki yana fad'in Allah yaka miki sauk'i"hmmm! mlm ka wani shigoma mutane gida da ledoji kamar wani magidanci"sannu da zuwa Akanme zanyiwa k'anina sannu da....shiru tayi sbd ganin yayo kanta ta rintse Ido "yaja tsaki yana fad'in matsoraciyar banza"magidanci kuma saura k'iris na zama"bud'e idon tayi tace"Ashema tsoro?"ta k'are maganar Asadda take matse under ware nata"kiyi ki gama wannan wankin gulmar"Azumi nakeyi ki had'amun Abin bud'a baki "ya k'are maganar yana cin magani ya Ajiye lodojin gabanta"Anutse yaci gaba da cewa"kiyi mun kunun gyad'a "ga kayan fruit nan ina son fruit salad"wannan naman kiyi farfesu dashi"Allah ko?"ban sani ba"ni wlh kana bani mamaki da wannan Abin da kake mun"sai kace wata k'anwarka ko wacce kake iko da ita? kuma babuma irin ko dan Allah kimun Abu kaza "ah ah umarni kawai kake bani"Eh na baki ko bazaki yiba ne ?"Eh banayi"Allah bara mamy ta tashi saina gaya mata "uhmm! mamyn Ai bata nan ta tafi sunan gidan uncle nuhu"ki tashi ki matse kayan kije toilet ki shanya"daga yau na hanaki shanya inner wears Atsakar gidan nan"murmushi ta saki tana mik'ewa tsaye ta nufi gaban tape d'in tace"yanzun Agabanka zan shanya saika hana idan ka Isa...bece komai ba ya zaro Allura daga cikin Aljihun wondonsa dake cikin siringi harda ruwa ma cikinta"ya wani tsuke fuska yana binta da wani irin kallo me wuyar fassara yaga ta zaro Ido"murmushi yakusan sub'uce masa "kinsan Allah?"mintina 5 na baki muje Agabana ki shanya ki fito muyi Aikin nan nata yaki ko kuwa babu ruwana da lafiyan ki qlau Allura zan d'irka miki....haba broth wannan wane irin mugunta ne?"nidai ka maida Alluran bana son ganinta, Ai zanyi yadda kakeso "dama fa wasa nakeyi"shiru yayi yak'i mgn ya maida Alluran inda ya fiddota yana cin dariya Azuciyarsa"gaba d'aya jikinsa ya mutu sbd yadda ta kwantar da murya tana mgn Amairairai ce....to ka d'auki robar muje na shanya"Amamakinta bece komai ba ya d'aukar mata kamar yadda ta buk'ata.....har cikin toilet d'in mamy ya Ajiye mata sannan ya fito ya barta ciki ya tsaya daga cikin parlourn gefen k'ofar bed room d'in yana kallon hamza dake kallon TV "wanda yayi hakane sbd yasan zata iya zuwa ta rufe k'ofar bed room d'in "shi kuma beson kad'aicewarsu Adak'in su kad'ai ,yasan mamy bata so kuma shima yana son bin dokar Allah da Abinda Addini yace Ayi"yana nan kiran bilkisu ya shigo cikin wayarsa wacce tuni yama haddace number nata"saidai harta tsinke be d'aga ba"sai tsaki yaja sbd ganin ko Awa guda basuyiba da rabuwa yanzun ba"taje chemist nashi wai tana zazzab'i yamata Allura"shine yace"saidai ya mata ga hannu"ta Amince ya mata yabata magani"zata biya 1500 Amma saita bada 50k "harara ya wurgo mata"ya zari y'an 500 guda ukku yace"ta d'auki sauran kud'inta taje ta bashi waje"yana jin k'awarta na cewa haba *Ikkhee* ! ba girmanki bane ki tsaya namiji na miki irin wannan cin fuskar.....yaja tsaki yana tunanin meyasa mutane ke nuna zasu iya mallakar komai idan sunada kud'i? dama tunda yafara ganin yarinyar ya fahimci y'ar gidan masu dashi ce"kuma sangartacciya ce.....ka matsa na wuce"siririyar muryar Ahyaan ta katse masa tunani"saida ya d'an lumshe Ido yakoma bud'ewa kafin yad'an gyara ta wuce rik'e da robar"saiya biyo bayanta zuwa tsakar gidan"ganin zata wucesa ya sakashi shan gabanta"oh yah rabbih! pot& knife zan je na d'auka a kitchen" wlh matarka ta shiga ukku da fitinarka haba"ta fad'a tana wucesa"shi kuwa Akaron farko ya saki k'ayataccen murmushi yaje ya zauna kan kujerah d'in data tashi"yana nan zaune ta iso gefensa ta Ajiye tukunyar ta jawo ledar naman"kaji ne manya guda biyu "Amma yayyankasu daga can inda ya siyo su"kawo na kama miki"to baka zauna mun kar kujerar ba"ta fad'a tana zuwa ta zubo ruwa cikin tukunyar"beyi mgn ba ya tashi ya tsugunnah"tana dawowa ta zauna"ta fara wanke naman yanata kallon yatsun hannunta dana k'afarta"can kuma ya fara kama mata tana ragema masu girma yawa"daga k'arshe suka wanke naman atare, ita ta yanka Albasa"bayan takai tukunyar kitchen ta fito da morning fresh sbd su wanke hannuwansu"dukda ba wata fira sukeyi ba"Amma tayi mamakin tayata Aikin da yayi"jefi jefi idan sun had'a Ido dashi harara take sakar masa "shima yana kallonta ta k'asan Ido"yak'i ya tankata"zoki zubamin na wanke hannuna"ya fad'a yana tsayawa gefen tape d'in yad'an duk'a"batace komai ba ta matso ta zuba masa ya fara sab'e duka hannayen nasa"ita kuma ta kunnah tape d'in ya fara wankewa"koda ya idar sbd Jan mgn saiya watso mata ruwan hannunsa saman fuska yana fad'in" *Amun dago* kema zoki wanke saina zuba miki ko?"ba k'aramin haushi tajiba ,ta rasa mesa be iya kiranta da Ahyaan ?Amma saita sharesa"tak'i bashi yazuba mata saita zuba da kanta"koda yaga haka saiya wuce kitchen ya d'akko wata robar da wuk'a yadawo yasamu ta gama wanke hannun "tashi muje parlour"batayi mgn ba ta d'auki ledar fruits d'in tabishi"kashe kayan kallon yayi sbd ganin hamzan yayi bacci"Akanme zaka wani kashe bayan kuma Ina kallo?"Akan naga dama ne"hmmm! sbd kaga mamy bata nan ko kake wannan Abin?"Allah saina maka mugun gami da ita idan ta dawo"to shikenan y'ar jaridah karki damu.....Ina yasan meta karanta?"ta tambayi kanta tana kallonsa"ya d'age kafad'a had'e da tab'e baki ya zauna gefenta"sai batace komai ba tafara zaro fruits d'in tana yankawa shi kuma yana dannah waya"parlourn ya d'auki kusan mintina 15 babu me mgn Acikinsu....dan Allah nidai na gama sai Ashafamun lafiya ko?"sauran kayan kuma yanzun danayi sallar la'asar zan Aza girkin"ta fad'a tana d'aukar robar ta shiga kitchen"bata jimaba ta dawo ta samu yana waya da mu'az"ta tab'e baki sbd jin yace"gata nan lafiya qlau indai wannan magulmaciyar ce"tokai kuma miye za'a kiraka dashi?"ta fad'a cikin masifa tana gallah masa harara"yanke wayar yayi ya kalleta ya saki murmushi "ke wai baki gajiya da masifa ne?"Eh d'in kayi maganina mana in zaka iya! ni kuwa keda hanyar yin maganinki"dan Allah idan kika shiga hannu zaki san ni yaro ne da hujjah"uhmm !saidai fa ni kasan ban cika gane magana Abaibaice nakeba" garama kiyita zahiri"ta fad'a tana kok'arin zama "karki zauna wuce muje muyi Alwallah lokacin sallar yayi"yadda yayi maganar cikin tsare gida yasaka ta kasa yi masa musu"saidai ta tab'e baki ta fito yabiyota suka nufi wajen tape d'in...ka fara mana"mudai fara"to wai dole sai tare dakai zanyi ne?"Eh mana keda baki gane ba sai yanzun?"in kuma Alluran kika fi buk'ata fine"ya k'arasa zancen yana d'age kafad'a"saida ta gallah masa harara ta murgud'a masa d'an bakinta sannan ta d'ebi ruwan ta watso masa daga fuska har zuwa jiki"ta d'auka zaiyi mgn saiya k'yaleta yafara Alwallah d'insa cikin nutsuwa"yayinda itama takeyi"bayan sun gama yasha gabanta yace"oya yi Addu'ar gama Alwallah malama"baza'a yiba....ganin ya matso gab da ita ya saka tafara karantowa"saidai yana lura bata son suna had'a Ido dashi ,saiya tab'e baki ya deb'o ruwan abazata ya watso mata.....shine ka jik'ani?"ke meyesa ni kika jik'ani?"ba kaine ka fara mun ba saina rama"shine nima na rama ai"baka isaba Allah nima saina rama"ta fad'a tana deb'o ruwan cikin tafin hannuwanta zata nufesa ya matsa Aguje yana murmushi "biyosa tayi da gudu Adaidai lokacin daddy ya kawo zai shigo cikin gidan.......��


Sharhi kawai 🤓�


wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: � *AGE MATE'S* ��♀�




*13&14*








*Littafin kud'i ne!*






.......turus sukayi gaba d'aya daga shi har ita suna yin k'asa da kawunan su"dan shi Dr darma ma sosa k'eya yayi Ahankali yace daddy sannu da dawowa"kafin ya Amsa Ahyaan tayi saurin cewa"daddy ka gani ya jik'amun jikina da ruwa ko?...ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon kanta...ita cefa ta fara jik'ani daddy"Allah ya gyara mun ku gaba d'aya"ke mama nah wuce ciki kiyi sallah zan had'u dashi"daga haka daddy ya wuce yana murmushi"darma kuwa kallonta yayi ya mata gwalo yayi tafiyarsa"ta raka bayansa da harara kafin ta juya ta koma cikin gidan"saida ta fara tashin hamza daga bacci da nufin yayi sallah sannan ta wuce d'aki tayi tata sallar"koda ta idar kitchen ta wuce ta kunnah gas guda biyu....cikin mintina 45 ta kammala farfesun kajine da kunun gyad'a"kasancewar dama sunyi girkinsu tun d'azun "bayan ta kwashe komai ta jera cikin basket,sai ta fito parlourn da robar fruid salad d'in zata zuba k'ank'ara "tana zama Khairiyyah babbar k'awarta na shigowa cikin parlourn"Tasha gayunta cikin Dubai Abaya"ah ah "k'awata! Uhmm naga Ai bakida niyar zuwa inda nake nace ni bara nazo muga juna Agaisa"wlh ba haka bane ko d'azun nacema mamy zanje gidanku tace sai gobe"ta k'are maganar Khairiyyah na zama gefenta tace"ohni k'awata kinga yadda kikayi kyau da gogewa kamar 20yrs??"dariya sukayi gaba d'aya"bayan sun gaisa ta kamata ruwa da farfesun...ta kalleta tace ga wannan kici k'awata " okay thanks"daga haka fara shan farfesun "uhmm gaskiya yayi dad'i sosai"wlh broth ne ke Azumi shine na had'a masa Abin bud'a baki harda farfesun"wai dama har yanzun beyi Aure ba?"tab'e baki tayi tana yamutsa fuska tace"duka duka guda nawa ne shi da zakiyi mamakin beyi Aure ba?"in ma bacin yanada girman jiki Aida ba wani babba bane"hmmm ! k'awata bakiji wlh "Nina jima rabon da na gansa ma"ba kwanaki da kikace yana inaba ? nace miki yana London karatun likitah?"Eh hakane"yama dawo be jimaba Ai"Masha Allah ! kice kunada doctor Agida"tab'e baki tayi sbd tunawa datayi d'azun ya fiddo Allura wai zaiyi mata"kinga dan Allah Adena zancen mugun yaron nan"lallai ma *beauty*(sunanta na skul) .dukda bansan yaya yakoma yanxun ba,Amma ko Abaya duk kallon yayanki muke masa balle yanzun da kikace ya gir...."mitsssssuww! kinga idan zancensa zakiyi bara natura Akirashi sai yazo kuyi fira"rufan Asiri sarkin masifa me yayi zafi?"canza topic d'in Ahyaan tayi da cewa Ina imaan?"tana wajen daddynta daya zo ya d'auketa week end"okay tace daga nan suka cigaba da wata firan.... Ab'angaren darma sai k'arfe biyar saura ya baro masjeed sbd ya tsaya yayi Azkhar da karatun Alkur'ani me girma "cikin gidan ya nufo ,saidai sashen su mamah ya dosa....zanci ubanki ko ki bani wayar nan wlh"kome zaka mun saidai kayi Amma bazan bayarba" saika fitomun da kud'ina dubu d'aya daka dauk'amun Ajaka"darma daya shigo ya tsintsi muryar su yaja tsaki yana yin sallama beko kalli gefen da Mubarak da Khadija ke tsaye suna sa'insaba"directly parlourn mamah ya dosa"Adaidai lokacin kuma ummah ta fito daga cikin d'akinta tabi bayan darma da mugun kallo kafin ta harari Mubarak da Khadija tace"shegu y'an banza! kuna jamun Abin fad'a bayan muna cikin sa'idnawa"zaka wuce ka fita ko saina mareka"yana gunguni ya fita"yayinda Khadija ta wuce d'aki "ita kuma taja kujerah ta zauna tana zaman jiran fitowar darma taga bazai gaisheta ba....mama na zaune tana Azkhar Atsakkiyar parlourn"sai Asma'u dake zaune tana Assignment"itace ta Amsa sallamarsa tana fad'in yaya nurah Ina wuni?"lafiya qlau Autar mamah"tayi murmushi tace"kaga Anty Ahyaan haushi takeji in Akace mun Autah....ke sarkin mgn wuce ciki "nurah sannu da zuwa cewar mamah bayan ta shafa Addu'a"yauwa mama Ina wuni?"lafiya qlau "mamy ta dawo ne?"ah ah gaskiya "naso muje wajen sunan to ciwon kai nake fama dashi"subahanallahi! bara naje yanzun naka maki magani"Ai nasha yama sauka"baka gajiya Nura da hidima Allah yasaka da Alkhairi yayi zab'in Aiki na k'warai "Ameen yah Allah mamah" dama wata mgn zamuyi"Amma dan Allah karki tashi hankalinki ko wani Abu"to shikenan Ina jinka"bayanin ganin da yayima Mubarak ya fara yimata....saidai kafin yakoma cewa wani abu mamah na murmushi tace"uwarsa ce ta saka yayi hakan"dama kuma raina ya bani zatayi makaman cin hakan sbd Abinda yafaru shekaran jiya "luba ta jima tana bina da sharri tuni na sani"kawai dai na barta itada Allah "Ina k'ok'arin yin Addu'ar neman tsari nida zuri'ata shiyasa ko tayi mugun Abin baya tasiri "ko wannan gudun Auren dak'in son maza da Ahyaan keyi sarai nasan itace tayi wannan Asirin"saidai nasan komai lokaci ne"da lokacin Auren nata yayi sai tayi.... Ajiyar zuciya ya sauke yana jin matuk'ar zafin luba Aransa "Anutse yace"dama na kaima wani malamin mu na islamiya duka layun ya duba"ya sanar mun sihirine gaskiya daya danganci haka"saidai tunda Antona Angano ba matsala"ya bani shawarwarin Abinda za'a yi"sbd gujewa duk wani mugun nufinta "dukda dai ga yadda na fahimta Ahyaan na sakaki da Azkhar"Amma rubutun dayace na dinga yimata da tofin Ayoyin karya sihiri cikin ganyan magaryar "zanyi in sha Allah kullum "saina baki mamah saiki bata tasha ta shafe jikinta"to nurah ubangiji yayi maka Albarka yabaka macen k'warai"Allah ya had'a mana kawu nanku ku d'ore da wannan zumunci"cikin nuna jin dad'in Addu'arta yace" Ameen" dan Allah ka dinga yima Ahyaan nasiha"ko yau da safe saida na mata fad'an yawo ba d'an kwali"saima tace kasiya mata huluna, nace taje ta saka"hakane mama bara na wuce ciki Amma ko mamy karkuyi zancen nan da ita, zata damu ko kuma ta sanarwa da Ahyaan d'in "to shikenan bazan sanar mata ba"dato ya Amsa ya mik'e tsaye yafita"mamah ta sauke Ajiyar zuciya Afili tace"na rasa gane kan yaron nan game da Ahyaan? "tunda ta dawo"zan dai biku da Addu'a"Ina mata kwad'ayin samunka Amatsayin miji domin nasan zatayi dace"saidai ita d'in da wuya tayi maka irin wannan kallon "saidai ita zatayi ta musu Addu'a"tuni take fatan idan yaran sun girma su had'asu Aure "sai kuma take gani kamar da wuya, musammun mace da tafi namiji girma"sai gashi shi ya fima Ahyaan d'in girma"sai wanda yasansu yake yadda ita sa'arsace"ita kanta yanzun so takeyi Ayima Ahyaan Aure kafin ta cika 30 yrs"kodan sbd gori da yada maganar da dangin Abba ke mata......
Dr Darma na fitowa daga sashen su mama Ahyaan da Khairiyyah suma suna fitowa da Alama rakkiya Ahyaan zata mata...siririn mayafi ne saman gashin kanta, tama cire hular,ga rigar Atamfar jikinta ta kamata sosai"yana ganin Khairiyyah ya sheda fuskar ta dukda ya jima be gan taba"yasan kuma tayi Aure"saidai shigar d'aya ganta da ita Ayanzun,ransa ya bashi da wuya idan tanada Aure gaskiya.daga ita har Khairiyyah d'in kallon second 5 ya musu ya d'auke kai cike da shan k'amshi sbd bema san ta kamasa raini gaban wata"saima yayi tsaye yana dannar waya"Ahyaan ta wani d'aure fuska tak'i kallon gefen da yake.....likitah bokon turai! cewar Khairiyyah data tsaresa da Ido tana mamakin ganin yadda yazama wani gentleman "yayi d'an murmushin daya masa kyau matuk'a yana fad'in kwana da yawa Khairiyyah?"wlh kuwa Ina wuni?"ta fad'a tana koma satar kallonsa tana kuma kallon k'awar tata, Aranta tana furta Masha Allahu! shidai da lafiya qlau ya Amsa daga haka be koma mgn ba"yana ta son su had'a Ido da mutuniyar tasa Amma tak'i yadda"ganin zasu wuce kuma bata damuba haka zata fita jiki bud'e ya sakashi had'e rai yana fad'in *Amun dago*! zo kiji wata mgn"saida taji fad'uwar gaba data juyo ta kallesa"ada masifa taso tayi masa Amma ganin yadda ya had'e rai saita daburce tama kasa yi masa musu"zo mana"to niba rakkiya zan mata ba"kije zan jiraki daga waje"cewar Khairiyyah tana tura k'ofar get ta fita"harara Ahyaan ta wurgo masa tana nufar gefensa taja ta tsaya tanata wani ciccin magani"kud'i y'an 1k guda biyar ya zaro daga Aljihun wondonsa ya mik'a mata had'e da cewa " ki bata tayi transport"to broth ta gode"ta fad'a tana d'an sakin fuska sbd taji dad'in hakan"karki nuna nine na bata ki bata Amatsayin kece"okay thanks"ki wuce ki koma ki saka hijab ko babban mayafi"Amma wlh ba zaki fita haka ba"ya fad'a yana shan mur ya wani matso dab da ita...wai dan Allah meyasa sai muna zaune lafiya kake son tado fitinah ne?"kece kike kallon haka"sbd nace ki rufe jikinki sbd shed'anu da kare mutuncinki da bin dokar Allah shine na tado fitinah?"batayi mgn ba rai b'ace ta nufi cikin gida"ya tab'e baki yana nan tsaye ta fito fuuuuu ta wuce kamar zata tashi sama ta wani had'e rai "tana sanye da d'aya daga cikin sabbin hijaban daya d'inka mata"shidai tab'e baki yayi yana tunanin bazai fasa kulawa da tarbiyan taba"da wannan tunanin ya nufi k'ofar d'akinsa, sbd yaje ya watsa ruwa ya tafi masallaci yayi zakirin kafin magrib.....da kallo kawai khairiyyah ta bita, sbd ganin yadda ta wani d'aure fuska da Alama ranta Ab'ace yake"ga kuma hijab ta ganta dashi bayan sadda suka fito ba dashi ta fito ba...kin gaji da jira ko? ta katse mata tunani "ah ah" nayi dai mamakin ganinki da hijab"wannan magulmacin ustazah d'in ne ya tilastani sakawa"wlh ina ga saina nunama yaron nan Ainahin true colour d'ina sannan zamu daidaita

Please Login or Register in order to submit comment