Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

junane tun suna yara har zuwa girmansu"haifaffun garin katsina ne kowa nasu na'a can"kabeer iyayensa na zaune Awata Anguwa me suna *DARMA* ! yayinda iliyasu ke zaune da iyayensa a Anguwar *sabon layi*".....tun daga primary school har zuwa secondry skul tare sukayi har zuwa jami'a"sun shak'u da juna da wani irin sabo da juna, kuma da wuya aji kansu saidai halin yau da gobe"suna zumunci tamkar y'an uwan juna ne"ga wani irin had'in kai suna dashi"duk sun taso suna kasuwancinsu da kuma Aikin gwabnati"har Allah yasa kabeer ya tashi Aure da matar da zai Aura wacce ke y'ar Kaduna"lokacin kuma harma sun kammala ginin gidajensu dake jere"sai suka zagayesa da get babba"lokacin shi iliyasu be fidda wacce zai Aura ba"saidai shima yanada niyar yayi idan yasamu wacce yakeso"kwatsam da aka tashi hidimar bikin kabeer da kyakykyawar matarsa Maryam(Mamy)" sai Allah ya had'a jinin iliyasu da babbar k'awar Maryam me suna zainab(mama)"Aikuwa Ana gama hidimar bikin kabeer da Maryam soyayya me zafi ta k'ullu tsakanin iliyasu da zainab"saidai iyayen zainab masu kud'i ne matuk'a"mahaifiyarta taci burin bayan gama secondary school nata taci gaba da karatu"sai mahaifinta ya Ankara da zainab na soyayya yace ta turo da wanda takeso yazo zasuyi mgn"Hjy Amina (Ammah) itace mahaifiyar zainab"macece me nuna Isa da gadara akan dukiya bata son had'a zuri'arta da talaka "saidai bata cika wulak'anta mutane ba"tunda ta fahimci iliyasu bamai dukiya bane shikenan ta nuna bata son Auren Amma mahaifin zainab Alh murtala yafi k'arfinta,kuma zainab nason iliyasu,gashi beda matsala mutumin kirki ne"hakan yasa Akayi wannan Aure"yazo daga baya yace"bazata cigaba da karatu ba"Abin yayima Ammah ciwo matuk'a ta kuma k'ullaci iliyasu"saidai baban bece komai ba"zaman farin ciki da kwanciyar hankali su zainab da Maryam suka cigaba dayi Agida Jen Auren su"dukda zainab tafi Maryam komai na kayan d'aki Amma Maryam bata tab'a damuwa ba suna zamansu tsakani da Allah"zamansu Awaje guda yasaka mutanan Anguwar ke kiran gidan nasu da suna *gida biyu*" Maryam data samu ciki saiya b'are tun kafin zuwan Zainab "sai gashi cikin ikon Allah bayan zuwan Zainab gidan ta fahimci tanada ciki"bata jumaba da fara laulayi itama zainab ta fara"haka sukayi zamansu su girka wannan su su girka wancan duk Abin kwad'ayi"sannu A hankali cukun nan nasu suka fara girma saidai cikin Maryam na gaban na zainab da wata guda"sai Akayi sa'a Maryam ta k'ara sati biyu sannan ta haifi santalelen d'an ta namiji kyakykyawa (Nura)"kwanansa 8 Aduniya zainab itama ta haifi y'arta mace kyakykyawar gaske(Ahyaan)"sati na zagayowa iliyasu yasaka mata suna *Aminatu*"sai mamy ta dinga kiranta da Ahyaan"dukda Ammah Ammata takwara ba taji iliyasu ya burge taba kullum kushesa takeyi.....yara suka taso cikin gata da kulawa"har sukayi shekara biyu"lokacin iliyasu da kabeer suka biyawa kansu makka"sai mahaifin zainab yabiya mata"kuka ta kamayi ita bazata jeba sai tare da Maryam"sai kuwa babanta ya biyama Maryam suka tafi tare....tun lokacin da Ahyaan da Nura suka fara tasawa Maryam ke nuna tafi jida Ahyaan"itama sai zainab ta janye Nura"har zainab ta k'ara haihuwar Abdul Aziz"Maryam kuma ta haifi khaleel "lokacin dangin Abba (iliyasu)suka taso zainab gaba da nuna mata k'i waita shanyesa komai takeso shi yakeyi,komai yasamu kanta yake k'arewa"yana k'ok'arin fahimtar dasu Amma sun k'i su gane "zainab naji na gani iliyasu ya Auri lubabatu d'iyar k'anwar mahaifiyarsa"ba k'aramin tashi hankalinta yayiba itada Maryam"Amma iliyasu ya kwantar mata da hankali "Ammah kuwa data sami labari tun daga Kaduna tazo har gida tayima iliyasu da Amaryar cin mutunci ta d'auki zainab ta tafi da ita"lokacin zainab nada shigar k'aramin ciki"Aikuwa Ammah taga b'acin ran mijinta irin wanda bata tab'a gani ba"gashi Abban ya kirashi yana masa kuka shifa yana son zainab ,gashi sanadin tahowarta itama maryam tace bazata zaunaba sai kabeer ya sallameta"ga Nura da Ahyaan sunata koke koken ganin basuga maman suba"sosai baba yayi fushi da Ammah "kwanan zainab biyu ta dawo katsina suka cigaba da zamansu"bata shiga harkan Amarya bata kuma yadda ta kamata raini ba"yayin da me gidan kamar ya goyata sbd so, baya son b'acin ranta"hakan kuma ba k'aramin b'acin rai da bak'in ciki yake saka luba shigaba"tama zata yadda takema iliyasun kallon yanada kud'i Awaje Ashe ba haka bane ba"komai nasa harda rufin Asirin matarsa"tana kasuwancinta ga iyayenta na taimaka mata"ko makkan dataje sun zata shine yakaita"dandanan luba ta sakama kanta hassadar zainab"lokacin da zainab ta haifi d'anta na ukku murtala(affan)"lokacin luba nada tsohon ciki na fari"bayan ta haihu ta gama wanka ta fantsama bin bokaye da malamai itada mahaifiyar ta innah salame "saidai koma sunyi Asirin be wani cika yin tasiri ba sbd zainab na tsaye kan ibada kuma iyayenta sun shirya mata jikinta ,hakama Abba"mama yaranta 5 gidan saidai yanzun hud'u ne Araye, Ahyaan, Abdul Aziz,Affan ,sai Autah husnah"Mamy nada yara biyar duk maza ,Nura, Khaleel, Isma'il,Abbas, sai Auta hamza"luba kuma tanada itama guda biyar, mata ukku maza biyu" Mubarak,Khadija ,usman,Fatima sai wacce take goyo yanzun maimoon"ba kuma ta da niyar dena haihuwar, idan son samunta ne tama k'ara biyar tafi mama y'ay'a Agidan shine burunta "wanda idan baka saniba ka shiga gidan zaka d'auka mama ce Amarya, luba (ummah) itace uwar gida"sbd yanayin jiki....
Ahyaan ta taso da wani irin masifaffan kyau"wanda An tabbatar duk layin su babu mace me kyau da aji y'ar kwalisa kamarta "wanda wannan kyawun nata ba k'aramin kona zuciyar ummah yakeba , musammun da ita nata yaron basuda wani kyau na Azo agani"ga zafin yadda mamy ta banbanta Ahyaan da sauran duka yaran dake zaune Agida biyu"wanda be saniba zai d'auka Mamy itace mahaifiyar Ahyaan sbd yadda ta shak'u da ita ta sake da ita kamar mahaifiyarta"dan k'aunar tasu daga baya data juya saima Ahyaan d'in ta koma sashen Mamy kasan cewar batada y'a mace"saidai dukda haka tana d'an zama sashen nasu"takuma koma ne sbd b'eran ta ya tafi London karatun likitah"kasancewar tunda suka fara tasawa suka zama kamar mage da b'era"Nura son girma ita kuma Ahyaan ta rainashi sai tace k'aninta ne shi"dukda sarai sunsan su Age mate ne Amma sai Ahyaan ta basar"sau tari idan suna dambe yasata kuka mamy zata rik'esa tace tazo tarama"haka zaisha kukansa da fushi dasun tafi skul yasameta yadaka"tun suna Abin wasa wasa har suka kai matakin yin SSCE basu dena fad'a da juna ba"dan ma Nura Mamy na tsawatar masa"sai Akayi sa'a yana gama secondary school yasamu scholarship daga gwabnati kasancewarsa givted sai yatafi London karatun likitah"Aranar har fad'a sukayi shida Ahyaan"ta salhesa ta gartse masa d'an yatsa harya fasa.....tun bayan tafiyarsa *Ammah* dake masifar jida Ahyaan ta turo kud'i aka sakata jami'ar ummaru Musa university"wanda dama Ammah taci buri babba akan Ahyaan"musammun da taga yarinyar nada wani irin sihirtaccen kyau "shikenan saita dinga yimata hudubar tsiya kan ta bari saita gama karatu ta sami Aiki" sannan ta samu wani me kud'i ta Aurah"bazata bari yadda mamanta ta kashe rayuwarta ta Auri talaka ba itama ta Auri talaka ba"itadai Ahyaan saidai tayi murmushi sbd bataga talauci Awajen mahaifinta ba"iya bakin gwargwado yanada rufin Asirnsa,i babu rashin ci ko sha ko surutu"har motar hawa garesa"yasiya ma Abdul Aziz mashin shida Nura "ko karatunta danma Ammah taji tagani da shine zai biya mata"Ayanzun haka Mubarak yana Aji biyu FCE"wanda luba taso y'ar Adu'a university aka sakashi Amma Abba yak'i ya yanuna beda halin sakashi"yanzun kuma Khadija na SS3 Tasha Alwashin kota halin k'ak'a sai An kaita y'ar Addu'a university...tun tasowar Ahyaan masoya sukayi mata caaa"saidai Abin mamaki duk mesonta shine mak'iyinta"zata rufe Ido taci mutumcin mutum"shiyasa wasu badan sunsoba suke ja baya da ita"mama da mamy sunyi fad'an sun gaji"Amma Ammah dake Kaduna goyon bayanta takeyi"da k'ara shagwab'a ta"komai budurwa y'ar gata ke buk'ata sai Ammah da Mamy da daddy(mahaifin Nura) sunyiwa Ahyaan"shiyasa idan ta fita waje zaka d'auka y'ar wani hamshak'in me kud'i ce ita"sbd kyawun jiki da manyan suturu datake sakawa"yanzun haka data gama service nata uncle mustapha k'anin mama yasiya mata mota me tsada zai turo mata da ita data samu Aiki zata dinga hawan Abinta "wannan gatan da Ahyaan ke samu ba k'aramin zafinsa luba da sauran dangin Abba keji ba"dasu kansu y'ay'an luba d'in da itace ta hure musu kunne basu ganin kowa da gashin Arzik'i "wai Abba yana son kai yafi son mama sbd ita y'ar masu kud'i ce umman su kuma y'ar talakawa ce"haka su Mubarak ke fad'a......ummah taso ta had'e kai da mamy su zalinci mama sai mamy tayi mata tas ta nuna ita ba haka take ba"saima k'ara Jan mama tayi suna cigaba da Amincinsu"ummah taso itama Mamy Ayi mata kishiya kodan ta had'e kai da kishiyar"sai kuma Allah yasa ba'a yi mata ba.....Nura tun yanada 15 yrs yayi saukar Alkur'ani me girma"yanada 17 yrs ya haddacesa"lokacin da yake da 20 yrs yasan littattafai na Addini da dama"kuma koda yakoma London be fasa neman ilimi ba"yanada ilimin Addini sosai dukda be cika nunawa ba"yakuma kammala karatunsa na likitanci cikin samun nassara"Wanda takaranci fannin mata"yanzun Aiki ya rage masa"shima kuma takardunsa da komai na gidan gwabnati kira kawai yake jira"tunda yadawo yasami sabon mashin d'in da Abba yasiya masa"daddy kuma yabud'e masa babban chemist"acewar su gara ahada' da kasuwanci"tunda yadawo yaje yaga filinsa daya turo ma mu'az kud'i yasiya masa"bayan yaje ya gani,yafara zaton yanzun ginashi zai farayi"dukda yanaso yayi surprise na iyayen nasu saidai kawai su ganshi ga gidansa "yana jin tausayin su ,yanada burin ya kyautata musu da guminsa kodan sbd su huta suma"yadda ya d'auki daddynsa haka ya d'auki Abba"Mamy ma yadda ya d'auketa haka ya d'auki mama"ummah kuwa iyakarsa da ita gaisuwa tunda yadawo sbd ya fahimci ba mutuniyar kirki bace matar"befi 5 days da dawowa ba mu'az ya rok'esa Alfarma ya dinga koyarwa Ajin matan Aure na islamiyar da mahaifinsa ya bud'e"saiya nuna bazai iyaba"kawai dai zai dinga yin wa'azi duk ranar Wednesday,ya kuma Amsa tambayoyin addini"yayi hakane sbd yayi baya da mata"kuma zata yuyu idan yafara Aiki bazai samu lokaci ba"ko wa'azin ze yine sbd A, Amfana da iliminsa"tunda ya dawo ya saka Aka gyara d'akinsa"Aka saka soma sbd tasu ta lalace"ya kuma canzawa Mamy da mama kujeru saidai banda ummah😂"ta kuma shak'a sbd har Abba tayima mgn"saidai bece komai ba" kasancewar daya tafi can yana kasuwan cinsa ta online yaturo kaya zuwa nan"tunda ya dawo Nigeria be tambayi Ina Ahyaan ba? babu kuma wanda yamasa zancenta"saidai sarai yasan tana KD can take service nata"ta kuma zauna gidan ka kanninta"sau guda yayi wa'azi sati na farko saida ya gwammace dama beyiba sbd matan da suka dinga kiransa da turo masa tambayoyi"wasu da yawa cewa suke suna sonsa"saidai yaja tsaki"dan shi bema fara soyayya ba"yana dai da friends mata kawai "har turawa da yawa suna nuna suna sonsa koda zasu dinga Aikata Alfasha"duk wacce ta masa irin wannan zancen saita gane kuranta"tun yana can Aka saka ranar bikin mu'az babban Abokinsa wanda shima tare sukayi primary school har zuwa secondry skul "zuwansa London ya rabasu"shi yanzun mu'az Aikin banki yakeyi kuma iyayensa nada kud'i...... wannan kenan Anan gaba zakuji wani abun..


Cigaban labarin.......��


wannan book d'in na kudine !
Regular grp 500
Vip grp 1000
Special grp 2k wato 3pages in a day


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251 500 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira�


Y'an nijar kutuntub'i wannan n👉 +227 88 01 90 50


Regular 300f
Vip 700f
Special grp 1500f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: ����������


��AGE MATE���♀�


����������


Story & written by mommyn fareesa




*Dominki* my beloved sister hafsat Aliyu D 🥰 Allah yabaki miji na gari


Dedicate to all my commenters 💖😘Ina yinku irin sau trillion d'in nan


Free page 5&6


*cigaban labarin*.....koda ya gama parking d'in kin mgn yayi sai yama cigaba da danna waya "mu'az yayi murmushi kawai yana kallon Ahyaan da tacika tayi fam da rainin wayon Darma Anutse yace"karki damu Ahyaan fita muje ku gaisa da ita"inaso keda ita ku zama friends"ya k'are maganar yana kara wayar sa gefen kunne ya fito daga cikin motar da Alama Fatima yake kira"Ahyaan kuwa tsaki taja tana fad'in wlh mu zuba nida mutum....waye kike ma tsaki? ya fad'a murya Adake"ya juyo yana binta da wani razanan nan kallo, sbd ya tsani Amasa tsaki"cike da rashin kunya ta d'ago kanta suka had'a Ido! Duk sai taji ta daburce saboda mugun kwarijinin daya mata da cika waje... Amma dukda haka saita zabga masa harara tana janye Idanunta tace da wanda ya tsargu nake"Azuciye ya fito daga cikin motar har huci yakeyi ya nufi back sit d'in Azafafe"Adaidai lokacin kuma Fatima ta fito daga cikin get d'in gidan su"mu'az nata k'ok'arin dakatar dashi Amma yamasa banza ya bud'e k'ofar"Ahyaan kuwa ta gudan gefen damarta ta bud'e tayi wuf ta fito sbd tsoron Abinda zai mata musammun da taga ta fusatashi"saidai zuciyarta fes da fushinsa tayi tsaye daga gefen motar "be hak'ura ba sai nufarta ya komayi"ta wani tsuke fuska murya can ciki tace"wlh kana cin zalin nawa ba k'yaleka zanyiba saina rama na kuma baka kunya gaban yarinyar "ta kare maganar tana tab'e baki ta wani ci face "d'an dakatawa yayi domin zancen gaskiya beson mutuncinsa ya zube a idon Fatima, musanmun da yau ne zai fara had'uwa da ita"saidai da yake kaifi d'aya ne saiya nuna kamar zancenta be shige saba ya koma had'e rai yana tunkaro gefenta"itama saita dake ta tsaya tana satar kallon mu'az da Fatima da suke kashe juna da murmushi"ta tab'e baki Aranta tana fad'in" *jikinki yakeso* "sbd Aganinta duk idan namiji yace yana son mace tofa jikinta yakeso....wuce muje! sautin sanyayyar muryarsa me cike da dattako ta katse mata tunani "k'in kallonsa tayi"shi kuma be damuba ya matso ya finciko hannunta "kaga bansan wulak'anci Akanme zaka wani dinga tab'amun hannuna?"ko dama London d'in dakaje tab'ara ka koye ne?"idanma Akwai Abinda yafi tab'ara duk na koyo kuma Akanki zan sauke Abinda na koyo d'in"saidai da Alama har yanzun naga kanki na rawa"Amma fa Ashirye nake dana saita miki shi"ya fad'a normal tamkar maganar Arzik'i sukeyi"ita kanta Fatima ta d'auka masoya ne wuf d'aya data kallesu.....zaki wuce muje ko kuwa saina jaki ta k'arfi ne?"d'an murmushi ta saki me sanyi da yayi mata wani irin kyau kamar me rad'a tace "kaima kasan dama idan bata k'arfin ba Ai baka Isa ka tur sasani da kurin kaba har naje "mezai hana ka dena nuna k'arfin "*many Ansha tatala*" ?ta kare maganar tana kecewa da dariya domin tasan ta k'ulesa data fad'i hakan daga k'arshen maganarta ...."tun yana yaro haka yake cewa idan zasuje siyan k'ank'arar kwarbebe"sau d'aya ya kalleta ya maida idanunsa k'asa bece komai ba, saidai yata naji Abinda zai mata da saiya sata kuka"duk yadda taso taga ya fusatu k'in nuna ya fusatun yayi, be kuma cika hannun nata ba yajata da d'an k'arfi suka nufi wajen su mu'az dake tsaye gefen get d'in gidan su Fatima suna mgn.....kaga bansan iskanci ka cika mun hannuna mana"ta fad'a tana son turjewa"tamkar da bango take mgn haka yamata banza"kasan Allah cizonka zanyi! duk ya share yanama kallon wani wajen"saida suka iso gefensu yad'an saki fuska yana musu sallama"Fatima ta Amsa tana murmushi tace"na d'auka Ai bazaku iso da wuri ba sai Angama firan soyayya?"ya mutsa fuska Ahyaan tayi tace"Allah ya kiyaye nayi soyayya da k'a.....nayi soyayya da d'an uwana"ta furta ba shiri sbd wani Arnen mintsini da darma yasakar mata gefen hannunta"gurin har saida yayi ja"kasancewar ta chacoolate colour ce itama fatar jikin ta.... mu'az kuwa dariya ya kamayi sbd jikinsa ya bashi wata muguntar Darma yamata shiyasa tak'i furta Abinda tayi niyar fad'a tun farko"saita canza "Amma sbd kafiya irin tata sai ta kasa cewa yayanta ta juya zancen zuwa d'an uwanta....Masha Allah! Ashe yayanki ne? na d'auka Ai masoya ne ku"Ina wuni ya gida??"ta fad'a tana yaba tsarin had'uwar Abokin mijin nata dashi da sister nasa"Anutse darma ya Amsa mata da tambayarta y'an gida kafin yasaka hannunsa ya d'alli lips d'in Ahyaan yana fad'in baki iya gaisuwa ba?"bata kallesaba Amma taci burin saita rama"saita d'an yi murmushi tare da cewa na bari ku gama gaisawa ne"hakane Ahyaan "my princess ga Ahyaan nan Ina fatan zaku zama friends da ita"cewar mu'az"in sha Allah "ya gida yasu mama?"cewar Ahyaan "Fatima ta Amsa cike da kulawa tana fad'in zo muje ciki ku kuma kuje kuyi sallah"dukda Ahyaan bata so shiga ciki ba kodan sbd karta bi umarnin wannan d'an iyayin Amma saita nuna zata bita da nufin idan sun tafi ta fito ta hau Adaidaita ta koma gida"sai ta koma had'a masa bom wajen Mamy"duk Darma na hankalce da yanayin ta,kuma jikinsa na bashi Akwai Abinda zatayi idan sun tafi yasanta da shegiyar kaffiya kan ra'ayinta"kallonsa tayi ta zabga masa harara tana fad'in bazaka cikamun hannun ba?"be cikaba sai matsowa yayi da fuskarsa dab da tata murya can k'asa yace"kinsan Allah idan muka tafi na dawo na samu kin gudu zane miki jiki zanyi muka koma gida"karkiga kin koma wata y'ar lukuta kiyi zaton bazan iya hukuntaki ba......tsabar yadda ya kasheta da takaici kasa mgn tayi sai Ido kawai"ga k'irjinta nata fat fat fat!! sbd kusancinsu da yayi yawa"ga fad'uwar gaba datake ji"itadai Fatima na tsaye tana satar kallonsu zuciyarta na mata kokonton bata yadda shida ita yaya ne da k'anwa ba saidai ko cousin d'inta neshi"mu'az kuma yasha Alwashin yimata baya nin dangan takarsu daga baya.... Ajiyar zuciya Ahyaan ta sauke sbd cika mata hannunta da yayi"Fatima ta matso tana murmushi taja hannunta suka wuce cikin gidan"tana lura da darma na Aiko ma Ahyaan da harara......sosai Ahyaan ta yaba da kirkin y'an gidansu Fatima"badan tasoba tabi fatima d'akinta sukayi sallah"kafin su gama mamanta ta shiryama Ahyaan Abinci da lemo da ruwa"kasancewar yunwa takeji ga gajiyar mota saita daure ta fara cin Abincin suna fira da Fatima"Ahaka kiran Mamy ya shigo cikin wayarta k'irar IPhone 11 11"d'an murmushi tayi ta d'auka tana fad'in Mamy nah?"daga d'ayan bangaren Mamy ta sauke Ajiyar zuciya tace"Ahyaan duk na damu da naji shiru saida na kira Nura yanzun yace mun wai kun biya ta gidan su yarinyar mu'az zaku gaisa da ita?"Eh hakane Mamy"Ina fatan sababben me miki wani abu ba?"be yimun komai ba Mamy yanzun ma zamu taho gida sun tafine suyi sallah shida yaya mu'az"Amma ga Fatima ku gaisa"ta k'are maganar tana mik'a ma Fatima wayar"ta Amsa suka gaisa da mamy Amutunce kafin suyi sallama"ba'a fi mintina ukku ba da gama wayar tasu ba mu'az yakira yace su fito zasu tafi"Ahyaan ta wani tsuke fuska tana fad'in wlh saina b'ata masa lokaci "saida Fatima ta kashe wayar ta kalleta da murmushi sbd ta fahimci Ahyaan zata girme mata"wai dan Allah keda darma da gaske y'an uwa ne?"uhmm! Amma causin d'ina ne"daga haka tayi shiru taci gaba dacin Abincinta.....sau biyu mu'az na koma kiran su fito Amma Ahyaan tak'i fitowa"ba k'aramin hassala gogan naku yayi ba"sbd yana so yakoma gida yanada uzurin da zaiyi"ya lura saiya biyoma yarinyar ta bayan gida tukum zasu daidaita"Ayanzun beso ya tafi yabarta sbd yasan saiya sani Awajen Mamy"musammun data kirashi yanzun taji lafiya basu isoba sai fad'a take masa"wannan dalilin kawai zai saka ya jirata Amma zata gane kuranta..... gaskiya *Darma* baka kyautawa ko kad'an!ya wuce Ace har yanzun kaida Ahyaan kuna irin y'ar haka tsakanin ku.....kaga mu'az ka rabu dani "sanin kankane bazan d'auki rainiba"Agabanka fa yarinyar nan kemun Abinda ta gadama kana wani bata hak'uri"d'azun harda kama yimun dariya ko?"mu'az na k'ok'arin mgn Ahyaan da Fatima suka fito daga cikin gidan.....kicin kicin darma yayi da fuska beko kalli gefen da take ba, cike da shan k'amshi yace"princess d'in Abokinah zamu wuce"to shikenan ustazah muna godiya da ziyara"d'an murmushin gefen baki yasaki tare da cewa abakin Abokinah kikaji wannan sunan ko?"Eh mana"duk sukayi murmushi Fatima ta rakosu gefen motar ta musu godiya bayan ta Amshi contact d'in Ahyaan sannan ta wuce ciki"wannan karon mu'az ne yashiga driver sit sbd yasan halin mutumin nasa yadda ya shak'a d'in nan zai iya zubar dasu kan titi "saidai ganin Ahyaan taja tayi tsaye tana danna waya yasaka shi fad'in tsayuwar me kikeyi da bazaki shiga mu wuce ba?"ya mutsa fuska tayi tak'i mgn tana cigaba da Abinda takeyi"Afusace ya matso ya bud'e k'ofar back sit d'in "yana k'ok'arin kama hannunta da nufin yaturata ciki sai tayi wuf ta shige ta zauna tana yatsina tace" thanks my k'ani ,dama na tsaya saika bud'e mun k'ofar saina shigo"ta k'are maganar murmushi na sub'uce mata ",duk yadda mu'az yaso danne dariyarsa kasawa yayi saida ya fara"saidai DARMA bece musu uffan ba daga shi har ita"ya zagaya ya shige gefen me zaman banza zuciyarsa na k'una tare dashan Alwashin yanzun suka fara wasan zai barta tayi iya nata idan Aka fara nashi tofa ta shiga ukku"har suka doso cikin layin Anguwar tasu babu me mgn Acikinsu"tun kafin ya gama parking Darma ya bud'e k'ofar ya fito ya wuce cikin gida ko sallama be masaba sbd ba k'aramin haushi yabashi ba"yayinda Ahyaan zuciyarta fari k'ar ta fito tana fad'in dan Allah yaya mu'az bara na turo Ad'auki troley d'in kayan nan"dato ya Amsa ta masa godiya ta fito cikin takunta na Isa tamkar wata tarwad'a haka ta nufi bakin get d'in gidan nasu very slowly "mu'az ya bita da kallo ya girgiza kansa yana mamakin ko tsinin takalmin k'afarta basu takurata wajen tafiya, kamar bada takalmi me tsini take tafiyar ba"may be ta riga ta saba saka irin su"ya fad'a Azuciyarsa...... Akan idon babban yaron Mr mahuta dake bibiyarsu tun d'azun ta shige cikin gidan nasu"hakan ya tabbar masa da cewa Anan ne gidan su"sai kawai yaja nafef d'in ya wuce da nufin zuwa yamma sai ya dawo yayi binciken wacece ita,miye Alak'arta da darma??wanda Mr mahuta ne yabasa yin wannan Aikin.....kai tsaye sashen mamy ta fara nufa cike da kewarta"batama fara nufar sashensu mama ba"mamyn na zaune a parlourn tana lazimi da Alama sallar Azahar ta idar"Darma na zaune gefen kujerah yacire p.cap nasa ya aza k'afa d'aya kan d'aya goran ruwa me sanyi Ahannunsa yana sha"sai tambayarsa Ina Ahyaan d'in mamy keyi ?sau d'aya yace gata nan zata shigo.....Mamy najin sallamarta ta mik'e tsaye cike da murnan ganin y'ar tata tana fad'in ga Ahyaan d'in Mamy da daddy"da gudu Ahyaan d'in ta rungumeta tana fad'in I miss you so much my mamy! ta k'are maganar suna cika juna suka zauna kan kujerah"Ahyaan na d'an murmushi ta wani baje kan kujerah tana kallon parlourn sbd yadda ya canza mata"Ahankali tace"Ayyah broth troley d'in nacan Amota yamun nauyi bazan iya d'auka ba pls"ta k'are maganar cikin marairaice murya"Aranta dama Tasha Alwashin shine zai koma ya d'akko mata shi "d'ago kansa Darma yayi yabita da kallo saidai tak'i yadda ta kallesa"jin yayi shiru yasaka Mamy cewa katashi mana ka shigo mata da troley d'in "beyi mgn ba yanata cin magani ya mik'e tsaye Ahyaan ta kallesa suka had'a Ido"gwalo ta masa ta d'auke kai tana fad'in Mamy su khaleel fa?"sun tafi skul harma Autah"dukda yanata murnan dawowar ki"Allah sarki baby hamza"Amma mamy parlourn nan yayi kyau wlh "Eh Nura ne yamasa wannan gyaran"gaskiya broth ya kyauta daya k'ara gyara mana parlourn mu"ta fad'a cikin jin dad'i"Adaidai nan
ya shigo cikin parlourn rik'e da troley d'in kayanta yana turowa"Amamakinta fuskarsa bbu irin d'aurewar nan"sai kuma taji gabanta yafad'i! kodai ya shirmun wani abun ne?"ta tambayi kanta"sai kuma ta basar dashi cikin jin k'warin gwiwar ganin daidai take dashi"har d'akin baccin mamy ya shigar mata da troley d'in kafin ya dawo inda ya zauna ya d'auki p cap d'insa"itadai tana satar kallonsa tana mamakin yadda ya koma yakuma canza.... Ahyaan tashi kiyi wanka kici Abinci?"to mamy Amma Ak'oshe nake sai Anjima zanci"to shikenan me kikeso na k'walama sai Asiyo miki?"kauda kansa Darma yayi ya mik'e tsaye da nufin yanufi

Please Login or Register in order to submit comment