Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idonta ta shige parlourn mamah.....Hjy Ammah kyakykyawar tsohuwa"meji da izzah da Isa "tana zaune hakimce kan kujerah sanye da wata super me tsadar gaske"dukda tafara tsufa Amma son Adonta da kwalliyarta na nan"da Alama Anan wajenta Ahyaan ta gado izzah"fuskarta na mak'ale da medical glass fari, sai k'aramar waya baby Nokia na hannunta "yayinda kan Ahyaan ke saman kafad'arta tanata zuba mata shagwab'a"mama dai na zaune tana kallon su tana kuma kallon TV "Ahaka Mamy ta shigo cikin parlourn da sallama"Ahhh Maryam ki koma kawai"da Ina cewa bara nina zo na gaisheki"haba Ammah! Nina isa nak'i zuwa ne"na bari kud'an hutane shiyasa"ta fad'a tana duk'awa ta gaida ita cikin girmamawa tare da tambayar mutanan gida"ta Amsa da Alhamdulillah" Ina likitah bokan turai ?"gaba d'aya ya manta dani na rasa wane irin Aure ne wannan? mamy na murmushi tace"yana nan Ammah dole yazo yakawo gaisuwa"to da yake yatashi yau bejin dad'i "subahanallahi! meke damun sa?"cewar mamah"Ahyaan tace zazzab'i ne harda Amai yayima d'azun"Allah yasawaka ya bashi lafiya"cewar Ammah"mama na k'ok'arin mgn kiran Abba ya shigo cikin wayarta"saita d'auka tayi sallama"daga bisani kuma tace"Eh"daga haka ta yanke wayar suka d'an tab'a fira da mamy "kafin mamyn ta tafi"bata juma ba saiga hamza Autah yadawo rik'e da tray me marfi shak'e da snacks inji mamy Abama Ammah"baki washe ta Amsa tana godiya"bayan yaron ya fita ya sake komowa rik'e da leda bak'a ya kalli Ahyaan yace"inji yaya nurah yace" kiyi masa farfesu ki zuba yaji bakinsa ba dad'i"dato kawai ta Amsa tana karb'an ledar "Adaidai lokacin Abba da dr darma suka shigo cikin parlourn"Ahyaan tayima Abba sannu da zuwa "ta saci kallon mutumin nata Ashe ita yake kallo"broth ! uhmm "ya jikin?"da sauk'i "bata koma mgn ba ta mik'e tsaye tana d'an murmushi sbd jin yadda yaketa tsokanar Ammah da tayi kicin kicin da rai sbd ganin Abba"ita wlh tsohuwar har mamaki take bata"ta rasa me mahaifinta yakashe mata Arayuwa??.....sau kusan ukku Abba nayima Ammah sannu sai tayi kamar bata jiba ta biyema Dr darma suna surutu"mama tayi k'asa da kai gabanta na fad'uwa "lura da Abba na mgn yasaka Dr darma ya fita yana murmushi...Hjy sannu da zuwa"da k'yar tace yauwa"bayan sun gaisa shiru ya biyo baya"cike da isah Ammah tace"dama nazo ne Akan batun yarinyar nan Ahyaan"Alhamdulillah! tayi karatu ta gama ,gashi ta samu Aiki"to shima mijin ta samu"inaso ko bayan Auren Amata transfer d'in Aikin zuwa can kd sai ta dinga yi tun yaron Acan yake kuma nan zasu zauna"shidai Abba shiru yayi sbd yakasa fahimtar zancen nata"idanma ya fahimta to waye wanda takeso Ahyaan d'in ta Aurah?"....yauwa iliyasu Akwai yaron dana yaba da hankalinsa Abokin mustapha ne kuma yana sonta sosai"to shine nakeso yazo kuyi mgn yaji yaushe zai turo iyayensa?"yaro ne saurayi ya jima beyi Aure ba"yanada Abin hannunsa,kuma d'an boko ne"sanin kankane na tsayama Ahyaan tayi karatu bazan bari tayi Auren wahalaba kamar yadda zainab tayi.... d'ago kanta mama tayi sbd rashin jin dad'in kalaman Ammah"Abba na lura da ita tana girgiza mata kanta da kyafta mata Ido"ya saki murmushi me ciwo be furta komai ba"saidai yaci burin nunama surukar tasa iyakarta"jin tayi shiru Alamar tana son jin ta bakinsa sai yayi k'asa da murya cikin ladabi yace"to Masha Allah ! zan kira Ahyaan gabanki naji idan har tana sonsa "idan har yamata kuma nayi binciken halayen sa sun min to zan bashi ita"oh wato mu bamu iya bincike ba kenan?"sannan wayace sai Anji ta bakinta?"yayi shiru"dakai nake mgn"gaskiya Hjy saidai kiyi hak'uri sai naji ta bakin yarinya tukum"zancen yanada dukiya be dameni ba"dana bama me kud'i y'ata ya wulak'anta, gara na bama me rufin Asiri ya kula da ita da rik'e mutuncinta.... Ak'ule Amma ta d'ago kanta da nufin ta sauke masa kwandon masifar dake ranta sai uncle mustapha ya shigo"wanda daga shashen mamy yake, yana can shida ita sun tasa Ahyaan Agaba"harda kukanta da rantsuwar bata son Abokinsa Ahmed "kadawo ne?"Amma ka jima"cewar mamah"beyi mgn ba ya zauna suka gaisa da Abba cikin girmamawa har saida shi Abban da ita kanta maman suka ji dad'in hakan"kafin ya kalli mama yace"Anty zainab Ina can shashensu Anty Maryam Ina fama da Ahyaan ita bata son Ahmed"tsaki Ammah taja tana fad'in matsalarta ce"ita ta sani tunda tafi son tayita zama Agida ko kuma tayi Auren fatara"na rasa wace irin zuciya ce da yarinyar nan ana nuna mata gabas tana canza hanya?"to nidai bada gummu ta gado wannan mugun halin ba....Hjy ya Isa haka pls"cewar uncle mustapha sbd yasan halinta ba k'aunar Abba takeba tuni"sosai Abin ya faranta ran Abba"yaji dad'i da Ahyaan ta nuna bata son zab'in Ammah"Anutse yace"to Hjy kinji bayanin mustapha? sbd haka bama saina tambayeta ba"tundai bata so inaga Ayi hak'uri Allah yabata Wanda yafishi"sbd zancen gaskiya bazan yima y'ata Auren dole ba"mitsssssuww! kai tashi muje"Abba beyi mgn ba ya mik'e tsaye ya fita ransa Ab'ace "uncle mustapha na ganin ya fita ya fara fad'a rai b'ace yake cewa Alamomi sun nuna zancen kika masa bayan nace ki bari nazo Ayi mgn Agabana"wai meyasa kike haka Hjy ne hjy?"so kikeyi yaya iliyasu ya dena ganin mutuncinki.....saime idan ya dena ganin mutuncin nawa Allah na tuba? wlh idan naga dama sai nace yasakar mun y'a wata tsiyace"talakan banza da wofi"mamah dai ranta yab'aci sosai tayi dai shiru sbd gudun kar tayi wani Abu cikin fushi tazo tayi dana sani...dana san haka zakiyi daban biye miki nazo ba"kuma wlh Alh (mahaifinsu) yasan kinyi hakan kinsan yadda zaku kwashe"sbd haka tashi muje gida nasan zuwa 7pm mun iso gida"Anty zainab kiyi hak'uri dan Allah "kuma hakan bazai koma maimaita kansa ba"wanda Ahyaan ta kawo in sha Allah shine za'a bata"karki damu zan kirashi ta waya"Ammah ta mik'e tsaye tana gyara mayafinta tace"idan kin gama fushin juye mun snacks d'in aleda babba na wuce da Abina"ke y'ar dad'i miji sbd shi kike wannan fushin ko?"sai kace wata uwa ya miki Arayuwa...dan Allah Hjy kiyi shiru"ta tab'e baki batace komai"mamah ta juye mata ta mik'a mata ledar ta Amsa tana musu Allah ya tsare hanya"har bakin get ta rakosu ,tana gani Ammah ta hana uncle mustapha zuwa yakira Ahyaan suyi mata sallama"saidai batace komai ba ta wuce cikin gidan"su kuma suka fita wajen get inda motarsu take..... Misalin k'arfe 4:13 pm"Ahyaan na zaune d'aki ta gama sallar la'asar kenan" fuskarta bbu walwala sbd uncle mustapha yabata haushi"hamza ya shigo d'akin da yunifoam Ajikinsa yace Anty Ahyaan yaya yace kizo yana can zaune k'ofar d'akinsa"dato kawai ta Amsa ta tashi ta maida kayanta na d'azun"ta gyara d'aurin d'an kwali ta fito"ta kalli mamy suka had'a Ido"mamy zanje wajen broth"saikin dawo Ahyaan"naji Ai sadda yaturo hamza"Amma ki dena wannan fushin tunda dai kin nuna bakyaso shikenan"fatanmu Allah yabaki nagari"duk zagaye zagaye da guje gujen masoyanki da kikeyi da lokacin Auren yayi za'a yi"d'an murmushi tayi tace ba Amma bace duk keso"uhmm kawai mamy ta furta"ita kuma ta wuce kitchen ta d'auki basket d'in data shirya warmer d'in farfesun ciki"ga plate da service spoon ta saka"ledar bread sabo guda da ba'a tab'a ba ta d'auka ta saka masa"sannan ta d'akko goron ruwa da lemo fanta na gwangwani duk ta saka ta fito"mamy dai na zaune tana kallon ta Aranta tace" sun shirya kafin su koma b'atawa kuma"Allah dai ya shiryamun yaran nan......��




wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: *Littafin kud'i ne!*


.......Cike da nutsuwa had'e da sanyin jiki take tafiyar tana tunanin yadda zasu kwashe da Ammah idan taji labarin ta nuna zahiri bata son Alh Ahmed.tasan dole sai tayi dogon fushi da ita"hakan kuma be dameta ba, sbd ba zata cutar da kantaba ta zab'i namijin da bata ra'ayi ba"iya Abinda ta sani bata ra'ayin cewa dole sai mai kud'i zata Aura "indai namiji nada halayen kirki kuma yamata tana sonsa,taji ta yadda zata Auresa kud'insa ba damuwar ta bace"haka ka zalika in har yamata ko yanada kud'i zata iya Aurensa.....tunda ta doso inda yake,gaba d'aya ya maida hankalinsa gareta sbd ya fahimci tunanin zuci takeyi"shi kansa waya yakeyi da Ikkhee "wacce tafi wata 2 rabonda ta kirashi sai yau data kasa jurewa ta kirashi suna gaisawa"saidai yana ganin Ahyaan yama manta da wata waya"sai furta hellow! Hellow!!takeyi Amma Anyi shiru"hakan yasa tak'i yanke kiran tana dai son jin meyasa yayi shiru? sbd ranta ya bata ba matsalar net work bace.....Dr darma kuwa janye idanuwansa yayi sbd ganin tana gab da isowa gabansa"saiya basar yana d'an shafa lallausan gemunsa yana furta"*Amun dago*! numfashi ta sauke ta Ajiye basket d'in saman center table d'in data gani gabansa ,saita zauna gefen sa tad'an dubesa suka had'a Ido"shine Ammah ta tafi koki sanar mun nazo muyi sallama da ita?"wai da gaske kakeyi broth ta tagk?"nifa bansan tama tafinba sai yanzun daka fad'a"shine ta tafi babu sallama sbd tana fushi dani ko?"ta kare maganar cikin shagwab'a kamar zatayi kuka "shi kuwa uban gayyar ya zuba Ido yanata Aikin kallonta"Atake ya fahimci tayi kuka "kukan meye kikayi keda baki gajiya da saurin kuka??"ya furta Afili ,wanda Azuci yaso yayi maganar"ita kanta Ahyaan saida taji k'irjinta ya buga"ga muryar tasa ta saka mata jin kasala"saita kasa mgn ta sunkuyar dakai"tambayarki nakeyi fa?"ya fad'a yana dannah waya"Abin mamaki yaga Ikkhee bata yanke wayar ba"sai yaja tsaki ya kashe wayar"okay tunda tsaki kake mun bara naje na baka wane, zuwan nawa beda Amfani "ta fad'a ranta Ab'ace zata Mike tsaye"bece komai ba sai wayar tasa daya Aza mata saman cinyarta ya nuna mata da hannu"saita tab'e baki ta kalli fuskar wayar taga number d'in Ikkhee da baiyi seving ba"ga just now ! Alamar yanzun suka gama waya"saita tab'e baki ta fara k'ok'arin ture wayar"nifa da wata nake bada keba ko *bestie*? Ai fushi ba naki bane keda kike da patient"dukda kin tafi kin barni har saida na Aiko kizo kuma"yanzun haka Ake jinya?kasa mgn tayi sbd mamakin sa"ga sabon suna daya saka mata "ganin tak'i yin mgn ya saka shi cewa laifin meye kika yiwa Ammah d'in?"saida ta kwab'e fuska kafin tace"Allah kasan broth bata kyautawa haka kawai saina yadda naso wani k'aton tuzuru daya gand'ame Agida ya tuzurance "bayan haka kuma nifa bemun ba"wai yana sona bayan yana sa'an uncle mustapha"kusan 45yrs"never wlh! d'an jim yayi sbd yanzun ya fahimci shiyasa sukazo tare da uncle mustapha"kuma Abba yazo d'azun sbd suyi zancen kenan?"dariya taci k'arfinsa ya dinga b'abb'akawa harda rik'e ciki"kamar ba d'azun shine kwance magashiyan ba"Broth ka gani ka dena mun dariya ko?
Uhmmmm! *Aminatu* kenan! kece da abun dariya Ai"Amma tunda bakyaso na dena"dama shawarah zamu yi"saida ta hararesa tace"yanzun zaka nemi shawaran tawa bayan bakada mak'iyiyar data wuce ni?"nine yaka mata nace miki haka "Amma mu barshi bisaga Abinda ya wuce"kinga gobe sunday tunda ba office zanjeba zamuje ki rakani wajen friends d'in Fatima muyi mgn naji meye za'a basu na hidimar biki?"tab'e baki tayi tare da cewa Allah ya kaimu"Amma ni meye nawa na Aje dani?"kika san ko na samu budurwa idan ta miki saiki had'amu ko?"banza ta masa tana dannah waya, shi kuma yana kallon lips nata data tsuke.....wai yanzun bazaka ce Allah yasa Alkhairi da Aikin dana samu ba balle ka bani shawara me kyau?' "Inada niyar yin hakan sai kika yi maganar"tun last 2 days su Abba suka sanar mun nayi murna da Addu'a da fatan Alkhairi "batun shawara koda baki nema ba zan baki sbd wasu dalilai. Amma yanzun ki zubamin roman nasha inata jin k'amshi kin Ajiye "ba tace komai ba ta zaro kular ta bud'e k'amshin ya daki hancinsu"cikin wani plate me d'an zurfi ta zuba masa cinya da k'ugu(kwatar kaza) "gashi shine rabonka"ta fad'a tana wani shan mur"ya kalleta ya kalli plate d'in fuskarsa da d'an murmushi yace"haba bestie! koda rabon gaskiya zakiyi saiki zubamin k'irji da fiffike ko?"ya fad'a yana saka spoon ya d'ebi roman yakai bakinsa"lumshe Ido yayi sbd yamasa dad'i sosai"gashi yajin beyi yawa ba,beyi kuma kad'an ba"nidai shine rabonka gaskiya"to shifa wannan bread d'infa?"nazo maka dashi ne ka dinga dangwalawa da roman sbd nasan bakayi lunch ba, ka Isa jin yunwa yanxun"kamar kin sani"Ina jin yunwar Amma bakin ba dad'i"Amma ki zuba mana muci tare zanfi ci idan bani kad'ai bane"batace komai ba ta zuba kamar yadda ya buk'ata"d'an matsowa tayi suka fara ci"shi yafi cin bread d'in da romo"ita kuma naman Ayangance tana danna waya"k'asan zuciyarta tana mamakin wai Ammah ta tafi bata saka An kirata sunyi sallama ba..... k'arfe nawa zaki dinga zuwa wajen Aikin?"8 am, na dawo 1pm "tunda zuwa k'arfe d'ayan ne natashi, kaga bazan zauna ba zan dawo gida"banda ranar Friday da kuma week end"Asati sau 4 ne zuwan"okay Amma kamar wanne shirye shirye ne zasu baki?"Eh to saidai zuwa Monday d'in idan naje mugani"Amma dai nasan Akwai news na turanci da fassarasu"daga k'arfe 9 zuwa goma na safe"sai kuma Akwai shirin *mu gyara muhallinmu* "Amma duk ranar Wednesday ne Akeyi"duk shirye shiryen Akwai wacce zaku jagoranta tare da ita ne ?"bandai sani ba gaskiya"yayi shiru "can yace"da kamar 7 :30 am zaki iya gama shirinki saina jira ki mu wuce na saukeki"oh wai broth ba kama san nayi motaba ko?ban gane ba?"ga mota can gefen taka tamuce"uncle mustapha ne ya siya mun ita tun Ina KD"to dama nace saina samu Aiki zan fara hawanta"Masha Allah! naganta tayi kyau sosai"Allah yasa Alkhairi "da Ameen ta Amsa"d'an shiru ya biyo baya"can yad'an daure fuska tare da cewa"zancen gaskiya ki kula da kanki da nuna keme mutunci da tarbiya ce"domin duk inda mace ta shiga ta nuna Akasin hakan Tofa mutuncin gidansu ta zubar"bance dole ki saka hijab ba, Amma kiyi shigar data kamata"batun jan Aji da kamun kai dole Abaki 100% ta wannan b'angaren"sosai ya bata dariya har tayi murmushi dan kanta ya fashe....so ya kamata ki kama kanki da ajinki wajen iya hud'd'a da mutanan da kuke Aiki musammun maza"banda sakewa ko yin wata doguwar fira har akaiga jin sirrin juna"nidai shawaran da zan baki kenan...ni meyasa da zaka fara Aiki baka nemi shawarata ba game da yadda zaka mu'amalanci mutane ??"Abazata tambayar tata tazo masa"saida ya shanye romon daya deb'o kafin cikin cool voice d'insa yace"babu komai"Amma ko yanzun bata b'aci ba Abani shawaran zan d'auka..ya k'are maganar yana murmushi "Adaidai lokacin Abba ya wuce ta gabansu" wanda yayi mamakin ganinsu Ahakan suna cin Abinci cikin kwano guda" su ba suma lura dashi ba"Ahyaan kuwa tab'e baki tayi tana hararan plate d'in tace"saida nayi k'orafi sannan zaka so shawaran?"kuma ni ban yadda ba kafini cin naman ko?"shikenan juyo mana sauran mu cinye"Amma da dare meye zakimun na kwad'ayi?"zan soya maka kifi kaci da yaji"kina nufin shan yaji zaki koyamun?"bayan kema inaso ki dena ci"batace komai ba ta juye musu sauran"shi kuma ya d'auki fanta d'in ya bud'e yafara sha yana lumshe Ido"gaba d'aya jinsa yakeyi wasai beda wata damuwa"to muci mana"kece zaki fara"ni Allah kaine zaka fara ko?"sai yayi d'an murmushi sbd shi kansa yayi mamakin yadda Ayau taketa masa biyayya ba tare daya sha harara ko bak'ar mgn ba"cinya ya d'auka ya yaga "itama saita d'auki wani gefe me tsoka"kafin takai bakinta sai dungure mata lips da sauran cinyar kazar dake hannunsa yayi"Ai kuwa ta kai mata raruma ta wafce tsokar dake jiki tana dariya"hakan yafaru Akan idon mu'az da yake tunkaro inda suke "da Alama dubiya yazo yi.....sai kin biyani Abuna?"uhmm! ni kuwa dame zan biyaka broth?"komai ma"yayi maganar k'asa k'asa"saima lokacin Ahyaan ta lura da mu'az na nufosu"ba k'aramin kunya da nauyinsa na ganin nasu Ahaka tajiba"ita kanta bata san meyasa idonta ya rufe tayi wannan sakewar dashi haka ba?"bayan kusan wata nawa saiya gadama inya zama dole yake tankata"karfa yaga tama damu dashima yayi zaton shishshigi ne..... Atake y'an jan Ajin nata da izzar ta suka motsa"saita mik'e tsaye da hanzari tana jin mu'az na cewa" Abokinah barkanku da hutawa ! ba tare data kallesaba ta gaishesa. ya Amsa da kulawa da tambayar ta yamai jiki?"da Alhamdulillah! ta Amsa ta wucewarta zuwa sashen su mamah sbd tana so taji dalilin da yasa Ammah ta wuce bata neme taba...... uhmmm ?mutumi nah ka cika k'uminiya da Abu fa"kamar ya?"cewar Dr darma yana d'age gira"saida mu'az ya zauna kafin yace"naga kaida mutuniyar kun shirya ko?"gashi harda cin Abinci kukeyi tare"matsalata dakai sanya Ido"tunda kazo ganinka ya saka ta tafi Ai shikenan"batun shiri da kake mgn nima bansan meyasa muka shirya d'in ba?"hmm ! Anan gaba zaka sa dalilin daya saka kuka shirya"saidai fa kaida ita sai kukayi kamar irin sabbin Auren nan"ga wani kyau kunyi,ita sai tayi kamar Amarya....d'aure fuska uban gayyar yayi tare da cewa "kaga dan Allah kadena zancen daka san bama tabbata zaiyi ba"wannan samun namu dakayi sbd bani lafiya ne"shiru kawai mu'az yayi tare dashan Alwashin ya gama yima dr darma zancen Ahyaan "ya lura ko kallonta beso yanayi,saidai zuciyarsa ta jima da zargin Dr darma ya mace A soyayyar Ahyaan"kodan sbd masifaffen kishinta daya ke nunawa k'arara"jin kansa da izzarsa ya hanashi nunawa yaketa basarwa"Amma duk wanda yasan meye so ya gansu Ahaka dole ya zargi wani Abu...kaga mlm idan tasani gaba zakayi kana gulma kaida zuciyarka pls kaje kawai"okay to shikenan "ya fad'a yana d'age kafad'a ya mik'e tsaye"kana nufin tafiya zakayi da gaske bayan dubiya kazo?"of course zan iya tafiya tunda baka buk'atata"uhmm! kaga gobe zamuzo nida bestie muga friends d'in nata"Amma bana so yarinya sama da biyu tazo gaskiya"ya fad'a yana wani yamutsa fuska"dariya mu'az yayi yace"kana yadda kaga dama darma"wacece bestie kuma?"banza yamasa yak'i yin mgn "shi kuma ya dinga tsokanarsa wai babynsa ce bestie d'in.... Ahyaan na shigowa tsakar gidan ta sami innah Asabe da ummah zaune kan tabarma suna k'us k'us suna dariya"nunawa tayi kamar bata san da zaman suba ta nufi k'ofar parlourn su....ke! yanzun dan ubanki kina ganina Amatsayina na yayar mahaifinki ba:zaki gaisheni ba?"juyowa Ahyaan tayi ta kalleta sama da k'asa tana yamutsa fuska tace"karki koma zaginah! Iyye? kar kiyi mamaki yaya Asabe koni bata gaisheni"Ai tana gadara zata fara Aiki ko?"Aikin banza da wofi"da tayi Aikin Ai gara taje tayi zaman Aure "yo Allah na tuba da Ace y'ata na yawan gantali Asunan Aiki Ai gara Ace tana gidan mijinta....ya Isa haka yaya Asabe! kinzo inda bazan iya jurewa ba"Allah yaraba y'ata da yawon gantali"datayi Auren da shekaran na zagayo ta fito ta tulke mun Agida ba Aure ba karatu balle Aikin "Ai gara tayi Aikin zaifi riba "muna zaune Allah zai kawo mijinta da lokacin zuwansa yayi"da wanda keso da wanda beso"sai dai d'an bak'in ciki ya mutu"ni ban gaji da y'ata ba daga ni har mahaifin ta "to Akan me za'a sama na Ido sai kace bisa kan wani take.... shigowar Abba tsakar gidan yabsaka mamah tayi shiru "da Alama yana cikin Anguwar daya fita beyi nisa ba.....Ahyaan na huci tabar tsakar gidan ba tare data ce komai ba"saidai Azuciyarta taji dad'in kalaman mama, sbd mgn ce da gugar zana ta yiwa inna Asabe da ummah"dan inna Asabe y'arta safiya na nan zaune tana zawarci "daga gama secondary school wani me kud'i ya ganta ya nace yana so"inna Asabe ba wani k'wakwran bincike ta yarda Akayi Auren sbd mijinta bayan raye"Ashe Auri saki Alhajin yakeyi"kuma Auren,yayi ne dan sha'awa ,shine shekara guda ya saketa....dole kiyi shiru sbd kingan shi ko?"cewar inna Asabe "mamah tace" koda yana nan kikayi Abinda kikayi saina fito na miki mgn"iya Abinda na sani kin riga kin zubar da girmanki Awajena....."zainab karna koma jin bakinki "ba tace komai ba ta wuce d'akinsa dake A bud'e"Abin yasosa ran ummah sbd Aganinta kwananta ne"kallon innah Asabe yayi yace"dan Allah ki dena zuwa min gida tunda dai fitinah ke kawoki"kuka ta fashe dashi had'e da salati tana cewa" ni kake kora dg gidanka iliyasu?"yanzun sbd matarka da y'arka tamun rashin kunya shine zaka goyi bayansu??"bece komai ba ya nufi d'akinsa "da sauri ummah tayi k'unar bak'in wake ta mik'e tsaye ta biyosa"saidai tana shigowa ta samu mama rungume Ajikinsa ya rik'e hannayenta yana mata mgn k'asa k'asa da Alama rarrashinta yakeyi....kukan b'akin ciki ummah luba ta saki"daga Abba har mama kallonta sukeyi"shidai Abba yacika hannayen nata da sauri"Amma mama k'ememe tak'i janye jikinta daga nashi....wlh kaje kuda Allah "ranar kwanana na sameku mamuke da....saurin janye jikinta daga nashi mama tayi ta baro d'akin wanda dama da biyu tayi hakan"tun Asali da yace tayi shiru saita wuce d'akin nasa"tayi hakanne sbd ta k'untatama umman"(hmm kishiya🥹) ,tana kuma ganin plaine nata yayi sai tabar d'akin"taci burin kuma cigaba da yin Abinda zai sosa ran umman in har yaransu basu gidan,tunda batada mutunci...ummah kuwa Allah ya Isa ta dinga yima Abba "harya fito da nufin ya mareta saiga daddy ya shigo tsakar gidan sbd yanzun da innah Asabe zata fita tayi clashing dashi zai shiga sashensu shine da kukanta take sanar masa Abba ya koreta"shine ya shigo ya samu kuma ummah nata haya yaga da furta Allah ya Isa"haba Alh iliyasu! rabu da ita dan Allah"ya fad'a yana rik'esa"Abba yaja tsaki yana fad'in kije gidanku saina nemeki"wlh bbu inda zanje"sbd na ganku kana rungume da ita ranar kwanana shine zaka nad'e tabarma kunya....tamkar daddy yayi dariya haka yaji"sai kawai yaja hannun Abba suka fita"saidai suna fitowa Abba yaga innah Asabe Atake ya had'e rai"daga k'arshe daddy yace taje gd zasuyi mgn daga baya zaizo gidan nata suyi mgn "shi kuma yaja daddy suka wuce parlournsa.....duk Dr darma da mu'az dake zaune suna lura dasu"dandai basu jin me suke fad'a"saidai Dr darma ransa ya bashi wani d'iban Albarkan inna Asabe da ummah sukayi ma mamah da Ahyaan "sbd itama yaga yadda ta wuce Azafafe"hakan yasa mu'az na tafiya ya wuto cikin gidan"lokacin yamma tayi sosai befi saura 45 minit Akira sallar magrib ba..... Ahyaan na kwance saman cinyar mamy tana tunanin"in sha Allah nan kusa data sami wanda ke sonta zata Amince tayi Auren nan kodan sbd mahaifiyarta ta huta da y'an saka Ido"ita kanta har cikin ranta bata so ta cika 30yrs batayi Aure ba"taga iyayenta da mutanan Arzik'i basu damu ko yada mata mgn ba sai kishiyar uwa da dangin ubah..... k'amshin turarensa da sanyayyar muryarsa da taji ya saka tad'an lumshe Ido "mamy ta kallesa bayan ya zauna tace"ya jikin?"Alhamdulillah ! so nakeyi idan Anyi sallar magrib naje na sake Alluran na fara jin Alamar zazzab'in zai dawo"subahanallahim! Allah ya sawak'a "ya Amsa da Ameen..... Adaidai lokacin kuma sadeeq yayi sallama ya shigo cikin parlourn"ya sha wankan farar shadda yanata k'amshi shida tsiya zance yazo wajen Ahyaan....lolx"Atake mutumin naku ya had'e rai"duk mamy na Ankare dashi"ita dai sunama gama gaisawa da sadeeq ta janye kan Ahyaan daga saman cinyarta tabar musu parlourn"tana ya mutsa fuska ta gyara zamanta ta gaida sadeeq da suka gama gaisawa da Dr darma" satar kallonsa tayi taga ita yake kallo "saita sunkuyar dakai"yayi k'asa da murya "menene kuma, naga duk kin b'ata rai, kinata fushi??"yafad'a ko Ajikinsa da ganin sadeeq na wajen zaune"itama sai bata damuba ta wani turo baki gaba tace"ba wannan ummah d'in da innah Asabe bace"sai kuma ta saka kuka"beyi mgn ba sai isowa gefenta yayi ya kama hannunta"tashi muje ya Isa haka" batayi mgn ba suka fita daga cikin parlourn.....��




Adinga sharhi 🥹☺�☺�


wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251


dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba


Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn


Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba


#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: *Littafin kud'i ne!*






........Baki galala sadeeq ya saki yana kallonsu har suka fice daga cikin parlourn "ya sauke numfashi zuciyarta na zafi"ya san dama tabbas Ahyaan ba sonshi takeyi ba"ta nuna masa k'arara "saidai yasan sarai Dr darma yasan sonta

Please Login or Register in order to submit comment