Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan Allah malam ka duba kaga yadda take kuka kamar ranta ze fita…” hassana ta fadi tana kara kara fashe wa da kuka sosai . M-wanzan da dauriya kawai yakeyi yace “Bakomai karki damu hassana ni nasan me nakeyi, , ki kyaleta tayi kukanta ko zataji sauki a zuciyarta, insha Allah kukan nan ze Zamar mata farin ciki da dariya nan gaba, harke se kinyi farin ciki…” hassana sam ta kasa gane me yake cewa ma sbda tashin hankali, kuka take sosai, tace “kaduba Kagani malam rabani akeso ayi da yarinyata bayan tanada karancin shekaru, za a dauketa akaita cikin manyan mata, tayi kankanta wlhi malam, yama zatayi ya dauki namiji dan Allah?…” ta sakko kasa tayi knell akan guiwowinta a gaban mijin nata wanda keta kallonta se kuka takeyi majina shabe-shabe a hanci tacigaba dacewa “Kaduba girman Allah ka rufamin asiri malam Dan Allah nide a raba Aurennan, yarinyar nan tanada wanda takeso, kawai gaya maka ne batayi ba tin tini, dan Allah ni hankalina be kwantaba da wannan Auren, kar akaimin yarinya cikin manyan mata, kawai kwara a bata wanda takeso dan Allah ka dubeni ka duba damuwata dan Allah!…” “Baku isa ba daga ke har ita, Bazaku zubarmin da mutumci ba, ni ba yaro bane kamar ku, inada tunani, sannan ni nake aurenki bake kike aurenaba, ita kuma yata ce, dan haka ba wanda ya isa ya raba wannan Auren Se ubangiji, in kuma kince zaki fara sa’insa dani toh mu zuba mu gani nida ke..” malam wanzan ya fadi cikin fada, ya mike ya barta nan falon durkushe, ya haye upstairs cikin fishi. hassana ta bisa da ido, ta zauna zaman dirshen a kasan falon tayi kuka-tayi kuka ma ishi. harga Allah tana ma m-wanzan biyayya , da ladabi amma a wannan Karan wlhi zata iya bijire masa, sbda duk san datake masa wlhi tafisan yarta akanshi. Seda hassana rayu kuka ma’ishi kana Ta mike jiki na rawa ta nufa dakin BATOOL har yanzu kuka takeyi sosai kamar ranta ze fita. Ta kwankwasa dakin hadi da kiran sunanta, BATOOL ta amsa tana kuka, ta taso ta bude mata ta shigo ta rungume yarta jikinta, ta dinga rarrashinta, harseda taga ta dena kukan wuraren 2:am kana ta nufa dakin mijinta, tasha ko yayi bacci amma setaga idonsa biyu shima, yana zaune dagani koda be gaya mata ba tasan tunani yakeyi. “Malam dan Allah ka duba girman All…” ta bude baki zata masa doguwar magana ya dakatar da ita dole taja bakinta tayi shiru ta kwanta, tana hawaye. Ranar bacci sede barawo. BATOOL kam haka ta kwana tana hawaye bata rintsaba. Washe gari hajiya Fatima tazo gidan bayan sallar Azahar, daman malam wanzan ya sanar da ita yaune tarewar, sbda ita daman tabari seta warke ne ayi tariyar. Ta kawo akwatuna dozing uku, kowanne cike da kayayyaki na alfarma, ita duk tayi akwatunan JAROOD besanma anyi ba, sannan ta kawo ma BATOOL special perfumes najan hankali miji, masu kyau na Companyn Rukie. Hassana da Malam wanzan suka dinga godiya, har ita hassanar seda hajiya tamata uku na kayayyaki masu kyau da tsada. Sam kayayyakin basa Gaban hassanar, kawai de godiyar taketa mata, amma ahalin yanzu farin cikin yarta yafi mata komi dadih a rayuwarta ta duniya. BATOOL tazo ta gaida Hajiya fatima ta amsa tana kare mata kallo, ta kula da yarinyar ta rame ba kmr randa sukazo ba, sannan da damuwa akan fuskarta, hajiya fatima ta kalleta cike da kulawa duk suna zazzaune a falon. “Kinacikin damuwa , sbda bakisan Aurennan kou?” Hajiya fatima ta tambayi batool. Dagowa tayi ta kalli hajiya fatima cikin girmamawa tace “Aah inaso…” hajiya fatima taji dadin abinda yarinyar tace dukda tasan batasan Auren Amma setace mata Tanaso, bayan ita ba karamar yarinya bace, tana ganin damuwa akan fuskar yarinyar. “Zuwan JAROOD nawa gidannan?” Hajiya fatima ta tambayi malam wanzan. “Yadezo gaskiya …” malam wanzan ya fadi ne kawai gudun kartama JAROOD fada, ya kula tana matsa masa sosai. Seda akayi sallar karfe hudu duk Amour na nan gidan saboda da kanta takeso takai BATOOL har dakin mijinta. Aka shiryata cikin shiga ta alfarma irin ta gidan sarauta, Tasha Alkyabba fara karr, kamar yadda kowacce mace ta JAROOD takesa alkyabba inde za a kawota gidan jarood. BATOOL tayı kuka sosai na rabuwa da mahaifiyarta, kamar ranta ze fita, hassanama tayi kuka sosai da kyar aka kwace BATOOL ajikin mahaifitar aka sata a mota. Kafin asata a motar seda malam ya mata natsiha sosai da Lallami da tausasan lafazi, BATOOL tadanci sanyi a ranta atlast de ta dan farajin malam ne mahaifinta amma de tasan an mata abinda ranta beso.
Daman motoci uku sukaxo dasu gidan, daya BATOOL da Amour suka shiga ciki. akasa akwatunan a motoci biyun kmr yadda sukazo. Malam wanzan shima daurewa kawai yakeyi, amma shikadai yasan me yakeji. Da kansa yayi driving motar da hajiya fatima da BATOOL suke ciki so yakeyi shima yakai yarsa da kansa dakin miji. har yanzu kuka BATOOL keyi tana kiran sunan Ammuhnta, se rarrashinta hajiya fatima keyi ta jawota jikinta sosai ta rungume ji takeyi kamar ita ta haifi BATOOL, tana tausayinya duba da yarintarta, tasan rabuwa da iyaye se an daure musamman uwa. Tana kuka har suka iso gidan JAROOD, sam shi goganma baya gidan besan wace wainar ake toyawa ba. Suna isowa hajiya fatima tasa maza masu aikin gidan suka kwashe akwatunan BATOOL aka kaita mata part dinta dakinta na sama, nan hajiya ta umurcesu su kai.

hajiya Fatimar da kanta ta kama hannun BATOOL ta kaita part din H-zulaikha suka gaisa, se kallonta zulaikha keyi, dukda bataga face ba amma tasan yarinya ce danya sharaf, yau da ace burar JAROOD lafiya lau ya Auro musu yarinya dasun bani. H-zulaikha se tabe baki kawai takeyi, a ranta tace “Ayi de mugani, in tusa zata hura wuta…ki zauna muga uwarda zakici a gidan…” Hajiya fatima ta musu natsiha, kana ta dawo da ita part din aisha suka gaisa, ta musu natsiha ananma itama Aishar se kallon BATOOL takeyi ta ciki na ciki, se yake takeyi irin na bariki, tanataso
Taga fuskar BATOOL amma bata samu gani ba, kowacce de daga zulaikha har aisha duk kishi ya taso musu, wai a hakama dan ba a uwar komi da ace anayin wani abu ai da kishin seyafi haka, daman bura mata kema kishi toh wannan bata tashi balle yaci. Daga zulaikha har aisha duk sun kula da yadda Hajiya fatima ke bama BATOOL muhimmanci dan haka se suka tsani BATOOL tin kafin ma su ganta daman sun
Tsaneta, yanzu dasuka ganta sunga alamun tafisu komi dukda ba face suka gani ba se suka kara tsanarta, amma kuma in suka tuna ba mamora sesu basar, su barwa cikinsu.

“Shiga da bismillah, da lahaula wala quwwata…” hajiya fatima ta fadama BATOOL dai-dai da suka iso part dinta, BATOOL tayi yadda hajiya fatima ta umurceta, ta sako kai dankareren falonta dake kasa, lokaci kankani BATOOL taji tana kaunar hajiya fatima amma harga Allah batasan d’anta kuma tasan bazata taba kaunatarsa ba, aduniya namiji daya rak takeso kuma shi zatayita SO har karshen rayuwarta. Hannun hajiya fatima na rike dana BATOOL suka iso har kan luntsumemiyar kujerar BATOOL ta zaunar da BATOOL akan kujerar 2cttr ta zauna kusa da ita, hadi da bude mata fuskarta da aka rufe da Alkyabba, ta kalli cikin idanuwan BATOOL wanda suka gaji da kuka sunyi jajawur, tausayinta ya ratsa hajiya fatima, ta sakarma BATOOL murmushin kwantar da hankali a hankali ta fara mata magana cikin nutsuwa “Bakyason Aurennan ko ? Ki gayamin gaskiya ni mamankice ba maman mijinkiba…” BATOOL tayi shiru ta sadda kanta kasa batare datace komi ba. “Karkimin karya kinji yanzu babu kowa daga Allah seni seke…bakison Aurennan kou? Kinfi so kije ki zauna tare da Ammuh kou Fatima?” Daga mata kai BATOOL tayi alamar eh, idanuwanta suka kawo hawaye. Cikin muryar kwantar da hankali hadi da dumbin tausanta daya rufeta ta dafata tana fadin “Toh kiyi hakuri karki dinga kuka, hakuri zakiyi ki zauna anan na wani dan lokaci, zan dinga zuwa ina dubaki, Ammuh ma zata dinga zuwa tana dubaki kinji Takwarata” batool ta daga mata kai Alamar toh. “Sekin kwantar da hankalinki fa amman? Zanzo in daukeki wata rana da kaina in maidaki gun Ammuh,,,” BATOOL ta dago ta kalli fuskar hajiya fatima tace “Allah zaki maidani gidan Ammuh? Ai Ammun tace nazo nan kenan wai bazan koma gidantaba?”
Cikin yarinta tayi mgnr se tausanta ya kuma Ratsa zuciyar hajiya fatima. “Aah zaki koma inde kikayi hakuri kika zauna anan din kinji? Ai kin iya girki kou?” BATOOL ta dagama hajiya fatima kai alamar eh. “Toh ki dinga dafama mijinki abinci dasafe, in an kwana biyu kin huta, yanasan tuwo miyar kuka ai kin iya kou?” BATOOL ta daga mata kai alamar Eh. Hajiya fatima taci gaba da magana “Toh ki dinga dafa masa abincin safe, dana rana dana dare kinji?” BATOOL tace toh. Hajiya fatima dukta gaggayama BATOOL abubuwan da JAROOD keso, kawai tace toh tanata bin hajiya fatima da ido, Atunaninta in tana dafa masa abincin zesa amaidata gida da wuri, yadda brain dinta na yara ya bata kenan. “Zansa akawo miki babbar mace kamar Ammuh tadinga tayaki zama da Aiki kinaso kou?” Cewar hajiya fatima. BATOOL tayi Jim kana tace “Badake zamu dinga zama anan ba?ina zakije?” Hajiya fatima tayi murmushi azuciyarta tace “Yaro, yarone…” a fili tace “Aah, ni zan tafi gidanane yanzu,innaje zan aiko miki da abinci, karki sake wani ko wata ta baki wani abu kici in ba ni da daadahnki, da Mijinki kinji kou?…” BATOOL tace “Toh,,,,yanzu ni kadai za a bari anan in kwana?” Ta karashe mgnr kamar zatayi kuka idanuwanta harsun ciko da kwallah. Hajiya fatima tace “Ehh…” BATOOL ta fara hawaye tana bin ko ina a gidan da ido, Kato ne sosai harma yafi gidansu girma, da kyar ma take iya kwana a dakinta ita kadai a wancan dakin saboda tsoro ne da ita sosai, toh anan gidan yaya kenan zatayi?. “Gaskiya inajin tsoro sosai bazan iya kwana anan ni kadai ba, Sede in zaki tafi in biki hajiya…” BATOOL ta fadi tana hawaye, harda Ajiyar Zuciya. Hajiya fatima tace “kicemin Amour ba sunana hajiya ba…” BATOOL tace “Tohhh,,,” tasan meye ma’anar suna Amour. “Sannan ko zaki koma part din mijinkine ki zauna açan seku dinga kwana tare ai bazakiji tsoro ba kou?” BATOOL ta zaro ido waje harda dafe kirji tace “aah dan Allah, Da namiji? Aah gaskiya nide ko in biki ko dan Allah a maidani gun Ammuh in Daadah bazemun fada ba…” hajiya fatima tace “Toh kawai yau zan aiko me tayaki zama da abincinki, danaje zan aikota aiya miki kou?” Batool ta dağa kai alamar eh ita sam ba haka taso ba, taso ace su zauna tare da hajiya fatima a nan ko kuma ta tafi da ita gidanta, tanasanta sosai. Hajiya fatima ta zagaya da ita a part din nata , ta nuna mata ko ina, se kallo batool keyi , ko ina yaji kayan kudi, yayi kyau Amour ta narka mata dukiya sosai a part din nata, duk part dinta yafi part din sauran matan kyau, kujerunta na kasa Light brown ne, Dayan falonta na kasan kuma kujerunta milk ne, falonta na sama ash color ne kujerunta, ko ina yayi kyau dinning table dinta yayi kyau sosai, dakuna 6 ne a part din kuma duka akwai gadaje na alfarma nagani na fada. Hajiya Fatima da kanta ta zaba ma BATOOL dakin dazata dinga kwana a Saman upstairs din, ita de ada a kasa taso tadinga kwana, amma tinda hajiya Fatima ta Zaba mata daki a saman dole ta hakura ta dauka. Anan hajiya fatima takai har isha’i, taso JAROOD ya dawo ta hadasu da BATOOL ta musu natsiha, domin taje ta dubasa a part dinsa taga baya nan, ta kirasa awaya be dağa ba, dole ta hakura 8:02pm hajiya Fatima tabar gidan, dreva dinta yajata zuwa gidanta, malam wanzan baya nan yana gidansa tin Dazu yana lallashin hassana tinda ya kawosu hajiya tace ya tafi gidansa ya lallashi matarsa, sbda hajiya Fatima ta kulada yanayin da hassanar tashiga.

Hajiya fatima na fita BATOOL dake zaune a falon kasa, ta kwanta akan kujerar 3cttr ta fashe da kuka, tana kiran Ammuhnya, kuka takeyi sosai kamar karamar yarinya yar 3yrs.

Hajiya fatima na isa gida, ta hado abinci iri-iri çıkın wanda aka shirya mata na dinner, ta bawa wata Amintacciyar me Aikinta wadda ta taho da ita dağa Agadez yar maradice bazawara ce, akallah zata kai 45yrs, kamar hassana take, itama hassana kusan 45yrs take. Hajiya ta sanar da Asiya zata koma gün BATOOL ta dinga mata Aiki, Asiya ta amince da hakan saboda daman ita tanasan zaman nigeria, sannan dataji ance amarya ce BATOOL din tasan ba aiki sosai dan haka taji dadih. Dreva yakai Asiya gidan JAROOD ya nuna mata part din BATOOL. BATOOL taji dadin ganin Asiya, ta tashi ta goge hawayenta, Asiya tadinga bawa BATOOL hakuri saboda hajiya ta gaya mata in taje tadinga rarrashinta, hajiya fatima tasan kuka BATOOL zatayi tayi harse tasaba da gidan zata Dena kuka. Asiya tazubama BATOOL abinci cikin abincin datazo mata dashi, dafadukan shinkafa ce da farfesun naman kaza, BATOOL taki ci, Asiya ta tambayeta taci abinci ne?. BATOOL tace aah kawai de ta koshi ne. Asiya tayi-tayi da BATOOL taci abincin taki ci saboda bata mood din dako ruwa zata iya hadewa inta sawa bakinta,. Haka suka kwana da BATOOL da Asiya daki daya suka kwana, kmr yadda BATOOL tasaba tinda tazo Nigeria Kwana kuka, toh yauma haka ta kwana tana kukan,.

Tin Daren ranar hajiya fatima tace JAROOD yazo gida yasameta. Bayan JAROOD yazo Amour tasanar dashi BATOOL ta tare yau. Şam ba haka JAROOD yaso ba. “Tin yanzu haba Amour?ki duba ki gani, in wani yaji maganar nan aise mutumcina ya zube, ace na Auri wata wai yar 14yrs,,,,,” JAROOD dake zaune a kasan carpet yace hakan. Wani kallo kawai hajiya Fatima ta watsa masa batare datace komi ba, sbda ma be isa ta basa amsar mgnr banzarnan tasa ba. Tadinga masa natsiha kan ya kula da hakkin yar mutane, sannan duk yadda ake ciki ya gaya mata, wato tana nufin akan warkewarsa. JAROOD yace toh kawai ya baro gidan da tunani-tunani a ransa, shide yasan dukda bega yarinyar nan ba amma besanta, kuma gaskiya shi koya warkema in banda abun Amour mezeyi da yar 14yrs, dukda bega uwarta ba amma harga Allah shi ko age mate din uwar yarinyar ta masa karama, yanzu harga Allah baze iya Auren ko yar 35yrs ba sede 40yrs ko 45yrs ko age mates dinsa (besan age din mahaifiyarta bane shiyasa ya fadi hakan). “Kona warke kawai se in wani ciro gabana insa a gaban yar 14yrs, gaskiya me maganinnan beda hankali…” JAROOD ya fadi aransa yana driving bisa hanyarsa ta komawa gidansa. Se tsuki yakeyi. Harya isa gidansa yana tsuki, yayi packing , ya fito direct ya nufa part dinsa, shi Sam acikin part’s din gidanma besan wani part bane inda BATOOL din take ciki. Yayi wanka ya kwanta, saboda shi besan meze mata ba inyaje part dinta yanzu. Tunanin sumar daya gani tadawo masa rai, wannan tunanin ya zama jini da tsokarsa, yanzu da tunanin yake rayuwa acikin duniyarsa, bayaso amma abin yaki fita aransa, yasha da an masa saukar Alqur’ani abun ze fita a ransa amma abu ya nace ya makale masa a zuciya yaki fitar, ga jijiyarsa har yanzu taki komawa yadda take, shi abunma mamaki yake basa, da daure Kai, ya rasa waze gayama wannan abun al’ajabin ya fiddasa a duhu. Har akayi 2week JAROOD beje part din BATOOL ba be taba ganintaba har yanzu, amma sede kusan 10days kenan yanzu kullum se yaga abinci iri-iri kuma favorite dinsa Akan dinning dinsa na safe dana dare, ranar Saturday da Sunday harda na rana ake masa amma se yasha ko Aisha ke masa yasan de ba zulaikha bace saboda tace ita ta ajiye masa girkinsa tinda ba cinta yakeyi ba. JAROOD najin dadin abincin sosai be taba cin abinci me dadin sa, yayi mamakin ina Aisha tasamo me aiki kwararra a girki har haka, yasan de ba Aishar ke dafa masa ba, daman can masu aiki ke dafa masa duk abincin da yakeci agidan. A 10days din har kiba yayi saboda yana samun abinci me dadih yanaci. Besan BATOOL bace ke dafa masa da taimakon Asiya ita ke kawo masa part dinsa, BATOOL kam batasanma part dinsa ba, kuma bataso tasani, rashin shigowarsa part din tinda aka kawo BATOOL sam be dameta ba, ita ko azaninta, dade ace Khalid ne ya mata haka shine zata damu. Asiya cema take magana tace “har yanzu de ango be shigo ba ko lafiya? Aiya kamata ke kije tinda shi bezo ba…” sede BATOOL tace toh kawai, amma bataji aranta ko zata mutu zata dauki kafafuwan taje part din JAROOD, dade Khalid ne ai da tini take, itafa wlhi adadintama dabezoba. Satın batool daya da zuwa gidan Amour tase mata waya İPhone XR. sbda tadinga jin ya suke ciki a gidan, ta tambayeta JAROOD ya shigo BATOOL tace Eh saboda tasan in tace aah, Amour zatasashi seya shigo dole, ita kuma batasan ganinsa. Har yanzu wani abu be shiga tsakaninku ba?” Amour ta tambayi BATOOL. BATOOL ta rasa wani Abu Amour ke nufi, kawai se tace Aah, dukda de batasan inda ta nufa ba. first da aka kawowa BATOOL wayar ta kira Khalid, tana kiransa ya daga, farin ciki kmr ya kashe BATOOL da Khalid, sukasha soyayyarsu, Kwana suke suna waya yanzu, da BATOOL da Khalid, hajiya Fatima nasama BATOOL card sosai, aiko card din agun kiran Khalid yake karewa, seta shige wani daki a saman tayita wayarta yadda Asiya bataza jiba, sam BATOOL bata gayama Khalid an mata Aure ba, shi kuma kullum cikin tambayarta yakeyi yaushe zasu dawo, tace masa in sun sa Rana zata gaya masa. Asiya na sane da namiji BATOOL ke waya, tanasa mata ido sosai saboda hajiya Fatima tace tadinga sa mata ido sai. BATOOL kam yanzu damuwarta ta ragu, abu daya ya rage mata yanzu taga Khalid eyes 2 eyes, saboda suna yunwar ganin juna.

Hajiya fatima tace da JAROOD ya cire malam wanzan a dreva ya bashi wani aikin, JAROOD yayi yadda tace, daman shima yanasan hakan, yace malam yaje yaci gaba da kula masa da Gidan mansa dake nan cikin garin kaduna. Malam wanzan yace aah saboda shide yafiso ya kasance a dreva dinsa, yanajin dadin tarensa da JAROOD, maana yanajin dadin kasancewarsa da jarood, kunsan ance sabo turken wa-wa, kuma shi malam wanzan mutum ne da besa kwadayi a ruhinsa ba. Hajiya fatima da JAROOD sukayi-sukayi malam wanzan yace aah shi yafisan aikinsa na dreva dole aka barshi. A bangaren mahaifiyar BATOOL yanzu ta d’an rage damuwa saboda kullum suna waya da BATOOL, yau dasukayi waya hassana ta tambayi BATOOL “Yame gidan naki,,?” BATOOL tace lafiya lau. Hassana tayi shiru tin-tini tanaso ta tambayeta wani abu kuma tanajin nauyi, ta daure tace “kun kwana daki daya?” BATOOL tace “Aah…” hassana ta shiga mamaki tace “Har yanzu Bakuyi wani abu ba?” BATOOL tace “Meye wani abun Ammuh? Bamayin komi ai, kinga fa Ammuh bema taba shigowa daki naba, kawai de ban gaya miki ba ne…” cikin mamaki hassana tace “Kamarya?” “Eh Wallahi tinda nazo gidannan ban taba ganinsa ba…” hassana taji dadin jin hakan, domin tasan in namiji ya shiga gaban yarta ai sede gawa, balle babban mutum kmr JAROOD, a ido ma firgita mata yakeyi. “Toh kishiyoyin naki fa, su sun shigo?” BATOOL tace “Aah suma basu taba shigowa ba, inaga ma basa fitowa…” hassana tace “Toh shikenan ki dinga Askar kullum kinji safe da yamma, Allah ya tsareki kuma ki kara kwantar da Hankalinki…” BATOOL tace toh sun jima suna waya kana dağa bisani sukayi sallama.


Yau kusan 5weeks tana gidan amma basu taba haduwa da JAROOD ba, be shiga amma duk abinda take buka Malam wanzan ke sawa akai mata, yanzu ya kara girma sosai a gidan komi ta hannunsa yake fitowa, fin ada, aisha kam ta kara tsanarsa. kusan kullum se sun hadu da BATOOL, data gansa ta window dinta zatazo ta gaidasa, yanajin dadin ganin ta kwantar da hankalinta, tanacin me dadih Tasha me dadih ta kara yin fresh zatinta ya kuma bayyana, Gashi ta kuma haske, Amour tase mata lafiyayyen cream Agurin SaaadatubintuAbdullahi. Duk abinda ke faruwa malam wanzan na gani na rashin shigar JAROOD part din BATOOL, malam wanzan beji dadih ba, amma be taba nunawa JAROOD ba, a zuciyarsa sede yayita cewa “Kamar an kawowa mutum dabba,,,” lokuta da dama yana kallonsa duk ze shiga part din sauran matansa amma baya zuwa part din BATOOL, malam wanzan nada tsananin kawaici domin da wani uban ne da yanzu yayi magana, ganin aiko dabba aka kawowa JAROOD yaci ace yaje ya dubata yaga ya take ciki, jikin malam wanzan ya mutu, ya fara tunanin auren BATOOL da JAROOD bazeyi lasting ba, kuma gaskiya a age din yarsa bayaso tazama bazawara yanzu, dan haka Adduah kawai yakeyi ba dare ba rana Akan BATOOL da JAROOD.

Yau takasance Monday ne, an tashi da yanayi me dadih, kasancewar anyi ruwa sosai da Asubah, gari yayi dadih sosai , ga iska na kadawa, bishoyoyi nata juyi, yau an samu niimah kasancewar weather zafi ake ciki. Yaudin JAROOD ya tashi da tafiya zuwa Kano zasuyi meeting da governor din Kano, akan kasuwancinsa dake kanon, yanada companoni dayawa akanon har yafi na kaduna. Already har Amour ya sanar mawa jiya da daddare ma sunyi sallama ta masa Adduar dawowa lafiya sosai. 10:pm ya gama shirinsa, ya fito cikin danyen boyel light nude color, me mugun sheki da tsantsi, an masa dinkin yar shara, besa hula ba, ya taje sumar kansa ta buzaye, ta kwanta luf se shekin kudi takeyi, se yanzu na kula akwai furfura daya-daya acıkın kansa. ya feshe jikinsa da narkakkun perfumes dinsa, masu kwantar da hankali. ya saka danyen watch dinsa a tsintsiyar hannunsa, ya dauki wayoyinsa already duk abinda ze bukata tin jiya yasa a motar dazeyi tafiyar da ita. Yayi breakfast, da abincinta me mugun dadih, har yanzu besan wake masa wannan abincin ba, shi sam be saba shan shayi dasafe ba, yafison inya tashi dasafe yaci abinci me Maggie a bakinsa, shiyasa kullum a rayuwarsa da tuwo yake break sede in ranar be samu abinda yakeso ba shine zesha tea me madara. yanzu kam alhamdulillah yana samun abinda yakeso, har wani d’an karamin tumbi ya fara ajiyewa. Ya fito ya shiga part din hajiya zulaikha da part din aisha duk ya sanar dasu zeyi tafiya,duk suka masa fatan dawowa lafiya, tinda yama zulaikha fadan Fıta ba izininsa ta rage masa rashin hankali, amma fa bawai ta Dena bane. JAROOD ya fito ya nufa motarsa da Malam wanzan zasuyi tafiyar, an Riga an shirya komi, an shirya motar securities, har JAROOD ya shiga mota seya tuna da BATOOL ai ya kamata de yau yashiga kodan ya mata sallama zeyi tafiya, tinda Amour ta makala masa karfen kafa. malam wanzan na kokarin tada motar JAROOD ya dakatar dashi dacewa “dan dakata baba na manta, ban duba yarinyar nan ba, Mesunan Amour, Awani part ma take,?” Sam malam wanzan beji komi a ransa ba, ya fito JAROOD ma ya fito da hannu malam ya nunawa JAROOD part din BATOOL. JAROOD ya kalli malam wanzan yace “babana Bari inje part dinta in dawo semu tafi naga time ma ya tafi…” ya karashe yana duba watch din hannunsa. Malam wanzan yace “Ai daka bari kawai semun dawo tinda yau zamu dawo kou?” JAROOD ya kalli malam wanzan yayi mamakin abinda yace, se yau ya kara tabbatar da mutumci da hakuri da juriya

Please Login or Register in order to submit comment