Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hango fitarsu wani iska mai zafi ya furzar ya kuma duƙar da kansa yana sauraron bugun zuciyarsa.har cikin bedroom Khadija taja Halima kafin ta sakar mata hannu tace"watau bakiji kashedin Daddy ba kenan?,Halima me kika gani ga Ɗan daba da kika maƙale masa har kina zubar da girmanki da hawayenki a gabansa?,meye ya shiga kanki ne?".wani kallo take bin Khadija dashi kafin tace"kada ki sake ce masa Ɗan daba,nace bana so,ko daban yake yi aike be maki ba".sakin baki Khadija tayi tana kallonta kafin tace"koma me zakice karesa da kikeyi be isa yasa a daina masa wannan kallon ba tunda ya aikata,kuma ki sani bazan taɓa baki goyon bayan kiso Sudais ba har abada".tsuka Halima taja kafin tace"dama ban roƙa ba"ta ƙare maganar tana buɗe ƙofa ta fice daga ɗakin bin bayanta Khadija tayi a daidai ƙofa suka ci karo da Lamis,wani irin faɗuwa gaban Halima yayi ta koma da baya tanayin ƙasa da kai.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 17
Dedicated this page to Balkis Adam Bello

Khadija kam da wani irin kallo tabi Lamis mai wuyar fassaruwa,murmushi yayi yana cewa"sarkin ɓoyo yau kin fito kenan".cewar Lamis,kasa cewa komai Halima tayi kafin Khadija tace"ai kwanan nan Yaya sauyi kala-kala ma ka ganshi".harara Halima ta bita dashi kafin tayi ƙasa da kai tace"ina yini Yaya Lamis",da lafiya lau ya ansa yace"muje kuga wani abu".be jira cewarsu ba yayi gaba suka bisa baya a chair ya zauna yana ɗauko wani ƙaramin box ya miƙawa Halima sannan ya ciro agogo mai kyau ya miƙawa Khadija yace"ga naki ƙawarmu,bansan zamu haɗu ba aeda kema an maki naki na daban"murmushi kawai tayi tace"na gode kwarai Yaya hakanma ae yayi".baki Halima ta turo kafin tace"thanks".kallonta kawai yayi kafin ya janye kallonsa daga gareta.miƙewa Khadija tayi tace"muje ki rakani tau".murguɗa baki Halima tayi yace"wallahi baza ni ba".sakin baki Khadija tayi,murmushi kawai Lamis yayi yace"muje na ajiyeki ƙawarmu".dariya tayi tana cewa"kinga na samu rakiyan da yafi naki".gwalo kawai tayi mata ta wuce ɗakinta,a haka suka fita a motar Lamis,tunda suka tafi babu mai cewa komai can Lamis yayi breaking silent ɗin da yace"Khadijatau ya kike da ƙawar taki?",ɗan murmushi tayi tace"Yaya ina lafiya,Halima sarkin rigima ma tana lafiya".kansa ya shafa yana cewa"bari ta jiki nikan in ce bansan anyi bama".dariyan itama tayi tana faɗin "tuba nake" a haka har suka ƙarasa gidan su Khadija,10k ya bata amma da ƙyar ya samu ta ƙarɓa sannan ya juya ya tafi abunsa....shiru yake yana shafa kansa yayinda idanuwansa suke lumshe a hankali ya ware su wanda harsun canza launi ,iska ya furzar yana cewa"wai me yake damuna yanzu?",ina so na ganta".ya faɗa yana miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka yana fita yayinda zuciyarsa ke masifar azazzalarta da masifan son Halima tabbas yasan son Halima ya shammaceshi yayi masa mugun kamu shi kansa bazai iya faɗin taya hakan ya faru ba,burinsa kawai ya kasance da ita,duk wani motsin da zaiyi sai ta faɗo masa a rai,ɗaura kansa yayi akan sitiyari cikin sanyin murya yace"sonki yana azabtar da ni Halimana".tuno rigimarta yayi lokaci ɗaya ya saki ƙayataccen murmushi ya kuma dannawa motan shi key ya nufi unguwar su Halima.a waje yayi parking daidai ƙofar gidan Aunty Aysha kafin ya fito zai shiga gidan kamar kullun sanye yake da wando jeans ash colour sai t-shirt black colour mai dogon hannu sosai yayi matuƙar kyau sai fitar da sihirtaccen ƙamshi yake yi ga tsadaddiyan agogon gucci ɗaure a tsintsiyar hannunsa,cover's black ne a ƙafarsa sai sheƙi sukeyi ,a hankali ya tura ƙofar gidan Aunty Aysha ya shiga sai da yaje ƙofan parlo sannan yayi sallama da gudu Khalifa ya rugo ya rungumesa yana cewa"oyoyo Uncle".ɗaga yaron yayi sama yana shafa kansa kafin yace"ina Bilal?".ɗan shiru yayi kafin yace"yaje gano aunty Halima ,kuma Umma bata sani ba yace kada na gaya".lumshe idanuwansa yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarasa ta buga da ƙarfi ga wani irin tsinkewan zuciya lokaci ɗaya,dafe kansa yayi da yaji ya matuƙar sara mashi yayi saurin sauke Khalifa ya juya zai fito da sauri,riƙesa Aunty Ayaha tayi tace"Sudais lafiya kuwa?" shiru yayi kafin yace"Bilal,zan kira sa".be jira cewarta ba ya fice da sauri,hijab ta saka itama ta bi bayansa dan kwata kwata bata yarda da yanayinsa ba tasan dole akwai abunda ke damunsa.zaune Halima take akan bene sai jujjuya kai takeyi tana jin ansa kuwwar ihun da kuma maganar da ake gaya mata,Bilal kam yana ta tsaye gabanta yana riƙe da hannunta yana jijigawa yana cewa"Aunty ki buɗe idonki don Allah,nifa ke nazo gani ko Umma bata sani ba"ya karashe maganar kamar zaiyi kuka.a hankali ta soma buɗe dara-daran idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir kamar gauta lokaci ɗaya suka juye,zumbur ta miƙe tana rufe kunnanta da ƙarfi ga wani irin rikitaccen ihun data saki,raɗau haka Abu bilal yaji dodon kunnansa ya ɗaukar masa ihun Halima wani irin bugawa ƙirjinsa ya kuma yi ya tura gate ɗin gidan da sauri ya shigo ,Daddy,Amma da fitowarsu kenan dan jin ihun Halima yasa Daddy saurin ɗaga hannu yana cewa"ka sani hukuma ce zata fita da kai a gidan nan Aliyu,tabbas yau sai kayi dana sanin da baka taɓa yi ba a rayuwanka".ko kaɗan Abu bilal be gane abunda Daddy yake faɗa burinsa kawai yakai ga in da su Halima suke dan ya gama gane meke faruwa da wata irin murya da azabar ƙarfi ya furta"Bilal,Bilal".juyowa Bilal yayi yana ɗagawa Abu bilal hannu yana cewa"Abbana,ina sanka sosai,da fatan kazo man da Chocolate,Aunty Halima ma zata sha tunda ina santa zan sammata ko Abu bilal?".runtse ido da ƙarfi Abu bilal yayi yana cewa"no,no Hale..ee...ma,kada kimun haka".a kuma daidai lokacin ne Halima ta saki ihu tana saka hannu ta bangazo Bilal daga kan bene da azabar ƙarfi.da wani irin zafin nama Abu bilal ya ture Daddy dake gabansa yana cewa"a'a".ya ruga wajen a guje,sai dai kash kafin ya ƙarasa Bilal ya kai ƙasa idanuwansa a buɗe yana kallon Abu bilal ga hannunsa ya ɗaya yana miƙawa mahaifin nasa,shima Abu bilal ɗin hannu ya miƙa da niyar kamo na Bilal amma hannun Bilal ya riga nasa zuwa ƙasa,akan gwaiwowinsa ya faɗa yana kallon yarda jini ke malala daga cikin kan Bilal wanda ya fashe,daskarewa yayi a wurin wata irin kyarma na kwace masa ya kasa ƙwaƙwaran motsi a wurin da masifar ƙarfi ya rungumi Bilal wanda idanuwansa suke buɗe akan fuskar Abu bilal ,wasu hawaye ne suka zubowa Bilal kafin a hankali idanuwansa suka rufe ruf,Daddyma tsaye ya tsaya cak Aunty Aysha kam numfashinta ke niyar ɗauƙewa ta saki ƙara.a hankali Abu bilal ya soma ɗaga rinanun idanuwansa wanda i zuwa yanzu baya fahimtar komai miyan bakinsa ya ƙafe,kamar a mafarki haka yaga Halima kamar an jefota daga bene ta nufo ƙasa itama,wani irin ƙarfij hali yazo masa yayi saurin miƙewa ya tarota ta faɗo akan hannayensa,tana kuma sandarewa alamar ta some.da gudu Daddy ya karaso yana janyeta daga jikin Abu bilal yana jefa masa wani kallo mai wuyar fassaruwa.shikan kamar marar lakka haka ya faɗi a gaban Bilal,kuka yake son yi amma sam yaƙi zo masa ji yayi kansa na jujjuyawa kamar juwa na katantanwa da shi,da gudu Amma ta karaso tana janye Bilal daga jikinsa tana sakin kuka mai cin rai tana faɗin"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "a guje Faruq ya karaso wurin yana ansar Bilal daga hannun Amma yayi ɗakinsa dashi dan basa taimakon gaggawa,dishi dishi haka Abu bilal ke gani ko kaɗan ya kasa furta komai sai bin jinin Bilal dake malale a wurin yake da kallo kamar wani dolo,da ƙyar ya iya tattaro sauran yawun dake bakinsa masu masifar ɗaci ya haɗiye da ƙyar yana lumshe idanuwansa yasa hannuwa ya shafi fuskarsa.a rikice Faruq ke duba Bilal kasancewar yana da kayan aiki a gida amma sam Bilal yaƙi ko da motsawa a nan kuma ya tabbatar da cewa Bilal ya mutu,in da ya ajiyeshi kam gaba ɗaya wurin ya ɓaci da jiki,ji yayi kafafunsa sunyi sanyi kamar ba zasu iya ɗaukarsa ba,jan zani yayi ya lulluɓe gawar Bilal yana cewa"Allah ya karɓi baƙuncinka Bilal".kafin jiki a sanyaye ya fito parlo,tsai tsaye ya gansu Aunty Aysha sai kuka takeyi kamar zata shiɗe ,Amma ma kukan takeyi Daddy ne zaune a chair yasa Halima a gaba sai kallonta yake wanda har lokacin bata farfaɗo ba,kallonsa ya mayar ga Abu bilal dake tsaye a jikin bango ya lumshe idanuwansa yana kallon sama ,jijiyoyin kansa sun fito radau raɗau kamar an zana su kallo ɗaya zaki masa kiga tsantsar tashin hankali ƙarara a tattare dashi.cikin rashin ƙwarim gwaiwa Faruq ya ƙarasa gabansa yana dafa kafaɗarsa.a hankali ya buɗe idanuwansa yana kallon fuskar Faruq dake nuna tsantsar karaya lokaci ɗaya,idonsa ya mayar ga ash ɗin wandonsa wanda duk jinin Bilal ya ɓata,jan hannunsa kawai Faruq yayi zuwa cikin ɗakin da Gawar Bilal take a rufe,har gaban gadon Faruq ya kaisa yana bubbuga kafaɗunsa.wani irin tsinkewa gabansa yayi zuciyarsa ta harba da masifar ƙarfi hannu na ƙyarma yasa ya yaye zanin da aka rufe gawar Bilal da ita.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA ƘYAƘYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 18
Baya Sudais yayi saurin yi kamar zai faɗi tarosa Faruq yayi ,kasa cewa komai yayi gaba ɗaya ya koma batun-butumi zamewa yayi daga jikin Faruq ya zauna a chair tare da dafe kansa da duka hannu biyu,a daidai lokacin ne kuma Halima ta farka daga mugun mafarkin da takeyi tana raba ido,ƙoƙari takeyi ta tuna abunda ya faru amma ta kasa,ganin su Amma na kuka yasa ta yunƙura da ƙyar tana kuma kallonsu,safko ƙafanta tayi tana binsu da kallo kafin ta hango Faruq a ɗaki,miƙewa tayi kai tsaye ta nufi ɗakin jiki ba ƙwari,kamar marar gaskiya haka ta ƙarasa shiga ɗakin.saurin runtse ido tayi tana jin zuciyarta kamar zata fasa ƙirjinta ta fito saboda ganin gawar Bilal da tayi ,mayar da kallonta tayi ga Abu bilal dake duƙe har lokacin gabansa ta duƙa tare da ɗaura hannuwanta a kan jikin shi,cikin dishewar murya tace"Yaya talk to me,is'n't you talking".ɗagowa yayi yana kallonta hawayen dake maƙale a idanuwansa suna safkowa akan fuskarshi,ba ƙaramin tsorata tayi ganin hawaye a idon Abu bilal,idasa zama kawai tayi tana fitar da numfashi a hankali..lokaci ɗaya mutuwar Bilal ta zagaye ko ina kasancewar yaro ne na mutane ga fara'a .miƙewa Abu bilal yayi yana barin ɗakin da Gawan Bilal take,da Dattiya yaci karo a gate da Mama uwani da Karima ,kuka wewe haka Dattiya yakeyi yana sharar majina yana ganin Abu bilal ya kuma rushewa da wani sabon kuka yace"wallahi wannan yarinyan ta cucemu,Allah sai ya saka mana,dole yanzu mu wuce da ita chazi ofis idan na yarda Allah ya tsinan,meye wani Halima ?,a'a kaini raba ni dole ta biya Dilalu".ta gefansu Abu bilal ya raɓa ya wuce karima ta bisa da kallo hawaye na safkowa idonta ganin yarda lokaci ɗaya ya gama fita a hayyacin shi.ciki suka ƙarasa wani irin ƙwalalo ido Dattiya yayi yace"kul ba ruwana,meye wani gidan Alhaji Abu,wanda dasa hannunsa aka kore ni ina galantiyo a titi,tona tabbata da gangan ƴarsa ta kashe wannan yaro Dilalu,alqur'an hukuma ce zata rabamu,ni ba ruwana".kallonsa duk mutanan ɗakin suke yi a haka su Mamy suka ƙaraso harda Abba babu wanda yake komai har aka gama shirya Bilal .raba ido kawai Halima takeyi ta makure jikin bango .a haka aka shigo aka ɗauki Bilal zuwa waje dan yiwa gawansa sallah.babu wanda yaga fitar Halima sai dai aka jiyo muryarta da ƙarfin gaske tana kiran"Yaya Aliyuuu".daga duƙen da yake yayi saurin miƙewa ganin yarda ta fito babu ko hijab bare hula,tana hangosa tayi kansa da gudu tare da shaƙareshi tace"Yaya kace su dawo mana da Bilal ɗinmu Allah be mutu ba,kana kallo zasu tafi maka da ɗanka"kuka ya ƙwace mata ta kasa ƙarasa abunda take son faɗa,sosai ya kamata ya riƙe amma ya kasa cewa komai,gaba ɗaya ya nemi kalamai a bakinsa ya rasa .Lamis ne ya ƙaraso yana janyota luuu ta tafi ta sume a jikin Abu bilal,miƙawa Lamis ita yayi yana saurin juyawa ganin Abba da Daddy sunyo in da suke.haka Lamis ya ɗauketa ya wuce da ita cikin gida kafin ya fito aka sallaci Bilal aka tafi dashi maƙwancinsa(Allah kayi mana kyakyawan ƙarshe).kowa ya watse a wurin sai Abu bilal dake duƙe a gaban kabarin,wasu hawaye masu ɗumi suka zubo masa yana taɓa kabarin cikin cushewan murya yace"Allah ya jikanka Bilal,ka tafi ka barni,bana da wani farin ciki ko sauran amfani a duniya bilal haka na rasa Rumana kaima gashi yau na rasaka,hasbunallahu wani'imal wakeel".dafa kafaɗunsa Lamis yayi yana ɗagosa kasa kasa cewa komai yayi sai hannunsa da yaja,bin bayansu Faruq yayi shima he's restless a haka suka dawo gida.a cike unguwan take ta ko ina da maza manya da yara harda mata ko wannensu hannunshi ɗauke da muggan makakai kowa da abunda yake faɗa.da ƙyar suka kutsa zuwa gaban gate ɗin gidan Daddy.cikin rashin fahimta Faruq ya zaro ido yace"ban gane me kuke nufi ba".a fusace ɗaya daga cikin mazan yace"abunda kaji an faɗa dai,dole a fito mana da Halima muma mu kasheta mu rama abunda take yi mana,dama itace ta kashe Junaid ta kuma kashe Zahra ƴar gidan saneta jiya da dare ta kashe Habu da Lawali daga sun ganta tana bakin kango ita da wasu la'annanun irinta yanzu kuma sai ace ta kashe Bilal yaro bawan Allah ,wallahi mun gaji da shiru ana cutar damu".sakin hannun Abu bilal Lamis yayi da sauri ya shige cikin gidan kafin su lura.a dabarbarce yace"Amma ina Halima" Amma da suke tsaitsaye suna jin bala'in da ake waje ta nuna masa Halima da aka kwantar kan chair har lokacin bata farfaɗo ba,be jira cewarsu ba ya sunkuceta ya fito parlon rufa masa baya sukayi da gudu ya fice ta gate ɗin baya ya fice da Halima daga gidan.wata nannauyar ajiyar zuciya Amma ta sauke ganin sai da aka fita da Halima sannan mazan nan suka samu karfin buɗe gate ɗin gidan suka shigo cikin compound ɗin,sai kuma ga ƴan sanda da sojoji sun iso wurin ,take wurin ya hargitse sai da aka yi halbi sama sannan aka samu rangwame aka kora maza a waje
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment