Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings ,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too,ABU BILAL daban yake da saura.😘😍😀
FREE PAGES
PAGE 1

Tafiya takeyi da sassarfa ,idanuwanta dake sanye cikin farin medical glasses ɗinta wanda yake tamkar na gayu ya kuma ƙawata fuskarta takai dubanta ga tsadaddiyar Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta,ɗan zaro dara-daran kyawawan idanuwanta tayi tana kallon lokaci da alamu ta makara sosai.kayan jikinta na kalla dan ganin irin saurin da takeyi sanye take cikin uniform blue wando da hijab doguwa har ƙasa mai hannu sai farin ɗankwali wanda duk yarda ta janyoshi be hana gashin kanta bayyana ba,wanda yake kwance lub a goshinta harya kusa haɗewa da giranta,a kafaɗarta kuma irin jikkarnan ta goyo da mata ke yayine saƙale ta saka hannu ɗaya ta bar ɗaya yana yawo a bayanta.Halimatu Doguwace daidai misali bata da ƙiba ko kaɗan sai dai kuma jikinta ko ina a ciccike yake bata da irin farin nan sai dai tana da matuƙar kyau komai nata kamar ita tayi kanta,Halimatu bazata wuce shekara sha bakwai ba.A daidai bakin layin ta tsaya tace "washh Allah Khadija wallahi na gaji"ta ƙare maganar tana kallon Khadija dake tsaye ta haɗe fuska.juyo idanuwa Khadija tayi tace"Malama idan zakizo mu wuce kizo,haka kawai kin samu latti da wannan shiriritar taki".rausayar da kai Halima tayi tare da shagwaɓe fuska ta wuce gaba kawai.bin bayanta Khadija tayi tana mita kamar zata ari baki.dafe kai Halima tayi tace"billahil azeem kin dameni!!,zamu raba hanya yanzu ku...".kasa ƙarasa maganar tayi tana kallon gefenta.zaune yake akan farar kujerar roba yayi ɗaya kan ɗaya duk da yana zaune bazaisa ka kasa gane cewar shi dogo bane ba,yana da faffaɗan ƙirji,chocolate colour ne,in da fuskarsa ke ɗauke da daradaran idanuwa ga gashin girarsa baƙi siɗik kamar wanda yayi jagira,yana da dogon hanci mai ɗaukar hankali ga ƙaramin bakinsa dake ɗauke da laɓɓa masu tudu sunyi kamar browni kamar lite pink.yana da matsakaicin gemu sai gashin baki in da gefen fuskarsa ke da ɗan siririn saje kaɗan har zuwa saitin kunnensa,gashin kansa gwanin burgewa baƙi siɗik yasha aski sai ɗaukar ido yake yi.sanye yake da wando fari 3 quater sai farar T-shirt ,idanuwansa a lumshe ga hannunsa ɗaya ya ɗaga yana shafa sumar kanshi fuskarnan ɗaure babu alamar wasa a tattare da ita ABU BILAL kenan.wani irin ƙwalalo ido Khadija tayi ganin yarda Halimatu ta saki baki tana ƙarewa ABU BILAL kallo,hakan kuma yayi daidai daya soma buɗe lumsassun idanuwansa jin ido na yawo a jikinsa carab idanuwansa suka faɗa cikin na Halima da azabar ƙarfi ta rumtse idanuwanta tana ja da baya yayin da zuciyarta ta harba da masifar ƙarfi.wani irin fizga Khadija tayi mata suna barin wurin da sauri wani irin kallo Khadija tayi mata da masifa tace"kinyi hauka ne?,meke damunki haka?,kina so ki janyo mana bala'in da kab danginmu baxasu iya kare mu ba?,ni dai ki rufamun asiri yarda kike zuwa unguwar nan lafiya toki koma gidanku lafiya kin daiga ta silata kike shigowa unguwar nan".galala haka Halima kebin Khadija da kallo wanda ko kaɗan ta kasa fahimtar abunda take cewa.har lokacin gabanta be daina faɗuwa ba da ƙyar ta haɗo magana can cikin maƙoshi tace"waye shi?".Harara Khadija ta xabga mata tace"ban sani ba,kuma ni daga yau ki riƙa wucewa islamiyyan kawai na sameki a can".siririn tsaki Halima ta saki tace"banxa masifaffiya kawai"ta fizge hannunta tana shigewa cikin islamiyyan ,duka yinin ranar a haka Halimatu tayi shi gaba ɗaya bata fahimtar komai babu abunda ta koya a makarantar duk tayi kamar wata marar lafiya,gaba ɗaya Khadija na lura da ita amma haka ta share dan bata son tado maganar ɗazu.tunda aka tashi islamiyyan bakin islamiyyan yake cike da ɗalibai da gudu yaron ya ƙaraso gaban Halimatu ya janyo hannunta yace"Aunty dan Allah ki gyaramun"ya ƙare maganar yana kallon takalmar ƙafarsa da zaren su ya warware,juyowa tayi tana kallon yaron kyakyawa dashi yarone ɗan kimanin shekara biyar a duniya sosai uniform ɗin islamiyyar suka yi matuƙar amsarshi ,murmushi ta sakar mashi ta shafa kanshi tare da duƙawa tace"to brother".ɗaure masa igiyar takalmin tayi kafin yace"thank u".da murmushi a fuskarta tace"what's your name?".hannu yasa ya shafi sumar kansa ya furta"BILAL ALIYU".kafin tayi magana taga zaratan maza su biyu sun janye hannun Bilal daga jikinta a tsorace taja baya da sauri kamar zata faɗi ganin su ya matuƙar tsoratata babu annuri ko kaɗan a tattare dasu.numfashi Khadija ta mayar tare da ɗago Halima daga ɗuƙen da take cikin sanyin murya tace"Sadiya why all this?,please na roƙeƙi karki janyo wani abun daba shi bane".a daddafe suka wuce gida,tunda suka tunkaro in da tabar wannan mutumin na ɗazu take kallon wurin kamar idanuwanta zasu faɗo sai dai babu kowa a wurin,lokaci ɗaya taji ko kaɗan bata jin daɗin jikinta,haka a saɓule sukayi sallama da Khadija ita kuma ta kama hanyar gida tana tafiya da tunanuka iri iri a ranta.a matuƙar razane take bin jikinta da kallo wanda aka malale mata shi sharkab da ruwan kwata duka jikinta ya ɓaci har a saman glasses ɗinta ji tayi ranta ya matuƙae ɓaci da azamar sauri ta rufawa motar baya har in da sukayi parking ta tsaya tana ƙarewa Drivern motan kallo cike da masifa tace"ka kallah yarda ka ɓata ni da ruwan ƙazanta,ko dabba kayiwa haka aika tsaya kaga lafiyarta balle kuma mutun".a fusace ya ɓalle marfin motar ya fito yana binta da mugun kallo yace"anje an ɓata zan zuba maki tafi a wurin nan wallahi".tuni idanuwan Sadiya sun sauya kala a hassale tace"wallahi ko da wasa balle a gaske,duk wani abun da kake ji dashi to nawa yafi ƙarfin naka,idan kuma kana ganin wasa toka gwada,wanda besan darajar Ɗan adam ba kawai".sosai zuciyar Jagwado ta ɓaci dajin furucin yarinya ƙara a kansa hannu ya ɗaga zai kifa mata mari,ganin Abu Bilal ya buɗe murfin mota ya fito a hankali cikin takun ƙasaita ya ɗaga masa hannu sosai sautin muryarsa ya daki dodon kunnenta in da da ƙyar ya iya furta "kiyi...haƙu...ri"ya ƙare maganar da nisa a tsakani ya juya ya shige gaban gidan da suke tsaye.wani irin daskarewa a wurin Sadiya tayi tana bin wannan mutumi da kallo tuni taji duk wani ɓacin ranta ya gushe a haka ta juya ta nufi hanyar unguwarsu da babu nisa sosai tsakaninta da wannan...daidai ƙofar wani tanƙameman gate naga ta tsaya ,hannunta tasa tare da tura ƙofar masu gadin dake wurin su biyu suka miƙe da sauri sanye da uniform suna mata sannu da zuwa,fara'a faɗaɗe fuskarta tace"ina wuninku,nikam nace a daina tashi mun haka ku ɗin ai tamkar iyaye kuke a gareni".cike da jin daɗi da irin karramawa da dattako irin na Sadiya suke mata fatan alkhairi.tana ta ansa addu'ar da suke mata kafin ta nufi main Entrance na gidan.Sai lokacin na samu damar ƙarewa gidan kallo wani irin tanƙameman gida ne wanda zaka iyakiransa gari guda tsayawa faɗin tsaruwar gidan ɓata lokaci ne dan ko rade's ɗin dake parking lot abun kallo ne.ko ina ga masu aikin gidan nan sai shawagi sukeyi suna kuma yiwa Sadiya sannu da zuwa tana ansawa murmushi faɗaɗe a fuskarta ,masha Allah shine abunda na faɗa lokacin data shiga parlon aljannar duniya kenan babu wasu tarkace a parlon sai dai ya tsaru iya tsaruwa daga cikinsa ne kuma ya rabu har ɓangarori ukku.ɓangaten dama naga ta shiga tun a parlon ta soma kwaɗa sallama tare da kiran "Amma!,Ammana!!".wata farar dattijuwar mata ta fito cikin shiga ta alfarma fuskarta ɗauke da murmushi kallo ɗaya zaka mata ka hango tsantsar kamarta da Halimatus sadiya."ƴar albarka sannu da dawowa,ya akai na ga jikinki haka?"Amma ta faɗa.cike da soyayyar mahaifiyar tata ta langwaɓar da kai gefe tace"Ammana ruwa ne aka watsamun a hanya,amma yanzu zan gyara jikina "ta ƙare maganar tana tura ɗaya daga cikin ƙofofi ukku dake parlon.da alama kuma nan ne bedroom ɗinta,ɗakin ya tsaru komai na cikinsa royal blue ne ko ina ɗakin gyare yake tsab sai zuba ƙamshi yakeyi ,jakkar dake rataye kafaɗarta ta ajiye a ma'ajinta sannan kai tsaye ta wuce toilet,uniform ɗin ta soma cirewa sai da ta saka su a injin wanki ta wanke tas har inner's ɗin jikinta sannan ta sanyasu a wurin shanya dake toilet ɗin,sannan ta ƙarasa ciki ta soma sakarwa kanta shawa.da ƙarfi ta runtse idonta ganin wannan saurayin na ɗazu yana mata gizau babu abunda take gani sai siffarsa da kuma kunnenta dake tariyo mata dadaɗar muryarsa,a daddafe ta samu tayi wankan ta fito ɗaure da towel sai ƙamshin daɗaɗan sabulan wankanta takeyi kai tsaye gaban mirror taje ta busar da yalwataccen gashin kanta wanda yake baje har tsakiyar bayanta sannan ta shafa lotion da sauri sauri ,doguwar riga na kanti ta saka fara ƙal da ita ta feshe jikinta da turaruka masu daɗi sannan ta janyo agogonta ta saka ta kuma saka glasses ɗin idanuwanta taja veil ɗinta black tayo waje.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 2

kai tsaye parlo ta fito tana kallon wayar hammunta ƙirar samsung kusan cin karo sukayi da sauri taja baya tana ƙarewa Faruq kallo tun daga sama har zuwa ga fuskarsa dake ɗauke da faffaɗan murmushi,murmushin itama ta saki tace"Yaya Faruq yaushe ka dawo ne?".far yayi da idanuwa yana buɗe hannayensa yace"lokacin da little Ammiena ta manta dani note(Faruq yaron yayar Daddyn Sadiya ce wacce ta rasu,su biyu iyayensu suka haifa sanadin hakan Daddy ya sakawa ƴarsa Halimatus sadiya).murmushi tayi tace"ni dai ban manta da Yaya ba Allah".matsa masa tayi ya wuce ciki wurin Amma yayin da Halimatu ta fito main parlo na gidan tana kallon Hajiya mama dake hakimce akan chair hannunta ɗauke da remote tana canza tasha.duƙawa Sadiya tayi tace"Mama barka da gida".sakin fuska Hajiya Mama tayi kamar ba ita bace ke ɓata rai yanzu tace"a'a ƴar albarka an taso daga tahfeez ɗin kenan?".Gyaɗa kai Sadiya tayi alamar eh tana ɗago kanta tana kallon Daddy da shigowarsa gidan kenan fuskarta ɗauke da murmushi ta ruga tana karɓar jikkar hannunshi tace"Daddyna barka da dawowa".shafa kanta yayi yana janta a jikinshi cike da soyayyarta yace"lafiya qlau little,ya Tahfeez?".cikin sanyin murya tace "Alhmdllh".wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Hajiya Mama ganin Daddy ya janyo Halimatu jikinsa ji tayi kamar zuciyarta tayi zallo ta hito saboda tsananin kishin ita bata taɓa haihuwa a gidan ba,kuma Sadiya ita kaɗai ce ƴarsa duk duniya.a fili kuma sai ta saki murmushi tace"Daddyn Sadiya barka da dawowa,ya aikin?".cike da murmushi yace"lafiya qlau Hajiyar Halimatu ,ya fama da ƴar rigimar tawa?".nan ma dariyar tayi tace"ai kasan yau ana Tahfeez rigiman da sauƙi yanzu dai ake shirin farata"dukansu dariya suka saka kafin ta karɓi jikkar hannun Halimatu ita da Daddy suna wucewa babban part na cikin parlon.
Ɓangaren Abu bilal kuwa yana shiga madaidaicin gidan nasu ya soma halbar da bucket ɗin daya ci karo dashi a hanya,saurin miƙewa tsaye Mama tayi tana gyara kashin ɗaurin ɗankwalinta tana ƙarewa Abu bilal kallo wanda ta taso ne da masifa taji uban waye ya halba mata bokiti,wata dariya Datti ya saki yace"su Uwani masifa to ba ni ɗin da kika raina bane,masu gidan ne da kansu,sai naga kinyi shiru kamar ruwa ya ciki".ƙanƙance ido Mama Uwani tayi tace"to ai ina da gaskiya tunda bakai ka sayar mun bucket ɗin ba".ko kallonsu Abu bilal beyi ba ya wuce zai shiga part ɗinsa da gudu Bilal ya rugo tare da rungume Abbansa daga baya.wani irin lumshe idanuwa Sudeis yayi yana jin abun har cikin ransa yasan duk duniya yaron shi tilo ɗaya ke iya yi masa haka,fuskarsa kada ran kada han ya juyo tare da ɗaga yaron sama ,dariya sosai Bilal ya saki yana cewa Abbana"welcome".dawo dashi yayi akan ƙirjinsa tare da sunbatar goshinsa yace"thank u".shiru yayi alamar yana son sake wata maganar,fahimtar hakan da Bilal yayi duk da ƙananun shekarunsa yasan halin Abbansa tsab yasa yace"Tahfeez alhmdllh,nayi karatu da yawa,Abba yau har Aunty nayi a scul"."amma nan nan ka shigo mu ka fara iskewa ko sallamar bamu samu arziƙinta ba bare kuma gaisuwa,Allah na gani Aliyu halinka sai kai,haka kawai kaita cutar mu".rufe ido da ƙarfi Sudeis yayi yana kuma taunar lips ɗinsa kamar zai huda kafin ya juyo da runannnun idanuwansa yana watsawa Datti harara,ganin yana yin idanuwansa yasa Mama uwani shigewa ɗakinta da sauri tana kyarmar jiki.ba shiri Datti ya kwashi silifas ɗinsa yana niyar yin waje kusan cin karo sukayi da Aunty Aysha wacce tasha ado na alfarma daka ganta kasan hutu ya gama ratsata, kallo ɗaya zaka mata kaga tsantsar kamarta da Sudeis fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa shigowa tace"a'a ba kanta Kawu guduwa da silifas a hannu?,da alama yau ka taɓo ɗan rigimar taka kenan?".wiƙi wiƙi yayi da ido yana washe baki dan yasan yau kam yayi arziƙi bashi ba zuwa maula.ƙwafa yayi yace"kedai bari Aysha ,cutar dani kawai Aliyu ya gama yi,Allah yasan ko kallon banza ban taɓa yi masa ba".sauke Bilal Sudeis yayi bece komai ba ya wuce part ɗinsa yana ɓalle buttons na gaban rigarsa.ɗakine madaidaici parlo ne ɗauke da kujeru da kayan kallo komai na ɗakin fari ne tas gyare yake tsab sai zuba masifar ƙamshi yake yi,kai tsaye bedroom ya shiga nan ma ɗakine madaidaici ɗauke da gado da wadrobe da miro komai tsab,toilet ya shiga ya cire wandon jeans na jikinshi ya soma sakarwa kansa shawa ya ɗauki lokaci a toilet ɗin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa ga ƙarami yana goge kansa da shi,ƙarar wayarsa yasa ya fito parlo kallon Aunty Aysha yayi ya ɗauke kai ya kwashi tsaɗaɗɗun wayoyinsa ya koma bedroom.kallonsa tayi ta girgiza kai ta juyo tana sauraran surutun da Bilal ke zuba mata tana murmushi tana ɓare masa chololate ɗin data masa tsaraba.kai tsaye gaban mirrow yaje ya shafa lotion ɗinsa yayi ya feshe jikinshi da ɗaɗɗan turarensa masu masifar ƙamshi sannan ya buɗe wadrobe ɗinshi boxer ya ɗauko da singlet ya saka sannan ya saka crexy trouser ya saka T-shirt blue colour,agogon gucci ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa kafin ya tako a hankali zuwa parlon cikin ɗaya daga cikin kujerun ya xauna yana kallon Aunty Aysha ciki ciki yace"sannu".ko kaɗan batayi mamakin yarda yayi mata ba tasan halinsa sarai nan ma yayi abun arziƙi daya ce mata sannu,juyowa tayi ta kallesa tace"Sadauki Aliyu ni na rasa me wa'ancan tarkacen yaran keyi a ƙofar gidan nan,Aliyu kallo ɗaya xa'a maka ai maka kallon ɗan daba ɗan shaye-shaye wannan wacce irin rayuwe kake yi?,ka koma gida Aliyu ka ƙi ,kabar zuwa aiki ni na rasa meye matsalanka,to ka sani yau nazo ɗaukan Bilal ne,baxan iya bari ya taso yana ganin mahaifinsa a cikin irin wannan bauɗaɗɗiyar rayuwar ba".sosai maganar ɗauke Bilal ya daki zuciyarsa duk tsawon maganar da takeyi sai yanzu ya ɗago yana ƙare mata kallo.tabbatar masa tayi tace"yes,yau zan ɗauki Bilal ko kana so ko baka so,ace yaro ko islamiyyah yaje wa'ancan ne zasu je ku ɗauko shi?".lumshe ido yayi ya rasa abun cewa da ƙyar ya iya haɗo kalaman"Aunty no..kada..ki"shiru yayi ya kasa ƙarasawa yana jin bugun xuciyarsa na tsananta,shareshi tayi ta wuce bedroom ɗinsa akwati ta ɗakko ta soma saka kayan Bilal a ciki tas ta kwashe komai niƙi niƙi ta fito da akwatin parlo ,shikam Abu bilal kasa cewa komai yayi illah kallonta da yakeyi,janyo hannun Bilal tayi tace"ka fito da akwatin xanje mu gaisa da Mama Uwani sannan mu wuce.bata jira cewarsa ba ta wuce ɗakin Mama Uwani.da sallama a bakinta ta shiga ɗakin ,ansa sallamar Mama uwani tayi tace"a'a Aysha ce,sannu da zuwa".da yauwa Aunty Aysha ta ansa ta ƙarasa shiga tana janye da hannun Bilal a saman tabarmar da Mama uwani ta shimfiɗa mata ta xauna bayan sun gaisa tace"Mama nazo tafiya da Bilal ne".zaro ido Mama tayi tace kice mana yau gidan ba lafiya kawai muyi ta kanmu,ɗauke Bilal a gidan nan ai tamkar kafa wani tashin hankali ne".dariya sosai Aunty Aysha ta saki tace"lallai yaukam akwai rigima ku ƙyalesa yayi ya gama"miƙewa tayi ta buɗe jakkarta ta ibo kuɗi masu yawa taba Mama uwani tayi mata sallama,sosai tayi mata godiya sannan ta rakota ƙofar ɗaki.tsaye Aunty Aysha ta hango Sudeis ya jingina bayansa a bango ya lumshe idanuwansa ga hannuwansa rumgume a ƙirji.matsowa tayi kusa dashi tasa hannu ta janyoshi tace"haba autan Mamy ka daina ɓata ranka,kaga ba nisa ne tsakanina da kai ba ko yaushe idan kaso zaka iya zuwa kaga Bilal,kayi haƙuri zanyi hakan ne duk dan tarbiyarsa ta gyaru".shagwaɓe fuska yayi tare da langwaɓar da kai kamar wani ƙaramin yaro shafa kansa tayi tace"am sorry my lovely bro"..murmushi ya sakar mata wanda yayi matuƙar ƙawata fuskarsa.sama ya ɗaga Bilal yana shafa kansa suka fito waje,a nan suka samu Datti yana ta kwashewa su Jagwado albarka san ranshi,miƙewa yayi da sauri yana gyara hular kanshi yana matsowa kusa da Aunty Aysha,a lokacin har an saka akwatin Bilal a motar da tazo dashi.kuɗi da yawa ta bawa Dattiya sannan tayi masa sallama kafin ma ta idasa maganarta yayi gaba abunsa tunda ya kwashi kuɗi,zagayawa gefen motar yayi ya durƙusa ya kama hannuwan Bilal yana kallonsa karo na farko da naga yayi magana mai tsayi yace"Allah yayi maka albarka,ka kula da karatu sosai ,ka zauna wurin Aunty xanzo ko yaushe ina ganinka kaji".ido cikin ido Bilal ke kallon Abbansa can yace"Abba zaka riƙa kawo mun chocolate ɗina a gidan Aunty ko?".gyaɗa masa kai yayi.sannan yaci gaba da cewa "to Abu Bilal na gode"ya faɗa tare da rungume Abban nasa,shima rungumesa yayi yana jin zuciyarsa na zafi a haka ya cireshi daga jikinshi ya sakashi mota ya rufe,har motar ta ɓace Bilal na ɗaga masa hannu.juyawa kawai yayi ya koma cikin gidan,kai tsaye bedroom ya shige ya faɗa saman bed tare da rumtse idanuwansa abubuwa da yawa suna dawo masa a kai.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

FREE PAGES
PAGE 3

Ko kaɗan a daren Abu bilal kasa runtsawa yayi gaba ɗaya tunaninsa da komai nasa ya gama birkicewa,ganin abun bamai ƙarewa bane yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya soma sallah,wannan yana ɗaya daga cikin nagartan halayansa duk tsanani be manta da sallah ba da kuma azumin alhamis da litinin ,haka zalika yaransa ko me sukeyi basa bari lokacin sallah ya wuce su.sai bayan yayi sallahn asuba ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi akan sallayar.Tun sassafe Karima ta fito tsakar gidan ta soma share-share(Karima ƴar mama uwani ce).bayan ta gama ta tattaro wanke wanke tana wanke wa,kamar yarda ta saba duk kullun tana gamawa ta ɗaurawa Mama uwani girkin wainan da takeyi na siyarsa,a hankali gidan ya soma tara mutane masu siyan waina,hayaniyarsu ce ta tashi Abu bilal daga bacci wanda dama shi duk irin nauyin baccin da yakeyi motsi kaɗan kan iya tashin shi,wani siririn tsaki ya saki saboda ya tsani wannan sa'an ta Mama Uwani babu abunda suka rasa amma ko kaɗan ta kasa haƙura da wannan sana'ar,zura jallabiya yayi ya fito fuskarnan murtuke sai ɗacin rai yakeyi saurin duƙar da kai Karima tayi ganin irin mugun kallon da yake jefarta dashi,da sauri ta miƙe tayi baya,ji kakeyi gidan yayi tsit gaba ɗaya masu siyan wainan sunyi shiru a tunaninsu yabar gidan tun da sukaga su Jagwado basa ƙofar gida.wiƙi wiƙi da ido Datti yayi sana baya baya yana faman boye rigar dake jikinshi dan rigar Abu bilal ɗince an mashi shanya jiya ya ɗauke yace"Allah ya soni dama Uwani tace in ɗauka in gwada muga ko zaiyi mun kyau,banni dai ban taɓa satar maka kaya ba,ah tau Allah na tuba me akayi akayi wani kayan Sude can bare shi Sude ɗin".wani irin mugun kallo Abu bilal ya jefesa dashi kafin ya halbar da ƙatuwar robar da Karima ta gama zuba ruwa ciki,tuni su Jagwado suka shigo a guje suka kora masu siyan waina,ƙafa yasa ya halbar da ƙullun wainan.da sauri Mama uwani ta miƙe tace"Amma Dattiya kaji tsoron Allah ni nasan kama ɗauki kayanshi bare nace kasa ko xai maka kyau?".ganin da gaske Abu Bilal ƴan ɓannar yake ji sai ɓarin kaya yake yi yasa ta dauke roban kuɗinta tayi ɗaki a guje tana danna kuba.Karime dake rakuɓe ya dakawa tsawar da yasa ta soma sakin ƙara da ƙarfin gaske tace"Yaya Aliyu na tuba wallahi bazan sake fita nayi dare ba".wani kyakyawan mari ya sakar mata wanda yayi sanadiyar dauke jinta da ganinta na mintoci kafin da ƙyar ta fizgo baki da niyar yin ihu ,suman tsaye tayi lokacin da Rambo(karen Abu bilal)yayo kanta yana sinsinanta,a guje Jagwado yazo ya shiga tsakaninsu ya riƙe Rambo yace"Allah ya huci zuciyar mai gida,hakan bazata sake faruwa ba insha Allahu".da kausashiyar murya ya kalleta yace"kin san sauran ai".ya wuce ɗaki yana hararar Dattiya dake laɓe bakin kofa yana niyar sakin fitsari a wando.yana shiga ɗakin towel ya ɗauka ya wuce toilet yin wanka.minti 40 yayi ya gama shiryawa tsab cikin ƙananan kaya kamar kullun yau kam harda p-cap ya murza a kansa sai tashin masifar ƙamshi yakeyi duka kayan jikinsa dark blue ne dama Abu bilal ba daga baya ba wurin saka takalmi sau ciki,sosai ya fito ɗan gaye dashi yana kuma ɗaukar hankali.jin ƙamshin turarensa ya fara tunkaro waje yasa Karima yin saurin ɗauraye robar dake hannunta tayi saurin lafewa bayan kitchen tana raba idanu,wani irin taji lokacin da taga ya fito,ƙura masa ido tayi kamar zata zazzago idanuwanta.tsaye yayi bakin ɗakinshi babu kowa a tsakar gidan kuma ta gyara ko ina tsab.ƙwafa yayi yace"zan kwakwale idanuwanki masu kama dana mayu".da sauri Karima tayi saurin yin ƙasa da kanta tana jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito dan masifar tsoro,tasan ko be ganta ba yana gane idanuwa a kansa,kai tsaye waje ya fita in da ya iske yaransa a wurin miƙewa sukayi suna musabaha dashi kafin ya zauna kan kujera tare dayin ɗaya kan ɗaya ya kuma lumshe idanuwansa.Aguje Halima ta fito tana saka Ahlari a jakar dake rataye a kafaɗanta saurin riƙeta Amma tayi tace"Little ae baki makara ba bare kuma kiyi mani wayau ki fita baki karya ba".wani irin kwaɓe fuska tayi kamar zata saki kuka tace "wallahi Amma basan karin nan nake ba,ki barni dan Allah".zaro ido Hajiya Mama tayi tace"haba Sadiya babbar budurwa Tahfeez fa zakije ina amfanin fita baki ci abinci ba,yanzu tau bara na haɗa maki a lunch box".kyawawan idanuwanta ta lumshe kafin ta waresu tace"to Mama".cike da tsananin soyayyah Faruq ya kalleta yace"ƴan mata yau ni zan ajiyeki a school gaskiya".raurau tayi da ido kafin ta zagaya da sauri wurin Daddy ta saƙalo hannuwanta akan wuyanshi ta kwantar da kanta a kafaɗanshi cikin turo baki tace"Daddyna ka gaya masa ni nafi son zuwa Tahfeez a ƙafa,ƙwaɗayin ladan nake yi".murmushi Daddy yayi ya shafo kan ƴar tasa yace"dandai kince lada Ammina amma ko ni basan fitanki a ƙafa nake yi ba,kinsan yanzu duniyan ta lalace".juya idanuwa tayi kamar mai tunanin wani abu can tace"to Daddy kuyi mani addu'a zanje lafiya na dawo lafiya da yardar Allah".murmushi Hajiya Mama tayi tace"insha Allah kuwa,zoki wuce kada kiyi latti kinji".karɓar box ɗin tayi cike da ladabi ta dan durƙusa tace"na gode

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment