Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yaji kayan yaji sai da ya tabbatar ta ƙoshi kafin ya taimaka mata ta kwanta yayi mata addu'a ya shafa mata sannan ya rufeta da duvet ya fita.ikon Allah ne kawai ya mayar da Abu bilal gida ko kaɗan be kula karaɗin Dattiya ba ya faɗa ɗaki ya saka key yana ji zuciyarsa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito saboda tsananin xafin da take masa,naushi ya kaiwa bango ya soma ɓarar da duk abunda yazo gabansa yana fitar da wani nishi marar daɗin ji.a guje Karima tazo ƙofar ɗakin tana bugawa da ƙarfi cikin muryar kuka take cewa"Yaya dan Allah kayi haƙuri ka buɗe,yaya kada ka illata kanka,dan Allah ka buɗe".ta ƙare maganar tana jijjiga door ɗin ɗakin.ganin bashi da niyar buɗewa yasa da gudu tayi waje babu ko hijab a jikinta cikin sa'a kam taci karo da Jagwado wanda zuwansa kenan cikin kuka tace"Abu bilal ne,Abu bilal ne".be jira jin me zata ce ba ya tureta yayi cikin gidan da gudu.itama ta rufa masa baya ganin ɗakin a kulle yasa ya fito da key's ɗinsa ya buɗe ɗakin dan shi kaɗai keda key ɗin ɗakin Abu bilal.a daidai lokacin ne kuma Abu bilal ya dafe kansa da ƙarfi yana ganin ɗakin na jujjuyawa dashi ya tafi luuu zai faɗi,da matuƙar ƙarfi Karima tayi tsalle cikin ɗakin ya faɗo a jikinta suka faɗi tare .lokacin da Jagwado ya ɗagoshi a sume yake .

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.

2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 12
Kamar ana mintsininta haka takeji a baccin a matuƙar razane ta farka daga bacin babu kowa a parlon dama bacci ne yaɗan ɗauketa kai tsaye hanyar waje tayi,babu kowa a farfajiyar alamun duka maza masu aikin gidan sun wuce masallaci don yin sallar la'asar gate ta ɓuɗe tana ci gaba da tafiya.fitowarsa kenan daga gidan Aunty Aysha sauri yakeyi ya tafi masallaci dan shigowarsa unguwar kenan da ido ya bita ganin ko shoe babu a ƙafarta balle kuma hijab wanda tunda ya santa be taɓa ganinta ko da veil a waje ba sai hijab saɓanin rana daya da dare ya ganta ta fito a haka.taɓe baki yayi duk da yana da yaƙinin ba ita bace ba yayi wucewarsa masallaci gudun kada ya rasa jam'i.minti 10 da faruwan hakan ya fito daga masallaci gaya mutane tsaye a ƙofar gidan su Halima,shafa kai Faruq yayi yace"tabbas da kowa ya tafi sallah ta fito,abun tashin hankalin ma ba'asan ina ta nufa ba".ta gefansu ya raɓa ya wuce ko kallonsu beyi ba.da gudu Khalifa ya shiga gida yana cewa"Ummi,Ummi Yaya Halima ta ɓata ba'a ganta ba".dungure masa kai tayi tace"liar,ka dai san ba kyau ƙarya"."wallahi Ummi da gaske nake ga Uncle Faruq can a waje ma".kallonta ta mayar ga Abu bilal dake shigowa gidan hankalinsa kwance tace"Aliyu wai da gaske ne".tsura mata idanuwa yayi yace"what"."wai Halima ta ɓace"ta ƙarashe maganar tana ajiye bucket ɗin sock's na yara data wanke.taɓe baki yayi yace"i think so".kafin ya kuma magana ta zare hijab ɗinta dake ajiye a parlo data gama sallah tayi waje hankalinta a matuƙar tashe dasu Faruq ta fara cin karo cikin tashin hankali tace"Faruq anga Haliman?,ina taje? yanzu khalifa ke gayamun".kasa magana yayi sai dai Lamis yace"a'a of to now ba wanda yasan in da take ma"."innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "ta faɗa tana shihewa gidansu Halima a tsaitsaye ta samu su Amma wanda tsantsar tashin hankli ya gama bayyana a jikin Amma.nisawa Imam yayi yace"tabbas ba zata wuce cikin wani wurin ba a kusa da gida ,iskan jikinta ne suka fitar da ita ,kada ku damu insha Allah data dawo daidai zata dawo gida".zufa Daddy ya goge yana cewa"hasbunallahu wani'imal wakeel,Allah ka tsare mun ƴata a duk in da take"gaba ɗaya ya gama rikicewa duk addu'ar data zo bakinsa ita kawai yake yi kafin ya taso ya dawo gida a ƙofar gida ya zauna shi da su Faruq suna jiran tsammani.Junaid matashin yaro kuma yaron maƙwabcinsu yazo da sauri gaban Daddy ya duƙa yace"Daddy ga Halima a kangon can".be ƙarasa rufe baki ba dukansu suka miƙe tsaye suna hango tsohon kangon da yake nuna masu wanda tsawon shekaru babu wanda yake gigin zuwa wurin duk shuko kin kuka ne wurin da abubuwa iri iri.kai tsaye wurin suka nufa kowa da abunda yake ayyanawa a ranshi.Halima kam kwance take a cikin kangon sai juye-juye takeyi kamar macijiya gaba ɗaya duk ta jiwa kanta ciwo ga azabar ciwo dake cinta.Oga sam ne ke zagayeta yana yayyafa mata baƙin ruwa mai masifar wari.jin ruwan takeyi tamkar zubar wuta a jikinta gaba ɗaya ta banban ƙare ta gama sauya launi duka jikinta a juye yake yayin da idanuwanta suka koma kamar garwashin wuta .tsaitsaye sukayi ƙofar kangon jin irin ihun dake fitowa daga ciki da sauri Junaid,Lamis da Faruq suka kutsa kai cikin kangon Junaid ne ya fara ƙarasawa ya ɗagota carab idonsu ya haɗu ido cikin ido,bismillah Lamis yayi ya ɗagata tsaye yana janyota waje tana tirjewa babu abunda take kallo sai fuskar Junaid hannu tasa da ƙarfi ta ingije Junaid yayi baya xai faɗi Faruq yayi saurin taro shi"yace what's that?,saboda ya taimaketa tana mace kun kawota wurin ƙazantar nan?".ko kula Faruq bata yi ba suna fitowa waje ta langwaɓe alamar ta sume,akan idon Abu bilal Lamis ya ɗakkota .wani irin tsuka yaja yana buga ƙofa da ƙarfi,saurin kallonsa Aunty Aysha tayi wanda isowarta ƙofar kenan cikin zafin zuciya yace"waye shi daya ɗaukota?".riƙe baki tayi tana ƙare masa kallo tsantsar kishi ta gani ƙarara a idonsa sharewa tayi tace"kana da damuwa da wannan ne,ina kana ganinta ta wuce ae,yanzu ake faɗa wai ka ganta,shine baka tsayar da ita ba?".taɓe baki yayi yace"did i send her?".wani haushi ne ya kama zuciyar Aunty Aysha kamar ta fashe da ihu haka ta ture Abu bilal ta wuce ciki dan tun ɗazu Abban Khalifa ya dawo.da Hajiya Mama Lamis ya fara cin karo.wani irin kwalalo ido tayi tace"Lamis ka haukace ne?"daburburcewa tayi ta kasa komai tana tunanin abunda zaije ya dawo.a saman carpet ya shimfiɗar da Halima ya soma cicire mata ƙayoyin da gashinta ya kwaso,sosai sukayiwa Junaid godiya kafin ya tafi gida.kusan awa ɗaya tana wanan baccin kafin ta miƙe tana faɗin Junaid da iya ƙarfinta riƙeta sosai Faruq yayi ya soma tofa mata addu'o'i kafin ta fara natsuwa.kamar saukar aradu haka suke yin mutuwar Junaid a cikin unguwar.kafin sallar magrib tuni ko ina ya ɗauka cewar Junaid ya mutu.tsurawa Hannuwanta ido tayi tana tuna mafarkin da tayi wai tana shaƙare Junaid wani wahalallan kuka ta saki tana rungume Amma da ƙarfi ,itama Amman riƙeta tayi cikin muryar kuka Halima tace"Amamana na kashe shi,wallahi ni na kashe shi,me yasa ya taimake ni?,me yasa yazo kusa da ni?".ta ƙare maganar kuka na ƙwace mata,saurin rife mata baki Amma tayi tace"kada na ƙara jin irin wannan,bake kika kashe shi ba kiyi masa addu'a dama lokacinsa ne yayi kinji".kuuuu haka cikin Hajiya Mama ya juya ga zufa dake karyo mata fizgar hannun Lamis tayi ta wuce bedroom ɗinta dashi tare da danna key cikin hassala tace"shin wai ni ko dai Amina(Amma) ta haifa mun kai ne,ita Haliman ƙanwar uwarka ce nace?,ka duba halin da ake ciki kowa ya gagara ɗaukota sai kai sallamamme,na rasa ina hankalinka da tunaninka suka tafi Lamis,kai baka ganin duk wanda yaje da niyar taimaka mata sai ta kashe shi?".tsurawa Hajiya Mama ido yayi cike da alamomin tambaya ya ɗaure da ƙyar yace"in dai zan mutu akan taimakon Halima a shirye nake na bada rayuwata ta,kuma ba ita ta kashe Junaid ba kwanansa ne kawai suka ƙare,idan bamu taimake ta ba waye xai taimaketa a wannan halin".hannu Hajiya Mama ta ɗaura saman kai ta sauke tace"yauni maga abunda ya isheni ni jamila,to bari kaji lai kaɗai na mallaka ban kuma shirya rasaka ba".murmushin takaici yayi yace"in dai baki cutar da Ɗan kowa ba toki kwantar da hankalinki babu abunda xai samu Muhammad Lamis"."ban gane wannan tambayar ba Lamis?,kana xargine akan condition ɗin Halima".shafo gemonsa yayi yace"a'a wai magana nayi kawai".rasa abun cewa tayi kafin ta nuna masa hanya tace"maza ka tafi gida wallahi idan na safko parlo na sameka ranka zaiyi matuƙar ɓaci Muhammad,zan saɓa maka ".shiru yayi kafin yace"to sai anjima",ya fice daga gidan.Faruq kam yana parlon Amma yana ta kallon Halima dake xaune taci kuka harta gaji har muryarta ta fara disashewa i zuwa yanzu kam wani mugun tsoron wani ya kusance tako ya taimake takeyi ta gama firgita da duk abunda ta gani a mafarki ta to tabbas tana buɗe ido dashi zata fara cin karo,hawaye ne suka kawo idonta ga zuciyarta tana bugawa da ƙarfi,hannu tasa tana janye eye glasses ɗinta tana share hawayen idonta."kiyi hakuri,bana son kukan nan"shine abunda Faruq ya faɗa.girgiza kai tayi tace"kowa in yi haƙuri yake faɗa mun,tabbas baku san abunda nakeji a zuciyata bane,baku san me yake faruwa bane shiyasa har kuke da bakin bani hakuri"."duk tsanani yana tare da sauki Ammina kiyi hakuri komai xaizo da sauki,kuma hakuri shi yake kawo nasara".

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 15
Nisawa Amma tayi tace"Sudais ya kasance yaro mafi soyuwa a wurin mahaifansa watau Alhaji Ahmad da Hajiya Maryam yaransu huɗu Aysha itace babba sai Aliyu sai kuma ƙannensa ƴan biyu watau Khaleel da Khaleem,Alhaji Ahmad kuwa ya kasance Aminin Mahaifinki tun yarinta suke tare kuma shima babban ɗan kasuwa,yaso Aliyu ya biyosa shima yayi kasuwanci sai dai Aliyu tunda ya tafi waje karatun Architecture ya daɗe bai dawo ba a kuma can ne ya samu aiki,yayin da ni ban taɓa ganin ƴarsu Aysha ba tunda aka haifeta Hajiya Maryam ta bawa ƙanwarta marigayiya Hajiya Aysha ita,a can ta girma a can kuma tayi aure,Aliyu ya taso cikin gata da soyayyah da kulawa sai dai ya kasance mishkiline na gaske wanda ko iyayensa sai sunyi da gaske yake iya buɗa baki yayi magana,wannan son da suke masa yasa suka lallaɓashi ya dawo gida nan Nageria in da aka buɗe masa Company ɗinsa yana harkar zane zane,a kuma lokacin ne Hajiya Maryam ta haifi yaranta ƴan biyu maza watau Khaleel da Khaleem yara masu matuƙar kama da juna kuma ya zamana duk duniya babu abunda Aliyu yake so sama da Khaleel da Khaleem duk in da zaije yana tare dasu kowa ya sanshi yasan twins ɗinsa rainonsu gaba ɗaya shi yayi".nisawa Amma tayi ta kurɓi ruwa dake kusa da ita sannan taci gaba da cewa"a kuma daidai wannan lokacin ne Hajiya Maryam ta buƙaci da Aliyu yayi aure,hankalinsa yayi matuƙar tashi saboda shi bashi ma kula ƴan mata bare kuma yace ga wacce yake so,kasancewar kusancin iyayenku maza yasa ni da Hajiya Maryam muka zama aminai komai a tare mukeyi sai dai ni matsalar dake damuna a lokacin shine da na samu ciki sai ya ɓare sai bayan su Khaleem sunyi wayau aka samu cikin dana samu ya tsaya har yakai matakin haihuwa,ina dab da zan haihu kuma Hajiya Maryam tazo mun da shawaran tana so taga Aliyu yayi aure tunda ita Aysha ta daɗe dayin aure,sai dai uwar riƙonta ta rasu kuma tabar ƴarta mace mai suna RUMANA rumana kyakyawa ce ajin farko son kowa ƙin wanda ya rasa gata da haƙuri da kuma kawaici hakan yasa na bawa Hajiya Maryam shawarar mexai hana su haɗa auren Rumana da Aliyu,sosai tayi na'am da shawarar tace kuma xata turomun Aliyu tunda taga ɗan gida na ne sai na masa bayani,hakan akayi tunda na masa magana bai musa ba haka ya yarda akayi auren duk da ba Son Rumana yakeyi ba a lokacin.bayan aurensu da Sati ɗaya kuma na haifi ɗana namiji lafiyayye yaci suna Ahmad watau sunan Abban Aliyu kenan".zaro ido Halima tayi tana kallon Amma kafin cikin rawar murya tace"shine wanda naga pic ɗinsa ɗakin Daddy na tambaya waye aka cemun na ajiye kawai?".gyaɗa mata kai Amma tayi tace"eh shine,kuma yayanki uwa ɗaya uba ɗaya"."Amma meyasa kuka ɓoye mun?,kuma yana ina?".girgixa kai Amma tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta tace"saboda faɗan hakan yana tada wani tsohon ciwo da kuma mumunan tabo ga dukkan ahalin guda biyu".shiru Halima tayi amma ta kasa fahimtar me Amma ke nufi da hakan.ci gaba Amma tayi da cewa"bayan na gama wankan Ahmad mahaifinki ya samu wata kwangila da zaiyi shekaru a ƙasar waje,bamu so rabuwa da juna ba saboda zamana da Ahalin Hajiya Maryam yana mun daɗi mun zama tamkar wanda muka fito ciki ɗaya,gadan gadan tafiya ta kama saboda shaƙuwar dake tsakanin su Khaleem da Ahmad yasa suka roƙemu damu bar masu Ahmad har Allah ya dawo damu lafiya,tabbas na firgita dajin wannan magana ganin shi kaɗai Allah ya bani amma Hajiya maryam tafi ƙarfin komai a wurina a nan take na mallaka mata Ahmad kuma muka tafi muka bar mata shi,sai dai ta waya mu gaisa.shekarar Ahmad huɗu su Khaleem kuma 6 daga lokacin ne kuma mumunar ƙaddara ta fara faɗawa a wannan family mai cike da soyayyar juna da aminci da zaman lafiya,kuma har lokacin bamu dawo ba ko ziyara bamu taɓa zuwa ba,Hajiya Maryam ta kirani tana gayamun cewa Alhaji Ahmad zaiyi aure,ni kaina na shiga ruɗu amma haka na daure ban nuna mata ba ina bata baki da haƙuri wata biyu aka yi auren Alhaji Ahmad da wata wai Hajiya Jamila wanda harta gama zamanta a gidan ban taɓa ganin ko da hoton ta ba.a lokacin kuma komai ya daidaita tsakanin Rumana da Aliyu yana matuƙar son matarsa yana kuma riritata baya son abunda zai taɓa mashi ita.bayan wata biyar da Auren Hajiya Jamila komai ya canza a gidan,Alhaji Ahmad bayajin maganar kowa sai tata,kuma sai abunda tayi a gidan be isa ya tsallaka koda kara ta gindaya ba,kuma ta shiga ta fita ta raba shi da Aliyu sai da yakai ko da kallo Alhaji Ahmad baya son ganin Aliyu bare kuma ya raɓesa,hakan ya dasa muguwar gaba tsakanin Aliyu da Hajiya Jamila wanda ita hassada da ƙyashi yasa bata son Aliyu kullun burinta bai wuce taga ya faɗi ba,haka naita bawa Hajiya Maryam Hakuri dan bana so tabar gidan uban ƴaƴanta,a kuma lokacin ne Rumana ta kamu da wani matsanan cin ciwo ta koma kamar mahaukaciya ta zaune,sai dai a kullun idan ciwon ya tashi a ɗaɗɗaureta da sarƙa a kuma rufeta a ɗaki,dan xataita yagar fatar jikinta ne tana kuma neman illata kanta,wannan al-amari ba karamin girgiza wannan ahalin yayi ba,anyi magani anyi har an gaji,wanan abun kuma shine farkon fara tarwatsa rayuwar Aliyu duk yabi ya susuce ya lallace baya bacci be da kwanciyar hankali saboda ciwan Rumana,har lokacin shekararsu goma sha biyu da aure amma ko ɓari Rumana bata taɓa yi ba,kuma duk ciwanta besa Aliyu ya rabu da ita ba ko kuma ya ƙara aure,haka yake xama ya bata abinci tana t dukansa tana yakushinsa amma be fasa kula da ita ba,gaba ɗaya ma ya tattara yabar zuwa aiki sai kula da Rumana.a wannan lokacin ne kuma Hajiya jamila da Aliyu sukayi wani gagarumin faɗa saboda ya kamata tana zuba magani a abincin Rumana,ya shiga tashin hankali wanda yakai har ya mari Hajiya Jamila ita kuma tayi amfani da wannn daman tayi masa alƙawarin zai biya marin daya mata ko ta wacce hanya".shiru Amma tayi tana share hawayen daya ƙi tsayawa a idonta tana kallon Halima tace"a cikin wannan yanayin kuma na haifeki kikaci sunan Ammin Faruq wanda itama a lokacin ne ta rasu riƙon Faruq ya dawo hannuna aka dangin mahaifinsa suka kai mana shi har Amerika,a wannan yanayin ne Aliyu ya fita dasu Ahmad ,a yarda yace ya barsu a mota kafin ya dawo ya samu babu Khaleel ,khaleem da kuma Ahmad,yayi ruɗewa iya ruɗewa in da a wurin suka bashi tabbacin wata mata ce tazo ta tafi da yaran,yacce suka kwatanta masa surarta lokaci ɗaya zuciyarsa tayi na'am da Hajiya Jamila ce,gida ya dawo yana tuhumarta ita kuma tace bata san anyi ba don duk ranar be fita ba,a kuma cikin ɗakinsa aka tsinci kayan su Khaleem ɗuk jini da wasu irin abubuwa da suke bada tabbacin Aliyu ya faɗa kungiyar asiri ne,sosai hankalin kowa ya tashi da ƙyar Abba ya kira Daddy yake gaya mana mutuwar su Khaleem da kuma Ahmad,ya girgiza sosai amma sai ya ɓoyemun yaƙi sanar da ni case ɗin dake faruwa kuma ya hanani yin waya da kowa.sam Aliyu ya birkice yaƙi ansar laifinsa ya kuma ɗauki alƙawarin ɗaukar mataki akan Hajiya Jamila ,a wannan lokacin kuma wani tashin hankalin ya doso kai in da Abba da kanshi ya kama Hajiya Jamila tana ihu a ɗaki ga Aliyu kwance kwance a ɗakin akan gadonta yayin da take fitar da jini tana ihun Aliyu yayi mata faɗe".wani irin miƙewa Halima tayi da sauri tace"be yiwuwa,wannan ba gaskiya bane,Yaya Aliyu bazai taɓa aikata haka ba ".ta ƙare maganar hawaye na zubowa a idonta.girgiza kai Amma tayi ta kasa tsayar da hawayenta tace"Ayyah Halima ki daina saurin yanke hukunci haka,mahaifiyar data haifesa ita da kanta ta bada shedan Aliyu yayiwa Hajiya Jamila fyaɗe".daskarewa a wurin Halima tayi ga tsananin tsoro daya bayyana ƙarara a idonta da ƙyar ta haɗiyi wayu mai masifar ɗaci cikin rawan murya tace"yaya za'ayi uwar data duƙa ta haifi ɗanta wanda tafi kowa yarda da ɗanta ta bada wannan ƙazamar shaidan ga ɗan data haifa da cikinta,anya Mamy itace mahaifiyar Yaya Sudais kuwa?".

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAMYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 16
Kallonta kawai Amma tayi tace"wannan kuma ko waye ya kallah yasan gaskiya,kuma da bata tabbatar da hakan ba da bata bada shaida ba".wasu hawayen ne suka kawo idon Halima ta kasa cewa komai kafin Amma taci gaba da cewa"a lokacin ne Abba ya kira Daddynki yana sanar masa da baƙin ganin da yayi"haka Daddynki ya kwasa ya tafi gidan amma ba abunda ya canza dan Abba yayi matuƙar fushi a nan ne yake faɗin ya rabu da Aliyu har abada kuma ya ciresa daga cikin ƴaƴansa ko da mutuwa yayi kada Aliyu yazo kan gawarsa kuma duk abunda yasan ya masa toya tattaro ya dawo masa dashi".ko kaɗan Daddy be nuna beji daɗi ba dan shima ya yarda ɗari bisa ɗari Aliyu ya aikata hakan saboda lura da shaidu da kuma yarda Hajiya Maryam ta bada shaida da kanta akan ɗanta,shima cikin fushi ya yayiwa Aliyu faɗa da wulaƙanci sosai ya kuma yi ala wadai da irin halin da Aliyu ya canza kuma a nan ne ya yarda Aliyu ya shiga ƙungiyar Asiri,shima yace bashi ba Aliyu kuma bazai yafe masa ran ɗansa daya salwantar ba,a takaice dai haka suka kori Aliyu da matarsa Rumana wacce take cikin halin ciwo,Allah kadai yasan yarda suka rayu bayan shekaru kuma akaji labarin Rumana ta samu ciki kuma a lokacin Aliyu yana zaune da Dattiya tsohon mai gadin da Hajiya Jamila tasa aka kora ,yanzu kuma bazan iya ce maki ga in da Dattiya yake ba,a wata majiyar wai Hajiya Jamila ta tari Aliyu ta faɗa masa lallai yayi hankali da kansa wannan duk yana daga cikin sakamakon marin daya yi mata ne kuma ya jira abunda zai faru na gaba,bayan ta dawo ne kuma Abba ya saketa duk wani asirin data masa ya warware,.a lokacin Daddynki yaso ya ganta yaji meya haɗa su amma sam Abba ya hana yace ba amfani kawai ya barta shi bazai iya ci gaba da zama da ita bane,wannan takaicin sakin yasa ranar da Rumana ta haihu ko tashi daga in da take bata yi ba Hajiya Jamila ta shigo ta kasheta har lahira ga yaro jariri kuma,a nan ne kuma Aliyu ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani saboda tsaban rikicewan da yayi ,daga wannan lokacin kuma babu wanda ya kuma jin labarin Hajiya Jamila har gobe kam,amma kuma Aliyu yana da ƙudirun nemanta a ko wanne yanayi ko da hakan zai zama abu na ƙarshe da zai aikata a rayuwarsa,mu kuma tun daga wannan lokacin alaƙar mu taja baya zan iya ce maki rabon dana ga wani cikinsu harna manta,Ammi kinji iya abunda na sani a rayuwar Aliyu,sanin gaskiyar wannan al-amari kuma sai Allah sai kuma wanda yayi fatanmu dai Allah ya bayyana gaskiya kowa ya gane matsayarsa".kuka sosai Halima ta fashe dashi gaba ɗaya ta gama rikicewa,idanuwanta sunyi jajir tace"Amma har raina ban yarda Yaya Aliyu zai iya haka ba,duk iya halinsa na fahimci yana da kirki ga addini sai dai ban musa shaye-shayen da yake ba shima wannan kuma na ɗauka duk ƙunci ne yasa ya faɗa wannan harkar amma ki yarda yana da zuciya mai kyau".murmushin da yafi kuka ciwo Amma tayi tace"nasan waye Aliyu ,kuma Aliyu a da babban malami ne yana da matuƙar ilimi na boko dana addini,fatanmu dai muyita yi masa addu'a har Allah ya bayyanar da gaskiya".kasa cewa komai Halima tayi ta miƙe ta fito tana share hawayen dake kuma zubo mata.tsayawa Faruq yayi yana ɓata fuska yana kallon yarda idonta ya canza launi alamun taci kuka sosai,langwaɓar da kai yayi yace"meyasa kike son wahalar da kanki haka?,dan Allah kiji tausayinmu Ammina,ki sani kece farin cikinmu a gidan nan,kuma kinsan yawan ɓacin ranki abunda zai iya janyowa".murmushin ƙarfin hali tayi tana cewa"na daina Yayana".murmushinsa mai kyau yayi kafin ya jata suka zauna yana mata fira har yaga taɗan sake tana dariya kafin ya tafi ya barta..
Ɗuƙe take ta rasa abunda ke mata daɗi yau kimanin kwana biyar kenan bata saka Abu bilal a ido ba bare kuma taji daga garesa kusan kullun sai ta shiga gidan Aunty Aysha amma bata ganinsa kuma kota tambayeta itama sai tace kwana biyu bata ganshi ba.miƙewa tayi tana jan Hijab ɗinta ta leƙo parlo ganin babu kowa yasa ta fita da sauri a gate kam babu wanda ya tareta ta fice daga gidan,gidan Aunty Aysha ta shiga da sauri ta ƙarasa ciki tana kallon motar Abu bilal a parking lot ,har tuntuɓe takeyi wurin saurin ta shiga,cak ta tsaya tana ƙare masa kallo wanda shi ɗinma ita yake kallo kamar yau ya soma ganinta,gani tayi yayi rama sosai da alama yana cikin damuwa.ƙasa tayi da kanta,sai lokacin shima ɗauke idonsa daga kallonta ya wuce kan chair ya zauna beko kulata ba,cikin parlon ta dawo daidai gabansa ta tsaya cikin rawar murya hawaye na kawowa idonta tace"Yaya ina ka tafi na daina ganinka?".banxa yayi mata ko kallonta beyi ba bare kuma tasa ran zai bata ansa,zama tayi a gabansa tana tanƙwashe ƙafafunta tace"dan Allah ka gaya mun Yaya".wani irin ɗaure fuska yayi kamar an saukar masa da mutuwa yace"i'm not your Yaya".wani irin haushi ya kama Khadija da shigowanta parlon kenan ta kalli Halima tace"malama tashi muje gida dallah"ko kallonta Halima batayi ba saima saurin miƙewa da tayi ganin Abu bilal yabi hanyar fita cikin ɗaga sauti tace"i know who you are".cak ya tsaya tare da lumshe idanuwansa da suka fara sauya launi ya juyo yana kallon Halima yace"then what?,everything you hear about me just believe it babu wanda bani nayi ba,duka ba zargi bane sai kuma me kike so ki sani bayan wannan?".wani irin kuka mai cin rai Halima ta saki da matuƙar ƙarfi ya runtse idonsa danji yayi sautin kukanta har cikin ƙwaƙwawalwar kansa ya rasa wanne irin yanayi ne yake ji a kanta a lokutan nan,cikin muryar kuka tace"wallahi bazan taɓa yarda ba,tabbas akwai wani abu a ƙasa ba zaka taɓa aikata irin haka ba".wani tsaki yaja afin ya tureta daga gabansa ya wuce abunsa.a nan wurin ta duƙe tana sakin wani kukan da gudu Bilal ya iso wurinta ya duƙa tare da tallabar fuskarta yace"Aunty,ki daina kukan bana so,ki daina zance wa Abba ya daina maki faɗa ina sanki kinji,duk wanda nake so Abbana yana sanshi ".sosai ta riƙe Bilal a jikinta amma ta kasa cewa komai bare ta tsaida hawayen idonta,hannu yasa yana goge mata hawayen fuskarta yana nuna mata alamun tayi dariya,murmushi ta ƙirƙira tana ƙoƙarin miƙewa.Khadija kam ta cika tayi faful a wurin ƙiris take jira ta fashe,jan hannun Halima tayi fuuu suka fice Bilal na binsu da kallo.ta baya Abu bilal

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment