Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mamana"kafin ta wuce tace"sai anjimanku kafin in dawo yau ayimun abun daɗi".ta fita tana kwashe hijabinta sama tana gyara riƙon box ɗinta.sake baki Amma tayi tace"naga ranar da Sadiya zata girma,kwatakwata yarinyar can bata da wayau sai shirme,kuji yarda ta fita tana yaye hijabi,duk ta wani sakalce a gari".murmushi Daddy yayi yace"ni dai a barmun Ammina tayi abunda take so,komai lokaci ne insha Allah zata daina data ƙara girma".cikin natsuwa take tafiya tana kallon littafin dake hannunta tana gyara haddanta,hankalinta kwance tana tafiya harta ƙaraso ƙofar gidan su Khadija,a daidai soron gidan ta samu Khadija tsaye da alamu fitowarta kenan itama da shiga irin ta Sadiya,washe baki Halima tayi tace"to ki fito muje dan ni nan ba tsayawa zanyi ba".murmushi Khadija tayi tace"a lallai yau dan an fito da wuri ba ae dole kice haka,ni wuce muje".a haka suka jero suna tafiya.yauma Halima ce side din da su Abu bilal suke zaune.ganin unguwar ƙwalam ba kowa yasa Khadija zaro ido shaf ta manta da yaune lahadin ƙarshen wata kuma yaune yaran Abu bilal ke gyara unguwa kuma babu wanda ya isa ya fito bare ya biyo ta hanyan.tsayawa sukayi da sauri ganin su Jagwado sun tsaya a gabansu,ras ras haka gaban Khadija ya bada sauti yayin da Halima kam ko a jikinta dan tsab ta gane Jagwado shine wanda ya watsa mata ruwan kwata a jiki.littafin dake hannunta ta rufe ta kwashe Hijab dinta ta saka littafin a jakka,cikin rawar baki Khadija tace"dan Allah kuyi haƙuri wallahi na manta shiyasa na janyota muka biyo ta nan hanyar"gaba ɗayansu juyowa sukayi suna ƙarewa Halima kallo wanda ko kaɗan bata san me sukeyi ba gaba ɗaya ta zuba kyawawan idanuwan ta ƙure Abu bilal da ido ko kiftawa bata yi.idanuwansa a lumshe kamar ko yaushe cikin kausasshiyar murya yace"bar kallona"ko kaɗan taƙi dainawa saima lumshe ido da tayi lokacin da raji daddaɗar sautin muryarsa ta sauka a dodon kunnenta.wata uwar tsawa Jagwado ya daka mata wacce tasa ta juyo da azabar ƙarfi cikin hassala itama tace"dallah malam kabar mun tsawa tun da kai ba uban.."kasa ƙarasa maganar tayi ganin Abu bilal tsaye a gabanta yana jefarta da mugun fusataccen kallo.har ƙasa Khadija ta duƙa tace"Abu bilal dan girman Allah kayi haƙuri baƙuwace anan,insha Allah ba zata sake kallonka ba ko yiwa yaranka rashin kunya"cikin sauri Khadija ta janyo Hijab ɗin Halima tace"ki basu haƙuri".sakin baki Halima tayi kafin tace"tabɗi,wallahi bazan bashi ba,ko ba shine ba jiya ya watsa mun ruwan kwa.."saurin saka hannu tayi ta rufe bakinta ta kuma fashe da kuka saboda ɗallin da Abu bilal yayi mata a baki fuska ɗaure yace"uwar rashin kunya".ƙasa tayi da kai tana rusa ihu tare da bubbuga ƙafafuwanta tanayin baya baya tana cewa"Allah sai na gayawa Daddy,dama kaima mugune irin wancan"ta ƙare maganar tana nuna Jagwado da hannu.wani uban haushi ne ya turnuƙe zuciyar Abu bilal cikin cool voice yace"bara na maki duka sai ki kawo kaka ba Daddy ba".wani irin zaro ido tayi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta yarda box din hannunta ta fasa wata gigitacciyar ƙara wanda sai da Abu bilal ya rufe kunnuwansa ya kuma rumtse ido da ƙarfi,sannan Halima ta sheƙa a guje har tana ture shi.ƙwafa yayi yana kallon gudun da takeyi wanda taƙi biyu xaiyi ya kamata ya juyo yacewa Khadija"bar nan".har ƙyarmar jiki takeyi ta miƙe zata bar wurin a tsawace Jagwado yace"your box".kwashe box ɗin tayi itama ta runtuma a guje tana godewa Allah daya sa basu faɗa tarkon Abu bilal ba.a hanya ta samu Sadiya,tana ganinta ta ƙalƙale da dariya harda riƙe ciki .wani uban harara Khadija ta jefa mata tace"kici gaba tabbas wata rana bazaki dara ba in dai akan Abu bilal ne,dan baki san waye shi ba shiyasa sakarcinki yake sawa kike neman cutar da rayuwarki a banza,ina mai tabbatar maki kuma Mugun da kika kirashi tabbas zai maki aikin mugunta".wani irin lumshe ido Halima tayi tace"wow nice name Abu bilal"sai kuma ta saki ƙayataccen murmushi.tsaki Khadija taja ta wuce warta cikin islamiyya har lokacin gabanta be daina dakan ukku ukku ba.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

FREE PAGES
PAGE 7


```Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans

Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.

Lumshe ido Halimatu tayi kamar mai bacci sai kuma ta ware idanuwanta akan fuskar Khadija tace"ni bance maki am in luv with him ba,just dai i want to be with him that's all".Dafe kai Khadija tayi tace"lallai kam kice tashin hankali na dunfaromu kuwa,wannan mutumin kina tunani yana da feelings akan wani abu wai soyayyah?,to bari kiji Abu bilal besan meye tausayi ko soyayyah ba,a duk duniyar nan ina ga yaronsa da yayarsa kawai yake tausayi yake kuma ɗagawa,ina tunanin idan kika fahimci waye Abu bilal kece mace ta farko da zaki fara nisanta kanki dashi".wani irin faɗuwa gaban Halimatu yayi sai kawai ta share tace"ashema yana da feelings tunda har yana iya aure ya haifi yaro".ƙwafa Khadija tayi tace"ina dai faɗa maki idan ma son shi kika fara to kiyi gaggawan cirewa dan a duniya babu wanda ya tsana sama da mutun yace yana son shi".fari da ido Halima tayi tace"what ever".suna a haka Faruq yayi ƙwanƙwasa ƙofan jin tace"yes come in "yasa yace"Faruq ne".dariya khadija tayi tace"eh Yaya ka shigo".tura ƙofan ɗakin yayi ya shiga bakinsa da sallama kai tsaye gaban Sadiya ya duƙa yace"Ammina sannu,how is your body"ƙasa tayi da kanta tace"Alhmdllh".kallonta yayi kafin yace"ina kike jin pain ".lumshe ido tayi tace"no where,dama fever ne".gyaɗa kai yayi kafin ya miƙa mata Drugs ɗin hannunshi yace"kisha yanzu and at the night kuma".a hankali ta furta thank u.murmushi yayi kafin ya juyo yace"Khadija ya gida da Ummi?".sakin baki tayi tana dariya tace"haba Yaya Faruq ni da ka manta ko ina existing ma a room ɗin nan,saboda ƴar rigima ba lafiya".murmushi ya saki yace"ba haka bane,kinsan dai Ammin tawa uwar raki ce ae".murmushin itama tayi tace"haka ne kam,su Ummi suna lafiya,ai kwana biyu baka leƙa ba".shafa kansa yayi zuwa gemunsa yace"when i'm less busy zan shigo na gaishe ta"daga haka ya miƙe ya fita yana janyo masu ƙofan.nannauyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace"ke ga namiji daya ansa sunansa namiji mai nagarta amma ki wani maƙalewa wani".cikin rashin fahimtar in da zancen nata ya dosa tace"who's that".harara Khadija ta zabga mata tace "zaki cemun baki san Yaya Faruq yana sonki bane?".a bazata tambayar yazo mata ta wani ƙwalalo ido tace"haba mana is just your imagination he's my Yaya fa,mu duka Amma ne fa ta rainemu".Dariya zancenta yaso bawa Khadija tace"ai naga dukanku ita ta haifesu kuma babu aure a tsakaninku"."kinga Khadija i can never imagine dating Yaya Faruq,please let's call up the chapter".Halima ta faɗa.
Shiru Khadija tayi bata kuma cewa komai ba ta miƙe tsaye tana cewa"malama tashi ki raka ni".miƙewa Halima tayi tana janyo long hijab ɗinta mai hannu ta saka tace "muje".a jere suka fito a babban parlo suka samu Daddy da Amma suna kallon news.Har ƙasa Khadija ta duƙa ta gaishe da Daddy shima cikin sakin fuska ya ansa yana saka mata albarka 10k ya bata yace ta gaishe da su Ummi.langwaɓar da kai Halima tayi tace"let me escort her".jinjina kai Daddy yayi yace"a kula da hanya".da to suka ansa kafin tayiwa Amma sallama ta fito,a jere suka fita daga gidan.har sun soma tafiya daidai ƙofar gidan Aunty Aysha Halima taci burki tare da kallon Khadija tace"ki rakani nan mana,2days ban shiga wurin Aunty Aysha ba".kallonta Khadija tayi tace"amma baxamu daɗe ba gaskiya bana son magriba yamun a hanya".ta ƙare maganar suna tura ƙofan gate ɗin gidan.da gate man suka fara gaisawa da yake yasan Halima ya barsu suka wuce ciki,babu lefi shima gidan yana da girma ,suka tura main entarance na main parlo bakinsu ɗauke da sallama.tsaye yake ya juya baya yana zuba ruwa a mug,sanye yake da ƙananan kaya kamar kullun yayi sagging trouser ɗinsa har kana iya hango farin boxer ɗin dake jikinsa,duk yarda sukeyin sallaman hakan besa ya juyo ba sai da Aunty Aysha ta fito daga kitchen tace"kai dai Aliyu naga ranar da zaka bar wannan mishkilancin naka ace sallama ma anayi ba zaka iya buɗe baki ka ansa ba".juyowa yayi yana kafeta da ido bece komai ba nan idonsa ya safka akan Halima da yake janyo hijab ɗinta daga jikin door,murmushi Aunty Aysha ta saki tace"haba Halima ai nayi fushi gaskiya,yaushe rabonki da gidan nan saboda Allah,ko jiya kina tahfeez na leƙa na gaishe dasu Amma".da fara'arta itama ta ƙaraso cikin parlon tana cewa"wallahi Aunty school ne baya bari".ta ƙarashe maganan suna zama karab idanuwanta suka sarƙe cikin na Abu bilal wanda yake kai Mug ɗin ruwan sanyi bakinsa wata uwar harara ya afka mata ,da sauri tayi ƙasa da kanta tana cewa"Aunty ina su Nahnah?".juyawa tayi tace "ae kinsan da yake mun ƙara yawa gidan na tabbata Bilal da Khalifa sun janye mun ƴar auta suna baya ana hawa keke".Sai lokacin Khadija taga Abu bilal zaro ido tayi tana addu'ar Allah yasa kada Halima ta ganshi.miƙewa Aunty Aysha tayi tace"bara a kawo maku ruwa".ruwa da lemu ta ɗauro a ƙaramin tray ta kawo masu tare dasu Bilal dake biye da ita.da gudu Bilal yazo ya faɗa jikin Halima yace"la Aunty ni kika zo nema a gidan mu?,kinga Abbana taso muje ki gaishe shi".ya ƙare maganar yana jan hannun Halima dake kallon fuskarshi da murmushi sai a lokacin ne taga tsantsar kamar Bilal da Abu Bilal."ka santa ne"Aunty Aysha ta tambaya.Nahnah dake lafe jikin Halima tace"eh Momy ita ce Auntyn da yake baki labari ta tahfeez".juyowa tayi tana kallon Abu Bilal tace"Aliyu yauga Auntyn Bilal ka gani sai ku gaisa".wani irin haɗe fuska yayi yana kallon Aunty Aysha data tsare shi da ido.cikin ƙasa da kai Halima tace"ina wuni".tana kuma maimaita sunan Aliyu a ranta.yana tafiya yace"lafiya" .yayi hanyar waje wani irin haushi ya turnuƙe zuciyar Khadija kawai tace"to zamu wuce"."da wuri haka kuma".Aunty Aysha ta faɗa.miƙewa Halima tayi tace"dama rakiya zan mata na biyo,insha Allah zan shigo ai".itama Aunty Ayshan miƙewa tayi tana jan hannun Bilal daya maƙalewa Halima tana cewa"to Allah ya kaimu,sai kin shigo".da ƙyar ta janye Bilal daga wurinta sannan suka fita Khadija sai masifa takeyi dan khadija badai faɗa ba.banza Halima ta mata har suka rabu kafin ta dawo gida zuciyarta cike da tambayoyi iri iri.Ɓangaren Hajiya Mama kam duƙe suke a gaban wani ƙaton mutumi baƙi ƙirin dashi sai mazurai yake yi cikin murya marar daɗin saurara yace"me kike so ayiwa yarinyar?".nisawa Hajiya Mama tayi tace"boka ina so a turawa yarinyar baƙaƙen aljannun da zasu hanata zama lafiya,wanda zasu rikita mata rayuwa wani lokacin ma ayi tunanin mayyah ce ko kuma ta haukace,so nakeyi idan suka tashi a kamota can dawa,kuma duk wanda ya kusanceta da sunan so ko tausayinta to ya mutu ya zama kuma ace ita ake tunanin tana kisan".jinjina kai Bokan yayi yace" zaki biya million 1,aikinki an gama da batun shi yanzu haka suna niyyar shiga jikinta,sai dai duk ƙarshen wata xaki basu jinin baƙaƙen dabbobi wannan dalilin ne zaisa duk tsanani su kasance tare da ita".wata irin murmushi ya suɓucewa Hajiya Mama tana jin damuwanta yazo ƙarshe ta buɗe jakkarta ta kwaso kuɗin ta jibgesu gaban Bokan sannan ta tashi suka bar kan dutsen ita da Hajiya talatu.daidai Halima zata shiga gida taji wani irin masifar sanyi na ratsa duka sassan jikinta ga tsigar jikinta data mimmiƙe gaba ɗaya,lokaci ɗaya kuma taji ta daina jin sanyi .gate ɗin gidansu ta buɗe ta shige.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMETS
SHARE
DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING..
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 4

Zagaye ɗaki Hajiya mama takeyi tana faman ture ɗaurin ɗankwalin da tayi na shadda,ciza hannu tayi tana zancen zuci da kuma tunanin maganarsu ta jiya tana kuma zancen zuci,lokaci ɗaya tayi na'am da abunda zuciyarta ta saƙa mata,waya ta ɗakko tare da danna wa lambar aminiyarta kira bugu ɗaya ta ɗaga bakin ta da faɗin"kaga uwar mugai,kaga Hajiya Jamila mata ga Alhaji Abubakar amarya shalele,angulu bata jewar banza,yau kuma da wacce akazo?,me aka ƙunso mana?".murmushi Hajiya Mama ta saki tace "wallahi talatu kinsan kan tsiya"ta ƙare maganar tana muskutawa da gyara zama sosai ,sannan taci gaba da cewa "nifa na gama yanke hukunci,yarda ban taɓa haihuwa a gidan nan ba,bana kuma iya bawa mutanan nan Lamis wallahi,shi kaɗai Allah ya bani wannan dalilin yasa na gama tunanina tsab na yanke shawarar basu ƴar mijina Halimatu".wata muguwar dariya Hajiya Talatu ta saki tace"gaskiya kin ƙware a fannin mugunta,kina ganin Alhaji Abubakar bazai gigice ba idan ya rasa Halimatu?,kifa tuna yayi tsawon shekaru be samu haihuwa ba sai daga baya ya samu Halima kuma ke shaida ce lokacin da yazo neman aurenki sai da ya baki tabbacin in dai kika so Halima to babu abunda bazai gagare sa yayi maki ba in dai a duniyar nan ne".tsuka Hajiya Mama taja tace"to sai meye daga wannan?,ni meya ruwana in ma mutuwa xaiyi ya mutu a raba gado a bani wannan uwar dukiyar daya tara in kwashi kasona in yi gaba,ko da Halimatu ranshi ce sai dai yayi haƙuri dan na gama yanke shawara ita zan bada,kuma ni kinsan basan shegiyar yarinyar nan nake ba mai kama da aljannu,ko kaɗan ita da uwarta bana ƙaunar ganinsu bare kuma naji tausayin su,bayan na gama da ita zan juyo takan uwar ne ae itama ".dariya sosai suka saka kafin Hajiya Talatu tace"hakan yayi,kuma wannan itace hanya mafi sauƙi da zaki kawar da maƙiyanki ba tare da kowa ya sani ba,yanzu idan dare yayi sai ki sanar kawai"da haka sukayi sallama kowa da abunda yake saƙawa a ranshi.tunda suka tashi tahfeez babu wanda yasan dawowanta kai tsaye ɗakinta ta shiga tare da faɗawa akan bed tare da lumshe idanuwanta dake niyyar canza launi,zanen surarshi kawai take gani tana mata yawo da yarda bakinsa ke motsawa yana magana,wani irin ƙayataccen murmushi ta saki tana kuma sauke tagwayen ajiyar zuciya tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da tsananin tunaninsa tun daga jiya zuwa yau bata da sukuni sai faman tunanin Abu bilal,ganin duhun magriba ya taho yasa ta miƙe ta shiga toilet sai lokacin ta cire Unifoam tayi wanka kafin ta ɗauro alwala ta fito,cikin sauri ta shirya cikin riga da siket na material kafin ta kabbara sallah tunda ta gama sallahn bata tashi ba sai da akayi sallan isha sannan ta miƙe tana tattara kayan da tayi sallah kafin ta wuce gaban mirrow dan gyara jikinta.."wai ni kan ina Halima?,tun ɗazu banji alamun shigowarta gidan nan ba bare kuma motsinta"Hajiya Mama take tambaya.nisawa Amma tayi tace"ina jin shigowarta kuwa kinsan ƴar taki halinta sai ita wani lokacin shiyasa nima na shareta".gyara zama Faruq yayi yace"wayyo Ammanmu mun tuba ae da sai ki duba mana ita".ya ƙare maganar yana langwaɓe kai kamar zaiyi kuka.jinjina kai Amma tayi tace"Lallai ma Umar tunda an gaya maka nima bani da aikin yi ne ,tayi ta gama zata fito ta same mu ne".murmushi ya saki wanda ya ƙara fito da ainahin kyawun shi.Umar faruq irin mazan nan ne masu tsayi da kuma kaurin jiki sai dai ba sosai can ba,fari ne tas yayin da fuskarsa ke ɗauke da daradaran fararan idanuwa ga bakinshi gwanin kyau red,yana da saje da kuma gemu da gashin baki ga gashin kanshi baƙi sidiƙ kamar na larabawa.Ɗaga kanshi yayi yana dubanta tana tahowa cikin natsuwa tallabar kumatunsa yayi duka biyu yana kafeta da idanuwa ko kibtawa baya son yi.kai tsaye itama kusa dashi tazo ta zauna tana cewa"Yaya lafiya".taɓe baki yayi sannan yace"hala yau gidan lefi akayi maki kenan?".turo ɗan karamin bakinta tayi kafin tace"ko ɗaya fitan ne bana ji".dariya Hajiya Mama tayi tace"banga lefinki ba ƴar gado,kinga duk yau Daddynki yana waje can bukka shima haka ya faɗa mana".da sauri ta miƙe tana yin hanyar waje tana faɗin"ashe Daddy yana gidan shine ko a sanar da ni".miƙewa Amma tayi tana yin hanyar kitchen tana cewa"aifa shikenan,shima Daddyn ya gama sukuni ae".miƙewa Faruq yayi ya rufa mata baya.kai tsaye gate ɗin gidan ta buɗe babu kowa a wajen shiru sai hasken fitulin da suka ƙawata unguwar fita tayi tare da rufe gidan tana ƙoƙarin shiga ɗayan gate ɗin dake jikin nasu in da nan ne wurin shaƙatawar Daddy kuma suke kiransa bukka saboda gaba ɗaya wurin rufin bukka ne ƴar yayi wurin ya ƙawatu matuƙa.ko kaɗan bata kallon gabanta take tafiyarta burinta kawai taga Daddy ji tayi ta faɗa wa abu.cikin wani irin masifar tsoro da zaro ido taɗanyi baya tana niyar kurma ihu.saurin saka hannunsa yayi ya rufe mata baki yana kuma dallah mata harara cikin tsawa yace"ki rufe mun baki a wajen".wani irin ruɗewa ta kuma yi ko kaɗan bata ɗauki muryarsa ba saboda tsananin tsoron da take ciki tuni hawaye sun soma zarya akan kumatunta ta soma kyarma.kallo ɗaya yayi mata ya ganeta ras tsaki yaja tare da murɗe mata kunne yace"ke saurareni kona faffala maki mari".carab kunnuwanta kamar a mafarki suka amsa sautin daddan muryarsa dib dib haka ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi,a hankali ta soma buɗe daradaran idanuwanta wanda suka soma sauya launi tana ƙarewa fuskarsa kallo.wani irin haɗe fuska yayi yace"nifa bansan kallo".kunyace ta kamata tayi ƙasa da kanta yayinda murmushi ke suɓuce mata wanda batayi niya ba.cikin sanyin murya tace"Ayyah Hamma ka bani tsoro ".matsawa yayi daga kusa da ita yayi wucewarsa da sauri ta juyo tana bin bayansa da kallo .daidai nan Faruq ya ƙaraso tsareta yayi da idon tuhuma shima yana bin bayan Abu bilal da kallo kafin yace"waye shi?".taɓe baki tayi tare da buɗe hannuwa alamar bata sani ba tace"na bigeshi ne kawai".jinjina kai yayi kafin yayi gaba tabi bayansa a nan suka samu Daddy kishin kiɗe yana karatun jarida.kai tsaye matsawa tayi kusa dashi ta lafe a jikinsa tana tunanin me ya kawo Abu bilal unguwarsu.kallonta Daddy yayi ganin tayi shiru yasa ya shafo kanta yace"Ammina kina lafiya dai ko?".gyaɗa kai tayi alamar eh,sai wurin 9 suka koma gida shima dan gobe monday yasan Halima zataje school.da tunanin Abu bilal bacci ya ɗauketa.Ɓangaren Abu bilal kuwa yana shiga gida ya samu duka ƴan gidan zaune a tabarma.da sauri Karima ta miƙe tana masa sannu da zuwa beko kalli in da take ba ya ansa da "lafiya"zaiyi wucewarsa.Dattiya dake kwance ya ɗago yace"yanzu Sude sai dai kazo ka wuceni ko gaisuwar arxiƙi babu?",tsakani da Allah baka kyauta mun ba,ni mema na haɗa da kai banda tsoron Allah,nan nan Uwani ta gama kwashe maka karama amma na murje ido ina yayyafim ruwan bala'i"wani irin zabura Mama Uwani tayi tace"wallahi Dattiya kaji tsoron Allah ka canza Hali,ina ce kaine ka fara maganar Aliyun".wiƙi wiƙi da ido haka Dattiya yayi sai kuma yaja gefen babbar riga yana matsar ƙwallah tare da faɗin"shi dai ai Allah yana gani,kuma ba azalimin kowa bane,waye wani Sude can Allah na tuba bare da girmana na zauna ina gulmarshi".ihun da Karima ta saki ne yasa su duka miƙewa kowa yana raba ido a guje tayi ɗaki tana danna kuba,Mama Uwani ma tayi ɗakinta da gudu,kafin Dattiya yayi aure tuni Rambo ya iso kusa dashi yana niyar cabkar ƙafarsa wani irin tsalle yayi ya kama katanga ya afka gidan Malan Audu ya faɗa a bisa tuƙwanan ruwan labara yana ihu iya ƙarfinsa,Abu bilal kam ko a jikinsa ya buɗe ɗakinsa ya shigewarsa.a guje Malan Audu ya fito yana salati tare da kama Dattiya yana miƙar dashi tsaye yana cewa"kai kuwa lafiya ?".fizge rigarsa yayi daga hannun Malan Audu yace"da lafiya ka ganni haka?,wancan mugun yaron ne ya sako mana alkaba'i a gida,amma ka barni da Sude nasan tsiyar dazan ƙullah mashi,Allah zaiga tsiya zaiga Dattiya ma ba daga baya ba mun daɗe a duniya ana damawa damu.Malan Audu da yake aminin Dattiya ne komai suke ƙullawa tare suke yi ya bushe da dariya yace"kai kake raga masa dama,da gida na yake aeda tuni wani labarin akeyi ba wannan ba,haka kawai yaro ya zauna a gari yana cutar mu?".jinjina kai Labara tayi tace"wallahi kudai kiyayi kanku,bakin rijiya ba dai wurin gaɗan makaho bane,Aliyu Sudais dai ba daga baya ba duka zai iya daku".wani irin hayayyaƙo mata da sukayi yasa tayi saurin shigewa ɗaki tana sharesu.Dare ya raba tsakiya misalin ƙarfe 2:30am daidai agogo ta nuna a lokacin ne kuma na hango Hajiya mama lulluɓe cikin shigar jan kaya da baƙi tayi wani iri babu kyan kallo wani baƙin kasko ne a hannunta a haka ta haɗa wuta a ɗakinta tana ƴan sirkullenta,wani ƙaton mutun mai kama da siffar da babu kyan kallo ya bayyana yana wani irin ɓaɓɓaka dariya yana cewa"lokacin sadaukarwarki yayi,dole ne kiyi sadaukarwa dole ne ki bada jini ,dole ne ki bada rai Jamila".cikin rashin tsoro da kuma ƙwarewa a harkan ta kwashe da dariyan itama cikin rashin wani tunani tace"na bada Halimatus sadiya ƴar mijina,yarinya mafi soyu akab ahalinmu".wani irin dariya ya saki hayaƙi yana fitowa daga bakinsa yana faɗin"zaɓi mai ƙyau,dodo zaiyi alfahari dake Jamila ci gaba da ɗaukaka ya samu rayuwarki,kin bada sabon jini"da ƙarfi ya soma ƙwala kiran Halimatus sadiya,Halimatus sadiya,Halimatus sadiya"sai da ya faɗa haka har sau ukku sannan ya ɓace ɓat tare da duk wani abun da Hajiya Mama ta haɗa a wurin.wani irin firgigit Halima ta miƙe tsaye yayinda idanuwanta ke a rufe babu alamar ta farka daga baccin da takeyi ɓat ta ɓace daga dakin babu ita babu alamunta .


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

FREE PAGES
PAGE 5

Zagaye wurin yake da mutane iri iri kowa irin shigarsu ɗaya watau ɓaƙi da ja,wutace keci a tsakiyar babban filin da suke zagaye dashi kowa da abunda yakeyi ,wani ƙaton mutun ne zaune ba kyan gani fuskar nan murtuƙe babu alamun annuri a tattare da ita ya riƙe wata ƙatuwar sanda mai zanan maciji.a daidai tsakiyar mutanan wanda ƙaton mutumin da ya ɗauko Halima ya bayyana,haka itama Haliman ta bayyana har lokacin idanuwanta a rufe suke alamar tana bacci,nuna ta yayi da wannan sandar ta hannunsa tuni ta faɗi akan gwaiwowinta tana layi kamar wacce tasha wani abu.wata iriyar dariya suka fashe da ita,yayin da wata mata mai suna Dosun ta taho riƙe da ƙwarya cikinta ɗauke da wani baƙin ruwa kai tsaye gaban Halima tazo ta ɗago kanta ta saka mata ƙwaryar a baki tsab ta ɗure mata fiye da rabin ruwan kuma ta shanye sauran kuma ta wanko mata tun daga kanta har ƙafafunta.wata irin miƙa Halima tayi tuni xufa ya fara keto mata ,a hankali ta soma buɗe dara-daran idanuwanta wanda suka soma riƙiɗewa ,cikin rashin kuzari ta soma kallon in da take tana kuma jin ihu kala kala a wurin,a kan fuskar wannan ƙaton mutumin ta sauke idanuwanta da sauri tayi baya tana furta"innalillahi wa'inna ialaihir raju'un".sosai muryarta ta shiga kunnuwansa ya rufe ido da ƙarfi ya kuma miƙe zumbur.Halima batayi aune ba taji sirinji a cikin damtsen hannunta ana jan jininta wani irin zafi da daɗaɗin azaban allurar ya shigeta lokaci ɗaya,runtse ido tayi hawaye yana kawo mata ta miƙe tsaye da sauri tana furta"ke lafiya".ko kallonta Dosun bata yi ba tayi gaba da jinin Halima data ɗauka.raba ido Halima ta fara tana kuma karanto duk wata addu'a data zo bakinta ganin wannan mutumin na doso in da take tsaye,kuma sai lokacin ta buɗe idanuwanta da kyau tana ƙarewa in da take tsaye da kallo ba ƙaramin tsoro ya shigeta ba.zagayeta Oga Sam yakeyi kamar zai cinyeta ɗanya haka yake zuro harshe.cikin muryar kuka tace"dan Allah kada ka cutar da ni,kaji tsoron Allah,ni ban sanku

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment