Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


```Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans

Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.

FREE PAGES
PAGE 9

Ƙarasowa Amma tayi cikin parlon tana ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin dake a tattare da ita,zama tayi tare da kamo hannun Halima she's spechless tama rasa abun yi tana a haka Halima ta saki wata uwar ƙara ta fara fizge-fizge,Faruq da shigowansa kenan gidan ɗaukan wasu files daya ajiye ya shigo gidan da sauri yana ƙarasowa cikin parlon ya kuma ci karo da Halima dake ƙoƙarin barin parlon a guje,saurin riƙota yayi yace"ke lafiya?,subhanallah me yake damunki haka?".kokoyi suka soma yi tana neman ƙwatar kanta,da iya ƙarfinsa ya riƙeta da ƙarfi yana gizgizata yana cewa"wannan wacce irin ƙaddara ce kuma,spirit a jikin Halimana"ya ƙare maganar cike da rauni.tsaye Lamis ya tsaya yana ƙare masu kallo kafin yace"me yake damunta haka"wanda shigowarsa kenan.cikin muryar tashin hankali Faruq yace"may be spirit".waro ido Lamis yayi ganin tana neman tafi ƙarfin Faruq sai kururuwar ihu take yi wanda tuni ta jefar da himar ɗin kanta tattausan gashin kanta ɗuka ya baje a jikinta har fuskarta baka gani,sai da sukayi da gaske kafin suka iya sakata cikin wani ɗaki da ke anan parlon da sauri Lamis ya rufe ƙofan da key yana jingina da wurin.da sauri Hajiya Mama ta fito tana cewa "me yake faruwa ne?,ina wanka nake jiyo ihun little".har lokacin Amma tana ta tsaye ta kasa yin ƙwaƙwaran motsi.Faruq da damuwa ya gama dabaibayeshi ne ya faɗawa Hajiya Mama abunda ke faruwa,kafin tayi magana taga yarda Halima ke buga door ɗin ɗakin da take kulle tana jijjigawa iya ƙarfin,ƙaran fashe-fashe suka soma ji,a matuƙar tsorace Lamis yace"kada fa ta jiwa kanta ciwo".kallon ƙasan ido Hajiya Mama ta bisa dashi cikin hikima tace"to idan kuma aka buɗeta ta gudu fa?,ko kuma maƙota suka taran mana fa?".kafin kowa yayi yunƙuri Lamis ya buɗe ɗakin ya faɗa jin ƙarar Mirrow alamun ta fashe shi.hakan kuwa akayi dan hannuwanta duk jini har ɗiga yake yi.kusurwar ɗakin take nunawa tana jefa duk abunda ya tari gabanta ,,,wata dariya Dosun ta kwashe da ita wanda Halima kaɗai take iya jiyo dariyar da iya ganin Dosun,jinin Halima dake ɗiga ta lakuce ta ɓace bat.wani irin juyewa hannuwan Halima sukayi gaba ɗaya ta fara murmurɗewa tana niyar zubewa,saurin riƙota Lamis yayi zufa na zubo masa yana furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yana kuma kiran sunanta.a hannunsa ta ƙarasa sandarewa ta koma kamar an nannaɗeta.wasu hawaye ne masu ɗumi suka soma zarya a fuskar Amma ganin ƴarta ɗaya tilo yacce take shan wahala waya ta ɗauka tana kiran Daddy ta daɗe kafin ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama,ansa sallamar tayi a sanyaye tace"Daddy kazo gida Little ba lafiya an dawo da ita daga scul".bece komai ba ya kashe wayan yana kwashe keys ɗinshi ya fito da sauri dan yasan da abun da sauƙi Amma ba zata taɓa kiransa ba musamman data kasance mace mai kawaici da haƙuri da kawar da kai ga komai..a katifan ɗakin Lamis ya kwantar da ita.Faruq kam ya gama daskarewa ƙwaƙwaran motsi ma ya kasa yi daga in da yake tsaye sai zufan dake zubo masa suna a haka Daddy ya shigo parlon ganinsu cirko-cirko yayi saurin shigewa ɗakin da yaga suna kallo,kai tsaye gaban katifan yazo yana duƙawa ya soma kiran sunan Halima tare da janyota jikinshi,ganin halin da take ciki yasa ya dafe kai yana jin matsanan ciyar damuwa na taso masa yace"what's wrong Aminatu"ya faɗa yana kallon Amma.cikin sanyin murya tace"i don't know kawai ance ta faɗi a school ne"."ina ga kamar iska ne fa"Hajiya Mama ta faɗa.kallonta kawai Daddy yayi kafin ya dawo da kallonsa ga Halima dake motsi.ido cikin ido Daddy ya kalleta in da idonta sun koma red ,eyes ball ɗin kuma suka koma black saurin janye idonsa yayi saboda jin wani abu na ratsa shi ,kaya suka soma zubowa na fashewa na fashewa duk abunda ta kallah sai ya lalace a time ɗin kafin ta sake sakin ƙara ta faɗi wani wahalallan bacci yayi gaba da ita.ɓoyayyan ajiyan zuciya Daddy ya sauke yana cewa"alhmdllh ta samu bacci,kafin ta farka sai musan abun yi"ya ƙare maganar yana miƙewa zuwa parlo...tsaye ya tsaya cak yana kallon Mami dake zaune cikin shiga ta alfarma kai da ka ganta kasan naira ta gama jiƙata,tsantsar kamarsu ta bayyana dan zakayi tunanin Mamy kaki tayi ta ajiye Aliyu,janye idonsa yayi kai tsaye ya nufi hanyar part ɗinshi.da sauri tace"Aliyu,Aliyu Sudais"cak ya tsaya ba tare daya juyo ba cikin kausasshiyar yace"nan ma kinzo ku ƙarasa kasheni da baƙin ciki ne?"..salati Dattiya ya saki yace"dan ƙari,kaji irinta,meye wani wai Sude Allah na tuba,to dai yau kin ganewa idonki irin halin da muke ciki,a kullun mune mararsa mutunci a idon Sude,tunda cin arziƙi mukazo dole muyi biyayyah,ahtau cin arziƙi mana in da ba haka b...."saurin haɗiye maganarsa yayi yana ja da baya ganin irin mugun kallon da Abu bilal ke jefa masa.miƙewa Mamy tayi ta ƙaraso bayanshi tasa hannu ta juyo shi yana fuskantarta,ko kaɗan kasa haɗa ido yayi da ita yayi ƙasa da kanshi yana jin zuciyarsa na zafi kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito."ka kalleni Aliyu,ka kalleni sai ka gayamun ni mahaifiyarka nazo na ƙarasa kasheka da baƙin ciki,meyasa kai ba zaka ɗauki ƙaddara ba?,meyasa kai bazaka miƙa lamuranka ga Allah yayi maka sakayyah ba?,Aliyu ka haƙura ka daina neman Hajiya Jamila dan nasan ba abu bane mai sauƙi ka iya samunta ba,ita ɗin tamkar alkaba'i take duk in da ta nufa to tamkar annoba ce ta bayyana Aliyu".ji yayi zuciyarsa ta buga da matuƙar ƙarfi wata irin zuciya ta ciyosa a kausasahe yace"i don't care ko da zai zama abu na ƙarshe da zanyi a rayuwata sai na nemota,meya kawoki wurina bayan yace ya cire ni a yaransa inyi nesa dashi har abada,kuma kuma yace ku nesanta da ni?".murmushin da yafi kuka ciwo Mami tayi tace"ka taɓa ganin in da aka raba uwa da ɗanta?,Aliyu ka shirya mu koma gida".da sauri ya zame hannunsa daga riƙon da Mami tayi masa yace"never,this will never happen"saurin yin shiru yayi yana danne saitin zuciyarsa da ƙarfi.girgixa kai Mami tayi tace"tunda kai bazaka koma ba zanje wurin Aysha na ɗauki Bilal aishi baka isa ka rabasa da kowa nasa ba".kallon Mami yakeyi kamar idanuwansa zasu faɗo kafin yace"Billah yau da ace bake mahaifiyata ce tsaye kike gayamun wannan ba to da bana tantama mutunanin ko waye ya ƙara awa ɗaya da kansa a gangar jikinsa ba,yarda nabar ku haka zalika Bilal ya barku har abada,kuma duk wanda yayi gigin ɗaukar Bilal zuwa wannan gidan ko waye tabbas zaiga mummunan abun da zai faru dashi wanda bazai manta da Abu bilal ba har abada".sakin baki Karima tayi tana tunanin ashe Abu bilal yana magana har haka?,tunda suke tsawon shekaru ko Mami tazo bata taɓa jin yayi magana haka ba.katse shirun Mamy tayi tace"to ni zan ɗauka idan yaso sai ka kashe ni ni".saurin zubewa yayi ƙasa akan gwaiwowinsa ya haɗa hannayensa duka biyun cikin rawan murya yace"kada kimun haka,kada ku ƙarasa kashe ni da raina,kada ku ɗauki farin cikina zuwa gida mafi muni da ƙyama a rayuwata,ina roƙonki da girman Allah kada ki taɓa mun yaro kuma kema kiyi haƙuri ki daina zuwa wurina".dafe kai Mamy tayi tace"Aliyu baka son ganina ne?,ko ka samu wacce ta fini ne?"ta ƙare tambayar a tsorace,idamuwansa da suka sauya launi ya lumshe yace"ko kusa Mamy,har abada bani da wacce ta fiki".hawayen dake ƙoƙarin zubo mata ta mayar tace"ƙaddara ta riga fata Aliyu,ka yafe mun ka daina ganin laifina a abunda ya faru,na zaɓi nayi hakan ne dana rasa ka bazan iya jurar ganin gawarka ba Aliyu,ka yafe mun"ta ƙare maganar kuka na ƙwace mata ta ɗauki bag ɗinta ta fice gidan da sauri.anan in da yake duƙe yabi bayanta da kallo yana jin zuciyarsa na barazanar tarwatsewa da ƙyar ya iya miƙewa ya shige ɗakinshi yana jin kanshi na sarawa.tuni fuskar Karima ta jiƙe jagab da ruwan hawaye hankalinta a matuƙar tashe ga tsantsar tausayin Abu bilal daya rufeta ta faɗa ɗaki itama tana sakin kuka mai cin rai.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMENT
SHARE
DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING
[11/13, 23:34] Jordan: 14
Cikin wani firgici Jagwado yayi kansu girgiza Abu bilal yakeyi yana kiran sunansa ganin wannan ba zata yiba ya sunkuce ya saka shi mota yayi asibiti dashi.wani kukan ne ya kwacewa Karima haka ma Dattiya ya ɗaura hannu saman kai"yace Allah kaji ƙaina ka tadamun kafaɗun Sude,wake gare ni in ba Sude ba,shi ne da daɗi da ba daɗi yana nan tare da ni,komai shi yake mun yo Allah na tuba in ba Sude ɗin ba sai wa"ya ƙare maganar yana bin hanyar waje yana ƙwala Malan Audu kira yana goge hawaye da majina da gefan babbar rigarshi.kama Karima Mama uwani tayi tana lallashinta da bata baki.
2hour's.
A hankali ya soma buɗe idanuwansa yana ƙarewa ɗakin da yake kallo dafe kansa yayi yana son tuno abunda ya faru amma sam ya kasa tuna komai,a hankali ya miƙe zaune a daidai lokacin ne kuma Jagwado ya turo ƙofan ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da leda da alama abinci ya siyo masu.kallonsa Abu bilal yayi yace"what i my doing here?".nusawa Jagwado yayi yace"how is your body?".tsura masa ido yayi kafin yace"Alhmdllh".yaye cotains ɗin window yayi yana kallon yacce garin yayi duhu safko wa yayi yana cewa"tsawon yaushe nake nan?".a taƙaice Jagwado yace"since azahar".waro ido yayi yace"u mean i missed asir and also magrib?".gyaɗa kai Jagwado yayi alamar eh,hakan yasa ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya fito ya samu harya shimfiɗa masa prayer mat,nan ya rama sallolin da aka biyo shi ,kaɗan yaɗanci jullub rice ɗin da naman kaza yasha ruwza ya ture plate ɗin yace"i'm full then i want to go home".ba yarda Jagwado beyi dashi akan ya haƙura safiya yayi ba amma sam ya ƙiya ba arziki akayi discharging ɗinsu suka koma gida..
Since 10 Khadija tazo gidan duba Halima suna ta zaune parlo Khadija tace"yaushe zaki koma islamiyyah?".shiru ta ɗanyi kafin tace"soon,kuma nifa ina da damuwa".gyara zama sosai Khadija tayi tace"what's the case?".lumshe dara daran idanuwanta tayi tana gyara zaman eye glasses ɗinta tace"i want to know him Khadija,jiya naji abunda ya ɗaure mun kai,hankalina ya tashi ina tashi daga raɗaɗin ciwo kunnuwana suka jiyomun munanan kalamai da ake faɗawa Yaya Aliyu,babban matsalan ma shine da Daddy yace har abada baya son sake ganin Yaya Aliyu bare kuma yagan na kulasa,kinsan halinsa as if he don't care ya kama gabansa,nikan na kasa bacci am deep in love with him Khadija,bazan iya rabuwa dashi ba,ina so nasan waye,na kuma san a ina Daddy ya san shi".ta ƙare maganar cike da rauni.ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace"duk da kinsan bana yin Abu bilal amma bazanga laifin zuciyarki ba danta so shi,sai dai ina ƙara gaya maki shi ɗin ba kalanki bane,kuma tunda kikaji Daddy yayi magana a kai tau tabbas akwai wani abu a ƙasa wanda mu basu sani ba,kamata yayi ki fara tambayan Amma idan kikaji daga gareta sai asan abun yi wanda duk da haka bana koyon bayan kiso Ɗan daba kuma drinker".runtse ido Halima tayi da ƙarfi tana jin zafin maganganun Khadija akan Abu bilal,sai wurin 12 kafin Khajija ta tafi,a kuma gate ne Halima ta haɗu da Lamis daya shigo gidan yanzu fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙaraso kusa da ita yace"hy cuttie me kike yi a gate?"."na raka Khadija ƙofan gate ne "ta faɗa itama cikin sakin fuska .juyawa yayi in da fararen kujeru suke wurin ya ƙawatu ba lefi yace "muje can zamuyi magana".bin bayansa tayi suka xauna suna fuskantar juna kafin yace"cuttie yaushe zakiyi aure?".waro ido tayi sai kuma ta saki dariya tace"kaima babba bakayi ba,bare kuma ni da ban ƙarasa secondry bama ina SS 2 nefa".lumshe idonsa yayi yana jin sautin bugun zuciyarsa yace"to kinga ni ina so nayi aure nan da 1year amma in wacce nake so ta yarda".cikin jin daɗi tace"nasan zata yarda ma,ka kalleka so handsome ga ilimi mafi abunda yafi ma gaka da addini to me mace zata nema kuma?".murmushinsa mai kyau yayi yace"ae so ba ruwansa da wannan".ɗan jim yayi kafin ga kama hannuwanta ya riƙe yana kallonta,saurin yin ƙasa da kai tayi tana jin wani iri a tattare da ita,sosai ya riƙe hannun kafin yace"Halima kece wacce nake so ,kuma nake burin aura,please karkice No ki dubeni ki yarda da soyayyata a gareki".ras ras haka ƙirjin Halima ya bada sauti saurin ɗago idanuwanta tayi tana kallonsa wanda har hawaye sun soma kwanciya saurin zare hannunta tayi daga riƙon daya yi mata a firgice tayi cikin gida da gudu tana haki bata ma san abun yi ba.runtse ido Lamis yayi tare da shafa fuskan shi kafin ya tashi ya shiga cikin gidan.jan hannunshi kawai Hajiya Mama tayi kai tsaye ta wuce dashi bedroom ɗinta tana danna key tace"uban meye kake gayawa yarinyar can?".shiru yayi mata a tsawace tace"Muhammad ina magana".lumshe ido yayi a rayuwansa besan meye ƙarya ba bare kuma yayiwa Hajiyan shi cikin dakiya yace"nace ina sonta kuma zan aureta ne".daskarewa Hajiya Mama tayi a wurin kafin a fusace taci kwalar Lamis tana girgizashi da ƙarfi tace"a gaskiya baka da hankali,kana ganin irin ciwan da takeyi mahaukaciyar zaka aura mai kwana kango?,mai lashe kurwar mutane?,anya Lamis kana da cikakken hankali kuwa?".kallonta kawai yake yana nazartar yanayinta yace"idan kuma ƴarki ce kema zaki so a samu wanda zai taimake ta ,i don't care ko zan mutu a hanyar taimako "."ka rufemun baki sakarai kawai,idan kai ka sallama ni baxan taɓa yarda da hakan ba,your the only son i have,i can't imaging halin dazan shiga idan na rasaka bam shirya ma wannan ba,ban yarda ba ban kuma amince ba in dai ina da rai hakan bazara taɓa faruwa ba Lamis i mean it".kallonta kawai yakeyi kafin yace"Hajiya do u know something about Halima's condition?,kina yi kamar kinsan komai a kanta".saurin sakin sa tayi tana dabur bur cewa"tace am ...au...kana zargina ne kenan Lamis?".shafa gemonsa yayi yace"ko ɗaya".be jira cewarta ba ya fice daga ɗakin.hannu kawai Hajiya Mama ta ɗaura a kai tama rasa abunyi motsin kirki ta kasa yi kawai saita fashe da kuka tana roƙon Allah ya tsare mata Lamis tana kuma kudiri niyar shiga malamai dan a raba mata Lamis da Halima.
Cikin natsuwa ta shiga parlon Amma ganin babu kowa yasa ta wuce bedroom ɗinta ta tura ƙofan bakinta ɗauke da sallama,a gaban mirrow taga Amma tana fesa turare,gefan bed taje ta zauna kafin cikin sanyin murya tace"Amma".sai da ta gama shafa turaren ta ajiyesa in da ya dace kafin ta juyo tazo gefan bed din itama ta zauna tace"menene?".ƙasa Halima tayi da kai ta kasa cewa komai sai hawayenta da take ƙoƙarin mayarwa."meye hakan kuma?,idan baki shirya magana ba ga hanya zaki sakani gaba kina mun kuka".ɗagowa tayi ta kallah Amma tace"Ammana dan Allah da girman manzonsa ki gaya mun waye Yaya Aliyu?,a ina Daddy ya sanshi?,wani abun ya taɓa haɗa su ne?".kallonta kawai Amma tayi tana nazartar yanayinta kafin tace"babu wani alaƙa tsakanin Daddy da Sudais,sanin waye sh kuma bazai amfaneki ba,kawai kiyi biyayyah ga abunda Daddynki ya saka kiyi".ta ƙare maganar tana ƙoƙarin miƙewa.saurin riƙeta Halima tayi tace"Amma ki taimaka mun,ina da tarin tambayoyi a tattare da ni,bazan samu sukuni ba har sai nasan waye Yaya Aliyu meyasa Daddyna baya sonshi,ki taimake ni ki faɗa mun Amma hakan zaisa nayi farin ciki na kuma warware tantamar dake raina".ƙura mata ido Amma tayi tace"kima dai san idan son Sudais kikeyi kiyi saurin ciresa a ranki dan hakan bazai haifar maki da ɗa mai ido ba".gayaɗa kai kawai Halima ta iyayi tana ƙure Amma da ido,nisawa tayi kafin tace" shekarun baya da suka wuce,shekara sha bakwai baya lokacin ina da tsohon ciki ki abun ya faru"....waiwaye adon tafiya,tuna baya.
17 YEARS BACK
WAYE ABU BILAL!!!

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 13
Tun rasuwar Junaid Halima bata ƙara kwanciyan hankali ba,bata so ko kaɗan wani abun ɓacin rai na haɗata da wani dan tsab tasan ciwanta sai dai abunda bata sani ba shine har wanda ya sota ma zai iya kasancewa cikin wannan tarkon,ko kaɗan bata son zama cikin mutane sai dai sam yanzu ta mayar da wannan kangon wurin zamanta kamar walƙiya haka take ɓacewa ta bayyana a cikinsa yanxu abun ya kawo har saman bishiyar kuka takan zauna ko kuma sai dare ta tafi kan kuka ta kwana can sai safiya ta dawo.girgiza kai Amma tayi tace"yanzu waye kake tunanin zai iya shiga kangon can ya fito da Halima?,ko kaɗan fa ƙofan ta rufe babu mai iya shiga"ta ƙare maganar hawayenta na ƙara zubowa.shafa kai Daddy yayi yana jin matsanancin tashin hankali na kuma ruskarsa yace"gashi Imam baya gari,kuma duka wayoyinsa a kashe,yanzu ki koma gida insha Allah za'asan abunyi a kai".kamar marar lakka haka Amma ta wuce cikin gida tana yi tana waiwayen baƙin kangon da Halima take ciki,yau kwananta biyu kuma taƙi fitowa duk wanda yaje da niyar shigo to baxai ga ƙofa ba kuma bazai iya dira katangan ba.cikin tashin hankali Aunty Aysha ke gayawa Abu bilal abunda ke faruwa taci gaba da cewa"babban tashin hankalin shine ba'asan wanne hali take ciki ba,gata mace gaskiya iskan nan yana wahalar da yarinyar nan" taɓe baki Abu bilal yayi yace"Allah ya kyauta"kai tsaye hanyar waje yayi yana fita kuma kangon ya dosa ko ɗar beyi ba,addu'o'i yake karantawa a ranshi har ya isa bakin kangon,tsaye ya tsaya yana ƙarewa kangon kallo,kallonsa kawai Faruq da Lamis suka tsaya yi sun gagara cewa komai Daddy kam ya shiga gida ɗauko phone's ɗinsa dan yasan abunyi.lumshe ido Abu bilal yayi bayan ya gama addu'o'insa yace"bismillah"yana kuma saka kai jikin bangon.a take suka ga ƙofan ta buɗe ya wuce ciki da izinin ubangiji.saurin rife hancinsa yayi saboda wani azabar wari daya daki hancinsa kalle-kalle ya soma yi a wani ɗaki da babu kowa a ciki sai kwanuka wasu da jini wasu kuma wani irin bakin ruwa me yauƙi,kamar a film haka yake ganin giccin mutane a wurin ƙwafa yayi ya kuma ambaton sunan Allah yace"Haleemah"shiru ba'a ansa ba sai ɓaɓɓakewa da mugun dariyan da akayi,sama ya ɗaga kansa yana hango Halima acan saman ƙaton bishiyan kuka,duk tayi wani hiri hiri ta gama sauyawa da halitta,addu'a ya riƙayi yana tofawa a saman kamar an jefota haka ta faɗo kafin ta iso ƙasa yayi saurin saka hannuwansa ya tareta ta faɗo a ƙirjinsa,wani irin bangajesa tayi ta tsaya tsaye akan manyan ƴan yatsunta na ƙafa tana wani irin gurnani.kallon ikon Allah yakeyi kafin ya fizgota ya matse mata babban yatsanta na hannun dama ,cikin wani irin sauti tace"ka sakeni,ka sakeni nace".ta wani juyo tana ƙwalalo masa muggan idanuwanta da suka fito kamar ƙwan fitila."ku fita daga jikinta,idan ba haka ba kuma zan ƙonaku yanzun nan,kuma ina gargaɗinku da kada ku cutar da wani itama ku barta ta huta haka".wata irin dariya Halima ta saki tana cewa"bazamu iya barin jikinta ba ".murza hannun nata yayi da ƙarfi aiko ta saki ƙara tana tafiya luuu zata faɗa akan ƙayoyin dake wurin.saurin tarbota yayi kafin ya rungumota kamar baby ya fito da ita daga cikin kangon.wani irin ajiyar zuciya Faruq da Lamis suka sauke a tare suna kuma mayar da kallonsu ga jikinta da yayi duƙu-duƙu gashin kanta duk a baje gaba ɗaya ta sauya launi.shikam Abu bilal ko kallonsu beyi ba ya fara tafiya suka rufa masa baya.har cikin gidan ya shiga da ita a parlo ya tsaya yana shimfiɗar da ita akan carpet.wata uwar ƙara Hajiya Mama ta saki tana cewa"Daddy ku fito ku gani,Daddy Amma".kusan a tare Amma da Daddy suka fito , da gudu Hajiya Mama tayi ɗaki dan a matuƙar tsorace take,da sauri Abu bilal ya ɗago yana bin bayan Hajiya Mama da kallo saboda jin muryarta a kunnensa,sai dai be samu ganin fuskanta ba.Aysha dake rakuɓe tana kuka ita ta taso da sauri Mamanta ma na take mata baya.ƙarasowa cikin parlon Daddy yayi yana maida kallonsa ga Abu bilal wanda ya ɗago daga duƙen da yake,kallo sukeyiwa juna ido cikin ido kafin cikin rawar murya Daddy yace"Aliyu kaine?,meya kawo ka gidana?".cikin kausasshiyar murya yana haɗa yatsunsa suna ƙara yace"get out of my hause wannan karon ya zama karo na ƙarshe da ƙafarka zata kuma shigowa gidana balle harka ɗauki kazamin hannunka ka ɗaurashi akan ƴata".da sauri Amma ta shiga gaban Daddy tace"haba Abubakar kai baka ganin irin taimakon da yayi mana?,ko last time shine wanda ya dawo da ita gida data faɗi a school,kome yayi maka ya kamata kayi haƙuri".wani tsaki Daddy yaja cikin ɗaga murya yace"wai ke baki gane shi bane?,it's Aliyu yaron Alhaji Ahmad ,why can't you look at his face very well Amina ".juyowa Amma tayi tsoro ya nuna ƙarara a fuskarta tabbas ranar firgici da tsoro ya hanata kallon fuskar Aliyu da kyau haka yauma sai da Daddy ya nusar da ita kafin ta ganeshi rabon data saka shi ido tun tana da tsohon cikin Halima 17years kenan.bakinta na rawa tace"Sudais".ƙasa Sudais yayi da kai don tun ranar daya zo gidan na farko ya gane Amma sai dai ganin bata ganeshi ba yasa ya share kawai,kuma yasan Aunty Aysha bata san Amma ba sakamakon ba'a gidansu ta tashi ba ko da tayi aure a london take zaune sai tsakanin nan ne ta dawo Nigeria da zama.cikin kausasshiyar murya Daddy yace"dama ashe shine wanda ya taɓa zuwa mun gida kuma baki gayamun ba,Aliyu idan ka kuma shigo mun gida hukuma ce zata rabani da kai and i mean it wallahi".cikin dakiya Aliyu yace"to Allah ya bada iko Daddy,babu wani abun da zai firgita ni tunda har a baya na rayu" .cikin muryar kuka Amma tace"please you people should stop that,komai ya faru ya faru ne a ta dalilin kuskure,kuma kai Daddy kasan an cuci Aliyu da yawa ko don taimakon da yakewa ƴarka bazaisa ku tausaya masa ba"."karki sake min irin wannan maganan,mashayin ,ɗan daban,wanda ya keta haƙƙin Allah,ya aikata saɓo mafi muni wanda ko a zamanin dabbibu banga ana haka ba".runtse ido Aliyu yayi da ƙarfi kafin ya waresu harsun soma canza launi dan tsananin ɓacin rai kasa furta komai yayi ya juya zai fita,ji yayi an riƙo hannunsa,tsaye ya tsaya cak ba tare daya juyo ba yaji sautin muryarta tana cewa"Yaya Sudais" wata uwar tsawa Daddy ya daka mata wanda tunda take a rayuwarta be taɓa mata tsawa irin haka ba.jikinta na ƙyarma tayi sauri ta lafe bayan Lamis dake kusa da ita."kada na kuma ganin kin danganta kanki da Aliyu,har abada babu ke babu shi,idan kuma kika saɓa zakiga irin abunda zai faru da ni da ke a gidan nan Halima".girgiza kai Abu bilal yayi ransa a matuƙar ɓace ya fice daga parlon dan har ji yakeyi bashi gani.hawayen dake zubowa idonta ta goge tana maimaita sunan da Daddy ya kirata dashi wanda tasan a iya rayuwarta xata iya ƙirga sau nawa Daddy ya kirata da Halima.kama hannunta Faruq yayi kai tsaye ya wuce da ita bedroom ɗinta yana lallashinta akan kada ta ɓata ranta baya so kanta yayi ciwo.binsu Amma tayi a ɗakin kafin ta kama Halima zuwa toilet ita da kanta tanwanke mata kai ta wanke ƴarta tas ganin babu wani kuzarin kirki a jikinta,kallonta takeyi yarda tayi masifar rama duk ta zabge a zaman kwana biyu kawai,doguwan riga marar nauyi red ta bata ta saka kafin ta gyara mata kanta.Faruq ne yayi sallama ya shigo ɗakin da mug ɗin tea mai kauri ya zauna yana bata tea ɗin a baki,ganin haka Amma ta wuce part ɗinta tana tuna rayuwar baya data wuce.sai da ta shanye tea ɗin kafin ya bata farfesun ƴan ciki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment