Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,in lefi nayi maku dan Allah kuyi haƙuri".wata uwar dariya suka saki gaba ɗayansu wanda ke iya gane abunda take faɗa.cikin hausa marar ɗaɗi da kuma murya marar ɗaɗin ji Oga sam yace"kin damemu da magana a nan wajen".wani wuƙa mai sheƙi da kaifi taga ya bayyana a hannunsa ya ɗaga da niyar caka mata.wani irin ƙwalalo ido tayi ta soma karanta ayatul kursiyyu da duka iya ƙarfinta da sautin muryarta.tuni hannunsa ya soma rawa yana ƙarewa kyakyawan fuskarta kallo wanda a yanzu ta riƙiɗe ta koma ja saboda tsananin tashin hankalin data tsinci kanta a ciki.Ɗan jim yayi kafin yaja baya xuwa wani ɗaki cikin sauri yawancin mutanan dake wurin suka rufa masa baya.ganin duk wanda ake buƙata ya shigo yasa ya fara magana yace"wannan yarinyar xai mana wahala mu iya kasheta da sauƙi,kuma tabbas idan muka takura akan hakan xata mana ɓannar da shekaru da dama aka mana irinta ko kuma in ce ta xarce wacce aka mana ma,wanan dalilin yasa na yanke shawarar mexai hana itama mu janyota a ƙungiyar nan,kafin idan ta gama mana amfani a lokacin babu Allah a bakinta sai mu kasheta kuma daga yanzu lokaci zuwa lokaci xata kasance cikin tsananin azaba da tsoratarta wannan shine hukuncin da xamu mata na kasa kasheta da mukayi a yanzu".babu wanda yaja da maganar tasa lokaci ɗaya dukkansu suka haɗa hannuwa suna karanta wani abu marar ɗadi da yin mubaya'a akan hukuncin da ogan nasu ya yanke.yarda sautin muryarsu ke fita haka hajijiya ke juyar da Halima kanta na matuƙar sarawa da masifar ƙarfi,lokaci ɗaya cikinta ya wani murɗa ta zube a wurin a kakkafe tana kyarmar sanyi wani irin azaba ne ke ziyartarta yayin da ta gara rolling a cikin ƙasar wurin kamar wacce take zagaye wurin.wani irin kukan wahala ta saki lokacin da take jin saukar wani ruwa a jikinta kamar ana yayyafa mata wuta,ga masifar wari,haka tana ji tana gani suka kuma ɗura mata wanan ruwan cikin nishin wahala ta sulale wurin wani wahalallan bacci nayin gaba da ita.nunata Oga Sam yayi da wannan sandar ta hannunshi tuni ta ɓace bat kamar ba'a taɓa kawota wurin ba.dukansu suka fashe da tsananin dariyan mugunta.a cikin daren kuma Talatu ta kirawo Hajiya Mama ta zayyane mata abunda ya faru da kuma hukuncin da Oga Sam ya yanke,a razane ta miƙe zaune tace"ina ce dai bata san wanda ya kawota wurin ba?".dariya Talatu tayi tace"kwantar da hankali ina zata samu damar sani bayan ciwan azaba daya sakata gaba,ae ina mai tabbatar maki ko ni da naje wurin bazata taɓa ganeni ba bare kuma ke".wata sanyayyar ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauke tace"wallahi har naji sanyi,ai ni ƙara ma aita gara mun ƴar iskar ta fitini kowa ta zama anno ba kafin tabar duniya,anjima kizo zaki rakani kan dutse can bicci insa a ƙara ingizowa shegiya abunda xai mun maganinta dan wallahi ni nafi kishi da ita akan uwarta ma".dariya sosai suka saka kafin suka yi sallama da rabuwa akan cewa da azahar zasu je bicci.tun da wuri Daddy yayi kari suka fita office shi da Faruq ko ganin Little be tsaya yi ba saboda kiran daya samu na gaggawa.kallon agogo Amma tayi a lokacin ne kuma agogo ta buga ƙarfe 8:00 daidai na safe,sallamar Iro Driver ta katse mata tunaninta ya matso ya rinsina a gabanta ya gaisheta cike da girmamawa ta ansa kafin yace"Hajiya Babban ,Ammin masu gida yau baxata je makaranta bane?".miƙewa tayi tace"nima yanzu xan shiga na dubota naga shirun yayi yawa ka jirani kaɗan".ta ƙare maganar tana nufan part ɗinta.kai tsaye ɗakin Halima ta tura.hangota tayi lulleɓe akan bed sallama tayi ta shiga ɗakin gefan bed din ta zauna tana yaye duvet ɗin da tayi rufa dashi,daga ita sai ƴar ƙaramar riga kallo ɗaya Amma tayi mata ta gane kwata kwata baccin baya yi mata daɗi ga wata wahalalliyar ajiyar zuciya da take saukewa lokaci zuwa lokaci,idonta ta mayar akan jijiyar kanta dake halbawa da ƙarfi gasu kuma sun fito ruɗu-ruɗu kamar wa'anda aka xana.hannunta na rawa takai akan dokin wuyanta da sauri ta janye jin yayi matuƙar zafi.bubbugata tayi tana cewa"Sadiya,Sadiya".wata irin miƙa Halima ta saki kafin lokaci ɗaya ta wara dara-daran idanuwanta wanda suka kaɗa suka zama jajir,brown ɗin ciki kuma ya juye ya koma baƙi-ƙirin.da ƙarfi Amma ta rufe idonta tana cewa"Hasbunallahu wani'imal wakil".sannan ta buɗe idonta cike da firgici tace"Sadiya meke damunki haka?,kinga idonki kuwa?,ko kinyi kuka ne?,amma kuma ko kuka baya riƙiɗar da idon ki haka,baki da lafiya ne?".a ruɗe Amma duka ke jero mata wanan tambayoyi,ɗago ido Halima tayi tana kallon Amma wanda a lokacin kuma tsab idonta ya koma fari ƙal da brown ɗinshi sai dai ƙallin hawaye dake kwance tab a idon ji tayi baƙinta yayi masifar nauyi ta kasa furta abunda ke ranta sai kawai ta tsinci kanta da cewa"Amma zazzaɓi nake kuma nasha Drugs".cike da al-ajabi Amma kebin idon Halima da kallo can dai tace"to Allah ya sawaƙe ki samu ki tashi ki watsa ruwa sai ko tea ne kishi sai ki ƙara shan maganin".da to kawai ta ansa kafin Amma ta fita taja mata ƙofar ɗakin.zumbur ta miƙe zaune,red haka eyes ball ɗinta yayi kamar wanda ya kawo danja kuma ya ɗauke glass cup ɗin data kallah ya faɗo daga table ya fashe a wurin.saurin runtse ido tayi kafin idonta ya dawo daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet ji tayi jikinta wasai kamar ba ita ta tashi tana ciwan kai ba,wanka tayi tayo alwala dan har lokacin batayi sallan asuba ba,da ƙyar tayi sallan wacce babu natsuwa a cikinta sannan ta saka riga da siket na atamfa kasa murxa komai tayi sai turaren data fesa ta ɗaura ɗan kwalinta ta faɗa kan bed take wani baccin ya kuma shureta wanda take yinshi cike da mafarkai iri iri mararsa daɗi.


ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
DAN GIRMAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING
[11/13, 23:34] Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*ABU BILAL!!!*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇

```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```

*_______________________
______________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


`Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans

Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.

FREE PAGES
PAGE 8

A hankali ta tura Gidan ta shiga babu kowa alamar kowa ya tafi masallaci yasa ta wuce ciki kai tsaye.kafin ta ƙarasa shiga Hajiya Mama ta shigo gidan Lamis na miye da ita tsayawa Halima tayi tanawa Hajiya Mama sannu da dawowa,da fara'arta ta ansa tana cewa "kai Alhmdllh jiki yayi kyau,Allah ya ƙara lafiya"da ameen Halima ta ansa tana mayar da kallonta ga Lamis daya ƙureta da muggan idamuwansa ko kibtawa baya yi,ƙasa tayi da kai tace"Yaya Lamis ina wuni".fuska ya saki yace"lafiya qlau tauraruwar mata,ya jikin naki?".da Alhmdllh ta ansa tana wucewa ciki ya bita da kallo.Harara Hajiya Mama ta jefa masa tace"kallon duk na uban menene?,wallahi Lamis ka kiyayeni kama ɗauke idonka daga kan Halima dan bama zan yarda da wannan ba".ajiyar zuciya ya sauke yace"to Mama akwai wata matsala ne dan naso Halima?,naga kuna shiri kuma zamanku lafiya"."rufemun baki ban yarda ba ban kuma amince ba,karma kasa wa kanka wannan alaƙan" ta ƙare maganar tana wucewa cikin.da kallo ya bita kafin ya bi bayanta yana murmushi.Lamis yaro ɗaya tilo ga Hajiya Mama duk duniya shine kawai take matuƙar so bata kuma iya cutarwa.Lamis irin maxan nan ne masu barƙwanci da son mutane ko kaɗan bashi da wani hali da zaka kushe.yana da matsakaicin kyau.har suka wuce part ɗin Hajiya Mama yana kallon Halima data fito daga kitchen ya daɗe rabon daya ganta saboda karatun daya fita ƙasar waje,duka kwanan shi biyu da dawowa kuma sai lokacin ya ganta.zama Hajiya Mama tayi tana kallon shi,saurin sunkuyar da kai yayi ya kasa cewa komai.taɓe bakinta tayi tace"ya Kawun naka".murmushi yayi yace"yana lafiya".miƙewa tayi tace" bara na kawo maka abinci".cikin cool voice ɗinsa yace"am not hungry".dawowa tayi ta zauna tace"kai ka sani ai".shiru bece mata komai ba kafin ya miƙe yace"bara na gaishe da Amma".taɓe baki tayi bata ce komai ba,daga haka ya fita ya shiga part ɗin Amma bakinsa ɗauke da sallama.Amma ce zaune da Faruq suna fira.da fara'a Amma ta ansa tace"lallai mutanan turai an sauka kenan,kai munyi ta barka karatu ya kammalu".da murmushi fuskarsa yace"barka da dare Amma,na sameku lafiya"."lafiya Alhmdllh "ta ansa kafin yaba Faruq hannu suka gaisa fuska sake."Ammi,Little maza kizo ki kawo wa Yayanki abinci duk da nasan always he's full".ɗan shafa kansa yayi yana murmushi yace"yau dai zanci abincin Ammana tau".fitowa Halima tayi ta wuce kitchen ta haɗo masa abinci a tray tazo ta duƙa har ƙasa ta ajiye tace"kuma duka zaka cinye".cikin alamun sun saba yace"daina kula ni,bayan ɗazu kin nuna kamar baki sanni bama,ko murnar dawowa na baki yi ba".zama tayi tana kama kunnenta tace"Allah nayi murna kawai dai ɗazu ima jin jikin duk sai a hankali ne".dungure mata kai Faruq yayi yace"what ever ai kinyi murna Yaya Lamis ya dawo".dariya suka saka duka Lamis yace"Allah ya ɗayyi ba Ummaruje abunda nake so ta fahimta kenan".tsuke fuska Faruq yayi yace"har gobe ba zaka daina ɓata mun suna ba Lamis".dariya kawai yayi yana safkowa dancin abincin da Halima ke zuba mashi.haka suka sha fira sai wurin 9pm ya tafi zuciyarsa cike da tunani kala kala.ko da yazo kwanciya fir bacci yaƙi zo masa babu abunda yake gani sai fuskar Halima da ganin bacci ba xai zo ba yasa ya tashi ya ɗauro alawala ya soma sallah...tun sassafe ta tashi ta soma shirin makaranta bata tsaya ɓata lokaci ba ta shirya cikin trouser ash colour sai riga iyakarta gwaiwanta mai tsaga daga 2sides ɗinta kalar milk sai ƙaramin himar sosai kayan suka mata kyau white socks ta saka da black toms ta saɓo ƙatuwan school back ɗinta itama black ta fito tana saka eyes glasses dinta tana Kuma kallon black watch ɗin dake daure a tsintsiyar hannunta,kai tsaye dining ta nufa in da ta samu ƴan gidan gaba ɗaya a zaune,side hug tayiwa Daddy dake zaune tace"Good morning sir",shafo kanta yayi yace"morning my little how is your body?".tace"alhmdllh" sannan ta juya ta gaishe da Hajiya Mama dake saka masu chips a plate,itama da fara'a ta ansa sanan ta gaishe da Amma da Yaya Faruq tana zama a chair ta kusa da Daddy,tea kawai tasha tana niyar miƙewa Daddy ya riƙeta yace"a'a little kici chips please yau na kawo maki tsaraban chocolate".ae ba shiri ta koma ta zauna tana ɗaukar fork tace"ai dole naci,dama Yaya Lamis yace yamun tsaraban Chocolate".ta ƙasan ido Hajiya Mama ke kallonta tana ayyana wani abu a zuciyarta.sauri sauri taci chips ɗin kafin ta miƙe da sauri tana duƙawa gaban Daddy ,ya gane nufinta dan haka ya ɗaura hannunsa a kanta yace"Allah yayi maki albarka ya kuma bada ilimi mai amfani".cikin jin daɗi ta ansa da "ameen ameen yh rabb"kafin tayi masu sallama tana cewa"Ammana kimun addu'a na tafi".ganin time be wuce ba yasa suka biya suka tafi da Khadija dan ita a napeep take tafiya school ɗinma Daddyne ya sakata saboda mahaifinta bamai ƙarfi bane.tunda suka shiga school ta fara jin yana yinta na canzawa kamar kanta zaiyi ciwo jin beyi ɗin ba yasa ta share ta soma harkokin gabanta har sukayi break tanajin ba daɗi,tana ta zaune akan seat Khadija ta kalleta tace"ki tashi muje muyi break".cikin rashin son yin magana tace"i'm full".kallonta khadija tayi tace"da kika ci mene zaki ce wani kin ƙoshi".tuni idanuwanta sun soma canza launi cikin ƙasa da murya tace"please leave me alone"saurin miƙewa Khadija tayi tsaye tana kallon yarda lokaci ɗaya idanuwan Halima da muryarta suka sauya.kiran da Uncle ɗinsu ya turo yana mata yasa ta fita tana tunanin meke faruwa haka da Halima.wani irin zumbur Halima ta miƙe tana jujjuya kai da gudu tayi hanyar waje ba tare da tasan in da ta dosa ba.da gudu Zahra tayi office ɗin Uncle walle danta gayawa Khadija.a hankali yake tafiya cike da natsuwa hannuwansa zube cikin aljihun wandon jeans dake jikinsa yana tsotsar lips ɗinsa kamar ya samu sweet fitowarsa kenan daga primary sections yazo ya siyawa Bilal textbooks . da ƙarfi ta bankesa tana niyar wucewa saurin riƙeta yayi ya fizgota da baya yace"ke baki gani ne".ganin fuskar Halima yasa ya waro idanuwa yace"again everywere you".dafe kai tayi da ƙarfin gaske ta kwarara wani uban ihu ta tafi zata faɗi , wani ƙaton stone ya gani wanda map ɗin school ɗinsu ke sama yasa yayi saurin tarbota ta faɗo jikinshi gudun kada ta faɗawa stone ɗin.a daidai lokacin kuma Khadija da sauran class mates ɗinsu da tearcher's suka ƙaraso wurin.dafe kai Uncle walle yayi yace"heee oh my God Halima,Halima".wani irin kuka Khadija ta saki ta duƙa tana girgixa Halima tana kiran sunanta.tsaki Abu bilal yaja dan ko kaɗan baya son hayaniya.xame jikinsa yayi daga nata ya miƙe xai tafi da sauri principal na secondry ya riƙesa yace"please your'e muslim help us and solve tha problem".taune lips ɗinsa yayi da ƙarfi kamar zai huda ya shafi gashin kanshi ya duƙa ya sunkuci Halima yace"i will take her home".ba yarda Khadija bata so ta bisu ba amma sam aka hana sai dai suka tafi da Uncle Walle.a motar Abu bilal suka tafi gidan sai da Uncle Walle ya nuna masa gidan kafin yayi horn gateman ya leko ganin besan motan ba yasa yace"daga ina?,wa ake nema?".wani siririn tsaki Abu bilal yaja kafin yace"ƴar mai gidan aka kawo".da sauri ya buɗe gate ɗin ,Shikam ya danna hancin motarsa ciki bai ƙarasa parking lot ba ya kashe motan ya fito baya ya zagayo ya ɗauko Halima wanda har lokacin take kwance tamkar gawa,kamar ya ɗauki baby haka ya rungumota ya nufi main entrance na gidan ya fara danna bell ɗin gidan.Amma dake kitchen tace"Aysha kije ki duba waye a ƙofa".da to Aysha ta ansa tana ajiye bowl ɗin hannunta ta fito zuwa ƙofan tana buɗewa ta zaro ido da ƙarfi tace"Yaya Halima".ae da gudu ta koma kitchen bakinta na rawa tace"Amma,Amma Yaya Halima come and see her".kallonta Amma keyi ganin taƙi natsuwa yasa Amma tace"bana son sakarci idan ba zaki natsu kiyi magana ba kije ki cire uniform ɗinki kixo ki wanke mun cavage ɗin nan".haɗiye yawu tayi da ƙyar tace"wallahi Amma Yaya ce aka kawo ".ajiye knife ɗin hannunta tayi ta fito parlon ta nufi ƙofa Aysha na biye da ita.wani irin sororo Amma ta tsaya tana kallon Abu bilal da ƙyar ta iya lalubo magana tace"subhanallah ku shigo".ciki Abu bilal ya shiga yana daura Halima akan ɗaya daga cikin royal chairs na parlon.tamkar gawa haka ya ajiyeta kafin ya kalli Amma yace"barka da gida"yana ɗan risinawa."barka me yake faruwa ne?".shiru Abu bilal yayi ya kasa cewa komai sai Uncle walle ya shigo ya mata bayani,ajiyar zuciya ta sauke tace"na gode ƙwarai,Allah yayi maka albarka".murmushinsa mai kyau yayi yace"ameen,ameen Allah ya bata lafiya ya faɗa yana fita daga parlon.sai da ya fita da uncle walle sannan ya wuce gida.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMENTS
SHARE
DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING
[11/13, 23:34] Jordan: 11
Jan hannun Halima Khadija tayi tace"ki wuce muje class,Allah yaji kanta yayi mata rahma lokacinta ne yayi".wasu zafafan hawaye ne ke kawowa a idon Halima tana Kuma tuna mafarkin da tayi a jiya,jiki ba ƙwari tabi bayan Khadija suka wuce class.duk yinin ranar haka ta wuni sukuku ko kaɗan bata jin daɗin jikinta.zaune take a parlo sanye take da riga da siket na shadda ɗinkin yayi matuƙar yi mata kyau ga ɗaurinta irin zahra buharin nan tayi eye glasses ɗinta data saka ya kuma masifar yi mata kyau.a hankali ya turo ƙofan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ya ƙaraso cikin parlon ,bowl ɗin naman dake hannunta ta ajiye tace"Yaya sannu da zuwa".shafa kansa yayi zuwa sajensa ya ƙwaiƙwayi muryanta yace"lafiya qlau Matar Yaya".langwaɓar da kai Halima tayi tace"ayyah Hamma Lamis ni sunan nan yana mun nauyi sosai".zama yayi daga ɗaya daga cikin chairs ɗin yace"owk soon zaki daina,to ke baki da saurayi ne?".dariya ta saki tana saka hannunta ta rufe fuskarta,ƙura mata ido yayi yana kallon zanan jan lallan daya ƙawata yatsunta yace"bana da ansa kenan?".Abu bilal ya faɗo mata a rai murmushi kawai tayi tace"am too young for that ae,kaifa kana da budurwa?".ɗage gira ɗaya sama yayi yace"akwai dai wacce nake so amma bata ma san ina sonta ba".zaro daradarn idanuwanta tayi da alamun mamaki tace"Yaya As in how?".shiru yayi can yace"forget about that"."yanzu Lamis ashe tun ɗazu ka shigo gidan ka barni ina fa faman jiranka?"Hajiya Mama ta faɗa.sosai kai yayi yana yin ƙasa da kai Halima tace"ai Hajiya ya kusa awa a wurin nan".waro ido yayi ya ɗauki pillow na chair ya jefa mata yace"halan na fara wasa da ke?".daidai nan kuma Faruq ya shigo da ido ya kafesu ya kasa cewa komai kawai gently ya wuce room ɗinsa ba tare daya tankawa kowa a parlon ba.miƙewa Lamis yayi yace"sorry hajiyata bazan kuma barinki kina jira ba,muje na ƙarɓi saƙon".girgiza kai Hajiya Mama tayi ta wuce part ɗinta."maxa tashi ki kaiwa Yayanki lunch ɗinsa".Amma ta faɗa .turo baki Halima tayi tace"Amma why not Aysha".riƙe da baki haka Amma tabi Halima da kallo tace"owk Ma ae bara mu zauna kawai kici gaba da bamu umarni".saurin miƙewa Halima tayi bata ce komai ba ta wuce kitchen ta haɗa komai a cikin tray ta ɗauko ta nufi ɗakin Faruq.knocking ta fara yi kafin yace"come in".da sallama ta shiga a bakinta ,kafin ta ɗago idanuwa tana kallonsa sanye yake cikin 3quater ash colour sai t-shirt black sosai yayi kyau sai fiyar da sanyayyan ƙamshi yakeyi,a daya daga 2 chair dake bedroom ɗin ya zauna yana crosing legs ɗinsa.ta ƙaraso ta janyo table ta ɗaura tray ɗin tace "Yaya your lunch".lumshe idanuwa yayi yana jin soyayyarta na kuma fizgarsa yace"meye tsakaninki da Lamis?".a bazata tambayar yazo mata turo baki tayi tana kallonsa kafin tace"nothing".kafeta yayi da idanuwa amma ya kasa cewa komai ganin ya soma latsa wayarsa yasa tayi ficewarta ya bita da kallo.a wurin Hajiya Mama kuwa Lamis ta tsare da ido tana cewa"Amma ina ga Muhammad tambayarka nayi ko?".ƙasa ya kuma yi da kansa yace"Hajiya nothing".wani uban harara ta jefa masa tace"wallahi kada ka kuskura naji wani abu tsakaninka da ita beside zama tare da ita ma i don't want it balle kuma wani relation ya shiga".ajiyar zuciya Lamis ya sauke yana jan gemunsa yace"i see nothing bad in it Hajiya".kamar Hajiya Mama zata fasa ihu a hassale tace"Muhammad get out".jim yaɗanyi kafin yace"kiyi hakuri "ya tashi yabar ɗakin.rarumar waya tayi tana dannawa Hajiya Talatu waya bugu ɗaya ta ɗauka kafin tace wani abu Hajiya Mama tace"ki ganemun yaron nan yana niyar janyo mun bala'in da yafi ƴarfina talatu".daga ɗayan ɓangaren Hajiya Talatu tace"what's wrong".cikin tsananin tashin hankali Hajiya Mama tace"Muhammad Lamis mana,ga dukkan alamu yana son yarinyar nan Halima,and everytime day and hour idan yazo yana maƙale da ita".Hajiya Talatu dake kwance ta miƙe da sauri tace"sam wannan ba mai yiwuwa bane,kin daisan abunda kenan,aike kika haifesa ki nuna masa bakya so ki rabasu ko ta ƙarfin tsiya mana".ajiyar zuciya Hajiya Mama ta saki tace"aini kaina ya ƙulle nama rasa abunyi Talatu"."dole kam asan abunyi in ba kina so ki rasa yaronki bane".sun tattauna sosai kafin sukayi sallama."wannan tsayuwan a kaina na menene kuma?".zamewa yayi ya zauna yace"ina Bilal?".shiru Aunty Aysha ta masa sunkuyar da kansa ƙasa yayi yace"kada ki gaya mun kin basu yarona"."idan an basu Bilal aiya cancanta yaje yaga ƴan uwansa ne,ni yanzu ba wannan ba gobe zakaje airport ka ɗauko Abban Khalifa at 9".ɗago kansa yayi yana kallon Bilal dake cewa "oyoyo Abu bilal"da gudu yaron ya rugo ya faɗa a cikin Abban nashi ya rungumesa da ƙarfi.shima Abu bilal ɗim rungume Bilal yayi a jikinsa sosai yana jin wani irin sanyi a ransa shafa kansa yayi kafin yace"Allah yayi maka albarka".murguɗa baki Halima tayi tace"ai dai muma an saka mana albarkan".ɗago kai yayi yana kallonta yana ƙisisifa irin rainin da tayi masa shi sai yanzu ma ya ganta danshi idonsa ya rufe Bilal kawai yake kallo.zama tayi kusa da Aunty Aysha tana cewa"to waishi kullun sai yazo gidan nan ne".dariya Aunty Aysha tayi tace"yaronsa yake zuwa gani Halima kinsan soyayyar uba da ɗa".zazzaro ido Halima tayi tace"ni dai kibar cewa Bilal yaronsa ne,ni nan nazo ki bani kayansa ne yamun kwana"."bazashi ba,he's going with me".miƙewa tayi tace"Allah bazai bika ba".ƙwafa yayi yace"da yake ke kika haifa mun shi"."ya isa haka,ba rigima nace kuyi ba ni na rasa meke shiga kanku abarmun Bilal ban fara talla dashi ba".langwaɓar da kai Abu bilal yayi yace"even weekend's bazai mun ba?"."eh bazai je ba".cup ɗin dake kusa dashi ya ɗauka ya jefa mata da ƙarfi Allah yaso silver cup ne.kallon cup ɗin kawai tayi ya canza direction da idonta dake blinking da red colour,kallo ɗaya ya mata a lokacin ya gane ba ita bace hakan yasa yaja sirirn tsaki ya miƙe yana jan hannun Bilal,carab tayi da hannun shi tace"no".da kallon Mamaki Karima ta bisu tana kallon yarda Halima ta tare Abu bilal wanda tun shigowarta gidan take kallon yarda take masa,karasowa wurin Karima tayi tace"yau naji ikon Allah,mutun da ɗansa amma ki hanasa fita dashi?,a ƙauyenku haka ake yi?".ƙoƙarin juyowa Halima keyi ta kalli Karima .cikin cool voice yace"Haleemah".tun daga maɗigar kanta har zuwa tafin kafarta sai da taji kiran sunan for the firt time daya fara kiran sunanta ji tayi kamar babu wanda ya iya kiran sunanta sai shi duk da bata cikin hayyacin amma sai da taji kiran har ranta,shikam yayi hakan ne gudun kada ta kalli fuskar Karima.tsura masa idanuwa tayi .shikam cikin sanyin murya yace"ke kibar wajen nan kafin na ɓallaki da gulma".wasu hawaye ne suka kawo idon Karima tayi ɗakin Aunty Aysha.sakin hanun Bilal yayi be kuma cewa komai ba ya raɓa ta gefanta ya wuce.riƙe hannun Bilal tayi da kyau kafin ta dawo ta zauna a hannunta Bilal yayi bacci kafin da ƙyar Aunty Aysha ta mayar da ita gida lokacin har an gama sallan isha'i.sai lokacin Aunty Aysha ta samu damar shiga ɗakin da Karima take har lokacin kuka ta samu tana yi muryarta harta disashe.cike da tausayawa ta zauna gefanta tare da kama hannuwanta ta juyo da ita tana fuskantar ta tace"alamu sun nuna kishi ƙarara a tattare da ke Karima,na daɗe ina karantarki akan Sudais sai dai ban gazgata ba sai yau".ƙasa Karima tayi da kai tana goge hawayen dake kawowa idonta cikin dishewan murya tace"nima bansan ya akayi hakan ta faru da ni ba Aunty,nima tsintar kaina nayi a haka,na kasa cireshi a raina".cike da tausayawa Aunty Aysha ta kalleta tace"nasan kinsan waye Aliyu da halinsa kuma,bazan iya cewa komai ba sai dai in ce ki dage da addu'a hakan shine kaɗai mafita insha Allah komai zai zo da sauƙi idan da rai da rabo sai kiga Allah yayi nasa ikon akanku".babu laifi hankalinta yaɗan kwanta da maganganun Aunty Aysha sosai ta lallasheta kafin sukaji sallaman Jagwaɗo yazo tafiya da ita gida.a haka ta bisa suka koma gida,da sallama bakinta ta shiga gidan da sauri Dattiya ya ɓoye kwanon kifin dake gabansa cikin babbar riga yana raba idanu yace"ni dai banji daɗi ba,ace a gidanka ma baka da sirri kome kake yi sai kawai kaji an shigo ba enscuse(excuse),to ni dai ba komai nake ci ba,ahtau yo ba komai nake ci ba bare kuma a ƙwalalo maka ido ɗan abunda zaka saka a bakin salati ya gagareka a gidanka"."kai dai bakaji daɗi ba wallahi Dattiya ina kaga bakin salatin?,ko kuma bakin shiga abunda babu ruwanka ba,wai ƴarka ta cikinka ita kake wa rowar kifi".wani salati Dattiya ya saki hawaye ya kawowa idonsa yace"amma Uwani kin cuceni,meye wani kifi?,me akayi akayi wani kifi,yanzu Karimen kike cewa ina wa rowa,Allah ne kaɗai zai shiga tsakanina da ke gaskiya,ko in haɗa kayana in bar maki gidan ko na huta da baƙin cikin da kike so ya kashe ni".Dariya sosai Jagwado ya saki yace"aiko Kawu zan baka wurin kwana ma".tsuke baki Dattiya yayi yace"kai tafi can mai cin haram,duk wannan jikin naka ai kayan Allah ya isa ka tara".dariya Jagwado ya kuma saki yayi hanyar waje abunshi.

ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment